Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nashi is even worst don yayi auren ne kuma cikin sirri harda ‘da shekaru wajen bakwai da suka wuce, kuma ba tare da saninta ba.

Hannunta dake cikin nashi ta cizge, idanunta sunyi jaa sosai sai hawaye dake shirin kwaranyo mata, “da gaske ne kenan,”
Saurin dagowa yayi jin furucinta, da mamaki yake kallon bakinta dake furta, “wannan yaron danka ne?”
“Yes” ya amsa ta,
Wani irin jiri ne ya soma divanta, tuni tayi baya zata fadi ya taro ta, cikin sauri ta buge hannunshi tayi baya idanunta sunyi jaa sosai,

“I’m sorry fattu,”

“Shekara nawa kenan? Tun yaushe?” Ta jefo mashi tambayan nan

“Fattu duk wannan bashida amfani yanxu, listen to me…”
Saurin katse mashi hanzari tayi “abdallah!!!! Me kunne na ke shiri jiyo min? Wannan wani irin cin mutunci ne kayi min abdullah? Why why whyyyyy? Aure kayi a boye ba tare sa sani na ba for how many years? For 7years? Innalillahi wa inna ilahi rajiun? For good seven year? Kaci amata abdallah, ka cuceni?”

“Fattu please calm down”
Idnaunta da sukayi jaa ga hawaye kwance akai ta zuba mashi “don’t tell me calm down, you have no right to do such”

“Fattu please wannan dalilin yasa na kasa fada maki kamar yanda nace kaddara bata wuce kan kowa, i know you’ll be hurt shiyasa ban fada maki ba”
“Abdallah na gwammace na dauki wannan pain din shekaru da suka wuce akan yanxu shin Kasan abunda akayi kuwa? Kaci amanata kayi aure a baya na wannan shine d most humiliating abu da zan fuskanta a duniya, shin kasan ma’anar auren da kayi bada sanin na ba? Shin kasan tabon da kayi min a anan duniya? Ka mance da culture dinmu ne? Duk matar da hakan ta faru da ita tana da tambarin….”

“Fattu!!!!!! Abunda nayi addini bai haramta ba, aure nayi na sunnah, idan addini bai haramta ba then why abunda community zasu ce zai dameki?”

“Aure ba haram bane ba shiyasa nace daka fada min tun wuri, wannan abu da kayi is the most disgusting and evil doing, how could you? Shin kasan me hakan ke nufi kuwa? Kayi aure this all time bada sani na ba? In my entire life da tarihin iyaye na bamu taba fuskantar wannan humiliation din ba yanxu sai akaina? Kayi min babban tabo da har abada bazai goge ba?Duniya zata kalleni da wannan and the worst part shine harda da? Harda da????? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun?””””

Nan take ta sake burkicewa ta fashe da wani matsanancin kuka sosai, ihu zagi insult words babu wanda batayi mashi ba, yaci amanarta yaci amanarta ya cuce ta wannan auren da yayi ba karamin bakin fenti yayi mata ba harda da, da ace babu yaro da sauqi ita bata ma damu da sanin ya akayi yayi auren ba, amma yanxu idan duniya ta san da wannan shikenan, she can’t face the world don anan kasar sun maida abun kamar wani babban zinibi, abunda yafi tsaya mata shine gashi ita bata taba haifar da namiji ba, abu ya gama tarar mata, ga auren boyen daya boye mata, ga yaro kuma da namiji, at that moment ji tayi dama mutuwa kawai tayi akan ta fuskanshi wannan baqin tabo a gaban duniya, ita kanta to her self batajin she can accept this,

Babu yanda abdallah baiyi ba don rarrashinta amma kiff ta rufe ido, jikinta har rawa yake yi don abun ya shigeta sosai, “fattu please”
“No please get out get out bana son sake ganin fuskanka abdallah yalla yalla get out,” ta karashe da larabci

Hidaya data hauro saman babu abunda bata ji ba, saida taji motsin futowar abuh yasa ta labe a corridor don kar ya ganta, yana futa kuwa fattu tayi banging kofar, girgiza kanshi kawai yayi yana tausaya mata, dole zata shiga irin wannan hali daman yayi hasashen haka, kasa ya sauka zuwa wajen khaal,
Yana wucewa hidaya ta karasa bakin kofar, tun daga bakin kofar ta soma jin kukan ummuh, kuka sosai takeyi tana screaming da larabci, words of insult babu wanda bata rafko ma abdallah.

Bangaren su abdallah, yana karasowa kasan ya tadda yaron zaune shi kadai wajen kayan wasan su fadwa, suna wasa hardashi, jiki a mace ya karaso inda khaal yake zaune kafin ya zauna,kallon yanayin shi khaal yayi hakan ya tabbatr mashi da abunda yayi hasashe, haka nan ya fara tausasa shi yana bashi words of encouragement tunda babu yanda za ayi da wannan alamarin.

Bangaren fattu haka ta wuni a dakin nan tana kuka kukan baqin ciki, bata taba tunanin zata taba fuskantar rana irin ta yau ba, bata taba kawo hakan ba kwata kwata abun yazo Mata unexpectedly, bata jin zata taba yafema abdallah akan wannan abun da yayi mata.
Hidaya dake tsaye bakin kofa har barci saida tayi ta farka, kuka dai itama babu wanda batayi irinshi ba tana mai sauraron yanda mahaifiyarta ke kuka.
She was so shattered, dukda batasan karfin laifin mahaifinta ba but damuwanta shine kukan da mahaifiyarta keyi.

Haka aka shafe wata guda fattu na cikin kunci, abu dai gaba yake yi kullum, kullum tana kulle a daki ta rame ta jeme sosai, idanunta sunyi ciki ciki kamar ba fattu ba, duk wanda ya rabe ta korarshi take, abdallah kam bata yarda ma ta ganshi, ta tsaneshi yanda ta tsani mutuwarta, hidaya ce kadai ke samun shiga wajenta, duk sanda ta shiga dakin a zaune zata taddata ta kafa ma window idanu.

Taj kuwa yana samun kulawa wajen sabuwar maid da abdallah yayi employee wadda zata kula dashi, bangaren su fadwa da afiya basu san meke faruwa ba don gaba dayan su ba wani wayo ne dasu ba, saidai sun fuskanci mahaifiyarsu tana cikin kunci don rabon da su ganta har sun manta.

Yau dai abdalla kasa hakura yayi wajen karfe goma na dare ya wuce dakin fattu, allah yaso kofar a bude take don hidaya bata dade da futa ba don hado ma mamanta tea ko zata sha don kwata kwata bata cin abunci ta zama kamar wata kurma bata cin komai bata cewa kala sai kuka.

Koda ya shigo dakin a bakin gado ya tadda ta, ta rame sosai daga ita sai rigar barci da alamu kayan ma sun jima a jikinta kuma dasu take kwana take wuni, gashin kanta duk ya yamutse ya barbarzu don kwata kwata bata bashi attention don bashi ne a gabanta ba.

Batasan da zuwanshi ba sai ganinshi datayi a gabanta ya duqa yana mai kamo hannunta, cikin sauri ta zame hannunta ta sauko daga kan gado kamar taga wani abun kazanta, saurin kauda kanta tayi don ko ganin shi bata san yi.
“Meysa ka shugo min daki? I taught nace maka ko ganinka bana son yi? Bana son mu shaqi koda iska daya ne dakai munafiki, azzalumi, maci amana”

Yaji zafin maganarta amma hakan bai sashi nuna mata ba yace “fattu kiyi hakuri, ya kamata ace komai ya wuce, please, yaranki are loosing you, I’m losing you too, you’re not your self, dan allah kiyi hakuri mu hadu mu kula da yaranmu please”
Wani irin mugun kallo tayi mashi kafin ta raramo mashi wasu manyan curse word “munafiki, annamimi, wasu yayan zamu runguma? Don’t ever call your self a father, you are nothing but a hypocrite, you’re worst than a devil”
Marin daya sauka ne akan fuskanta yasa ta dagowa tana kallonshi, jikinta har tsuma yake, shima ranshi a mugun bace yake sosai don bai taba tunanin zata kirashi da wannan mugayen kalaman ba dole yayi putting some sense akanta.
Ba zato ba tsammani yaji saukan mari shima a fuskanshi, the next thing kuwa sai shaqo mashi colar datayi “har kai ka isa ka mareni? Har ka isa ka sanya tafin hannunka akan tsaftattciyar fuskata? I hate you, na tsani saninka da nayi arayuwata, you’re nothing to me but a peace of shit, na baka komai a duniyar nan na baka yaya har uku saboda ban baka namijin ba shine ka kasa hakura saika cuceni ka nunama duniya abunda zasuyi min dariya akai? babu abunda zaka sakamin dashi sai wulaqanci mafi muni? Ka kawo min shegen danka cikin gidana sannan kace min wai mu hadu mu kula da yaranmu? Kana tunanin after all you have done komai zai koma yanda yake ne a da? Eh?” Ta kurma mashi uban kara tana mai dukan kirjinshi kamar mahaukaciya, saida tayi mai isarta kafin ta soma jifanshi da abubuwa, “get out, get out, you made me who i am now, ka maida rayuwa na miserable, kaima you will Never have that peace of mind cause i will never fogive you for this kuma ka fuce min da wannan tabon daka kawo min gidannan ka futar min da shegen danka daga gidana don wallahi bana kaunar ganinka da shi, out!!!!”
Yana futavta soma fashe fashe,duk wani abu dake cikin dakin saida ta tarwatsa shi da hannunta, jikinta yayi jaa sosai gashi harda jini, hidaya dake tsaye ta labe tana jin duk abunda ya faru, kasa rikewa tayi itama ta fashe da kukan saida abuh yabar dakin ta samu damar shiga bedroom din, tana shiga ta karaso inda ummu ke tsugunne tana kuka, lallashinta ta soma yi amma ina, tea din data kawo mata ma watsar dashi tayi a gefe sannan ta daka mata tsawa “get out!!!, bana son ganin kowa “
Dan dole haka hidaya ta fuce daga dakin tana kuka tana waiwayon mahaifiyar tata.

Bayan ta koma dakinta kasa kwanciya tayi haka nan ta sake futowa don zuwa duban mahaifiyar tata lokacin wajen karfe uku na dare, koda ta shiga magaifiyarta ta hango tana kokarin committing suicide a jikin wani karfen chandelier, cikin hanzari hidaya ta taho a guje ta tallabo kafarta tana kuka tana ihu,lokacin fattu harta jigata, badan zuwan hidaya ba da tuni ta mutu, da kyar hidaya ta samu ta kunce mahaifiyar tata kafin ta rungumeta tana hawaye, “ummu please, karki tafi ki barmu, ina rokonki please ki koma yanda kike kiyi hakuri, bazan iya rayuwa babu ke ba”
Saurin tureta fattu tayi kafin ta kamo kafadunta ta damke su tace “meysa zaki shugo? Wayace ki shugo?”
“Ummu mutuwa zaki fah? Kashe kanki zakiyi? Ya zamuyi”

Jijigata fattu ta somayi kafin tace “listen, mahaifinki yaci amanata ya cuceni, ya kawo wani dan daya haifa da wata matar, ya kulla wannan cin mutuncin da ya sanya duniya ta dunga kallona da wannan embarrassment din, look into my eyes, ko bayan raina don’t ever accept that child, don’t ever let him have all this power, make his life miserable as the result of what his parent makes me go truh, kinjini, don’t ever”
Ta karashe tana kuka, saurin girgiza mata kai hidaya tayi tana mai mata alkawari.

Bayan kwana biyu abubuwa sun dan sauya saidai har zuwa lokacin fattu tana cikin kunci, ba laifi tana yin wanka saidai abunci ne har zuwa yanxu bata ci kwata kwata.

Kuka kuwa duk dare saitayi shi, abdallah kullum saiya lekata saidai kuma baya bari ta ganshi don yanxu hauka takeyi mashi tuburan, bangaren su afiya kuwa sun fahimci tun zuwan abuh yayi da wannan yaron mamansu ta sauya, kuma suna ganin yanda take kuka sosai in sunje wajenta sai tayi ta korarsu, haka suka taso da wannan kuncin a ransu sannadiyar wannan yaron.
Bangaren tajudeen kuwa daman yaro ne miskili, babu ruwanshi da shiga harkar kowa, baya magana ma sosai saboda bashi da yarda, daga abuh sai wannan nanny din dake kula dashi, daman tun tasowarshi bai taso da sanin mahaifiyarshi ba infact bazai iya cewa ga fuskanta bama don bai taso da ita ba.
Su fadwa da afiya yanxu sun daina wasa dashi kwata kwata, kullum yana zaune shi kadai a daki don ko futowa baya yi saboda tsoron haduwa dasu afiya karsu dakeshi, har aka sauya mashi school zuwa irin tasu hidaya, baya magana kwata kwata saboda bashi da sabo.

Ranar wata laraba hidaya ta shiga bedroom din fattu don kai mata abunci, a yanayin yanda ta ganta ba karamin tashin hankali ta shiga ba don ta taddata kwance a kasan bathroom cikin, cikin hanzari hidaya ta karasa inda take tana mai kiran sunanta “ummuh ummuh” shiru babu response, cikin tashin hankali ta soma taba ta amma ina kwata kwata bata motsi hankali a tashe ta sauko kasa dai dai nan khaal ya shugo gidan da motar ambulance daga asibiti, wannan rana ta kasance rana mafi muni a cikin wannan ahalin, abuh ya mutu sanadiyar heart attack daya samu while ummuh kuma ta yanke jiki ita ma ta fadi zuciyarta ta buga,
Babu wanda yakai hidaya shiga tashin hankali da kidima don ita ce tasan zafin mutuwar, tayi kuka sosai ta futa hayyacinta.

Bayan kwana arba’in kula dasu hidaya ya dawo hannun khaal, shike kula dasu da alamuransu gaba daya harda taj.
It was a tough moment of life for all of them harda khaal daya rasa dan uwansa saidai yayi alkawarin kula dasu kamar nashi don bai taba aure ba.

Haka suka taso gaba dayansu, hidaya bata magana kwata kwata duk abunda ke wakana a gidan bata cewa uppan, haka zalika taj, bata kaunar ganin yaron nan kwata kwata, khaal kuwa yana kokari sosai wajen ganin ya kula dasu, da farko ya shaida yanda hidaya ta tsani taj sai kuma daga baya yaga sauyawanta lokaci guda, sai ya zamana babu wanda take da kusanci dashi daya wuce taj, ko su fadwa bata nuna masu so yanda take nuna mashi, tana kula dashi sosai haka ya taso bashida abunda yake so sama da hidaya, kukan shi hidaya, farin cikin shi hidaya komai nashi itace.

Hidaya was so smart, ta gama karatunta inda ta karanci business alokacin tana da shekaru ashirin da biyar chir a duniya, a lokacin ne ta nuna tana son shiga harkar business dinsu wanda khaal bai musa mata ba ya barta don daman shi yana kula ne kawai da dukiyarsu badai don san ranshi ba yake kula da company din ba Kuma inheritance yayi decending daga mahaifinsu zuwa kansu.

A lokacin su fadwa da afiya sun kammala secondary education suna kokarin shiga collage of education leaving taj behind don ba a sakashi a school da wuri ba, lokacin daya kammala duk sunyi nisa sun barshi, a wannan lokacin ne kuma hidaya stand on her feet,ta soma bujire ma khaal, itace ke da say a gidan, itace ke cewa kaza za ayi kuma dole ayi.
Khaal respected her as the elder of the family don yana son ta zama itace madafar da kannenta zasu jingina, ko bayan ranshi shima wannan yasa bai taba hana ta ba idan tayi making decision akan kannenta, lokacin da taj ya cika shekaru goma sha bakwai ciff a lokacin ya gama karatunshi wannan yasa ta yanke shawarar turashi kasar waje, khaal bai musa ba ya barta ta turashi karatu a england, inda itace ta mashi komai daya dangancin school din kuma ta kaishi da kanta, she provided duk abunda tasan zai buqata na gata da komai kafin tabarshi achan kasar.
Taj yayi kukan rabuwa da ita sosai don yana masifar sonta kuma ya shaqu da ita….

Ayi hakuri da wannan zuwa gobe zan cigaba bana jin dadi ne wallahi.
Thanks for understanding.





Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 33-34
After 10years
Bayan shekara goma da tafiyar taj, abubuwa da dama sun sauya ciki kuwa harda haduwar hidaya da jamid har zuwa ga auren su, sai kuma matsalolin da khaal ya fuskanta wajen hidaya,bashida control kwata kwata akanta, babu abunda ke gabanta sai aiki, arzikinsu kuwa alhamdulillah ya bunqasa sosai wajen sau uku, da taimakon hidaya da khaal, don ita ke running companyn.

Maganar taj kuwa tun bayan tafiyarshi ta hana kowa ya kusance shi ciki kuwa harda khaal, babu yanda baiyi ba akan ta dunga barin shi yana zuwa gida amma kiri kiri tace ah ah abarshi yayi Karatu, daga bangaren taj din shima bason dawowan yake ba don ya gama sabawa da nan din, gaba daya rayuwarshi da girmanshi duk anan yayi, and beside hidaya na zuwa ganinshi all the time wanda hakan yafi mashi komi a rayuwa kuma babu abunda ya nema ya rasa don ta gama bashi komai da ta san zai nema.

Damuwar khaal akanshi daman bata wuce sanin me yakeyi achan din ba, dukda hidaya ta kasa ta tsare akanshi ta hana kowa kusantarshi hakan baisa khaal ya barshi ba, shima haka zai shirya yaje har chan England din don ganinshi saidai duk sanda Zaije cikin rashin sa a baya samun shi wanda hakan duk shirin hidaya ne, da zarar khaal zaije ganinshi saita tura taj din vacation duk dan karta bari su hadu wannan yasa ya taso hidaya ce komai nashi, bai damu da kowa ba sai hidaya.
Da farko khaal bai kawo komai aranshi ba saboda yanda take son taj din sosai sai daga baya da abubuwan nata suka fara yawa ne yasa ya miqe tsaye akan taj, ya fara tunanin meysa take hakan,maysa bata son ya dawo? Daga karshe dai haryazo ya fara zargin ko saboda bata san ya karbi mukamin da take dashi a company ne? Tsoronshi daya daman akan hakan ne don baya fatan ranar da zatazo su fara samun matsala a junan su, duba da yanda kuma take son shi sosai wannan ya sashi jin ba hakan bane don haka ya zuba mata ido kawai har zuwa lokacin da taj din zai kai shekara talatin a duniya, da zarar yakai wannan shekaru dole ya dawo ya karbi legacy din family din.


Duk karshen wata hidaya ke zuwa ita kadai ta duba shi, haka zata shirya taje ta kwana biyu sannan ta dawo.
Har ya kammala karatunshi na degree fannin engineering for 5 years wanda shima itace ta zaba mashi abunda zai karanta din zuwa masters daya sake yi, bayan ya kammala ta sake saka shi dora wani karatun.

A ranar da taj ya cika shekaru ashirin da tara khaal ya samu hidaya da maganar dawowan shi, Lokacin daya fara maganar dawowan nashi bata nuna mashi komai ba Saima shaida mashi datayi zai dawo idan ya kammala second degree dinshi da yakeyi, wannan excuse din data bayar yasa khaal yyi shuru bai sake cewa komai ba, ana nan har shekara ta sake zagayowa inda taj ya cika shekara talatin cir a duniya, nan ne fa khal ya miqe tsaye shima akan dole sai taj ya dawo saboda ya karbi responsibility dinshi a matsayin shine da namiji a Cikin familyn, babu irin matsalar da khaal bai samu ba daga hidaya, inda ta nuna mashi cewa babu wanda ya isa ya fada mata yanda taj zaiyi rayuwarshi, she’s doing what is best for him, kuma karatun da yakeyi shi zai amfana, duk wannan excuses din data dunga bayarwa are not valid to khaal, don ya kasa gane wannan wani irin karatu ne, taj yabar saudi yana da shekaru sha bakwai a duniya and now it’s over 13 years.
sai a lokacin ya fara ganin true intentions dinta saidai har zuwa lokacin yaqi aminta da hakan ne, kwata kwata bata ganin girmanshi kamar ba kanin mahaifinta ba, har tazo ta kaiga bashida ta cewa akan alamuran family din, wannnan abu yayi mashi zafi sosai har ya fara tunanin rabuwa da ita da qannen nata suyi abunda sukaga dama don su afiya ma sun kangare, sai abunda sukaga dama sukeyi, saidai tunawa da dan uwansa da amanar daya bar mashi yasa kawai ya danne duk abunda ke mashi zafi ya cigaba da hakura da abunda takeyi.
Da taimakon jamid da shareholders khaal ya samu yayi forcing dinta dole ta sashi dawowa, ranta yayi mugun baci ganin harda jamid a cikin waenda suke jayyaya da ita akan taj, babu irin isa da bata nuna masu ba akanshi saidai tasan tunda shareholders suka shugo alamarin dole ta hakura kuma babu yanda zatayi ta sauya yanda rules din suke, saidai har zuwa lokacin bata nuna masu taqa maiman dalilin daya sa ta hanashi dawowan ba saima nuna masu shine baya son dawowa da takeyi.

Hidaya dai tsara ma taj rayuwar da zaiyi tayi, tun achan england ta chusa mashi qiyayyar dawowa kasar, saida ta tabbatar ya saba da nan din sosai har yaji baya son barin kasar.

England
Wayarshi dake cikin aljihunshi ce ta soma ruri, daga kwancen da yake ya ajiye dumbells dake rike da hannyenshi guda biyu, dagowa yayi zaune ya gyara zamanshi kan weight bench, greyish idanunshi da gashin ido suka kwata luff luff akai ya soma budewa, bin wajen yayi da kallo mutane maza da mata jajayen fata kowa na hada hadarshi, daman yawanci anfi zuwa during weekends.
Kyakyawan saurayi ne ajin farko, gashi fari tass shima, zufa ta gama wanke shi sanadiyar workout din da yakeyi incoming call din ya katseshi, Sanye yake da fitness hoodie mai gajeran hannu da ta dan kamashi don ana iya hango shatin 6packs din dake a shafe wajen cikinshi, gefen damtsen hannunshi wani dan baqin zane ne kamar tattoo dan karamin, sai wani short da leggings daya saka daga ciki, kayan sunyi masifar amsar jikinshi dayake maintaining physique dinshi, he’s so fit and huge.

Wayar dake ta faman ruri ya zaro yana mai kallon screen, ganin wadda ke kiranshi, ya sashi saurin cije lebenshi da sukayi jaa kafin ya sauke wani irin sanyayyan murmushi mai melting zuciyar mata.
Daga wayar yayi cikin hanzari ya soma magana yana mai lumshe idanunshi ya sauke ajiyar zuciya sound of relief
Puffy lips dinshi ya soma motsawa ahankali
“First love!!!” Ya furta cikin muryarshi wadda bata futa sosai at the same time yana lumshe ido jin muryarta kadai.

Saurin miqewa yayi, wayar har zuwa lokacin tana hannunshi don akwai airpod a kunneshi, dagowa nayi don kallon asalin height dinshi, yana da tsayi da jiki mai kyau, masha allah kawai za ace.
Magana akayi daga chan wadda ya sashi sakin wani irin murmushi kawai.
Wayar ya zura cikin aljihunsa kafin ya duki katon bottle dinshi ya nufi hanyar futa daga gym din.
Toilet din gym din ya fara shiga ya cire hoodie din tashi yayi wanka kafin ya sauya kaya zuwa waenda yazo dasu wasu arnayen english wears designers.
Sense of dressing dinshi is just different, daga gani yasan irin shigar dake mashi kyau.
A gurguje ya gama ya saqala agogoshin sannan ya saka wani shade baqi ya futo da back pack dinshi.

Daidai inda motarshi take ya nufa ya danna keys din, cikin arniyar sport car din tashi ya shiga, yana shiga ya kunnata kafin yayi reverse yabar wajen.

Anatse yake driving cikin kwarewa, fuskanshi har zuwa lokacin dauke da murmushi, hannunshi daya na kan steering yana murzawa cikin kwarewa ga sound din cool music na tashi.

Tafiyar minti goma ta kawoshi airport, yana parking ya fito bayan ya rufe motar tashi.
Cikin airport din ya nufa bai tsaya ko ina ba sai private lounge na arrivals,yana zuwa ya soma dube dube ko zai ganta, daga chan nesa kuwa ya hangota a tsaye tana waya, tana sanye da abaya sai baggage dinta dake gefenta.

Ganin fuskanta kawai ya sashi sauke wani irin murmushi mai wuyar fassara.
Takowa ya soma yi har zuwa inda take, sai a lokacin ta lura dashi, sanin abunda zaiyi yasa ta daga mashi hannu alamun ya dakata, chak kuwa ya tsaya yana murmushi yana kallon fuskanta ba tare da ya damu da gwale shin datayi ba don harya bude hannunshi yana shirin rungumeta, kallo daya ta mashi ta dauke kanta daga kanshi, saida ta gama wayan kafin ta maido da dubanta gareshi, fuskanshi kawai ta zuba ma idanu, ya kara kyau ba kafan ba compare to last zuwan da tayi, shi kamar ma kullum kara kyau yakeyi da cikar ido.
Cikin british accent dinshi a shagwabe yace “first love” kafin ya rumgumeta gaba daya, “i missed you so much first love”
Shuru kawai hidaya tayi tana mai sauraronshi harya gama kafin ya saketa, “daga ina kake? I’ve been waiting”
“Sorry for keeping you waiting first love”

Ba tare da ta kalleshi ba fuskanta na nan yanda take ba yabo ba fallasa, duban agogon hannunta tayi kafij tace “next flight dina zai tashi in the next 10 mins, seat let’s have a chat”
Zama sukayi yana kallonta da mamaki, ganin haka ya sata cewa “ba zama nazo yi ba, i had to stop by saboda inason muyi magana.”

Attention dinshi gaba daya ya bata ya natsu sosai cikin ladabi yace “okay first love”

“Get ready by monday inason ka dawo saudi”
Cikin sauri ya dago yana kallonta, girgiza mashi kai tayi alamun yes kaji abunda na fada,
“No but” ta katseshi don tasan abunda

Please Login or Register in order to submit comment