Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan zaisa ya sha, ai kuwa bata gama karashe maganr bama ya juyo ya zuba mata idanunshi, idanunshi da sukayi jaa ya zaro mata shi “zatayi fushi sosai?”
“Eh zatayi fushi dakai sosai”

Sauke idanunshi yayi kasa irin yanda yara keyi kamar bazaice komai chan kuma ya hadiye wani irin miyau mai daci a bakinsa
Hannunsa ya miqo mata, hakan yasa ta ajiye mashi bowl din a akan lap dinshi.
Kallon bowl din yayi kafin ya runtse idanunshi ya soma diban soup din yana kaiwa baki daga yanda yake sha zaka gane baya so kwata kwata kuma baya mashi dadi a baki, saida yasha kusan rabi kafin ya maido da dubanshi gareta yace “friend ya isheni”
“Saura kadan friend ka shanye please kaji? Bana son first love tayi fushi okay?”

Haka nan ya cigaba da sha harya shanye tas da kyar, sabeeha na ganin haka tayi saurin karban bowl din tace “yauwa friend,”
“Friend zanje toilet please i what to pee”
“Okay tohm” sabeeha ta amsa shi tana dan yin baya don ta bashi hanya ya wuce.

Kafafunshi ya soma saukewa kasa kafin ya miqe, taku daya yayi ya soma yin baya kamar zai fadi, cikin hanzari sabeeha ta karaso ta kama hannunshi, wani irin zafi taji dayasa ta sakin hannun ta kalli fuskanshi, layi taga ya soma yi wanda ya sata tsorata lokaci guda ta sake taba hannun nashi, yanda kasan daman neman makafa yake gaba daya ya sakar mata jikinshi, wani irin wahalallen nunfashi ta sauke “ wayyo allah na, zaka karyani”
Tururin da jikinsa ke fitarwa yasa hankalinta ya koma kanshi gaba daya “friend are you okay?, jikinka akwai zafi,”
Baya jin abunda take fada ma gaba daya saboda yanda gaba daya yaji wani irin dummm a kunenshi lokacin daya miqe
“Zanyi pee”

Da taimakonta suka karasa cikin bathroom din, hannunshi har zuwa lokacin yana cikin nata, koda yazo yin pee din ita ta taimaka ta zare mashi mazugin tana kauda ido kafin ta fuce daga bathroom din.

Dakin ta koma ta kwashe bowl din kafin ta fuce zuwa kicin.
Ta dan dade kafin ta dawo cikin dakin saboda wanke bowl din datayi, da mamaki ta karasa bathroom din ganin kamar bai futo ba, knocking ta fara yi, jin shuru yasa ta cewa “ka gama?”
Nan ma shuru babu response, hankalinta ne ya soma tashi,bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta bude kofar ta sa kai ciki, ganinshi a kasa helplessly yasa ta karasowa cikin sauri, babu abunda yake sai kakarin amai gashi aman yaqi zuwa, da sauri ta karasa inda yake ta tsugunnawa, gaba daya ya gigice, babu abunda yake sai kuka, yana jinta a kusa dashi ya nanukota, jikinta har rawa yake.

Daburcewa sabeeha tayi hartama fi shi shiga tashin hankali ganin yanda yake faman tura jikinshi ga nata, aman dake maqale a moqogoron shi ne ya soma zubowa, gaba daya ya amayar da wannan soup din a jikinta wajen gaban rigarta, baiwar allah ko kyankyaminsa bata ji ba saima dabbing bayanshi data dunga yi, struggling sosai ya dunga yi wajen amayar da abunda ke cikinshi tass, ga jikinshi yayi wani irin zumm sosai.
Saida ya gama tass kafin komai ya dan lafa mashi ya kwantar da kanshi a kafadarta jiki a mace ,gaba daya ya gama batasu daga shi har ita, “friend i want to see first love please,”
Fashewa yayi da kuka don daman idan yana rashin lpy irin wannan indai ba hidaya ya gani ba sai yayi ta kuka.

Wani irin kuka ne ya zo ma sabeeha, allah ya bata wata iriyar raunaniyar zuciya mai rauni, tana da tausayi sosai, musamman idan taga mara lpy, lokacin da aka tafi da inna asibiti kwana tayi tana kuka, duk da zaman su da inna ba wani dadi yake ba hakan baisata tausaya mata ba lokacin da za a kaita asibiti, balle kuma wannnan daya gama shiga ranta saboda lalurar shi,
“I’m so sorry friend, wallahi bansan ranka baya so ba da bazan baka ba, i’m so sorry please kaji”

Sun jima anan zaune, gaba daya ta zama kamar wata yar tsana a zaune gashi ya rufeta ruff da girman jikinsa daman gata ba tsayin kirki ba ga dan jikin nan nata.
Saida taji ya daina kukan kafin itama ta tsagaita, miqewa ta soma yi ya ruko hannunta “don’t leave me please, karki barni yanda first love ta barni, stay with me, i don’t want to be alone”
Wannan furuci nashi ba karamin narkar mata da zuciya yayi ba don saika rantse mai hankali ne yayi maganar, tasan yana da rashin lpy amma kuma bata san dalilin dayasa kullum yake daki ba dukda ta yanke hakan saboda rashin lafiyarshi amma harga allah yana buqatar yan uwanshi a kusa dashi koba komai shima mutunne kuma yana da zuciya ta dan adam bai chan chanci wannnan ba, saidai tunawa da kaddarar sa kenan yasa ta jin wani irin.

Hannunshi da jijiyoyinsa da suka futo rado rado ta zuba ma idanu don fatarsa fara ce tass, samun kanta tayi ta komawa ta tsugunna a gabanshi ta riko hannunshi “bazan barka ba friend, i promise,”
Murmushi kawai yayi mata kafin ta taimaka mashi ya miqe zuwa wajen basin, wanke mashi baki tayi da kanta kafin ta rakashi har bedroom ya kwanta ta jawo mashi duvet ta rufe shi.

Toilet din ta koma ta gyara shi tsaf sannan ta gyara gaban rigarta daya bata mata kafin ta futo, lokacin data fito har ya soma barcin wahala, sai a lokacin ta tina baisha maganinsa ba, don dole badan taso ba sai dan tsoron kar abunda ya faru kwanaki yasa ta soma tashinsa ahankali, maganin ta bashi yasha kafin ya koma,

Zama tayi daga chan gefe a kasa ta hade kafafunta a kirjinta ta zuba mashi idanu.
He look so innocent, daga yanda yake barcin ma kasan a wahale yakeyi don daga ganin yanda yake furzar da numfashi zaka san yana jin babu dadi.

Zaman awa kusan biyu tayi barci ya soma daukan ta tana gyangyadawa har ya fuzgeta, ba ita ta farka ba sai wajen karfe daya, cikin sauri ta tashi zuwa bakin gadon sa, yanda ta barshi haka ta taddashi yana barci peacefully, ko gyara kwanciyar baiyi ba yana mai fuskantar ceiling, jikinsa kwata kwata baya motsawa badan nunfashi da takeji yana futarwa ba zata rantse ko matacce ne, gaba daya jikinsa ya saki.

Taba shi ta soma yi a hankali, don jin ko da zafi jikin nashi, bataji wani zafi ba hakan ya tabbatar mata ya sauka zazzabin nashi, hamdala tayi ta dauke hannunta daga wuyanshi.
,Futa tayi daga dakin ta sauka kasa zuwan part dinsu don gabatar da sallar dhuhur.

Saida ta idar da sallah yar ghana ta shugo bangaren su, murmushi sabeeha tayi mata don yanxu sun saba sosai, “kin dawo?” Yar ghana ta tambayeta.
“Eh na dawo,mouryoum” (sunan yar ghana kenan)
“Ay nazo dazu inata nemanki ban sameki ba, ashe baki dawo ba, kinsha aiki”

Hijab dinta datayi sallah dashi ta nannade tana mai sauraron yar ghana, “ayyuka ne sukayi min yawa yau shiyasa ban sauko ba”

Kallon dakin yar ghana ta soma yi, ganin sauran yan dakin basa nan yasa ta jan sabeeha zuwa bakin gado ta zaunar da ita kafin tace “sabeeha niko inason tambayar ki wani abu out of curiosity”
Zama sukayi bakin gadon sabeeha kafin yar ghana ta cigaba da magana “dan allah menene a saman nan?,”
Atsorace sabeeha ta kalleta tana mai kokarin karantarta “meysa kike son sanin abunda ke saman?”
“Ba komai, I’m just so curious, ki fada min kinji”
“Ni bansan menene a saman ba” sabeeha ta bata amsa tana mai kauda kanta gefe, cije lebe kawai yar ghana Tayi kafin tace “zan baki kudi in kika fada min”

Wani tunani ne ya zoma sabeeha, ta kasa gane wannan yar ghana din da yanda take yawan tambayarta da bugar cikin ta akan al’amuran dake sama, kullum zille mata takeyi ta hanyar fada mata bata sani ba saidai yanxu ta fara bata tsoro don yawan tambayar nata yayi yawa, wata dabara ce tazo mata wadda batama san ta iya ba.

“Ni gaskia ban sani ba, amma nasan head ta sani idan kinaso zaki iya tambayarta saita fada maki”
Hankali a tashe yar ghana tace “ah ah bazan iya tambayarta ba ni fa daman kawai I’m curious ne”

Tabe baki sabeeha tayi kafin ta miqe tace “ki bari toh ni zan tambayar maki ita”
“Ki rufa mana asiri, wannan maganar zaisa a koremu daga ni har ke”
Toilet sabeeha ta wuce tana kunshe dariyar data zo mata, yanxu ta kara tabbatar da wannan yar ghanar tana da gulma sosai.


Hidaya!!!!
Anatse ta futo daga office, hannunta riqe da jakarta, employees dinta gaba daya babu abunda suke sai gaisheta, ko sau goma kuwa zata sauko sai sun sake gaisheta wannan policy din da kowa ya daukar ma kanshi kenan gudun kar a koreshi, wani baqin shade ne akan fuskanta, tasha mur bakin nan yasha red matte lipstick, yau dai a bossy hidayarta tazo office din, basement ta sauka wajen private parking lot dinta, key din dake hannunta ta danna Nan take blue LV car dinta ta hau kara, tana karasowa inda motar take ta bude tare da shigewa ciki, har zuwa lokacin wayarta ruri takeyi, Jakarta ta wulla gefe kafin ta kunna motar.

Connecting wayarta da motar tayi kafin tayi reverse, maganganu ta soma yi cikin turanci, kafin call ya shiga, harkar smart digital kenan, nan take call din ya shiga, ringing daya akayi picking, “go and pick up barad”
tana kaiwa nan ta futo da haddaiyar motar tata daga basement din, gate din futa daga wajen ma daban ne don an kebar da wajen just for ceo.

With high speed ta hau kan titi tana murza steering, kallon dash board din motar tayi ganin call na sake shigowa da wata unknown number, kara speed tayi kamar zata tashi ranta a mugun bace, tafiyar minti ashirin tayi ta karaso wani beach, sai a lokacin ta rage speed din motar tata, wata hanya tabi daga gefe inda ya kaita har wajen jiragen ruwa na cruise sai na wasu containers, daidai wajen tayi parking kafin wasu armed guard sukazo suka amshi key din don yin parking, bata tsaya amsa gaisuwar su ba ta wuce wajen tafkeken boat dinta, mutanen dake kula da boat din na ganinta sukayi saurin karasowa suna duqa mata, “welcome ma’am” ba tare data amsa su ba tace code 5
Sanin mai hakan ke nufi yasa sukayi saurin bin bayanta, nan take suka soma kunna engine boat din cikin gaggawa,
Ita kuwa tana shiga ciki ta samu waje ta zauna, fadin irin tsaruwar cikin boat dinma bata lokaci ne yanda kasan gida, babu abunda babu aciki ga girma.

Tundata zauna take girgiza kafafunta da yasha zobunan kafa kaf kaf, shade din fuskanta na nan gar zuwa lokaci, bini bini take duban agogon dake hannunta, saida suka dauka wajen awa guda kafin jirgin ya tsaya, kamar jira take kuwa tayi saurin miqewa ta dauki jakarta ta futo cikin qasaita.

Kallon wajen ta soma yi, yau wajen wata guda kenan rabonta data zo wajen nan sai gashi wannan useless mutanen nan suna son su saka mata ciwon kai.
Island ne mai shegen girma sai wani tafkeken gidan guda daya tal da ake hango shi daga nesa, gaba daya ciyayi ya rufe gidan, wajen nada shegen girma kamar daji.

Futowa tayi ta nufi hanyar cikin island din ko tsoron wajen bata ji, ni kaina mai kawo maku rahoto saida na danji tsoro, baka jin komai sai kukan tsintsaye da ciyayi.

Daidai bakin gate faya zagaye gaba daya wannan dajin ta tsaya tare da scanning kanta, nan take gate din ya bude,inda motar dake parke a wajen ta karasa, driver dake zaman jiranta yana sanye da uniform fari kal ne ya bude mata kujerar baya, zama tayi ta hakimce kafin ya rufo kofar.

Hannu ya daga mata ya rissinar da kanshi alamun gaisuwa kamar he’s deaf baya ji, hannu kawai ta daga mashi yaja motar suka miqi hanyar.
Sun kai wajen minti biyar kafun su karaso gaban wannan babban gidan dana hango daga bakin island din.

Gida ne babba sosai ba karami ba, bata ma jira driver ya bude mata kofa ba ta futo.
Taku dai dai takeyi harta karaso bakin kofar shiga gidan, thump print dinta ta saka kofar ta bude.
Abun mamaki daga waje dai gida ne mai kyau saidai daga ciki babu komai empty, takun tafiyarta yasa suka juyo a rikice, maza ne su kusan hudu gabzaza suna zaune akan kujerun karfe suna cin abuncin, suna ganinta kuwa suka mimike tsaye sukayi layi kafin su soma sunkuyar da kansu, “welcome ma’am”
Bata amsa su ba ta tsaya a gabansu, daya bayan daya ta bisu da kallo rai a bace, daya daga cikin su ne ya dauki kujera ya ajiye mata daga gefe kafin ya koma gefe ya tsaya wajen da sauran suke tsaye.

Kallon kujerar tayi kafin ta kaida dubanta ga abuncin da suke ci, lokaci guda taji wani maqoqon bakin ciki ya zo mata, takowa tayi inda suke har gaban wanda ya ajiye mata kujera, babu zato babu tsammani sukaji tasss tass har sau uku, saurin dafe wajen yayi sauran na ganin haka sukayi kneeling a gabanta,
“Har kuna da time din cin abunci?,shin kunsan problem din dake gaban mu idan har ya tabbata akwai wanda yasan da wannan al’amarin?”

Wanda ta mara ne yayi saurin duqawa shima, “we’re sorry ma’am”
“Sorry will not fix this? Wani irin useless mutane ne ku da bazaku iya aiki ba tare da kuskure ba? Looks like kuna son nayi wiping dinku ne?”

A tare suka soma cewa “no ma’am”
“Now tell me how did you handle it?”

Rarraba idanu suka somayi daya bayan daya suna kallon juna, ogan su ne yayi karfin halin cewa “madam kinsan bamu taba yi maki kuskure ba, kuma na tabbatar maki wannan karan ma bamu bar any lead da zai nuna cewa intentionally hit and run ac….”

Shade din fuskanta ta cire,bacin rai kwance a idanunta, dukda sun tabbatar mata basuyi wani mistake ba tana jin this is not right,”

Wani irin disgusting kallo tayi masu a kaskance bayan ta dakatar dashi kafin tayi pointing dinsu daya bayan daya da hannunta “be sure of what you said, don wallahi kusan abunda zai biyo baya idan har kunyi wani kuskuren”

Tana kaiwa nan ta fuce daga cikin gidan tana furzar da nunfashi mai zafi, idanunta har wani kif kif sukeyi tsabar masifa.
Tana fita kuwa suka miqe taaye suna kabe wandunan su.

“Kai wannan matar fah kamar she’s a psychopath, zata iya yin komai wallahi,”
Ogan su ne ya kalli wanda yayi magana kafin ya shago wuyanshi yace “ba saida na fada maka kan cewa karkace komai ba? “
“Sorry sir”
“Ina footage din, yau babu wanda zaibar wajennen, inason mu sake duba footage din again and again”
“Yes sir”



Karfe uku da rabi daidai sabeeha ta koma part din, dakinsa ta wuce direct bakinta kunshe da sallama, tundaga bakin kofar dakin ta soma jin fitar nunfashinsa kamar yana battling da breath dinshi.
Karasowa inda yake tayi hankali a tashe, yana nan kwance kamar an qame shi, nunfashi sa ne kawai ke fita da kyar tsabar zazzabin dake cinshi.
“Friend friend are you okay”
Duvet din ta yaye mashi, ya jike jargab gaba dayanshi,tabashi ta soma yi don ya tashi don duk a tunanin maybe mafarki yake yi saboda ayanda yake nunfashin da yanda zufa ta wankeshi saida taji zafin ne ta gane cewa zazzabin da yayi dazu ne ya dawo mashi.
“Friend friend” ta soma kiranshi, shuru babu response, at that point hankalinta ya gaba tashi, gaba daya tama rasa ya zatayi, takai wajen kusan 30mins shuru babu response, wani tunani ne yazo ranta, to kodai ya suka ne? Ta tambayi kanta, bata jira bama kanta amsa ba ta wuce bathroom ta debo ruwa a bowl ta dawo bedroom din, wash cloth ta tsoma cikin bowl din kafin ta soma shafa mashi a fuskanshi, nan ma dai shuru, ta dade sosai tana goga mashi tana hawaye har ruwan yayi sanyi, lokacin ana maganar wajen karfe hudu, kamar da wasa ta dago taga idanunshi sun soma budewa, idon yayi jaa sosai,
Hamdala tayi kafin tace “meysa Kaqi tashi? Hankalina duk ya tashi na dauka wani abu ne ya sameka”
Da hausa tayi maganar so bai gane abunda take nufi ba don haka kawai ya zuba mata idanu, wannan ruwan data goga mashi a jiki ya sashi jin sanyi sosai, saida ya farka nema zazzabin yayi doubling, take ya fara karkarwa kaf kaf, hakoranshi na gogayya dana juna, burkice dai sabeeha ta burkice sosai don unexpectedly ya fara jijiga ba kamar dazu da yake barci ba kwata kwata baya motsawa, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun” ta furta ganin idanunshi na neman qafewa, “na shiga uku don Allah meke damunka? Ka fada min menene?zazzabin ne?”
Ta sake tambayarshi hankali a tashe, burgimar daya farayi ne yasa ta shiga wani sabon hankali, kankace me bata ankara sai ji tayi dimm ya fado kasa, cikin sauri ta nufi hanyar fita daga dakin harma part din gaba daya, karar dataji na futowa daga sitting room dake saman ne yasa kawai ta nufi wajen hankali a tashe kamar an jeho ta, fadwa dake zaune tana waya afiya kima na daga gefenta tana cin pizza tana kallo suka zuba ma sabeeha ido da mamaki, jikinta na kyarma ta shugo bedroom din.
Kallonta sukeyi afiya ce tayi saurin cewa “ke bakida hankali ne, wannan illiterate dinfa ko harda mahaukata ne suke mana aiki”

Fadwa ce data gane ta tayi saurin katse wayarta ta kalli afiya tace “thats new maid din big baby”
“Oh da alamu itama haukan ya taba kanta kenan” afiya ta fada sounding so annoyed
Fadwa ce kawai ta kalleta tace “me ya shugo dake?
“Madam, frien…. Sorry sir ne bashida lafiya”
Afiya ce tayi saurin cewa “daman wayace maki shi mai lafiya ne? Ni bansan wake kawo irin waennan africans din nan ba? They are the stupidest people”
Sauke kai sabeeha tayi hawaye na gangaro nata, fadwa ce ta sake cewa “go and do your job properly”
Jiki a Mace sabeeha ta juya ta fito daga part din, gaba daya ta rasa ya zatayi, wajen wa zataje? Tunawa da head yasa ta saurin sauka kasa tana hawaye, daidai hanyar dazai kaita ga dakin head tayi karo da yar ghana, kallonta yar ghana tayi ganin duk ta burkice yasa ta cewa “sabeeha? Are you okay?”
Sabeeha batama lura da ita ba ta wuce dakin head, ciki ta shige ta rufo kofar, duve dube ta soma yi ganin bata nan yasa ta saurin fitowa, a bakin kofa ta sake tadda yar ghana a tsaye, “ina head?”

“I dont know but maybe tana kitchen”
Kitchen din sabeeha ta nufa hankali a tashe, tana shiga ta hangota cikin sauri ta karasa inda take ganin babu kowa a kitchen din.
“Head, please ki taimaka min, sir bashida lafiya”

A burkice head ta soma duban kitchen din kafin ta janyo hannunta suka fuce daga kitcehn din, wani corridor sukabi inda take tabbatar da babu kowa a wajen kuma babu wanda zai jisu
“Ke bakida hankali? Wayace maki zaki iya wannan maganar a ko’ina? Shin kin manta you’re not to disclosed abunda ya shafe shi ba?”

“I’m sorry head, wallahi bashi da lafiya he’s sick”
Buge mata baki head tayi “and wayace maki daman mai lafiya ne shi? Ina mai baki shawara idan har kinason rayuwarki da lafiyarki dole sai kinbi yanda aka kayyade maki, dont ever step down and say a word about abunda ke sama”

Tana kaiwa nan ta fuce, sabeeha dai hawaye bata bar yinshi ba anan tsaye, wannan wani irin masifa ne haka, ayanda take ganin yanda yake wahala zai iya mutuwa wallahi, tunawa da kalamanshi da yayi mata dazu inda yake ce mata karta barshi yasa ta komawa zuwa saman, a daidai nan ta bakin kofar kitchen din ta hango yar ghana a tsaye ta labe,bata ma tsaya bi takanta ba don ba wannan ne agabanta ba yanxu ta wuce sama.
Koda ta karaso sama tana jiyo yanda fadwa da afiya ke hirarsu suna kallo, tsugunnawa kawai tayi ta soma hawayen takaici, dukda batasan alakarshi dasu ba amma yanda taga kammanin su ta tabbatar yan uwansa ne suma, ranta yayi mugun baci da yanda suka amsa ta lokacin data shiga wajen su, wannan wani irin ahali ne? Ta soma tambayar kanta? Ita tasan mara lafiya zama ake dashi shi kuma wannan gudunsa akeyi saboda wani dalilin daban wanda bata san koma menene ba saidai tana jin harga allah ba ayi mashi adalci ba.

Tana nan tsugunne dadyn barad ya karaso saman shida barad, daman shi yaje ya daukosa yau, tun daga bakin stairs ya fara jin sheshekar kukan nata, da mamaki kuma ya ganta a zaune bakin kofar dakin tana kuka.

“What’s going on here?”
Cikin sauri sabeeha ta dago kanta, ganin wanda ke gabanta ya sata miqewa cikin gaggawa, “akwai wata matsala ne?” Ya sake tambayarta

Kamar jira kuwa take ta girgiza mashi kai “sir please friend bashida lafiya”
Shuru yayi yana wani nazari, ganin yanda take kuka yasa shi kallon barad yace “go and freshen up okay?”
Yana kaiwa nan ya nufi part din taj, kofar ya bude sabeeha na biye dashi har cikin bedroom din, tun daga nesa ya hangoshi a kasa kamar matacce ga hannunsa daya ballaqe shi gefe, cikin hanzari kuwa jamid ya karasa inda yake ya juyoshi, jikinshi ya koma jawur, har zuwa lokacin karkarwa yake,
“Innalillahi, whats going on here? Me ya sameshi?”
Jiki na bari sabeeha ta soma bayani, “sir tun safe yake zazzabi bayan na bashi medication dinshi sai yayi barci By 3 na dawo zan bashi second dose shine naga baya motsi.

Duk rikicewar sabeeha bata kai jamid ba, jijiga taj din ya soma yi “Tajudeen hey hey!!! Open your eyes”
Ay Inaaaa taj baya ji kwta kwata, idanun nan sun rufe ruff, rasa abunyi jamid yayi, tunani kala kala Na yawo a ranshi, karshe dai kawai yayi deciding daukarshi gaba daya,
“Zoki taimaka min”
Matsowa tayi ta kama hannunshi don taimaka mashi, dakyar take jan hannun tana zufa harda nishi, haka nan jamid ya daukeshi duk da shi namiji ne dakyar ya daga shi ya sashi a bayanshi don yana da girma sosai masha Allah.

“Bude kofar” ya umarci sabeeha,
Kofar ta bude ya fito dashi a bayansa, sabeeha na biye dasu tana kuka har suka fito daga part din, suna nufin sauka kasa saiga hidaya ta hauro last stair,da mamaki take kallon abunda idanunta ke ganar mata, tabbas big baby ta hango a bayan jamid.
Ganin yana neman wuceta yasa ta saurin damqo hannunshi ta daka mashi tsawa kamar ba mijinta ba
“Jamiddddddd…whats going on here whats this? Are you out of your mind ina zaka kaishi?”

Yasan halinta don haka ya amsa ta “bashida lafiya he’s in a critical condition?”

“Wait what? Ina zaka kaishe then?”
Wata iriyar tsawa ya daka mata “Shin bakiji me nace bane? He’s in critical condition and you’re still questioning me?”

“Toh daman wa yace yana da lafiya? Look jamid babu inda zaka kaishi, zan kira medical team dinshi suzo yanxu”

“Hidayaaaa!!! Meysa bakida tunani ne? Whys your heart sore? Shin kina jin abunda kike fada kuwa”

“Majid!!!!!” Itama ta daka mashi tsawa, su fadwa tuni suka fito suka tsaya suna kallon ikon allah
“ how dare you? How dare you? Kai waye nashi? Who are you to him? His guardian angel or what? Ni ce guardian dinshi? He’s under my care saboda shi kadai ne kanina, kana son ka nuna min ka fini sonshi ne ko ka fini damuwa dashi? You’re making me look at you as a hypocrite,”

Yanda kasan ta buga mashi arrow a kirji haka yaji, yau hidaya da bakinta ke fadin mashi cewa tana kallonshi a matsayin hypocrite?

Kasa motsawa kawai yayi, badan taj yana da special waje a tarihin rayuwar shi ba daya barshi da ita kawai saidai bazai iya ba dole ya zama strong and komai zata ce bazai taba saka shi giving up akan taj ba saboda karfin alqawari.

Wayarta ta daga ta soma dialing heath team din dake kula dashi.
Bawan allah taj yana nan ya gama galabaita sabeeha kuwa kukan da take ya wuce musali dukda kunshe kukan takeyi don karya futo fili, fadwa da afiya kuwa kamar suna kallon tv, yau wata takwas kenan rabon da su ganshi sai yau, ya chanza sosai kamar bashi ba, Taj mai kwalisa mai class da girman kai da aji shine ake fada akanshi, idan ance masu he will look helpless kamar yanxu zasu rantse karya ne,tabe baki afiya tafi ita ranta ya gama baci ganin yanda ake ta fada akanshi, sai taji tsanarshi na

Please Login or Register in order to submit comment