Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara jikinta ta shirya sosai,,,,, abinda aka samu suma aka shirya su,,,,,, sannan aka fito da raihana dan kaita ɗakin hutu,,,,,

da hafsat da zainab da momy da amina, sai murna suke wai yaya yayi twince yara masu kyau dukansu maza ne, sai farin ciki suke,,,,,,,

Momy ce tace hafsat taje ta faɗawa umma an aihu,, tanata kiran wayarta bata zuwa,,,, Amina tace Aunty hafsat ki tafi dani in riƙe ɗauka maki jariran ta gansu,,,,, momy tace aike mahaukaciya ce, a ina kika taɓa gani?"",, tace momy wai dan ta gani da idon, tsaki momy tayi ita kuma hafsat ta fita,,,,,

faruk kuma tun farlo yake kiran aciciya shiru,, ɗakinta ya shiga bata nan, ya duba toilet bai ganta ba,,, har zai fita yaji wayarta na ringing,,,, juyawa yayi ya kalli inda wayarta take,,,,,, sannan ya juya yabar ɗakin bai ɗauki wayar ba,,,,,

ɗakinshi yaje bai sameta ba, duk inda yasan zai ganta bai gani ba,,,,, yacw to ina aciciya ta tafi ne?""",,,,, wayrshi dake ringing ya zaro daga aljihu,,,, ganin zainab ne yayi tsaki, bai ɗauka ba,,,

kiran wayar ya sake shigowa,,, tsaki yayi sannan ya ɗauka da cewa miye?"",, zainab tace yaya albishirinka?""" tsaki yayi sannan yace idan zakiyi magana kiyi bana san albishir,,,,, murmushi zainab tayi sannan tace nidai albishirinka,,,,,,

yace naji,,,, tace sai ka fara bani goron albishir sannan,,, yace faɗa man abinda kike,,,,, zainab cikin zalama da haɗama tace miliyan ɗaya, murmushi faruk yayi sannan yace na baki, zainab cikin ihu da hauka tace matar ta haihu yara biyu maza,,,,, dariya faruk yayi sannan yace Allah ya raya, na ƙara maki miliyan huɗu,,, ihu zainab tayi sannan tace muna asibitiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii

ta kashe wayar,,,, faruk kuwa ɗakinshi ya shiga yayo alwalla yayi sallah don nuna godiya a wurin Allah, daya sauki matarshi lafiya ya kuma azurtashi da zuria, sannan yayi addu,a Allah ya shirya su ya albarkaci rayuwarsu,, ameen,

yana gamawa ya miƙe cikin farin ciki yayi ma asibiti tsinke,, ita kuma lokaci da hafsat taje gdan umma ta sanar mata aihuwa umma taji daɗi, sannan tace su bari aje a faɗawa gwaggo sai su tafi tare,,, hafsa tace to, lokacin da umma taje ta faɗawa gwaggo da farin cikin, amma a gwalshe gwaggo ta taɓe baki tare da cewa Allah raya,,, daga nan bata sake magana ba, umma tace to kuje asibitin gwaggo tace ban zuwa sai gobe, umma tace Allah ya kaimu,,,, daga nan bata sake magana ba, tayi tafiyarta,,,,

bayan ta dawo tace ma hafsa taje ashe ma gwaggon taje kauye,,,, hafsat tace ba damuwa,tayi tafiyarta,

Faruk kuwa yana zuwa asibiti,,,, cikin murna "yan uwanshi duk suka rungumeshi suna mashi murna,,,, bakin nan nashi yaƙi rufuwa, niko nace wayaga angon jego?""",,,,,,

bayan sun gaisa da momy ne,,, zainab sai rawar jiki take ta ɗauko jariran ta miƙa mashi,,,, ya ansa tare da bisimillah,,,,, ya riƙesu, yana kallo,,,,,, bayan ya kallesu ya fara masu addu"a,,,,, bayan ya gama, yacewa zainab ta ɗaukesu,,,,,

bayan zainab ta ɗauki ɗaya amina ta ɗauki ɗaya,,,, ya matsa inda raihana take kwance , tsaye yayi yana kallonta, murmushi yayi sannan yace ke aciciya bakya cewa aihuwa zakiyi?""", turo baki raihana tayi tare da ɗaure fuska batayi magana ba, dariya faruk yayi sannan yace Allah ya baki haƙuri, a daidai lokacin daya matsa kusa da ita daf ya ɗan duka sannan ya taɓa cikinta tare da cewa kinfayi ƙoƙari sannu,,,,,, harararshi raihana tayi shi kuma dariya yayi sannan ya nuna inda zainab da amina suke riƙe da yaran yace da "ya"yanki kike,,,,, yanda yayi abunne yaba raihana dariya,,,, shima dariya yayi sannan yace sannu,,,,,,, raihana tace yawwa, faruk yace gida zamu tafi gaskiya bana san asibiti,,,,

Faruk yasa aka sallamesu bayan likita yayi gwaje gwaje, dan tabbatar da lafiyar jarirai da kuma mai aihuwa,,, haka suka rantafa sukayi gida,,,,, umma kuma yayarta zata zauna da raihana wato maman kabir,,,,,

daren yau dai faruk yana wurin raihana da yara,,,, saidai ya ɗauki wannan ya ajiye ya ɗauki wancan,,,,, raihana tace sai ɗaukar yara kake ni baka ɗauka na,,,, dariya yayi sannan yace aike yanxun na yayeki,,,,, raihana tace to kaima na yayeka,,,, yace ƙaryane,,,,,, baki yaye ne ba,,,, dariya tayi, bata sake magana ba,,,,,

****

*K*ai kuxo kuga shagali a gidan soja,,,,, gaba ɗaya gidan ya cika da mutane su farida zulaihat ƙawayen raihana kakafff babu wanda aka rage,,, gwaggo da tawagarta sunxo,,,,, ƙannen faruk da bataliyar danginsu dan familynsu babba ne, dangin umma da duk mutanen arxiki, kai har badiyya saida taxo, wato wanda tayi ma raihana wulaƙanci kada ta auri mijinta,,,,,

Gidan cike yake dan gabatar da taron suna,,,,, yara kuma sunci sunan dadyn faruk ɗaya kuma baban raihana, wato ɗaya Ibrahim ɗaya Ahmad,,, sunyi masu laƙani, baban faruk Ahmad shine *Khairillah* ,,,,,,,baban raihana kuwa Ibrahim shine *Abulkairi*

haka akaci taron suna aka gama lafiya, duk wanda yaxo suna a gidan faruk ya samu flasmer tv, shine abinda raihana ta raba na tukuciii,,, haka aka gama suna lafiya kowa ya kama gabanshi tare da masu addu,ar Allah ya shirya kairillah da abulkhairi,

haka rayuwa taci gaba da tafiya, bayan suna faruk ya tafi yaci gaba da harkokin gabanshi,,,,, raihana kuwa tana samun kulawa sosai dan momy da ƙannen faruk wata irin kauna suke mata sosai,,,,, zainab kuma ta koma gidan mijinta, suna can zamansu lafiya abunsu kowa da kowa,,,,,

itama yayar umma da raihana ta gama wanka ta tashi tafiya,,,, lallai ta sheda cewa faruk ɗa ne,,,, danshi kwata kwata abun duniya baya gabanshi,,,,,,

Itama farida ta aihuwa, kuma raihana taje dan har yanxun faruk baya nan kuma duk da baya nan baisa raihana ta daina zuwa wani wuri idan abu ya faru ba,,,,, amma fitar ta bada tsaroce,,,,

dan idan taje wuri ko acan zata kwana driver baya tafiya sai ta gama abinda take zai ɗauketa ya mayar da ita gida,,,,, dan wannan saƙo ne daga OGA,,,,,,,,

****

*K*wanci tashi asarar mai rai, yau da gobe sai Allah kwanaki na tafiya takon rayuwa yana canjawa, kwanakinmu suna ƙarewa,,,,,,,

Umma tayo ma raihana waya taje ta gano umma sa"a bata lafiya,,, raihana tace to, sai gobe insha Allah dan yau mai gda zai dawo daga tafiya,,, umma tace Allah ya maidoshi lafiya,,, tace ameen,,,,,

khairillah dake kusa da raihana sai gwaranci yake ,,,, raihana tace anƙi a baka wayar kai kowa ana waya dashi sai kawani zo kayi ta yanyanayannn ,,,, dariya yayi, danshi a ganin shi wasa ne, ita kuma tsaki tayi sannan tabar farlo,

Da rairafe suka bi bayan raihana suna kuka,,,,, tace to ku taho muyi bacci tunda baban naku bai dawowa ba har yanxun,,,, ɗauko su tayi ta shige ɗaki dan bacci take ji,,,,,,

suna shiga gado suka haye saida sukayi bacci sannan ta ɗauko memo tayi rubutu a jiki, idan kazo kada ka tasheni tunda na jiraka baka dawo da wuri ba, sannu da zuwa, kuma kada kaci abinci lipton kaɗai zakasha ka kwanta bacci,,,,,

tana gama rubutawa ta kwanta ta riƙe takardar a hannunta,,,, bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauketa,, shi kuma lokacin daya dawo bayan ya shigo yaga saƙon raihana, dariya yayi sannan ya zaro takardar ya rubuta, saina tasheki kuma saina ci abinci bazansha lipton ba,,, bari inyi wanka,,,,

yana gamawa ya mayar mata da takardar a cikin hannunta,,,, ya fita,,,, saida yaje yayi wanka,,, alwallah yayi saidai ya gama sallahr shi yayi karatun alkur"an sannan yayi addu"a, ya fita daga ɗakin,, ɗakin raihana ya shiga,,,,, yana zuwa a bakin gadon ya tsaya sannan ya riƙe ƙafafuwanta ya jawota,,,, da sauri ta buɗe idonta, murmushi yayi sannan yace taso na dawo,,,,,

raihana tace baka ga saƙona ba ne?""" yace kema baki ga nawa ba?""",,,,, dubawa tayi , da sauri ta sauko daga saman gadon tace waye yace kaci abincin tana riƙe da takardar a hannunta tana nunawa ba nace kada kaci ba, dariya yayi sannan ya riƙe hannunta yajata suka bar ɗakin,,,,,,

a farlo yace sai ihu kike yara suce ga mama da baba suna hayani , muje ɗakina kada suce mun hanasu bacci,,,,, tace anƙi aje ɗakin naka, waye yace kaci abinci?"" yace muje ɗakin saiki tambayeni,,,,, dariya tayi sannan ta bashi hannu suka kashe,,,,, shi kuma gira ɗaya ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya, tana kashewa dashi bai saki hannun ba, ya riƙe suka shige ɗaki,,, nidai a bakin ƙofa na tsaya dan karatun ya girmi tunanina,,,,,,, meelat

***
*S*aida faruk ya dawo sallah , ita kuma raihana tana ɗakinta, shima yana dawowa, ɗakinta ya shiga, suka gaisa, yace ke tada yaran nan suma ,,,, raihana tace gaskiya kada ka tashesu, yace sai an tashesu,,,,, ya fara jijjjiga yaran,,, raihana tace to idan har suka tashi saida ka goya su,,, dariya faruk yayi sannan yace O aciciya kinfi sansu dani ko?""",,,, dariya tayi sannan tace kaidai ka sani,,,,, yace kema kin sani,,,,, zama yayi yaci gaba da zaulayarta, yana hayaƙata,,, tayi shiru ,,,saida yaga ta ƙufalu sannan yace tunda kin cika bara mutum ya tashi kafin ki fashe,,,,,, yana maganar yana dariya,,,,,

Har zai fita raihana tace mashi, anjima zanje unguwa,,,, yace ina zaki ?"" tacw umma sa,a bata lafiya, yace Alah yasa a dawo lafiya,,,, tace amin amma tare dakai,,,, yace wallahi yau ina da meeting, tace idan ka gama sai muje,,,, yace kai ba lokaci gaskiya, tace kayishi,,,,, juyowa yayi ya kalleta sannan yayi murmushi, yace tunda kin matsa wurin 12: saimu fita, tace to Allah ya kaimu,,,,, yace amin, ya fice daga ɗakin,

Ita kuma pampers ta cire ma yara ta canja masu wata,, sannan suka lulluɓe a bargo, dan bacci,,,,, faruk kuma yana ɗaki jin raihana bata zo, yasa ya taso ya taho ɗakin,,,,,, yana zuwa ya hangosu a bargo sun lulluɓe,, murmushi yayi sannan ya shigo, yana zuwa bargon ya kware,,

raihana tace wai miye??""" yace ke nifa ban gane ba, anyi gabas da kare, dariya raihana tyi sannan tace miye??""" yace idan kina man ware ware, Allah yaran nan rabasu zanyi da gidan nan,,,,, raihana tace ina zaka kaisu?""" yace wurin momy, ke dan kin haihu shikenan sai ki daina so na?"",,,,,

na dawo daga tafiya raihana ina buƙatar kulawa, amma sai kixo ki tisa yara gaba miye haka?"" ya ƙarasa maganar ne cikin sigar a tausaya mashi,,,, raihana tace yi haƙuri,,, yace sai a bani haƙuri ayi ta cutata ?"" tace yi haƙuri kaine idan naje dasu sai kace suna hanaka bacci,,, ɗaya ya ɗauka yace ɗauko shi muje,,,,, tace ina zamu ?"" yace wurin lami za,a kaisu,,,, tace to, badan ranta yaso ba ta ɗauka tabi bayanshi,,,,

yaran sai kuke suke, suna fotawa farlo faruk yace kuyi ma mutane shiru, yan rainin hankali kune kadai kuke da mamar ne?"" tsaki yayi yaci gaba da tafiya raihana tabi bayanshi,,,, saida suka kaisu wurin mai kula dasu , sannan yaja matarshi sukai ciki,,,,

Aha, faruk ne ya fito daga ɗakinshi cikin shiga mai kyau da kama hankali, kyanshi ya ƙara fitowa sosai, idan ka kalleshi so ɗaya zakayi fatan ka ƙara kalonshi, dan mai kyau da kyau yake,,,,,

Ɗakin raihana ya nufa,,,, ita gaban madubi tana sa ɗankune, ansa yayi yasa mata, kwallin hannunta ya ansa wai zai shafa mata, ido ta zaro sannan tace wallahi bazaka shafa man ka cake man ido ba,,, dariya yayi sannan yace aiko da kin rasa mai maki jagora,,, itama dariya tayi sannan tace gaka,,,, dariya yayi sosai sannan yace wallahi kuwa nine zan ɗaukeki in goyaki a bayana , bama hannunki zan kama ba,,,,,, agogon hannunshi ya kalla sannan yace,,,,, muje ,,,, yayi gaba tace dawo,,,,

komawa yayi kusa da ita sannan yace gani ,,, tace to ɗauki ɗaya in ɗauki ɗaya,,, dariya yayi sannan yace ke ko kunya bakiji kiyi tasani aiki kamar mijin tace ,,,,, raihana tace aiso nake ka koma mijin kan tace,,,,, dariya faruk yayi sosai sannan yaje ya ɗauki yaran dukansu yana cewa ɗauko min wayata,,,,,,

wayarta ta ɗauka da jakarya sannan tabi bayanshi,,,, lokacin data fita harya shiga mota,,, tana zuwa itama ta shige , ya rungume ɗaya a gabanshi itama ta rungume ɗaya,,, yaja suka bar gidan,,,,

a ƙofar gidansu umma sa,a kabir ne tsaye da kabir k"b, wanda yaso raihana, faruk yana yin farkin raihana ta miƙa mashi yaron tana cewa bara in zagayo,,,,,,,,,,,,,,,

Kafin ta zagayo shi kuma ya buɗe motar ƙafarshi bata sauka ba, tana saman motar amma ya ɗorata saman marfin motar,,,, k"b na gani faruk zai ruga faruk yace zo nan,,,,,,,, adaidai lokacin da raihana ta zagayo,,, shi kuma k,b a daidai lokacin ya iso wurin,,,, yana cewa ranka ya daɗe,

raihana ta kalli faruk amma ta kasa magana dan ita so take taji ina yasanta k,b ganin babu wasa fuskarshi yasa raihana bata tsaya ɗaukar yaro ko ɗaya ba, tayi cikin gidan,,,,,,,, kabir ne yabi bayanta yana gaisheta,,,, raihana ta ɗaure fuska tace ya akayi ne?""" yace dama cewa zanyi bata nan,,,, raihana tace ance bata lafiya,,,, yace ta samu sauƙi , ina taje?""" yace sunje unguwa ne,,,, raihana tace ga gaisheta idan ta dawo yace zataji Allah ya tsare raihana tace amin,

fitowa tayi ya biyo bayanta,,,, faruk ganin raihana ta fito yace ya akayi ne?"" tace basu nan,,,, yace to muje,,,, kabir yace Allah ya tsare ranka ya daɗe, faruk baiyi magana ba,,,,, raihana tace wayyo ɗan umma sa,a ne fa,,,, yace to sannu yace yawwa, faruk yayi masa ɗan alheri, raihana ta shige suka tafi,,,,,,,,

suna tafiya raihana tace ina kasan wanda ya tsaya wurin motarka?""" faruk yace saurayinki ne ko?"" tace waye ya faɗa maka?"" dariya faruk yayi sannan yace uwarshi naci ai, lokacin muna abuja kullum sai yaje yayi rashin kunya wa umma,,,,,,, inajin labari nasa aka nannaɗo man banza, saida yaci uwarshi sosai, dariya raihana tayi tace shege da yanxun an yayi ban cuta,,,, faruk yayi dariya yace dana kashe shi kuma, itama dariya, tayi khairillah da abulkhairi duk suna dariya, faruk yace keji yaran nan ,,,,,,, raihana tace murna suke taya meelat musa Allah yasa ta kammala labarin zawarci lafiya,,, faruk yace, nima na tayata murna, kuma masu karatu an tayaku,,,, faruk ya leko daga cikin mota, sannan yace meeeelatttt vyeeeeeeeeeeeeeeeee

yaja motarsu suka ƙara gudu dan tafiya gida,

Alhamdulillah Allah nagode maka da kabani ikon kammala wannan littafi nawa mai suna *ZAWARCI* ya Allah ina godiya a gareka daka bani ikon kammalashi lafiya, inda nayi kuskure Allah ka yafe mana baki ɗayanmu dani da masu karatu,,, Allah kuma yasa wannan littafin ya zama darasi ga mataye da suke zaune a gidan aurensu,,,,,

ubangiji ya zaunar damu lafiya dukanmu baki ɗaya,, Allah ya ƙara mana soyayya da ƙauna tsakaninmu da mazajenmu, ameen,,

Saƙonki yaxo a gareni, haƙiƙa meelat ba suna bane,,,,,, ainahin suna na jameela,,,, gari na kuma aikema kinsan katsina ta dikko ɗakin ƙara kunya garemu badai tsoro ba, 🤓,,,,

*JAMEELA MUSA*

Mu gama da littafina , *WANDA BAIJI BARI BA*

Masoyana ku biyo ni mu faɗa cikin labarin 👇🏼


*RASHIN RABO*

hmmm labarine mai ɗauke da al,ajabi , tausayi, rashin godiyar Allah,,, da baƙin ciki,,, ku lallaɓo mu tsunduma danjin labarin,,,,, sakaci akayi daga baya kuma aka tattakura aka jibga uban *RASHIN RABO* karki bari, ko ka bari a baka labari,,,,

*RASHIN RABO*

tare dani meelat musa,,,,,,



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment