Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shares sauran 25% kuma na sauran shareholders dinne dukda ba a raba nasun ba ita da qannenta saboda ba ayi presenting heir din company ba har yanxu.

Bangaren hidaya kuwa hankali kwance ta cigaba da ayyukan dake gabanta ba tare da tsoro ko fargaban komai ba, yanda take jin kampanin nan ba a cewa komai, zata iya yin komai don kare martabar family business line dinsu, bangaren completion she’s compatative kowa ya shaida haka, when it comes to business bata da sauqi kwata kwata.
Wayar hannunta ta kura ma idanu tana wani dogon tunani, cikin call log dinta ta shiga, wata special number ta kura ma idanu inda tayi saving da big baby T, ta dade idanunta akan wayar ta zurfafa cikin tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar kawai.

Tana ajiyewa karar message yayi popping, wayar ta dauka ta bude message din, ganin sunan khaal yasa ta ajiye wayar ba tare da ta bude message dinba.

Duban screen din laptop dinta tayi inda ta fara duban wani business proposal da Gucci brand suka tura masu, saida tazo daidai wani slide ta tsaya, rubutun slide din ta zuba ma idanu ina aka rubuta ‘’possession of control, authority, influence is power!!!’’
Ta dade sosai tana kallon wannan rubutun ko kifta idanu ta kasa, saida ta dauka kusan minti biyar kafin ta sanya hannu tayi banging laptop din ta mike tsaye ba tare da ta dauki komai ba ta zari handbag dinta ta fuce daga office din tana dialing wasu numbers a wayanta.




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 11-12
Update!!!!

Agency…
Zaune take har wajen karfe biyar a zaune,babu abunda ke miqar da ita sai shiga bayi ko sallah, gaba daya tayi laushi abun tausayawa,babu abunda take tunani sai rayuwarta, ba karamin tausayin kanta take ba, tun tasowarta sai yanda akayi da ita kamar kaya,tunda mutanen nan suka jinginar da ita anan basu sake waiwayonta ba, ita dai tasan cewa maidata gida zasuyi ayanda taji suna fada.

Tana nan zaune ogan agency din gaba daya da wasu yaranshi suka fito daga office din nasu, fuskarsu a washe suka karaso reception inda suke ajiye ma’aikata.
Har suka karaso kanta na kasa ta lula duniyar tunani, saida daya daga cikinsu ya kira sunanta kafin ta dago, da mamaki take kallonsu su uku a tsaye akanta suna washe baki.
Sanin bata jin larabci yasa daya daga cikin su ya kalli ogan nasu yace ‘’sir kana ganin bazaamu samu wata matsala ba idan muka tura ta?’’
Kallonshi ogan yayi kafin ya dan hade rai ‘’bana fatan haka, kai ni banma damu ba kasan irin kudin da zamu samu kuwa ta dalilin yarinyar nan?, ‘’

Daya daga cikin su ne ya sake Magana ‘’but sir, kasan dalilin da yasa ake korarta daga aiki, what if hakan ya jawo mana matsala’’

‘’na rigada nasan da wannan kuma inada plan akan wannan, this girl is the only option we have dole mu turata’’
‘’but sir yanda…’’’
Katseshi ogan yayi da gaggawa kafin ya dubi sabeeha da tayi tsuru kanta a kasa.

Jin kalamanshi na karshe yasa hankalinta ya tashi sosai, ta shiga rudu, dukda bata gane wasu abubuwan da suka fada da larabci ba, abunda ya danfi tsaya mata arai shine abunda ogan ya fada, me suke nufi Kenan waennan mutanen kodai inda za a cutar da ita zasu kaita? Tambayoyin data dunga yima kanta Kenan saidai ta tabbatar koma menene daga yanda suke Magana akai ba alkhairi bane.

Wata takarda suka bata domin tayi signing kafin daya daga cikinsu ya jagoramceta zuwa motar da zata tafi da ita.
At that point ta gama saddaqarwa kuma, sai yanda allah yayi da rayuwarta.

Tafiyar minti ashirin ta kawosu wani waje wanda ta kasa tantance ko’ina ne, driver ne ya futo ya bude mata motar kafin yace ‘’fito’’
Futowan tayi da Jakarta a hannu kamar za a kwace mata, shine yayi gaba kafin ta bishi a baya har suka shigo cikin wajen, har suka shiga wani daki bata tantance taqamaimai wajen don kamar dakuna ne burjik a bulding din.

Suna shiga ciki driver ya mata nuni da wajen zama kafin shima ya zauna a gefe.
Zaman minti goma sukayi kafin a bude kofar shugowa, mutane ne guda biyu suka shigo, daya nag aba dayan kuma na biye dashi a baya.
Miqewa driver yayi cikin ladabi ya gaishesu kafin ya basu waje.

Sabeeha na ganin haka ido ya raina fata, ko gigin dago da idanunta batayi ba don cike suke da tsoro da fargaba.

Zama daya daga cikinsu yayi while dayan na tsaye yana fuskantarta da kyau, gyaran muryar da akayi ne yasa ya maida dubansa ga ogan nasa.
‘’I’m sure kasan dalilin kawoka nan danayi ko?’’
‘’yes sir’’ ya amsa shi

‘’okay inason ka fada mata abunda zan fada yanxu da yarenku yanda zata fahimta sosai.

‘’okay sir’’ wanda ke tsayen ya sake bashi amsa.

Magana wanda ke zaunen ya fara cikin harshe larabci har yakai aya kafin ya nunfasa ya maida dubanshi gareta don jin response din da zata bayar, shi kuwa dayan yana ganin haka ya soma fassara mata yanda zata gane cikin harshen hausa don daman shi interpreter ne, aikinsa Kenan anan kasar, kuma yana samun kudi sosai.

‘’zakiyi mamakin kawoki nan da akayi, ba komai bane yasa aka kawo sai dan wani aiki da zakiyi mana cikin sirri, bawai muna neman yardarki ko amincewarki bane, dole kiyi abunda zamu umarceki inba haka ba rayuwarki da rayuwar iyayenki zata salwanta’’
Wani irin quuu cikin sabeeha ya bada lokaci guda, take taji wata irin zufa ta keto mata babu shiri, abu daya ne kawai ya fado mata rai a daidai lokacin nan shine ambaton allah, cikin gaggawa ta soma allahumma ajirni fee musibati, harta dan soma daidaitawa, tafin hannunta babu abunda yake sai zuba.

Mutumin ne ya sake Magana da larabci harya kai aya kafin daya ya sake fassara mata, ‘’aikin da zakiyi mana aiki ne mai sauqi na leken asiri,sannan kinada kaso mai yawa a ciki idan muka samu abunda muke nema, akwai takardar yarjejeniya da sa hannunki a ciki,saboda haka kamar yanda nace komai cikin sirri za ayi, idan har kika bari asirin mu ya tonu to rayuwarki da rayuwar mahaifiyarki da rayuwar duk zata shiga hadari,’’

Wata waya mutumin ya tura mata gabanta, sai a lokacin ta dan dago, bata yarda ta hada idanu dashi ba saboda harda soma hawaye tsarabar rudanin data shiga.

‘’ga wannan wayar, zamu dunga kiranki don jin bayanan da zaki samo mana,’’
Balaraben na kaiwa nan ya miqe ya fuce daga dakin, shiko interpreter kallonta ya cigaba dayi yana mai jin tausayinta, ita kuma kaddararta Kenan? Ina tasan waennan mutanen har sukayi clashing da ita.
‘’zan baki shwara daya yarinya, kiyi abunda suke so inba haka ba duk abunda suka fada hakan zai tabbata’’
Sai a lokacin ta dago ta kalli mutumin, typical bahaushe ne dukda shigar da yayi ta larabawa kana ganinshi kaga bahaushe.

Mikewa yayi ‘’muje ko’’ yayi gaba ta bishi a baya, da kyar take daga kafafunta don sun sage, har izuwa lokacin babu abunda take sai innalillahi a zuciyarta har suka shiga motar.

Tafiyar munti talatin sukayi kamar tafiyar bazata kare ba, sabeeha dake zaune gaba daya ta gama hargitsewa futsari ne kawai batayi ba a zaunen nan, babu abunda ke mata yawo akai sai maganganun wannan mutumin da ko fuskarshi kasa kallo tayi don daga yanda yake Magana bazaiyi Imani ba.
‘’leken asiri? Wani irin leqen asiri ne zatayi kuma idan batayi ba za a kashe mata iyayenta harda itama?,’’ abunda take tambayar kanta Kenan tana kuka kamar yarinya.
Yanda take kukan ma cikin sanyi abun tausayi, sautin kukan ma baya futa kwata kwata, sai ajiyar zuciya.

Alamun tsayawa da akayi da mota ne yasa ta dan dago kanta, nan take cikin ya sake hautsinewa don bata taba ganin mahaukacin gida mai shegen girma ba kamar wannan, dukda garin yayi duhu hakan baisa anguwar tayi haske ba bauu kamar hasken rana, saida aka gama buncikar su tsaf don ta baya suka biyo saboda tanan ne outsiders ke shigowa ko idan za ayi delivery na wasu abubuwan amfani, front gate kuma masu gidan ne ke shiga tanan sai family relations haka.
Parking driver yayi kafin ya futo ya bude mata kofar baya, futowa tayi anatse jikinta kamar an fasa kwai.
Driver na gaba tana biye dashi ta baya har suka karaso wata kofar shiga ciki, daga bakin kofar ya danna bell din shiga, cikin yan mintuna qalilan aka bude kofar.
Kallonsu maid din tayi daga shi har sabeehan kafin ta buqaci sanin zuwan su, drivern ne ya miqa mata takardu bayan ya mata bayanin daga inda yake, matar na ganin haka ta tsaidashi kafin ta koma ciki.

Bata dade da shiga ba saigata ta dawo da papers din a hannunta, wasu yan maganganu tayi mashi kafin ya juya yayi tafiyarshi yabar sabeeha anan tsaye.

Maid din kuwa kallonta ta dunga yi daga sama har kasa kafin ta mata nuni da cikin gidan.

Sauke ajiyar zuciya tayi kafin ta sanya kafafun ta, wani irin sanyi taji tare da sauyin bugun zuciyarta lokacin data sako kafarta cikin backyard din,da garden ta fara cin karo inda yasha kayan lambu da flowers masu kyan gaske, ko’ina fes fes sai haske daya bade ko’ina, haka suka miqi hanyar backyard dinnan har zuwa wata kofa again daga chan gefe, ciki suka shiga, ashe hanyar backdoor ne da zai kaika zuwa kitchen, yanda fadi da girman da kitchen din yake da saida gaban sabeeha ya fadi, mata ne a cikin kitchen din don zasu kai su kusan biyar, kowacce tana ta faman shige da fuce da warmers, wasu daga cikinsu kuma suna yin dishes a cikin machine, wasu kuwa sorting kayan abunci suke a cikin freezer da store.
Kallonta maids din suka dunga yi, kowannen su ya zuba mata idanu sai yan qus qus da suka fara yi suna nunata har suka fuce daga kitchen din ita da matar.

Wata hanya suka miqa har zuwa wasu dakuna dake nan ajere har kusan guda biyar, daya daga cikin dakin matar ta bude suka shiga sabeeha na biye da ita.
Daki ne babba mai dauke da bunk bed guda biyu, kowannen sama da kasa, dakin fess fess babu qazanta saima kamshi da sanyin ac dake tashi, kowanne bunk akwai wajen ajiyar belongings din mai gadon.

Empty gadon dake kasa matar ta nuna mata, kafin ta soma Magana cikin larabci, ‘’wannan ne gadon ki, ki huta zuwa gobe za’a nuna maki ayyukanki okay?’’
Kallon bakinta sabeeha ta soma yi don fahimtar abunda ta fada saida takai aya kafin tayi mata nuni da gadon, nan ta fuskanci abunda take nufi gashi daman ta dan soma koyon larabci ba laifi.
‘’shukran’’ sabeeha ta amsata cikin natsuwa.

Matar na fita sabeeha tabi dakin da kallo, fatanta allah yasa ba ita kadai zata kwana anan dakin ba don tunda suka shigo hankalinta yaqi kwanciya, sai take ganin kamar idan ta rufe ido a cikin gidan za a iya kasheta saboda yanda abun yayi yawa, daga kan tsaruwar gidan da girman gidan ma.

Gefen gadon da matar ta nuna mata ta zauna tana mai tuna abunda mutumin nan ya fada mata, wannan ay an kawota inda zata hallaka ne, tunanin dalilin kawota ta dunga yi, meysa zasu kawota liken asiri? Me zatayi masu? Meysa sai ita?’’ haka ta dunga tambayar kanta babu amsawa.
Tunawa da batayi salla ba yasa ta nufi wata kofa dake cikin bedroom din, as she expect toilet ne babba ma kuwa mai tsafta.
Alwala ta fara yi, tana gamawa ta soma jin surutai daga cikin dakin, tana futiwa kuwa ta tadda maids guda biyu, abunda ta lura dasu shine uniform din dake jikinsu ba irin na waenda ta gani bane, gashi kuma kowanensu daga wata kasa daban aka kawosu saboda yaren data ji sunayi.
Zuba mata idanu sukayi yanda itama ke kallonsu cikin face mask dinta, hijab kuwa yana nan maqqle a jikinta kamar matan malam, kwata kwata bata rabo dashi.
Saurin sauke kanta tayi ganin yanda suke mata wani irin kallon mai kama da na tausayi.

Wajen gadon ta ta nufa ta zauna tana mai tunanin yanda zata tambaye su gabas, gashi bata san ta yanda zata fara ba.

Bude kofar da akayi ne yasa suka dago gaba dayan su, kallon wadda ta shugo sabeeha tayi, kanta daure yake da dankwali ba kamar sauran ba sannan gata dai baqar fata ce saidai bata tantance koi ta din yar ina bace ba don batayi kama da Nigerians ba kwata kwata, kamar irin kabilun nan na yankin Africa.

Takowa budurwar tayi inda sabeeha take kafin tayi mata murmushi, itama murmushin ta maida mata dukda baa a ganin fuskarta.

‘’sannu fa whats your name’’
‘’sabeeha’’ ta amsata cikin natsuwa.
‘’where are you from?’’ yanda budurwar ke Magana sounds so friendly hakan yasa hankalin sabeeha dan kwanciya kadan kafin tace ‘’nigeria’’

Da mamaki budurwar ta kalleta don tabbatarwa, dukda bata ga fuskanta da kyau ba saidai idanunta da yanayin girarta yasa budurwar cewa ‘’nigeria hausa igbo or Yoruba?’’
Da mamaki sabeeha tace ‘’hausa’’

‘’wow!! You’re hausa?, by the way I’m from Africa as well but Ghana, and I can speak hausa as well but not flueintly’’

‘’nima na zauna a Ghana da mamana’’ sabeeha ta amsata
Sama sama budurwar ta dunga janta hira har sabeeha ta tambayeta gabas, nan ta nuna mata, ba karamin dadi sabeeha taji ba data hadu da wannn yar Ghana din, taso ace ma dakin su daya saidai ita abunda ya shafi harkar kitchen take, abunda yasa tazo yanxu ma saboda ta tambayi ko sabeehan musulma ce don ita kadaice musulma anan bangaren maids.

Sallah kawai tayi, ta dade sosai a zaune tana rokon allah, har wannan yar ghanan ta sake dawowa ta kawo mata abunci don taci.




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 13-14
Update!!!!



Ba karamin dadin haduwa da yar Ghana nan yayi ma sabeeha ba dukda ita bata iya sabo da muamala da mutane ba.Saidai ita wannan akwai jan mutane a jiki sosai hakan yasa ta jin dan sauqin abunda take ji aranta.

Sauran yan dakin kuwa wani irin kallo suke mata,babu wanda yace mata ci kanki a cikin su, daman su uku ne kawai sai ita kuma ta hudu.


Karfe sha daya nayi duk suka fara shirin kwanciya daman saboda sai an gama hidimar gidan kuma sai masu gidan sun kwanta kafin suma su kwanta saboda karsu buqaci wani abu.

Sabeeha dai na kan gado tana rarrabaa idanu har suka kashe fitilian dakin, ganin haka yasa itama ta kwanta cikin fargaba, ga saqe saqen da zuciyar ta ke mata game da maganganun wannan mutumin da bata ma san koshi waye ba, menene aihanin kudirinshi akanta? Meysa sai ita? ga nan wajen da aka kawota da sunan leqen asiri bata ma san taqamaimain mey zatayi anan din ba.

Hawaye ne masu dumi suka soma ambali akan fuskanta, tunawa da mahaifiyarta babu abunda take tambayar kanta akai sai ‘’meyzaisa mahaifiyarta ta turo ta nan?, shin haka daman kowa ke rayuwarshi ko kuwa itace rayuwarta tazo a haka? Bata san mene farin ciki ba ko kadan dukda tana masifar qaunar mahaifiyarta, tana farin ciki da ganin mahaifiyar.’
Tana cikin wannan tunanin tana hawaye har barci ya zugeta mai nauyin gaske saboda makwancin data samu is confortable, gado ne daidai mutun daya ga bargo harda ac a dakin nasu.

Karfe biyar daidai karar alarm ya karade bangaren nasu na ma’aikatan gida, afurgice sabeeha ta mike zaune don yanda karar ya sauka a kunenta saida yasa gabanta yayi mugun bugu, hasken dakin nasu ne daya bade ko’ina yasa ta duban dakin da kyau, daya bayan daya waennan maids din suka soma saukowa daga gadajensu cikin gaggawa, bandakin nasu suka fara shiga daya bayan dayan kamar yan boarding kafin suyi shiri ciki uniform dinsu na aiki tsaftsaf, kallonsu sabeeha ta dunga yi har suka gama suka soma fita daga dakin, tana jinsu suna yaren su suna kallonta har suka fice ba tare da sunce mata ci kanki ba.

Ita kuwa da mamaki ta bi kofar da suka fita da kallo,komai looks so weird to her, gashi bata san mey zatayi ba ganin duk sun fita gaba dayan su.
Tana nan zaune wadda ta shigo da ita jiya ta shigo dakin,gasheta sabeeha tayi kafin matar ta soma yi mata bayani, da farko wajen drawer ta nuna mata inda kayanta na aiki suke ajiye dasu toothbrush harda pad da dai sauransu.
‘’rule number shine ki kasance cikin tsafta koda yaushe,ki shiga kiyi wanka saiki saka uniform dinki ki fito’’ matar ta fada
Tana kaiwa nan ta fuce tabar sabeeha a tsaye, kamar yanda matar nan ta umarce ta hakan kuwa tayi, tana yin wanka ta saka uniform din ta zumbula hijab tare da mask dinta kafin ta fito daga dakin.

Koda ta fito rasa hanyar da zatabi tayi don kofofin wajen sunyi yawa, saida ta jiyo hayaniya da karar kwanuka da cokula daga wani saseh daban haka yasa ta nufi hanyar, allah ya taimaketa kuwa hanyar kitchen ne, da sallama ta kara kitchen din muryarta chan kasa kasa, gaba daya maids din kowannen su yana ta hada hadan ayyuka babu wanda yabi ta kanta, wannan matar kuwa na tsaye sai bada orders take, ayi wanchan ayi wannan, daman itace ogansu gaba daya, saida ta lura da sabeeha a gefe tukunna kafin ta doso inda take.
Kallonta daga sama har kasa matar tayi, nan take ta hade rai tamau ‘’rule no 2, you cannot dress like this, its so unhygienic, bakisan protocols din aykin ki bane’’
Kallon bakinta sabeeha ta dunga yi don kwata kwata bata gano inda matar ta nufa ba, saidai yanayin yanda take Magana strictly hakan ya tabbatar mata da kamar tayi abunda ba daidai ba, wannan yar ghanan nan ce ta matso inda suke ta fassara mata kafin ta koma wajen aykin ta don matar akwai masifa.

Komawa dakin su sabeeha tayi cikin tashin hankali, ita kwata kwata bata saba yawo haka ba ko agida ma, idan ta saka kaya babu hijab dinnan sai taji kamar tsirara take yawo, wannan yasa koda yaushe take yawan saka hijab.
Haka nan ta hakura ta soma zare hijab din nata harda dan hawayenta, tana cireshi ta ninke ta ajiyeshi gefen gadon kafin ta fuce daga dakin.

Kitchen din ta koma, daidai nan daya daga cikin maid din dake futa da abunci a cikin wani serving trolly ta shugo kitchen din, sabanin sabeeha na tsaye daga bakin kofar suka kusa yin karo da juna, wanda hakan ya janyo attention mutanen kitchen din ya dawo kansu ‘’excuse me, watch your step please’’
Maid din ta fada tana mai kallon sabeeha, itama kallonta sabeeha tayi kafin ta sauke idanunta hannunta na gaban rigarta tana kokarin kare kirjinta.
Gaba daya kitchen din zuba mata idanu sukayi, gata dai bata da kiba kuma itadai bazaace mata doguwa ba kuma baza a kirata da gajeruwa ba saidai allah yayi mata sura mai fuzgar hankali, baga mace bama balle namiji, full option, she’s well curved and pictured kamar an zana surarta saboda yanayin kayan jikinta riga da wando na aiki Kenan.
Tsugunnawa tayi ta kwashe savage din da suka zube a kasa kafin ta miqa ma maid din dake tura trolly din, ….No wonder take ta fama kakkare kirjinta ashe a cike suke kamar zasu yaga rigar jikin nata kuma daidai jikinta, a hakan ma bata ji hutu ta koshi bama tukunna,masha allah kamar yar Brazilian don sune masu irin perfect shape dinnan da ba kowa keda irinshi ba, one ina million Kenan.

Gyaran murya da akayi ne yasa duk suka koma kan ayyukansu, sabeeha dai na daga tsaye a gefe tana kallonsu suna abubuwan su cikin kwarewa.


**
Cikin isa ta soma sauko daga stair din cikin shigarta mai aji, babu abunda kake ji sai sautin takalminta da kamshinta, hanyar dining ta nufa hannunta rike da Jakarta.

Waigowa sukayi gaba dayansu suna kallonta daya bayan daya harta karaso dining din, itama binsu tayi da kallo, suna zaune har sun fara karyawa, afiya, fadwa da barad.

Wajen zamanta ta nufa kafin gaba daya suka soma gaisheta, amsa su tayi kafin maid din dake tsaye ta soma serving dinta as usual, daman ita bata cin abunci sosai daga coffee sai dan low calories English breakfast.
Baka jin komai sai karar cokula a dining area din, fadwa ce ta fara gama breakfast din kafin afiya, basuyi gigin tashi ba saida hidaya ta gama tukunna kafin ta miqe tana mai duban afiya dake zaune ta hade rai.
Barad ne ya fara futa daga dining din yana mai kissing din aunties din nashi a kuma kafin yabar dining din.


‘’naga kinyi requesting for kudade masu yawa,na tura maki approval letter’, anything else’’ ta karashe tana mai dubansu su biyu
Da mamaki duk suka dago suna kallonta, don kwata kwata basuyi expecting haka daga wajenta ba.
Kallon juna fadwa da afiya sukayi kafin suyi murmurshi, godiya sukayi mata kafin ta fuce daga dining din, head of maids na biye da ita da Jakarta a hannu.
‘’Ma’am yarinyar da aka kawo wadda zata kula da part din sir…’’
Tsayawa chak hidaya tayi tana wani nazari kafin ta dubi head of maids din, ‘’I trsut her with you make sure ba a samu matsalar da aka samu ba da previous one’’,

‘’okay ma’am’’
Maid din ta bata amsa kafin ta rufe mata matar dake janta zuwa office, barad na daga gefenta don ita ke kaishi school da kanta.

Futar matar nan ce daga kitchen din ya baima yar Ghana daman jan sabeeha, gaisawa sukayi kafin yar Ghana ta soma tambayarta akan aikin da aka bata.
‘’a bangaren ina aka saka ki?, girki ko gyare gyare?’’
‘’bata fada min ba’’ sabeeha ta bata amsa cikin nutsuwa

Nunfasa yar Ghana tayi kafin tace ‘’hmm ina maki fatan dai a wannan bangare guda biyu zaki yi aiki don…’’
Zuba mata idanu sosai sabeeha tayi don jin abunda take shirin fada, ganin haka yasa yar gana rage murya don suna da dan yawa a kitchen din ‘’kinga ayki a gidan nan yana da wasu qalubale daban daban,’’

Samun kanta tayi da cewa ‘’menene qalubalen?’’
Nunfasawa yar Ghana tayi kafin tace ‘’akwai wani part a sama wanda muke kira da demon palace, mudai da muke aiki anan kasa bamu taba zuwa saman ba kuma basusan menene a saman ba, saidai muna kallon duk wadda aka tura aiki chan saman bata wuce kwana daya biyu tabar aiki a gidan nan, a yanda naji ma wadda ta dade da ayki a bangaren bata wuce sati guda ba tabar gidan nan a burkice, shiyasa na tambaye ki don sanin inda zakiyi aiki’’

Wani tunani ne ya fado ma sabeeha nan take ta danji gabanta ya fadi, ‘’menene a saman to?’’
Yanda tambayar ma ta futo daga bakinta ita kanta batayi tsamanin haka ba.
‘’hmm babu wanda ya sani, saboda duk waenda sukayi aiki acahn din basa fadin komai game da part din, mudai musan nothing comes good daga part dinnan, wata qila wani mummunan abu ne a wajen’’


Bata kaiga idawa ba sukaji alamun matar ta dawo kitchen,lokacin wajen karfe tara na safe, kallon inda sabeeha take matar tayi kafin tace ‘’muje’’
Binta abaya sabeeha tayi har suka fuce daga kitchen din, girgiza kai kawai yar Ghana tayi tana mata fatan allah yasa dai ba saman za a kaita ba, don idan da anan kasa zatayi aiki da tuni head(head of maids) ta nuna mata ayyukanta, bangare su sabeeha kuwa zuba idanu ta dunga yi don ganin inda za a kaita don ba karamin tashin hankalinta yar Ghana tayi ba da batun part din saman nan da babu wanda yasan menene a saman, binta kawai take a baya har suka shiga cikin gidan tana sauraron bayanan da take mata.
‘’madam bazata samu ganinki ba, so ni zan maki bayanin ayyukanki’’
Girgiza mata kai sabeeha tayi kanta a kasa har suka soma hawa sama, ita tunda suka shigo ma ta burkice don baza ta iya cewa ga daga inda suke fito.

‘’aikinki ba kamar kowanne aiki bane, record dinki ya nuna kin kware ta bangare caregiving, so ina fatan baza a samu wata maatsala ba, sannan akwai rules din ayyukanki, abu na farko da zaki kiyaye dashi shine your job is confidential, you can not tell anyone irin aikin da zakiyi

Please Login or Register in order to submit comment