Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hira sosai inda nanna ta zauna kusa da yar uwarta anne suma suka fara hira.

Hannun anne na cikin na yar uwarta don murna, nanna da anne yan uwa ne, ciki daya suka fito,anne ce babba sai nanna mabiyarta dukda ta girmeta sosai.

Rarraba idanu nanna(grandma) ta soma yi kafin ta maida dubanta ga matar Sameer ‘’ina babban yayan ne ban ganshi ba?’’
Cikin ladabi da kunya matar ta dago ta kalleta ‘’ay ya tafi wani course a Europe yau wata guda kenan’’
‘’Ayya shiyasa kennan’’ nanne ta fada tana mata murmushi.
Sallamar da akayi ne yasa suka dago gaba dayansu, wadda ke gaba ce ta soma fada, ‘’wai ace mutun ya tsaya yangan banza da wofi, wallahi next time kika kara bata min lokacin bazan kara jiranki ba shirman banza kai, kai kuma hamad ka riqe package din da kyau karka yarda cake din’’
Wanda ta kira da hamad kanshi na kasa ya rike wani package da hannu daya,dayan hannunshi kuma key din mota ne da wayanshi, saurayi kyakyawan gaske black beauty, bazai wuce 22 years ba gefenshi kuma wata yar budurwar yarinya ce akalla bazata wuce 18 years ba, sanye take da wata doguwar rigar material datayi mata kyau, baka ce kuma kamanninta daya da hamad din saidai shi yafita kyau, hannunta itama rike da wayaa latest iphone fuskanta tasha makeup a wadda ya amsheta, wadda ke gaba da alamu mamansu ce.

‘’sannu da zuwa anty fadila’’ yaran suka fara fada suna gaisheta, sai alokacin ta dago don gaisheda anne, ganin nanna yasa ta sauri waro idanu tare da tahowa cikin sauri ta rungumeta ‘’nanna, saukan yaushe’’
Dariya nanne tayi ta rungumeta tsam itama tana mai jin dadin ganinta tace ‘’my daughter, nayi missing dinku wallahi, how are you ya mai gidanki’’
Murmushi tayi wanda yasa duk mutanen wajen suka zuba mata idanu, don da wuya murmushin anty fadila ya futo shiyasa kowa yafi son anty bahijja don ita tafi faran faran ga son mutane sosai, anty fadila kuwa akwai fada bata daukan nonsense, gashi ta iya dressing don ta iya buga naira a jikinta, to kudin ne ma gashi nan kamar zai kashesu.

‘’yana nan lafiya nanna, ya turkey,fatan kin dawo Kenan shekara kusan biyu fa rabonmu dake’’
Murmushi nanna tayi kafin tace ‘’na dawo Kenan insha allah bazan koma ba,’’
Yaranne suka soma cewa ‘’yay’’ suna murna,

Sama sama fadila suka gaisa da matar Sameer kafin ta maida dubanta ga anne tare da taya ta murnar cika shekara sittin a duniya.
Hamad ne ya karaso ya tsugunna har kasa ya gaisheta kafin Laila itama ta rungumeta tana mai farin cikin ganinta.

Haka suka gama celebrating 60th birthday din anne cikin jin dadi da murna har mutanen US saida suka kirasu sukayi video call inda suka taya anne murnar cika shekara 60th a duniya kafin su wuto gida.

Saudi Arabia……
Karfe biyar daidai jirginsu ya sauka a international airport dake garin jedda, daya bayan daya suka fito, gaba daya suka sauko daga jirgin inda wanda ke jagorantarsu ya jagorance su zuwa wajen barrier din dake controlling shige da fuce na kasar, mazan na daga gaba while matan ba biye dasu har suka shigo cikin airport din, checking dinsu aka fara yi daya bayan daya don ganin information dinsu, basu wani samu matsala da immigration din ba don haka ana gamawa dasu suka fuce daga airport din.
Bayan sun fito daya bayan daya wanda ke jagorantarsu ya soma karbar passport dinsu kafin su shiga bus din da aka tanadar masu ta agency company don tabbatar da babu wanda ya gudu.

Sanyayyiyar ni’ima ce tare da fargaba ta saukar ma sabeeh lokacin data shaqi iskar qasa mai tsarki,harga allah hankalinta yana gida musamman mamanta da inna dake kwance asibiti.

Rarraba idanu ta dunga yi har suka shiga cikin bus din, at that point ta hakura kawai ta barma allah komai, don babu abunda yayi saura kuma,baiwar allah saita zama wata iri, kuka dai tasha kuka kamar babu gobe, tsoron da take ji ya wuce musali, matar da suka taho tare ma bata ganta ba don bata shugo cikin bus dinba, abunda yafi bata mamaki atare duk suka fito juyawar da zatayi kuma ta nemeta ta rasa ta.
Sauran yan matan ma rarraba idanu suka dunga yi, wasu daga cikin su murna suka dungayi gashi a saudia wasu kuwa hankalinsu tashi yayi don basu san ya rayuwar kasar take ba.
Tafiyar minti talatin sukayi suka karaso company, dukda garin bai soma washe ba amma inkaga yanda mutane ke hada hadarsu kamar da rana.
Fitowa sukayi daga cikin motar kafin a wuce dasu cikin agency din, mazauni aka basu da ruwa da apple kafin gari ya waye.

Wanda ya jagorancesu ne ya nuna masu inda bandaki yake da wajen yin sallah na musulmai, mazan dai mikewa sukayi suka wuce wajen sallah while matan kuwa suka kasa miqewa saboda tsoron karsu bata, sabeeha ce kawai ta iya dannewa ta miqe ta wuce bandakin, saida ta biya buqantunta ta dauro alwala har tayi sallah a wajen sallah kafin sauran su shiga wajen suma.

Suna nan zaune har wajen karfe goma har aka kawo wasu daga wata kasashe daban kafin a tattara su waje guda, wata agreement paper aka basu kowanne don yayi sighing kafin a rarraba masu wani tag mai dauke da sunayensu a jiki tare da sunan agency kafin kowannensu ya saqala tag din a wuyanshi.


Sorting dinsu masu agency din suka fara yi base on shekarunsu da abunda suka fi kwazo wajen yi kafin a fara futar dasu, don tun daga kasashensu ake masu training kafin a kawo su, agency din data kawo sabeeha ma AA agency Kenan itama tana karkarshin waenda ke kawo masu aiki dukda basa bin dokokin daukan yan aikin saboda su basa yin wani training suke aiko wa, wasu daga cikin yaranma basu san inda za a kaisu ba ake daukosu kamar su sabeeha Kenan, don saida suka shiga jirgin matar nan take mata bayanin komai.

Wasu daga cikinsu manyan company za a kaisu wasu kuma gidajen da sukayi requesting maids za a kaisu, wasu daga cikinsu ma har asibiti za a kaisu shara da dai sauransu, wasu gidan abunci, wasu har makka ana kaisu suyi aiki a masallaci.

Sabeeha dai bata san inda aka wullata ba, haka aka tasata da wasu a gaba acikin motar agency su kusan biyar.

Tunda ta zauna cikin motar take bin titin garin da kallo dukda sunyi zaman kasar waje da maman ta kafin su dawo rayuwar talaucin da suke ciki hakan baisa ta danyi kauyanci ba da mamakin wai yau itace a kasa daban, gaba daya tunaninta yayi nisa ya tafi wani wajen har suka karaso wani gida, sunanta da balaraben daya dauko su ya kira ne yasa ta saukowa daga cikin motar, wata jakar goyo ya bata kafin su shiga cikin gidan.

Gidan bashi da wani girma sosai, irin tsoffin ginin nan ne wanda ya dan kwana biyu, ciki suka shiga inda mutumin ya jagorance ta, hannunshi rike da wata paper.
Koda suka kwankwasa kofa wata balarabiya ce ta bude kofar, daga ganinta ta dan manyanta, mutumin ne yayi mata bayani cikin harshe larabci kafin ta karbi paper din tayi sighning, tana signing ya wuce ba tare da ya kalli sabeeha ba.
Matar kuwa ganin ta tsaya a tsaye kamar wadda za a sace,sai faman zare manyan idanuwanta take, hakan ya sata ta mata nuni da hanyar cikin gidan.
Ciki matar ta shige sabeeha na biye da ita, gida ne gidan bene bashi da wani girma sosai.
Anan kasan matar tayi mata nuni da wani dakin kafin ta mata bayani da turanci kan cewa ta shiga tayi washing up.
Dan turanci da take ji ne yasa ta gane abunda take nufi, duk da karatunta baiyi zurfi ba, kanta kawai ta sauke kasa kafin ta shiga ciki,hawayen da take kokarin hana kanta yi ne ya sauko mata lokacin data shiga cikin dakin, dakin shake yake da abubuwan da sun kai kusan shekara ba ayi amfani dasu ba, hardasu tsohon keken dinky da wasu robobi, duk kura ta gama bade dakin gashi dakin bashi da wani girma sosai.
Jefa idanunta tayi wajen wata kofa, kusa da kofar akwai wani dan karamin gado, anyi laying gadon da zanin gado kamar anan ake kwana don harda pillow da abun luluba a wajen.
Takowa tayi har bakin wajen kafin ta ajiye yar jakar da mutumin nan ya bata akan gadon, bakin kofar tabi ta leka ganin bandaki ne a wajen yasa ta dawo ta zauna akan gado.

Wani irin barcin gajiya ne ke fuzgarta, ga tsoron daya addabeta na sabon waje.
Tana nan zaune barci ya dauke ta ba tare da saninta ba, saida ta shafe wajen awa biyu kafin ta tashi da kugin ciki saboda yunwa data addabi cikinta, tunawa da apple dinnan da aka basu yasa ta bude jakar, kaya ne kamar uniform kala uku a ciki riga da wando, gaban kowacce riga an rubuta sunan agency din a jiki harda phone number su a jiki.

Ajiye kayan tayi a gefe ta dauki apple din ta fara yi tana hawaye,saida ta cinye tass harda kwallon kafin ta shiga bandakin ta tara ruwa daga fanfon sink din tasha abunta tana kuka.

Satin sabeeha uku a cikin wannan gida, acikin kwana ukun nan abubuwa da dama sun faru wanda suka firgitata suka hargitsa mata tunani sosai, wato aikintaa gidan shine kula da wani tsoho, inda ita zata dunga kula da komai nashi don baya tafiya kullum yana kan kujera, tsohon yana da masifa sosai ga rikici, itake wanke kayan da yake kashi da futsari akai, itake zama ta bashi abunci dukda idan ta kawo watsa mata yake a jiki, wani sa’in har marinta yakeyi ko ya jefeta da objects, su uku ne kawai a gidan daga ita sai wannan tsohon sai matar wadda da alamu itace guardian din tsohon.
Zataci zata sha saidai kuma wannan rikicin tsohon ne ke tayar mata da hankali, data zauna babu abunda take sai kuka, gashi wannan yar tashi dataji ya fara kuka zatazo ta balbaleta da masifa wani sa’inma harda mari take hada mata.
Watan sabeeha guda a gidan wanda ya zame itace maid ta farko datakai har wannan lokacin, har zuwa wannan lokaci babu abunda ya sauya game da wannan tsoho da take kula dashi,kullum in zatayi aikinta kuwa zata saka uniform dinnan ta daura koren hijab din da aka basu tare da facemask dinnan kafin ta fara aikinta, mask dinma har ya fara tattogewa saboda tsufa don wankeshi takeyi.
Akwai wata ranar laraba, matar gidan bata nan daga sabeeha sai tsohon nan a gidan, bayan ta gama ayyukanta lokacin cin abuncinsa nayi ta zuba mashi ta wuce dakinsa don ta bashi, tana zuwa ya fara watsa mata abunci yanda ya saba yana masifa, yana cikin wannan masifar yana larabci ya cizge mask din nata, daidai nan yarsa ta dawo, jin ihunsa yasa ta taho aguje zuwa dakinsa, tana zuwa dakin ganin tsohon yashe a kasa duk yabi ya tsorata yasa ta juya don ganin inda yake kallo, sabeeha ce a tsaye itama tana kuka yanda yake kukan, ta janyo hijab ta rufe fuskanta, nuni tsohon ya dunga yi da sabeeha cikin furgici ya fara cewa ‘’shaytan shaytan,’’

Ba matar kadai ba har itama sabiha saida hankalinta ya tashi sosai,ganin haka yasa matar ta korata akan tabar daki.
Da daddare kuwa saiga motar agency tazo don tafiya da ita, haka ta tattara kayan nan nata guda uku ta tura a jaka tabar gidan.

Agency aka maidata ko kwana batayi ba aka dungumeta aka kaita wani gidan daban, wannan gidan da aka kaita bata samu wani matsala ba da matar gidan dukda shima aikin kula yara ne da raino aka bata, abu dai na tafiya tiryan tiryan aka sake korarta a gidan don ko wata bata cika ba, shima nan gidan yaran gidan ne suka nuna masa son ta don haka aka koreta.
Koda aka dawo da ita agency with same complain hakan yasa suka fara bincikarta don sanin dalilin korarta da akayi cikin wata biyu da zuwanta.
Nan suka gano facial appearance dinta ne ke jawowa a koreta, wannan dalilin yasa suka yanke shawarar turata gida Nigeria kawai dukda da wuya ake samun waenda ke yin irin aikin da information dinta ya nuna ta iya kuma ta kware which is mai kula da mara lafiya ko raino(caregiver/nanny) don shine aikin da yafi wahala sosai kuma ba kowa ke karban irin wannan aikin ba, baiwar allah ita bata ma san mijin Jamila aikin daya rubuta ta iya ba Kenan.
Nan suka fara preparation din turata Nigeria don basa son abunda zai shafi imagine business agency dinsu.




Taheel group of company
Wani mahaukacin building ne mai shegen girma da haduwa, fadin irin tsaruwar building din daga waje ma bata lokaci ne don ya gaji da haduwa gashi yana da tsayi sosai yakai international standard, tsagaye yake da mirror glass, daga gaban company din a rubuta Taheel group of company da manyan harufa tare da logo din companyn, mutane sai shige da fuce sukeyi.

Wasu manyan motoci ne suke shugowa cikin company inda aka rubuta factory asset a jikin motar, cikin gaggawa matukan motocin suka fito bayan sunyi parking, cikin motar cike yake da mutane, daya bayan daya suka fara fitowa gaba dayansu da kwalaye a hannunsu da alamu protest zasuyi, guards din bakin entrance dinne suka tsaya don hana su shiga cikin premises din, mutane ma’aikata kuwa haka suka dunga lekowa don ganin ikon allah, su kuwa protesters dinnan mai zasuyi banda ihun dole a kara masu kudin aiki saboda yanxu sun kwashe wata biyu Kenan sunayin wani project na wasu kaya da sukeyi a factory, babu dare babu rana haka suke aikin nan saboda pressuring dinsu da akeyi wanda sunsan daga wajen acting ceo ne wato Hajiyar da kanta gashi anqi kara masu kudin albashi wannan dalilin yasa suma suka fito protest.
Daga chan saman last floor kuwa, office daya ne na acting ceo wato wadda ke rike da mukamin ceo temporary kafin heir din company ya karba responsibility dinshi, daga kofar shiga office dinma kasan irin haduwar da zaiyi daga ciki, kamar wani A class hotel saboda da girma, katon table dinta ya cika bari guda na cikin office din inda akan table din documents ne sai katuwar desktop da laptop na brand din apple sai landline daga gefe, tsakiyar table din kuwa wani katon glass name plate ne akai inda aka rubuta chief executive officer Hidaya Talal Taheel.

Office din nata tsit baka jin komai sai karar ac dake tashi,a tsaye take daidai wajen glass mirror wall din office din wanda daga ciki zaka iya hango na waje, hannunta rike da cup of coffee, tana sanye da wata riga daidai gwaiwanta plain burnt orange color sai wandon rigar wanda yazo mata har kasa, kafarta kuwa sanye take wani hill baki sai kanta data nade shi da wani silk black veil, fuskan nan nata babu digon fara a, she looks so so serious, saida ta kare masu kallo sosai daga nan wajen wall din kafin ta juya cikin isa da aji ta soma takowa wajen desk din office dinta, zama tayi tare da janyo file din gabanta, budewa tayi ta karanta file din tass kafin ta danna wasu number dake jikin lanline din, nan take tasa ayi mata connecting da securities din entrance, lokacin da call din ya shigo cikin gaggawa security din ya daga saboda security call box dinsu na kusa da inda mutanen keyin protest, a gaggauce ya amsata kafin ya fito waje ya soma Magana ‘’we have a call for abdullah head of factory service’’
Abdullah dake tsaye hannunshi da rike da board yana jin an kira sunanshi ya tako inda securities din suke, atare suka shiga cikin landline box din, inda daya daga cikin securities din ya bashi landline din, mutanen dake waje dai zuba masu idanu sukayi don jin dalilin kiran head dinsu.
Magan daya biyu tayi mashi kafin ya sauke wayan, yana saukewa ya fito wajen mutanen ya tsaya tare da daga hannunshi don su bashi attention.
‘’na samu Magana da madam, and ta buqaci ganina yanxu, inason ku natsu zanje muyi negotiating yanxu.’’
Ihu duk suka farayi cikin murna kafin su zazzauna anan kasan gaban company don jiran dawowanshi.

Daga cikin company executive secretary ya jagoranceshi don ba kowa ne yake zuwa ganin madam ba balle a shiga office dinta sai manyan shareholders da mutanen da suke partnership dasu don ceo ba karamin muqamin ba ne dukda ita acting ceo ce.

Cikin lift suka shiga inda secretary ya danna floor din da zasu tsaya,daman floor goma ne, inda madam take kuma 9th floor ne.
Button din floor dinma na office dinta ya fita daban don duk wanda ya shiga cikin lift din zai tabbatar da wajen na daban ne.

Suna karasowa kofar lift din ta bude, secretary n agama Abdullah na biye dashi abaya, saida suka wuce office din excutive secretary tukunna suka kaiga nata offce din.

Saida secretary yayi knocking kafin ta basu access wanda nutton din access door din na jikin table dinta.

Ciki suka wuce Abdullah sai rarraba idanu yake yi yana kallon ikon allah, ay inbanda ya gani da idanunshi zai iya karyata akwai waje kamar haka a doran kasa, yasha ayyuka a companys daban daban dukda yafi dade anan saboda sune yan farko farko da marigayi taheel mutun mai nagarta ya daukesu aiki.

Wata kujerar baqi dake facing din table dinta secretary ya nuna mashi, zama yayi yana washe bakin kafin ya soma gaisheta, wato kudi duniya ne duk girmanka shekarunka dole saika girmama wand aka kusan haifa ma.
Bata amsashi ba haka zalika bata dago ba saida ta gama abunda take kafin ta dubeshi da kyau, wannan file din ta mikama secretary ya miqa mashi, karba Abdullah yayi yana mai sauraron dalilin miqa mashi da akayi.
Cikin muryarta mai dauke da iza da isa ta soma Magana ‘’abdullah Muhammad right?
Dagowa yayi ya kalleta yace ‘’yes madam’’
‘’why are you trying to tarnish my image?, shin kasan idan nakai karar ka zan iya charging dinka for defame of reputation’’
Wani irin kallo ya mata kafin ya soma Magana ‘’cikin book of record na rules din companying nan ya bamu daman yin protest akan abunda ba ayi mana daidai ba’’
‘’and who said your part of the company? Youre fired 10mins ego’’
Hankali atashe ya dago zaiyi Magana ta dakatar dashi ta hanyar daga mashi hannu ‘’ouff no need for that, check that profile first then I have 2 reasonable options for you’’

Jin haka ya sashi bude file din, fadin irin tashi hankali daya garzayo mashi ma bata lokaci ne, sunanshi ne baro baro a cikin file din inda takardunci suka tabbatar bashida qualification din shigowa company din ya shugo, daman requirement din dole sai kana da background ma’ana babu any criminality record da good education qualification, shi kuwa an taba kamashi lokacin about 20 years ago shi kanshi bazai iya tuna dalilin kamashin da akayi ba saidai yasan tabbas lokacin da yarinta akanshi, yanxu kuwa komai has been buried danko matarshi bata sani ba balle yayanshi, cikin sauri ya dago ya kalleta idanunshi sunyi jaa sosai, bamanashi kadai ba harda wasu abubuwan da babu dadin ji daya dangance shi da iyalanshi tayi digging and shes using it against him ko ince take threathning dinshi akai.

Yau shekara goma sha biyar Kenan yana aiki da taheel group, tun lokacin ubanta na raye, kuma shi ya daukeshi aiki ma, mutumin kwarai wanda yasan darajar mutane dukda yana da arziki mai tarin yawa hakan bai rufe mashi idanu bay au gashi lokaci yazo da yayanshi suke wulaqanta waennda suka taimaka masu suka daukaka company, don idan babu mutanen nan babu yanda za ayi companying ya dunga moving dukda kudi suke basu, acikin employee din company din masu kula da harkar factory suna da amfani sosai, shiyasa ake basu mahimmanci sosai don da gumunsu suke yin komai.

Kaste mashi tunaninshi tayi har lokacin coffee dinta na hannunta tayi relaxing bayanta akan kujerar ‘’I know wat you’re thinking right now but ina tunanin ba wannan ya kamata kayi ba, don’t be corny,’’

Ajiye cup din coffee din tayi ta mike tare da takowa har wajen masaukin baqi kafin ta zauna opposite dinshi fuskanta babu alamun digon rahama ta soma Magana ‘’inada option biyu da zan baka masu sauqi, na farko ka sauka kasa ka tattara workers dinnan ku koma bakin aikin ku, maganar qarin kudin salary ku cire shi daga aggender dinku don ko penny bazan kara ba, you don’t owe me an explanation for that, na biyu zaka iya miqewa ka fuce min daga office like I said’’
Ta dan dakata kafin ta duba agogon danyen gold din dake hannunta ‘’like I said this is 25mins Kenan da sallamarka, sannan ka jirayi charges din da zanyi pressing su kuma waenchan nasan how I will deal with them, anyways ko ban fada maka ba kasan how I will deal with them just how I did with you, and lastly I want to give you a sounding warning wallahi wallahi babu wanda ya isa yayi tarninshing image dina ya zauna lafiya, I’m going to sue yall and rot you in jail mark my words, this is how I do my business, yanxu zabi ya rage naka‘’

Tana kaiwa nan ta miqe ta wuce wajen sit dinta, Abdullah kuwa kasa motsawa yayi tsabar tashin hankali, bai taba tunanin matarnan bata da Imani ba sai yau, bai taba tunanin zaka haifi da yaqi gadar ubansa ba, shes completely opposite din mahaifinta.
Turkashi, wani irin zufa ne ya wanke mashi fuska anan zaune, yama rasa irin tunanin da zaiyi saida secretary yace yazo ya futa kafin ya dawo daga tunanin daya fada, koda ya fito daga office din saida yayi kwalla don wannan ba karamin cin mutunci tayi mashi ba da girmanshi da shekarunshi, gashi yanxu ta bashi zabin da dole saiya dauki daya, na farko idan yace zai dau gaskiyar daya fito protesting to fa abin zaiyi affecting dinshi da iyalanshi don da wannan aikin ya dogara, na biyu kuma ta bangaren mutanen dake karkashinsa a matsayin san a head, sun bashi amanar su akan ya karbo masu encin su da halaliyar su sai gashi yanxu ya rufa dashi.
Kwallar data zubo mashi ya sharce yana mai jin wani irin nauyi a zuciyarci, matar nan ko shekarun da yayi yana masu bauta dukda suna biyanshi bata gani.
Haka ya fito premises din company jiki a mace, suna ganin shi kuwa duk suka mike daga zaune suna mai farin cikin jin ko anyi dace, gaba daya zagaye shi sukayi suna jiran jin furucin da zaiyi, abunda ya fada masu ba karamin tayar masu da hankali yayi ba nan suka tabbatar ba ayi dace ba, suna kokarin cigaba da protest din ya roke su akan su bari saboda madam tace duk wanda yake son barin aiki to zai iya cigaba da protest din wanda kuma yake son aikinsa ya koma factory.

Zuba mashi idanu sukayi gaba daya suna mamakin furucinsa, kamar ba head Abdulla ba mai sn gaskia,lallai tabbas akwai matsala kuwa, ganin kamar basa sauraronsa yasa ya juya ya shiga cikin motar factory din, wasu daga ciki haka suka biyoshi a baya wasu kuwa qin bin bayanshi sukayi don gani suke kamar shima an saye shi ne.

Shiko tausayinsu ya dinga ji, karshe dai sai juya katuwar factory bus din yayi suka koma factory house, sauran kuwa suna nan tsaye secretary ya fito,hannunshi rike da papers dinsu ta sallama kusan guda ashirin, hidaya dake zaune a office tana hango duk abunda yake faruwa daga cikin laptop dinta saboda akwai cctv cameras ta kowani lungu da sako dake cikin company.

Tana kallo secretary ya watsa masu takardar sallamarsu inda ya umarci securities su fitar dasu.
Ranar dai ma’aikata sunga tashin hankali, gashi babu wanda ya isa yayi questioning dinta sai shareholders.
On top korar datayi masu saida tayi pressing charges akansu, wasu ma basu san hawa ba basu san sauka ba ake laqaba masu sharrin abunda basuyi ba, haka aka dunga kamasu ana kullesu.

A office kuwa haka aka dunga circulating magana saidai babu wanda ya isa yace uppan don itace oga kwata kata, familynsu sunfi kowa shares a companyn don ko share din gaba daya shareholders din bazai kai koda rabin nasu ba suke da 75%

Please Login or Register in order to submit comment