Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa basu bar tsayawa ba kuma daga gani ta torota sosai.

Wannan kukan nata ya sashi sarewa anan take kawai, sai yaji wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyarshi kamar an zuba mashi ruwan sanyi a kirjinshi, he was never soft towards kowa sai first love dinshi, baitaba yarda da kowa ba sai first love dinshi don duk wanda aka kawo don kula dashi tsoronsu yake ji kuma baya son ganin su kwata kwata, shi a ganin shi saboda su ne first love bata zuwa wajen shi kuma bata kulashi, sai gashi a karo na farko yaji wani iri game da wannan din.

Nan take ya tsugunna a gabanta kamar wani dan yaro dan shekara goma, musculine hannunshi ya dago ya dora shi akan fuskanta dake cikin mask, nan take ta bude idanunta data runtse ta sauke shi akan fuskanshi, ‘’í’m so..rry don’t cry’’
Mamakin yanda yake yi da fuskanshi da yanda yake goge hawayen idanunta take yi, wasu abubuwa yake yi kamar wani dan karamin yaro, hawayen fuskanta kuwa basu bar kwaranya ba dukda yana goge su don kamar tunzurata yake yi dayin hakan,
‘’don’t cry for me please’’
Ya sake fada yana mai hade fuskanshi abun tausayi kamar zaiyi kuka shima, ai kuwa kan kace me shima yayi zaman dirshen a gabanta ya soma kuka wiwi kamar karamin yaro, mamakin hakan ya sata dan tsagaitawa nan take kuwa ya soma bugun kasan tiles din da kafafunshi har yana zungurinta, tashin hankali, nan take itama ta zabura sai kuka jikinta har rawa yake yi tsabar furgici, ita abun da ya tayar mata da hankali shine, ya za ayi ace dingiqin zabgege mutun dinnan ne yake kuka kamar yaro, haka suka dunga kuka daga shi har ita kamar kananun yara suna nan zaune aka budo kofar dakin kamar za a balla kofar, maido da dubansa yayi ga kofar nan take kuwa ya miqe cikin sassarfa ya nufi wajen kofar baiyi wata wata ba ya rungume hidaya data shigo dakin hankali a tashe kamar an wullota.

Kankameta yayi sosai jikinshi na rawa, yanda ya rungumeta kamar wani dan karamin yaro, itama dai sai ta zama wata yar kif a gabanshi, hidaya dai kasa motsawa tayi tana mamakin wannan al’amarin, bubuga bayanshi ta soma yi don ya saqalo hannayenshi a arms dinta tana mai duban maid din ranta a mugun bace.,

Yana nan a jikinta ta soma jan shi zuwa bakin gadonsa ta zaunar dashi, sabeeha dai tunda ta dago sau daya ta kallesu bata sake dagowa ba haka zalika kukan nan nata bata dainayin shi ba.

Hidaya na zaunar dashi ya matso kusa da ita ya kwantar da kanshi kan kafadarta, ‘’first love, she’s crying, for me tell her to stop crying’’
Ya karashe yana nuna sabeeha dake zaune dabas a kasa, kallon inda take hidaya tayi kafin ta maida dubanta gareshi, ‘’clean those tears’’ ta bashi umarni nan take, shi kuwa yana gama sauraronta ya goge fuskan tass, yana mai kallon ta yana murmushi sosai saboda dadin ganinta, shidai idan kaganshi yayi murmushi to sai idan yaga first love dinshi.
Miqewa hidaya tayi tsaye, kamo hannunta yayi da sauri kamar zaiyi kuka irin yanda kananun yara keyi, ‘’sit down and let go of my hands’’ ta bashi command, ay kuwa tana karashewa ya koma ya zauna ba tare da ya sake koda motsawa ba.
Tana ganin haka ta nufi hanyar futa tana mai kallon inda sabeeha ke zaune, ‘’ke kuma fito’’
Tana kaiwa nan ta futa daga dakin, miqewa sabeeha tayi tana mai kallonshi, yanda kasan baya fidda nunfashi yanda ya zauna ya natsu sosai, futa itama tayi daga dakin kafin ta janyo kofar.

A sitting room ta tadda hidaya dake zaune cikin shiri da alama office zataje, ta daura kafa daya kan daya fuskannan babu annuri, karasowa sabeeha tayi dan nesa da matar kafin ta tsugunna anan wajen har kasa.

‘’ke are you stupid? Bakida hankali ne kema aka kawoki ko kina da mentality, where are you from? Wani agency ne suka kawo ki?’’ abunda hidaya taso fada mata Kenan, saidai ta hana kanta da fadin hakan don yanxu dole ta hakura da duk maid din data dauka don kula dashi saboda bazaiyiyu a barshi shi kadai ba koda yaushe gashi ita kadaice a gidan ya yarda da ita sosai,wannan yasa ta hadiye duk wani abun dake bakinta ta soma Magana with so much class.
‘’whats your name’’

‘’sabeeha’’ ta bata amsa

‘’I’m sorry for that, patient ne,wannan da kike gani brother nane, he’s battling with amnesia caused by brain damage, nasan kin tsorata da shi, he’s not harmful at all sannan baya yin anything weird or strange, he’s just mentally unstable’’

Tunda ta fara Magana kan sabeeha na kasa bata dago ba haka zalika itama hidayan ita take kallo dukda bata ganin fuskanta saidai kwayar idanunta,
‘’brain dinshi ke controlling mind dinshi, shiyasa yake acting kamar 13 year old child, which was the neurological effect of the amnesia, ba wani abun zakiyi mashi ba fa ce kula dashi da maganinshi sai movement dinshi that’s all’’

Sai a lokacin sabeeha ta dago don da farko bata gane bayanan matar ba sai a yanxu,ko ba a fada mata ba tasan wannan itace madam din da head tace bazata samu ganinta ba, nan take taji wani iri aranta, a nata tunanin da farko ta dauka mahaukaci ne ganin yanda shima ya dunga kuka saida wannan matar ta mata bayani ta gane cewa ashe ba mahaukaci bane, larura ce dashi.

Nunfasawa madam din tayi don this is the first time ta zaunar da wata kaskantacciyar caregiver tayi ma bayanin shi, shima hakan ya zama dole ne don bazai yuwu ace ita zata kula dashi koda yaushe ba tunda maa’’aikatan guduwa suke yi, ita kuma bazai yuwu tabar ayyukan gabanta ba saboda situation dinshi, shiyasa ta zaunar da sabeeha tayi gaslighting dinta yanda bazata yi kokarin barin aikin ba dukda tasan yana da hot temper musamman idan abun kan nashi ya motsa ko idan ya furgita.
‘’zaki iya kula dashi ko bazaki iya ba babu wanda zai maki dole ‘’ hidaya ta tambayeta
Shuru sabeeha tayi tana nazari, yau ita ake bama zabi? Tunawa da wani abu yasa ta kawai tace mata eh don bata da wani zabi, da sauqi ma dai tunda matar tace bazai mata komai ba

Katse mata tunani hidaya ‘’ina fatan zakiyi aikin ki daya kamata?’’
Samun kanta tayi da amsata ‘’yes madam’’

‘’great decision, I hope you know that your job is confidential, wannan maganar no one is allowed to know about this, so be careful’’
Cije lebe tayi don taso ta danyi threatning dinta saidai kuma bzatayi hakan ba saboda plans din da take dashi.

Wasu yan maganganu ta fada mata game dashi kafin ta miqe tsaye, dakin suka nufa atare, yana nan zaune yanda tabarshi kmar statue, tana karasowa kusa dashi ta kama hannunshi, nan take kuwa ya sauke mata wani murmushi mai sanyaya zuciya, he looks so innocent.
‘’big baby, wannan ce new friend dinka kaji’’ ta nuna sabeeha dake bayanta kamar munafuka, ‘’she will play with you okay? She’s my frind as well bazatayi maka komai ba, nasan you will be friends with my frend ko’’
Kallonshi hidaya tayi gashi nan dai a haka saika rantse lafiyarshi kalau, gashi da wani irin kwarjini da cikar haiba,kuma kamar lafiyayyan mutun,

Hannunta ya sake rikewa cikin nashi hakan ya sata zamakusa dashi kan gado, fuskanta ya shafa cikin so da kaunar ta yace ‘’yes first love, if she’s your friend then we are friends’’, murmushi tayi mashi tare da zame hannunta daga nashi ta mike,
‘’I love you first love’’, ya fada ahankali kamar helpless child,batace mashi komai ba ta juya inda sabeeha ke tsaye a bayanta
‘’if there’s any issue zaki iya kiran line dina direct daga landline’’ tana kaiwa nan ta fuce tana mai yima sabeeha murmushi don ta dago da fuskanta.

‘’okay ma’am’’
Hidaya na futa ta dubi agogon hannunta tana mai yin tsaki rai adan bace, saboda tayi latti sosai gashi yau din is a very important day saboda suna da share holders meeting.
Bayan futar hidaya wani irin sanyi sabeeha taji aranta, batayi tunanin haka madam din take so nice ba, gashi shikuma wannan dan uwan nata abun tausayi,maido da dubanta tayi gareshi ganin disappointed expression akan fuskanshi.
Takowa tayi inda ta zubda magungunan ta kwaso su da ruwa kafin ta komo inda yake,tsugunnawa tayi har kasa tana mai kallon fuskanshi, shiko da sauri ya dauke fuskanshi daga dubanta a shagwabe, ganin haka yasa ta cewa ‘’Hii’’
Qin juyowa yayi saida ta sake cewa ‘’hii’’ nan ba shuru, ganin haka ya sata cewa ‘’ka manta madam tace nima na zama friend dinka?’’

Sai a lokacin ya juyo ya kalleta, dukda bai ganin fuskanta both yanayin yanda idanunta ke nuni da murmushi tayi mashi hakan yasa shima ya mata murmushi, baiyi wata wata ba ya sauko daga kan gadon ya zauna zaman dirshen a kasan ya kamo hannunta yana mata murmushi, ganin haka ya sata miqa mashi maganin hannunta, tabe baki yayi kamar yaga abun kyama,
‘’haba friend dina, kasha sai muyi wasa’’ hakan data fada kuwa yasa shi washe mata baki ya bude bakin shi, zuba mashi maganin tayi kafin ta bude ruwan ta bashi a baki.
Yana gama sha ya tabe baki irin yanda yara keyin kafin yace mata ‘’thank you’’ da mamaki ta dago ta kalleshi, yanda ya fada zaka rantse wani mai hankali ne ya fadi hakan.

‘’whats your name friend?’’ ya tambayeta yana kura mata idanu alamun son jin abunda zata fada
‘’sa..bee..ha’’ ta bashi amsa, dariya yayi ya maimaita abunda ta fada,
‘’zan iya kiranka da friend?’’
Girgiza mata kai yayi shima yace ‘’nima zan kiraki da friend okay?’’

Sun dan dade a zaune tana kallonshi shiko wasa yake da kananun yatsun hannunta don sai hannun nata ya zama dan karami a cikin tafin hannunshi.

Duk yanda sabeeha tayi ta karbi hannunta kin sakar mata yayi haka ta zauna tana kallonshi yanata faman jujuya yatsunta ita mamakin wai ace babba haka ne yake abubuwa kamar karamin yaro, daga yanda yake Magana da shagwaba da yanda yake murmushi kamar karamin yaro, yanayin yanda halittarshi take idan ba a fada maka ba zaka rantse lafiyar shi kalua kuma yasan inda kanshi yake, take taji wani irin tausayinshi aranta, ashe ita da take ganin bata samu jin dadin rayuwa ba kamar kowa har take questioning ko shin ita din ta daban ce ashe akwai mutanen ma da su they are helpless, basu san ma inda kansu yake ba, nan take ta yi godiya ga allah daya barta a yanda take, shi kuma wani irin tausayin shi ne ya fara yawo cikin jikinta, allah kadai yasan what he’s going through.
Lokaci guda taji kawai she want’s to help, don taimakon wanda ke neman taimako ba karamin lada mutun ke samu ba.

‘’friend?’’ ta kira sunanshi
Kallonta yayi kamar wani mara wayo yana mata murmushi,
‘’kana son muyi wasa’’
Da murnarshi kuwa ya girgiza mata kai, mikewa sabeeha tayi hannunta na cikin nashi, ganin haka ya sashi shima ya mike, koda ya mike a gabanta saida gabanta ya fadi, he’s so huge, ga girma ga kyau, komai nashi ya fita daban, daga ganinshi kasan ba karamin mutun bane, saurayi ne mai jini a jika saidai lalura da take kan kowa wanda allah ya kaddara saita shafe shi babu makawa kuma kowa da irin kaddararsa.

Da kyar ta samu ta zame hannunta daga cikin nashi dukda yana kokari sake chapke hannun nata, ‘’bari na kawo maka breakfast sai muyi wasa okay?’’

‘’okay friend’’ ya amsata
Juyawa tayi ta nufi hanyar futa daga dakin, harta fuce yana kallonta yana murmushi, kitchen din ta nufa ta duako mashi apple dinnan da warm water kafin ta dawo dakin.

Da sallama ta shigo, bin idanunta ya soma yi da kallo yana karantar abunda take fada, saida ta karaso har inda yake kafin shima ya maimaita abunda tace, kallonshi ta tsaya yi confusedly, kamar mai koyon abubuwa haka yake, wani irin tausayinshi ne ta sake ji kamar tayi kuka haka kawai taji she’s so emotional.
‘’friend sit’’ tana fada kuwa ya zauna,
Miqa mashi apple din tayi tace ‘’bismillah’’
‘’bismillah?’’ ya sake fada yana kallonta confusedly,
‘’ína nufin ka karba kaci’’ nan ma kallonta ya dunga yi saida tace ‘’eat’’ tukunna ya karba.

Abunda ta lura dashi kamar yana koyon abubuwa ne yanxu, ko kuma maybe saboda lalurar tashi ne yasa shi haka oho.

Yana kokarin cin apple din tace ‘’ga ruwan’’
Karba ya sakeyi yana murmushi yace ‘’thank you’’

Tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi, kwata kwata bata yarda ta dauke idanunta daga ganinshi ba har y agama cin apple din a natse kamar wani hamshakin babban mutun, ita dai har yanxu wanna abu mamaki yake bata sosai, yana gamawa ya miqa mata glass din ruwan daya sha.
Juyawa tayi ta sake futa daga dakin kafin ta sake dawowa, lokacin data dawo ya cire rigar jikinshi gaban dayanta, yana kokarin zame dogon wandon jikinshi, tana arba dashi kuwa tayi saurin runtse idanun ta ‘’na shiga uku ni fatima’’ juyowa yayi a tsorace ya kalleta, mazugin wandon na hannunshi bai kaiga saukewa kasa ba, takowa ya somayi don ya dan tsorata sosai saboda baya son ihu ko hayani ko sound ko kadan, hakan na furgitashi sosai, yana karasowa baiyi wata wata ba ta riko rigar jikinta kamar zai shige jikinta, take ta damke bakinta kuwa don kiris ya rage ta doka wata uwar kara jinshi a bayanta.
Karjarwar da jikinta ya soma yi ne yasa shi sake rikota sosai, ‘’friend friend, I’m scared’’
Wannan furucin nashi ne ya sata jin wani irin,sai a lokacin ta tuna fa bashi da lafiyar kai, kuma yana abune kamar yaro don haka ta dan dake ta juyo ba tare da ta sake kallon jikin shi ba tace ‘’sorry friend don’t be scared, me zakayi?’’

‘’I want to shower and play friend’
Sai a lokacin ta tuna dole ita zata taimaka mashi yyi freshen up don haka ta soma kokarin zame rigar ta daya qanqame ba tare da ta sake kallonshi ba, hannunta ya sake rike wa don har lokacin a furgice yake, bata hanashi ba haka ta nufi hanyar kofar data gani a dakin, cikin ta shiga yana biye da ita, koda ta shiga kofofi biyu ne a wajen, daya daga cikin kofofin ta bude kafin su shige a tare.
Duk wani abunda tasan zai buqata wajen wanka saida ta hada mashi, yana tsaye daga gefe ya rike gefen rigarta, saida ta gama ta nuna mashi wajen wanka ‘’bismillah’’
Kallonta ya sakeyi sai maida mata abunda tace nan take tace mashi ‘’you can freshen up now’’ tana kaiwa nan ta soma cire hannunshi daga rigarta, yana ganin haka kuwa ya sake damqe rigar, ‘’wait for me friend’’
Waro idanu sabeeha tayi jin abunda ya fada, ganin yana shirin janta zuwa wajen bathube din hakan ya sata kallonshi don dole badan taso ba ‘’no, zan jiraka a waje’’
Haba wa tana fadin haka ya soma bubuga kafarshi a kasa kamar yaro, tashin hankalin da ba a saka mashi rana, yanda kasan tayi kuka haka take ji, anya zata iya wannan abun kuwa.

Wata dabara ce tazo mata ranta ‘’friend zan jiraka a waje kaji?, idan k agama sai muyi wasa tare’’
Tana fadin haka kuwa ya saketa yana murmshi, tana ganin haka kuwa tayi saurin fucewa daga bathroom din tana haki.

Dayan dakin ta bude, wanda take tunanin nanne closet dinshi,kayan dake wajen kusan duk iri daya ne, fararen riga da wando, ko color daya babu, agurguje dai ta kwaso kayan ta ajiye mashi akan gado kafin ta fuce daga dakin.




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 17-18

Update!!
Koda ya fito bai ganta ba sai yaji babu dadi aranshi,shiryawa yayi yanda hidaya ta nuna mashi don yana jin maganarta sosai yana gamawa ya zauna bakin gadon.
Tunda ya zauna ya zubama kofar shugowa dakin idanu ko zai ganta, sabeeha kuwa bata koma dakin ba saboda an gindaya mata sharudan shiga dakin, daman zata bashi maganin shi ne saita bashi breakfast daganan kuma saita taimaka mashi yayi wanka daga nan kuma bazata sake shiga dakin ba sai da yamma idan tazo bashi second dose.

Bayan Futar sabeeha daga dakin batayi gigin komawa dakinba saboda koba komai namiji ne kuma yana buqatar privacy bayan wannan ma bata son ta gane ma kanta abunda bai kamata ta gani ba saboda baya cikin hayyacinshi, don tundaga yanda ya soma kokari zame wandoshi kuma ya ganta ta tabbatar akwai gyara sosai a al’amarin.
kasa ta koma bayan ta kakkashe komai yanda head ta fada mata, harta sauko kasa yana ranta, saitaji kamar ta koma don ganin ko ya futo daga toilet din ko bai futo ba ko yana buqatar wani abun.

Jiki a mace ta shiga dakinsu, gaba daya tama manta da cikinta don ko karyawa batayi ba kuma it’s past 10, yar Ghana da tsegumi ashe tana ankare da ita don ta jiyo lokacin da sauran maids ke gulman ta.
Abuncinta ma itace ta karbi nata ta ajiye mata don a pack pack ake basu kullum safe rana da dinner.

Koda ta shiga ko zama batayi ba saiga yar Ghana ta shugo itama da pack din abuncinta a hannunta,’’new comer’’
Yar Ghana ta kirata,juyowa sabeeha dake shirin zama bakin gadon tayi tana mai kallonta, cikin sassarfa yar Ghana ta karaso inda take kafin ta miqa mata pack din data shugo dashi, ‘’ga break dinky na karba maki’’
Murmushi sabeeha ta yi duk da ba a ganin fuskanta kafin ta sanya hannu biyu ta karba pack din tace ‘’nagode.’’
Murmushi yar Ghana tayi kafin ta soma rage murya ‘’ina aka kaiki?’’
Shuru sabeeha tayi tana kallonta kafin ta sauke kanta kasa tace ‘’sama wajen madam’’
Shuru yar Ghana tayi tana kallonta cikin nuna rashin yarda da abunda tace, chan kuma sai tayi murmushi tace ‘’na dauka wannan wajen aka kaiki, thank god ba nan bane, bari na koma wajen aikina bye’’
Girgiza mata kai kawai sabeeha tayi kafin ta zauna nan bakin gadonta,pack din nata ta bude, fries ne sai kwai da aka soya yasha albasa.
Bismillah tayi kafin ta soma turawa cikin natsuwa, duk sanda zata kai bakinta haka zata dan janye mask din ta tura kafin ta maida shi.
Bayan ta gama zamanta tayi anan dakin ta doka uban tagumi, tunanin wannan mara lafiyan ne ya fado mata arai.

Taheels groups…..
Zaune take cikin kayataccen office dinta, the most trusted secretary dinta na gabanta, ga kuma wasu file dake ajiye akan table din office din, gaba daya yau ranta a mugun bace yake tun daga gida, ga kuma abunda ta riska anan office.
Kallon agogon dake maqale a hannunsa yayi kafin ya maida dubansa ga madam din nasa, ‘’ma’am lokaci yayi fa’’

Tafin Hannayenta data rufe fuskanta dashi ta sauke kasa, sai kuma fuskanta data dago ta zuba mashi waennan idanuwan nata masu firgitawa, karantar facial expression dinta is so hard don gaba daya bazaka iya tantance a wani yanayi take ciki ba.
Mikewa tayi tsaye tare da ture kujeran dake bayanta kafin ta sagayo ‘’lets go’’
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar futa, shikuwa da hanzari ya bi bayanta da wannan files din, cikin takun isa ta fito daga cikin office din nata ma’aikata duk wanda ya ganta saiya tsaya yadan duqa mata cikin respect dukda bata bi ta kansu ma kwata kwata.
Bata tsaya ko’ina ba sai shareholders hall, secretary yana biye da ita a baya, koda tazo bakin kofar hall din shine ya bude mata kofar kafin ta shige ciki.

Mutanen dake zaune cikin hall dinne wanda akalla zasu kai su kusan guda goma sha biyar ne sukayi saurin mikewa don girmamata, bata tsaya wani amsar gaisuwarsu ba ta nufi hanyar wajen zamanta na musamman a tsakiyan dogon table din.
Zama tayi kafin kowannen su ya zauna suma, shuru ne ya biyo baya baka jin komai sai saukar nunfashin manyan mutanen dake zaune.

Secretary ne yayi opening meeting din kafin ya fara koro masu bayanin progress din da aka samu a wannan shekarar, hidaya dai binsu take da kallo daya bayan daya tana jiran taji wanda zai fara Magana, cikin waenda ke zaune kuwa harda uncle khal don shima shareholder ne sai sauran mutane da sukayi investing kudadednsu da waenda sukeyi partnership dashi.

Daya daga cikin manyan mutanen ne ya katse secretary, mutumin kowa yasanshi he’s so bold kuma shi baya wani rufa rufa, don haka ya soma Magana ‘’wannan bashine purpose din meeting dinnan ba, munyi’’
Sai a lokacin hidaya ta dago ta kalleshi, babban ne sosai don a haife zai haife ta kuma yana cikin waenda suka dade sosai suna investing a cikin company ma’ana sune waenda suka dade a cikin company kuma suna bada gudumawa sosai don ganin cigaban company tun marigayi taheel na raye.
Yanda take kallonshi haka yake kallonta, babu wani conering ya cigaba da Magana ‘’dalilin wannan meeting din shine, munason sanin dalilin dayasa wanda ya kamata ya karbi ragamar wannan company dinnan baiyi presenting kanshi ba har yanxu, yau kusan wata takwas Kenan, a yanda ka’idar business dinnan take da kowane company shine dole heir din owner of the company ne zai gaji wannan company ko next person In line’’,
Hidaya najin haka ta maida dubanta ga uncle da ya hade hannayenshi a kirjinshi yana kallon wannan show din,
‘’madam munason sanin dalilin presenting dinshi bayan kowa yasan yanxu he’s 30 kuma wannan ne ka’’idar company, we understand your help and contribution in making this company standing on it’s on, but…’’
At this point idanunta sunyi jaa sosai, shi kuwa bai tsagaita bay a cigaba, ‘’but you’re not enough madam, you can’t run the company ko badan ka’ida ba, babu inda aka yarje mace ta rike company anan kasar, a woman can’t rule the company, that’s a disgrace to the taheel family and the company reputation as well’’

Yana kaiwa aya gaba daya office din suka karade da cewa ‘’yes, that the fact’’
Kan kace me nan take hall din ya kacame, wannan yace kaza wannan yace kaza, saida hidaya ta bari suka gama tass har lokacin kallon uncle take dake mata wani irin kallo,irin na barki dazu,
Runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta daga hannunta biyu ta daki table din dake gabanta, nan take duk sukayi tsit bakajin komai.

Babu tsoro babu fargaba ta daga ma secretary hannu, cikin hanzari kuwa ya miqa mata wannan file din, yana miqa mata ta bude cover din file din kafin ta watso masu shi gaba daya,

Daya bayan daya suka soma dauka papers din don karantawa, ‘’idan kun gama karantawa let me know’’
Tana kaiwa nan ta hade hannayenta a kirjinta tana jiran su gama, nan take kuwa suka soma zuru zuru da idanu don kowa da sunanshi a jikin papers don da duk abubuwan da sukeyi ta bayan fage, sunan uncle ne kawai babu a ciki, wanda yayi Magana ta fara pointing babu tsoron komai ta soma Magana ‘’you!!! with due respect, inason ka fada min waye a cikinku ya kamata na miqa ma company dinnan?’’

‘’you!!’’ ta sake fada tana nuni da wani dake gefenta, shi har ya soma balle maballin buttons din suit dinshi tsabar tashin hankali.
‘’kai dake da record of molesting workers, da harassment tsakanin ni da kai waye yafi dacewa ya jagoranci wannan company?’’

Mutumin najin haka ya sauke kanshi kasa, idanunshi sunyi jaa sosai, wannan shine babban embarrassment din da akayi mashi agaban bainar jama’a kuma manya kamarshi.

Wata iriyar dariya tayi mai bayyanar da hakoranta kafin ta tafa hannunta ta maida dubanta ga dayan dake gefenshi tace ‘’and you… kaida kake da record of homosexuality, gayzism, kana nufi kaine ya kamata yayi ruling wannan company din?, how are you all better than a woman ku fada min’’

Daya daga cikinsu ne ya dake, daga gani zaiyi kafiya yace ‘’mu bamuce muna son amsar legacy din family dinku ba, what we just want to know shine maysa har yanxu heir din wannan company din bazai karba muqaminshi ba’’

Shuru hidaya tayi ta kasa cewa komai sai kuma chan ta saki wani murmushi, ‘’seems like you’re are not understanding this language’’

Jin haka ya tabbatar masu da abunda take shirinyi, wata bankadar zatayi masu gashi kowa yana tsoron kar ta fidda wani abun nashi don basu taba tsammanin hatsabibya bace ba sai yanxu,
‘’we’re done for

Please Login or Register in order to submit comment