Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada kiyi masu horon yunwa kada ki hansu makaranta ki riƙa aza masu talla, komai zakiyi masu kiyi don Allah, ki ruƙa tunawa akwai ranar sakamako,

Ranar da zaka girbi abinda ka shuka , "ya"ya amana ce a wajenmu, da kuɗi da "ya"ya ba"a masu mugunta don Allah ne kaɗai yasan wanda zai moresu a gaba,

Kada ki wulaƙanta "ya"yan kishiryarki ki azabtar dasu kiyi abinda miji zaifi san naki "ya"yan ya wulaƙanta wa"ancan kinsan arxikin da Allah yayi wa wa"ancan ❓ kinsan mai zasu zama nan gaba❓ baza fa su taɓa manta tsanar da kikayi masu ba,baza su taɓa manta irin ƙiyayyar da kika gwada masu ba,

Ko kuma kin taƙura wa kishiyarki kin tsani "ya"yan kina gallaza masu azaba kin shanye mijin duk abinda ya samo a tafin hannunki yake kina shirya wa kanki rayuwar duniya, kwatsam sai kika faɗi kika mutu, kinga kin bar mata mijin da "ya"yan naki duk sun zama a ƙarƙashin ikonta ,

ke kuma kina kabari kina karɓar mummunan saƙon da kika aikata a duniya, saboda haka duk abinda zakayi ka tuna Allah yana kallonka kuma duk abinda ka aikata alkairi ko kishiyarsa a rubuce yake cikin littafinka, ɗauki rayuwa da sauƙi sai komai yazo maka da sauƙi, Allah yasa mu dace,

****
*ZAWARCI*

*R*aihana dake kwance ƙasa kamar gawa, ganin faruk ya fara rubutu yasa ta miƙe da sauri jikinta yana ƙarma ta matsa kusa da faruk ta riƙe biron gam tana cewa ka rufa man asiri don girman Allah kar ka sakeni, shima faruk hawaye yake sosai,

momy tace wallahi saika saketa idan ba haka ba, ban yafe ba, cikin kuka raihana tace faruk ka rufa man asiri kaga ka rusa man rayuwa kayi haƙuri ka barni in zauna tare dakai don Allah,

momy fita tayi daga farlon , raihana na ganin ta fita, taci gaba da cewa faruk ka taimaki rayuwata kowa yana man kallon banda natsuwa ni karuwa ce, amma ka ka sheda ni ina da natsuwa kuma kaine mutum.na farko daya fara keta man rayuwata, kaine ka samu farin cikin da babu wanda ya samu kamarshi kodan wannan ka rufa man asiri faruk kada ka sakeni nayi maka alƙawari zakayi alfahari da aurena zan zamar maka farin ciki kuma zan zama mai biyayya a gareka,

Nayi alƙawari bazan barka kayi kuka ko da nasanin aure ba, kayi haƙuri don Allah, insha Allah aur..............."""" bata ƙarasa maganar ba taji duka ta ko ina momy dukan raihana take kamar an aikota,

faruk da sauri ya miƙe ya kare raihana haka momy taci gaban da dukan raihana da faruk babu ji babu gani, wata ƙatuwar dorina ce take dukansu, tun raihana tana iya magana har bakinta yayi shiru tun tana nunfashi har takai ta some,

Faruk da yake rungume da raihana yaji jikinta ya saki idanuwanta sunyi sama sun kafe hankalinsa ya tashi ya shiga jijjigata yana wani irin kuka, idanuwansa gaba ɗaya sun kaɗe sunyi wani irin ja,

kallon momy yayi sannan yace momy kin kashe masu ɗiya, kin matar da raihana, momy tace na kasheta kuma kaima saika gama rubuta takardar sakin in kashe ka, faruk yace haba momy miye don Allah wani irin mari takai mashi , sannan tace rubuta dan ubankan,

jikin faruk yana ƙarma ya dauko takardar da biron ya ɗora daga inda ya tsaya,

*ni faruk ahmad hukuma, raihana ina baki haƙuri akan abinda ya faru, kiyi haƙuri kuma kiyi ma momyna uziri nidai bazan iya rabuwa dake ba, ki zauna gida insha Allah da zaran komai ya daidaita zanzo in dawo dake, ina sanki*

yana gama rubutawa ya nannaɗe ya bawa momy, ba tare data duba ba, ta buɗe jakarta ta saka a ciki, inda raihana take kwance taje ta kama hannunta sannan ta fara janta ƙasa ƙiyyyy kamar wata karya,

haka ta fita da ita daga farlon a bakin get taje ta buɗe mota ta jefata, sannan ta bawa wata mata takardar tace kuje shi yasan gidan ki shiga kibawa uwarta kice ɗana bazai iya zama da karuwa ba,

matar tace to, haka ta anshi takarda sannan ta shiga cikin motar driver yaja suka bar gidan,

Faruk kuma ganin irin wulaƙanci da tayi ma raihana abun yayi mashi babu daɗi sai kuka yake har yanxun ya kasa samun natsuwa, tunanin darensu na jiya yanda ya kasance kawai yakeyi,

Tunanin raihana kawai yake lallai ya yadda ko wane irin mace akwai irin baiwa da kuma ni"imar da Allah yayi mata, haƙiƙa raihana ta dabance, dan yayi aure aure ya auri mace sama da sha wani abu amma ita dai raihana ta dabance, banban kuma abinda yafi tsaya mashi a rai shine, yanda raihana ta kasance budurwa yana cikin wannan tunanin ne , yaji an kwaɗa masa wani abu akai ya faɗi ƙasa sumamme,

Momy tana ganin yayi ƙasa tace kaɗan ka gani kan wannan yarinya ina iya kashe ka har lahira, tun yanxun kana kuka zaka rabu da ita, wato da na bari tafiyar tayi nisa ashe dani nake cikin matsala, dan yanda take wani sinsinne kai kila sai ta kwace man kai,

Saida ta gama cas kaɗa masifarta sannan ta fice daga farlon tabar faruk cikin matsanancin hali,

Alhajin daya auro wa faruk raihana , da yake zaune ƙofar gidansa tun shigar momy bai tashi ba har yanxun fitar ta, yana nan don haka tana fitowa, wurinshi ta tsaya sannan ta riƙe ƙugu cikin masifa da tijara tace to baƙin munafi na wargaza wannan cutar taka , idan ka sake shiga cikin sabgar ɗana sai nasa anci uwar kaa garin nan, dan ɗana ne, nice a haifi abuna ba wani yasha man wahalar naƙudar ba, kaji na faɗa maka,

kaje ka auro ma ɗana karuwa, taxo ta kashe man ɗa ta tattara abinda gareshi a raba a baka kashi ɗaya ita kuma sauran ta riƙe to Allah yasa na gano ku kuma wallahi ni kaɗai ma gayyace, tana faɗin haka tayi gaba zungui zungui,

Alhaji saida ya tabbatar da momy ta ɓace kwata kwata, sannan ya miƙe ya nufi cikin gidan faruk, sallama yake amma babu mai amsawa, saboda haka bai tsaya ɓata lokaci ba, ya ƙusa kanshi cikin farlon gidan, sallama yayi sannan ya kutsa ka shi ya shiga farlon , haggo faruk yayi a ƙasa baje kamar wanda baya nunfashi, dan haka da sauri ya isa wurinshi ya fara jijiga shi, yana kiran sunan shi,

Amma shiru kake ji, alhaji tashi yayi da sauri yaje ya samo ruwa ya fara yayyafawa faruk amma shiru kakeji, hankalin Alhaji ya tashi sosai, dan haka wayarsa ya ciro ya kira wani ɗansa cewa maza ya fito da mota, ya sameshi gidan faruk su fito dashi zadu kaishi asibiti,

ɗan yace baba ina drivern shi kuma ina masu kula dashi?"" kamar faruk mu fita dashi haka babu tsaro kasan fa akwai matsala Alhaji yace to mamanshi tace bata so ya zauna dasu saboda matar daya auro taxo ta hana ɗanta zaman lafiya, ta rusa mashi mashi jin daɗi kawao mota dai, ɗan yace tom Alhaji ya kashe wayar, yaɓa rungume da faruk a jikin shi,

A ƙofar gidan su raihana motar tayi farkin itama matar babu tausayi a tare da ita bare imani, tana fitowa daga mota ta zagaya inda raihana take ta buɗe kamar yanda momy taja raihana itama haka ta jata har cikin gida ƙasa,

umma dake duƙe tana wanki taji shigowar mutum kuma babu sallama da sauri ta juyo dan ganin waye?"" a daidai lokacin da take sakin raihana ƙasa tifff, Umma tace lafiya baiwar Allah?""

matar tace saƙo ne daga mai girma, umma tace waye kuma mai girma?"" matar tace kinji ana faɗin Faruk Ahamad Hukuma?"" soja mai harbi da bindiga , yayi harbi ya kashe babu abinda za"ayi kamar ya kashe cin naka, kuma ya taka wanda yake so kamar motar tana wucewa a kwalta,

haka kuma mace ba komai bace a wurinsa ta ƙarasa maganar tana ɗaga ma umma gira, kinga shi mace a wurinsa hula ce, da kuɗinsa zaisa ya idan ya gama keta ma mace rayuwa sai ya bada saki kamar dai yanda kikaga ya bawa "yarki,

Murmushi tayi sannan taci gaba da cewa haka yake kuɗinsa yake kashewa dan biyan buƙatar kansa amma fa baya neman mata, jakarta ta buɗe sannan ta zaro takardar ta ajiye a saman raihana dake kwance tana fitar da wani irin lumfashin wahala,

matar tace hajiyata na barki lafiya sai kuma munzo kawo maki katin gayya dan gobe iwar haka soja nacan ya zama ango, ɗiyar gidan masu kuɗi ba talakawa da suka ƙare a gidan haya ba, wata irin dariya take irin maicin rai , tana kyakyatawa, sannan ta fita tabar gidan,

innalillahi wa"inns ilaihir raji"un umma take faɗa a daidai lokacin da take ɗuƙusawa kusa da raihana , a hankali ta ɗaga ta sannan ta nufi ɗaki da ita dan gudun kada wasu suxo suga halin da ake ciki,

bayan ta shiga ɗakin ta kwantar da raihana saman katifa, tana kallonta hawaye yana zuwa daga idon umma, cikin tausayawa tace ke kuma taki kaddarar haƙa taxo?""" raihana bata iya magana sai kuka take,

umma tace kiyi haƙuri duk abinda yayi tsanani sauƙi yana kusa, takardar umma ta ɗauka ita dai bata iya karatu ba, kuma bata san abinda aka rubuta ba, kallon takardar tayi sannan ta kalli raihana dake kallonta kamsr ɗan bitinbutumi, ɗaga tatifar tayi sannan ta ajiye wasiƙar ita kuma ta fita dan dafa ma raihana ruwan wanka,

Ɗan Alhaji da shi Alhajin suka kama faruk suka fito dashi, a mota suka sakashi suka kwantar dashi a gidan baya amma shima alhajin a baya ya shiga ya rungume faruk ɗan alhaji yaja motar suka nufi asibiti,

ita kuma momy tana tafiya tana faɗa wai Alhaji yayi munafinci dan yaga faruk yana da kuɗi a kashe mata ɗa a kwashi dukiyar suje su raba ita kuma a barta da tagumi, koda taje gida ta faɗaw "ya"yanta wato ƙannen Faruk hankalinsu ya tashi, sukayi ta nunawa momy bata kyauta ba, sannan kuma tunda har tayi haka lallai ƙarshe hukunci akansu zai dawo, dan haka suka tilaswa momy lallai su koma suga halin da faruk yake ciki, yanda suke nuna abun da ƙara ma abun girma da wuce shi akan yanda momy ta faɗa itama momy ta shiga ta rarrabi,

haka suka tashi wata ƙanwarshi itace taja motar suka nifo gidan faruk, ni kuwa nace ai kun makara,

Asibiti mai kyau da tsada alhaji yakai faruk , suma ganin waye shi yasa likitoci suka taru kanshi dan ceto rayuwarshi,

Alhaji da ɗanshi sun ware a gafe ɗaya suna magana, har yakr bashi labarin yau a masallaci da safe faruk yake ce mashi ya ƙarawa raihana wata ɗaya, dan yana san yayi mata alkairi mai girma kafin su rabu, ajiyar zuciya Alhaji yayi sannan yace ashe uwarshi baza ta bari tafiya tayi nisa ba, a daidai lokacin da wani doctor yazo wurinsu, yana cewa lallai yana buƙatar tsaro sosai, saboda haka su kula,

Tun kafin mota ta gama parking momy ta fito jikinta yana rawa, da ɗan gudu gudu suma sauran duk bayanta suka biyo, suna shiga parlour suka ga wayam, hankalin momy ya tashi haka suka ƙaraɗe gidan kaff amma basu ga faruk ba, bayan sunyi tsaye a wuri ɗaya suna maida nunfashi kamar wanda sukai dambe da zaki, maibin faruk tace momy ai ga irinta nan, saboda wannan halin naki gashi nan mun jibge maki a gabanki duk wadda tayi aure sai an sakota, tunxa kema kanki bakiyi ma yaya nasiha yayi haƙuri ya zauna da "ya"yan mutane ,

kin ɗaure masa ƙugu yayi abunda yaga dama, ya auro waccan ya saki wancan ya wulaƙanta waccan ki faɗa ma ke wace ce da baza"a akan "ya"yanki ba, yanxun ga mata ukku a gabanki duk *zawarci* ga ɗaya nan katuwa batayi aure ba, wace irin rayuwace wannan?""

haka kika sa mukaxo mukaci uwar yarinyar nan momy muka wulaƙanta ta, amma ke shine kima tsareshi ya saketa, muma gamu a gabanki amma kullum kina cikin damuwa da addu"ar Allah ya bawa "ya"yanki mazan aure, kina wannan halin labari yana karaɗe duniya waye zai so mu?""

Momy tayi shiru kamar wadda aka zare wa lakka, lallai tayi babban kuskure, basu da mafita dole suka haƙura suka koma gida,

Raihana bayan ta fito wanka Umma ta zubo mata tuwo amma raihana ko kallon tuwon batayi ba, kuka kawai takeyi , umma ta zauna kusa da ita sannan tace wai saki nawa ne ya baki,?"" cikin kuka raihana tace umma bansani ba, umma tace anshi duba mana, adaidai lonacin data ke miƙa mata, raihana tace bazan iya karantawa ba, umma ki ƙona ta, Umma tace bazan ƙona ba, zan haɗa inda na ajiye ta aminu in ajiyesu tare ,

raihana tace haka zakiyi ta ajiye wasiƙun sakin aure a ɗaki sai kace jere?"" Umma tace sheda ce, dan idan mutum yace bai sakeki ba, ko kuma yace sakin da yayi maki bai kai haka ba, sai a ɗauko a raba gardama ,


Raihana tace to shikenan, Umma taje ta saka takardar ta ajiye a inda ta ajiye ta aminu, bayan ta ajiye tazo ta zauna kusa da raihana, raihana ta kwashe komai ta faɗawa umma, umma tace to babu komai Allah yasa haka shine alkairi raihana tace amin,

faruk bai farko ba sai 10:35pm kuma Alhaji bai tafo ba, haka kuma ɗansa suna tare amma dai yayi waya ya faɗa ma iyalinsa kuma yace kada a faɗawa kowa suna asibiti ,

Faruk yana farkowa ya kalli Alhaji, hawaye suka ci gaba da zubowa daga idonshi cikin damuwa da yanayi jin jiki ya maida kallonsa sama yana kallon silin ɗin ɗakin murmushi yayi sannan yace masoyin raihana ya dawo daga duniyar mutuwa, hawaye suka ci gaba da bulbulowa daga idon sa, lokacin guda kuma ya sake rufe idonshi yace gaba da kuka,

Alhaji yace kayi haƙuri , kicin ƙarfin hali faruk ya miƙe yace ina?""sannan yace miyasa momy tayi haka ne?"" Faruk dai ya kwashe komai ya faɗa ma Alhaji sannan yace amma ban saki raihana ba, Alhaji yace to Alhamdulillah , komai zaizo da sauƙi,

Faruk yace ma alhaji muje gida, Alhaji yace mu bari saida safe mana, Faruk yace muje kawai , saukowa yayi daga saman gadon likitocin suna bashi haƙuri ya bari ya ƙara samun sauƙi amma baibi ta kansu ba suka nufi gidan faruk ,

bayan sunxo ya ɗauki wayarsa ya tattaro duk wanda yasan yana bashi kulawa, don haka suna gama haɗuwa aka shirya motoci , Faruk yayi wa Alhaji godiya sosai sannan yayi masa fatan alkairi, ɗakinsa ya shiga ya ɗauki wayar raihana bayan ya fito yayi umarni da a rufe ko ina na gidan,

Bayan an kulle ko ina faruk yace suje, suna fitowa a wajen gidan yayi ma Alhaji ban kwana, haka suka shiga mota suka tafi, akabar daga alhaji sai masu gadi, shima daga baya ya tafi gidanshi, masu gadi kuma sukaci gaba da tsaron gida,

***

*T*unsa safe umma tana yin sallah n asuba, bayan ta gama ta tashi raihana tayi sallah, bayan raihana ta gama sallah n ne, umma tace ga ruwan zafi kije kiɗan watsa ko zaki sake jin ƙarfin jiki, bayan ta gama wankan ta fito, suna nan zaune suna fira, gar gari yayi shaaaa sannan umma tace bara taje ta samo masu abinda zasuyi kalaci...............
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 3⃣8⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

****

*KISSAR KALLO*:• Kallo kala kalane, akwai harara akwai kallon banza akwai firgitaccen kallo akwai gigitaccen kallo, to duk irin wa"nnan kallon mai gida yafi ƙarfin ayi masa su, mai gida saidai ayi masa kyakkyawan kallo kiyi masa tattausan kallo wanda zai riƙa tsundumashi cikin halin sha'awarki,

Ki rinƙa yi ma maigida kallon soyayya kina yin fari da idanunki, kina kaɗa masa su, idan kuna hira cikin nishaɗi ki ɗan riƙa sheɗaniyar dariya,

Kina ware masa idanuwan cikin yanayin salon kissarki, ki rinƙa masa kallon ƙasa ƙasa, kina lumshe ido kiɗan riƙa ƙanƙancesu kin shanyesu, kina lumshesu cikin salon iya jan hankalin mai gida,

Ki tsumduma shi cikin wani hali tsundumm, ki riƙa ɗan ƙasa da idanuwanki kina lumshesu kina rufe su kaɗan kaɗan kina buɗewa kamar mai shirin yin bacci, idan ya ɗan taɓoki sai kiyi harrr da idanuwan naki, ki buɗe su ki warsaya masa su, kiɗan shanye ki lunshe su, wannan shine kallo mai saukar da kasala,

Ya kashewa mai gida gaɓoɓi, bashi da buri sai dai yaji ki tare dashi, A kula hajiyata, ba a zarewa wa miji ido , ba a kuma harar miji, saidai hararar kiss cikin salon soyayyarku idan miji ya ɗan ɓata maki,

To anayin hararar kiss cikin salon ƙauna , hararar zaiyi ladaf, ya amsa laifinsa nan da nan,

*****

*U*mma tana fita raihana ta sulala ƙasa ta kwanta, hawaye masu zafi suka fara kwararowa daga idon ta, tayi ajiyar zuciya sannan tayi magana a bayyane, lallai kowa da irin ƙaddarar sa wasu a jarabe su da uwa, wasu uba , wasu miji , wasu abokiyar zama { kishiya } wasu "ya"ya wasu wasu kuma dangin miji wasu ƙannen miji wasu kuma uwar miji,

Lallai haƙiƙa ni kuma da uwayen miji Allah ya bani tawa jarabawar, shi aminu ya aureni saboda shine yake so na, maman shi ta koroni tasa ya sakeni, shi kuma faruk bansan sa bak sannk ba, amma ina ƙoƙarin gina mana rayuwarmu mai kyau da jin daɗi shima mamanshi tasa ya sakeni, goge wayenta idonta tayi sannan tace wai miyasa rayuwa take tsanan tawa?"""

Umma dake tsaye bakin ƙofa, tace duk yanda rayuwa ta bada ki karɓa, a daidai lokacin take shigowa cikin ɗaki, raihana ta tashi ta sake rushewa da kuka, yanda take kukan yiiiiiiiii wani iri dai mai shiga rai,

itama umma hawaye ta fara, sannan tace ma raihana kiyi haƙuri , dan baki san wulaƙancin da akaman gidan koko ba, raihana dake kuka ta tsagaita da kukanta sannan tace mi aka maki ne umma?"""

Umma ta goge ɗan kwallar data zubo mata a ido sannan tace, koko naira ishirin nake siye, yau danaje nace a bani na arba"in, shine tace man ko nayi baƙuwa ne?"" nace mata raihana ce babu lafiya, tana nan gida, dan nasan yanxun sun san kina gida, dan duk abinda ake akan idonsu akeyi,

Umma taci gaba da cewa kinsan abinda tace?""" raihana tace ah ah, umma tace dariya tayi sosai sannan tace wai har na fara masu yanga ɗiyata ta auri mai kuɗi ai gaki nan yanxun an sakoki sai in ajiye yanga, tana faɗin haka ta kece da dariya, umma tace raihana nace mata kiji tsoron Allah a ina nake maki yanga?"""

tace haka nike, nace to babu damuwa, bani kokon, raihana bakiji yanda naji ba, babu daɗi naji, raihana tace ai kema umma miye kika faɗa masu don Allah?"" umma tace rabon ayi, raihana tace to Allah ya sawaƙe, umma tace amin,

umma ta zubawa raihana koko a kofi ko alewa babu bare sugar, sannan ta bawa raihana taɓe ɗaya tace tasha kokon zata samu kuzari, niko nace tasha dai wahala koko da taɓe ai baya maganin yunwa,

A ɓangaren faruk kuma yana cikin damuwa sosai, tunaninshi ta ina zai fara ma lamarin?"" lallai zaije ya ɗauki raihana ya sake mata wurin zama, wata zuciyar kuma tana hani ga shawarar shi, yayi haƙuri dai ya sassauto da zuciyar mahaifiyarsa dan tunda bata santa ko ta dawo gidanshi lallai zaman doya da manja zasu ci gaba dayi,

Wayarta ya ɗauko da yaji tana ta kuka, dubawa yayi dan ganin mai kiranta, abinda yaga an sa, babbar ƙawa, taɓe baki yayi sannan ya maida wayar ya ajiye, wani kiran ne ya sake shigowa, amma faruk bai ɗauka ba, haka tayi ta kira har ta gaji ta daina wahalar da kanta,

Gwaggo ce ta shigo cikin gidansu raihana bankam bankam babu ko sallama , ta fara cewa fatima ashe kuma raihana aure ya mutu?"" kam ai dama ina ganin gidan nan nasan ba wurin zamanta bane, gidan "yan gayu haka?"" mutum da kuɗinsa?"" a duniya yayi fice haba nace ina shi ina ɗiyar gidan mai wankin takalmi,..??

Ai kema fatima kinyi wauta, saboda tsabagen san abun duniya kika bayar da "yarki gidan kuɗi to gata nan anci uwarta ansha ruwan kanwa,

daga umma har raihana babu wanda yayi ma gwaggo magana, haka tayi ta wulaƙancinta, da ɓatanci tana dariya kanajin dariyar kasan dancin rai akeyinta,

ran raihana ya gama ɓaci dan haka tace, idan an sakoni miye damuwarki?"" ai kema inace da baba ya aureki aurenki bakwai, kuma duk inda aka sakeki baƙin halinki da mugunta yasa ake sakinki, da kika auri baba shima haka yayi ta haɗiyar gubarki saida kika kashe shi kika zauna lafiya,

Gwaggo tace kam bura"ube?"" keni dan uwarki?"" dan kunga kun samu gidan haya ba"a tasheku ba?"" lallai zaki san na iya sharri yau ɗin nan sai kunbar gidan nan sannan kuma dan ubanki hukuma zata rabank dake, tana faɗin haka tayi waje da gudu tana ihu,

gwaggo na fita Umma ta kalli raihana tace ke waye ya faɗa maki tayi aure aure ?"" raihana tace Umma gani nayi zata man wulaƙaci, ai baba yace zawarace ita ya aureta, umma tace to sai yace maki auren ta bakwai?"" raihana tace dan taji yanda naji a zuciyata,

umma tace tunda shi mutum ɗan sharrine ai saika kiyayeshi, raihana tace to Umma ai maganar ta fito bazata koma ba, saidai a tari gaba,


gwaggo na fita, bata shace ko ina ba, sai gidan wanda ya bawa su raihana hayar , gida, tana zuwa ta fashe da kuka, wai ta tadda suna shawara zasu siyar da gidan su gudu, shima yana ji hankalinshi ya tashi gwaggo tace idan ƙaryane yazo suje, haka gwaggo ta tattagoshi yana biye bayanta ita kuma tana gama zungum zungumm buzum buzum har gidan su raihana,

shi kaɗai yayi sallama amma gwaggo batayi sallama ba, bayan sun shiga suka gaisa da umma, sannan yace miyasa zaku siyawarwa daka tsalle da gida?"" umms tace ranka ya daɗe muda akayi ma halakci ya zamuyi mu zama butulu?"" gwaggo tace wallahi a gaban idon ka take maka daɗin baki ka tashe ta kafin a yaudare ka, yace a,a ku saurara ba haka akeyi ba, ke fatima na barmaki gidan nan bisa amana idan kika cuceni ubangiji yana kallonki zaiman sakayya, Umma tace ni kuma zaka sameni mai amana,

Yace ina kyautata maki zato amma kinsan shi mutum canjawa yake, umma tace bana ɗaya daga cikin masu irin halin nan insha Allah, to babu damuwa yace sannan ya fita daga gidan,

raihana ta kalli inda gwaggo take sannan ta ƙalƙale da dariya, tace don Allah ya kikaji?"" kai andai ji kunya, kukan kura gwaggo tayi taje ta haye kan raihana tayi ta dukanta, saida ta gaji dan kanta ta barta, dariya raihana tayi sannan tace kiyi wannan itace damarki dan wallahi wata rana da kuɗi aka haɗaki ki dakeni baki iyawa,

Gwaggo tace shegiya a haka dai za"a balbaɗe an rasa mai aure kullum kayanki na saman kai saboda baki zannuwa, raihana tace tunda dai ke mai baƙin hali kƙa zaunu nima sai an samu wanda zai zaunu dani insha Allah,

wata tukunyar ƙasarsu gwaggo ta ɗauko ƙaton dutse ta rufasa ta ruwan cikin suka fito bull bull gwaggo tayi waje tana cewa sai kin rasa ubanda zai aureki,

raihana ta ɗaga muryata tana cewa haka kike cewa kullum kuma Allah yafi ki, gwaggo na fita Umma tace Allah idan kika sake biye mata raihana saina ɓata maki rai, raihana tace Allah ya baki haƙuri uwa ta gari, ta ƙarasa maganar tana dariya,

*****

*S*atin raihana huɗu a gida, abubuwa sunci gaba da faruwa, rayuwa dai tayi mata haggunce, amma har yanxun faruk baizo ba kuma bai aiko ba, danshi yana can abubuwa sun mashi yawa, amma raihana tayi mashi tsaye a zuciya, dan duk matan da yake aure bai taɓa auren matar data hana ma zuciyarsa saƙatta irin raihana ba, yayi magana da momy amma tace ya saurarareta,

Raihana kwance a saman "yar yaɗin katifarsu tana ta tunani iri iri, kallon umma tayi sannan tace don Allah umma ki barni zanje gidan farida, umma tace gaskiya bazakije ko ina ba sai kin gama idda raihana zatayi magana umma ta dakatar da ita, sannan taci gaba da cewa kin manta ko rabuwarki da aminu haka babanki yace, to tunda bashi raye yanxun dole nima in ɗora yanda yayi maki idan kuma na sake ki satata sai ace kin zama ɗiyar mace babu kyara,

raihana tace to Allah yasa mu dace , Umma tace amin, Umma taci gaba da cewa kiyi haƙuri kada kiga kamar na matsa maki kinji?"" raihana tayi murmushin ƙarfin hali don

Please Login or Register in order to submit comment