Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace ita ba shinkafa bace dazaita sasuqarta.



Dawo da MARYAM xaiyi domin ya fara gane kuskurensa na saurin rabuwa da ita. Saboda haka xai dawo da ita ta zabe masa ruwan kashe shaawarsa a duk sanda ya buqata. Ita kuma Nafee yaci gaba da ajiyeta a matsayin matar so ya kuma ci gaba da haquri da halinta domin har yanxu yana sonta, dan San tsakani da Allah ya ke mata itace dai ta rufeshi. Dan haka ko gida daya bazai hadata da Nafee ba kartaga irin abunda Nafee take masa itama tace xatayi, wani gidan zai kama mata haya anan kusa da Nafee.



Yana kaiwa nan a tunaninsa wani farin ciki ya shigeshi, πŸ˜„ harya fara hangosu shi da MARYAM cikin yanayin auratayya. Yasan xuwa yanxu ta nemi maganin ciwonta na sanyi, sannan kuma gata da qaramin ciki yasan xai shana kwarai dan MARYAM yar baiwa ce ko babu ciki bare da ciki. Sai yanxu yaji yana son cikin jikinta kuma yanason ganinta da cikin yasan cikin zaiyi mutuqar kyau ajikinta dan komai nata me kyau ne (Dan rainin sense 😏) da wannan tunani bacci ya daukeshi cike da mafarkin MARYAM wanda ya kaishi ga wanka.



Ganin kansa a jiqe yasa Nafee fallara masa harara, tace ina ruwan dan anace mafarki kai kenan? Bai kulata ba saboda bayason ta bata masa mood, dan daga masallacin asuba gidansu zai tafi gurin Abbansa suje bikon MARYAM.



Mrs 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 3⃣2⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Bakwai saura kwata (6:45 AM) a gidansu tai masa. Yasha shadda fara sol yar ciki da babbar riga, ya dankwafa hula kamar kansilan qauye. 🀣



Har cikin dakin Abbansu ya shiga, ya samu Umma tana hadawa Abban shayi. Ya tsuguna har qasa ya gaishesu, Abba ya gama shirinsa tsaf da alama fita xaiyi.



Badaru ya qara sunkuyar dakai cikin sigar neman alfarma yace "Abba dama nazone dan Allah muje mu dawo da MARYAM, Na janye sakin da nayi mata. Naga gara ta dawo mucigaba da xama ta haihu a dakinta, na huce da fushin da nake da ita." Umma ta ware ido tace 😳 au dama MARYAM din ciki gareta amma ka saketa? Kuma shine baka taba fada ba? Wannan yaro ka jawo mana abun kunya wlh, ai da munsan da ciki da mun dunga xuwa dubata." yayi dan murmushin alamun samun nasara yace "Umma kuyi haquri lokacin rainane a bace shiyasa ban fada muku ba." tace " eh ai yayi kyau hakan, yaro yarone, yaro bakasan wuta ba saika taka. Yanxu kuma da xaka dawo da ita ka manta da xagin naka da kace tanayi? Ka sheqa kaji babu kwaya kenan.Hmmm to wlh bakayi
daya ba kaji dadi duk randa ka kuma sakin wata mace bama MARYAM ba daga ranar ka canja uwa domin ni bazan xama uwar mai auri saki ba"



Abba yayi gyaran murya yace "tunda dai yayi kuskure kuma ya gane kuskurensa shikenan, kuma itama MARYAM din nasan yanxu tayi nadamar abubuwan da tayi masa. Yanxu xanje Dawaki daurin aure amma in shaa Allahu bazan kai sallar juma a acan ba. Yanxu xanje insamu kawunka in fada masa, inyaso ina dawowa daga masallaci sai mu wuce dashi muje gidansu MARYAM din."



Badaru ya dunga murmushin farin ciki, sai yakeji a ransa kamar ta dawo ta gama. Dan haka yace "Abba inaga gobe kawai su dawo da ita, yanxu xanje inga inda xata zauna acan gurin Nafee kafin in samar mata gida" Abban yace to hakan yayi, bari intashi kar inyi rana.



Bayan komawarsa gida, yana kashingide yana tunanin maryam har wani lumshe ido yake inya tuno sweet moment dinsu. Ya gama tsara cewa dakinsa da yake ciki zai bawa maryam din kafin ya samu gida ya sai mata, bazai qara sakinta ba zai zauna da ita saboda buqatarsa.



Yana cikin tunanin ne Nafee tazo ta dangwarar masa da baqin shayi (lipton) da breadi. Tace gashinan babu madarar.Bai ce mata komai ba, sai dariya da yake mata a xuciyarsa. Tanai masa kallon biri yana mata kallon ayaba, domin bazai fada mata xai dawo da maryam ba sai dai taganta. Ya qudure suna dawowa daga gidansu Maryam din zaije yayo mata shoping na komai da komai ita kadai, Nafee kuwa taji a salansa, dan yagaji da barnar da Nafee keyi masa.



Kamar yadda Abban Badaru ya alqawaranta tare sukayi sallah da Baffa a masallacin jumaar gidan sarki, kuma daganan yabi Baffa gida yace suje zasuyi magana me hamimmanci. Baffa dajin haka yasan maganar Komece farinciki ya cika zuciyarsa. Abba tare da qaninsa da Baffa sukaci abinci tare a gidan Baffa. Kuma dama ga al adar Baffa ranar juma a daga sallar juma a gida yake tahowa baya komawa kasuwa.



Suna gama cin abinci suka labartawa Baffa maqasudin xuwansu da kuma saqon Badaru na amaida maryam din gobe (kunji fa kamar wata yarsa) harda labarin cikin Mimi sai da suka fadawa Baffa. Babu wani nuna ja ko tauna tsakuwa dan aya taji tsoro ko kuma tsawatarwa dan kar Badaru ya kuma yin saki anan gaba Baffa ya yadda da komen maryam gidansa (dan Allah ku duba inda ake wulaqanta ya mace. Ba dole namiji yayiwa mace wulaqanci ba dan yasan inma ya saketa bazai sha estalar dawo da ita ba) suka sha hirarsu cikin nishadi ya basu tabbacin gobe ana magriba A dar uma yaxo ya dau maryam su tafi.



Suna tafiya Baffa ya shiga gida, a lokacin qarfe uku na yamma. Tunda tsakar gida ya dunga kwallawa mama da Mimi kira, har ya bude parlourn SΓ‘ ya shiga bai fasa kiransu ba. Mama ta fito ta bishi dakinsa, yace jeki ki rawomun maryam yana fara a. Taje ta taso Mimi take bacci, Umma da Anty jin kiran da Baffa kewa Mimi yasa suka fito suka shiga dakin Baffa kamar an gayyacesu. Dan Susan tunda ya kira Mimi watace ta taso dan inba haka ba sai yayi sati bai kirata ba. Ya jafar ma yanxu ya shigo gidan xuwansa kenan daga kaduna yazo weekend kuma yana xuwane saboda Mimi, jin kiran da Baffa yake mata yasa ya tsaya daga gefen kitchen kusa da dakin Baffa dan yaji dalilin kiran, babu wanda ya lura da xuwansa.



Baffa ya kallesu, Umma, mama, Anty sai kuma Mimi dake gefe daya. Ya fadada faraarsa tare da cewa "ALHAMDULILLAHI, Allah ya sani tunda abunnan ya faru nake adduar Allah ya sa a daidaita, to Allah maji roqon bawa yanxu Alh Inuwa da qaninsa suka xomun da xancen mayar da auren maryam da Badaru. Domin shi Badarun da kansa yau yace ya janye sakin ta koma dakinta. Dan haka maryam sai ki hada kayanki gobe zaizo da almuru ya daukeki, basai nace miki komai ba in aurenki ya kuma mutuwa karki dawomun gida"



Mimi ta kwalolo πŸ‘€, jin abunda Baffa yace wai Badaru ya maida ita. Ta juya ta kalli da nufin mama tayi magana, domin ita bazata iya cewa da Baffa ta gama iddah ba.



Ai kuwa mama ta magantu "Alh wani irin kome kuma? Ai aure ya qare, tunda yau kwanan Mimi 6 da gama iddar Badaru."



Baffa ya dakawa mama tsawa tare da cewa "Faduma karki kawomun zancen banxa mana, yarinya da akace tana da ciki itace xakice ta gama idda?"


Mama ta hade rai cikin shirin ko ta kwana😑. Umma tai saurin sa musu baki a maganar da cewa "a ciki kuwa akwaishi dan ko mu munsan dashi, sai dai in Faty ce ta jagoranci " maganar ta katse a dalilin hararar da mama ta watsa mata. Abun ya bata mamaki domin ko da wasa mama bata taba harararta ba, dan haka yau da taga fadiman na shirin canjawa taja bakinta ta tsuke saboda kar girmanta ya xube.



Baffa shima ganin mama tayi fuskar shanu tana hararar Umma yasa ya bar maganar ciki. Yace "to shikenan ai duk da haka akwai mafita bara in kirawo Alh inuwan suxo da daddare a daura aure ya wuce da matarsa"



Mimi da mama suka kalli juna a razane. Mimi ta dago kanta cikin dakiya tace "Baffa karka kirawoshi, nikam nagama auren Badaru in shaa Allah, Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi"



Baffa ya taso mata cikin hargowa yace "ke ki kiyayeni kuma aure dole ki koma, kina zaton akwai wanda zai aureki inyaji abunda kika shukawa tsohon mijinki ya sakeki a wata 5? Kinsa ana zagina a gari kamar ni ace inada bazawara a gidana? Kin batamun record din gida. Saboda haka dole ki koma gidansa ayau basai gobe ba"



Ba tare da wani shayi ba ko shakka, domin xuciyarta ta gama bushewa. Ta dago kanta tace "Baffa bazan koma ba wlh, saboda ni kadai nasan irin wahalar da nasha a gidansa"



Baffa ya dauketa da wasu irin maruka guda 2, tare da cewa "ni xance kiyi abu maryam kice baxakiyi ba? Lallai na yadda Badaru yayi haqurin zama dake. Kuma wlh sai an mayar da aurenki ayau, inyaso ni dake aga wanda ya haifi wani"



Idonta jajur saboda zafin marin da Baffa yayi mata, ta kuma dagowa ta kalleshi tace "wallhil azeem bazan koma gidan Badaru ba, da inkoma aurensa gara inshiga duniya."


Umma da Anty dake gefe suna kallo tun abun na burgesu har ya koma basu tsoro, suka kwalalo ido dan yau Mimi ta shayar dasu mamaki.


Baffa kuwa baiyi wata wata ba ya tashi yasa hannu ya rufe mimin da duka kota ina. Nan take kuwa jini ya fara fita ta hancinta wato habo. Mama ganin jini na xuba a hancin Mimi ta runtse ido, xuciyarta na tafasa tana kai kawo. Mimi kuwa duk dukan da Baffa ke mata bata fasa fadar "wlh ko kasheni xa ai bazan koma gidansa ba" Baffa yaje ya ciro wayar receiver ya nufi Mimi da niyyar sake dukanta dan yagaji da dukanta da hannu, yana cewa "to ayau kuwa xaki barmun gidana bayan na gama fasa miki duk jikinki da duka dan ban haifi dan da zai fada in fada ba"


Mama tai saurin tashi tasha gabansa (ta shiga tsakaninsa da Mimi) tare da cewa Alh Buhari karka qara dukarmun ya, domin baka tayani naqudar kawota duniya ba. Haka kawai kasa marainiyar Allah a gaba sai jibga kakeyi kamar kana dukan namiji dan uwanka. Ai ko musulunci bai baka dama kai mata auren dole ba a matsayinta na bazawara"



Umma da Anty dake gefe abun ya basu mamaki kwarai, Anty ta kasa haquri ta miqe tare da cewa "amma kam kedai fadima baki da kunya baki da kara, yanxu sunan mijin naki kike ambata tare da yi masa tsawar ya daina dukar miki ya? Ai ab" kafin ta qarasa abunda tai niyyar fada mama ta dauketa da mari, tare da nunata "πŸ‘‰πŸΌ ke! Na kasa dake balle ki dauka? Da wanda ya ajiyeki nakeyi" Anty da tasha mari ta dafe kunci tana kallon mama cikin kidima, Umma kuwa nan take ta kuma shiga taitaiyinta.


Mama ta maida kallonta ga Baffa da ke tsaye nayi mata kallon mamakin abunda takeyi taci gaba da cewa "ni har a fadamun kara akan yayana? Nagaji nagaji da abunda kake jagorantar matanka kukemun haqurina ya qare. Kuma yau na tabbatar da AL AMIN baya duniya, domin da yana raye da ko cikin shege maryam tayi zai karba ya rufa mata asiri. Duk cikin yayanka wa kayiwa auren dole? Sai yata, saboda qasa ta rufe idanun ubanta ko? Nagaji da abunda kakemun nagaji da wariya akan yayana, ai koda ace ba yayan dan uwanka bane kayimun kara. A karatu ka fifita yayanka akan nawa, a wajen tarbiya da nuna soyayya ka fifita naka akan nawa, a wajen aurar da yayama salon auren yayanka daban da nawa, sannan ka debi yayanka ka dunga kaisu saudia kabar nawa, to shin ubansu bashi da gado a dukiyar da kake facaka da itane ko kuma sudin shegu ne? Duk abubuwan da kakeyi ina sane kuma ina ganewa domin ni ba mahaukaciya bace kamar yadda kuke xata. Sannan akan wani banxa Badaru ka mayarmun da ya baiwa me aikin gidanka, sannan kuma yanxu kana nema kasa yata ta shiga duniya saboda Badaru? Shin wai maryam yar dan uwanka ko Badaru? To tunda kana qaunar Badaru ka dauki daya daga cikin yayanka ka aura masa. Tunda anyi ruwa qofar dakin kowa ta jiqe (ma ana kowa yana da yaya) duk cikin yayanka wacece take maka biyayyar da Mimi take maka? Amma duk da haka kafi tsanarta kafi wulaqantata bansan abunda ta tsare maka da kai da yayanka da matanka ba kun tsangwamarmun ya kun takurata, to wlh duk wanda ya qaramun abunda bai gamsheni ba akan yayana sai yaga tashin hankali. Ko kasan cewa akan takurar da kaiwa Mimi har yunqurin kashe kanta tayi? To wlh Buhari duk randa maryam ta kashe kanta saboda takurar da kake mata wlh sai nayi sharia da kai daga nan har kotun duniya. Kamar yadda kasha fada kuma kake nunawa a aikace cewa Mimi ba yarka bace to yau na tabbatar maka cewa FATIMARYAM ba yayanka bane yayan AL AMIN da FADIMA ne. Saboda haka na yanta yayana daga barin yi maka bauta. Abu na qarshe dazan fada maka shine : kamar yadda kace Mimi tabar gidanka xata bari, amma ni da ita xamu barmaka gidan tare domin saboda su nake zaune a gidannan inkuma ankore su banga xaman da xanyi ba."


Ta juya ta kama hannun Mimi tare da cewa "taho maryamu daga yau na yanta ki" Baffa yayi sakato kamar an dasashi jikinsa yayi mugun sanyi wata irin kunya wacce bai taba zato akwaita ba yakeji. Ashe duk abunda yakewa fadima tana sane? Lallai ya dade yana zaluntar wannan baiwar Allah da yayanta, yau ta fada masa abunda bai taba tunani ba kuma shi kansa baisan hujjarsa ta nuna banbanci tsakanin yayansa da yayan dan uwansa Al amin ba. Lallai mai haquri bai iya fushi ba yau fadima ta zame musu horo, yasan tabbas abunda ta fada gaskiyace tsantsan duk yayansa babu mai masa biyayyar da Mimi keyi masa kuma babu wacce yayiwa auren wulaqanci irinta. Kuma wlh baisan abunda yasa yakewa Mimi haka ba, kuma yasan da Anty ko Umma yakewa yayansu abunda yakewa Mimi wlh da sai anyi yaqin duniya na uku. Muryarsa a tausashe yace da mama dake shirin fita daga parlourn "ban baki izinin fita daga gidannan ba daga ke har maryam" Umma da Anty suka kalleshi jin abunda yace suka jinjina kai. Domin sun dauka zai saki fadima ne nan take, da daya daga cikinsu ce da tuni ya sender ta gida.



Mama na fitowa daga dakin Baffa ta tsugunar da Mimi a bakin fanfo da nufin wanke mata jinin daya bata jikinta. Jafar da ya gamajin abunda ke wakana yayi saurin xuwa kitchen ya dakko mata ruwa a freezer ya miqa mata, ta karba ta wankewa Mimi fuska dashi. Nan take habon ya tsaya, taja hannun Mimi suka shige dakinta.


Jafar ya furta "jarumar uwa" ta jure abubuwa da yawa akan yayanta sannan lokaci daya ta kwatarwa Mimi yancinta. Ya dunga farin cikin jin Mimi ta gama iddah yace "in shaa Allah maryam matata ce"



Har magruba tayi mama bata fito ta dora girkin dare ba duk kuwa da cewa ita ke da girkin. Anty ta samu Baffa har daki yayi tagumi tanayi masa mitar cewa, mama bata dora girki ba mai zasu bawa yara suci? Ya dago ya kalleta yace "ku masu yaya bakuje kun girka kun basu ba sai ita me ya guda daya? Saboda haka karku dameni" Anty ta ruqe haba cikin ranta na jinjina soyayyar fadima a gurin Baffa, wato duk abunda tayi batai laifi ba kenan? Har marin da tayi mata 🀣. Ala tilas taje ta dora jellof din taliya dan lokaci ya qure kuma itace me qananan yaya.


Bayan ta gama ta hana kowa sai Baffa kawai ta xubawa ta kaima masa daki, shi kuma ya tambayeta da cewa kin kaiwa fadima? Ta harzuqa tace "aini bata shanye ni ba kamar yadda ta shanyeka ba, saboda haka ban kai mata ba dan ba xamanta nake ba. Ana cikin hakan Umma ta shigo tana tambayar Anty ina nata abincin? Tace nima dafawa nayi ni da yayana kema kije ki dafa dan ba baiwarku bace ni. Umma tace dakata karkiyimun fitsara inba haka ba yanxu in wanka miki mari dan naga sai anmareki kike samun nutsuwa πŸ˜‚. Anty da jin haka ta harzuqo suka fara cacar baki ita da Umma. Baffa ya katsesu da cewa ko suyi shiru su bashi guri ko kuma kowacce ta tafi gidansu. Anty ta cije lebe da cewa ai dole kace mu tafi gida, ita wacce ta qare maka zagi daxu ai ta kwana lfy saboda ta iya bun malamai.


Daya fita sallar isha ya biya ya siyowa mama da Mimi qatuwar kaza da fura roba biyu, jin cewa ba a basu abinci ba. (lallai mama ta motsa kwanji πŸ˜„) ya shigo Anty na alwala a tsakar gida kuma taga ledar daya shiga da ita dakin mama. Har ta miqe xata bishi sai ta tuna marin da tasha daxu dan haka ta koma ta xauna.


Yasameta xauna akan kujera ita da Dady suna kallon mbc 3 Mimi kuma tana kujera zaman mutum daya da digital casbaha a hannunta tana dannawa. Baice musu komaiba sai ajiye ledar da yayi kan qafar mama ya fita.


Dimin da taji shiya tabbatar mata abinci ya kawo musu, kuma dama shiri take ta tashi ta samar musu abunda xasuci. Dan yau jin ranta take sawai, abunda yake ranta shekara da shekaru yau ta amayar dashi. Dan haka ta dakko musu faranti da cups sukaci kazar suka sha fura suka qulle dakinsu suka kwanta, daga ita har Mimi basu garka ba sai asuba sun sami bacci me nauyi. (dole tunda anraba xuciya da damuwa)


Mrs
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 3⃣3⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)



Baffa kwana yayi yana tunani, haqiqa yayi kuskure yayiwa fadima abubuwa da yawa kuma babu wanda ya taba fada masa yayi ba daidaiba. Tabbas yaci amanar Al amin, yayansa kwaya biyu yakasa hadawa cikin nasa yayan ya rike. Kuma dole su Faty sunada gado a dukiyarsa domin tunda Al amin ya mutu ya tattara abunda yabari ya riqe, ko mama bai sallama ya bata tumunin takaba. Su bai basu dukiyarsu sun mora ba su baiyi masa da tasa ba. Dole zaisan abunyi akan dukiyarsu, ko bebawa su Faty tasu ba dole zai sallami mama da tumuninta.



Ta bangaren Mimi kuwa, baisan dalilin tsanar da yayi mata ba. Amma yasan akwai tagomashin matansa wadanda Kullum cikin kawo masa sukar Mimi suke. In yayi kallo xuwa hallayyar yarinya sai yaga yarinyace sassanya wacce ko acikin gida ake hira da wahala kaji harshenta, sai dai in anyi abun dariya tayi. Gata da kirki da qarfin xuciya, duk da bata cika lfy ba Kullum xaka sameta cikin aiki ko a tsakar gida ko a dakin uwarta. Bata da qashin cewar bazatai aiki ba saboda akwai yan aiki a gidan kamar yacce yayansa keyi. In kuma yanason ai masa abu misalin gyaran daki ko wani aiki to Mimi yake sakawa domin tana tsayawa ta yishi babu hainci wanda ko matansa basu iya yimasa shi tsaf kamar nata.


Dan haka ya fuskanci xuga ce jigon tsanar da yakewa Mimi, sai kuma issue din rashin aurenta da wuri wanda ya dauki hakan iya shege. Dole ya kawo canji domin yanason fadima kuma bazai iya rabuwa da itaba, yanxu gashi tana shirin rabuwa dashi saboda Mimi. Nan take yaji rabin tsanar da yakewa Mimi ta tafi. Afili ya furta Fadima nagode da kika karantar dani kuskurena da wuri tunkan in mutu Allah ya kamani da haqqin xumunta dana marayu. Kuma daga yau xan sakarwa yarki mara tayi irin rayuwar da take so.


Lokacin da yafito domin tafiya masallacin asuba ya kirawo masu aikin gidan yace su karbi aikinsu yau sannan ya fita.


Mimi kuwa bayan ta iddar da sallar asuba ta gaida mama, mama tace mata kije kiyi registration din tafiya service din yau. Mimi tayi rau rau tace " mama ai anrufe sun kusama tafiya camp domin har call up dinsu ta fito" mama tace to kiyi haquri haka Allah ya shirya kaje wata shekarar"
Anan kitchen din cikin parlour suka hada break fast sukaci, domin mama ta quduri aniyar kwatar yanci. Tunda ya hanata tafiya ai sai tayi yajin a dakinta.


Badaru yadda suka kwana da Nafee jiya yauma haka suka kwana, domin shima ya bar mata abunta yace ta jiqa tasha. Aransa kuwa cewa yake ni da xan kwana da maryam yau dan anhanani wannan ruwan daurayar ai ba wani abu bane.



Wajen qarfe goman safe yaje gidansu, dake asabar ce kuma basa fita kasuwa weekend da wuri duk ya samesu a parlour. Har Badamasi da yazo weekend.


Ya zauna ya kwashi gaisuwa gurin iyayensa, ya juya suka gaisa da Badamasi sama sama domin Badamasin yanxu yake samun lbrin saki da kuma maida maryam da Badaru yayi sannan da zancen auran da yayi. Dan haka yaji yayi mugun tsanar Badaru sabida maryam.


Badaru ya kalli Abbansu yace "Abba inaga da yamma xanje in dauko maryam din, saboda inason inkaita store tayi shoping din kayan abincinta da kanta inyaso sai mu wuce gida daga can"


Abban yace to babu laifi, bari na fadawa Alh Buharin saboda karkaje bata kimtsa ba" Umma dake gefe tana murmushi aranta taji dadi ga dukkan alamu Badaru ya gane mahimmancin maryam, dan haka tace "Alh ai da ya kira maryam din da kansa yace ta shirya da wuri zaizo da yamma"


Badaru ya sunkuyar da kai cikin kunyar abunda xai fada yace "ai bani da lambarta" babu wanda yace masa komai sai Badamasi dake watsa masa harara kamar ya tashi ya dakeshi.


Abba ya ciro wayarsa yace bari na fada masa da kaina. Lokacin da kiran Abba ya shigo Baffa na xaune yana karyawa Umma na gefensa ga dukkan alamu itace tayi girkin tunda mama tayi bore.


Ya daga suka gaisa, har yanxu jikin Baffa a sanyaye yake. Abba ya fada masa buqatar Badaru. Baffa yace "ai Alh inaga sai dai mu haqura domin yarinyar har ta gama iddah, kaga babu maganar kome kenan?"


Abba dajin abunda Baffa ke fada yasa wayar a hands free domin Badaru yaji abunda Baffa yace. Abba ya maimaita abunda Baffa yace "ta gama idda?" Baffa yace "eh"


Badaru ya dafe qirji yace "to cikin jikinta fa? Xubarwa tai?" Baffa da yaji abunda Badaru yace saboda hands free din da aka saka yace "ita dai tace babu ciki kuma iddarta ta cuka tun kwana 6 baya"


Abba yayi saurin cewa "to ai abun bai baci ba har yanxu, tunda yayi nufin maidata sai mu kawo sadaki in anjima a maida auren" Badaru yayi saurin gyada kai cikin gamsuwa da abunda Abba yace"


Sai dai muryar Baffa ta katse masa hanxari inda yake cewa "Alh sai dai muyi haquri inaga iyakacin xaman da Allah ya rubuta musu kenan, domin nima na kawo batun maida auren maryam ta nuna bata da raayin kuma xama dashi dana takura sai anmaida auren adalilin hakan nima xaman lfyar gidana

Please Login or Register in order to submit comment