Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ninkuwa a ranta, whys the world revolve around him? Kowa is trying to protect him, abunda yafi damunta shine yanda hidaya ta tsaya akanshi, ita wannan abun yana damunta sosai.

****
Cikin yan mintuna kadan saiga health team sunzo, lokacin jamid ya maidashi daki ya kwantar dashi.
Cikin gaggawa suka soma dubashi suka sa mashi ruwa da allurori irin nasu na masu matsalar amnesia, wani irin special care aka bashi na gaggawa har aka samu ya soma dawowa daidai.

Saida doctor ya tabbatar masu cewa zaiji sauqi kuam he’s stable kafin ya fita da team dinshi.

Sabeeha na rabe daga gefe ta kasa tafiya, baiwar allah ta tsorata sosai.

Hidaya ce ta futa ba tare da ta kalli inda sabeehar ke tsaye ba, tana fita jamid ya miqe shima, “please take care of him dan Allah karki bar kusa dashi i trust you okay?”
Girgiza mashi kai tayi alamun gamsuwa kafin ta karasa bakin gadon ta zuba mashi idanu abun tausayi.

Majid na fita dakin su ya wuce, yana shiga ganin bata dakin yasa ya wuce closet room, kofar ya banko ya shiga, yana shiga ya ganta tana kokarin rage kayan jikinta,
“Hidaya!!!”
Wani irin kallo tayi mashi, “ please bani da time din wannan surutan naka? Na fada maka whatever comes around matiqar yayi involving big baby ne babu ruwanka, don babu ruwana da kai mijina ne duk abunda nayi…”

Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa “Wow,hidaya, you always don’t fail to amaze me so impressive, bazan tsaya muna jayayya dake ba but inason ki sani, babu wanda ya sanki sama dani? Ciki da waje, i know all your movements da intentions dinki, kina ganin wannan abubuwan da kikeyi shi zai rufe abunda ke zuciyarki dana karanceshi tun shekaru da suka wuce? Idan har zaki yaudari duniya ni bazaki taba yaudarata ba, i’m warning you, don’t try my patience, mu tafi a haka har allah ya bashi lafiya, saidai ina so kisan cewa ko me zakice bazai taba hanani shiga al’amarin taj ba, you can never stop me, duk abunda zakiyi kiyi,”
Yana kaiwa nan ya fuce rai a bace.

Saurin runtse idanunta tayi da sukayi jaa sosai, ya zatayi da jamid, ya zatayi da jamid, kamar mahaukaciya haka ta soma watsar da kayan dresser dinta, me yake nufi kenan? Dole yasan da wani abu kenan,? Whats in his mind?
Tabbas tasan jamid shi yafi kowa saninta da halinta tunda shike zaune da ita saidai bata taba tsammanin zaiyi threatening dinta ba,

Zarya ta soma yi tsakanin dakin tana tunani, “i need to do something, kafin lokaci ya kure”
Ta fada ma kanta……..




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 25-26

Washe gari da safe likitan dake kula da Taj ya sake dawowa don duba lafiyarshi, lokacin da suka shigo sabeeha na daga zaune tana goge mashi jikinsa da ruwa mai dumi, gaba daya ya zama pale har zuwa lokacin barci yakeyi ga drip din hannunshi daya kare da ba a cire ba.
Jamid ya shugo dakin yafi a irga, duk after an hour sai ya shigo ya duba sa.
Ba karamin dadin ganin yanda sabeeha ke kula dashi yaji ba, a yanda yaga alamu ma kamar batayi barci ba kwata kwata, daga yanayin idanunta he can tell how worried she is, sai yanxu yake ganin asalin yanda ake damuwa da mutun tsakani da allah dukda basu da wata alaqa su kuwa yan uwanshi kuma jininshi babu wanda ya damu kamar haka.

Hidaya ce ta fara shugowa sai doctor dake biye da ita a baya yana mata bayani.
Jamid na daga tsaye a gefe while sabeeha ta shiga bathroom don zubarda sauran ruwan.

Gaisawa jamid yayi da doctor, hidaya kuwa ko kallon inda yake batayi ba daman ba a dakinsu ya kwana ba, dayan dakin ya tafi.

Yan dube dube doctor yayi kafin ya cire mashi drip din hannunshi, wasu magunguna ya futo dasu da wasu allurai ya soma yi mashi, yana gama wa ya soma masu bayani akan magungunan da za a dunga bashi kullum saboda kar zazzabin ya dawo.

“Meysa bai tashi ba har yanxu?” Jamid ya jefo masa tanbaya
“Saboda alluran da akayi mashi na zazzabin yana da karfi sosai, kuma tasu allurar ba normal injection bane kamar na normal mutane
“Inason bayanai akan magungunan shi da progress dinshi, hope hakan babu matsala?”
Murmushi kawai doctor yayi kafin ya dubi hidaya data kauda kanta gefe, “no problem sir”

Girgiza kai jamid yayi ya nade hannayenshi a kirji, hidaya dai ranta ya gama baci, ashe dai da gaske yake, hada ido sukayi da doctor kafin ya girgiza mata kai, tsaki kawai ta doka wanda yasa suka kalleta gaba daya.

“Babu wani matsala yanxu, kawai yana buqatar proper care ne, nayi mamakin zazzabin shi daya sauka da wuri haka na dauka ma zan dawo na tadda he’s still having it, looks like kunyi natural remedy don shi kadai ke sa zazzabi ya warke lokaci guda ba kamar medication ba, medication process yana daukan lokaci”

Girgiza kai jamid yayi alamun gamsuwa daidai nan sabeeha ta sake futowa da wani warm ruwan data sauyi harda wash cloth a hannunta.

Kallonta sukayi gaba dayansu, ita bata ma lura dasu ba don jamid ta bari anan tsaye, kallonta doctor yayi kafin yace “madam, i have a suggestion, i think keeping her around him so that she can keep an eye on him is safe, don naga last time danazo na ganta anan”

“Okay doctor” hidaya ta amsashi, godiya sukayi mashi kafin ya fuce.

Yana futa majid ya kalli sabeeha yace “please keep an eye on him”
“Okay sir” ta amsa shi
shima fucewa yayi don ranshi a bace yake da hidaya ko kallonta baya son yi, sai a lokacin hidaya ta kalli sabeeha dake tsaye da bowl a hannu.

Hanyar futa daga bedroom din ta nufa said atazo daidai bakin kofar tace “futo”

Bin bayanta sabeeha tayi lokacin harta zauna akan kujera ta daura kafa daya kan daya, sabeeha na karasowa ta dan tsaya nesa da ita kafin ta duqa, kallon ta da kyau hidaya tayi tana wani tunani mai zurfi, at this point babu abunda ke ranta sai abunda tasa kanta, ko hango risk din batayi, bayan wannan ma bata da wani option daya wuce wannan din.

nuni tayi da fuskar sabeeha tace “Remove that thing”
Sai a daidai lokacin sabeeha ta dago da idanunta don ganin abunda take so ta cire, nan take ta soma rarraba idanu, tsoro da fargaba babu wanda bai dirar mata ba, “i said remove that thing”

A tsorace sabeeha ta soma daga hannunta zuwa ga fuskanta, wani irij fargaba takeji da abunda zai biyo ba, idanunta harya soma kawo ruwa, hannunta kuwa har karkarwa yake.

Hidaya dai kafa mata idanu tayi tana kallonta harta soma zame mask din dake fuskanta,Kasa dauke idanunta tayi daga kanta na yan seconds, gaba daya na kasa gane reaction din hidaya don kafa mata idanu tayi kawai kamar mai nazarin wani abu,kafin tayi mata wani disgusting look “kamar yanda doctor yayi suggesting zaki iya zama tare dashi, karki sake ki barshi shi kadai, keep an eye on him”

“Okay madam” sabeeha ta amsata.
Hidaya na fucewa sabeeha ta miqe jiki a mace ta koma bedroom din bayan ta maida mask din fuskanta, lokacin data shiga ya soma bude idanunshi da sukayi mashi nauyi, sabeeha bata lura dashi ba saida taji ya kira ta, cikin hanzari kuwa ta karasa inda yake, “friend friend ka tashi? Ya jikinka? Are you okay now? Meke damunka yanxu? I was so worried about you”

Murmushin nan dai da baya dainawa yayi mata, kokarin tashi ya sake yi ta taimaka mashi ya zauna da kyau, bakinshi ya bushe yayi jaa sosai har wata yar rama yayi, “friend” ya furta ahakali
“Yes me kake so friend?” Ta amsa shi
“Ina first love dina, inason naganta please” shuru sabeeha tayi tana jin babu dadi, wata dabara ce tazo mata tace “laa, yanxu ta fita anan a ta kwana tare dakai”

Washe baki yayi yace “da gaske?”
“Yes, lokacin kana barci, tace you should get well soon kuma ka dunga shan magani zata zo ta ganka anjima”
“I missed her” ya fada yana sauke kanshi kasa gwanin ban tausayi,
“And she missed you too” ta amsa shi

Da taimakon sabeeha yayi wanka ya shirya don ya danji karfin jikinsa sosai saboda allurar da akayi mashi, sabeeha sai nan nan take dashi, tana son ta dafa mashi abu saidai tana tsoron abunda zai biyo baya gashi fridge dinshi babu komai sai abunda aka rubuta za a dunga bashi, wannan corn soup din kuwa tayi alqawarin bazata sake bashi ba.

Saida ta tabbatar yaci abunci kafin ta bashi magungunan da doctor ya bayar na zazzabi yasha duka da magungunan shi.


Hidaya na komawa daki ta shiga study room dinta, tana shiga ta rufo kofar study room din,
Daki ne cike da littafai sai table din da take amfani dashi wajen karatu ko research, wajen wani katon frame ta tsaya, hannunta ta sanya ta tura frame din nan take wani dan secret cupboard ya bayyana, hannunta ta sanya ta bude cupboard din nan take wani safe ya bayyana, pins din safe din ta saka ta bude, kudade ne different currency daban daban a ciki sai wasu documented papers, daya daga cikin document din ta dauka ta soma budewa, ta dade sosai tana kallon rubutun dake kan paper kafin ta dauke idanunta “wannan ne kawai zaisa komai ya dawo hannuna, thats the only way i can keep this legacy, I’ve come this far, i can’t give up”
Haka ta fada a fili kafin ta maida paper cikin safe din ta rufe.


Karfe daya daidai na dare ya miqe zumbur kamar wanda aka tsugunla, ko kallon inda sabeeha ke zaune baiyi ba ya sauko da kafafunshi, hannunta dake ajiye gefen gadon ta dan rankwafa bata ma san barci ya tafi da ita ba ya taka, nan take taji wani irin zafi ya ratsa kwakwalwarta, a razqne ta bude idanunta tayi yar kara don daya taka ta kamar ya balla mata yatsunta.
Idanunshi dake rufe ya budesu ya soka dube dube kamar mahaukaci, ganin babu abunda zai kama yasa ya nufi bango ya soma bugun kanshi yana wata kara, a razane sabeeha ta miqe da gudu ta karasa inda yake,
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun” ta doka salati,
“Friend friend” ta soma kiranshi, ina baya ji kwata kwata kanshi harya soma fashewa, wato wata iriyar jijiga yake yi kamar mai tabin hankali, tunda ya dafe bango da hannayenshi biyu yake bugun kanshi ga jini ya soma fitowa

Wani irin mahaukacin tsoro ne ya durar mata ganin yanda ya sauya kamar bashi ba, “na shiga uku, dan Allah ka bari, zaka jika kanka ciwo wallahi, dan allah ka bari friend i beg you”
Hannunshi na dama daya kama bango dashi ta rike da hannayenta, hauka fa yake muraran don kwata kwata baisan inda kanshi yake ba.

Kuka sosai ta fashe dashi tana buga kafarta a kasa “dan allah ka bari, friend ka bari,zakayi ma kanka illa”
Ay bata karasa ba ya gabje hannunta ta fadi wanwas a kasa har tana bugun damtsen hannunta, baima san yayi hakan ba ya cigaba da bugun kanshi, at that point ya gama jigata, ihunshi ya ninka na wanda ya soma yi, fuskanshi yayi jina jina,
Saurin miqewa sabeeha ta sakeyi ta koma wajenshi ta dafa shi, “ka bari dan Allah”
Haka ta dunga mashi magiya har muryarta ta soma dishashe wa, ganin fa yaqi dainawa yasa ta juya zata fita daga dakin, ko taku biyu batayi ba ya damqo ta, tare da shaqe mata wuyanta, kamar wani mai aljanu haka ya dunga jujuya idanu.

Wani irin kakarin amai ta so mayi, idanunta take sukayi jaa sosai suka fito, hannayenshi biyu daya shaqe ta ta riko wajen damtsen sa, a wannan lokaci har kamshin mutuwa sai dataji, saboda mummunan riqo da yayi mata bana wasa ba, gashi namiji ne ingarma,struggling ta dunga yi da hannunshi, ihun ma da take son yi ya gagara, take jikinta ya saki hannunta dake riqe ta damtsen sa ta saki, idanunta ya soma rufewa jiki a ta sulale, binta yayi har kasan, kamar ance ya bude ido kuwa kawai sai ya saketa ya soma komawa da baya “no no no no” ya dunga furtawa a gigice, bangon ya sake komawa ya dunga bugun kanshi yana fadin no no no

Sabeeha data sulale da kyar ta tattaro nunfashinta dake barazanar barin gangar jikinta, batayi giving akanshi ba dukda ta tsorata da makurar dayayi mata gaka ta sake komawa inda yake tana kuka, ganin babu sarki sai allah kawai ta rungumeshi ta baya tare da saqalo hannayeta wajen cikinsa, sai ya zamana gaba dayanta tsayinta bai wuce wajen ba.Muryarta ce ta soma dawo dashi inda ta soma sauke ajiyar zuciya ga hawayenta dake zuba akan rigarshi, she’s so weak ta jigata sosai haka nan ta soma mashi magana, “dan Allah ka bari, zaka jika kanka ciwo, first love zatayi fushi dakai please ka bari friend dan Allah,”
“Leave me alone!!!” Ya daka mata tsawa a shagwabe
“No bazan barka ba, dan Allah ka bari ka daina jima kanka ciwo i beg you”

Shurun dataji yayi da bugun kan nashi sai kuma kasan daya zube yasa ta sakeshi, abu kamar tsafi lokaci guda kawai kanshi ya warware ya dawo big babyn shi, kanshi ya shafa yana mai duban hannun nashi, “friend jini, ciwo ne ciwo ne bana so” ya soma blabbering hankalinshi a tashe,

“Friend tsaya kaji, zan cire maka shi ka daina kukan nan please”
Kankamota yayi sosai duk ya gama burkicewa, wani sabon tashin hankali, wannan jinin da ya gani ya sake burkita shi don baya son ganin jini ko kadan, gashi jinin har sauka yake akan fuskanshi, “bloo….” Luuu ya sume, binshi sabeeha tayi tana kiran sunan Allah, waze kawo masu dauki yanxu? Innalillahi.

Kofar da aka bude ne cikin hanzari yasa ta kallon wanda zai shugo, jamid ne ya shigo, hidaya na biye dashi a baya.
Cikin tashin hankali hidaya ta karaso inda suke tana kallon yanda jini ke bin fuskanshi, nan take ta burkice itama “mey ya sameshi? Meya faru? Me kikayi mashi”
Jamid daya karaso ne ya ture hidayar gefe ya duqa gaban taj, hankali a tashe ya soma tatttaba fuskanshi “taj taj, me ya sameshi, wannan jinin fah?”
Sabeeha ce da hidaya ta bangajeta gefe itama ta soma magana tana hawaye, “wallahi bansan mey ya sameshi ba, yana barci kawai ya tashi ya fara bugun kanshi, na rokeshi ya bari yaqi”

“Meysa baki zo kin kirani ba?, bana ce maki ki kira landline dina ba?”
Kallon hidaya sabeeha tayi kafin ta sunkuyar da kanta,
“Innalillahi what’s happening with my brother, big baby? Hey! Hey wake, wai meke faruwa ne, ki fada min me kikayi mashi? Whys he bleeding? Kasheshi zakiyi? Me kikayi mashi haka?

“Wallahi maam banyi mashi komai” sabeeha ta fada tana hawaye ga sheshe qar kuka

“You useless idiot Dibo ruwa”
Ta karashe tana yoma sabeeha wani irin kallon,hanzari kuwa ta miqe ta wuce bathroom ta debo ruwa aka soma yayyafa mashi, saida jamid ya shafa mashi wajen sau uku kafin ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya soma bude idanunshi da suka kumbura, da hidaya ya fara cin karo, duk yanda jikinshi yayi tsami hakan bai sashi tashi zaune ba ya rarrafa wajenta ko kallon inda jamid dake gabanshi baiyi ba ya yunqura zuwa inda take ya rungumeta kamar zai shige jikinta, kuka sosai ya dunga yi mata yana kiran sunanta, jamid dai miqewa kawai yayi ya kasa kallon sa don zai iya zubda mashi hawaye, taj abun tausayawa ne, wai ace gashi nan dai mutun kamar kowa saidai hankalin ya banbanta, shin yaushe ne zai samu sauqi a cikin rayuwarshi wannan yaron?


Abunda ya bama jamid mamaki shi yasa shi juyowa yana kallon hidaya data soma kuka itama, “I’m sorry big baby, I’m so sorry ka yafe min please bazan kara barinka ba i promise, I’m so sorry, majid mu kaishi asibiti, wallahi i dont care about our family reputation anymore,i don’t care about the family or what so ever, bazan kara grouding dinshi ba, his mental state is what i will focus on, I’m so sorry taj, abun duniya da company legacy dinmu yana neman rudana har yakai ka ga hallaka,”

Kuka fa take yi sosai, daga ita har taj din, jamid dai kasa dauke idanunshi yayi don abun kamar almara, kamar ba hidaya ba? Anya kuwa?”

Saida ta sake kiran sunanshi ya dawo daga dogon tunanin daya fada ya kalleta “jamid call an ambulance right now please, mu kaishi asibitin, ka kira khaal ma, inason mu kaishi duk inda ya kamata, i can’t stand to see my only brother loosing it, i can’t lose him, wallahi taj is my life, he’s my everything, shiyasa I’m over protective over him kuke ganin kamar bana mashi adalci”

Jamid dai kanshi ya kasa daukan abunda yake ji kuma yake gani, sai abun ya zama kamar drama take shimfidawa don he can’t believe it, hidaya? Hidayar dai daya sani? Mai shegen kafiya? Da shegen girman kai? Da dagawa?
Saurin kauda tunanin dake barazar rudashi yayi ya soma dialing number doctor, don ya karba numbershi dazu dayazo tafiya don sanin abubuwan daya shafi taj da progress dunshi.
Ringing daya kuwa ya dauka don he’s available 24/7, “doctor, we have a emergency muna son kazo yanxu”
Daga chan ne akayai magana kafin jamid ya kashe wayan, bayan kamar munti goma sai gasu sun iso, ko da yaushe they are allowed to enter don haka koda sukazo tahlia street din basu sha wahala da security din dake patrol din dare ba anan anguwar saboda anguwa ce ta masu kudi sosai kuma suna samun threat kodayaushe musanman family taheel.

Cikin gaggawa doctor ya soma dubashi, allurai akayi mashi sannan sukayi mashi dressing ciwon nashi.
Saida ya gama aikinsa kafin ya masu sallama akan washe gari zai dawo zai masu bayanin komai after an yi mashi running test din kwakwalwarshi.

Sallama yayi masu ya tafi, gaba daya kasa motsawa sukayi anan suka kwana harda hidaya, sai wani nan nan take da taj din, jamid dai kallonta kawai, yanxu tunaninshi baya kanta sai taj ya farfado tukunna.

Washe gari doctor ya sake dawowa, har zuwa lokacin bai farfado ba, jamid harya fita ya dawo, nan ya tadda hidaya, shifa lamarin tsoro yake bashi saidai ta bashi tausayi ganin yanda kamar ta damu sosai saidai sanin halinta yasa ya kauda tunaninta aranshi kawai.

Koda suka gaba gwaje gwajen su doctor ya soma masu bayani.
maida dubansa yayi ga hidaya hannunshi na rike da file din taj din. “madam this is a not a good sign”

“ dalilin dayasa nace wannan is not a good sign shine, daman na fada maki, ba tun yanxu ba, kanshi ya soma tabuwa, ba komai ya kawo mashi haka ba sai maybe akwai abunda ke triggering dinshi, is there any sabon activity da yake yi?”
“Babu” ta amsa shi, “shiyasa na hana kowa muamala dashi saboda abunda ka fada min” ta sake bashi amsa yanda kasan sun tsara yanda suke maganar, yana fada tana bashi amsa, “hold on a second!” Jamid ya dakatar dasu,
“Kuyi min elaborating yanda zan gane da kyau? Menene dalilin dayasa kika hana kowa mua’amalar dashi”

Ajiyar zuciya doctor ya sauke kafin ya soma jero masa bayani, “sir, maganar gaskia stage din da yake yakai traumatic, wannan yasa mukayi blocking duk wani abu da zaisa ya tuna rayuwarshi a baya saboda wannan zai iya leading to trauma kuma wannan shine babban risk din condition dinshi yanxu ma haka we should be thankful akwai wani a kusa da shi don da babu kowa da zai tsayar dashi zai iya kashe kanshi don abun na triggering dinshi”

Hankalin majeed ba karamin tashi yayi ba, hidaya dai na daga zaune ta rike hannunshi taj din tana sauraronsu harda dan hawayenta.
“So what’s happening to him doctor?”

“A gaskia for now dole haka zamu hakura har ya wuce stage din,ma’ana dole abar wani a kusa dashi kuma abun da ya faru jiya kan iya faruwa
Koda yaushe anytime, sannan i must say, who ever is staying with him should be someone who knows him so well and knows how to calm him down”
Jamid ne ya kalli hidaya yace “as far as i know yafi yarda da hidaya akan kowa”

“No sir” doctor ya katse shi, hidaya dai cije leve kawai tayi jin abunda jamid ya fada
“Sir, i will advice kar madam ta Zauna dashi, zamanta dashi is the biggest risk, saboda ita kadai ce bai mance ba, saboda tana da matsayi babba a zuciyarshi da gangar jikinshi, ganinta koda yaushe kan iya jawo wata matsalar daban”

Charab hidaya ta chapke, “wannan dalilin yasa na hana kowa kusantar shi ciki kuwa harda kai da khaal harma dani kaina, I’m doing all of this for him,”
Jamid dai bai kalleta ba saidai yana sauraronsu daga ita gar doctor din.
“So what do you suggest?”
“Ina ganin wannan yarinyar dake zaune dashi, why not ita ta zauna dashi koda yaushe, she’s the only person da bai taba sani ba a rayuwarshi achan baya, and ina ganin keeping her around will help him in someway”

Tunani jamid ya soma yi, “but kace leaving her around him will be risk, and you advise a barta tare dashi how those that make sense?”

“Majid please, kamar yanda doctor yace lets do whats best for him, … ” ta katseshi.
Maido da dubanta ga doctor tayi tace “doctor please what else? Please let us know abunda ya kamata ayi?”

“For now, zamu cigaba da monitoring dinshi saidai kawai wannan yarinyar ta kasance tana tare dashi kawai”

Godiya hidaya tayi mashi shima jamid ya mashi kafin ya fuce daga dakin, yana futa jamid ya kalli hidaya “ki je ki huta, i will take it from here”

Kamar jira kuwa take tace “okay kafin ta miqe”
Kissing kumatun big baby tayi kafij ta fuce daga dakin, jamid dai har zuwa lokacin mamaki yake.

Hidaya na fita ta wuce bedroom dinta,wayarta ta zaro ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma magana “good job,”
Tana fadin haka ta kashe wayan ta danyi yan danne dannen ta kafin ta ajiye wayar ta wuce bathroom.
Doctor na fita ya shiga motarshi daman baizo da health team dinshi ba, yau shi kadai yazo, yana shiga motarshi ya soma waya,
“successfully……” yana fadin haka ya kashe wayar ya fice daga compound din.





Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 27-28

Update!!!

Da sallama ta shugo dakin, tsakanin jiya da yau harta fada, wajen wuyanta yayi jaa sosai sanadiyar shaqeta dayayi, babu wanda ya lura da hakan, “good morning sir”
Ta gaishesa cikin ladabi, “morning” ya amsa ta

Yana son tambayarta abu saidai kuma baya son yasa ta fara tunanin wani abu dakyar dai ya soma mata magana cikin dabara, “did he do that?” Nuni yayi da wuyanta, ashe ya lura, sunkuyar da kanta tayi kasa ta kasa bashi amsa, sai hawayen dake shirin zuwan mata.
“I’m sorry about that but why didn’t you call me?”
Nan ma shuru tayi ta kasa ce masa komai, saida ya sake maimaita tambayar “karkiji komai tell me why?,“
Harga allah tsoro take ji saidai yanda taga ya damu yasa take jin kodai ta fada mashi, amma ta ina zata fara? Me zata ce mashi, madam ce ta hanata kira ko me? Zaima yarda da hakan kuwa? yatsun hannunta ta soma murzawa yawanci haka take idan tana tsoron fadin abu, ita kanta ta kasa gane alamuran dake gudana a gaban idanunta, komai is questionable daga wunin jiya zuwa daren jiya,
Tattaro sauran maganar data rage mata a baki tayi ta soma magana “sir i couldn’t leave him, sabod aina tsoron inna tafi wani abu zai sameshi”
Badan ya gamsu ba ya girgiza mata, sun dauki kusan yan mintuna a haka kafin ya kalleta yace “shekarun ki nawa?”
“I’m 19 sir” ta amsa shi.

Girgiza kai yayi yana tunani, Haka kawai he just feel like explaing to her about the condition, bayani ya soma yi mata da avunda doctor yace, to his surprise sai yaji ta amince, dukda yaga abunda taj din ya mata a wuyanta, she’s willing to stand by him.

Ba karamin mamakin haka jamid yayi ba, toh kodai dan kudi take yin duka wannan? Ya tambayi kanshi tunawa da yanda take kula dashi da nuna damuwa dashi ya tabbatar mashi kudi bazaisa tayi hakan ba maybe haka take kuma zuciyarta ce mai kyau.

Fita yayi ya barsu a daki, koda ya fito bai wuce ko’ina ba sai gidan khaal don ya mashi bayanin al’amarin

Please Login or Register in order to submit comment