Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar taheels ba da su kasuwancin su suka gaje sa daga wajen iyayensu har yayi accending to yayansu.

Abdullah ibn basit shine babban dan adawar taheel, tun kafin marigayi taheel ya rasu har zuwa bayan mutuwarsa, bayan mutuwarsa ya dauka kamfanin zai durkushe sai kuka yazo yafi da ma habaka, babu irin bibiya da harin da abdullah baya yi ma taheel company, amma abun yaci tura shekara da shekaru ya kasa samun abu guda daya dazai kama wanda zai sashi ya danqwafar da kamfanin a bayan fage kenan, a gaban duniya kuwa an shaida abdullah as aminin taheel kuka na hannun damanshi don shine wanda ya maida abdullah mutun a yanxu, ya dauke shi ya bashi aiki a companyn shi lokacin da bashi da kowa har ya maidashi mutun ya ajiye shi a kusa dashi.


ABUJA…
Kallon maqudan kudin dake gabansu jamila tayi kafin ta kalli mijinta, “jamila, anya wannan abun kuwa babu wata matsala? Wannan uban kudade ki duba fa ki gani?”

“Mai gida mai kake nufi kenan? Waye zai sani? Kaga ni wallahi babu abund aya shafeni, kudi kuma wallahi kashesu zamuyi muma mu shigo gari, wannan miliyan biyun ka ajiyesu kason mu ne sauran miliyan daya dake account dinka kuma zamu dinga bawa hadiza da kadan kadan karta fuskanci wani abun”

“Amma hadiza bamusan fah wani hali yarinyar nan ke ciki ba, an kira mu ne kawai an bamu kudi kuma ance saboda ita, Basu fada mana mene kudinrinsu ba fah? Da dalilin turo kudin? nidai tsoro nake ji wallahi”

“Kai matsalar ka kenan in kasan haka ne meysa kayi karyar kaine mariqin ta kuma maisa kayi karyar iyayenta duk sun mutu ? Ay naga son kudin ne kaima yasa kayi karyar, saida muka karba kuma zakace wani tsoro kake ji?, amma dai tsaya yanxu da gaske daga chan kasar saudiyyan aka aiko? To saboda me? Kai koma dai saboda menen oho chan ta matse masu, koma mey ya sameta achan ko sayar da ita akayi wannan ba damuwata bace ba, ita kanta uwarta ba damuwa zatayi da hakan ba dukda bazan fada mata ba”
“Toh shikenan” mijin jamila ya amsa ta.




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 29-30

Saudi Arabia…..
Monday morning!!!

Washe gari ta kama monday, wannan rana ta kasance rana wadda mutane da dama suke jiran zuwanta, hidaya tun wajen karfe bakwai ta bar gida don ko breakfast batayi ba.

Jamid ne ya kai barad school kafin ya dawo, lokacin daya dawo wajen karfe takwas na safe, abubuwan da suke faruwa tsakanin jiya da yau sun tsaya mashi arai ga fargaba da yake ji, anan compound din soma jin hayaniyar ma aikata sun hade waje daga, da mamaki yake kallonsu don sunbar ayyukan da sukeyi.

Kauda kanshi yayi daga kansu kawai ya wuce cikin gidan, bai tsaya ko ina ba sai hanyar dazai sadashi da stairs zuwa sama daidai nan fadwa ta fito daga bangaren ta, batama lura da jamid ba ta nufi wajen tv ta kunna news wayanta na hannunta, daman kiranta mijinta yayi ya shiada mata abunda ke faruwa.
Rasa ma wace tasha zata shiga tayi .

Headline din da jamid yaji ne yasa ya tsaya chak bai sake daga kafarshi da niyar tafiya ya yayi saurin maida dubanshi ga tv din, ga headline nan a kasa anyi rubutu da manyan harufa, “ reported news; heir of taheel groups has been grounded and hidden to the world because of amnesia”

Saurin chanzawa fadwa ta sakeyi ta shiga wani news channel din, nan ma cece kuce akeyi akan wannan breaking news din, akan company taheel, da gudu jamid ya sauko kasan baima san sanda ya warce remote din hannunta ba ya soma kara volume don jin abunda ake cewa,

Nan take kuma aka sauya headline din zuwa sabo, inda aka hasko hidaya a zaune zatayi press conference, dabas jamid ya zauna akan kukera yana kallon tv babu ko kiftawa,
Intoduction ta farayi kafin reporter din suka fara mata tambayoyi, “ madam shin da gaske ne heir din kamfanin taheel group kuma qani a wajenki yana fama da ciwon hauka? Madam meysa kuka boye wannan? Munason musan dalilin da yasa duniya bata san da haka ba?”

Saida ta gama jin tambayoyin su wasu ma sukarta sukeyi da tambayar, suna gamawa ta soma magana.
“Na farko wannan official announcement zanyi Tabbas heir din kamfanin taheel group yana fama da critical traumatic amnesia wanda yasa bayyanashi ya zame mana babban threat a gareshi da mental illness dinshi”

“Does that mean grounding dinshi kukayi for your benefit ko saboda kada tattalin arzikin kamfanin ku sauka?”

“Noo, i can’t publicly explain why but saboda health dinshi ne”

Wani reporter ne daya rufe fuskanshi da mask yace “does that mean situation dinshi is critical kenan meaning hauka yakeyi kenan?”

Shuru tayi suka zuba mata idanu sai faman haskata ake da cameras, jamid dai kasa dauke idanunshi yayi akanta yana jiran jin abunda zata ce, to his surprise sai yaji tace “ yes, situation dinshi is critical, i dont want to use the word hauka but i can say something similar cause he’s like good for nothing”

Wannan statement datayi ba karamin hargitsa komai tayi ba mutane sunyi mamaki sosai don kamar tayi destroying komai,

Wani ne cikin reporters yace “yanxu a wani mataki taheel group yake ciki? Zaku sayar da kamfanin ne? Ko zaku bari wannan ya zama downfall din legacy din? As we all know babu yanda za ayi companying yayi running without the heir”

Murmushi hidaya tayi kafin ta kalli wanda yayi magana tace “bazamu bari gumin iyayenmu da a sacrifice din da sukayi mana ya tafi a banza ba,“

“Babu yanda za ayi mahaukaci yayi rulling company madam…”
Hannu ta daga masu, kafin ta sauke ta dago wata yar paper, tana daga zaune ta mike tsaye, “i Hidaya taheel, the present acting ceo of the taheel group will take over responsibility of the company as the legal ceo”

Nan take aka soma hotuna masu zooming suka soma zooming documents din, kowa da abunda yake son fada.
Wannan reporter daya tambayeta kan cewa taj mahaukaci ne ya sake jefo mata tambaya,
“How is that possible? A yanda muka san law din business industry dinku babu yanda za ayi mace tayi ruling musamman idan akwai heir?”

Kai tsaye ta amsa shi, “you mean heir din da is not stable? Well there is, papers don’t lie, i am legally the chief executive director of the taheels, my brothers sickness bazaisa mubar abunda iyayen mu sukayi building ya lalace ba,we’re sorry for hiding this from the world, we did it for the sake of our only brother for his protection, thank you”
Tana kaiwa nan ta fuce daga conference room din, babban lawyer kamfanin taheel na biye da ita a baya, reporters kamar mayu haka suka soma kiranta madam madam madam, harta fuce.

Bayan ta shiga motarta tare da lawyern ta sauke wani sigh of relieve,” weldon madam your decision of hitting 2 birds with a stone is absolutely incredible”
“Thanks barr” ta amsa shi.
Wasu papers ya miqa mata tayi sighning duka kafin yace “madam you’re the current president of taheel groups, congratulations”
“Thank you, ka ajiye copy din zan karba original document din”
“Okay ma”
Gaba daya paper documents din ya tattara ya bata kafin su wuce office.

Jamid daya gama kallon tashin hankali, miqewa yayi cikin sauri ya wuce gidan khaal, koda yaje gidan shi shima already yaga abunda hidaya tayi.
“Khaal na fada maka, na fada maka wallahi wallahi hidaya bazata taba chanzawa,wannan rashin lpy taj is an opportunity to her, and tayi using dinshi to her benefit,“
Shuru khaal yayi yana wani nazari kafin ya kalli jamid yace “jamid, ina ganin we wrongly accused her, intentions dinta are pure kuma protecting taheel groups tayi”
Da mamaki jamid ke kallo khaal, babu abunda yake nema sai karin bayani,

News paper dake gefenshi ya dauka ya bama jamid din, take ya soma karantawa, jarida ce da aka buga ta tun daren jiya za a fidda ta ayau, abunda aka rubuta dai babu dadin ji duk kuma akan taj, wasu irin concrete false evidence aka tattara akan cewa yana drugs wanda shine sanadiyar samun amnesia da yake dashi yanxu wadda ta zama critical sosai, wanda kowa yasan me hakan ke nufi.
Da mamaki jamid ya dago, khal ne yayi saurin cewa “wannan jaridar itace first headline data fito kafin hidaya Tayi conference, badan ta hada conference dinnan ba da tuni companyn taheel a rufe shi gaba daya, wannan yasa aka dakatar da futarda wannan news din,”

Girgiza kai jamid yayi yace “how? Waye zai yi wannan? Ni ina zargin duk aikinta ne”

“Mutun daya nake zargi Abdullah ibn basit”
Gingina kai jamid yayi kawai, sai ya kuma fara jin rashin dadi game da yanda ya dunga zarginta.

“Ni wannan abun ma yamin dadi, saboda koba komai boyeshi da akeyi zaizo karshe.
Khal ya fada yana mai kallon jamid

Ya dade sosai wajen khaal suna tattaunawa kafin ya koma gida.

Taheels residents…..

Duk abunda ya faru yau kwata kwata afiya bata sani ba, hasali ma fada suke ita da fadwa don ta daina mata magana, hidaya kuwa haushinta takeji sosai ba kadan ba.

Karfe shida hidaya karaso gida, ba karamin yaqi tayi ba a office donma tana da gagarumar shaida wadda babu wanda ya isa yayi jayyaya da takardar, a take kuwa suka soma ganin asalin rashin mutuncinta don yanxu kamfanin ya dawo hannunta gaba daya, duk wanda tayi niyar kora har cikin shareholders zata iya yi, gaba daya kowa ya shiga taitayinsa.

Lokacin data shigo babu kowa ya kasa, daidai zata wuce sama afiya ta fito daga dining room, wani irin kallo afiya tayi mata mai wuyar fasaara kafin ta doka tsaki, fadwa dake shirin fitowa daga dining room din don dinner sukayi, ganin abunda afiya tayi yasa ta zaro idanu, “ke baki da hankali” fadwa ta fada

“Eh bani dashi” afiya ta amsa ta kai tsaye, “ ni banida munafurci kamar ke,” ta karshe tana mai dauke kallonta ga fadwa ta maida kan hidaya “ukty wallahi i hate you, i hate you so much” kuka ne ya sake kubce mata, “yanxu har kin manta da halin da ummuh ta shiga? Kin manta pain din datayi suffering dashi over the years? Kin manta abunda yayi sanadiyar mutuwarta? Why ukty, why? Maysa bakya kishin ummuh? Tana kabari amma na tabbatar tana allah ya wadai da protecting wanda yayi sanadiyar mutuwarta da kikeyi,”

Idanun hidaya sunyi jaa sosai, fuskanta ma haka ta koma jaa lokaci guda tsabar bacin rai,
Jan afiya fadwa ta soma yi tana kokarin hanata magana ta daka mata tsawa “dallah kyaleni, ni ban iya munafurci ba saina fada mata gaskia, wallahi wallahi wannan hatred din bazai taba barin zuciyata ba”

Kauda kai hidaya tayi kafin ta runtse idanunta ta bude su tarr, hannun afiya ta damko ta soma janta zuwa part dinta, fadwa na biye dasu hankali a tashe, suna shiga hidaya ta saki hannunta ta wanke fuskanta da mari, saida ta mareta wajen sau uku kafin ta kalleta da jajayen idanunta ta nunata da yatsa, “how dare you? How dare you say that eh answer me, ke a tunaninki da wannan karamar kwakwalwar taki ina yin wannan abubuwan ne saboda me? Saboda ina son TAJ? The child that destroyed our family? The child that destroy our happy home with our parents? The child that brings so much sadness to ourselves? Ehhh!! Answer me” ta karashe tana girgizata da hannunta,

“Let me remind you, ranar da taj ya bayyana a gidan nan akwai wanda ya kaini shiga tashin hankali? Daga ke har fadwa bakuda hankali bakusan meke faruwa ba a lokacin, I’m the only person who knows pain din da ummuh ta shiga, baku san komai ba don bakuga komai ba, her lonely nights, her painful days, the pain in her eyes, the screams of her pains zaki iya tunawa? Eh answer me nace zaki iya tunawa?,”
Ta daka mata tsawa mai rikitarwa wanda yasa ta furgita, hawayen fuskanta na kwaranyowa babu qaqaautawa,

“tunawa da wannan kadai yakan sakani samun sleepless night, kina tunanin ina rufe ido ba tare da wannan tsohon baqin cikin daya dade kwance a zuciyata ba? How dare you say that na zabi protecting wanda yayi sanadiyar baqincikin daya kwanta a zuciyarta har yayi sanadiyar mutuwar ta? How dare you”

Kallonta suka somayi gaba dayansu kuka ya gama wanke masu fuska, hidaya dai idanu sunyi jaa, babu hawayen ko kadan,
“I’m sorry ukty I’m sorry wallahi na dauka….”

“Shii, shut up, ay ban gama ba” ta karashe tana kallon cikin idnaun afiya da jikinta ke kyarma.

“Kina tunanin daukanshi da nayi na reneshi? Na rufe kaff rayuwarshi daga ni sai ni gaba da baya, Na hanashi kusantar kowa, na bashi soyayyar da babu uwar datayi ma danta irinshi don ko barad dana haifa banyi mashi irin soyayyar nan ba, sannan na tura shi karatu wata kasa chan sannan nayi pampering dinshi na bashi duk abunda yake so anan duniya duk kina tunanin nayi hakan ne saboda ina sonshi? No!!!!!!!!!!!!! I only did that don na juyashi son raina, to have him on my palm,”

Nunfasa tayi kafin ta cigaba, har hannunta na karkarwa “na nuna mashi so ne fiye daku da kuke jini na saboda ta wannan hanyar ne kawai zanyi yanda nake so dashi and thats the only way i can make him miserable, inajin takaici sa baqin ciki idan na tuna wani part na jini na na running a jikinshi,”
“And lastly ina son ku sani gaba dayanku, a duk duniyar nan babu wadda naso kamar ummuh, ko abuh banyi mashi irin son danayi mata ba,

Wanda yayi sanadiyar mutuwar ta shine babban maqiyi na, kuma bazan taba bari yayi enjoying wannan rayuwar ba yanda ummuh tayi suffering over that year, i will make him miserable thousand times over and over, ko ganin sa bana sonyi, kuma na tabbatar wannan hatred din saidai idan mutuwa nayi, so you better open your eyes clearly kisan yanda akw tafiyar da rayuwa yanxu keep that in mind”
Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin rai a bace, gaba daya memories din komai ya dawo mata, all the painful moments da hatred.


Jama’a Allah ya kaimu monday zamu shiga cikin labari, by next week free page zai kare💃🏻😭
Yanxu ainahin farkon shirin zai fara😆💔
Sabeeha dai ta zama matar taj, hidaya ta samu abunda take so, company ya dawo hannunta gaba daya….
Shin me zai faru nan gaba? Hidaya ta daura damarar shiryama TAJ miserable life, wato a yanxu ma somun tabi ne kenan?…
Ku biyo ni don sanin abunda zai faru a cikin labarin Matar TAJ….






Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 31-32
Farkon labari.
Asalin ahalin Taheel Abdullah Tajudeen.

Taheel Tajudeen babban dan kasuwa ne, business tycoon wanda ya sha’hara kuma ya zama jajirtattce a cikin fashion business industry, yayi fuce sosai a kasar saudi inda duk duniya babu wanda bai shaida nasarorin daya samu ba, yana da yaya uku tal a duniya wanda allah ya mallaka mashi, danshi na farko shine Taheel Abdullah tajudeen wanda ya gaji sunan mahaifinshi da sunan kakan sa sai mabiyinshi Abdul gaffar Tajudeen (khaal) sai Halima tajudeen.
Wannan ahali sun taso cikin soyayyar mahaifinsu har allah ya dauke ran mahaifinsu don mahaifiyarsu ta dade da rasuwa, a lokacin kowannen su ya taso da raayin abunda yakeso, Abdullah shine wanda ya ya taso da kudirin riqe legacy din familyn, inda yayi karatu bangaren business kuma cikin ikon allah yayi expanding family business dinsu har ya wuce yanda mahaifinsu yabar masu business din.

Tsakanin yan uwan nan akwai wani special connection tsakanin su musamman abdullah da khaal, saboda yanda mahaifisu ya koyar dasu son juna da kuma yarda da junan su.
Basu taba samun wani misunderstanding ba tsakanin su sabida yanda basa yima junan su baqin ciki ko hassada.
Khaal bai taba nuna son shiga harkar family business dinsu ba dan shi aikin government ya zaba, don haka koda akazo zaban wanda zai gaji taheel company as heir bai nuna disagreement ba ya cire hannunshi gaba daya daga business din ya barma dan uwanshi wato abdullah.

Shekaru sun jaa sosai inda abdullah yayi aure kuma auren soyayya,inda ya auri fattu ya ga babban dan kasuwa a bangaren southern arabia kuma abokin kasuwanci ga late taheel tajudeen, aure ne dai akayi shi badan soyayya ba saidai business inda mahaifinta ya roki alfarmar su hada hannu don taimakekeniyar juna, duba ga hakan zai kara daukaka taheel company yasa abdullah ya amince kuma ya aureta amma badai don soyayya ba saidai kuma kasancewar shi mutun ne na kwarai kuma mai cikon alqawari da addini yasa bai tauye mata komai ba ya nuna mata so da qauna, ta bangaren fattu kuwa so take mashi sosai kamar ranta, da farko bata amince dashi ba sai daga baya,rayuwa mai dauke da kwanciyar hankali da farin ciki da kula fattu ta shimfida masu ita da abdallah, harkar company kuwa sai bunqasa take sosai.
Bayan shekara daya da aurensu allah ya albarkacesu da ya mace wadda suke kira da hidaya, hidaya ta taso da soyyayar iyayenta, musamman fattu (ummuh) fattu na masifar son hidaya kamar ranta, haka zalika hidaya itama ta taso da kaunar mahaifiyar ta sosai fiye da soyayyar da take ma mahaifinta, halayenta da dabi’un ta sak na mahaifiyarta, bata daukan raini sannan akwaita da girman kai sosai.

Tun bayan haihuwar hidaya allah bai sake basu wata haihuwar ba kuma basu damu ba har takai shekaru goma ciff a duniya, acikin wannan shekaru abubuwa da dama sun sauya inda ummu ta soma shiga harkar business din taheel company as assistant director, she was so into the business don sai alokacin ta fahimci dalilin da yasa iyayenta are so obsessed with harkar business.
Kudi dai da fame ba a magana don ya shigeta sosai wanda hakan yasa ta daura damarar rike mijinta sosai don tun farko tasan ba auren soyayya sukayi ba, but ita kam sonshi take kamar hauka, samun hidaya cikin rayuwarsu kuwa ba karamin ci gaba bane a wajen ummu,
Lokacin da ummu ta gane policy din company din kan cewa wanda zai gaji wannan comapny din dole sai da namiji ba karamin tashin hankali ta shiga ba don tana da dogon buri, anan ne hankalinta ya soma tashi game da rashin haihuwar su saboda tasan idan har bata haifa da namiji ba to fah khaal ne zai karba wannan company din idan har mijinta baya raye wanda bata fatan hakan kwata kwata wannan ne ma yasa qiyayyar khaal ta fara wanzuwa a ranta dukda tasan he’s not into the business kuma bashi da raayin haka, kanwar su halima kuwa ita aurenta ma tayi a kasar waje, tun bayan tafiyarta bata sake dawowa ba, wannan dalilin yasa suka fara neman magani ita da abdallah don sanin dalilin rashin haihuwar.
Da farko sun samu matsaloli sosai ta bangaren lafiyar fertility wanda daga baya kuma cikin ikon allah ta samu wani cikin.
Fadin irin murnar da ummuh tayi da samun cikin nan bata lokaci ne don ta kwallafa rai sosai akan cikin kuma burinta akan cikin nan ya wuce misali don ta tabbatar ma da kanta da namiji zata haifa wannan karan.
Bangaren Taheel abdullah yayi farin ciki shima da samun karuwar tasu saidai shi bai wani damu da da namiji ko mace ba duk wanda allah ya bashi shi mai godiya ne da Hakan, kulawa ta musamman dai yana yima fattu sosai don ayanxu kam zaman lafiya sukeyi sosai.

Bayan wata tara fattu ta haifi diyarta mace, ba karamin tashin hankali fattu ta shiga ba don burinta na haifar namiji bai cika ba, wannan yasa taqi amincewa da sanin gender din babyn dake cikin mararta. Bayan kwana bakwai baby taci sunanta fadwa,

Daga kan haihuwar fadwa ne mafarin sauyawar fattu ya fara afkuwa, kwata kwata kudirinta da burinta yana ga samun power da fame,soyayyar da hidaya ta samu wajen mahaifiyarta kwata kwata fadwa bata samu ba, haka fadwa ta taso ta fara girma har fattu ta sake samun wani cikin bayan shekara uku shika da kyar aka samu cikin don sun kashe kudi sosai, wannan karan kam hankalin fattu a matuqar tashe yake don bata san yanda zatayi ba idan ta sake samun ya mace, hankalin ta kwata kwata bai kwanta da cikin ba haka dai take rainonshi saidai burin nan har zuwa lokacin yana nan.
After nine month allah ya sake bata haihuwar mace,(afiya) this time around frustration yasa tayi giving up kawai, abunda yasa hankalin ta ya kwanta ma shine ganin yanda khaal baya nuna interest akan company din hakan yasa ta fan tsagaita.
tsakanin fadwa da afiya kuwa bazan ce ga wadda ta jata jikinta sosai ba, kwata kwata bata jansu a jikinta saboda burin dataci na haihuwar maza sai kuma allah ya bata mata, matsayin hidaya dai yana nan aranta, tana masifar sonta kamar ranta.
A sannu a hankali ta soma jan su fadwa da afiya suma, lokacin data karancesu gaba daya fadwa is so smart and snicky while afiya kuma is so slow, hidaya dai har zuwa lokacin itace bold and strong among them don halinta irin na mamanta kamar photocopy.
Mahaifinsu kuwa ba karamin so yake masu ba su duka, baya banbancesu kwata kwata haka suka taso cikin soyayya da kulawa, a definition of a big happy family indeed, kwata kwata basu taso da wani hatred ko wani abu a ransu ba, daga su sai iyayensu, saima dai khaal da ummu ke janye su daga jikinsa, don shi kam ba karamin threat bane a wajenta, ganin wannan farin cikin da kwanciyar hankalin yasa fattu ta sassauta burikan da take dashi ta maida hankali kan ahalinta wato mijinta da yayanta.


A shekarar da hidaya ta cika shekaru sha takwas cip a duniya, a lokacin kuma fadwa na da shekaru takwas while afiya na da shekara bakwai.
A daidai wannan gab’a komai ya sauya masu, rana mafi muni ta bayyana a garesu, ranar data tarwatsa duk wani farin ciki da kwanciyar hankali na wannan ahali, wannan rana itace ranar da abdullah ya bayyanar da tajudeen taheel tajudeen ga yan uwansa.

Wannan rana ta kasance rana mafi muni da baqin ciki a zuciyar fattu,lokacin da abdullah ya bayyanar da danshi daya tilo wato tajideen.

Safiyar ranar lahadi..
Zaune suke a sitting room na kasa, hidaya dasu fadwa na wasansu while fattu na aikace aikacen ta daya shafi office din datake running, sallamar da suka ji ne yasa duk suka dago gaba dayansu, Khaal ne ya shigo hannunshi rike dana kyakyawan yaron da bazai wuce shekaru shida ba gaba daya a duniya, sai abdallah dake biye dashi a baya, saurin miqewa fattu tayi tana mai kallonsu, daya bayan daya take kallonsu har ta maida idanunta kan yaron, tsantsar kamannin su da abdallah harta wuce musali saidai abdullah daya fi yaron haske sosai, karasowa sukayi cikin sitting room din, inda khaal ya zauna bayan sun gaisa da fattu, daman gaisuwar sama sama ce, kallon yaron khaal yayi kafin yace “jekayi wasa da yan uwan ka”
Wani irin damm gaban fattu ya bayar, kwata kwata ta kasa dauke idanunta akanshi, samun kanta tayi da tambayarshi “habibi waye wannan?”

Kasa hada idanu yayi da ita saima dauke ma ganinta da yayi yace “muje bedroom inason zamu tattauna akan wani muhimmin abu”
Bata musa mashi ba tabi bayanshi suka haura saman, suna karasawa saman jikin ta har bari yake, kofar bedroom dinma bata kaiga rufewa ba ta nufi inda yake.

Zuba mashi idanunta da sukayi jaa tayi kamar tasan daman akwai wani abun a kasa sai dai kuma jiran confirmation da takeyi daga wajenshi,
Hannunta ya janyo ya riqe gam cikin nashi kafin ya soma magana “habibity! I want to tell you something, please karki tayar da hankalinki okay? Kaddara ne kuma tana kan kowa”
Girgiza mashi kai ta sake hannunta dake cikin nashi yana karkarwa, “I’m listening, ina fatan dai ba wani abu bane serious, ko?”

Tunda ta soma magana ya kasa hada idanu da ita, tabbas baiyi mata adalci ba bai kyauta mata amma ta yaya zai fara mata bayanin nan? Ya za ayi ta gane? Ya za ayi ta saurare shi? Matan saudi babu abunda suka tsana kuma suka kyamata kamar kishiya, da kayi masu kishiya gwara sun bar maka gidan ka auro wadda kake so, wasu daga cikin su suna yarda da second wife saidai abunda yafi tsananta kuma yafi cin mutunci a wajensu shine mijin da yaje yayi aure a boye ba tare da sanin matansu ba, shi

Please Login or Register in order to submit comment