Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da condition din sir, idan kika kuskura kika fada kuma’’
Dan tsayawa matar tayi kafin ta juyo ta maida dubanta ga sabeeha,’’ba sai na fada maki mai zai buyo ba, just keep that in mind’’

Dam dam gaban sabeeha ya bada, idan har batayi kuskure ba wannan aikin da za a bata shine aikin da aka turo ta tayi liken asiri akai ko menene?, maganar mutumin nan ce ta fado mata arai ‘’idan kinje zaki san irin aikin da zakiyi’’
Tabbas wannan ne abunda yake nufi Kenan, hannunta har wata irin zufa ne ke tsatsafo mata, sai a lokacin ma ta lura da stairs suke hawa.
Haka suka dunga hawa stairs din mai tsayi kafin su iso saman, kallon wajen sabeeha tayi kirjinta na tsananta bugu kamar ana buga ganga, bin matar ta dunga yi kamar raqumi da akala har suka karaso petion din dake tsakanin part din guda biyu.
Nuni head tayi mata da bangaren hannunta na dama ‘’babu ruwanki na nan bangaren, sannan chan’’
Tayi mata nuni da dayan part din, ‘’anan ne zaki yi aikinki as a caregiver’’

Takowa suka soma yi har zuwa part din kafin head din ta dannan security pins, ‘’wannan ne pin din shiga ciki, daga ni sai wadda zata kula da wajen sai madam ne kawai muka san pin din, kin gane me nake nufi?’’
Girgiza kai kawai sabeeha tayi kafin su shige ciki, suna shiga maid ta rufo kofar, nan take haske ya bade ko’ina hanyar walkway zuwa cikin part din, gefen wajen kofar maid din ta dan latsa wani electric dispenser nan take sanitizer ya futo, hannunta tayi sanitizing kafin ta umarci sabeha datayi hakan itama.
Tana gamawa ta soma cire takalmin kafarta daga gefe akwai wani rack da aka jera crocs, daya head ta dauka kafin ta bama sabeeha dayan.


‘’rule number 2, you should be very clean sosai, sannan duk sanda kika shugo ki tabbatar kin saka mask and kinyi sanitising hannunki, uniform dinki should be clean as well,ko digon datti a kayanki is not allowed’’

Girgiza mata kai tayi alamun gamsuwa dukda a tsorace take sosai,ciki suka fara shiga, haske ne ya gauraye ko’ina bau nan take komai ya bayyana, parlor ne mai girma da kyau fari qal komai is organise babu wani karikice sai camera’s ta kowanne lungu da sako acikin parlorn.
Sabeeha dai bata ma tsaya duban parlorn da kayu ba don tunaninta yayi nisa da abunda matar nan ke fada ma da wanda yar Ghana ta fada mata ga kuma wanda aka turo ta akai.

Saida suka zo dan nesa da kofar dakunan cikin part din matar ta tsaya, ‘’karfe shida zaki fara aikinki, sannan daga inda karfe hudu tayi ki tabbatar kin gama komai kin sauka kasa, daya daga cikin ayyukan da zakiyi shine gyaran part din nan, akwai kitchen da duk wani abubuwan buqata,’’
‘’the most important part of your job shine,kula da movement din sir,da abuncinsa, sai medication dinsa,sannan akwai timetable din abunda yafi buqata on a daily basis zaki samu wannan a kitchen, and lastly I will advice you duk abunda zakiyi kiyishi cikin natsuwa banda hayaniya saboda baya son hayaniya.’’

‘’waye kuma sir?’’ abunda ya fado ma sabeeha arai Kenan, tasan me caregiver ke nufi, saidai abunda bata gane bane shine dalilin da yasa aketa wannan boye boyen da wannan ka’idojin, komai looks so strange.
Kofar dake facing dinsu suka nufa, nan matar ta bude ta soma mata bayani, ‘’nan ne activity room din sir, duk ranar Friday zaki dunga kawoshi nan’’
Kallon wajen sabeeha tayi, wajen cike yake da kayan wasa na yara, babu abunda babu mota ne jirgi da keke dadai sauransu da mamaki take kallon wajen har suka fito daga dakin.


Nuni da kofar tsakiya matar tayi kafin tace ‘’nan ne kuma bedroom din sir,first thing first by 8 dot yake tashi so duk abunda kikeyi na gyara ki tabbatar kin gama kafin lokacin, idan zaki shiga bedroom din ba’yin knocking saboda baya son any sound ko karar komai, zaki bashi first medication dinshi by 8:30 dot, sannan kafin yaci abunci zaki taimaka mashi yayi wanka ya shirya by 9 zaki bashi breakfast, sai second dose of medication dinshi’’

Jin haka yasa sabeeha shiga tunanin waye wannan sir din, kalaman matar dataji ne da yanda komai suke yin shi cikin tsari da ka’idoji yasa ta soma tunanin to kodai raino aka sake kawota, to amma rainon da zatayi ne leken asiri?, ita gaba daya ma kanta ya burkice da ala’amarin,

‘’that’s all for now, zuwa gobe zaki fara’’ matar ta karashe tana mai nufar hanyar futa daga part din sabeeha na biye da ita a baya.
Kasa suka sauka, maids din dake gyara gyare suna kallonsu ta wutsiyar idanu kamar hankalisu baya kansu, saida sukaga head ta wuce kafin daya daga cikin su ta soma Magana kasa kasa ‘’nandini, ayna fada maki, wannan a sama zatayi aiki kai amma I pity her,’’
Dayar da aka kira da nandini ce tace ‘’to me she looks like she’s happy, bata san inda ta jefa kanta ba, ki duba kiga yanda last maid dinnan ta gudu, ta bani tausayi ko kwana biyu bata yi, ni im curious wallahi, menene a saman nan’’
Matsowa dayar tayi ta rada ma nandini wani abu a kunne………

Bayan sun sauko daki sabeeha ta koma na bangaren su, tana shiga babu kowa a dakin don koda suka sauko daga sama ta gansu suna aikace aikace anan kasa, daman yan dakin nasu bangaren aikace aikace suke handling.
Zama bakin gadonta ta doka uban tagumi, tunani kala kala na yawo a kwanyar kanta.


California……
Envision academy high school…….
School Bus ce ta fito daga cikin school din, dauke da student, babu abunda ke tashi a cikin bus din sai hayaniyar yara, maya da gang dinta na zaune daga gefe su uku ashe wata yarinya suka saka a gaba suna bullying,yarinyar na gabansu a tsugunne maya ta daura kafar ta akan labs din yarinya, su kuma student me zasuyi banda dariyar mugunta, saida aka zo first stop kafin wasu few daga cikin student din suka fita daga cikin motar ciki kuwa harda maya da kawarta inda suka shige cikin yaran da suka futa don kar a gansu.
Suna fitowa maya da kawarta kloe suka yanki wata hanya cikin sauri gudun kar driver yayi noticing din futar su, saida sukayi ma bus din nisa kafin su dan tsagaita, dariya kloe ta fara kafin ta maida dubanta ga maya ‘’kai babes this is the toughfest part of running away from school, I can’t wait to be 18 and free muyi mu gama exams’’
‘’hmm, nima kaina na gaji da guje gujen nan just to have fun, meysa sai lallai mutun ya zama 18? Other countries baa yin haka’’
Daidai nan suka karaso kan titi inda wata mota ke parke daga gefe, cikin hanzari suka karasa wajen motar, maya na gaba while kloe kuma na daga baya.
Suna shiga wanda ke zaune mazaunin driver ya miko hannu zai rungumeta, ‘’come here babe’’wani irin kallo ta watsa mashi wanda ya sashi komawa mazauni yana mai kunna mota, saurayi ne white American yasha wasu kananun kaya, daga baya kuma kloe ce ita ma da nata saurayin black American,
Wanda ke bayan ne yace ‘’girls where are heading to?’’
Maya ce tayi saurin cewa as usual, tana kaiwa nan wanda ke tukawan ya zugi motar suka bar wajen.
Basu tsaya a ko’ina ba sai a wani wajen shakatawa, wajen kamar restaurant, ciki suka shiga, inda daga nan basu tsaya ko’ina ba sai wani sirrintaccen bangare dake cikin restaurant din, kamar koda yaushe zaida wannan black American din yayi Magana da mai wajen don abokin yayansa ne kafin abarsu su shiga ciki don ba a yarda underage su shiga.

Wurin so very dim sai blue light kamar dare, maza da mata na zazzaune kowanne yana harkarshi da drinks a gabansu wasu kuma na cin abunci wasu kuma hayaki suke busawa.

Zama sukayi wajen da suke zama koda yaushe inda sukayi nasu order drinks din, wannan white ameriacn dinnan dai yana kusa da maya, da alamu saurayinta ne don daga yanda yake ta faman bata hakuri kamar yayi mata laifi ne.
‘’shut up u cheater,’’ ta daka mashi tsawa wanda yasa hankalin kowa ya koma garesu

‘’maya please’’ kloe ta fada tana kallonta don suna zaune opposite dinsu.
Hannunshi ya sake sanyawa ya riko nata ‘’bebz please im sorry, there nothing between us, its just accidental kiss please’’

Ajiye juice din maya tayi ta maida dubanta gareshi, ‘’you’re a cheater and a liar, you think I’m stupid? Kiss by accident? For goodness sake rick Zara is my friend, how could you kiss her and call it by accident, I see both of you with my 2 eyes’’

Shima saurayi harzuka yayi yana mai kallonta ‘’look, I don’t fucking care about the kind of thought you have on this, how many times do I have to apologies, I’m done please’’
Kallonsu kloe tayi da saurayinta don ganin yanda zasu kare, kamar yanda sukayi hasashe kuwa sai gani sukayi maya ta sauko lokaci guda, don bata taba taba yarda yayi fushi shima don tana masifar son nick kamar ranta, shiyasa duk abunda yakeyi take daga mashi kafa, gashi bai wani girmeta sosai ba, he’s just 22.
‘’okay but promise this should be the last time’’
Amsata yayi yana mai hugging dinta so tightly, ganin haka yasa kloe gyaran murya tana mai duban saurayinta tace ‘’I told you, bazata iya hakura dashi ba’’
‘’what are you gossiping?’’ maya ta karashe tana duban kloe da saurayinta, kafin ta tabe baki ta maida dubanta ga black American dinnan tace ‘’ I cant stay long guys, daddy nay a dawo and its been a week now bai koma ba, my phone has been seized, so lets just do what we have to do, how far with the?’’
Bata gama fada bama ya zura hannunshi cikin aljihunsa ya zaro wata yar takarda ya ajiye a gabansu kowa ya tura mashi gabansa harda maya.

Wani irin murmushi maya tayi mai wuyar fassara kafin ta dauki nata nannadaddiyar paper ta soma warwarewa jikinta har tsuma yake…..





**
Abuja Nigeria.
Gidan Marigayi alhaji santuraki..
Safiyar juma’a Kenan, yau gidan a cike yake tam saboda dama duk Friday ake taruwa a cikin main house bangaren Anne duk da estate daya suke kuma kowa da part dinshi.
Matan uncle Sameer babban dan gidan anne kennan da aunty fadila da iyalanta duk sun hallara ga jikoki harda da yaya ma.
Rana irin ta yau ta zame masu kamar double celebration saboda ayau uncle Sameer zai dawo daga Europe after shekara daya Kenan da tafiyarshi zuwa wani course.
Yaran duk suna zaune a sitting room na kasa don gidan nada girma sosai while iyayen su kuma suna sama wasu kuma suna kitchen ana hidimar girki dasu.

Anty Laila (uwar gidan uncle sameer)ce ta shigo dakin da sallama don zuwanta Kenan gidan, don bata samu tazo da wuri ba saboda ta dan tsaya don shirye shiryen tarbar mai gida don anan gidan ta zai sauka,

Da sallama ta shugo cikin dakin, anne dake zaune akan gado da wasu tarkacen takardu a gefenta ne ta dago ta kalleta tare da amsa sallamarta fuskanta babu yabo ba fallasa, nanna ce ma dake zaune kan kujera tana cin dambun sadakar Friday da aka kawo ne ta kallata cikin fara’a tace ‘’ah ah matar babban yaya sai yanxu’’

Sunkuyar dakai anty Laila tayi harta karaso tsakiyar dakin ta zauna kan carpet tace ‘’barka da hutawa nanna, barka da huta wa anne’’

‘’barka dai’’ suka amsata a tare
‘’ya iyali, yau mai gidan naku zai dawo ko’’ nanna ta fada tana mai kallonta
‘’eh yau zai dawo insha allah’’
‘’toh masha allah ga dambu bismillah’’ nanna ta fada tana mai kallonta
‘’alhamdulillah nanna, sai zuwa anjima zan diba’’
Shuru ne ya biyo baya adaidai lokacin fadila ta shugo dakin hannunta rike da mubin, yaron(aunty mubina) amaryar uncle sameer kenan.
‘’mubin dai akwai barci yaron nan shiyasa yake burgeni’’
Jin muryarta yasa suka dago suka kalleta banda anty Laila da kanta ke kasa, kallon inda take fadila tayi kafin tace ‘’ashe kin iso’’
Kamar anty Laila bazatyi Magana ba tace ‘’eh yanxu na shugo’’
Tana kaiwa nan ta mike ‘’bari na sauka kasan’’
Nanna ce kawai ta amsa ta da toh, anne kuwa hankalinta na kan pappers din dake gabanta, anty fadila na kwantar da mubin ta dubi hanyar futar da anty Laila tayi kafin ta tabe baki tace ‘’hmmm’’
Kallonta nanna tayi fuskanta ya dan sauya tace ‘’haba fadila, har yanxu dai bakwa jituwa da yayar taki?’’

‘’nanna bazaki gane bane, Tsakani na da ita waye ya kamat ya gaisar da wani?’’
Rai adan bace nanna tace ‘’lallai fadila, karkiga wai don tare kuka taso, matar wan k ice kuma uwar yayansa, dole ki bata respect dinta, anne kina kallon wannan shashanci da girmansu’’
Sai a lokacin anne ta dago ta kallesu cikin glass din dake fuskanta ‘’ay sun san daidai basai nayi Magana ba, and besides ita da take babba itace ya kamata taja girmanta’’

‘’anne please karki goyi bayan kowa a alamarin nan saboda wani abu chan daya faru a baya wanda ya zama tarihi’’
Kallon yar uwar tata anne tayi tace ‘’hajara!!’’

Jin yanda anne ta kira nanna yasa anty fadila fucewa daga dakin, tana futa kuwa anne ta kalli nanna tace ‘’bana son a sake maimaita maganar nan, bana bin bayan kowacce a cikin su, laifin shi Sameer dinne daya bar hakan ta kasance shiyasa bana Magana akai’’

Nunfasawa nanna tayi kawai kafin ta maida hankali wajen abuncin da take ci.

Fadila na futa daga dakin kuwa ta sauko kasa zuwa kitchen, a tsaye ta tadda anty mubina da masu aiki suna ta hidima, karasowa tayi har inda suke tayi kafin tace ‘’amaryar babban yaya, baki koma daki kin hutaba?, kije ki huta tunda mubin yayi barci nakaishi dakin anne’’

Juyowa mubina tayi hannunta duk flour gashi tasha apron da alamu dai aykin takeyi bil hakki da gaskia, ‘’anty fadila ay mun kusa gamawa, cake dinne kawai ked an daukan lokaci’’

‘’toh shikenan, bari naje na dubo ko hamad sun dawo daga kai sadakar tunda naga an sauko daga masallaci, wannan yar banzan yarinyar ashe guduwa tayi ta barki’’
Dariya kawai mubina tayi kafin ta maida dubanta ga ayyukan dake gabanta.

Anty Laila kuwa bayan ta futo kasan ta sauko ta hakimce akan kujera, tana nan zaune fadila ta sauko ta wuce kitchen harta futo daga kitchen din ta sake komawa sama, su inti da amla da kareem sai wasansu suke….

Basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara da rabi bayan kowacce taje tayi ma anne sallama.
Part din anty Laila yana opposite na anty mubina, sai part din anty fadila dake chan nesa dasu sosai, sai kuma wani part din daban, duk sun zagaye bangaren anne dake a tsakiya…….








Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 15-16



Update!!!
Saudi Arabia…!!!
Washe gari da safe kamar safiyar jiya haka alarm din bangaren ma’aikata ya soma qugi, agurguje kowa ya tashi duka maaikatan harda sabeeha, lokacin wajen karfe biyar daidai.
Sabeeha na zaune cikin hijab dinta kamar ko da yaushe, saida suka gama kafin ta shige bathroom din tayi wanka tare da dauro alwala, saida ta gama ta maido da hijab dinta ta futo daga bathroom din.
Agurguje tayi shirinta cikin uniform lokacin kusan duk maaikatan dakin duk sun fuce, aggagauce itama ta gama saka kayan nata ta tada kabbarar sallah, tana idarwa ta cire hijab din ta ninkeshi a gefe kafin ta zura mask dinta ta fuce daga cikin bangaren nasu.

Anatse take tafiya kamar wadda kwai yafashe ma a jiki, jikinta duk a mace game da wannan sabon almarin cikin rayuwarta wanda ya hanata sukuni, tunani iri iri daban daban nayi mata yawo akai ga tsoro ga fargaba.

Lokacin data shugo main house babu kowa a kasan hakan ya bata damar tsayawa don yin nazarin inda zata bi kafin taje saman,tana cikin wannan tunani sauran masu gyaran main house din suka shigo suma, bin inda suke bi itama ta soma yi harta gane inda zata nufa.

Lokacin data karaso saman bin wajen ta soma yi da kallo, nan take idanunta ya sauka dayan bangaren nan, wani abu ne yazo ranta kafin ta yaqice ce ta nufi part din da zatayi aikinta.

Tana zuwa bakin kofar ta tsaya ta saka pins din tare ba bude handle din kofar ahankali kamar mara gaskia, tana budewa ta sa kai ciki.

Tana shugowa wajen ya bade da haske, sanitizing hannunta ta farayi kafin ta cire takalmin dake kafarta ta zura crocs kamar yanda head ta nuna mata jiya, tana gamawa ta wuce cikin parlor.

Bin ko’ina ta soma yi da kallo kamar yaune ta taba ganin wajen, babu digon datti ko daya saima kamshi dake tashi, kwata kwata batayi gigin kallon wannan kofofi guda biyu ba saima dayar kofar dake wajen dining data nufa wanda haka ya tabbatar mata da nan ne kitchen, hanyar tabi ta shige cikin kitchen din a natse kafin ta sanya hannu ta tura kofar.
Gasping breath dinta tayi tare da sauke ajiyar zuciya saboda yanda kirjinta ke bugawa tunda ta shugo cikin part din wanda ta alaqanci hakan da fargabar da take ciki, dan yanxu ta qayyade koma menene a nan saman to abun cutarwa ne saboda tunawa da maganar da yar Ghana tayi mata akan cewa previouse ma’aikatan da sukayi aiki anan din ko kwana biyu basayi suke barin aiki anan saman shiyasa kowa ke tsoron nan din, ga yanda aka zuba uban dokoki.

Sauke ajiyar zuciya tayi tana mai addua aranta na neman tsari ga allah, ta dan dade a tsaye tana rarraba idanu kafin ta yunkura ta fara duban ko’ina, time table din abuncin da zatayi yana nan an mannashi jikin fridge sai wani dan box din medication da date harda time a jiki, saidan karamin timer dake reading time komai dai cikin sauqi.

Neman abun shara ta soma yi da mopper, tana ganin komai ta kwaso ta koma parlor ta soma gyara, allah ya taimaka ta iya gyaran ma sosai saboda gidan data baro bayan aikin kula datayi har da gyaran daki tana yi, agidan wannan tsohon kuwa har abunci tana dafawa irin nashi wanda matar gidan ta koya mata musammam idan ita bata gidan.

A gurguje ta gama komai saboda babu datti ko digo sai yar kurar da baza a rasa ba, dakin activity room ta shiga, nan ma saida ta gyara ko’ina ta goge kafin ta fito, duk wannan abubuwan da takeyi cikin natsuwa takeyi gudun kartayi wani kwakwara motsin.

Mamakin kayayakin wasa dake dakin activity ta soma yi, wasu abubuwan wasan ma tun tasowarta bata taba ganin su ba, yaran larabawa dai suna shan gata.

Kitchen ta koma ta soma preparing abunda ke rubuce a timetable din, duban date ta fara yi a jikin time table din, yau Wednesday, abunda ke rubuce ne a wajen ya dan bata mamaki don ruwan zafi kawai ta gani da just 1 apple for breakfast, wakeyin Karin kumallo da ruwan zafi zalla bama ruwan shayi ba sai kuma slice of apple, sanin bata da hurumi a cikin dokokin da aka bata yasa ta bude fridge din, babu wani abun kirki a cikin fridge din na ci saidai fruits da chcolate sai vegetables… Apple din ta zaro guda daya ta soma slicing kafin ta jona ruwan zafi a heater kettle lokacin wajen karfe takwas tana gamawa ta samu waje anan kasan kitchen din ta zauna ta tankware kafafunta.

Duk bayan yan mintuna qalilan haka zata dubi time gudun kartayi kuskure har barci ya soma dibanta a nan zaune, haka nan ta hana kanta barcin nan har wajen karfe takwas rabi daidai.
8 dinma nayi alarm din kan timer dinnan yayi ringing, a furgice ta miqe tsaye jikinta na bari ta nufi wajen kettle din ta sake reboiling ruwan, tunawa da saiyasha magani a cewar matar nan yasa ta bude wannan box din ta zaro pack din magungunan ranar kafin ta dauka ruwan dake jere a wajen ta fuce daga kitchn din.

Daidai bakin kofar dakin ta tsaya, sai a lokacin taji wani sabon tashin hankali ya tunkarota, she’s just so anxious haka kawai.

Kai tsaye ta bude ahankali gabanta na bugawa kafin ta shige cikin dakin, dakin duhu babu wani haske kwata kwata daga inda take tsaye, dagowa tayi ta fuskanci cikin dakin, sai a lokacin ta dan hango hasken rana dake haskowa daga wajen labulen dakin.
Takowa ta soma yi anatse ba tare da tayi making any movement sound ba har ta karaso tsakiyan dakin, shuru ta danyi tana yin nazari nan take haske ya zagaye ko’ina ya gauraye dakin, duban ko’ina ta soma yi da kyau, daki ne babba sosai mai dauke da gado dayasha beddings sai carpet a tsakiya, ko tv babu sai gefe kuma wata kofa ce kamar wani dakin daban kuma.

Duban gadon tayi ganin babu kowa akai kuma babu alamun da akwai mutun a dakin yasa ta danji sauqin fargabar da take ciki, ‘’toh ay babu kowa nan’’ ta fada aranta

‘’kila yaron yana bandaki’’ ta sake fada aranta, don daga yanda wannan matar ta fada cewa karfe takwas yake tashi, shuru shuru dai tana tsaye har wajen minti goma babu wani motsin, hakan yasa ta tunanin anya lafiya kuwa.
‘’first love’’ furucin data faraji Kenan, tabbas taji anyi magana saidai ta kasa gane daga ina ne tajiyo wannan sound din dake futa ahankali, dube dube ta soma yi har idanunta ya sauka wajen labulen nan dake facing dakin, chan kuma ta hango tudun abu ta wajen labulen wide glass din dakin ahankali ta soma takawa zuwa wajen,

tsugunnawa tayi daidai wajen curtains din sannan ta fara yaye labulen, tundaga yatsun hannunshi daya ajiye agefenshi zuwa bayanshi that is so wide zuwa sumar kanshi da take akwance kamar gashin jariri da alamu an aske mashi gashin ne ma amma ya fara fitowa,zaune yake ya tankware kafafunshi ya hade su waje guda ya zuba ma windown fararen idanu babu ko kiftawa.

Afirgice ta koma da baya, hankalinta atashe azuciyar ta fara karanto addu’oin tsari kamar an kira sunan shi kuwa ya juyo ya kalleta, shima saida yadan razana.

Lafiyayyan saurayi ne zankadede a zaune, fari tass dashi, yana da yalwan gashin jiki da gashin baki daya cika mashi round innocent face dinshi, akalla zai kai shekaru talatin da yan kai a doran duniya, yana da wani irin kyawu da cikar haiba masha ALLAH gashi da girman jiki na mazan taka(masculine) dukda a zaune yake.

Kallon juna suka soma yi tsakanin shi da ita,sabeeha dai kasa dauke idanunta tayi akanshi, saboda kamar anyi magneting idanunsu waje guda babu abunda take tambayar kanta sai wannan ne sir din? Shi wannan din mutun ne? tsabar furgici ma kallon shi take kamar aljani saboda kyawun shi ya wuce musali.

Shikuwa ganin tana kallonshi yasa ya zuba mata idanu shima, jikinshi harya soma jaa, take yanayin fuskanshi ya sauya zuwa na furgici har jijiyoyin kanshi sun bayyana rado rado, sanye yake da wata farar riga mai dogon hannu sai wando shima fari tass masu laushi,, zumbur ya mike tsaye wanda yasa ta dago da kanta sosai kamar tana kallon sama don yana da tsayi sosai, saita zama kamar wata yar dwarf a gabanshi, bakinshi ya soma juyawa kamar wanda ke son yin Magana ‘’who are you?’’ ya fada a hasale, wannan kalmomi sune kalma ta biyu daya furta da kunnenta ya jiyo mata,

Inda take ya soma dosowa kamar wani zaki, ‘’who are you?’’ ya sake fada yana binta daf da daf, tana ganin haka ta koma baya cikin sassarfa har tana harde kafafunta, saida suka karaso tsakiyar dakin ya fara dube dube da alamu yana neman abunda zai dauka ya buga ne a kasa, ganin babu komai a kusa yasa shi kwala uwar kara wanda yasa sabeeha burkicewa sosai, take ta saki maganin da ruwan duka a kasa, ‘’na shiga uku’’ta furta bakinta na karkarwa,

wata uwar tsawa daya sake doko mata yasa ta zubewa a kasa sai hawaye wiwi, tata ta kare, wannan mai kama da aljanun ko mahaukaci ne? shiyasa ake ta tsoron hawa sama kenan,abunda yazo ranta Kenan.

‘’dan..dan allah kayi hakuri, karka min komai dan allah’’ ta karashe tana mai hade hannenta waje daya tana rokonshi, hwayenta

Please Login or Register in order to submit comment