Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka taddashi idanunshi nakan news saidai kwata kwata hankalin shi ba’akan news din yake ba,babu abunda yake mashi yawo akai sai tunanin last zuwanshi da yayi cikin gidan, ba da karamin bacin rai yabar gidan ba saboda y’ay’an dan uwan nashi musamman hidaya, kwata kwata bata ganin girmashi, tafi karfinshi ma, don sai abunda tace za ayi, darajar alqawari da kuma mahaifinsu ne kawai ke sashi zuwa gidan badan haka ba da bazai sake saka kafafunshi cikin gidan ba, bayan wannan akoda yaushe idan ya zauna babu abunda yake dana sani akai sai tilasta dawowar taj da yayi, dukda ya yarda komai muqaddari ne daga allah saidai deep down yana regretting dawowarshi don shine ya tsaya tsayin daka akan dole saiya dawo, sai yake jin kamar ta dalilin nan ne abunda ya faru wata uku da suka wuce ya faru.’……

Muryoyin su da ya soma jiyowa ne ya sashi fargawa daga tunanin daya fada, duban tafkeken wall clock din da akayi ado dashi a parlon yayi, karfe 5 da rabi Kenan na yamma,
sallamarsu ya sanya shi dagowa ya kallesu daya bayan daya, zaman half an hour yayi a wajen sai aynxu suke saukowa, shidai yana mamaki hali irin nasu koda yake baa abun mamaki bane don yanxu kam ya saba da halayensu, .

kauda kanshi gefe yayi daga garesu ya maida kan tv, kowannen su sanye take da kayan zaman gida gashin nan a bude don ko rufewa basuyi ba,bayan wannan yasan su da practicing rayuwar turawa so su hakan ba komai ne a wajen su ba dukda shi dai hakan a wajenshi ba wayewa bace da girmansu kuma da shekarunsu, shigar fadwa ne ma yafi tsaya mashi arai don ita tana da aure ba kamar afiya ba amma idan ka gansu zaka dauka gaba dayan su basu da auren
.
Karasowa sukayi inda yake zaune dan nesa dashi, kan kujerun single chairs dake facing nashikafin su zauna, fadwa ne tayi saurin cewa ‘’marhaban khaal’’
Ba tare da ya kalleta ba fuskanshi adan hade yace ‘’shukran fadwa,’’
Afiya ce ta dan tabe baki don daman itace tafi rashin kunya kuma yawanci yafi sa ido akan ta musamman rashin auren da bata dashi.
‘’Marhaban khaal’’
‘’shukran’’ ya amsata kai tsaye ba tare da ya sake kallon inda suke ba.

Takun sahun kafafun da sukaji ne yasa duk suka dago, wani dan yaro ne ya shugo kyakyawan gaske bul bul dashi, bazai wuce 12years ba, yana sanye da kayan paw patrol sai wata yar cute jaka a bayanshi, hannunshi rike da pack of doritos chips da nintendo switch gaming pad, sai faman cin doritos din yake.
Cikin sitting room din ya karaso aguje yana washe hakora ‘’Jadd’’ (meaning grandpa)
Inda dattijon yake zaune yaron ya nufa cikin farin ciki da jin dadi, farin ciki ya gama lullubeshi,

Hannu dattijon ya bude mashi ya taho a guje ya shige jikinsa kafin ya rungumeshi shima dadi duk ya gama lullube shi sosai, ‘’Barad’’
Dattijon ya kira sunan yaron bayan ya fiddoshi daga kirjinshi, murmushi yaron ya soma mashi kafin ya soma gaishesa, kumatun shi dattijon ya kama irin yanda ya saba yi mashi koda yaushe‘’I missed this cute baby face’’
Turo baki yaron yayi kamar zaiyi kuka yace ‘’jadd I’m not a baby anymore, I’m turning 13 next month’’
Shafa kanshi dattijon yayi kafin ya sumbaci kumatunsa yace ‘’kaje school yau?’’
‘’yes jadd’’ yaron ya amsa dattijon.


Wani irin kamshi ne ya danno cikin parlorn mai tsada don lokaci guda ya bade parlor kamar anyi ruwan turare, takun tafiyar ta ne ya biyo baya ‘’qwas qwas qwas’’wanda yasa duk suka juyo suna kallonta banda dattijon da yayi mata kallo daya ya dauke fuska sai yanayin fuskanshi ya chanza gaba daya kamar bashine ya gama yima yaron nan dariya ba.

Nima dai kallota na soma yi, kasa dauke idanuna nayi akanta, wato wata irin classy matace a tsaye, daganin fuskanta kasan ta soma manyanta saidai tsufan ya boye sosai don kwata kwata bazaka iya tantance shekarunta ba dukda tana early 40s, farace tass kamar a bula fatarta jini ya futo,ya allahu, tana da kyau sosai don doguwace, sanye take da wata azababbiyar abaya baqa wadda ta haskata sosai tayi mata kyau don ta haska fuskanta data dan hade girar sama da kasa, gaba daya zubinta irin na matan nan ne da basa daukan nonsense, ga jii da kai da kudi da aji, waya ce kawai a hannunta kirar iphone 15 pro max latest, gefenta kuwa wata maid ce rike da Jakarta da wasu document tana biye da ita a baya don kusan taku uku ne tsakaninsu saboda ita ba a jerawa da ita.
Idanun matar sunsha kohl baki wuluk tayi lining idanun nata sai bakinta dayasha jan matte lips stain.
Kamaninta sun fito sosai da su fadwa saidai kamannin nata yafi zama visible da afiya don tama fi yanayi da afiya akan fadwa dukda kamanninsu ta jini itama ta fito.

Saida ta gitto parlorn ta hango dattijon sai kuma maganganunsa da barad data jiyo.
Chak ta tsaya tana kallonshi kafin ta tako cikin kasaita ta karaso parlorn, fadwa ce tayi saurin miqewa tana mata sannu da zuwa kafin ta bata inda ta zauna ta koma gefe.

Kamar an mata dole haka ta dago ta kalli maid din kafin ta bata umarnin wucewa da Jakarta zuwa sama, kallon barad tayi kafin ta mashi nuni da hanyar stairs ba tare da tace uppan ba, miqewa yayi yana ma dattijon murmushi kafin ya fuce daga parlor.

Gyaran murya tayi kafin tayi relaxing bayanta akan kujerar ta daura kafa daya kan daya duk akan idanun dattijon yana kallon ikon allah, saida ta dan dauka yan few seconds kafin ta soma Magana anatse with class
‘’marhaban khaal’’
‘’shukran Hidaya fatan na sameku lafiya’’
A gatsale ta yatsine fuska tace ‘’alhamdulillah’’
Shuru ne ya biyo baya, su fadwa dai kallonsu suke daga shi har ita, yanda kasan maqiya sun hadu.
A duniyar nan hidaya bata kaunar ganin mutumin nan agidannan,a yanu tana mashi kallon kamar maqiyinta dukda yana matsayin qanin mahaifinta marigayi Taheel, duk yanda taso akan ganin ya raba hanya da gidan abun yaci tura don ita gani take yana son ya shiga tsakaninta da big baby dinta ne to wama ya isa? Babu shi a doran kasa.
Bata qaunar kowa ya rabe shi kwata kwata,wannan yasa duk yanda zatayi saitayi don ganin tayi pushing uncle away.

Ganin shurun yayi yawa ne yasa hidaya cewa ‘’ko zan iya sanin dame kake tafe?’’
Mamakin jin tambayarta yayi da yanda tayi mashi tambayar saidai saninta da halinta yasashi dannewa kawai ya gyara zama don idan har zai bi abunda zuciyarshi ke raya mashi akan yayan dan uwan nashi marigayi Taheel to fah bazai kara waiwayar su ba, gyara zama kawai yayi ya danyi relaxing bayanshi kafin ya soma magana.

‘’ba komai ne ke tafe dani ba sai maganar Tajudeen,’’
Saurin rintse idanu tayi kafin ta budesu ta sauke akanshi,
Ganin haka yasa shi cigaba da cewa ‘’yanxu wata uku Kenan babu wani progress akan condition dinshi, shine nace ko zamuyi trying wasu expert health organization da suka kware sosai ta wannan fannin na wasu kasashen daban ko za a samu dacewa’’
Tsagaitawa yayi kafin ya nunfasa ya cigaba da Magana cikin kamala ‘’ ni ina ganin idan muka dage sosai akanshi za a samu cigaba akan matsalar tashi’’

Wani irin kallo take mashi mai wuyar fassara wanda yana hango tsantsar bacin rai a cikin idanunta saidai fuskanta bai nuna hakan ba shima hakan bai sashi ya tsagaita ba don hakan bazaisa yayi shuru ba.

Cikin muryarta mai tafe da wani irin salo mai jan hankali ta soma Magana ‘’so yanxu kana ganin babu abunda nakeyi akai ne?well likitocin nan kasar ma top notch doctors ne kuma there are one of the best in the whole world and I trust them, khaal I know what is best for him, babu wanda zai nunamin damuwa akan matsalar big baby, so please idan kazoo ne akan wannan maganar ka ajiyeta don I know what is best for him baka fini sanin abunda zai taimakeshi ba don nice komai nashi, so please..’’ta karashe tana mai kallon cikin idanunshi babu ta kunya balle ganin girmansa

Fadin irin bacin ran da dattijon da suke kira da khal yake ciki ma bata lokaci ne, yau yaga karshe rashin mutunci wajen yar dan uwansa, yarda aka haifa a gaban idanunsa.

Wani irin heavy abu yaji a kirjinsa kamar an buga mashi dutse, haka yayi saurin runtse idanu yana danne abunda yake ji.

Mikewa yayi tsaye ba tareda ya kalleta ba yace ‘’shikenan na barku kuyi abunda kuka ga yayi dace, saidai ina tunasar dake, ba’a wasa da amana duk qanqantarta zan samu ganinshi yanxu?’’
Cikin sauri ta dago ta maida dubanta gareshi da jajayen idanunta kafin ta maida dubanta ga agogon rolex dake maqale a hannunta ‘’I’m sure he’s asleep by now, don…’’
Kasa daukan wulaqancin yayi don haka yayi saurin katseta ta hanyar cewa
‘’ ba damuwa na barku lafiya’’

Yana kaiwa nan ya masu sallama ya nufi hanyar futa, harya fuce hidaya bata bar kallon hanyar dayabi ya fuce ba, tafarfasar da zuciyarta keyi kamar an zuba tafashen ruwan zafi, su fadwa kuwa kasa cewa uppan sukayi sai zuba mata idanu da sukayi suna kokarin karantar reaction dinta,
‘’tirkashi ana wata ga wata,interesting’’ fadwa ta fada a zuciyarta tana mai tunanin wani abu.
Ganin ta mike tsaye yasa suka bita da idanu harta wuce hanyar stairs anatse kamar wata dawisu.

Kallon juna sukayi atare kowannen su da irin tunanin dake yawo a zuciyarshi…








MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍)
❤️🔥Romantic love story❤️🔥
Written by QueenMarh
Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai…

Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba.

I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.
The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃
Enjoy!!!!!


Free page
Chapter 2-3
*
Saman hidaya ta wuce anatse, tsayawa tayi tana kallon parts din dake saman, duk girman gidan nan part biyun nan yafi haduwa, daya na gefen hannun dama dayan kuma na hagu, saidai kofar part din daman yafi kyau sosai don wata iriyar koface mai shegen girma da kyau security door, handle din kofar ma automatic digital biometric lock ne irin na zamani wanda ba kowa ne ke shigan wajen ba.

Ta dauka yan mintuna qalilan kafin ta kauda idanunta daga wajen ta nufi hanyar dayan part din dake hannun hagu .

Chak ta tsaya ba tare da ta sake daga kafarta ba da niyar tafiya Jin karar bude kofar dayan part din, da mamaki take kallon kofar don ganin wani gwanin ne zai fito daga part din a wannan lokaciin don shige da ficen part din saida izinin ta, don ta gindaya sharudan shiga part din.

Da mamaki take kallon maid din data futo, ga hawaye akan fuskanta, gaba daya kana ganinta kasan she’s stressed daga yanayin yanda take tafiya, tana sanye cikin uniform dinsu na aiki, hannunta rike da tray mai kyau, asaman tray din an daura wani bowl na corn beef porridge sai glass din ruwa’.

Maid din na ganin madam gaban ta ya fadi, shikenan tata ta qare, daman tsoron data dunga ji Kenan na qin futowa don idon ta futo da abuncin ma matsala ne don job dinta ne ta tabbatar anci abuncin sannan kuma akwai time schedule da aka bata na musamman na yanda zata kula da abunda ya shafi part din bayan wannan ma akwai kashaidin da aka bata akan duk sanda ta tsallake rules din to fa sallamarta za ayi.

Duk inda karfe hudu tayi babu maid din dake zuwa part din kwata kwata hatta saman ma basa haurowa gaba dayan su.
A cikin gidan akwai over 10 maids daban daban banda waenda ke kula da alamuran daya shafi premises din gidan.

Dauke ganin ga daga kan maid din tayi ba tare da ta ce mata qala ba ta nufi hanyar dayan part din, maid din na ganin haka kawai ta sauka kasa don tasan an sallameta Kenan, ita a dadinta ma don har wani sign of relief ta sauke.

Hanyar walkway din dazai sadata da living room tabi, babu sautin dake tashi sai karar hills din dake kafarta na saint Laurent red color wanda ya fidda clean kyawawan yatsunta.

Kamshin bakhoor ne kawai ke tashi a parlorn sai sanyin ac daya bade ko’ina, tana karasawa tsakiyan parlorn ta tsaya tabi ko’ina da kallo, babu datti ko digo, har sparkling wajen keyi, parlor yayi mugun haduwa komai na parlorn black and gold ne.

Motsin dataji ne yasa ta maida dubanta ga hanyar kitchen din part din nata, wata budurwa ce ta fito sanye da uniform riga da wando irin na dayar maid din saidai color ya banbanta don ita wannan blue ne hannunta rike da electric cleaner da alamu gyara ta gama yi, tana ganin madam din ta tayi saurin rissinawa kanta a kasa.

‘’wani time ne ya kamata a gama aikin yamma?’’
Hidaya ta tambayi maid din tana mai kallonta irin kallonda zan fassarashi da kaskanci.

Jikin yarinyar ne ya soma kyarma kanta a kasa ta soma rarraba idanu
‘’4pm madam’’
Yarinyar ta bata amsa da harshen larabci wanda baya futa sosai saboda ba yar kasar bace yar Senegalese ce.
‘’shekaranki nawa kina aiki anan? Wani agency ne suka kawo ki nan? Bakisan rules dina bane? Duk inda 4 ta wuce bana son ganin kowa a part dina?’’

Yarinyar harta soma kuka don tsoron abunda zai biyo baya cikin shesheka ta soma Magana ‘’jiya aka kawo ni ma’am, ina cikin waenda akayi recruiting sabbin workers this month madam, I’m sorry madam ban sani bane’’

‘’you must be very stupid,you’re fired’’
A kidime yarinyar ta dago jin abunda madam din tace, sanin cewa ayanda ma’aikatan data tarar a gidan ke yawan fada bata son hayaniya yasa ta hadiye kukanta daya ciyota, don ba’a musayar yawu da ita, har a lokacin tana nan tsugunne bata motsa ba.

Ba tareda ta kalleta ba ta wuce hanyar bedroom dinta idanunta har lokacin sunyi jaa sosai,tana shiga dakin ta banko kofar,yarinyar kuwa haka ta mike ta fuce inda wata yar aikin daban ta fito daga cikin kitchen din part din hannunta rike da tray an daura glass jug mai shegen kyau sai glass cup da wasu vitamins a gefe, kana ganin yarinyar kaga yar india itakuma.

Hanyar bedroom din madam tabi tare da shiga cikin bedroom din,don aikinta Kenan itakuma duk abunda ya shafi harkar personal buqatun madam din, tana shiga cikin mintuna qalilan na soma jin karar fashe fashen abubuwa daga cikin dakin, kafin daga baya kuma aka bude kofa, yarinyar data shiga ce ta fito a rikice ta rufo kofar kafin ta sauka kasa itama.

Mamaki bai hana ni shiga don ganin me ke faruwa cikin bedroom dinba, a tsaye take hannunta rike da wani document data taho dashi daga office, sai kuma wayarta dake yashe a kasa don wani muhimmin call ta dunga expecting tunda safe sai yanxu akayi responding dinta sai gashi kuma abunda take buqata din bai samu ba saima wasu dogayen dokoki da aka fado mata wanda dole sai an bi dokokin ne zata samu abunda take so,Rayuwar ta yanxu gaba da baya aiki ne kawai tasa a gaba.

Babu abunda take sai zagayen dakin from one end to the another, tama rasa tunanin da zatayi, ‘’I have to do something cikin gagagwa, wannan ne kawai last chance da nake dashi to make it mine, wallahi wallahi bazan yi kaffara ba, bazan taba bari taheel groups ya kubuce daga hannu na ba, no never not now and not ever.’’

Hannunta ta sanya a daidai tsakiyar goshita tana wani nazari kafin ta dafe kanta ‘’dole ne nayi shiri I need to plan accordingling, bazan taba bari legacy din famyln nan da sacrifice din da Abii yayi ba to go to waste I can’t let them have it all inaa’’,

Haka ta dunga safa da marya tsakanin dakin abubuwa da dama sun tsaya mata arai, ga wannan matsalar data kunno mata da taso ta kasheta cikin sanyi ba tare da sanin kowa ba sai gashi plans dinta suna neman rugujewa, na biyu kuma ga maganar khaal data tsaya mata arai.

Gaba daya dakin ma ta haukata shi saboda bacin ran da take ciki, daman ta haka take sauke takaici akan duk abunda ta samu na anfani, nan take zata tarwatsa shi ya tashi daga amfani,
Wayar ma na daya daga cikin abubuwan da suka tarwatse don da alamu tana gama wayar ta wullata kasan tiles, gefe kuma glass jug dinnan ne da maid ta shugo dashi akan wani stool, gabanta kuma glass cup ne afashe da wasu kwayoyin vitamins.
Kallon papers din take jikinta har kyarma yake kamar mazari kafin ta watsa su kan gado ta wuce hanyar wani glass petition…..

Zuge glass din tayi nan take bathroom dinta ya bayyana sai wata yar kofa a gefe da alamu closet ne, toilet din ta fada, saida ta dauka yan mintuna kafin ta fito daure da towel, jikinta luwailuwai kamar fatar jariri, hanyar walk in closet room tabi inda aka zagaye dakin da wajen ajiye kaya daban daban, gefe guda kayan maza ne a wajen hakan ya tabbatar min da qila na mijinta ne.
Bata tsaya ko’ina ba sai wajen kayanta, wasu kayan zaman gida ta zaro masu laushi kafin ta ajiye su kan table din dake tsakiyan closet din, tana ajiyewa ta nufi wajen wasu drawers, nan ta soma jawowa ta fiddo da kayan shafenta da kamshi, komai dai is organize ba a cewa komai, saida ta gama shiryawa tsaf ciki kayan kafin ta nufi wata drawer daban inda a jikin drawer an manna wani tag da manyan harufa ‘’first aid’’

Bude wajen tayi ta zaro wani roban magani da plate din daura maganin, kafin ta fuce daga closet din.

**


**UNITED STATES **
San Diego California 11:55pm

Cikin sauri sauri take tafiyar dukda hasken daya gauraye street din hakan baisa ta daina jin fargabar data fara jiba tun da ta sauka daga motar data ajiyeta, sanye take da riga da wando jeans, kayan sun amsheta don tana dan jiki, gashin kanta ya sauko a har bayanta, babu abunda take zai zabga sauri, hankalinta yayi gaba kawai wanda hakan yasa ban hango yanda yanayin fuskanta yake ba,Daidai hanyar wani street tabi inda aka rubuta Boulevard California street a jikin symbol dake nuni da hanyar ne zai kaika har street din, motar data sauketa ne kirar benz ta wuce ta gabanta inda daga gaban motar matukin ya zuge aka dago mata hannu, cikin matsuwa ta daga masu hannu itama kafin su wuce, babu abunda ke tashi sai kida wakar hip hop daga cikin motar, cikin abunda bai wuce minti biyar ba ta dunga wuce titin dake street din wanda iska ke kada bishiyoyin kan hanyar sai gidaje masu shegen kyau terrace a man manne an tsara gidajen da bricks masu shegen kyau.
Ganin ta tsaya chak nesa da wani gida yasa na zuba mata idanu,kallon hanyar dazai sadata da gidan take inda aka saqala wani symbol ajikin ginin gidan da manyan rubutu kamar haka, (Barr Majeed res flat c) maido da dubana nayi wajen inda take kallo ganin ta kurama symbol din idanu kafin ta sauke wata nauyayyayyar ajiyar zuciya ganin babu motar dady kafin ta shige cikin gidan cikin sassarfa daman ta tabbatar bayau zai dawo ba, mummy kuma na night duty a asibiti saboda doctor ce.
Bata tsaya a ko’ina ba sai daidai stairs din dazai sadaka da kofar cikin gidan,leqe ta soma yi kamar mara gaskia ganin lights din windows din gidan duk a kashe yasa ta tsugunnawa ta cire igiyar takalminta duka biyun kafin ta fiddo da kafarta, bata da haske saidai skin dinta yana glowing don irinsu ake kira da caramel complexion, kamar bata taba taka kasa ba, yatsun kafafunta sunsha nail paint pink sai wani zoben kafa data saqala, tana fiddo da kafar tayi saurin bude back pack dinta mai kyau, wata abaya ta zaro ta zura akan rigarta kafin ta tura takalminta cikin jakar, tana gamawa ta haura stairs din da baifi guda uku ba harta tsaya gaban kofar, ta dauka kusan minti daya anan tsaye kafin ta daga hannunta ta danna door bell, tana dannawa sau daya ta janye hannunta ta tsaya chak, ta dauka kusan minti biyu a tsaye jin shuru yasa ta sake danna door bell din, daidai nan aka bude kofar, wata mata ce ta bude kofar, idanu yarinyar ta zuba ma matar ganin hankalin matar adan tashe, itama kallon ta matar ta soma yi da yanayin shigar jikinta.
Matsa mata gefe matar tayi ba tare da tace mata uppan ba harta shugo ciki kafin ta rufe kofar, tana rufewa matar ta wuce ba tare da ta sake waiwayonta ba don ta tsaya chak a tsaye kamar munafuka
‘’nanny bee I’m sorry’’
Chak matar ta tsaya jin abunda tace, karasowa yarinyar tayi ganin haka kafin ta kamo hannunta ta cigaba da Magana ‘’nanny bee bansan time ya tafi har haka ba, please I’m sorry na saba alkawari’’

‘’where…are.. you coming from’’
Wata kaushashiyar murya ce daga cikin sitting room ta doki kunnenta, nan take gabanta ya fadi dam batama san lokacin data saki hannun nanny bee ba, nan take idanunta suka soma kawo ruwa, yau tata ta kare, badai muryar dady take jiba, daman yau zai dawo? But mummy tace mata sai Monday zai dawo yau kuma Friday, shikenan tata ta kare yanxu tsoronta irin punishment din dazai bata saboda last warning ya bata, nan take ta soma hawaye har tsoron juyowa take ji don ta bama hanyar sitting room din baya.

Wani magidanci ne a zaune akan kujeran sitting room din, parlorn yayi dim saboda lights din parlor ba’a kunne suke ba sai side lamp dake kunne guda daya wadda haskenta bai gauraye parlorn ba, fuskarshi kawai na iya hangowa, fari ne sosai ga hanci kamar biro, suman kanshi a kwance cikin wata hula fara tass, yana sanye da farar jellabiya ya daura kafa daya kan daya yana girgizawa da alamu ranshi a bace yake sosai duba ga yanda yayi Magana,daman zaman jiranta yake yaga ta yanda zata shugo, dawowanshi 5 hours ago, da farko yayi tunanin ko tana daki ne, don kwata kwata daya dawo baiji motsinta ba kuma yasan time din dawowanta daga school ya wuce, saida yaje dakin ya tabbatar da bata nan koda ya tambayi nanny bee wadda ita ke kula da ita tun dawowan su nan California tun tana karama harta girma zuwa yanxu, nan ta shaida mashi inda ta fada mata zata je kuma da saninta ta futa ita kuma dalilin barinta datayi ta futa shine ta shaida mata cewa zataje School prep na upcoming exams din su don shiga higher institution.

Saida ta wuce time din daya kamata ta dawo ya soma fada sosai saidai kuma yasan ba laifin nanny bee bane don haka kawai ya zauna anan parlor don yaga gudun ruwanta da rashin hankalin ta don ranshi yayi mugun baci kuma yayi alqawarin this time around saiya koya mata hankali don daman ya bata last warning amma duk da haka ta tsallake sharudan daya gindaya mata.
Wannan karan bazai saurarin mommyn ta ba kwata kwata daman itake hanashi displine dinta yanda ya kamata.

Yana nan zaune har sha biyu saura, fadin irin tashin hankali da baqin ciki hade da bacin ran da yake ciki ma bata lokaci ne, bai gama tabbatar da maya ta kangare ba sai yanxu.

11:55pm dot kuwa saiga karar doorbell, har nanny bee ta fito daga bedroom dinta ta bude kofa baice komai ba don bata lura dashi a zaune a parlorn ba daman itama hankalinta ya gama tashi tun bayan time din datace zata dawo ya wuce, harga allah tana masifar son maya shiyasa bata iya hanata wasu abubuwan.
‘’nanny bee excuse us please’’
Sunkuyar dakai nanny bee tayi don sai taji kunya ya lullubeta saboda batajin dadin abunda maya keyi musamman da kulawanta ke hannunta.
‘’okay sir, goodnight’’
Tana kaiwa nan ta wuce bedroom dinta, maya dai kasa motsawa tayi sai data sake jin muryarshi ‘’come here this instant!’’

Cikin saurin ta karaso parlorn har tana tuntube

Please Login or Register in order to submit comment