Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qazanta sai kamshin turaren tsinke dake tashi.
Direct inda dan mataccen fridge dinsu yake ta nufa ta bude kafin ta zaro pure water guda daya mai dan sanyi.

Tana fitowa a zaune ta tadda inna yanda ta barta tana bude ledar data shugo dashi, yar shinkafa ce ta auno masu ta awo kwano daya sai taliya itama wadda ta auno saidan manja da maggi da kuka.

Anatse sabehaa ta tako inda inna ke zaune kafin ta zauna gefenta cikin ladabi tace ‘’inna ga..shi’’
Kurama fuskar ta ido tayi data danyi duhu, baka ganin komai sai kwayar idanunta sai dan karan hancinta,saboda yanda ta janyo wuyan hijab din daidai wajen bakinta.
Ruwan hannun nata inna ta karba tana mai yin wani tunani da yake bata mamaki tun da sabeeha ta soma tasowa.

Saida ta shanye ruwan tass kafin ta kalleta tace ‘’jeki karasa abuncin kizo ki tafi, karta dawo ta fara zazzaga masifar fitar ki data saba, ni na kasa gane wannan wani irin abu ne, yoh idan baki futa ba kema kin nemo mana abunda zamu rufama kanmu asiri ya zamuyi?, wallahi bazai yuwu ba kuwa, mun gajii nema don haka kema saikin nema na kanki wallahi,zaman banza bazai yuwu ba, ni yanxu da futa ke neman yimin wahala ga ciwon kafa’’

Cikin sanyi tace
‘’toh’’
Mikewa tayi ta wuce hanyar rumfar girki, maficin data ajiye a gefe ta dauka ta soma rura wutar, saida ta dauka kusan minti goma ta samu wutar ta kama da kyar, hamadala tayi kafin ta mike da robar shinkafar data tsince tsakuwar ciki ta juye cikin tukunyar.

Bakin rigiyar dake hanyar bandaki ta nufa ta janyo ruwa a buta ta wuce bandaki, dakyar ta karasa cikin bandaki kamar zatayi kuka saboda dattin daya yi, kuma da safe saida ta wanke shi tass kafin mamanta ta futa don duk safiya saita wanke mata idan tazo shiga,sha’anin gidan haya dai sai a hankali, shiyasa yawanci bata shiga bandakin cikin gidan, idan ma zata shiga sai bayan mamanta ta futo nan ne take samun damar yin wanka idan bata samu shiga a wannan lokacin ba haka zata hakura saita futa. Ruwan butar data debo ta tutule ta dauraye inda zatayi amfani dashi kafin ta futo.

A gurguje ta gama dafa dafadukar shinkafa, ta juye cikin kular su dukda dahuwar bataji kayan kamshi ba da nama hakan baisa kamshin abuncin yaqi fitowa ba.

Dakinsu ta nufa da kular lokaci inna ta wuce ciki, ganin bata parlor yasa ta ajiye inda take ajiyewa koda yaushe.
Cikin uwar dakin ta shiga da sallama, a kwance ta tadda inna kan gadon karfensu sai kwasar munshari take, gefenta masarar data gama ci ne ta yasar anan kan gado.

Kauda kanta tayi ta wuce wajen da akwantin kayanta ke ajiye gefen sip, budeshi tayi ta zaro wani hijabi wanda shima yadan soma kodewa, tana zarowa ta rufe akwatin ta fito daga cikin dakin zuwa parlor.
Hijab din jikinta ta soma zarewa daidai nan aka daga labulen dakin nasu, cikin sauri ta sauke hijab din ba tare da ta cire shi ba.
Kamar an wulloshi haka ya shugo cikin dakin, kallo daya tayi mashi yana sanye da riga yar shara sai wani wandon jeans daya dan yage daga kasan wandon, idanun nan nashi jajawur kamar gauta,dauke idanunta tayi da sauri daga kanshi kafin tace‘’sannu da dawowa kawu’’ cikin ladabi
Baima tsaya amsata ba yace ‘’an gama abinci?’’
‘’eh an gama’’ ta bashi amsa
‘’zubo min’’ ya karashe yana wucewa wajen kujerar parlor,
Abuncin ta zuba mashi kafin ta ajiye mashi a gabanshi sannan ta dauko pure water ta ajiye mashi.
tana gamawa ta janyo robar kwan da take futa sayarwa kafin ta fuce daga dakin, saka hijab din da batayi ba Kenan.

Silifas dinta ta zura ta fuce daga gidan nasu dayayi gaja gaja, haka ta dunga kutsa layikan anguwan kafin ta fito hanyar titi, har lokacin bata cire hijab dinnan daga fuskanta ba.
Saida tazo dadai bakin titi inda suke tsayawa kafin ta dan tsagaita, yara ne da yawa harda waenda basu kaita shekaru ba kowannen su da abunda yake saidawa, masu saida muruci, masara gyada, ayaba da sauransu.

Da ansamu traffic haka zasu wuce wajen motocin nan suna tallata abubuwan da suke saidawa, daman titin yawanci matafiya ne suke wucewa,haka ta dunga bada himma itama wajen saida kwan zabo har saida takai wajen karfe biyu da rabi kafin ta wuce tsallake wajen wani gidan mai inda anan ne take samu ta shiga bandakin wajen don yana da tsafta sosai kuma akwai fanfo da bokiti, wani sa’in ma anan take yin wanka idan bata samu tayi daga gida ba.

Bangaren mata ta nufa ta wuce bandakin ta dauro alwala kafin ta fito anatse da hijab din nata.
Masallacin kusa da bandakin ta wuce, da sallama ta shiga wajen,kamar koda yaushe yana nan fess fess don ana kula da wajen sosai.
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke saboda wani irin ni’ima zataji ya sauko mata, tana samun natsuwa da zarar ta zo cikin masallacin nan.

Babu mutane ko daya a cikin masallacin don haka ta nufi wani sako ta tada kabbarar sallah, ta dade sosai wajen sujud tana pouring abubuwan dake cikin ranta, kafin ta salleme.
Tana idarwa ta jingina da bango ta lumshe idanunta, tunanin rayuwarta shekara hudu da suka wuce ta fara, a lokacin idan da za ace mata rayuwar ta zata juya haka zata musa dukda bata samu rayuwar yanci ba, sallamar dataji ne yasa ta amsa ba tare da ta bude idanunta.

Ta dauka kusan minti goma a haka kafin ta bude lumshenshun idanunta ta mike, daidai nan matar datayi mata sallama daxu ta fice daga masallacin, bayanta tabi da kallo kafin ta nufi hanyar futa itama, daidai nan idanunta ya sauka akan purse, kamar bazata dauka ba chan kuma wani tunani yazo mata tunawa da lokacin da ta shigo ita kadaice sai matar data futa yanxu.
Cikin sauri ta dauki purse din ta fuce daga cikin masallacin tare da daukan bucket dinta data ajiye a bakin kofar masallaci.
A gaggauce ta zura silifas dinta tabi bayan matar har tazo daidai wajen da matafiya suke parking motocinsu, ware idanu ta soma yi tana fatan ganin matar, cikin ikon allah kuwa ta hango ta don wani gold peachy mayafi ta saka kuma shi ta gani a jikinta dazu da zata futa daga masallacin.
Ganin matar na shirin shiga zabgegeiyar motar ta yasa tayi saurin hanzarta karasawa wajen motar har tana haki.
‘’assalamu alaikum hajiya hajiya dan…tsa..ya’’
Chak matar ta tsaya kafin ta juyo, masha allah, matar fara ce tass ta dan manyata sosai, daga ganinta kasan hajiya ce babba mai ji da nera,kallonta matar tayi kafin ta ajiye wayar dake maqale a kunnenta.

Kallonta sabeeha ta tsaya yi kirjinta na bugawa kafin tace ‘’hajiya kinyi mantuwar jakarki’’
Ta karashe tana miqa mata purse din nata, cikin sauri matar ta kalleta kafin ta kalli purse din, da mamaki matar ta sake ta kallon yarinyar
‘’subhanallahi a ina na yarda purse din?’’
‘’ah masallaci ne kika barta’’ sabeeha ta amsata
Murmushi matar tayi kafin ta amshi purse din ta bude, zunzurutun dollars din dake ciki suna nan intact harda identifications card dinta da atms dinta duk suna nan, mamaki ne ya lulube matar don babu wanda zaiyi irin wannan tsuntuwar ya maidota.

‘’kai amma nagode sosai kinji yarinya’’
‘’ba damuwa hajiya’’ ta karashe tare da juyawa
‘’tsaya’’ matar tsaidata, kafin ta bude bayan motarta, handbag dinta ta bude ta kwaso wasu kudade da bata ma san ko nawa bane kafin ta rufe motar ta fuskanci yarinyar
Kallon kudin da matar ke miqa mata tayi kafin ta dago da fuskanta ta kalleta
‘’karba wannan, nagode sosai kinji ko,’’
‘’ah ah hajiya basai kin ba..ni ko..mai ba’’
Matar Bata jira amsanta ba kamo hannunta ta danqa mata kudin kafin ta juya tana mamaki sosai, ashe akwai honest mutane wannan generation din, kuma yar talla ma abun mamaki.

Da mamaki sabeeha ta dago ta kalli matar tare da hannunta, kudi ne masu yawa don akalla zasu kai dubu goma, tana kokarin yin Magana matar ta tada motarta ta fuce daga gidan man.

Kallon kudin sabeeha tayi kafin ta dauka bokitin ta ta fuce daga cikin gidan man, saida ta tsallaka titi kafin ta dan tsagaita, kudin cinikin datayi na kwai ta fara irgawa, dubu uku ne daman, qullesu tayi ta saka cikin robar, kafin ta maida dubanta ga kudin da matar nan ta bata shima irgawa ta farayi tana tunanin me zatace a gida, chak ta tsaya da irgen ganin wani dan passport photograph, kyakyawar fuskar matar nan taci karo dashi, da mamaki take kallon passport din ‘’wayyo, yanxu haka batasan ta hado dashi ba’’ sabeeha ta fada kafin ta ciro passport din sannan ta nannade kudin.
Hanyar gida ta nufa cikin sauri saboda yau tayi yamma sosai, daman tsoronta kar mamanta ta dawo shiyasa kullum inna ke nanata mata akan ta dawo da wuri gashi yau takai har wajen uku da rabi.

Hankali atashe ta shigo layin nasu har ta karaso gidan, da sallama ta dage labulen zauren gidan, daidai nan aka watso kaya waje, kallon kayan tayi kafin ta maida dubanta ga wanda ke watso kayan.
‘’get out ungrateful woman’’ wani mutumi ya fada
‘’papa kemi, why are you doing this to me, wallahi bazanje ko’ina ba, bazan tafi nabar yaya na ba saboda ka kawo yan iskan matanka’’
Tass bayaraben ya wanke ta da mari, dafe kuncinta matar tayi kafin itama ta dago ta wankeshi ji kake tass,
Karshe dai dambe suka fara babu kunyar ganin idanun mutane da yayansu haka suka dunga jibgar juna, mutanen cikin gidan kuwa babu wanda yace dasu qala, sabeeha dai kauda kanta tayi gefe hankali a tashe don lokacin data shugo har an fara kiraye kirayen sallar la’asar wanda hakan ke tabbatar mata da mamanta ta dawo.
Fadin irin tashi hankalin dake kwance cikin idanunta bata lokaci ne don kamar har jikinta rawa rawa ya fara.

Tsallake kayan tayi ta nufi hanyar dakinsu, silipas din kafafunta ta cire kafin tayi sallama a natse.
Labulen dakin ta daga tare da shigewa ciki, gabanta ne ya bada dam ganin maman ta a zaune gefenta kuma kawarta ce kuma aminiyarta.
Kamar munafuka haka ta shugo tsakiyan dakin kafin ta tsugunna, ‘’barka da hutawa ina wuni mama’’
Daya daga cikin su ce ta kalleta babu yabo ba fallasa tace ‘’yauwa’’

Dayar kuwa ko kallon inda take batayi ba, saima maida hankalinta datayi wajen rubutun da takeyi a cikin memo, ganin haka yasa sabeeha wucewa uwar dakinsu, a zaune ta tadda inna tana ta faman qulle qullenta data saba.
Sallamar da sabeeha tayi yasa ta saurin dagowa ta kalleta, ‘’ke kuma sai yanxu kikaga damar dawowa?, me kika tsaya yi?’’

Karasowa tayi kusa da innar ta ajiye bokitin kwan a gabanta kafin ta fiddo kudin dake ciki tace ‘’yau banyi ciniki ne da wuri ba ne shiyasa’’
‘’ay ga uwarki nan zaki mata bayani ne bani ba, miqon kudin, yau nawa kika samu?’’
‘’duka na sayar’’ sabeeha ta bata amsa.
Washe baki inna tayi tana karbar kudaden kafin tace ‘’jeki dauki ragowar abunci kici’’,…da toh ta amsata kafin ta mike ta dauki kular, budewa tayi kamar yanda tayi expecting daman ba wani da yawa zata samu ba don haka ta hakura ta zauna kawai ta soma turawa, allah ya taimaka bata fiye cin abunci sosai ba dama dai ruwan lipton ne, bata gajiya dashi, saita sha ruwan lipton kusan sau goma arana indai zata samu ba zata damu da abunci ba.

A parlor kuwa sai bayan wucewar ta ciki suka cigaba da Magana, ‘’yanxu ke hadiza barin yarinyar nan kikayi tana futa? Ko tsoro bakyaji?’’ ta karashe tana mai kallon wadda ta kira da hadiza
‘’jamila ya kikeso nayi toh?, nayi duk yanda zanyi akan inna ta daina bata tallan kwan nan taqi,jiyama da haushi na ta kwana, wai dole ta fita nema itama’’

‘’hmm bakya hango risk din dake cikin barinta ta fita ne shiyasa baki tsaya tsayin daka ba, amma idan ta tsohuwar nan ne ko cikin dan kudin kayan da kike sayarwa ay zaki iya fidda yar dubu ki dinga bata duk sati kina toshe mata baki’’
Nunfasawa hadizar tayi kafin tace ‘’wallahi bazata karbi dari biyar ba, kinsan cinikin nawa takeyi idan ta daura mata kwan nan kullum?’’

‘’nidai wallahi shawara nake baki, karkiga wai yanxu an shafe shekaru wallahi karamin kuskure zakiyi komai zai dawo kanki musamman idan dangin uban…’’
Saurin katseta hadizar tayi ta ta hanyar cewa ‘’dan allah Jamila kibar zancen nan,kinsan yanda na tsani maganar na,ni yanxu zan samu dubu goman?’’
Jamila ce ta kalli aminiyar tata kafin tace’’ gaskiya yanxu bazaki samu ba saidai nanda karshen wata idan anyi albashi,’’
Shuru hadizar tayi tana wani tunani kafin tace ‘’wallahi Jamila ina buqatar kudin nan da gaggawa, matar nan bata da kirki indai ba kai mata nayi ba bazata bani sarin kayan nan ba, gashi mun shiga karshen shekara, yanxu zakiji mutumin nan ya fara doka sallama daki daki, ’’

‘’toh gaskia saidai kisan yanda zakiyi don wallahi nidai banida dubu goma yanxu, kema wallahi kinyi rashin tunani da kika sayar da gidanki, yan kudaden da kika dawo dasu da business kika fara dakin rufama kanki asiri, haka kikazo kika dunga kashesu kamar babu gobe, samun muhalli nakai a wannan lokaci ay ba karamin rufun asiri bane yanxu gashi wata nayi duk sai kibi ki rikice akan dubu hamsin a wannan tsinannan gidan,’’.


‘’hmm Jamila kinfa san dalilin sayar da gidan da nayi, shikennan zan hkura har zuwa lokacin, inkin karba albashi saiki bani’’ hadiza ta bata amsa
Daga nan wata hirar suka shiga sai wajen yamma liss jamila tayi masu sallama.

Sabeeha dai bata fito ba tana nan zaune a dakin nasu kusa da inna don tsoron haduwa take da maman nata.

Tunawa da wanke wanken dake jiranta yasa ta miqe jiki a mace ta tattara na cikin dakin kafin ta fuce, anan parlor ta tadda maman nata, fuskan nan nata a hade, kallo daya tayi ma sabeeha ta watsa mata wani kallo dayasa ta dauke idanunta cikin gaggawa kafin ta sunkuyar da kan nata.
‘’zo nan’’
Takowa sabeeha tayi ta karaso kafin ta durkusa gefe ‘’dan ubanki me kika tsaya yi kika dade?

Shuru sabeeha tayi jikinta na kyarma don duk a tunanin yau dukanta zatayi saboda yanda ta hade fuskarta sosai, ‘’ki amsa ni nace dan ubanki, me kika tsaya yi har kika kai wannan lokacin?’’

Bakinta da kyarma dan tsoro ta soma Magana, ‘’wallahi ban tsaya komai ba, sallah kawai na tsaya nayi bayan na sayar da kwan, shi..ne shi..ne’’

Sanin tana kakarewa wani sa’in cikin Magana musamman idan a tsorace take yasa hadiza saurin cewa ‘’shine mai?’’

‘’wata mata ce ta yarda Jakarta shine na tsinta na bata, dalilin daya tsayar dani kenan’’ ta kaarshe tana sheshekar kuka kasa kasa
‘’matso nan’’ hadiza ta umarceta babu alamun wasa a tattare da ita

Rarrafawa tayi ta karaso dab da maman nata, tana kaarsowa ta damko gaban hijab dinta kamar zata shake mata wuya tace ‘’wallahi idan baki fada min abunda ya tsayar dake ba sainaci ubanki, ba karfe biyu kike dawowa ba meya tsaidake har akayi la’asar? Idan kikamin karya wallahi ranki sai yayi mumunan baci,wurin wa kika tsaya?’’

‘’na rantse da allah mama ban tsaya ko’ina ba, wallahi gaskia na fada maki, inbanda matar nan wallahi ban hadu da kowa ba, kingama har kudi ta bani’’
Sakinta hadiza tayi ganin tana kokarin zaro kudade, wani irin kallo ta jefe ta dashi bayan ta kalli kudin da take miqo mata hannunta har karkarwa yake saboda tashin hankali ‘’uban waye ya baki wannan? Dama ke yar iska ce ban sani ba yaushe kika fara iskanci?’’

Saurin runtse idanu sabeeha tayi daman tasan haka zata kasan ce don tsoron hakan ne yasa ta boye kudin, ‘’idan baki daina kukan munafurcin nan ba saina kashe ki anan wallahi, daman iskanci kika fara ban sani ba? Ke ko iskanci kike yi saiki bari na sani eh?’’

‘’wallahi mama bana iskanci, kinga hoton matar ma, acikin kudin na tsinta’’
Ta kaarshe tana miqa mata passport photograpy din, karba maman tayi kafin ta kurama picture din idanu, saida ta dauka kusan minti biyu babu ko kiftawa tana kallon hoton, nan take idanunta yayi jaa sosai ta maida kallonta ga sabeeha wani sabon tashin hankali ya wanzu a fuskarta
‘’ina kika samu wannan?’’

‘’a cikin kudin da matar ta bani naga hoton,’’ ta amsata da gagagwa
‘’dama chan kinsanta ne?’’
‘’wallahi ban santa ba, a masallaci ta yarda purse dinta shine na dauka na bata, shine tayi min godiya ta bani kudi’’
‘’Ba nace karki sake kiyi mu’amala da mutane ba?uban waye yace maki idan aka yarda abu ana tsinta a baiwa mai shi,ko na taba ce maki idan kin dauki abu ki maidawa maishi inama ruwanki da abun wani? ‘’ ta karashe tana daka mata uban tsawa dayasata qamewa kyam, tana masifar tsoron mama kamar ranta.

Zufar dake keto mata ta sharce kafin ta sake jero mata tambayoyi ‘’a haka kika futa yau?, me matar tace maki?’’
‘’eh haka naje, godiya kawai tayi min’’ ta amsata

‘’tashi kije’’
Sabeeha najin haka ta mike tsaye ta tattare kwanukan parlor wanda kawu yaci da wanda maman taci duka ta fita dasu.

Tana fita kuwa hadiza ta miqe tsaya, babu abunda ke kwance a fuskanta sai furgici da tashi hankali, hannunta har karkarwa yake saboda tsabar tashin hankali mara misali, hijab dinta dake gefe ta zura kafin ta fuce daga cikin parlor.

Koda ta fito batabi takan mutanen tsakar gidan ba ta fuce daga gidan gaba daya kamar zata tashi sama.

Hanyar gidan su Jamila ta nufa don yana dan nesa dasu, cikin mintuna qalilan ta karaso gidan, shima gidan haya ne saidai baikai nasu yawa ba don dakunan haya uku ne kawai a gidan.

Ko sallama batayi ba ta wuce bangaren Jamila, kamar daga sama kuwa Jamila ta ganta hankali atashe
‘’hadiza lafiya inace yanxu nabar gidanku ko nayi mantuwa ne?

Hannunta hadiza taja suka zauna akan kujera mai zaman mutun biyu kafin ta mika mata hoton da sabeeha ta bata.

Kallon hoton Jamila tayi tana tunanin ko lafiya don bata dago komai ba kwata kwata, muryar hadiza ce ta katseta ‘’na shiga uku Jamila,duba kiga’’

‘’wace wannan din’’ Jamila ta tambayeta
Kallonta hadiza tayi kafin tace ‘’ki duba da kyau mana’’

‘’kinga dan allah kimin bayani, wacece wannan din’’ Jamila ta karashe tana gyara zaman dan kwalin kanta

‘’bata maki kama da yan gidan su ba?’’
zaro idanu Jamila tayi cikin kidima tace ‘’toh fa, ina kika samu wannan to?’’ ta karashe tana kallon idanun Jamila, bata ma kaiga jin amsarta ba ta gane abunda take hasashe.

Cikin kidima itama ta miqe tsaye, ‘’na shiga uku ni Jamila, kinga abunda nake fada maki ko?’’
Jan hannunta hadiza tayi ta zaunar da ita kafin tace ‘’dan allah Jamila ki bani shawara ya zanyi eh?’’
‘’ay saida na fada maki hadiza, wallahi da kanki zaki jefamu cikin masifa, sau nawa na fada maki ki daina barin yarinyar nan tana futa, wallahi idan dagin ubanta suka…..’’

Saurin toshe mata baki hadiza tayi idanunta yayi jaa sosai lokaci guda kuma bacin rai ya dabaibaiye fuskarta ‘’dan allah karki mana bakin fata, ay wallahi bazan taba barin haka ba ko bayan raina wallahi har abada, a yanxu dai yata ce ni kadai nina haifeta kaf duniya babu wanda ya wuce ni, kuma babu wanda ya isa ya rabani da ita tunda duniya ta shaida hakan nina tsugunna na haifeta kuma na rantse da wanda ke busa min rai bazan taba sakin ta ba, wannan alwashi ne dana dauka’’
Ganin haka yasa Jamila sauya zancen tace ‘’toh yanxu ya zakiyi kennan’’

Nunfasawa hadiza tayi tana kumfar baki ‘’bani kiga saida safe’’
Ta karashe ta nufi hanyar futa daga dakin jamila bayan ta karbi passport din, ko amsa gaisuwar yayan Jamila da suka dawo daga islamiyya batayi ba ta fuce daga gidan.

Koda ta fito nan take taji wani irin ciwon kai ya saukar mata, zuciyarta a cunkushe don nan take komai ya soma dawo mata, wannan baqin cikin, hatred dinnan da ta kwashe shekaru da dama tana dakonshi ya dawo mata fill a zuciyarta.
Take bakar zuciyarta ta dawo kamar sabuwa, babu abunda jikinta keyi sai karkarwa don tana da zafin zuciya sosai daman yanxu ne ta danyi sanyi saboda girma dayazo mata.

A wannan yanayi ta karaso gida lokacin har an soma kiraye kirayen sallar magrib, a tsakar gida bakin dakali ta tadda inna, ko kallon inda take batayi ba balle ta amsa tambayarta daga inda take.

Uwar daki ta shige ta zauna bakin gado tare da zare hijab din jikinta da zufa ta wanke shi tass, ta shafe wajen awa guda tana saka da warwarewa a cikin zuciyarta har akayi sallar isha’I kafin ta samu ta mike dakyar ta dauro alwala.

Sabeeha kuwa taga lokacin futarta da dawowarta don tana runfar girki ta daura masu abuncin dare tuwo da miyar kuka, mamakin maman nata take koda yaushe, baka taba iya contemplating mood dinta kwata kwata, yau she’s soft gobe kuma she’s opposite, maganganun da sukayi dazu ya tsaya mata arai sosai, ayau da ace iskanci take to fa babu wanda zai fara sani sai mamanta saboda ta santa ciki dabai, don ko kalar nunfashin da take futarwa mamanta ta sani ballatana kuma motsinta.
Ko tsoronta dake kunshe a cikin ranta bazaisa tayi iskancin bama, don a duk duniyan nan babu wadda ta zagaye rayuwarta kamar mahaifiyarta, duk wani motsinta akan mahaifiyarta, shiyasa tun bayan dawowar su Nigeria bata kara futa ba da sunan zuwa makaranta ba, gashi ta haneta mu’amala da kowa don ko qawa bata dashi, bata ma san menene qawance ba saboda she has a very dark experience lokacin tasowarta saboda halittarta, kowa is just a stranger to her hatta maqotansu da suke zaune gida daya mamanta bata yarda tayi mu’amala dasu ba kwata kwata, daga inna sai mamanta sai kawu wato qanin mamanta Kenan, shiyasa take nan kamar mai rayuwar qunci mara freedom.
Tun tasowarta da girmanta bata taba barinta ta zama socialize ba, bata taba barinta ta shiga cikin mutane ba, she hid her to the world gaba daya, tun bayan da ta fara zama budurwa, bata taba koda taka kofar gidan suba lokacin suna tsohon gidan su kafin yanayin yau da kullum yasa zaman nasu ya gagara a cikin gidan …..

A lokacin da suka koma gidan haya ko tsakar gidansu bata futa kwata kwata, bata isa tayi koda dogon nunfashi ba saboda how highly strict with movement dinta da maman ta take,duk wani motsinta saida izinin mahaifiyarta abun yakai hatta kalar nunfashin da zata futar da duk motsin da zatayi saida izinin mahaifiyartaa, shin wannan so ne ko kuwa wani abun ne daban? Haka take yawan tambayar kanta koda yaushe.


Free page
7-8

MATAR TAJ(Destined with you🩵🤍)
❤️🔥Romantic love story❤️🔥
Written by QueenMarh
Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai…

Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba.

I hope you’ll enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.
The suspense and the plot twist is a top notch🙃🙃
Enjoy!!!!!




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Free page
Chapter 7-8

Washe gari da asuba ta tashi as’usual kamar kullum, a parlor ta kwana saboda kawu bai kwana a gidan ba, daman yawan ci asabar da lahadi ne kawai yake kwana a gidan, sauran kwanakin kuma achan tasha yake yi saboda sana’arshi ta tukin motar haya, kano to Abuja line.
Saida ta fara yin sallar asuba kafin ta fara gyaran parlorn nasu inda ta tattara katifar, da dan qyallen zanin da take shimfidawa a kan katifar don katifar soso ne kawai ba bu komai a jikin katifar,sai kuma hijab din da take luluba dashi dayan kuma dashi take sallah.
Ragowar kayan wanke wanken da sukaci abunci dashi ta kwashe ta fita dasu don wankewa.
Gaba daya gidan basu tashi ba sai mazajensu dake futa aiki,wannan yasa take futowa tayi duk wasu ayyukanta da wurwuri kafin sauran matan gidan su fito, don ko dibar ruwan rijiyar gidan ma layi sukeyi.

Zama tayi ta soma yin wanke wanke cikin natsuwa ga sanyi asuba dake busawa, sanye take da hijab din datayi sallah dashi, hijab dai koda yaushe bata rabo dashi, kuma yana nan yanda take sakawa ta rufe bakinta dashi.
Saida ta

Please Login or Register in order to submit comment