Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

today’’
Uncle ya fada yana miqewa, sauran mutane na jin haka kuwa suka mike kowannensu ya soma fita daga hall din, gaba dayan su tashin hankali ne karara a fuskansu, gashi a junan su ma baqin ciki suke ma juna kuma basa kaunar juna gashi lokaci guda wannan la’ananniyar ta tona ma kansu asiri a junansu.

Suna fita tayi ma secretary nuni da hannu akan ya basu waje, yana fita kuwa ta kalli khaal kafin ta soma tafa hannayenta tace ‘’wow, wow, wow, wonderful, that’s a great attempt khaal, ni da kai kasan cewa idan mutanen nan suka san cewa wanda suke tambaya akai is not mentaly stable zasu iya komai don ganin sun karbi wannan company din daga hannu mu, kana tunanin zan bar haka ta faru?, no never, this is my parents legacy, my parents hard work, abuh and ummuh, so this is just the beginning khaal’’
Tana kaiwa nan ta mike ta fuce daga office din ta barshi saqe a tsaye, hannunshi daya dungule yayi jaa sosai kamar gauta.

Hidaya kuwa na futa secretary ya mara mata baya zuwa office, wani irin sign of relief ta sauke kafin ta kalli secretary ‘’mun tsallake wannan, nasan bazasu hakura ba, zasu ta kawo hari with much questioning, inason kayi providing komai, da yanda mukayi planning komai’’

‘’okay ma’am’’ ya amsata kafin ya fuce yana murmushi.

Bayan futarshi Kenan ta, ta bude wata safe locker, wayoyi ne guda biyu sai wasu papers a cikin locker din, daya daga cikin karamar wayar ta zaro kafin ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma Magana anaste ‘’bana son dogon bayani, so guda nawa ne suka shigo hannu?’’
Daga chan ne aka bata amsa kafin ta sake cewa ‘’okay!!’’

Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta maidata cikin locker din kafin ta maida dubanta ga papers din dake cikin safe locker, tunani ta soma yi chan kuma kawai sai ta rufe locker din ta cigaba da ayyukan dake gabanta.



Bangaren sabeeha, karfe uku da rabi nayi ta koma dakin nashi, a hankali ta soma bude dakin kamar wata barauniya, dakin duhu dum yanda kasan dare yayi babu haske babu sound din komai kamar babu rai a cikin dakin, ahaka ta dunga rarrafawa ta karasa tsakiyar dakin, sai data karaso bakin gadon ta samu dan hasken bedside lamb,
Bin kan gadon ta soma yi da kallo, barcinsa yakeyi hankali kwance hanunshi rike da wani puzzle solver da ake jujuyawa, ya nado jikinshi da pillow ya rungume.
Tsugunnawa tayi agaban gadon ta zuba ma innocent kyakyawar fuskanshi idanu daga kan lashes dinshi da sukayi zaro zaro ga dogon siririn hancinsa a mike kamar pile zuwa ga lips dinshi da suke a cike sunyi jaa kamar ansa mashi filler ga sexy jaw line dinshi mai daukar hankali sosai, kasa dauke idanunta tayi daga jaw line din nashi don wajen is so attractive duk da bata san attracting dinta wajen yake ba,maido da dubanta tayi ga huge kirjinshi zuwa ga arms dinshi, ya zakalo hannunshi ya rungume pillow a kirjinshi, ya rike wannan puzzle box din da yatsunshi, daga ganinshi yana amfani da musles equipment saboda yanda ya damke pillow din kamar za a kwace mashi pillow din har jijiyoyin hannunsa sun bayyana.
Samun kanta tayi kawai da murmushi ganin yanda yayi wani irin juya bakinshi alamun kosawa da barcin, samun kanta tayi da qin tashinsa saima kallonshi data cigaba da yai harta sakankance lokaci ya kure.

Kokarin tashinsa ta soma yi saidai tsoron yanda zai tashin take don ance yana furgita, wata dabara ce tazo mata kai don haka ta daga dan karamin hannunta ta soma shafa karan hancinsa ba tare da tayi making sound movement ba ko hakan zaisa ya tashi, shuru dai babu motsi saima nunfashi da yake saukewa a hankali, ta dade tana hakan harta maida tafin hannunta kan bare fatar skin din fuskanshi mai laushi kamar na sabon jariri, shafa fuskan nashi ta soma yi ko hakan zaisa ya tashi har zuwa wajen silk gashin sajen fuskanshi daya zagaye fuskan nashi, dukda hakan ma datayi shuru ganin haka kawai yasa ta miqe ta futo daga dakin bayan ta tabbatar yana nunfashi.

Lokacin data futo karfe hudu yayi kowa ya sauka kasa gaba daya maids babu wanda ya tsaya anan saman don wannan dokar ba a tsallaketa.



Hidaya……
Bayan wannan shareholder meeting dinnan bata bar office dinba sai wajen yamma liss, school din barad ta fara zuwa suka daukeshi kafin ta dawo gida.
Akan hanyarsu ta dawowa gida ya soma nuna mata medal din da aka bashi na competition din da sukayi kuma yaci second position, kallon medal din kawai tayi kafin ta kalleshi, first tambayar datayi mashi is ‘’why would you take second position, ban haifi danda za a wuceshi a komai ba so buckle up and make me proud next time with a first position, not this rubbish okay’’
Girgiza mata kai kawai yayi in response,
Bawan allah yana jinta ta gama kanshi a kasa, yau kwata kwata baya cikin jin dadi saboda koda yaushe shi mai faran faran ne, dalilin fushinshi kuwa shine kowanne student parents dinshi na zuwa suyi supporting din yayansu, but shi babu wanda yazo mashi, daman daddyn shi yafi bashi attention akan harkokin nan shiyasa yafi shaquwa da daddyn nashi akan mamanshi, wannan yasa koda yaushe yake missing dinshi sosai.

Koda suka karaso gida kamar koda yaushe maids na tsaye suna jiranta, daya na kula da harkar barad while dayar kuma tana daukan Jakarta da sauran files dinta da sun dawo.

Saukowa tayi daga cikin motar maids din na mata sannu da zuwa, idanunta ne ya sauka akan motar dake parke a parking lots, barad daya zagayo yana ganin motar kuwa shima ya saki jakarshi a wajen ya ruga da gudu cikin gidan tsabar murna ya soma kiran ‘’daddy!! Daddy is back’’
Kwasar jakarsa maid dinshi tayi kafin ta shige ciki, hidaya na gaba suna biye da ita a baya harta shige cikin gida.

Su afiya na zaune a second sitting room suna zaman da suka saba na kallo da ci, barka da zuwa sukayi mata kafin ta wuce, suka bita da idanu, afiya dai har yau a kule take da alamarin yayar tasu, wani sa’in kuma inta tuna da rayuwar su a baya sai taji wani irin tare da tausayin yayar tata don tun bayan mutuwar ummuh ta koma wata iri gaba daya don tana masifar son ummuh dinsu sosai, yanxu kuwa she’s not friendly at all,komai harshly take yinshi, dama dama su kannenta ma, suna samun wani soft side of her.

Saman ta wuce direct zuwa, koda ta karaso saman saida ta dan tsaya ta dubi part din big baby, ayanxu ta tabbatar yana barci don haka ta wuce bedroom dinta kawai.

Da sallama ta shugo parlorn part din nata, da barad taci karo da wani babban mutun sak kamar barad din har kamarsu ta soma baci, wasa sukeyi sosai mutumin na mashi chakulkuli barad na dariya yana fadin ‘’daddy stop daddy!!’’
Kallonsu hidaya tayi kafin ta kauda kanta gefe ta nufi hanyar bedroom dinta, mutumin da barad ya kira da daddy ne ya kalleshi kafin yayi sqeezing face yace ‘’wake squeezing face kamar haka’’ kyalkyale da dariya barad yayi harda buga kirjin dadyn nashi yace ‘’that’s mummy’’ nan take suka kyalkyale da dariya,
Saida suka tsagaita kafin barad ya kalli dadyn nashi yace ‘’daddy please zan iya ganin uncle taj? I missed him so much I want us to play, daddy Please please ‘’
Shuru dadyn yayi kafin ya shafa kanshi cikin lallami yace ‘’I’m sorry barad, uncle baya jin dadi kaji? He needs medical attention ka bashi time tukunna, ka tuna last time abunda ya faru ko?,’’
‘’but daddy inason naje wajenshi’’
‘’no barad you can’t mummy zatayi fushi dakai, you can’t play with him for now, ka manta that little incident daya faru’’

Sauke kanshi kasa barad yayi cikin rashin jin dadi don shine yayi causing, ‘’yes daddy,but I’m sorry bazan kara hakan ba’’
‘’yes you made a mistake ka bude kofa ka fito da uncle kunyi wasa ya fadi a bene,shiyasa mummy bazata bari ba, and I’’m hoping bazaka sake hakan ba’’
‘’Yes daddy’’
Ya amsa mashi ‘’good boy,’’
mikewa daddyn yayi yana mai nuna mashi hanyar bedroom dinshi yace ‘’go and freshen up boy, kana yin tsami’’
Dariya sosai barad yayi kafin yace ‘’dad sunkuyo na fada maka wani abu’’
Rankwafowa mutumin yayi barad na ganin haka kuwa ya kama fuskan dadyn nashi ya dannan hammatarshi a wajen, nan take daddyn ya soma kakarin amai da wasa, nan take suka kyalkyale da dariya, yanda suke communication da juna gwanin burgewa don daga gani akwai soyayya mai karfi tsakaninsu.

Yana wucewa daki ya sauke wata ajiyar zuciya kafin ya nufi bedroom din nasu, da sallama ya shiga cikin bedroom din, da ita yayi arba, tana tsaye tana kwance takalmin kafafunta data nannde kafafunta da igiyarsu, karasowa yayi cikin kulawa ya zauna bakin gadon, tunda ya shigo bata dago ba haka zalika ba tace mashi kala ba.

Fuskarshi a hade ya nufi hanyar dresser ya soma kwance tie din dake wuyanshi, saida y agama ya cire agogon hannunshi ya ajiye kan dresser din kafin ya zame belt din kugunshi, yana gamawa ya wuce cikin closet ba tare da yace mata ci kanki ba itama kuwa bata tanka mashi ba saima kokarin zare takalmin nata da takeyi, tana gama warware igiyar ta mike da takalmin a hannunta ta nufi closet room dinsu, juyowa yayi ya mata kallo daya kafin ya cigaba da zame wandon daya rage mashi, itama kallo daya tayi mashi ta wuce wajen closets dinta, duk wani accessories dinta ta soma cirewa kafin ta maida dubanta gareshi yana kokarin daura towel a kugunshi, ‘’ka dawo ashe’’
‘’yes’’ ya bata amsa kai tsaye kamar bashine y agama wasa da barad ba,
Daga yanda ya amsa mata tasan cewa daga inda suka tsaya Kenan zasu cigaba, kamar yanda ta saba gaslighting akan mutane dukda duk yanda taso tayi akanshi ya gagara don shi baya yin shuru kwata kwata shiyasa take shakkansa sosai, ‘’wai meysa bazamu tsaya on a one page ba eh,as my husband abunda nafi buqata shine support dinka bawai ka dunga….?’’

Tsagaitawa yayi daga abunda yake ya juyo ya mata kallo daya kafin ya girgiza kanshi ya cigaba da abunda yakeyi, tana ganin haka ta cigaba da Magana…..
‘’I made you who you are today Jamid, your parents your siblings, kowanen su suna under my wealth shelter meysa kai bazan juyawaka yanda nake so ba? Why can’t you support me kodan saboda……..’’

‘’’hidaaaaaaayaaaaa!!!
Ya daka mata wata uwar tsawa daya sata yin gum ta zuba mashi idanunta da sukayi jaa sosai,
‘’point of correction, you don’t owe me, because I’m your husband, and we have two different personalities, bazaki taba sakani abunda banyi niya ba, I will never work for you nor under you,kuma duk abunda nasan kinyi ba daidai ba saina fada maki, so keep that in mind’’ yana kawai ya fuce daga dakin.

Yana futa ta doka wani uban tsaki kawai ta cigaba da abunda take, what she wanted from him was just an apology ‘’I’m sorry’’ saidai bata jin zata taba samu daga wajenshi, don tana masifar shakkarsa sosai, bata kawo mashi wargi ko kadan ita kanta ta rasa dalili.

Karfe tara daidai ta fito daga closet room cikin shirinta na kwanciya,yau ko sauka kasa yin dinner ma batayi ba, babu abunda take sai kamshi mai dadi sosai, tana sanye da sleeping dress baqa mai sirirn hannu kamar vest wadda ta sauko mata har wajen gwaiwarta
Akwance ta taddashi ya bata baya don he’s not ready for her drama, itama kuwa kwanciyanta tayi ta juya mashi baya.

Sunyi nisa sosai cikin barcin wayarta dake gefen bedside ta soma ruri,karar wayan yakai kusan minti goma yana yi saida jamid ya mike zaune ya dubi inda take kwance ‘’hidaya!! Hidaya!!’’
‘’uhm’’ ta amsashi don barcin nata baiyi nisa ba,
‘’ki tashi mana, bakiji wayanki na kara bane’’
Tsaki tayi kafin ta miqa hannunta ta miqe zaune, duban screen din wayar tayi kafin ta shiga app din dake detecting warning alert din gidan, rai adan bace tace ‘’what sort of nonsense is this’’
Dubanta yayi kafin yace ‘’whats the issue’’
‘’Big baby ne’’ ta bashi amsa kai tsaye rai a bace.
Yana jin haka hankalinshi ya tashi lokaci guda ya mike tsaye ya zura bedroom slippers dinshi ‘’haba hidaya, yanxu kinsan cewa warning alert din dakinsa ne shine kika zauna calmly kamar ba komai ba? What if wani abu ne ya faru?’’ yana kaiwa nan baima bi ta kanta ba ya fuce daga dakin rai a bace.
Yana fita saida ta dauki kusan minti biyar kafin ta miqe ta bi bayanshi.

Direct part din big baby ya nufa kai tsaye, yana zuwa a gaggauce ya danna pin din dakin ya shige ciki.
Daga yanda yake sassarfa zaka gane hankalinshi a tashe yake, dakin ya bude tare da danna light din dakin, nan take ko’ina ya bade, jefa idanunshi ya soma yi cikin bedroom din nan take ya soma jin sound din kukan shi sosai, yana daga zaune bakin gado daga chan sako ya nannade jikinshi gaba daya.
Karasowa daddy barad yayi inda yake kafin ya tsugunna a gabanshi,
‘’Taj!!! Taj!!!, calm down okay?’’
Dagowa taj yayi jikinshi sai faman kyarma yake kamar wanda ya kwana yana zazzabi, idanunshi gam ya kullesu, farar rigarshi kuwa ta baci da jini da alamu ya yanke hannunshi da wani abun ne,

Dafa kafadar shi daddyn barad yayi kafin yace ‘’taj open your eyes, it’s me, uncle jamid’’
Saida yaji hakan yayi saurin bude idanunshi, dukda ya gane uncle jamid din hakan bai sashi ya dawo daidai ba, hakoranshi sai faman gogayya suke da juna kaf kaf tsabar tsoro.
Ture hannunshi dake kafadarsa ya somayi bakinshi na karkarwa ya soma ihu ‘’no no, I’m scared, first love please help me’’

A daidai nan hidaya ta shugo dakin, tun daga nesa ta tsaya ta harde hannayenta tana sauraron yanda jamid keta faman rokonshi akan he should calm down don gaba daya ya hade jikinshi waje daya kamar wanda za a yanka, saida ta shafe yan sakanni kafin ta karaso inda suke.
Zama tayi bakin gadon nashi kafin ta soma Magana ‘’big baby’’
Yana jin sautin muryarta ya bude idanunshi tar akanta, rarrafawa ya somayi har zuwa inda take kafin ya rungume kafafunta, gaba daya y agama burkicewa babu abunda yake sai kuka ‘’first love don’t leave me alone, stay with me please, I’m scared.’’

Tunda ya soma Magana bata ce kala ba saima kallon suman kanshi data soma fitowa datayi, ga kafarta daya qanqame kamar her life depend on it, ga laps dinta daya jiqa da hawaye.

Jamid dai kallonshi yake cikin tausaywa da kaunarsa, aduniyar nan bai bata ganin wanda ke qaunar yar uwarsa kamar yanda taj ke kaunar hidaya ba tun kafin wannan lalurar ta sameshi, tun tasowarshi da girmashi bashida kamar hidaya gaba da baya, babu wanda ya isa yayi comparing hidaya da kowa don tana da space na musamman a zuciyarshi dukda yanxu ya samu wannan amnesia din hakan bai sashi identifying dinta ba, kaunarta kuwa taa nan daram a cikin zuciyarshi.
Haka zalika har a yanxu ma babu wadda ya yadda da sai hidaya, ita kadai ke iya controlling dinshi.
Sun dauka kusan minti biyar a haka kafin hidaya ta soma shafa kanshi, ‘’shuuu, stop crying I’m here’’ ..Ta fada tana mai dago fuskanshi da yayi gaja gaja, ‘’wipe those tear’’ ta bashi umarni, nan take kuwa ya soma goge hawayen nashi yana gamawa ya kamo hannunta ya riqe gam cikin nashi, har zuwa lokacin yana tsugunne a gabanta, wayarta dake rike a hannunta ta dauka ta soma dialing number head.
Head dake ta faman sheka barcinta tana jin karar wayarta tayi zumbur ta mike, ganin sunan madam yasata saurin daga wayar cikin hanzari tana kokarin goge miyau din dake yawo a gefen bakinta.

‘’yes madam’’
Daga chan bangaren ne aka soma Magana, tana cikin sauraron madam din tayi saurin miqewa hankali atashe, dan blanket veil dinta ta janyo ta yafa akan rigar baccin dake jikinta kafin ta zura takalminta ta fuce daga dakin da take kwana,
Bangaren maids din gyare gyare ta nufa direct, tana shiga ta kunna futilar dakin kafin ta buga masu kofar dakin yanda duk zasu tashi
A furgice kuwa duk suka tashi, kallonsu ta soma yi daya bayan dayan kafin ta maida dubanta ga gadon sabeeha ‘’where’s this new maid, you!!’’ ta yi nuni da sabeeha dake faman rarraba idanu,
‘’fito’’
Ta bata umarni, hankali a tashe sabeeha ta miqe, sanye take da hijab dinta sai janyoshi datayi ya rufe mata fuskanta ya rage idanunta ne kawai a bayyane,
Futa head tayi kafin tabi bayanta hankali a tashe, sauran maid kuwa babu abunda suke sai tsaki bayan futarsu saboda tashinsu da akayi cikin tsakar daren nan wajen karfe uku, gashi zasu tashi da wuri,

Suna fitowa head ta dubi inda sabeeha take tace ‘’what mess have you caused? Matsalata da irin ku black people dinnan idan kuna abu kamar marasa kai, just simple instruction baku iya bi ba?, now what stupidity have you done?’’

Tunda suka fara tafiya head take surfa mata masifa ita kuwa baiwar allah gaba daya hankalinta baya kan maganganun head din don hankalinta a tashe yake, babu abunda take sai tambayar kanta shin me tayi? Gaba daya jiya ta fara aikin fa? Hartayi abunda ba daidai ba.

Suna karasowa part din headmaids ta fara shiga ciki sabeeha na biye da ita, zuciyarta na faman lugude tsabar tsoro, koda suka karaso bedroom dinshi head ta tsaya ‘’ki shiga’’
A tsorace sabeeha ta sanya hannunta kan mabudin kofar kafun ta shiga bakinta dauke da sallama, jamid ne kawai ya amsa sallamarta da mamaki, kallonta yayi daga sama har kasa kafin ya dauke idanunshi daga kanta.
Mikewa hidaya tayi, taj na ganin haka shima ya miqe yana mai kokari kamata da kyau, kallonshi tayi ‘’big baby seat down’’
Tana fadin haka kuwa ya zauna anan kan gadon idanunshi na kanta don baya son ta tafi, takowa ta somayi har inda sabeeha take kafin ta daga hannu ji kake tasss tass tass, ta kwashe sabeeha da maruka both sides din fuskanta, cikin sauri jamid ya karaso inda suke ya janyo hidaya baya rai a bace yace ‘’hidayaaa’’

Hannu ta daga mashi rai a bace, akan me zai jata baya tana kokarin saitama wannan dumbhead din kai, lokaci guda sai bacin ranta ya koma kanshi, bata kaunar irin abubuwan da yake mata wanda babu wanda ya isa yayi mata irin haka sai shi, Taj dake zaune kukan sabeeha na mashi eco a kunne, kasa hakura yayi dole ya miqe tsaye baima san ya tashi ba ya nufi inda suke,take shima ya soma hawaye yana jan hannun hidaya ‘’first love please I’m sorry, don’t hit her please, she’s our friend remember?’’
Haka ya dunga maganganun da baima san me yake cewa ba yana jan hannun hidaya irin yanda yara keyi, ‘’stop it’’ ta daka mashi tsawa, ‘’go back and seat down’’
Wannan tsawar datayi ba karamin abu bane a wajen taj, don baya kaunar yaga tana fushi dashi ko kadan, nuni tayi mashi da gadon shi,

Saurin sakin hannunta yayi ya nufi gadon ya zauna kanshi a kasa, har wani irin zazzabi ne ya rufe shi lokaci guda, ga wani azababben ciwon kai daya kawo mashi ziyara, jikinshi har rawa yake ga jijiyoyin kanshi da suka fito rado rado.

Saida ya zauna hidaya ta maida dubanta ga sabeeha kafin tayi kwafa ta fuce daga dakin rai a bace.

Bayan futarta jamid ya dubi sabeeha dake kuka innocently harda shesheka abun tausayi, ‘’I’m sorry about that okay?bansan me kikayi ba but Please be careful next time okay?, ranta ne ya baci sosai that’s why tayi acting that way’’
Tsagaitawa sabeeha tayi da kukan tana sauraron yanda yake Magana anatse cikin mutunci, girgiza mashi kai kawai tayi alamun gamsuwa
‘’you’re the new caregiver right?’’
‘’yes sir’’ ta amsa shi.

‘’please work on his injuries okay?’’
Girgiza mashi kai sabeeha tayi kafin ya fuce daga dakin ya barta a tsaye.
Sauran hawayen dake kan fuskanta ta goge, kafin ta maida dubanta ga inda yake zaune a bakin gadon ya runtse idonshi gam jikinshi na faman karkarwa.
Takowa ta soma yi anatse har zuwa inda yake zaune, tsugunnawa tayi a gabanshi tana mai kallon fuskanshi, kawai saita fashe da kuka ganin yanda fuskanshi yayi jaa sosai ita a tunaninta shima ko bugunshi akayi, har zuwa lokacin bata san taqamaimain laifin datayi ba saidai koma menene ta yanke shi ne a dalilinshi ne.

Idanunshi ya bude ya sauke akanta yana kallon yanda take kuka, hannunshi ya dago ya dora akan fuskanta, hannun nashi dake kan hijab din fuskanta tabi da kallon, wani irin dumi ne taji ya ratsa fuskan nata wanda ke futowa daga tafin hannun nashi ‘’don’t cry for me friend’’
Runtse idanun ta tayi ta dora hannunta akan nashi dake fusknta, wani irin zafi taji sosai kamar wuta, hannunshi is so soft kamar bai taba amfani dasu ba.
Sun dauki kusan minti biyu a haka, ta kasa sauke hannunshi daga kan fuskanta, ga wani mixed feeling dake shiga cikin jininta, lokaci guda ya shiga ranta sosai, tausayinshi ya gama yi mata katutu arai, da zuciya daya taji tana son shiga cikin rayuwar shi ta hanyar taimakonshi da kulawa dashi don iya abunda zatayi mashi Kenan.
Bakinta na rawa ta soma Magana ahankali cikin muryarta mai kwantar da hankali
‘’sir, you’re burning up,’’
Zame hannun nashi tayi daga kan fuskanta ta maida dubanta ga hannun nashi, jinin data gani ne yasa ta tuna da maganar wanda ta tarar tare da madam wanda take tunanin shine mijinta,
Mikewa tayi tsaye yana ganin haka shima ya miqe yana mai jan hijab dinta, kallon hannun nashi tayi kafin ta daga kanta don ganinshi, ‘’I’m scared friend bazan iya zama ni kadai ba’’
‘’zaka rakani?’’
Girgiza mata kai yayi kafin ya sauke mata murmushin sa mai tsada, wanda ya sata kasa dauke idanunta akanshi, yanda yake murmushi zaka rantse lafiyar kalau, he looked so matured.

Batace komai ba ta nufi hanyar fita yana biye da ita har suka wuce zuwa kitchen, bin hanyar ya dunga yi da kallon kamar yau ya taba shiga wajen, suna shiga kitchen ta nufi wajen da taga first aid box, janyowa tayi ta soma budewa kafin ta zaro spirit da cotton wool harda wound plaster.
Komawa sukayi dakin yana biye da ita a baya har suka karaso bakin gadon, ‘’seat down friend’’
Tana fada kuwa ya zauna, tsugunnawa tayi tana mai kallon hannun nashi, mika mashi hannunta na dama tayi yana ganin haka kuwa ya daura hannunshi akan nata, goge mashi hannun ta soma yi da spirit, ‘’ouch’’ ya furta
A dan furgice sabeeha tace ‘’sorry, sorry akwai zafi ko’’
Girgiza mata kai yayi, haka ta gyara mashi hannun kafin ta saka mashi plaster, tana gamawa tace ‘’ka kwanta kayi barci friend’’
‘’no I don’t want to, nasan tafiya zakiyi kamar yanda first love ta tafi, I’m scared don’t go please’’ ya fada cikin rada, ganin haka ya sata zama a kasa tace ‘’bazan tafi ba friend, ka kwanta to’’

Tana fadin haka kuwa ya kwanta, dan motsawa tayi yana jin haka yayi saurin kamo hijab dinta ya riqe gam,
Haka suka zauna yana kallonta tana kallonshi, gashi idanunshi tarr yaqi yin barcin saboda baya iya barci dole saida maganinshi shiyasa ba a skipping lokacin maganinsa, ganin kusan har karfe hudu yasa ta miqe tsaye,yana ganin ta miqe kuwa shima ya mike har yana kokarin karo da ita, matsawa tayi baya kadan kafin tace ‘’toh ka bari nayi sallah’’
Da mamaki yake kallonta yace ‘’no firnd zaki tafi ki barni ne, lets go together’’
Shuru sabeeha tayi tana tunanin yanda zatayi dashi, don taso ya barta ta futa ta koma part dinsu ko alwalar ne ya barta ta dauro saita dawo nan, ganin hakan bazaiyuwu ba kawai ta nufi hanyar bathroom dinshi a tsorace.
Yana biye da ita a baya ta tsaya tana bin bathroom din nashi da kallo, kallonda batayi ba bathroom din ba daxu, komai fari qal qal ya hadu ba kadan ba, zata iya rantsuwa akan bata taba ganin bathroom mai girma sosai kamar daki irin wannan ba,.. wajen wash hand basin ta nufa yana biye da ita, alwala ta dauro yanata kallonta hart agama, tana idawa ta juyo sauran kiris su gwaru don suna dab da juna.

‘’muje toh’’
Matsa mata yayi ta wuce kafin yabi bayanta kamar jela

Please Login or Register in order to submit comment