Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

surutu, can gurin aikina xan tafi dake sai dai kixo da yawo."


Ganin cewa kamar baya cikin hayyacinsa yasa tayi niyyar yimasa dabara. Dan haka tadan dauke kanta daga fuskarsa, yayi saurin dawo da fuskarta kusa da tasa har tanajin numfashinsa, yace "yimun magana a haka in san cewa mafarkina ya kusa xama gsskiya." tayi qasa da murya tace "kadan bani lokaci inyi tunani inkuma yi istikhara"


Tunda ta fara magana, ya lumshe ido yana shaqar hucin bakinta. Sai data gama sannan yace "to shikenan, xanso hakan nima kuma nima zanje inyi sallatul istikhara. Saboda haka wani satin xan dawo saboda gobe xan koma Dutse" ya dakko kudin da ya ware zai bata 10k ya lalubi hannunta ya manna mata.


Ta kalli kudin ta kalleshi tace "ai basai ka bani kudi zan soka ba." ya kalleta hankalinsa ya kuma kwanciya da ita yace nasani maryam amma ai kyauta ce. Tace "nasani amma ka riqe wata rana ka bani" yayi murmushin cin nasara yace "to my soul"

Ya nemi ta bashi no dinta tace wayar na gida kuma bata ruqe no dinba, dan haka ya bata tasa xata kirashi. Dake ya makance a soyayya be gane cewa wayo taimasa ba, ba musu ya dakko katinsa na gurin aiki ya bata.


Mama tayi matuqar kaduwa dajin wai Badamsi keson Mimi, tace "duk da ba haramun bane ai ana barin halak dan kunya, kuma naji dadi shine gari. In shaa Allah ko wanda sunansa ya fara daga BA bazaki auraba. Yazaki qara fita yayi haukansa ya gama"



Ranar litinin ranar Baffa ya dau azuminsa na qarshe, kuma yau ya shirya tunkarar mama akan fushin da take dashi.


Da yamma ya shiga har dakinta, ya sameta xaune a kan kujera Mimi tana kwance tayi pilo da cinyarta tanacin chocolate. Tana ganinsa ta miqe daga kwanciyar, mama tace mata Mimi shiga ciki. Ba musu ta shige bedroom din.



Baffa ya xauna ya fara da bata haquri akan dukkan abunda ya dade yana yimata da kuma godia akan tunasar dashi da tayi, kana ya dora mata da abunda baban Badaru ya kawo masa yaji a waya da kuma abunda yaji da kunnensa Badaru na fadawa Mimi. Yace yagane kuskurensa kuma ya canja daga yanxu, kuma Dan Allah ko anan gaba taga yana nufin kauce hanya a wani abun tayi gaggawar tunasar dashi, domin yagane itadin macen arxiqice. Sannan yayi mata xancen tumunin takabarta yasa an fitar mata a kotu tasamu gidaje biyu da wajen miliyan biyu (saboda andade ana juya kudaden) ya karbi acct no ta da nufin tura mata kudaden ya kuma danqamata takaddun gidajenta.


Ya kwallah Mimi kira, ta fito ta tsuguna. Rayuwa kenan duk wanda yayi haquri zaiga haske domin wai yau Baffa ke neman yafiyar Mimi da kuma bata haquri akan abunda duk ya faru a baya.


Mimi tana hawaye tace "komai ya wuce Baffa, kai ubanane duk duniya bani da wanda ya fika, nima ka yafemun abunda nayi maka rannan saboda bani da xabi sai hakan shiyasa nayi" yace baki komai ba MARYAMU Allah ya miki albarka ya baki abokin xama nagari sakamon biyayyar da kikaimun.


Mama na gefe na share hawayen farin ciki, ta dunga godewa Allah. Tace da Baffa nagode da kulamana da dukiya da kayi. Amma inaganin wadannan ka karba ka riqemun."


Yace "riqe abunki Haj Fadima, nadai riqe na yayana Faty da maryam kuma suma na rubuta da shedu saboda halin rayuwa, gidajen dai xantsaya a xuba yan haya." tace to duk yadda kayi nagode.



Yace " to ai bazan yadda kin huce ba sai kin karbi girki, ga cefane can nakawo inaso aimun special girki dan azumin nake kuma nadade banci delicious dinki ba."



Mama ta miqe tabi bayanshi tana dariya tace " yau kuwa xakici domin xan tabbatar maka na huce." Umma da Anty da tunda ya shiga dakin mama suke tsaye suna jiran suga abunda xa ai suka qiqim qiqim ganin mama da Baffa tare suna dariya. Mimi ma ta biyo bayansu da nufin taya mama girki itama tana tata dariyar.


Mrs 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }

Writing & story by
Rahma Muhammad {hajia}

Editing by
Mmn khairat 😍


Page 1⃣4⃣


Cike da farin ciki Baffa ya shiga gidan, gami da kwalawa mama kira tunda daga tsakar gida, ta fito a gigice saboda Jin kiran farautar da yake mata ta iskeshi daki gami da yimasa sannu da xuwa. Ya amsa yana washe baki kamar bebe yaga wawan zama (Lol) sannan ya dora da cewa wani abun farinciki ne ya samemu fadima shiyasa ki ganni gida yanxu, wato yaronnan dan wajen Alh Inuwa shine yaga Maryamu yace yanaso, kuma ga dukkan alamu akusa sukesan auren dan Alh inuwa da kansa yayimun maganar ni kuma nayi dattako nace kawai in sun shirya su kawo kayan aure kawai ayi. Mama ta kalleshi shagarai tare da daure fuska tace, Alh wannan wane irin neman aure ne sai kace auren yar tsana? Daga yaro yaga Mimi yace yanaso sai ace ya fito anbashi? Ita mimin baza aji raayinta ba? Kuma banaji ma Mimi tasan maganar domin da tasani xata fadamun, sannan shin kayi bincike akan yaron? Ko kuma dan ansan mahaifinsa shikenan? Aure fa in anaso a zauna lfy sai anyi da yardar maauratan, kuma naga ai bakai da Alh inuwa ne zakuyi xaman auren ba, yaran ne masu xama saboda haka inaga ku basu dama su fahimci juna inyaso daga baya insun dai daita kwa shiga lamarin. Baffa dake kallon mama tun da ta fara magana a dage tare da fallara mata harara wacce ita sam bata kula ba, ya magantu da cewa sai yanxu nasan ke babbar mahaukaciya ce fadima. Ta miqe tsaye tare da qara daure fuska tamau tace hauka kuma? Yau kuma nice mahaukaciyar? Nan da nan kuwa ya dai daita nutsuwar domin ya farga da kasassabar da yayi (ya tuna da fadima yake magana wacce Sam bata daukar irin cin mutuncin da yakewa ragowar matansa, ta nuna masa tasan ciwan kanta dan haka ko fada xai mata yakan tausasa kalamansa) dan haka yanxu ma sai yayi saurin yin kwana da cewa ai kece naji kina qoqarin yiwa Allah butulci, shekarar maryam din nawa ana neman miji? Ba a taba budurwa mai shekarunta ba kaf danginki da nawa, sai yanxu Allah ya kawo kice ga xance ga magana. Ta kalkeshi tace ni ba butulu bace kuma ba butulcewa nai ba inaso ne dai a gina auren akan fahimtar juna da soyayya, amma tunda haka kace shikenan Mimi yarka ce kana da ikon xaba mata miji, Allah ya sanya alkhairi yasa tsohuwar gida ce. Yawwa yanxu kikayi magana fadima da tun farko abunda kikace kenan ai da ba a tsaya sa insa ba, amin Allah ya yi miki albarka cewar Baffa.

Maryam kwance saman gadonta acan hostel na law skul rubda ciki take tana danna system, qarar Waya ya katseta daga typing din da take a system din, ta tsurawa screen din wayar ido gabanta na dukan 3 3 , tun tana qanqanuwarta ta tashi da tsananin tsoron Baffa da kuma dison qiyayyarsa acan qasan zuciyarta saboda halin ko inkula da yake da al amarinsu, duk da cewa mahaifiyarsu awancan lokacin tana boye musu lamarin baffan garesu kafun su girma su gane, sai kuma alokacin mama take yawan cemusu halin Baffa garesu ajixanci ne irin na Dan Adam. Amma AL AMARIN MARYAM na jinkirin aure da kuma takura gami da gorin Baffa akanta yasa dison qiyayyar Baffa ta samu girma a zuciyar maryam wanda takai tayi yado ta zama tamkar bishiya mai rassa, domin ji takeyi kamar ta raba auren Baffa da mahaifiyarta domin auren Baffa ba abunda ya qari mama dashi sai muzgunawa da gori daga gurin matansa daga gareshi kuma xa a iya kiran abun da yaudara domin kulawar da take kwadayin yayanta su samu inta aureshi basu sameta ba. Wayar ta sakeyin qara akaro na wajen 4 wanda hakan ya yankewa maryam tunaninta, tai shahada ta daga wayar. Ta gaisheshi cike da tsoro da firgici, ya amsa farai farai tare da tambayar karatunta da kuma lokacin kammalawa, lamarin daya daure kan maryam tamau, acikin ranta ta farta Baffa da tambayar karatuna? 😳 first in history.

Bayan hakanne kuma ya zayyano mata dalilin kiranta a waya akan maganar Badaru, sai da ta nutsu kwarai sannan ta gane wadanda yake nufi domin ita tamanta da haduwarsu, amma kuma tayi mamaki dajin cewa wai har ana zancen qarbar kudi ba tare da sun zanta da wanda ya nuna raayin a kanta ba, (domin ita a zatonta wanda yayi mata magana shike sonta wato Badamasi) amma da yake mama batai musu tarbiyyar ja da maganar Baffa ba sai kawai tace masa to Baffa Allah ya xaba mana abunda yafi alkhairi, yaji dadin furucinta kwarai ya dunga samata albarka. Koda ta kashe wayar tunani ya cikata to meyasa yaya Faty da mama babu wanda ya mata maganar ko dai suma basu sani ba? Sannan ta shiga wassafa siffar guy din da azatonta shine Badarun, ta dan tabe baki 😏 tare da furtawa a fili "yayi babu laifi he is handsome " amma ba irin mijin da nake mafarkin samu bane duk da bashi da muni amma bashi da tsahon da nakeso daga da namiji " πŸ™ˆ ta rufe idonta cike da kunya kamar wani yana ganin. Wannan dare dai haka ta qareshi cikin tunanin irin nata salon neman auren cikin gaggawa wato haka Allah ya shirya mata kuma dama fauxa (wata qawarta yar unguwarsu) tasha fada mata in Allah ya tashi bata miji in shaa Allah gaba daya zai fito jinkiri zai kawo mata alkhairi, ta miqe cike da farin ciki da kwarin gwiwa ta dauro alwala ta tada sallah aranta tana cewa ashe nima zanga ranar aurena, ashe ankusa a daina yimun gorin aure 😊.

Ranar jumaar data kasance aranar aka karbi kudin auren Mimi da kuma lefe, da misalin qarfe 2:30 pm Faty ta shiga dakin babarta afujajan, daga gurin aiki take. Yau dinnan zancen kawo kayan lefen ya isketa daga bakin Ahmad mijinta. Tai sallama danta na fari dady (AL Amin) wanda yaci sunan babanta yazo da gudu ya rungume qafafunta da yake a gurin mama yake tun daga yaye, na biyun kuma wato Muhsin dan kimanin shekara 2 tun safe suke gurin mama dashi dame rainonsa. Ta sunkuya ta sumbaci dady tare da cewa sannu babana, muhsin ma ya gangaro ta daukeshi tana shafa kansa. Ta zauna akan kujera gefen mama tare da bawa laure (mai rainon muhsin) umarnin ta dakko mata maltina a fridge, da kyar ta ida bari suka gaisa da mama saboda xance na cinta, suka qule uwar daki. Ta kalli mama da alamar tambaya tace mama wanene mijin Mimi? Wane irin neaman aure ne wannan bamuji neman aure ba banusan mijin ba sai kawo lefe mukaji da sa rana? πŸ˜’ . Mama ta gyara xama cikin hikimar uwa ta gari da sigar lallashi ta kwashe zancen tas ta fadawa Faty sannan ta dora da cewa kuma shima Baffa besan har lefe zasu kawo ba, shi kudi sukace masa kawai sai gasu da kayan lefe. Kuma banaso ki dau dumi a lamarinnan tunda baffanku yace yayiwa Mimi maganar ta bada goyon baya kinga hakan ya nuna tanason yaron, kuma kodan mutan gidannan inaso ku karbi lamarinnan haka Allah ya tsara muyi mata addua da fatan alkhairi. Tace to mama ai tunda kince mimin tanaso shikenan 😊 dama ni banaso a danne haqqinta ne, yanxu ina kayan lefen? Suna can dakin ummanku. Ta miqe ta nufi dakin Umman, tanasa qafa a falon ta fara cin karo da cosmetic din kayan lefen alamar angani duk an watsar ba a gyara ba. Umman na ganin Faty ta dan saki fuska da yake makira ce tare da cewa a a Faty har kin qaraso? Tace eh suka gaisa tare da yiwa juna murna akan auren na Mimi, ana cikin hakan ne anty ta shigo baqin cikinta sam be boyuba akan fuskarta, ta kalli Faty tare da cewa sai kuma kikaji abu babu zato? Ai bana dai yan kwantai sai aure suke, Faty da maganar ta bata ranta tayi murmushi da cewa aishi aure lamarine na Allah in lokaci yayi sai kikaga duk hassadar mutum sai anyi kuma sai kiga duk dadewarka babu aure abun ya zama tarihi. Ta fada tana duba kayan Anty da taga Faty ta dagota sai tai saurin sakin zancen tare da kama wani gadai lefenan akwati 4 da kit ne kaya kala 30, takalma qafa 5, jaka guda 3,
Sai mayafai 6. Kodan gold qaramin Set babu, babbar atamfa a cikin lefen itace cote d voire, leshi bafi tsada acikin kayan kwanaki Safna (yar antyn ce) ta saimun irinsa a gurin aikinsu biya 2 8k kinga a kasuwa baifi 6k kenan? Ai wlh a tarihin gidannan ba a taba matsiyacin lefe irin wannan ba, wai lefen mai kwalin degree a hannu kenan ta qarasa fada tare da sheqewa da dariyar mugunta 🀣, sannan ta dora da cewa ana cewa jinkiri na kawo alkhairi ni dai banga alamun alkhairi ga wannan auren ba nashaji ana cewa in guga ya dade a rijiya yana jawo ruwa tsullum amma shikam gugan gidannan yayi shekaru aru aru a ruwa ya dago fayau. Faty ta dago tai qayataccen murmushi cikin qoshi da ilimi da wayewa tace "mashaallah kaya kam sunyi mu sun ishemu haka duba da babu irin tufar da Mimi bata saba indai a duniya take kuma da kudi ake siyanta, to kinga kuwa indai ka saba saka sutura me tsada ai ta lefe baxata dameka ba, kuma ai lefe bashine xaman aure ba mu alkhairin abun muke nema, kuma bamusan arxiqin da Allah ya yiwa Mimi ba anan gaba kinga kuwa be dace mu sare tundaga kan lefe ba. Tana gama fadar haka ta tattara kayan ta maida komai muhallinsa ta dubi umma wacce ke kan kujera tana kada qafa ga dukkan alamu xancen Anty akan Mimi yayi mata dadi domin ga fuskarta nan ta nuna alamar hakan. Tace Umma Allah ya sanya alkhairi ya kuma kaimu lokacin sannan ta fice . Haka sukaci gaba da shirin biki wanda xa ayishi da zarar Mimi ta gama law skul da sati daya.



Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }

Page 1⃣5⃣


NA RAHMATULLAH (Hajia)




Kammaluwar karatun Mimi da kawo IV din bikinta abune da ya kasance a tare, kuma aranar data dawo ne Badaru yaxo domin suga juna tare da tattauna al amuran biki ( kuji fa kamar auran qauye), da taimakon yaya Faty wacce kullum sai tazo gidan saboda shirin biki ta shirya kanta cikin atamfar sΓΊper wax ja ta yafa mayafi kalar atamfar da dan takalminta shima ja plat, fuskarta tasha make up wanda ya fito da idanunta sukai tar saboda eye liner da mascara da akai amfani dasu wajan qayata idanunta. Jikinta na tashin qamshin turarurukan companyn Al rehab, domin ita a raayinta tafison Arabian perfume .

Zaune ta iskoshi a sitroom din gidan, qamshinta ya fara sanar masa ta iso, ya dago ya qura mata ido tare da hadiye wani irin abu da ya tsirga masa maqogaro ya saki murmushi aransa yana qisima bai taba ganin macen da ta birkita masa hankali ba, idan aka dauki lokaci bai samu maryam a matsayin mata ba tabbas zai iya sabawa ubangijinsa akanta, duk wani abu da ake buqata ajikin mace maryam tana dashi , wata irin muguwar sha awa yakeji akanta, feelings din dabe taba sanin yana dashi ba akan mace maryam tasa yana jinsa , shiyasa ya yanke shawarar auranta duk da baya sonta kuma baya raayin mace me shekaru da wayewarta, zai ajeta amatsayin wacce zai dunga kashe qishirwar shaawarsa akanta, sannan gefe kuma ga burin ransa wato Nafeesa a matsayin matar so. A bangaren Mimi kuwa tana hada ido da Badaru gabanta ya yanke ya fadi a fili ta furta "innalillahi wa innah ilaihi raju un " saboda tsananin firgici data shiga na ganin Badaru amatsayin mijin auranta nan da yan kwanaki, ashe wanda take zato ba shi bane? Ashe ita duk hauka take? Ashe Badamasin ma da take ganin be cika irin sharadin mijin da takeso ba , ba shine mijinta ba? Ashe kasan Badamasin ne? Shin meyasa ta dauri kanta ta cewa Baffa ta yarda da mijin da ya bata tunkan taga kalar mijin? Yanxu fisabillah ina ita ina wannan dan tsamurmurin bafillacen wanda tasan tafi tsaho nesa ba kusa ba??? Tambayoyi burjik ta dunga yiwa kanta a xuci a fili kuma tana hawaye, wata irin muguwar tsanar Badaru ta shiga xuciyarta nan take. Badaru da tun daxu yake kallon Mimi cikin mamaki, ya magantu " yanaji da ganina kin furta adduar da sai anga masifa ko abin qi ake yinta? " cikin baqin ciki da bacin rai idanunta jazur ta kalleshi tare da cewa meyasa kaimun haka? Dan me baka nemi yardata ba ko Jin raayina akanka kakai maganar gurin Baba na? Wane irin neman aure ne haka? Ya bata amsa da cewa irin neman auren da addini ya tsara, batare da tunanin komai ba tace to kasani ni Banasonka wlh πŸ˜ͺ shima cikin nasa sigar bacin ran da tsantsar rashin mutunci yace to nima anfada miki ina sonki ne? Kawai dai xan aureki ne saboda bani da xabin da ya wuce auran naki, xancen rashin neman yarsarki kuma sai kije ki tuhumi babanki wanda daga ganin sarkin power yasa miya tai zaqi, dagaji ance ina sonki yace in fito wanda hakan ya nuna baki da wani sai ni din danake shirin rufa miki asiri shine xakimun iskanci, wlh maryam bani da auran mace me shekaru kamarki kawai qaddara Allah ya doramun akanki. Ance inxo ne in mutsara lamarin biki to ni kisani bani da raayin wasu bidi 'o'i saboda haka sisina baxan bayarba nayi abunda yake wajibi wato sadaqi. Yana fadar haka yasa kai ya fice.

Jage jage fuska duk ta dame saboda make up daya hade da hawaye ta shiga dakin mama, Faty ce kawai ta kula da shigowarta dakin ta sauri tashi ta tareta ta fada jikin Faty tare da qara fashewa da kuka, yaya Faty dama irin mijin da Baffa ya zabamun kenan? Sam be dace dani ba wlh banasonsa na tsaneshi bana raayin auren mutum irin wannan. Faty ta dago kanta cikin rashin fahimta tace Mimi yimun bayani yanda xan gane, ba ance kun taba haduwa ba? Tace ba shi bane sister wanda nake zato ba shi bane 😭😭 wannan mugune wanda baya qaunata kuma ya furtamun da bakinsa, bazan aureshi ba sai dai in duk abunda za ayi ayi. Mama ta iso kansu ta tsaya cike da al ajabin abunda mimin ke fada, ta durqusa a gabansu tace Mimi babu abunda za ai wanda ya wuce ki yarda da qaddara kinsan wlh auren nan babu mai hana faruwarsa sai Allah tunda baffa ya tsaya akai, kuma turjiyarki ga wannan lamari yana nufin tashin hankalina acikin gidannan. Ta share kwalla tare da cewa mama yanxu auren dole kike nuna goyon baya ayimun? Tai saurin tareta da cewa a a wlh Mimi ko maqiyina bazanso auren dole akansa tunda anyimun banji dadi ba, bare ke yar cikina, amma inaso kiyi haquri ki dauki wannan aure a matsayin qaddara mutum baya taba gujewa qaddararsa wlh tun kan nasan waye mijin da Baffa ya xaba miki naji Sam lamarin bai munba, MARYAM indai ni na haifeki bazaki kaucewa umarnina ba, umarnina kuma gareki ki karbi wannan aure, in shaa Allah bazaki danasani ba. Ta dafa mimin tare da cewa kin yarda xakibi umarnina MARYAM? Tai saurin kwada kai tare da cewa yar halak ce ni mama bazan taba kaucewa umarninki ba, naji nagani na yarda. Kukan da take yasa dady dan yaya Faty shima yasa kuka tare da xuwa ya rungume Mimi yana share mata hawaye da cewa Anty yi shiru ki dena kuka Anty, ta kalli yaron soyayya ce me qarfi tsakaninta da dady ko uwarsa be shaqu da ita ba yadda ya shaqu da Mimi saboda a hannunsu ya tashi, tayi dariyar yaqe cike da qaunar dady tace nayi shiru Baba na ta rungumeshi suka kwanta akan cinyar yaya Faty.

Badaru tsaye qofar gidan su Nafee, yafi 30 minutes a wajen yana dakon fitowar ta amma shiru, har ya fidda rai ya juya zai tafi sai kuma gata ta fito tana yatsina wacce take nuna dab take da tayi rashin mutunci.

Ya dan matsa kusa da ita tare da cewa ranki ya dade yana washe baki 😁. Tai far da ido πŸ™„ sannan tace meya kawo ka? Ai canake kanacan gurin masoyiyarka?

Yayi saurin tareta da cewa ai bani da wata masoyiya da ta wuce ki, ai ban zaci ma zaki fito ba kusan fa sati 2 ina xuwa bakya fitowa. Ta fallara masa harara sannan tace ai dole ce tasa na fito, tunda naga rashin fitowar tawa be hanaka abunda kake niyya ba wato auren Maryam. Ta fada tare da
fashewa da kuka πŸ˜ͺ.

Tausayin Nafeesa da sonta ya qara qamari a xuciyarsa cikin sigar lallashi yace yi haquri Nafee wlh auren maryam qaddarace a guri..... Dakatamun βœ‹πŸ½ ta tsai dashi a hassale, Kullum abunda kake fada kenan a matsayin abunda xaka kare kanka a wajena kuma nagaji dajin hakan, ai wlh Badaru ka cuceni, ingama jiranka inbar karatuna sabida kai amma yanxu kaimun haka. Yanxu bani da ikon fita sai aita nunani ana zundena, wasu har cewa suke ka fasa aurena.

Nafee kiyi haquri wlh babu abunda xai hanani aurenki sai mutuwa, kuma duk masu yi miki dariya a sannu zasusha mamaki domin aurenmu na barshi daganan xuwa bayan sallah in shaa Allah.

Amma dai kasan bazan zauna da ita ba ko? Saboda haka ka nemar mun gurin zama tun wuri saboda na tabbatar bazan iya hada kishi da wata ba a kanka.

Nasani Nafee shiyasa ma na nemar mata gurin xama shi kuma wancan gidan dama nakine ke kadai keda yayan da zamu haifa.

Nafeesa ta dan sakko jin wannan furuci na badaru kuma ta tabbar har yanxu yana sonta, tace wai muga photon ta kyau ta finine naga kanata rawar kai a kanta? Yayi murmushin cin nasara yace wlh bani da photon ta amma wlh ko kama qafarki batai ba Nafeesa. Wai shin kinsan ma dalilin auranta? Nan ya kwashe abunda ke ransa game da Mimi ya fadawa Nafeesa ba tare da tunanin illar da hakan kan iya haifarwa ba nan gaba.

Lamarin da yayiwa Nafeesa dadi kwarai da gaske, domin tasan

Please Login or Register in order to submit comment