Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rantse bahijja wallahi this time around I’m going to deal with maya, duk abubuwan da takeyi ina Kauda idanu this time around bazanyi ba, and don’t even think of saying a word kinji na fada maki’’
Yana kaiwa ya miqe ya fuce daga dakin, tana ganin futarshi tabi bayansa, dakin maya ya nufa kai tsaye ya bude kofar ya kunna lights din dakin, barcinta take hankali kwance kamar ba itace tayi aika aikar nan ba, ‘’maya!!!’’ ya doka mata uwar tsawa, tashin farko ta mike zaune zumbur,
‘wani irin furgici ne ya durar mata ganin daddy nata a tsaye, daidai nan mummy ta karaso cikin bedroom din, ‘’step out now’’

‘’daddy please I’m sorry bazan sake ba please’’
‘’shut up your dirty mouth, I said out to, don’t make me repeat my self, ‘’

Ya karshe hannunshi har karkarwa yake tsabar bacin rai,
‘’mummy please talk to dad dan allah, wallahi banason zuwa displine room dan allah’’

Tana kaiwa nan ta karaso inda mummyn take ta boye a bayanta, ‘’daddy please, for god sake laifi tayi kuma tayi nadama, maya is not a kid fa da za a kulleta a daki, she will be 18 in a month’’

‘’bahijjaaaaa!!!!,’’
‘’majid please….’’
At that point ranshi ya gama baci sosai, ba maya ba hatta mummyn ma ta gama bata mashi rai sosai.

Kasa cewa komai yayi kawai ya fuce daga dakin cikin bacin rai sosai, shi kadai yasan meke cikin ranshi da matakin dazai dauka akan sus u duka ma.
He’s trying so hard to understand bahijja, wani sa’in yana kauda ido sosai akan rashin jin da maya keyi saboda maya kadai ce yarsu, kuma bazasu sake haihuwa ba saboda matsalar mahaifa da bahijja ta samu bayan haihuwar maya.

Wannan rana dai cikin bacin rai sukayi gaba dayansu daga daddy har mummy, haka suka kwashi wajen sati guda babu wanda ya kula wani cikin su, maya kuwa harkarta ta cigaba ba tare da damuwa ba, ita dadinta daya mummy ta bi bayanta, saidai ta gindaya mata sharuda sosai tare da warnings akan cewa idan ta sake ta sake maimaita abunda tayi bazatabi bayanta ba.



Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 21-22

Update
NIGERIA ABUJA
Santuraki family…
Yau family an tashi da jimamin mutuwar babban aunty amarya (matar uncle sameer), gaba daya cikin shiri suka fito inda zasu je gidan gaisuwa, already uncle Sameer ya wuce da aunty amarya chan gidan gaisuwar don tunda asuba aka kirashi aka shaida mashi, lokacin ma ba’a bangarenta yake ba yana bangaren anty Laila don kwananta ne ya zagayo a ranar, anne ce da nanna suka fito cikin shiga ta mutunci da alfarma sai sauran matan gidan, anty fadila da yaranta mazan, hamad da laily karama sai sufyan da abil, kananun ne kawai aka bari a gida wajen nannies dinsu.

Gaba daya suna tsaye a compound din har kowa ya futo gaba dayansu banda anty Laila,
Anty fadila ce tayi saurin cewa
‘’mamanku fah’’
Anty fadila ta fada tana mai duban su abil,kallon juna suka fara yi shida sufyan, ‘’tace driver zai taho da ita’’
Tabe baki antie fadila tayi kafin ta shige cikin katuwar lexus inda hamad ke driving motar while sufyan ke driving dayar motar dasu anne ke ciki.

Cikin anguwar GRA dake cikin maitama suka nufa, anguwar ta masu shi ne don anguwar dai ta hadu sosai, daidai wani babban gida suka karaso, daga wajen gidan mutane ne burjik.
Parking sukayi kafin su firfito, uncle Sameer ne yayi masu iso zuwa cikin gidan inda mahaifiyar aunty amarya ke karbar gaisuwa.

Gidan kana shiga kasan anyi rashi babba don ko’ina shuru mutane ana zazzaune,Allah ya jiqan musulmai baki daya wanda suka rigamu gidan gaskiya, muma idan tamu tazo allah kasa mu shika da Imani Ameen.

Har cikin babban parlor hajiya babba suka nufa da sallama inda suka fara gaggaisawa da mutanen dake parlor, anne ce ta farayi ma hajiya babba gaisuwa kafin su nanna dasu anty fadila, ba karamin dadi hajiya babba taji ba ganin dangin mijin diyar tata.

Anty fadila ce tayi saurin cewa ‘’ina aunty mubina’’
‘’tana ciki, bari a kirawo ta’’ hajiya babba ta fada
‘’ah ah bari na shiga daga ciki’’ anty fadila ta fada.

Cikin dakin ta shiga nan ma dai akwai mutane amma basu kai na parlorn ba, mubina na daga zaune bakin gado, ta dafe kanta da alamu kuka take kanyi har zuwa yanxu, ga mubin a gefenta yana ta barcinshi hankali kwance.

Gaisawa ta farayi da matan wajen kafin ta karasa inda mubina ke zaune, jin an dafa ta yasa ta dago, ganin anty fadila yasa ta soma share hawayen fuskanta, idanunta sunyi jaa sosai, ‘’aunty fadila kunzo?’’
‘’munzo mubina, ya hakurin mu allah yayi masa rahama, ai duk mun zo harda su anne duk suna parlor’’
‘’ameen anty fadila nagode bari naje parlorn’’
Atare suke wuce parlor inda su anne sukayi mata gaisuwa da sauran yaran harda samarin gida gaba daya.
Wayar aunty fadila ce tayi ringing, ganin wanda ke kiranta yasa tayi saurin picking call din, ‘’wa alaikum salam’’ ta amsa sallamar da akayi daga chan bangaren kafin ta sake cewa ‘’tohm gani nan zuwa’’
Ajiye wayar tayi kafin ta miqe ta fuce daga parlor, daidai tsakar gidan inda babu mutane sosai ta hangoshi daga chan nesa, cikin sassarfa ta karaso inda yake tsaye, babban mutun ne magidanci, kamanin su daya sosai don kamarma har ya fita kyau saidai girma dayazo mashi sosai, yana sanye da farauncle Sameer Kenan.
‘’gani yaya ya hakuri, allah ya jikan sa’’
‘’ameen ya Allah’’ ya amsa ta
‘’banga Laila ba ku kadai kuka zo?’’
Tabe baki anty fadila tayi kafin tace ‘’mun barta a gida tace wai driver zai kawo ta’’
Girgiza kai kawai yayi kafin yace ‘’shikenan, bari na koma gidan’’
Sallama tayi mashi kafin ta koma ciki shi kuma ya shige motarsa zuwa chan zuwa gida.

Tafiyar minti ashirin ta kawoshi gidan, daidai apartment dinsu yayi parking kafin ya futo.

Da sallama ya shigo cikin gidan, babu kowa a kasan sai househelp din dake fama kwashe kayan wasan yara, ‘’barka da dawowa’’
‘’barka dai,’’ ya amsata kafin ya wuce saman, bai tsaya ko’ina ba sai bedroom dishi dake chan saman, da sallama ya shiga bedroom din, ko’ina tsaftsaf sai kamshin bakhoor dake tashi.
Wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin manyan kasa, yana gamawa ya zari key ya wuce bedroom din anty Laila.
Da sallama ya bude dakin yasa kai ciki, dakin lum lum babu haske sai karar ac, hasken dakin ya kunna kafin yakai dubanshi ga tsakiyan gado, da mamaki ya hangota kwace hankali kwance, karasawa yayi har bakin gadon ya zuba mata idanu
‘’laila laila’’ ya soma kiranta,
Saida ya taba kafadunta kafin ta farka, kallonshi tayi kafin ta kauda kanta gefe ta miqe zaune, daga ita sai wata doguwar rigar barci da alamu ko wanka ma batayi ba,
‘’sai yanxu ka dawo tun asuba?’’
Ran shi ya dan soma baci, yanayin yanda take mashi maganar kamar bata san daga inda yake ba da kuma dalilin futar tashi, ‘’eh sai yanxu na dawo, maysa baki buyosu ba kunzo gaisuwa?’’

A hasale ta amsashi, ‘’basu fada maka nace zanzo daga baya ba’’

‘’kewai Laila yaushe zakiyi hankali ne? rasuwa fa akayi ma yar uwarki? Wannan wani irin shahsan ci ne, ke kullum sai kin jawo ma kanki abun Magana sannan kizo kina kuka kina cewa bana kyautata maki bana bin bayanki? Yanxu ke hakan ya dace? Duk gidan nan gaba daya sun tafi ke kina daga kwance’’

‘’kaga Sameer karka qara hadani da matarka, ka taba ganin inda kishiyoyi suka zama yan uwa? ni ba yar uwata bace ba, sannan mutuwa allah na tuba wanda ya tafi ya tafi Kenan, zuwana bazai dawo dashi ba, kuma naga dai bance bazan zo ba, mutuwar nan fa kowa anyi mashi ita saboda ka daina wasu maganganu don ka nuna min matarka ta fini shiyasa yan uwanka ke min abunda sukaga dama suka raina ni basa ganin mutunci na’’

‘’laila kishi fa ba hauka bane ba, you better stop this nonsense, girma kikeyi ba rage maki shekaru ake ba’’

‘’naji ka fadi duk abunda zaka fada, daman baka ganin laifin kowa sai nawa’’ tana kaiwa nan ta fashe da kuka
‘’wallahi Sameer na gaji, na gaji da wannan wulaqancin da yan uwanka ke min’’

‘’wake maki wulaqancin? Fada min particularly’’ ya bata amsa
‘’kowa ma, kaga yanda fadila ke yi min, fisabilillahi kamar banice matar wanta ba, saboda tambarin agola da nake dashi a gidan nan, hatta anne ma ba sona take ba kuma na sani wallahi na gaji kaf danginka babu wanda ke sona, ita matar da aka auro maka ay ba a mata haka, sunfi janta a jiki ni kuwa da nake bare an kawo ni agola bani da qima da mutunci’’
Mikewa tayi tsaye rai a bace tana share hawaye shiko babu abunda yake sai kallonta
‘’laila, duk maganganun da zakiyi ya tsaya akan su fadila amma karki sake sako anne a ciki, sannan kina maganar basa kaunarki basa janki a jiki, ya akayi kika san basa kaunarki bayan ke kike janye jikin ki daga wajen su, bakya kaunar kusanci dasu, ke gani kike kinfi karfin shiga cikinsu’’ ya bata amsa shima ranshi ya dan soma baci.

‘’daman gaskia ce dai ba a son jinta,’’

‘’bana son jin wata Magana daga bakinki, kije ki shirya kizo mu wuce’’
Kai tsaye ta amsashi, ‘’bazani ba’’
‘’saboda me?’’
‘’banyi ra’ayi ba’’ ta amsa shi kafin ta shige bathroom tayi ramming kofar bamm

Ranshi yakai kololuwar baci sosai, when it comes to Laila tasan yanda zatayi ta bata mashi rai, yau shekara nawa Kenan abunda takeyi kullum gaba yakeyi, ada abun nata ba komai bane ba saboda bata comparising yanxu kuwa tunda ya auri aunty mubina bata da Magana sai ba a sonta a tsane, which shi yasan ba haka bane kuma duk wani problem daga ita ne, a komai saita nuna ta isa.

Fucewa kawai yayi daga gidan ya koma gidan gaisuwa, basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara na dare, inda suka bar aunty mubina da Laila karama saboda zata zauna da ita.




Saudi Arabia…..
A yau sabeeha ta cika sati biyu ciff a gidan da aka turo ta liken asiri, gaba daya tama manta da wani batun leken asiri.
A cikin sati biyu nan wata iriyar shakuwa ce ta wanzu tsakaninta da TAJ sosai, ita ke mashi komai, ita ke kula da duk wani abunda ya shafe shi, a cikin kwanakin ta gano halayenshi da abubuwan da baya so da wanda yake so.
Ta bangarenta ba karamin tausaya mashi take ba, don gaba daya a yanda ta fuskance shi da yanda yake abubuwa da tunaninsa gaba daya na yara ne, don kamar an shafe gaba daya tarihin rayuwar na shekarun baya an sako mashi na lokacin da yake yaro, ko sallah ma bai iya ba idan yana yi kamar dan koyo, abunda yafi bata mamaki dashi shine he’s very smart sosai, don duk abunda ta koya mashi ciikin lokacin qanqani yake dauka, gashi yana bala’in son yayar shi madam Kenan, wannan soyayya sabeeha ta shaida ta don bata taba ganin irin wannan ba, bashi da Magana sai first love first love, idan abunci zaici first love, idan barci zaiyi zaice yana son ganin first love, wani sa’in haka kawai zata taddashi yana kuka yana kiran first love indan ya kwana biyu bai ganta ba.

Ta bangarenshi kuwa, bashi da friend din data wuce sabeeha ita kadai ce friend din daya fara yi, kullum ita ke wasa dashi yanxu ita ke bashi abunci, yana ji da ita sosai saboda first love dinshi tace mashi friend dinta ce saboda haka shima friend dinshi ce, don babu abunda hidaya zata fada ko ta nuna tanaso shi kuma yaqi wannan abun.

Yau weekends duk kowa na gida ana hutawa, hidaya na part dinta while su fadwa na wajen garden ita da afiya.

Zuwan doctorn big baby da hidaya tayi hiring yasa ta futowa zuwa part din nashi, yau sati guda Kenan rabonta da zuwa part din wanda hakan ba karamin dadi ya mat aba don ya bata damar concentrating akan abubuwan dake gabanta da ayyukanta, sai a lokacin take jin data kori sabeeha datayi dana sani don wannan ce first caregiver din data dade har warhaka tana handling situation din taj, don da kansu suke guduwa saboda idan abun nashi ya tashi tsorata su yake yi don handling mai irin lalurar shi ba abu bane mai sauqi,

daddyn barad ne ya shigo da doctor din sai wasu maza kamar ma’aikatan dake karkashin sa ne, saman ya jagorance su har zuwa part din, daidai nan hidaya ta fito daga nata part din, gaisawa sukayi da doctor kafun su nufi part din nashi, itace ta bude masu kafar kafun su shige daga ciki.

Ko’ina fess fess babu qazanta as always don part dinshi kwata kwata ba a barin shi unhygienic.
Daidai nan sabeeha ta futo don bashi maganinshi na yamma, tana sanye da uniform dinta kalar ruwan kasa sai face mask data rufe fuskanta dashi, ‘’step out’’
Hidaya ta bata umarni, hakan kuwa yasa ta tattara abubuwanta ta fuce daga dakin gaba daya.
Cikin bedroom dinshi suka shiga, hidaya ce ta fara shugowa, yana zaune ya kafa ma kofar idanu yana jiran ganin sabeeha, cikin murna da farin ciki kuwa ya miqe tsaye har zai tunkaro inda yake ta daga mashi hannu hakan yasa suka karaso, wani iri dadyn barad yaji ganin yanda tayi mashi shima kanshi taj din saida yaji babu dadi, don he was so happy ganinta kawai da yayi, yanda yake wage baki kamar an mashi albishir da wani abu mai muhimmaci.

Su doctor na biye dasu a baya har zuwa inda yake, zama hidaya tayi baking ado inda ayke zaune kafin ta riko hannunshi, saida doctor suka karaso ya soma zaro ido, har jijiyoyin kanshi sun soma firfitowa rado rado alamun yana neman furgita.
‘’big baby’’ ta kira sunanshi, gaba daya attention dinshi ya tattara ya bata dukda tsoron ganin doctor dinnan da yayi, daman normally idan zasu zo kuka yake yi saboda allurer da suke mashi duk wata, baya so kwata kwata, ga wani abu da suke zuwa dashi kamar inji wanda suke saqala mashi a kanshi, wannan abun yana tayar mashi da hankali sosai.
‘’look at mee, your’re a good boy ko?’’
Girgiza mata kai yayi alamun eh kafin ta sake cewa ‘’bana son wannan kukan naka, ka natsu, im by your side kaji?’’

Saida ta tabbatar tayi capturing mind dinshi kafin ta dubi doctors din,babban dake cikin su ne yace ‘’sir ko zaka dan bamu waje’’
Ya fada yana kallon daddyn barad, wani irin kallon hidaya jamid yayi, tana ganin haka ta kauda kanta gefe kafin tace ‘’ba damuwa, you say anything a gabanshi’’
Gyaran murya doctor yayi kafin ya karaso inda taj din ke zaune ‘’hello handsome how are you, na kawo ma cholate’’
Cikin murna kuwa yace ‘’da gaske’’
‘’yes amma saika tsaya mun gama dubaka saina baka ka yarda’’

Girgiza mashi kawai taj yayi kamar wani dolo kafin yace ‘’no injection please uncle’’
‘’babu injection I promise’’
Sauran yaran doctor ne suka karaso da abun gwajin kwakwal war tashi, abun is handy ana connecting dinshi da computer, inda sauran igigiyoyin kuma kamar hula haka zaka nada su akanshi.

Haka suka fara sassaka mashi wannan wireing din akanshi, saida suka tabbatar sun saka ta ko’ina kafin daya daga cikinsu ya dauko wani dan syringe mai shegen tsayi kamar allurer doki, shidai daddyn barad na daga tsaye yana kallonsu.

Sai da suka shanmace shi dayan ya tsira mashi wannan doguwar allurer, idanunshi har sun soma jaa don saida aka soma zuba ruwan allurer ya tabbatar allurer dai akayi mashi, nan take ya fashe da kuka kuwa, hidaya dai idanu kawai ta zuba mashi, saida kukan ya isheta tace ‘’shut up, kai karamin yaro ne kake kuka’’
‘’madam ayi hakuri karamin yaron ne ay ayanxu,’’ doctor ya fada,
Jin haka yasa ta hade rai sosai, taj kuwa tunda tace yayi shuru dinnan haka ya gume baki yana hawaye idanunshi sunyi jaa sosai ya kafa mata idanu dasu ko gajiya da kallonta baya yi, dadyn barad dai kasa kallonshi yayi don ba karamin tausaya mashi yake ba, yau wata takwas Kenan da faruwar wannan mummunan hadarin daya sauya mashi rayuwarshi lokaci guda, Taj was a definition of a perfect young innocent man, he’s the sweetest yet the most controlling duk da he’s tough musamman ga waenda bashida kusanshi dashi, daga danginsa sai danginsa gaba da baya, da wuya mutun ya shiga rayuwar cikin sauqi don he’s very tough with his lifestyle.

Bayan an gama mashi wannan allurer kawai sai ya soma jijiga, hidaya dai miqewa tayi sauran yaran doctor nan suka zauna inda ta tashi suka ririke shi, wannan jijigar tashi effect din allurar ne, saida suka tabbatar ya futa hayyacinshi kafin doctor ya soma duba kwakwalwarshi da emotions dinshi don komai yana reading ta cikin laptop din, ya dauka kusan minti goma yana dube duben shi kafin ya sa yaran suka cire mashi wannan wiring din daga kanshi, a daidai wannan lokacin kuma jijigar ta lafa, kwantar dashi sukayi kafin likitan ya duba pulse dinshi, ganin komai normal yasa suka dan tsaya nay an mintuna, don allurar cikin minti ashirin take sakin mutun gaba daya.
Ai kuwa lokacin na cika sai gashi ya bude idanunshi ya zuba masu idanu daya bayan daya harya sauke akan hidaya, cikin sauri kuwa ya miqe zaune ya riko hannunta, ‘’first love, yaushe kikazo, I missed you please karki tafi!!’’

Ba tare da ta kalleshi ba tace’’doctor, whats his progress?’’
Nunfasawa doctor yayi kafin ya soma koro mata bayani, ‘’gaskia babu wani changes, saidai he’s stable kawai, brain dinshi na functioning saidai babu wani alamun change a tattare dashi.’’

Daddyn barad ne yayi saurin katse shi, ‘’wannan barcin da yake yi all the time fah?’’
‘’effect din magungunan shi, idan baisha sub a brain dinshi bazat huta ba, saboda zata dunga confusing dinshi da wasu flash memories dinshi na baya’’

‘’ya za ayi yayi recovering idan bamu barshi ya samu wannan flash memories dinba? Stopping him from having wannan memories din bazaisa a samu any progress ba, are you kunsan yanayin aikin ku kuwa?’’

Doctor ne ya kalli daddyn barad don baima son koshi waye ba, ‘’sir are you a doctor ne?’’
‘’no I’m not, but dis is a common sense, babu aynda za ayi yayi regaining memory dinshi idan har aka hanashi hakan’’

Sai a lokacin hidaya ta soma Magana ‘’jamid please, are you going to teach him how to work ne?’’

Dakatar da ita doctor yayi ta hanyar cewa ‘’first of all, you need to understand the psychological and medical reasons din daya sa yake shan wannan medication din, first of all, ayanxu his brain works like a child, sannan kwakwalwarshin ita ke controlling mind dinshi, kaga yanxu both 2 are connected, dalilin dayasa muka hanashi ya samu wannan flash memory din kuwa shine, any flash daya zo mashi zaiyi confusing mind dinshi dake controlling brain dinshi wanda hakan zai iya jawo mana wata matsalar, brain din itace center of universe din komai nashi, zata iya saka zuciyarshi ta buga ma tunda ayanxu ma he’s not normal, ina fatan wannan bayanin yayi maka’’

Nunfasawa jamid kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, wasu yan bayanai hidaya tayi mashi game da abubuwan daya shafesu kafin suyi mata sallama, suna gab da futa taj ya soma Magana ‘’first love ina friend, I was waiting for her yanxu ta futa, kin ganta? Yau munyi wasa nida ita’’ washe baki yayi excitedly yana bata labarin

Tsayawa doc din yayi yana sauraron bayanan nasa da mamaki, na farko abunda ya bashi mamaki shine ya akayi ya tuna event din dazun na futar yarinyar don bai kamata ace ya tuna ba saboda allurar tana da karfi sosai wanda karfinta kesa wanda akayi ma ya manta da duk abunda ya faru dashi a ranar, da wannan tunanin ya futa daga part din da yaranshi, daddyn barad kuma yayi masu rakiya don shifa yana jin kamar bai yarda dasu ba kwata kwata.

Suna fita suka tadda sabeeha tsaye bakin kofar part din hankalinta a tashe , da mamaki duk suke kallonta ganin haka ya sata cewa ‘’sir baisha maganin shi na yamma ba’’
Daddyn barad ne ya amsata ‘’don’t worry about it kije’’
Tana wucewa doctor ya bita da idanu kafin ya sauke wani murmushi ta gefen baki.

Bayan tafiyarsu doctor hidaya ma bata wani dade ba ta futo daga part din big baby ba ta wuce nasu, bata dade da shiga ciki ba kuwa saiga daddyn barad, tasan maganganun daya saba zai mata don haka ta zauna ta daura kafa daya kan daya.
‘’hidaya, kina ganin wannan…’’
Daga mashi hannu tayi alaman ya dakata ‘’jamid please not today, na fada maka koma menene indai akan batun big baby ne don’t ever question me, wannan tambayoyin da kake ma doctors din shi na menene? I trust them so please’’

Saida ya bari ta kai aya, kafin yayi wani murmushi mai kama da na taqaici kafin yace ‘’at this point ke nake tsoro HIDAYA!!!!!!!’’
Yana fadin haka ya fuce daga bedroom din, harya fuce bata bar kallonshi ba tana mamakin abunda ya fada, ‘’me yake nufi Kenan da wannan furucin nashi?, itafa har yanxu tana jin akwai abunda yake boye mata wanda bata sani ba, shike sashi questioning dinta koda yaushe, yanda yake kallonta anya kuwa bai gano……
Saurin kauda tunanin tayi “no that’s impossible’’ ta bama kanta amsa, nan take wani irin fargaba ta durar mata,…..



Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 23-24

Update!!!!

Washe gari da safe tun kafin alarm dinsu yayi ringing ta tashi, don yanxu ta fara gane komai na gidan da yanda alamuran gidan ke tafiya, wanka ta fara yi ta saka uniform dinta kafin ta fara nafilfilu, ta dade sosai kanta a kasa tana kiran sunan allah har alarm dinsu yayi kara.

Karfe biyar daidai ta fito daga part din nasu na ma’aikata kafin ta wuce sama, kamar kullum yauma ko’ina shuru babu motsi saima haske daya bade ko’ina, saman ta wuce cikin natsuwa kanta a kasa, daidai nan daddyn barad ya futo don zuwa sallah, gaishesa tayi kafin ta wuce part din taj.

Koda ta shiga part din batayi gigin shiga bangarensa ba saida ta gama gyaran parlorn kafin ta nufi bedroom din.

Lokacin data shiga yana daga zaune kamar kuwa jiran ta yake yi, murmushi yayi mata wanda ya sata sauke ajiyar zuciya mai nauyi, yau bata shugo ta taddashi yana kuka ba kamar kullum, “friend!!!”
“Naam friend good morning”
Ta amsa shi, murmushi kawai yayi mata kafin yace “first love batazo ba?”

Yanda yayi maganar abun tausayi, saida ta karaso ta gane yanayin da yake ciki, he looks so pale, bakinshi ya vushe sosai yayi fariii tarr kamar wadda ke jinya, ga idanunshi sunyi jaa sosai.
Haka kawai taji kamar he doesn’t sound like yanda yake koda yaushe, “friend kayi brush?, ga breakfast na kawo maka”
Daidai nan ta karaso bakin gado ta dan duqa don ajiye tray din gefen bedside table.

Kallon corn soup din yayi, take ya soma jin wani abu ya soma zuwan mashi maqogaron shi kamar amai, batama lura dashi ba ta dauka bowl ta miko mashi, daidai nan kuwa ya soma kakarin amai, lokaci guda ya burkice, amai yake son saidai cikin nashi babu wani abun arziki a cikinsa da zai amayar, ganin yanda yake struggle tare da riqe maqogaron shi yasa ta saurin ajiye bowl din hankali atashe.

“Subhanallah!! Menene? Wani abun ke damunka”
Nuni yayi mata da bowl din kafin ya kauda kanshi gefe, “bana so”
Sai a lokacin ta lura da abuncin ne baya so, gashi batasan ya zata ya ba, abunda aka rubuta kenan a breakfast timetable dinshi kenan, gashi dole saiyaci abunci zaisha magani.
“Baka son wannan?”
Ta karashe tana nuna mashi bowl din, girgiza mata kai yayi abun tausayi, “meysa baka so?”
“I hate it” ya sake fada
“Kayi hakuri kasha kaji friend saboda ka samu kasha magani Okay?”

Juya mata baya yayi a shagwabe tare da nade hannayenshi a kirjinshi “no noo banaso”
Ya karashe kamar zaiyi kuka.

“Friend dan Allah ko kadan ne kaji? Kaga maganinka ma baka sha ba kar lokaci ya kure”

“I don’t want to”
“Idan baka sha ba first love zatayi fushi dakai” sabeeha ta fada hoping

Please Login or Register in order to submit comment