Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karka kuma zagarmun uba, domin yana kabari akwance". Yayi saurin cewa "an zageshi uban ubanki ma yaci ubansa, kiyi abunda xakiyi" ta mayar masa da martanin cewa "babu abinda xanyi domin xagi xagawa yake, kuma duk abunda kakemun Allah ya na jinka, yana ganinka kuma zaimun sakayya."



Ya watsa mata wani kallo sannan ya funciko hannunta ya hankadata bakin qofa tare da cewa "fita ki tafi gidan ubanki shegiya mara tarbiyya gayyar tsiya." Badamasi ya daka tsalle tare da dakawa Badaru tsawa kamar shine gaba da Badarun yace "wlh Badaru ka kiyaye ni, na rantse da Allah xaka tarkowa kanka bala'i, domin yanxu xanje na fada Abba abunda gidanka yake ciki" yana kaiwa nan ya figi muqullin motar Badaru dake kan kujerar parlourn (domin shi baixo da mota ba) ya fita. Mimi ma tasa kai ta fita yayi saurin cewa " ban baki izinin fita ba" ko takansa bata biba tai waje ya bita da gudu ya jawo ta ya dawo da ita tare da furta "maryam akanki ake shirin hadani da iyayena, kowa nawa sai ya rabu dani a kanki. Abokaina, yan uwana, yanxu kuma iyayena? Meyasa haka?"


Acikin motar Badaru kuwa Badamasi ne a kifa kansa a sitiyari yana jin quna a ransa, wlh da yasan yacce xai tarar da Mimi kenan da bai zoba. Bazai juri ganin Mimi cikin wannan halin ba, yanxu meye abunyi? Yayi dan gajeran tunani, baxai fadawa iyayensu abunda gidan Badaru ke ciki ba yanxu. Domin inyayi silar mutuwar auren Mimi sannan daga baya yazo yace yana sonta cewa xa ai ya kashe mata aure dan ya aureta. Ya dakko wayarsa yayi saving recording din da yayi saboda wata rana.



Hannunsa yakai kan aljihun motar ya jawoshi, saiga kwalayen magani guda 4 duk iri daya (maganin da mekudi ya bawa Badaru, yake ajiyarsa amota saboda kar Mimi ta gani) ya dakko ya duba kwalin hotunane ajiki na mace da namiji tsirara suna xxx kala kala hutunan abun ba kyan gani. Ya duba rubutun jikin maganin, yaga illar da yake, a qa'idar maganin ma matan banxa masu blue films akewa amfani dashi dan su fita hayyacinsu, kuma suma din sai anyi aggrement. Amma dan zalunci da son zuciya Badaru yakewa yar mutane amfani dashi, kuma bama kwali daya ba, alamu sun nuna ya dade yana mata amfani dashi tunda ga kwalaye nan har guda 4.


Ya share hawayensa ya dauke ragowar maganin a fili yace "MARYAM Allah ya saka miki, Allah ya miki canjin alkhairi domin Badaru ba miji bane.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣6⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Cikin kwanakin da suka biyo baya tai wata irin ramewa kamar me ciwon SIDA (AIDS). Ta fita hayyacinta kwarai, ga wani irin mugun qaiqaiyi dake addabarta a qasanta, ga dukkan alamu ciwon sanyi infection yayi mata mugun kamu. Domin har gari gari take gani a gabanta a memakon danshi da akasan ya mace dashi, ga wani irin wari danma bata ramo da inserting almuski.


Badaru tsakaninta dashi dangantaka tayi tsami kwarai da gaske, domin sai suyi 3 dayz koma fiye da hakan bai mata magana ba, kuma inma tayi masa baya amsawa. Walau kuwa koda gaisuwa ce, sai dai tagaji da tsuguno ta tashi. Wanda hakan shiyasa kawo mugun koma baya a lfyarta, sau da yawa sai dai ta ganta a kwance kamar gawa batasan abunda ya faru ba tunda babu kowa a kusa balle ya karanta ta mata abunda ya faru kafin ta tsinci kanta a hakan.



Babban abun takaicin shine : duk wannan takun saqa da suke da shi, hakan baya hana in dare yayi yazo ya mutsutstsuketa da sunan yazo neman haqqinsa na aure. Sakamakon ciwon sanyi da yayi mata illah yasa ko yazo baya samun komai (babbar illar ciwon sanyi kenan, wato qafar da ni'imar mace) wanda hakan ke jawowa ya fusata yayi ta xaginta da aibatata.



Data kula sosai sai ta gano cewa ba ita kadai ciwon ke damu ba, saboda Badaru ma Kullum cikin sosa al aurarsa yake, alamu shima ciwon na addabarsa.


Dan lfyar kanta da kuma maganin wulaqancin da Badaru kemata a shimfida (domin tana kyauta zaton rashin samun biyan buqatarsa na daga abunda ya sa wulaqancinsa ya kuma ta azzara) yasa ta tunkareshi da sunan ya barta taje asibiti domin ciwon sanyi ke damunta. Da farko be kulata da maganar ba, sai daga baya ya jiyo qanshin gaskiya a maganarta. Domin ciwon da tai masa bayani yayi kama da wanda masu magani ke bayani a kasuwa. Hakan yasa ya sameta har daki yace "kawai kinje kin kwaso ciwon sanyi kinxo kin gogamun, wlh in hakan yayi sanadiyar raguwar qarfin mazantakata bazan yafe miki ba"(🀣🀣🀣).


Ta dago arazane jin abunda yace, cikin sanyin murya tace "ni kuma Badaru? Ni ina fita ne? Canake tunda nazo gidannan fitata daya? A ina xan kwaso ciwon? Nafi zaton kaine ka dakko mana a kasuwa" yasan tana da gaskiya shiyasa bece komai ba ya kada kai yayi gaba.


Da yamma kuwa sai gashi da ledar magani, ya siyo a irin gurin masu saida maganin hausar nan na kasuwa. Wadanda ke yawo da mota suna tallah a speaker. Ya miqo mata wani qaramin qulli "wannan gashi ki juyeshi a madara yanxu ki shanye, ya miqo dayan wannan kuma ki dunga turare dashi kina tsugunawa akai" (kunji fa! Mtsew komai aka hada da jaki sai yaci kara) tace "to" ta karba, azuciyarta take tunanin shidai asibiti ne bayaso arayuwarsa. Ta qudure bazatai amfani da wandannan magungunan da batasan ingancinsu ba haka kawai ita ba qoshin lfy suje su illatata.



Tofa! Abu fa ya kacame, komai ya xama chocolate πŸ˜‚. Iskancin Badaru da wulaqancinsa kanta ya kazanta, ko alabari bata taba jin inda ake cin mutuncin matar sunnah yadda Badaru kecin mutuncinta ba. "Banxa jaka, na tsaneki" sune kalaman da Badaru ke fada mata adun sanda suka hada shimfida dashi saboda baya samun biyan buqata Sam. Gashi ita a kanta tanajin yadda tai wata irin budewa tai sako sako, kamar matar data haihu bata gyara kanta ba.


Bama sai sun hada shimfida ba, a rana daya yakan ce mata "na tsaneki" yafi sau cikin carbi. Sunanta kuwa a gurinsa ya koma "jaka" dan sau tari zai sata aiki sai yace "ke jaka yimun abu kaza" yayin da agefe guda kuma ya dage da aikin ginin da yake, domin ya auro Nafee wacce yanxu Kullum a gurinta yake kai 11 dare.



Mimi, yar kwalisa yanxu ta xama wata muguwar siriri mara fasali, tayi fari fau kamar me amfani da mayunkan kwaile fata (bleaching) yar kewayayyar fuskarta ta koma tsuru sai manyan idanuwa πŸ‘πŸ‘ da hancinta πŸ‘ƒπŸΎ wanda rama tasa yayi bodardar. A taqaice dai ta xama mummunar qarfi da yaji.



Babbar matsalar dake addabarta itace rashin ganin al adarta (period) rabonta dayi tun tana wata biyu a gidan, wato lokacin da taje asibiti ta biya gidan Faty. Tayi tayi Badaru ya barta taje taga likita ko wata matsalar ce yaqi. Data dameshi da xancen saboda ciwon marar dake addabarta sai yace karta dameshi, saboda ba akanta aka soma CIKI ba. Tunda daganan itama bata qara xancen ba, saboda itama data duba cikinta sai taga tafi kama da masu qaramin ciki.



Kuma wani ikon Allah sai ta tsinci kanta cikin farinciki da cikin, saboda kasancewarta meson yara tunda basu taso sunga kowa a dakin mama ba sai su biyu. A fili tace " Baby ki rasa lokacin da xakixo sai lokacin da ake sa toka sa katsi? Allah ka rabamu lfy, Allah ya miki albarka yata😊" ta fada hannunta na dafe akan cikin.



Badaru dake gefe yana sauraranta yayi saurin matsowa kusa da ita yace "au mace kikeso ki haifa? To ai se ki roqi Allah kada ya baki me irin BAQIN JININKI, domin in ta rasa miji wlh sadakarta xan bayar" ta dago ta kalleshi tayi murmushi 😊 tace " Badaru in tayoka ai bazatai baqin jini ba, tunda ka ganni ka taimaka ka aureni itama sai Allah ya dubi kyakykyawan aikin da kayi a kaina ya kawo me auranta 😊"



Yasan magana ta fada masa dan haka yayi tsit.

******* ******** ******

Tun jiya cikin dare take murqususun ciwon mara, har xuwa yanxu 9:43 na safe. Tun tana iya yunquri har qarfinta ya qare ta kasa. Badaru tun shekaran jiya yayi tafiya Lagos akan harkar kasuwancinsa, kuma gashi bata da lambarshi kamar yadda bashi da tata.


Badamasi da yau ya shigo kano yazo daga inda yake aiki (Dutse) tunkan ya qarasa gida hankalinsa yake akan maryam. Tun rabuwar da sukai da Badaru akan ciwa maryam mutunci hankalinsa ya kasa kwanciya, dan haka direct ya wuce unguwar su Badaru.


Tun daga soro yake kwada sallama amma ba amsa, ta bangaren Mimi ta dakko waya da nufin kiran Faty ta fada mata halin datake ciki sallamar ta rusketa. Kuma tana amsawa amma dake muryar a shaqe take saboda wuyar ciwo shiyasa bayaji. Ya sako kai parlour tai miqe daga kwanciyar cikin qarfin hali tana haki tace "inata amsawa bakaji" ya dubeta a razane yace "maryam badai ba lfy ba? Ina mai gidan ya fita ya barki cikin wannan halin?"


Tai murmushi tace "yayi tafiya tun Lagos, bayan tafiyar ne ciwon ya riskeni shi......" bai qarasa jinta ba ya dakko waya a aljihu. Sai ji tayi yana xancen rashin lfyrta kuma ga dukkan alamu da Badaru yake. Can yaji yana cewa "babu batun ragonta, dan mace na da ciki bazatai ciwo ba sai ace tacika ragonta? Nidai yanxu xan kaita asibiti ya kashe wayar"



"Tashi ki shirya muje asibiti, " ya bawa maryam umarni. Sannan ya zarce da mitar cewa kasan lalurar ciki ne? Inda kai Allah ya dorawa wayasan kwakwazon da zakai? Kaiwa yar mutane ciki ka tafi kabarta da wahala. Itadai ta yunqura dakyar ta miqe tayi hanyar toilet tana godewa Allah da ya kawo me temakonta.



Cikin qarfin xuciya tai brush da wanka suka tafi. Ganin yadau hanyar yan kaba yasa tace "Aminu kano nake ganin likita ai" ya waiwayo ya dubeta yace " rana tayi shiyasa xan kaiki asibitin wani abokina da mukai karatu tare, amma shi likitan mata ne" tace ai a Aminu kano akwai yayata dake aiki acan, inka kaini ko likitan yamma ne sai nagani"



Yana kallon titi yace "sry bari na kaiki private din xaki fi samun kulawa inyaso har awo da haihuwa sai kije can. Yasan aikinsa sosai" ta sunkuyar da kai cikin kunya jin yayi maganar cikin jikinta. Ya qura mata ido cikin burgewa dan yanason mace me kunya. Aransa yana aiyana rashin imanin Badaru dan kowa yaga maryam yasan ba a dadi take ba kuma ga ciki na wahalar da ita.


Sun tadda layi kasancewar safiya ce. Badamasi yayi masa waya da kansa ya fito ya shiga dasu bayan ya nemi alfarmar na kan layi.



Yana dubata suna dan taba hirar yaushe gamo da Badamasi, ya kalleta yace maryam alamu sun nuna kina da qarancin jini a jikin ki, shiyasa kika dashe kikai haske. Badamasi yace " ba ciki bane ya kawo hasken?" Dr yace "bazan iya cewa da ciki ba ko babu, amma dai bari nayiwa sister sarah magana ta tafi da ita can nursing station tayi mata checking sosai akan hakan"


Ya kirata a waya nan da nan sai gata yace "kuje da wannan yayi mata bayani" Mimi ta bita yayin da Badamasi ya koma reception dan bawa ragowar marasa lfyar damar ganin likita.



Acan gurin nursing din sun dubata sosai taji wacce ta dubata na fadawa dayar cewa, tana buqatar aimata wankin ciki. Lamarin da yasa Mimi tsorata, domin tasha ji ana fadar wahalar wankin ciki. Dan haka ko takan mayafinta da jakar bata biba ta ranta ana kare πŸƒπŸ½β€β™€.


Badamasi na zaune yaga fitowarta daga dakin a harkitse, tana tafiya tana waiwayen bayanta taga ko nurse din ta biyo ta. Ya taho gurinta da sauri cikin rashin sani suka gabxa karo. Tai qasa xata fadi yayi saurin tarota jikinsa, jinta jikin mutum yasa ta qanqameshi tana cewa "Badaru kaji wai wankin ciki zasuyimun, kuma da xafi sannan xasu wankemun Baby dan Allah karka bari suyimun." shidai Badamasi tunda yaji maryam ajikinsa ya tafi wata duniyar, ya xaci irin mafarkan da yasa ba yine akanta dan haka ya rungumeta jikinsa tsam yana sauke ajiyar xuciya. Akayi sa a itama ta xaci mijintane ta kwanta lub.


Nurse din data biyo Mimi da jakarta da mayafi ce ta dawo dasu hayyacinsu. "oga gashi ta gudo dakaji ance xa ai mata wankin ciki" yai saurin rabata da jikinsa daya farga ba mafarki yake ba, a xuciyarsa ya dunga cewa astagfirullah Badaru kai ka jawomun da ka kula da matarka da ban kawota asibiti ba balle harna rumgumeta. Itama Mimi sai yanxu ta dawo hayyacinta, ta dunga jero neman gafarar Allah.



Suka koma office din Dr, nurse din tayi masa bayanin matsalar Mimi da kuma qin yadda ai mata wankin cikin. Ala dole ya rubuta mata maganin ciwon mara dana qarin jini. Badamasi ya tambayeshi akan cikin. Yace "yanxu kam bazan iya cewa da ciki ba ko babu tunda akwai lalura da yawa a tare da ita, sai dai ko in kun kuma dawowa ayi scanning. Ga maganin ta dage da cin abinci da shansu kuma basu da qarfi koda da cikin baxasu illatashi ba" sukai sallama suka tafi.



A hanya suna tafiya tace masa "dan Allah karka maidani gidannan na kwana ni kadai jiya nasha wahala, bansan abunda hali xaiyi ba yau." ya dubeta yace "to Maryam ai bani da ikon kaiki wani gurin bada ixinin mijinki ba, amma bari in masa magana saboda akwai hatsari abari ki kwana ke kadai" ya dakko waya ya kirashi tanaji yana masa bayani, can ya miqo mata wayar yana cewa gata. Tai sallama be amsa ba bare ya saurari gaisuwar da take masa ya hau masifa " kince bazaki kwana gidanki ba ko? Uwar langwai to kitafi duk inda xaki tunda kinsa anmun titsiye inna dawo kya dawo." yana kaiwa nan ya kashe wayar, itama ta kashe ta miqa masa tare da cewa kaini yahya gusau gidan yaya Faty.



Koda suka isa gidan sun samu ya Ahmad na nan, dan haka koda yaya Faty ta fito domin temakamata su shiga ciki yaga bata lokaci ne dan haka ya dauketa cak yakaita har cikin parlourn. Badamasi ya dunga kallonsu cikin birgewa, domin sai ka xata Ahmad ne dan uwan Mimi ba Faty ba.


Badamasi ya dade a gidan suna hira, saboda family din sun burgeshi. Faty ta dunga jerawa Mimi sannu ta duba magungunan da aka bata. Tare sukayi dinner sannan tasha maganin kana Badamasi ya tafi.


Yau dadi takeji xata kwana gidan yaya Faty, har dare sunata hirarsu cikin nishadi sannan suka nemi makwanci, yaya Faty ta dunga mitar ramar da Mimi tayi amma koda mimin ta fada mata ciki ke wahalar da ita sai mitar ta koma murna. Suka raba dare suna hirarsu sannan sukai bacci.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣7⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Kwanaki uku da tayi gidan Faty yazo mata da wani irin canji, har mamakin nishadin da take ciki takeyi. Sai take ganin rayuwarsu kamar lokacin da suke gida kafin suyi aure. Suci abinci tare, bacci tare, sannan gashi ya Ahmad duk sanda xai shigo saiya shigo mata da abun kwadayi, yakance me ciki ba a rabata da kwadayi, sai kace shi xa a haifawa dan. Amma aduk sanda ta tuna xata koma gidan Badaru sai jikinta yayi mugun sanyi sannan gabanta yayi ta faduwa.


Rana ta biyar a gidan Faty wanda ya kama da satin Badaru daya a Lagos, da yammaci suna zaune ana hirar da aka saba anata dariya. Mimi zaune a gefen Faty akan kujera 3 sitter tanacin guava, yayin da ya Ahmad ke gefensu akan kujera 1 sitter yana basu lbr sai dariya suke.



Badamasi yayi sallama ya shigo, Mimi na ganinsa gabanta ya yanke ya fadi. Nan take nishadin da take ya qare kuma duk wanda ke parlourn ya lura da wannan canjin na Mimi. Ko Badamasi bai fada ba tasan Badaru ya dawo kuma xuwa yayi ya maida ita kamar yadda ya alqawaranta.


Suna gama gaisawa ya fada musu labarin dawowar Badaru tun safe, kuma yace yaxone ya maidata gidan. Ya Ahmad ya katseshi da cewa "shi maiyasa bazaizo ya dauki matarsa ba? Sati daya baka gari? Inka dawo ai iyalinka ya dace ka nema kaji lfyarsu, ko akuya ka bari da ciki sati daya inka dawo ai ka binciki lfyarta. Wannan abunda yakeyi sam babu tsari a cikinsa, na kuma gaji dab nake da indau mataki akai " ya qare maganar cikin bacin rai πŸ˜”. Badamasi ya bude baki da nufin kareshi ya Ahmad ya tsai dashi "karkace komai, nasan halinsa kuma shirun da akai masa baya yana nufin Mimi bata da gata bane, kawai muna kau da kaine saboda iyayenmu" Faty na gefe na share hawaye .



Sha tara ta arxiqi suka hada mata, kamar wacce xatai tafiyar shekara. Har Badamasi ya dunga jinjina soyayyarsu ga Mimi. Faty bata fito rako Mimi ba saboda kuka da take bataso tasa mimin kuka itama, sai ya Ahmad ne ya tsaya aka loda kayan a bayan motar sannan ya kawo kudi ya bawa Mimi, har anrufe motar ta fito da gundu ta fada jikin ya Ahmad tasa kuka ya kamo fuskarta ya share mata hawaye yace "maryam kici gaba da haquri Allah ya na tare dake, baxaki taba tabewa ba a rayuwarki" ya bude motar ya sakata suka tafi.




***** ***** ******

Bata canja xani ba rayuwar da suke a baya itace dai, gashinan abun babu tsari kamar a jahiliyya period.



Kimanin kwana 11 da dawowarsa daga Lagos kenan daren ranar suna kwance, ya hauro kanta yasa qarfi ya danneta. Kimanin sau uku kenan yana yin hakan, inya gama buqatarsa yaji bai gamsuba yayita zaginta yana ci mata mutunci.



Yanxun ma hakace ta kasance, ya shigeta da dukkan qarfin da Allah ya bashi. Taji xafi kwarai harta kwallah qara, yaja dogon tsaki yace "qarar me kikemun? Wai nufinki xafi kikaji? Abunda duk kin bude kin tale, innaxo shigarki kawai ji nake na rufta babu wata madatsa πŸ˜³πŸ™ˆ shine har xakice kinji xafi?"


Tai qasa da murya"wlh Badaru tun lokacin da ciwon sanyin nan ya samemu inkanayi ji nake kamar kana xubamun yaji daurewa kawai nakeyi, da kabari naje asibiti da tuni mun warke." cikin hargowa da daga murya yace "ya sameki dai, dan ni tuni na warke, ai nakawo miki magani kikaqi amfani dashi ke lallai sai na asibiti ko Baturiyya? To wlh baki isa ba dan mugunta kin hanani inji dadi dake? Wlh wlh whl yau ko xanyi sau dari sai naji dadi xan kyakeki ya rage naki"



Yana kaiwa nan ya farmata kota ina juyata yake yayi, tun tana jin xafi harta denaji. Numfashinta ya fara gazawa. Batasan iya lokacin da ya shafe yana durxarta ba, ita dai tasan yayi mugun dadewa yana abu daya. Sannan ya sauka ya koma gefe ga dukkan alamu gajiya yayi bawai biyan buqatar ya samu ba.



Kukansa ya dawo da ita hayyacinta, inda cikin kukan takaici yake cewa "maryam kin cuceni, kin xalunceni, ni zakiyiwa haka ko? Ni zaki hana jin dadi dake ko? Kimanin wata daya kenan Kullum cikin buqata nake kin kasa biyamun ita. Kije Allah ya isa ban yafe miki ba, in Allah ya yadda bazaki gama da duniya lfy ba. KE MARYAM ALLAH YA TSINE MIKI." 😳😳😳😳



Jin furucin Badaru na qarshe yasa tai xunbur ta miqe, tare da cewa "Badaru me yayi zafi haka??? 😳" ya bata amsa da cewa "ubanki ne yayi zafi" yana fadar haka ya fita daga bedroom din.



Wani irin yanayi ta shiga ita ba matacciya ba ita ba rayayya ba. Kukan ma ta kasa, tsinuwa daga mijin aurenta? Akan abunda bata da iko akai? Tab akwai matsala. Saboda da gajiyar dirxar da Badaru yayi mata batasan sanda bacci ya kwasheta ba. Sai ana kiran sallatu ta farka, qasanta wani irin xugi yake mata kamar ansa reza an ketata taje tai wanka tai sallah ta roqi Allah sauki da gaggawa kan halin da take ciki.


Sukuku ta yini saboda tsinuwar da Badaru yayi mata ta taba xuciyarta sosai, ta qudure a ranta inya kunna inji da dare ta samu chajin waya xataiwa ya Faty maganar infection din ta kawo mata Magani, domin wulaqancin ya isheta haka gara ta naimi magani ya dunga samun biyan buqata axauna lfy domin ita batasan tashin hankali (Allah sarki rayuwar ya mace, Kullum cikin sadaukarwa namiji take.) babu abunda ta iyaci ranar illa ruwan lipton da lemon tsami.



Ta idar da sallar laasar, tadan kwanta kan sallayar tana azkar, ta qudure aranta yau laraba intasamu dan aike xata bashi kudi yayi mata sadaka domin yau yini tayi gabanta na faduwa. Bazai wuce hudu da rabi ba 4:30 lokacin da taji dawowar Badaru, tayi mamaki kwarai dan bai cika dawowa haka ba sai inda muhimmin abu da xaiyi.



Ya wuce daki fuu sai gashi da tulin kayansa masu dauda. Ya fita tsakar gida, sai gashi ya dawo ya danqi gashin kanta ya fita da ita, ya nuna mata tulin kayan wankinsa yace "ga wanki nan kiyimun, tunda baki iya biyamun buqata ba kimun wanki, dan baxan dunga baki abinci a banxa ba" tai tsam sannan tace "to kayi haquri kaga nawa ma bayi nake amma in ya Faty ta aiko karbar nawa wankin in shaa Allah xan hada maka da naka."



Ya danqi wuyanta ya hadata da bango, sannan cikin huci da tsabar tsanar yace "ke kin isa insaki aiki kice baki ba? Wlh baki isa ba, na tsaneki wlh da inka kashe rai babu wani hukunci a kanka da kece mutum ta farko da xan fara kashewa, maryam ban taba tsanar wata halitta a duniya kamar ki ba. Saboda haka dole kimun wanki dan ubanki" ta fusge wuyanta tayi gefe ganin yana shirin kaita lahira, tana maida numfashi tace "wanki bazanyi ba kisa kuma bisimillah ka kasheni." cikin bacin rai take furta wadannan maganganun domin ranta yakai matuqar baci da xagin da Badaru kewa ubanta.



Kafin ta ankara ya tsinka mata mari ji kike kau! 😳 tayi baya cikin azama ya dora da cewa "lallai wuyanki ya isa yanka? Yauni kike maidawa magana? To dan ubanki...... "ta tari numfashinsa kafin ya qarasa. "karka kuma xagin ubana domin nasan darajarsa, kuma da yana raye wlh bazan auri wanda besan darajar iyaye kamar ka ba, maraicine ya jawomun"


Ya kuma dauketa da wani gigitaccen mari, "na xagi uban

Please Login or Register in order to submit comment