Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gama fitowa da kayan duka sannan daga ƙasa taga takarda , da sauri ta jawota, ta buɗe, kuɗi ne ciki 5k, a jikin takardar kuma anyi rubutu kamar haka,


```Assalam ƙawata da farko dai ina godiya sosai dan banma san da bakin da zan gode maki ba, naxo gdanku a rufe , naxo maki bankwana ne, munyi tafiya saudiyya, wannan saƙon kuma mai gda yace a baki, kuma shima yana godiya sosai, insha Allah zan maki addu"a sosai kema Allah ya baki miji na gari, daga mai ƙaunar aminiyarki farida ahmad```

Hawaye ya gangaro daga idon raihana tace Allah sarki rayuwa, wallahi naji maki daɗi Allah ya ƙara ma duk macen duniya haƙuri da juriya a gidan mijinta, dan idan kayi haƙuri a gidan aurenka shidai aure ibada ne, idan kuma mutum ya zalinci wani Allah dai shine mai sakayya,

Goge hawayenta tayi sannan ta maida kayan a leda tace bara inje inkai ma umma baiwar Allah kila ma har yanxun bata ci komai ba,

Bayan ta gama maidai kayan kaff ta ɗauki ledar ta nufi shagon shamsu ta bashi kuɗinshi data ranta, ta amso kayanta , bakin titi ta nufa dan hawan abin hawa wai tunda ta samu kuɗi bara ta more su tunda idan suka tafi tana shan wahala kafin ta samu,

Abin hawa ta hau tayi ma gidansu ummarta tsinke, lokacin data isa ta samu umma ita kuma tana fitowa daga cikin gida a ƙofar gida suka haɗu,

Umma tace lafiya kika dawo?"" dariya raihana tayi sannan tace lafiya fess umma, kusa da ita umma ta matsa, wuri raihana ta samu ta zauna itama umma zaman tayi, kallon raihana tayi sannan tace gwaggon ƙoroki tayi ne?""

raihana tace a,aa abun arxiki na samu, tana magana tana fiddo kayan tana miƙa ma umma, umma sai yashe baki take tana cewa waye kuma ya baki?"" jikin raihana yana ƙarma ta fiddo wayar ta miƙa mata , tace umma kalli harda waya, umma tace ni sai nuna man kaya kike faɗa man wanda ya baki, dariya raihana tayi sannan tace kamar lefe ko umma?"" dariya umma tayi sannan tace gaskiya ke yanxun yanda kike zawarcin nan kika samu kamar wannan ai kinyi goshi, dariya sukai gaba ɗayansu sannan raihana tace wallahi farida ta bani,

umma tace farida taki?"" raihana tace farida tawa kau, kinga kuɗi nan, saboda haka muje mu kama haya umma kema kibar wannan gidan don Allah, hannu umma ta miƙa ta karɓi kuɗin sannan tace itama tana da 1k saboda haka akwai wani gda nan kusa da gidan gwaggo sai muje mu kama ko?"" raihana tace wannan gaskiya ne,

haka dai sukayi ta firarsu cikin tausayi da kuma hali na damuwa, bayan wani lokaci raihana tayi ma umma sai anjima, umma tace zata shigo idan Allah ya kaimu zata shigo dan suje su biya kuɗin hayar, raihana tace to sukai ban kwana umma ta shige gida raihana ta nufo gdan gwaggo,

a ƙofar gida raihana tayi zaune har yanxun gwaggo bata dawo ba, tana nan zamanta tana jiran zuwanta, tun daga nesa ta hango zulaiha ta tun karo wurinta sai yage baki take kamar ƙefen sakara, tana tafiya kamar ana ingixo ta,

da ɗan gudu ta iso tana zuwa takai ma raihana duka , tace banza albishirin ki?"" kallonta raihana tayi sannan tace miye, zulaiha tace naje gidansu umma tace man yanxun nan kika taho, kinsan abinda ya faru?"" raihana tace ah ah sai kin faɗa,

Zulaiha tace an saki kishiyata, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un raihana tayi tare da zaro idanuwa cikin tashin hankali taci gaba da salati, tana cewa kam amma na tausaya mata wallahi,

zulaiha tace ke bar "yar iska, raihana tace haba kiji tsoron Allah kinyi *zawarcin* nan kinji yanda yake kinsan wahalar da take cikin shi da yamutsi sai kiyi murna dan an saki wata?""

Zulaiha tace wallahi nayi, raihana tace duk miye yayi zafi haka?"" zama tayi kusa da raihana sannan ta fara cewa,

ke tunda kika bani shawarar in mayar mashi da yaran shi na maida su, tace ita Allah ya kasheta bata zama da su, yace tayi haƙuri tace wallahi bata zama da wa"an nan tsinanin "ya"ya dan ita ba ɓautarsu taxo ba, idan ya zama dole sai sun zauna saidai ya dawo da uwarsu,

yace mata shi bazai maidoni ba, tace to wallahi bata zama dasu , saidai ta tafi gidan ubanta itama, haka dai sukayi ta tashin hankali idan ta dafa abinci bata basu da sunyi abu sai zagi sai duka, idan yace mata yaro saida lallashi sai tace ba yara bane iskanci ne sunsan abinda suke,

wannan saɓanin ne dai yasa har aka rabu, raihana ta sake salati tace lallai amma tayi hauka , matsalarmu mu mata wani lokaci bamu da lissafi, in banda hauka ka nuna ma namiji baka san yaranshi?""

kama so su wace Allah cika?""" kuma idan ta girka abinci ta basu ina zata ragu?"" ai duk macen da bata san yaranka kaine bata kauna, yanxun kinga ita wanna haukan yaja mata sanadin mutuwar aure?""

keda kika raɓa kici arxiki?"" kuma da nata ne yaran idan taso tazo dasu *agolanci* idan yace baya rigewa sai kiga kuma ta nuna damuwa, don Allah mata mu riƙa haƙuri da "ya"yan miji duk abinda zakai kayi tsakaninka da Allah komai kayi Allah yana kallonka baka da tabbas kai zaka rayu da naka idannka ci zalin na wani, idan babu rabuwa akwai mutuwa , duk abinda kayi a rubuce yake baya canjawa dole wani abun sai mu riƙa danne zuciyarmu dan sama ma kanmu salama, Allah yasa mu dace ameen,

raihana ta kalli zulaiha da take ta faman rawa, girgiza kanta tayi sanann tace ai dama haka duniya take sai wani ya rasa wani yake samu, amma ita dai wannan rashin haƙuri yaja mata,

zulaiha tace ke banza ranar juma"a za"a ɗaura mana aure ,idan na shirya sai in tare haka yace, raihana ta kalleta tace in baki shawara?"" zulaiha tace bani aike baki bada shawarar banza, murmushi raihana tayi sannan tace kada ki yanda sai wani lokack ki tare ana ɗaura aure a ranar ki rufa ma kanki asiri kiyi gidan mijin ki,

sannan kin ɗanɗana kinji abinda yake cikin *zawarci* yanzun saidai kiyi ma wasu nasiha, idan kin koma kuma kici gaba da haukan da kikai a baya, zulaiha dariya tayi sannan tace haba ai ɗan ba ƙari godiya da kwanan garke, idan na koma kinsan abinda zanci da safe?"" raihana tace a,aa zulaiha tace wallahi shayi zansha da wainar kwai, wata irin munafikar dariya raihana tayi sannan tace shegiya shi kike yunwa ne?"" zulaiha ta ɗaure fuska tace kema matsalarki iskanci wallahi raihana tace Allah ya baki haƙuri,

zulaiha taci gaba da cewa wallahi rabon da insha shayi kinsan Allah ba wasa ba har mantuwa ta manta, kai ai idan naje akwai abubuwan da zanma yaushe rabo, tsaki tayi sannan taci gaba da cewa bira"uba babu a gida babu a maƙota,

Gaskiya raihana *zawarci* baiyi ba, kema Allah ya baki naki kije kindan raɓa, murmushi raihana tayi cikin sigar tausayi sannan tace aini kila ma ban sake aure, zulaiha tace saboda mi?"" raihana tace to ai har yanxun ma na rasa wanda zaice yana so na, bare azo maganar aure , ni wallahi gani nake kamar hada alhakin Aminu, na samu yana kauna na, da nayi haƙuri nayi zamana duk da abun baikai haka ba,

zulaiha tace ba komai Allah yana tare da mai haƙuri duk abinda yayi tsanani sauƙi yana nan tafe, kiyi haƙuri wata rana sai labari,

raihana tace Allah ya nuna man ranar nan in ganni a gidan mijina ɗakina ni ɗaya inci abinda nake so inyi wanka da sabulu, danni tuni na koma wanka da omo dan yafi auki idan na siyo na 20 sai yayi man sati ina ɗan lallaɓawa, mai ma man gyaɗa nake amfani dashi idan na siyi na 100 yaman wata ukku,

zulaiha tace Allah dai yasa mu dace, idan kana zaman tun kana burge iyayenka har ka fita a ransu, miƙewa tayi tace bari in tafi dare ya gabato don Allah ki shigo gobe sai muga abinda ya kamata muyi, dan yau idan yaxo zan faɗa mashi ranar da aka ɗaura aure a ranar zan tare, raihana tace haka yayi , tare suka miƙe da raihana da zulaiha , zulaiha ta dafa kafaɗar raihana tace kinsan fa yaga canji dan yanxun idan yaman abu godiya nake sosai kamar wata "yar maula, kinsan namiji yana san yayi maki abu kina godewa tare da mashi addu"ar Allah ya ƙaro mashi buɗi daɗi suke ji har a ransu wallahi, raihana tace to ai duk abinda kasan zai fishshe ka sai kayi dan zaman lafiya, haka suka ci gaba da "yar tafiya saida tayi mata rakiya sosai sannan ta dawo ta zauna ƙofar gida tana jiran dawowar gwaggo,

ta ɗaɗe sosai dan har an gama sallar magrib sannan ga gwaggo ta ɓullo, raihana tayi mata sannu da zuwa sannan gwaggo ta amsa, makullin ta bata tace ta buɗe masu ƙofa yau akwai labari, raihana tace labarin mi?"" gwaggo tace kedai buɗe gida mu shiga kiji ikon Allah, raihana tace to, da sauri tayi ta buɗe gida suka shiga,

suna shiga rainaha tayi alwallah dan gabatar da sallah magrib , bayan ta gama sallah gwaggo tace , ashe ɗiyar ladi sata take ma mijinta?"" idanjwa raihana ta zaro tace wace ladin kuma?"" gwaggo tace wace kika sani?"" raihana tace ai ladi da yawa, gwaggo tace ladi aminiyata, tana nan gida mijin ya maidota, amma auren bai mutu,

tsaki raihana tayi sannan tace su suka sani, in banda hauka da taɓewa mi yakaika yima miji sata?"" ai yima namiji sata ba ƙaramar lalacewa yake sa mace tayi ba, kuma ko ba komai idan ka fita da tambarin sata wane namiji zai aure ka?"" tsaki tayi sannan tace Allah dai ya rufa asiri, gwaggo tace ameen,

miƙewa raihana tayi taje ta sako alwallah , tana tunanin irin halin gwaggo wato ɗiyar aminiyarta wanda take auren mijin daya saki raihana, tace umm kada ince wani abu kuma taje ta ƙarani, miƙewa tayi sanann ta nufi ɗakin gwaggo tana zuwa tayi sallahr isha"i, tana gamawa a wurin da tayi sallahr anan ta kwanta, bata daɗe da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita,


Allah yasa mu dace ubangiji ya ƙara mana haƙuri a gidan aurenmu idan bakayi haƙuri don Allah ba sai kayi dan banza, hausawa sunce wanda bai share masallaci ba ya share kasuwa, Allah ka zaunar da kowa a gidan mijinta lafiya, ameeeeeeeeeeen,


da haka nake cewa ku kasance tare dani, 💋💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 2⃣5⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*Wannan shafin naku ne ameenci writer's association, ƙungiya mai haɗin kai da kaunar juna, kullum ƙoƙarinsu ganin sun kyautata wa juna Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, ubangiji ya ƙara basira da hazaƙa , Allah kuma ya ƙara lafiyar idanuwa, abinda muke rubutawa wanda mukai daidai Allah ya bada ikon amfani dashi inda mukai kuskure Allah ya yafe mana , ku kuma masoyanmu muna maku fatan alkairi ubangiji ya barmi tare*

*Asmeenat xeeyan har yanxun ba zan daina maraicinki ba, saboda kina cikin babban birni zuciyata* 😜

*Hafsat isa maman katsina ta dikko ɗaƙin kara muna godiya sosai bisa ƙaunar da kike ma aminci writer's mun gode sosai da kulawarki alkairin Allah yakai aki har cikin bargon baccinki dan nasan yanxun dai baki tashi ba,*

*****

*G*ari na wayewa raihana bayan tayi sallah bata koma bacci ba, suna nan zaune da ita da gwaggo suna ɗan taɓa fira, har hantsi ya fito, gwaggo ce ta tashi ta fita daga ɗakin dan sarrafa abinda zata bawa cikinta,

Daga tsakar gida ta kwaɗawa raihana kira , tana cewa fito ki siyo man alewa, raihana ta fito daga ɗaki tana miƙa, da hijibin ta rataye a kafaɗa, naira 10 gwaggo ta bada ta siyo mata alewa, raihana tace wai mi zakiyi da itane?""

Gwaggo tace kunun tsamiya zanyi, idanuwa raihana ta zaro sannan tace banda abinki waye zaisha kunun tsamiya da alewa?"" gwaggo tace ni, raihana tace haba kiyi haƙuri a siyo maki sugar kona ishirin sai ki ɓalɓaɗa, gwaggo tace ƙarshen canjinta kenan, dariya raihana tayi sannan ta anshi kuɗin ta fita daga gidan,

Ita kuɗin ta suna hannun umma data siyar ma gwaggo sugar nan , tsaki tayi sannan tace Allah yayi mana tsari da talauci, niko nace ameen ,

Tafiya take sosai har ta isa shagon shamsu, akwai layi dan haka ta samu wuri ta raɓe, saida aka rage sannan ta miƙa mashi kuɗin , bayan ya riƙe kuɗin a hannunshi ne kafin ya ɗauko mata alewar ya fara cewa raihana jiya anxo binciken halinki amma nidak Allah ya sani na bada shedar halinki ikar wanda na sani amma ina nan naji shehu yace aike alashe money ne baki auren talaka sai mai kuɗi sannan kuma duk kinbi kin gama barbaɗewa saman titi, shekara ukku kina zawarci kada ya kuskura ya yayo ma kanshi jaraba,

Amma kiyi haƙuri ba faɗa maki wannan dan ranki ya ɓace ba kiyi haƙuri idan kinsan kina da wani hali wanda bai dace ba ki gyara, kamar yanda kike haƙuri akan rayuwa ki ɗaure kuma ki dage da addu"a, dan duk tsanani yaa tare da sauƙi,

Ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace shi a gabanshi nayi iskancin ne?"" shamsu yace wallahi banda ni kima tambayi duk wanda kike so, zai faɗa maki dan cewa yayi wai kwalba kika samu idan kika kama mutum ki fara aske mashi arxiki wahala take sa ya gudu da kanshi , kina jiran mai kuɗi yaxo ki aureshi,

Raihana tace to shida Allah, kuma idan lokacin aurena yaxo wallahi bai isa ya hana ba, idan kuma ina rabon hutawa haka shima bai isa ya tare man samuna ba,

taci gaba da cewa tunda yayi aure ya aihu shima wata rana anyi ma nashi, daga nan bata sake cewa komai ba, har shamsu ya bada alewar ta fito daga cikin shagon ta nufo gida,

Tana tafiya tana tunanin wanan sharri, tsaki tayi lokacin data wuto majalissar da ake janta suka fara , ko ka gane mana *zawara* uwar san banza ke wuta kanenki ɓarawo, suka fara sheƙewa da dariya, suka ci gaba da cewa nifa ban taɓa ganin zawarar gdan talauci ba wai ita can mai kuɗi take jira don Allah kalleta, sai su sheƙe da dariya hhhhhh *zawara* haka sukayi ta mata iskancin , ita kuma raihana hawayene kawai yake bin idonta rugawa tayi da gudun tsiya, tayi cikin gda, gwaggo tana bakin murhu tsugunne taji raihana ta shigo da guda,

da sauri ta miƙe tana tambayar lafiya?"" raihana da gudu ta faɗa cikkn jikin gwaggo ta rushe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, gwaggo ta fara salati tana cewa wai miye don Allah,

raihana tace wai gwaggo har takai idan anzo tambayar halina a anguwar nan ace man waini "yar iska ce, wai bana aure sai mai kuɗi, ni wallahi miji ko daga kauye yazo wallahi aurenshi zanyi, ni banma san mai kuɗi talaka nake so muyi zaman mu, in rufa ma kaina asiri, yanda take kukan tana ƙara ɗaga murya, abun yasa gwaggo taji tausayinta,

raihaina taci gaba da cewa ama barni da abinda Allah ya jarabeni amma sai ayi ta jaman sharri?"" to wallahi ni tunda nake ban taɓa iskanci ba, kuma duk wanda yaman sharri na barshi da Allah wallahi,

gwaggo taji tausayin raihana don haka taci gaba da rarrashinta tana bata haƙuri , raihana tace ba komai Allah zai saka man, tana cikin magana wani yaro ya shigo yace ance raihana taxo, ɗago jajayen idon ta tayi sannan cikin maganar kuka tace waye yake kirana?"" yaron yace ummarki ce, murmushi raihana tayi sannan tace ma gwaggo ina zuwa,

Tana faɗin haka tayi waje da gudu, tana fita a ƙofar gidan da zasu kama haya ta hango umma tsaye saboda haka da gudu ta isa wurin umma tana ta kuka, umma tace mi akayi maki kuma?"" raihana ta kwashe komai ta faɗa mata,

Har a ran umma bataji daɗi ba, amma dan tasa raihana taji natsuwa tace to miye?"" aidai ke kinsan baki iskanci ko?"" to duk wanda yai maki barshi da Allah, raihana tace haba umma sharri babu daɗi , umma tace mai sharrin zai isko maiyin da izin Allah,

ta kauda maganar ta hanyar cewa na biya kuɗin na wata ukku na bayar, yau zanje in kwaso kayanmu, raihana tace to, umma tace ki shiga kiga ɗakin, raihana tace umma basai na gani ba, ina sauri ne inje in shirya zulaiha tana jirana a gdansu,

umma tace to kije ki shirya ki tafi, raihana tacd umma kinga waya, nayi chargy ashe ma hada layi ta saka man, umma tace to Allah ya tsare , raihana tace amin, sannan tace ummana ki bani ₦20, inje in siyo ko koko insha,

Umma tace to sannan ta bata kuɗin, ta juya tayi gidan da suke siyo koko, ta siyo a leda sannan tayo gidan gwaggo,

tana shiga ta samu wuri ta juye kokon, babu sugar babu alewa, ta bara sha, gwaggo tace miyasa kika siyo?"" gashi nayi dake, raihana tace ai yau koko nake ra"ayi, gwaggo tace tou fa,

ita kuma raihana tayi haka ne dan zaman lafiya dan idan dai kana san zamanka da mutum yayi nisa dole saika nisanci abunshi, idan kaga mutum yana san abunshi tayashi sanshi sai ka zauna lafiya,

tana gamawa wanka taje tayi, kayan da taxo dasu dagan su umma ta saka , taci uban kyau idan ka kalli raihana sau ɗaya baka iya sauke idon ka, dan gaskiya raihana tana da kyau , kuma kyau mai ɗaukar hankali , tana da siga da diri mai ɗaukar hankalin duk wanda ya ganta, amma daka ganta kasan bata da wadata, danshi ƙoshi daban yake, kana kallonta zaka gane tana cikin damuwa,

haka ta gama shirinta tsaff ta fito, tayi ma gwaggo sai ta dawo, gwaggo tayi mata Allah ya tsare hanya,

tana fitowa ta ibi hanya sai gidansu zulaiha, haka tayi tafiya mai ɗan nisa sannan ta iso gidansu, a ƙofar gida ta samu zulaiha, suna gaisawa da wani abokin mijinta wanda shine zai kaisu inda zasu je, zulaiha da sauri ta iso wurin raihana ta rungumeta kawata kinfa haɗe, dan ba haɗuwa kikai ba haɗewa kikai wallahi, raihana tayi dariya, sannan zulaiha tace *K"B* ga ƙawata, sunan ta raihana,

kb ya kalli raihana sannan yace sannu raihana tace kaima sannu, ya tsareta da idanuwa sai kallonta yake, zulaija tace muje ciki,

suka shige ciki gida, suna shiga wata ƙanwar zulaiha ce ta fara cewa wallahi yaya zulaiha shine kika shafa man janbaki na?"" zulaiha tace janbakin banza, yarinya nida aka kawo ma lefe,

kanwar tace lefenkin banza ina ruwana dashi, zulaiha tace rashin kunya zaki man ne?"" wannan ba baƙuwa bace a wurina, tana nuna raihana tace da Allah wuce muje bar raihana bar banza,

babu kunya yarinyar nan tace gaki ƙatuwar banza, wanda kika kasa haƙuri da mijinki irin halin da kikai mashi ya koro ki kkke so muma nan kixo ki raina mana hankali tomu bamu barin takwana,

raihana tacd ikon Allah zulaiha tacd ke bar banza nan mi kika gani?"" ai nan ba"ai komai ba, muje ciki lokacin da take jan hannunta suka shiga cikin ɗaki,

Ita kuma kanwar zulaiha haka taci gaba da ɗago murya tana zungurawa uwar zulaihat zagi amma daga raihana har zulaiha babu wanda ya sake magana, suka fara buɗe kayan lefe,

akwati shidda hada wata katuwar jaka, an kashe kuɗi gaskiya akamar lefen budurwa, ga kaya masu tsadaɗ gaske, komai dai na aji ne aka sako mata tsayawa faɗin abun ɓata lokaci ne, raihana taima zulaiha fatan alkairi,

zulaiha tace nace mashi ranar da aka ɗaura aure zan tare ,yace to babu damuwa kuma ko kayan ɗaki da duk abinda zan buƙata shine yayi man, raihana tace masha Allah haka ake so ai,

bayan sun gama ganin kayan zulaiha tace suje kabir yana waje yana jiransu haka suka taso sukayo waje, suna fitowa kabir ya kwashe su suka biɗaɗa duniyar gayyar ƙawayensu,

haka suka yini suna gayya, amma ba kowa suka gayyata ba sun gayyaci ƙawayensu na kusa da kusa, sannan sukayo gidan su zulaiha , k"b yace to zulaihat bari inkao ƙwarki gda, raihana tace ah ah nidai ajiyeni anan , zanje dakai na, yace wallahi sai nakaiki,

zulaihat ta fita, shi kuma yace ma raihana ta dawo gaba, raihana ita tunda take bata taɓa shiga gaban mota ba, saboda lokacin data auri aminu baya da mota,

Raihana taƙi tashi , ya sake mata magana amma ta kasa motsawa, zulaihat tace haba ƙawata miye haka don Allah wannan babban mutum zai zama drivern ki?"" zo kiji, ta matso kusa da raihana tayi mata raɗa, bansan abinda sukace ba amma naga raihana ta tashi ta koma gaban mota,

tana shiga zulaihat ta rufe masu ƙofa, k"b yaja suka bar ƙofar gidansu zulaiha,

Lafiya suke babu wanda yayi ma wani magana, k"b ne yace muga wayarki, raihana ta miƙa mashi, amsar wayar yayi ya ɗan jujjuyata sannan yace wanne wayar kike riƙewa?"" raihana tace Eh, tsaki yayi sannan yace haba ai abun kunya ne ina tare da mai kyau kamarki kina riƙe wanann ƙaramar wayar,

saboda haka zan kawo maki waya mai kyau idan Allah ya kaimu gobe, raihana tace ai wannan sabune, yace nidai batai man ba gaskiya, raihana tayi shiru, haka yaci gaba da maganarshi wata ta bashi amsa wata kuma tayi mashi shiru har suka iso ƙofar gidansu , bayan yayi parking ne , yace ma raihana yana zuwa, fita yayi daga cikin motar yaje ya buɗe but, ya ɗauko wani abu, sannan ya dawo ya miƙawa raihana,

Nidai bansan ko miye ba, amma wani ɗan ƙaramin kwaline, raihana ta karɓa tayi godiya,, sannan tayi mashi saida safe, saida ta shiga gidan da suka kama haya yaga inda ta shiga sannan ya tafi,

Sallama raihana tayi sannan ta shiga, uma daga ɗaki ta amsa mata sallamar, raihana ta shiga, umma tayi mata sannu da dawowa, raihana tace yawwa daidai lokacin da take cire gyalen jikinta, ta raye a saman ƙofa, zama tayi dan ganin abinda k"b ya bata, umma tana cewa miye wannan ?"" raihana tace nima ban sani ba, amma bara mu buɗe mu gani,

Bayan ta buɗe ɗan ƙaramin kwalin daga umma har raihana zaro idanuwa sukai da sauri umma ta miƙe tsaye ta dafe girjinta dan ganin abinda ta gani , itama raihana gabanta sai faɗuwa yake, umma ta fara cewa raihana yaushe kika canja hali? Yaushe kika koma rayuwar da ba taki ba?"" wane irin rayuwa kika zaɓawa kanki haka"??""" ina kikaje kika samo wannan kuma?"" waye shi da har zai ɗauki wannan ya baki?"""kuma raihana cewa take wallahi umma bansan ko miye a ciki ba haka ya bani da nasan hakan ne ai da bazan karɓa, na ɗauka biscuit ne, umma tace keda yunwa ta ƙare maki ko?"" raihana tace umma ba haka bane, umma tace rufe man baki aikin mi kikai masji da zan ɗauki wannan ya baki??"""" wato kin fara halin da ake zarginki dashi ko?"" raihana ta fashe da kuma tace haba umma ki kyautata man zato don Allah wallahin banyi duk abinda kike tunani ba, idan kuma zatonki haka ne wallahi umma ki dubani na yadda kiga idan nayi iskanci, tunda nake wallahi ban taɓa zuna ba, tsaki umma tayi sannan tace faɗa man abinda kikai mashi ya baki wannan iyayen kuɗin...........................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 2⃣6⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

****
*K*ukan da take ta tsagaita dashi sannan tace umma babu abinda nayi mashi kuma shima baiyi man komai ba, kawai dai ya ɗauko kuɗin nan ya bani ne,

Umma tace to ai so nake inji abinda kikai mashi ne, tunda nidai banga kin fita da wani abun siyarwa ba, raihana tace wallahi umma ki yadda dani babu wani abunda mukai dashi, zulaihat tace man yace yana so na, shine daya kawoni gida ya bani kuma yace zaima canja man waya ,

Ajiyar zuciya umma tayi sannan tace to kidaiyi hankali dan idan anga mace na zawarci kowa kallon sakara marar kamun kai yake mata, kinga dai kin taɓa aure hukuncin zina ga wanda ya taɓa aure kisa ne, idan kuma kikaje kika ɓoye kikayi Allah ubangiji yana kallonki zai linka maki nauhin wahala wanda yafi wannan,

Raihana tace insha Allah umma bama zanyi ba wallahi, umma taci gaba da cewa kuma ga cututtuka sunyi yawa a duniya, kinga idan kikayi sakaci aka cuceki kinfa tashi aiki zaki rasa mai aurenki ne kiyi ta kanki kuma ki nema ma rayuwarkk mafita,

Raihana tace

Please Login or Register in order to submit comment