Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bawa mama da mumy wani hadadden lace iri daya sak sai banbancin kala, da hada musu da shoe nd bag cikin kayan data yo order ko kwancesu ba ayiba. Ta rasa mexata basu, ta dakko wannan ta dakko wancan wani abun ma baxai masu amfani ba kawai ta rasa mexata basu ne, duk abunda hannunta yakai kansa dakkowa take, harta fara bawa mumy tausayi. Tunani take mimi wace irin halitta ce ita? Ansha kawo mata suka cewa Mimi xata rabata da Bature inta yadda ya aureta, ko kuma su tattare arziqinsa daga ita sai uwarta da yar uwarta, amma ita kam ta qaryata domin sai yanxu ma take morar Bature da arziqinsa fiye da da, dan maryam ta koya masa sakin hannu da xuciya akan kowa nasa. Gidaje ya raba musu ita da ragowar yan uwansa kwanakin baya, mumy tace lallai itama maryam ya bata nata shine ya mallaka mata bayan warkewarta. Haqiqa irinsu Mimi a duniya dai daiku ne duk wanda ya xauna da ita saiya yabi halinta. Little kuma ta bata mayafai da 20k tace tasa katin waya. Drivern mumy ma bata barshi ba saida ta bashi tsaffin kayan Bature da 10k ya dunga godia dafatan Allah ya sauketa lfy. Yadda sukaxo da kaya niqiqi haka suka koma dasu. Dan kowa nuna musu Jin dadin xuwansu yake ta hanyar tsaraba. Suka rakosu har bakin mota Mimi ta riqe hannun mumy tace "mumy dama karku tafi kuyi xamanku nan" mumy tace "wato sai mu xauna gotai -gotai damu cikinku sabida a garin gaba -gaba ake?" haka dai aka rabu a marmarce Mimi harda hawayenta.


****** ******* ******* ***

Yaxo mata da labarin ansamu yan hayar da xa a saka a gidan ya kawo mata kudin da bank suka kawo miliyan 3 cis. Tai tai ya diba yaqi daga qarshe ma sai saka mata dariya. Tace kudin ka ajiye a gurinka so nake ka saimun motaci guda biyu iri daya. Yace "wa xaki bawa?" tace "mama da ya Faty" yace "to akwai yaran dake kawomun mota, a gunsa nake siyan mota xan masa magana ya kawo miki masu kyau"




Ko 2 wks su mama basuyi da tafiya ba, wani yammaci tana kwance bayan idar da sallar asr dan bacci ya kwasheta duk da tasan babu kyau baccin bayan laasar amma wannan ya shamceta.




Acan gate din gidan kuma jafar ne yaxo shi da matarsa. Saukarsu kenan Abuja ya taho gidan Mimi yabi kwatancen da Faty tai masa, kuma Baffa ne ya dunga jaddada masa inyaje ya tabbatar ya leqa gidanta ya qara duba jikinta. Semina ce ta kawoshi wanda aka turoshi daga gurin aiki ta kwana uku, ya yanke shawarar ya fara xuwa su gaisa da Mimi kana su xarce hotel suyi masauki dan inya fara aiki bexama lallai ya sami sukunin xuwa ba.




Dakyar me gadi ya bari ya shiga da motarsa cikin gidan domin saida yasha tambayoyi iri iri harda tambayar alaqarsu da Mimi din. Jafar ya qulu sosai, ga gajiyar da suka kwaso ga iskancin me gadi, shi inbadan Baffa ya tilasa masa ba mexai kawoshi gidan Bature? Dan tunda ya koma yaga ya dauke mimi yaji ya tsaneshi wato ya kawota da lalura ya ajiye sai data warke ya koma ya dauketa. Kamar yadda Anty ta fada masa. Shi kuma me gadi yana kan aikinsa ne dan har yanxu bai manta masifar Anty mami ba.



Ransa ya qara baci sosai da yaga sunfi rabin awa securities din gidan na musu tambayoyi kafin a barsu su shiga falon baqi. Gashi sai kiran Mimi yake a waya bata dauka ba, wato itama ganin ta samu duniya canja hali ko? Ya raya a xuciyarsa. Matarsa maryam sai mita take "kaima kaxo mu tafi, mun debo gajiya munxo sai titsiyemu ake da tambayoyi kamar xamuga shugaban qasa ita kuma yar rainin hankali taqi daga waya" ya sauke fushinsa a kanta yace "kimun shiru ko ranki ya baci, ina ruwanki, ba yar uwata bace?" ta murguda baki tace "tsohuwar baxawararka dai"




Tsuguno bata qareba, saiga Baqo yaxo yana ce musu me sukaxoyi gurin madam kuma ya suke da ita? Indai tasan da xuwansu suyi mata waya ta bada umarnin a kaisu falonta. Jafar yacigaba da kiran Mimi amma bata dauka. Ya kalli Baqo cikin bacin rai yace "in kana iya xuwa inda take kaje kace mata jafar Buhari ne yaxo" ya fita jim kadan ya dawo yace "bacci take, kuma in madam na bacci ba a tashinta" dan takaici bece komai ba. Aka kawo musu ruwa da lemo sunanan xaune duk motsin da sukai idon securities akansu kamar masu gadin barayi.


Can Baqo ya kuma komawa yace da Aisha taje taga ko Mimi ta tashi dan yaga alamun baqin daga nesa suke. Taje tace masa ta tashi wanka take ma. 10 minutes a tsakani ta fito ta zauna a falo tayi kwalliya me burgewa cikin doguwar rigar material wanda mama ta kawo mata. Ta kashe dauri da dankwalin kamar ba mai ciki ba tana tauna cingam. Baqo ya koma yace da jafar ta fito wa kace sunanka?" ya maimaita masa sunansa.




Babu jimawa saiga Baqo sun taho da Mimi dan bata yarda cewa jafar kunnanta yaji Baqo yace ba. Suka hada ido, taje da sauri ta tsuguna gabansa kamar xata shige jikinsa tace "ya jafar da gaske kaine?" ya fada mata yadda sukasha wuya kafin su ganta, ta kira securities din tana musu fadan a daina yiwa wadanda sukaxo gurinta walaqanci. Suka dunga neman afuwarta.



Ta jasu falonta, daga jafar har maryam matarsa sai da suka tsaya qauyancin ganin wannan aljannar duniya maryam a xuciyarta tace "a dole kiyi wulaqanci yarinya, ai koni nasamu wannan daular sai abunda yafi haka" ta xauna suka gaisa aka cika gabansu da kayan taryar baqi, suka fara hira ya fada mata abunda sukaxo yi. Yace "na kiraki a waya baki daga ba ai" sai yanxu ta tuna tasa wayar Silent tace "wlh na Sata silent na kwanta i m sry" yace"babu damuwa" ta kira landline tace a kawo mata wayarta, Aisha ta shigo ta miqo mata wayar. Maryam a xuciyarta tace "Tab yarinya Allah ya baki duniya kina daga zaune komai ai miki."



Sunanan xaune suna hirarsu Bature ya dawo aiki, kamar yadda ya saba ya shigo yana waqa, Sam bai lura da mutanen dake gurinba idonsa Mimi kawai ya hango masa. Ya taho gurinta yana waqa, yayin da su jafar suke daga bayansa, wato Mimi saitin qofa ta kallah shiyasa yana xuwa ita ya fara gani ya bude hannusa yana cewa "hlo my african queen" ya tsuguna gabanta tana kan kujera ya dafa gwiwarta, ta danji kunya tace "bakai sallama ba" ya lakace mata hanci yace "nayi kene bakiji ba, bakixo kin taroni ba kin rungumeni" ta dunga qifta ido tanason nuna masa da baqi fa a dakin amma ina bai ganeba saima cewa yayi "ki dainamun wannan farin nan, kixo muje ciki kimun in biyaki. Ya sumbaci goshinta,lips, dinta sannan ya sumbaci cikinta daga baya ya rungumeta. Su jafar na zaune a daskare suna kallon luv.




Tana tureshi daga jikinta ta rada masa "akwai fa mutane a falon" ya dago yakai dubansa bayansa, suka hada ido dasu jafar. Kunya ta kamashi ya dan sosa kai yace "jafar kune a garin namu yau?" jafar ya danyi yaqe yace "wlh kuwa aiki ne yadan kawomu Abuja na kwana uku shine na biyo duba maryam, yanxu xamu wuce masauki" yace "kai amma kun kyauta" yaje sukayi musabiha aka kuma gaisawa sosai da tuntubar juna. Bature yace "ai nanne masaukinku, ina xakuje bayan ga nan din. Duk girman gidannan ace kun fita hotel" jafar yace "a a wlh ai kuwa dai baxan sauka gidan qanwata ba da girmana" Bature ya dubeshi yace "au maryam kake kallo a matsayin yar uwarka? Ni bareni a cikinku? Hakan yayi, nagode sosai" jikin jafar yayi sanyi, yace "kayi haquri sulaiman ba nufina kenan ba." haka ya dunga bashi haquri Mimi tasa baki. Yace "is Ok, taso muje mu dakko kayanku" dole jafar ya tashi sukaje mota ya bude aka fito da kwatinsu. Bature da kansa ya dakko ya shigo da ita. Maryam din jafar kuwa kwanciya tayi bisa kujera, hakan yayi mata dadi xataso kwana a wannan aljannar duniyar dan tasan mijinta bashi da kudin da xai kama hotel din da xai kama koda kafar wannan gidan.



Suka sake xaman hira anan falon, ya tashi yaje kitchen yayi blending fruit ya xubo a cup. Sai da yasha ya rage ya miqawa Mimi ragowar ta shanye. Kiran sallah ya data su, maxan sukai masallaci Mimi ta ja maryam dakinta sukai sallah. Ta dunga kallon makeken bed room din, yayi girman wani gidan wai duk bed room ne, tab Mimi ta samu duniya. Bayan idarwa Mimi da kanta taje ta gyara musu daya dakin tasa sabon bed sheet ta fesa maganin saura ta kai musu duk abun buqata irinsu masubulun wanka, maclean da sauransu. Ta ja maryam suka koma bedroom din ta sake wanka, maryam kallonta take, yanxu bayan wannan wankan har wani aka sake? Tab ita wanka daya take. Taga Mimi ta kuma chada kwalliya cikin bubu din atamfa. Bayan dawowarsu masallaci kowanne ya shige dakin matarsa. Jafar yayi wanka ganin haka itama maryam tayi dan kar ace mata qazama.



Har daki Mimi taje ta kirasu xasuyi dinner. Suka hadu jafar idonsa akan Bature da Mimi yana ganin wata irin salon soyayya me ban mamaki da shaawa. Ya raya cewa da tuni shi Mimi kewa wannan kulawar. Bature ya tashi ya xuba musu abinci da kowa a plate dinsa kana ya xauna, ya dauki plate din Mimi yaci cokali daya sannan ya tura mata gabanta yace "Bisimillah Mimi luv" tace "to ya Bature" suna cin abinci cikin nishadi ana hira jefi jefi. Mimi ta janyo kwanan da aka gasa nama ta bude, yayi saurin karbarta ya tashi ya sakawa kowa a gabansa. Maryam din ya jafar a ranta tace "tabdi bata girki kuma xubawar ma sai anyi mata? Inama nice" cikin san nuna ita watace ta kalli naman da Bature ya ajiye mata gabanta, azatonta kaza ce ta yatsuna fiska tace "ni banacin naman kaxa" jafar kunya ta kamashi dan yasan qarya take. Mimi kuma ta yarda da abunda tace, dan tasan mutum iri iri ne kowa da yadda Allah ya halicceshi, tace "ayya sry Anty maryam ko in gasa miki red meat? Wannan ma ba kaxa bace, ba a cin naman kaxa a gidannan. Talo -talo ne." Bature yace "a a Mimi luv, cewa xakiyi tunda kikai ciki kika daina cin kaxa sai talo talo." dajin ance talo talo ne tahau yaga tanaci dan tasha ji ana cewa wanda ya saba cin naman talo talo baya iya cin kaxa sabida dadinsa.




A daren Mimi ta kwaba funkaso dan tasan shine favourite din jafar, ta hada miyar taushe ta dafa fari Sol din naman kan Sรก ta rufe.




Da sassafe yana kan gym ita kuma tana kitchen tana suyar funkaso, harya gama motsa jikin yaxo ya tayata aikin. Sai wajen tara suka gama komai ta bar Aisha ta shirya table ita kuma taje tai wanka. Goma sun gama komai har maxan sun fita aiki, ita da Anty maryam kuma kamar yadda take kiranta sunata hira tana janta duk gurin da xata a gidan tana nuna mata. Itama maryam ta saki jiki da Mimi suna hira duk da rabin hirar tata qaryace dan a tunaninta gara ta hada da qarya kar Mimi ta rainata, batasan ita ba haka take ba.



Yauma kamar jiya, sun hadu falo da yamma bayan dawowarsu office. Jafar yana ganin wata extra ordinary caring da Bature kewa Mimi, inxata xauna saiya miqe ta zauna sannan shima ya zauna kamar wani yaranta, in abinci xataci saiya faraci kamar mai tsoron kartaci guba kuma in ruwa xatasha saiya tsiyayo mata, duk maganarsa daya sai yace "Mimi luv"


Yauma suna zaune kan dinning Mimi da kanta tayi jellof rice wacce tasha baqin kifi busashshe tayi shar sun cinye abinci tas dan yayi dadi sosai.



Wajen 8:23 pm Farida ta shigo gidan tasha kwalliya sosai, da ritsetsen cikinta. Ta dubi Mimi tada taso ta dosota kana takai kallonta kan maryam matar jafar. Taci kwalliya da tufa me tsadar gaske ta xuba golds hannu da wuya a wannan daren kamar mai zuwa competition. Amma kash! Kwalliyar daban ita daban dan Sam bata iya kwalkiyar ba dagani bata da wayewa. Farida tai qasa da murya tace "money miss road" Mimi ta tsunkuleta ta nuna mata jafar da ido tace "matarsa ce" sai a lokacin taga jafar suka gaisa. Ta kalli Mimi tace "besty ya baki shirya ba? Cinema fa xamuje kallon wannan film din" Mimi ta dafa goshi tace "kash namanta bari in sake kaya" ta wuce daki Farida ta xauna kan kujera tana kallon maryam din jafar a sace tana dariya. Anata bangaren maryam tayi wannan kwalliyar ne dan nunawa Mimi itama fa tana da kayan qarya dan bata taba xuwa Abuja ba, daji ance xa a je ta kwaso kayan qasan akwati da nufin axo Abuja ai fafa dasu, sai akai sa a kayanta ya tsinke bakin kaba taxo gidan yan gayu dan haka ta fito da tanadi ta fara bawa Mimi mamaki a ganinta๐Ÿคฃ



Ishaq ya shigo yace da Farida "dabaki tsayani ba gashi duk saurinki na taddaki" tace "wlh kuwa ya ishaq Mimi wai ta manta" Bature ya kalli jafar yace "koxo muje cinema kallon wani nollywood film kuma da jaruman film din shiyasa su Farida ke rawar kan zuwa sunason ganin jaruma jackie appiea" jafar yace a ransa lallai Bature ka cika shedani anbaka yarinya me tarbiyya amma har Cinema ka koya mata xuwa" a fili kuma yace "ba damuwa maryam tashi muje" Farida kamar tace da wannan shigar xaki cinema din, sai kuma tai shiru.


Mimi ta fito cikin shiga english gown me taushi amrless ta dora boy friend jacket akai ta samu qaramin gyale tayi vieling fuskarta babu kwalliya sai powder da man lebe tayi kyau sosai. Suka kama hanya.




Daga wajen cinema suka tsaya suka sayi pop corn, Mimi taje gurin kayan sanyi ta dauki qaton roban ice cream tace da Farida kawo kudi ban fito da jaka ba, farida tace nima haka, amma ina zuwa. Taje gurin su ishaq dake tsaye ta xare masa willet dinsa be sani ba, sukaje suka biya kudin, sai gasu kowacce na tura ciki da robar ice cream. Farida ta miqawa ishaq willet dinsa. Yace "yaushe kika dauka bansani ba?" Bature ya dubi Mimi ta robar ice cream din yawunta har ya soma tsinkewa so take su shiga kawai tasha yace "wa ya sai muku? Ban hanaku shan sanyi ba?" ishaq yace "kyalesu shammatata sukai suka xaremun willet.



Sun nutsu a kallon film din kuma yayi kyau sosai, Mimi dai tunda ta cika cikinta da ice cream tai bacci a kafadarsa, koda aka tashi sai dakkota yayi yasata a mota da sukaje gidama haka ya dau barsa har dakinsu. Jafar kallonsu yake cike da burgewa.



A yan kwanakin da sukayi da su ya fuskanci qaryane ace Bature baisan Mimi, domin wannan kulawar da sukewa juna ta wuce misali. Farko ya dauka ganinsune yasa Bature yiwa Mimi irin haka amma daga baya saiya lura haka suka gina rayuwar aurensu, sonta yake tattalinta yake kamar ya maidata ciki ga kuma girmamata da yakeyi. Wani dare sun zauna zasuci abinci Mimi ta miqe tsam ta koma bisa carpet ta fara kukan shagwaba, ya miqe yace dasu, kuci abincinku ni yau Mimi rigimar ta motsa, ai kuwa abinciin da baiciba kenan ta dunga kuka tana burgima tsakanin qafarsa wai cikin yana mata motsi ya danne mata. Ya dunga lallabata har tai bacci ya kaita daki.



Har kwanakin aikinsu ya qare amma suka hanasu tafiya, wai sai week end ya koyi abubuwa da yawa a xamansu, wanda inka riqesu xaka xauna da matarka lfy duk tsaurinta. Kuma yayi aniyar gyara rayuwar aurensa in shaa Allah. Anata bangaren Mimi taja maryam ajiki ta dan koya mata tsaftar jiki wacce ta fuskanci tana da rauninta. Randa zasu tafi Mimi ta bata lace da mayafi sai fashion din yari da sarqa, shi kuma ya jafar ta dakko masa wani filtek a cikin kayan Bature wanda bai dinka ba, koda taje dauka tace in dauki wannan ya Bature? Yace dauki maryam dan nasan kyautarwa xaki Allah ya hadamu a ladan. Tace nagode yace "nima nagode da koyar dani da kikayi cewa mutum koda mawadacine in ammasa ihsani yana jin dadi" sun rabu cikin kewar juna. Jafar ya yadda soyayya ce me qarfi tsakaninsu babu xancen yaudara.



Passing out dinsu na gama service lokaci yayi ana gobe xa ai suka tafi kano a motocin data saiwa su mama, ita da Bature a guda daya driver ya Biyosu da dayar suka tafi tare.



Washegari da safe sukaje state sect P O P din, yana xaune yana jiranta suka gama ta amshi cert dinta na NYSC sukayi pics din tarihi da qawayenta aka rabu. Tana shigowa motar yace "BARRISTER MARYAM AL AMIN congrat" ta farareshi tace "kawai dai kace kanason fadar sunan Babana amma inba haka ba kace congrat din mana kawai" ya sheqe da dariya yana mamakin daru irin nata yace "sry ranki ya dade, na gyara congrat Maryam"



Basuje ko inaba tunda jiya sukaxo, da yamma suka shirya suka dau motacin iri daya sak ita daya shi daya. Gidan Faty suka fara xuwa, bayan murna da kewar juna da mamakin girman cikin Mimi da Faty tayi suka rabu ta rako su gate. Mimi ta shiga Mota ta debo takaddun motar ta ciro key din ta bawa Faty tace "gashi takice na saya miki" Faty ta daskare ta kasa magana sai bin Mimi take da ido har suka tafi batace komai ba.



A gidan mama ma bayan murna aka gaisa, mama tace "sakko daga tudunnan in matsa miki qafar ta fara kumbura. Mimi tace "kafin nan xo muje kiga" sukaje qofar gida ta dakko takaddu da key ta bawa mama tace gashi mama asa albarka mota na sai miki. Mama sai hawayen farin ciki, suna tsaye saiga Faty a tata motar taxo nunawa mama dan abun baxai fadu a waya ba. Ta tarar da wata mamakin. Suka hadu suka dunga kuka sunawa Mimi adduar alheri, sulaiman na gefe na dubansu yana mamakinsu kamar su cinye juna. Baffa ya fito yaga motocin yace "tofa aiki game qareka, fadima haihuwa ta miki rana Allah ya sa albarka yasa a kashe lfy" matan gidan kuwa kamar wadanda suka gamo haka suka burkice basu wani boye baqin cikinsu ba. Mimi ta nuna musu cert dinta na NYSC tace "mama i m now a Barrister maryam, na cika burinki ko?" mama ta rungumesu duk tace "kun cika burin mahaifinku da ace yana raye da bansan irin farin cikin da xaiyi ba" Bature sun burgeshi har vedio yayi musu.



Washegari suka koma Abuja sabida aikinsa



Farida ta haihu, yayin da Mimi cikinta ke 7 months daga asibitin aka wuce da ita gidansu dake Abuja, wanda Umman ta taxo ta xauna da ita.


Mimi ta sameta gidansu ita da Bature, bayan gaisawa da yiwa juna barka Umma ta basu guri, Mimi kallon Farida take a tsorace ganin yadda ta rame a lokaci daya duk idonta ya xurma. Ta karbi Baby girl ce ta miqawa Bature ta koma ta xauna tace da Farida "Farida haihuwa da wahala ko? Naga duk kin rame" Farida tace "Tab, ai wahalar ma baxata fadu ba, nifa inaga mutuwa nayi na dawo. Wai a hakanma dan ya ishaq ya temaka mun dan yana tsaye kaina harna haihu. Kuma wlh ina dawowa hayyacina ke na tuna" Mimi ta dafe qirji tace "na shiga uku" ishaq ya harari Farida yace "ke ya isa haka, Mimi wasa take miki kowa da irin tasa haihuwar wani baya wahala"


Tundaga ranar Mimi can take yini, Kullum inxai tafi office yake kaita in ya dawo ya biya su taho tare. Ishaq ma can ya tare kwanciyar bacci ke dawo dashi nasa gidan. Ranar suna yarinya taci sunan Umman ishaq Hawwa amma suna ce mata Jidda.


Mrs Hajia ๐Ÿ˜Š
[9/30, 1:05 PM] โ€ช+234 706 296 6299โ€ฌ: ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐ŸผAL 'AMARIN MARYAM ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ


Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)


๐Ÿ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 6โƒฃ5โƒฃ


Dedicated to
ANTY SIS,
MARYAM BAITA &
NAJA'ATU NAFI'U (yar malam

LAST PAGE


Farida nayin 40 dayz Umma ta tarkatota ta dawo da ita dan tace tagaji da xaryar ishaq, itama ta tafi kano nata gidan.



Mimi ancigaba da rainon ciki, tafi duhu sosai irin na masu ciki wuyanta yayi baqiqirin ta kumbura kamar xata fashe. Mijin Kullum cikin lallaminta yake dan ta tsorata da haihuwa tunda farida ta bata lbri.


Ta fito daga wanka ta xauna gefen gado, yana kwance akan gadon, ta dan bigi qafarsa tace "ya Bature aramun t shirt dinka insaka da zani banasan saka gown xafi nakeji." ya tashi ya bude drawer ya dakko mata wata qatuwar t shirt dinsa yana cewa "sannu Mimi luv kin kusa in shaa Allah" ta saka rigar taxo mata har gwiwa. Tace "shikenan ma na huta daura xani" ta bashi dariya, amma baiyi a fili ba sai a ciki, baisan ta jishi ta hade rai tace "ai dole kaimun dariya tunda na gama yimaka amfani ka maidani haka" yayi rau rau, baiji dadin maganar ba, ya rasa abunda yasa Mimi ta xama haka abun kadan sai fada, yace "haba maryam, nasan ba haka na aureki ba nine silar komawarki haka kuma in shaa Allah kin kusa haihuwa kiyi haquri my luv" ta dan samu sauqi jin kalamansa. Ganin tana gumi ya qure AC amma duk da haka zuffa take. Yaje ya kira yadukko taxo taga yadda Mimi ke nishi da gumi. Tana xuwa tace "sulaiman wannan yarinyar naquda take ku tafi asibiti." tace "maryam kina jin ciwo?" tace "eh tun jiya amma ba sosai ba. Mamace tace in dunga daurewa" yaje ya dakko akwatin da suka dade da hadawa ya tattagi Mimi suka tafi. Sun sami ishaq yasa aka dubata nurse din tace tabbas labour take amma yanxu tana 1 stage da ragowa sosai. Haka aka kwana tun ciwo na qarami har ta fara jigata sosai.



Da sha biyun rana tayi washegari wanda Mimi tayi 24 kenan tana abu daya ya Taheer ya buga ya sanar da mumy dan tun akan rashin lfyar Mimi yayiwa kansa alqawari baxai qara dakata Bature ba a boye AL 'AMARIN MARYAM.



Bature kam baya cikin hayyacinsa kai kace shi yake labour din, sai shige da fice yake a dakin xuwa office din ishaq.



Dab da magrib saiga su mumy ita da mama da ya Faty, sukaxo da rubutu tsibi tsibi wanda aka karbowa Mimi a gurin malamai daban daban na naquda. Lokacin Mimi ta gama fita hayyacinta, aka dunga durawa Mimi rubutun. Bature kawai aka bari ya shiga dakin, su kuma suna tsaye a qofar cirko cirko daga ciki suna jiyo nishin Mimi. Ya fito yanawa su mumy bayanin har yanxu da ragowa amma xuwa 8 din dare inbata haihu ba xa ai mata CS. Nurse ta leqo tace yaxo, ya tafi Faty tabi bayansa amma ta hanata shiga, ta

Please Login or Register in order to submit comment