Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciro ID card dinta na aiki ta nuna mata, ta barta ta wuce. Tasa safar hannu ta fara duba Mimi, tabbas da ragowa dan naqudar inta taho gadan gadan saita koma. Ta kalli Mimi cikin tausayawa duk tayi laushi ta hada xuffa kamar ruwa ya daketa tace "Mimi ki daure kiyi nishi Kinji" bata amsa ba. Bature yaje saitin fuskarta yace "maryam kiyi nishi ko kadan ne, daure kiyi danmu xaki kawo mana duniya" ta bude jajayen idanunta tace "baxan iyaba, numfashina iya qirji yake tsayamun baya kaiwa ciki kasan ina sonka da xan iya ya Bature da nayi" ya share kwallah aransa yace dama haka mata ke wahala wajen haihuwa.? amma wasu matan suyi ta haihuwa kamar mahaukata ko ciwon jikinsu basaji? A fili kuma yace "nasan kina sona Mimi, tunda kina wannan halin ma baki manta soyayya ta ba kuma kina wannan wahala ne don ki haifar mana sanyin idaniyarmu." ya miqe ya fita ya koma office din ishaq.




Ya daure fuska yace "ishaq na rasa dalilin da yasa kake haka, na rasa me Maryam tai maka kake mata wannan hukuncin. Kai lokacin da aka kawo matarka ai tsayawa kai ta haihu cikin sauqi, saini xaka azabtar da tawa, tun jiya take abu daya gashi tana neman kuma kwana duk qarfinta ya qare" ishaq ya dan diririce dan tunda aka kawo Mimi yaqi shiga dakin da take sai nurse da likitoci mata yake turawa su dubata. Shi anasa ganin xuwa kan Mimi a halin labour kamar keta alfarmar aminin nasa ne. Tun safe Bature ke fama dashi yaje yaga meya hana Mimi haihuwa a matsayinsa na babban likitan mata, amma sai sun tafi rimi rimi sun kusa xuwa dakin sai ya xame yace ya manta be dakko wani abun ba.



Ya kalli Bature yace "kayi haquri, na tura Dr Salma yanxu ta dubata inda matsala xata fada ko banjeba" Bature ya fusata ya buga table din gabansa yace "ishaq wlh in Mimi ta rasa ranta bisa wani dalili naka marar ma'ana Allah baxan duba tsakaninmu da kai ba makaka xanyi a kotu" ishaq yace "to Allah ya baka haquri muje in ganta" ya miqe ya fara duba lokar jikin table din kaman yana neman wani Abu. A zuciyarsa kuwa addua yake Allah ya kawo masa mafita dan bayaso ya keta alfarmar Bature ya duba masa mata. Dr Salma ta turo kofa tashigo, yayi hamdala a xuciyarsa tace "Dr. Na dubata, da naxaci fitsari ya hanata haihuwa amma na xuqe mata har yanxu shiru qarfinta ya ida qarewa inaga CS ya kamata atafi da gaggawa kan wani abu ya faru." Bature ya runtse ido, ishaq ya miqe ya dakko takadda ya tura masa yace kasa hannu xamu shiga CS da ita. Dr Salma ta fita bayan ishaq yace taje ta shirya Mimi xuwa dakin operation. Shima ya miqe ya fara saka kayan aiki, Salma ta dawo da sauri tace "Dr yanxu muka hadu da sister zubaida a hanya, maryam din ta haihu yanxu." ai kafin ta gama fada Bature tuni yayi waje yana hamdala. Yaje shiga dakin ya ganta a kulle an rufe ta ciki, ya juya ya kalli su mama suma fuskarsu na nuna alamun murna yace "suna ciki ne?" tace "eh su ukune ciki har Faty ta hudu" sunata xaman jira har ya gaji yaje yayo sallar da ake binsa beyi ba ya dawo amma basu bude ba.




Sai da suka kusa 2 hours ciki suka bude lokacin harya fidda tsammanin lfy kuwa? Suna budewa suka duru dakin, angyara komai qal dakin sai qamshin dettol yake. Anwa Baby wanka, Mimi ma anmata tana sanye da kayan asibitin dark blue kamar yadda dokar take me jinya bayasa kowane kaya se nasu. Tana kwance sunata daukar Baby ita kuma tana kallonsu tana murmushi, ta kafe mama da ido wani masifar san mama take a yanxu data xama uwa, ashe haka iyaye mata kansha baqar wuya kafin suga dansu? Gaskiyar farida da tace mutuwa tayi ta dawo. Duk Dan dabebi uwarsa ba ya shiga uku.



Mumy ta dubeta tace "sannu maryam, kin samu diya mace" batace komai ba sai lumshe ido da tayi, tayi baccinta sabida allurar da akai mata. Sama sama taji shigowar ishaq ana xuxuta kyan Baby.




Tayi bacci me yawa ta tashi batasan ko qarfe nawa ba lokacin, Faty ta rakata bandaki tayi brush ta canja pad kana ta dawo ta fada mata tea a qaton cup ta shanyeshi tas. Mama xaune da jaririya a hannunta tace a xuciyarta "wai yau nice riqe da dan Mimi? I kon Allah kenan, mimin da akasha fama akan neman mijin aure yau gashi abu ya wuce lallai komai yayi farko xaiyi qarshe, kuma komai lokaci ne"




Aka miqa mata yar, ta karba a kunyace tana kallonta, babu inda tabar mumy, kamarsu daya sak, sumar kantace kawai irinta Mimi dan gatanan a cike. Mumy tace "bata nono tasha tun daxu take tande baki da Bature ya bata dabino" Mimi tace "mumy ai babu ruwa" tace "bata haka ta kama xata xuqo" Mimi ta fara yarfe hannu tace "mumy wlh da xafi abata madara kawai" abu dai ya xama babba tun suna ganin abun wasa har ya xama gaske dan Mimi ta hana Baby nono. Suka fita xuwa office din likita dan tambayo wace madara ya dace a bawa new born Baby.



Bature ya taso bayan fitarsu ya kwanta kan gadon suka saka yar a tsakiyarsu, yace "dan bata nono Mimi luv, kinga inkika bata yanxu shine first anaso Baby ta fara shan nonon uwa dan ya wasar mata da kwalkwalwa, inkika bata shikenan sai acigaba da bata madara" tace "to" ya miqo mata yar ta xauna ta fara bata, tana cije baki dan da xafi, yana bata baki harta haqura ta saki jiki. Ya matso yana mannata a jikinsa ko anan aka tsaya burinsa ya cika, Mimi ta haihu dashi tana kuma shayar da diyarsu nono. Yace "Mimi kiyi haquri, naso ace yadda kika wahala sunanki na sakawa Baby, amma sai dai na riga nayi alqawarin saka sunan mumy tun sanda scanning ya nuna mace xaki haifa" tace "babu komai ya Bature nima nafison taci sunan mumy dan da mumy take kama kamar ita ta haifeta." yace "to nagode Mimi amma naji mumy tana cewa wai kamarmu daya ina jariri"



Faty ta shigo ta gansu ta koma da baya ta tarar dasu mumy riqe da takaddar madarar da likita ya rubuta tace "mumy ina xaku?" mama tace "sunan madarar xamu kaiwa Bature yaje ya siyo abata" Faty tace "to ku koma, Mimi dai da mukasha fama da ita ta bawa Baby nono taqi, gatacan mijinta ya lallabata tana shayar da diyarsu." mama da mumy suka kalli juna.




Sun shiga daki sun taddasu kamar yadda Faty ta fada musu, yana ganinsu ya sanfe yace "mumy takwararki aka samu HALIMATU" suka hada baki da mama sukace "mashallah Allah ya rayata" murnar sunan mumy da aka ya mantar dasu abunda ya faru.




Washegari aka sallameta suka wuce kano akabar Bature da kewar family dinsa.



A can kano gidan Baffa kuwa tun bayan sewa mama mota kowacce a cikinsu ta tasa yayanta gaba da takurar lallai suma sai sun saya musu motoci dan ba daya suke buqata, in sukai daya ai sunyi kunnen doki da mama. Yayan gaba daya sunyi karatun ta nutsu suka hada kai sukace basu da kudin siyan musu mota su bari komai lokaci ne, kuma ai akwai motar gida wacce Baffa ya siya ake kaisu duk inda zasu, bayan haka kuma sunsan mama a nata bangaren baxata daga musu kaiba sabida tana da Mota basu da ita.



Rashida kuma mijinta ya dawo tun bayan dashi da amarya kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta, ita kuma ta qeqashe qasa tace ai sun rabu kenan. Bai haqura ba yanata naci ita kuma tana yangwanashi.



Mimi jego ta samu irin na mutanen da, mama macece me kula da Dá ko ruwan sha sai ta tafasa take bawa Mimi tasha. Tsakaninta da Baby kuwa sai dai in bata nono xatai, Kullum tana bayan mama. Mutane kota ina barkowa suke, fauxa taxo daga Lagos kuma ta kawowa Mimi wani yoruba lace irin wanda suke sawa a event dinsu 15 yards, kana ganin lace din kasan tsayi masifar tsada kuma duk wanda ya badashi a matsayin kyauta tabbas hannunsa ya cudi baya. Daga ninta kasan ta fara kama qasa harda motarta taxo wacce sunusi ya siya mata. Mimi ta dunga murna, mama ta karbi lace din takai shagonta na dinki wanda ta bude ta xuba yara maxa. Suka dinkawa Mimi buba da xani Bature kuma sukai mai irin dinkin yarbawa. Alheri kota ina barkowa yake. Bature ko tsinke bai saiwa Baby ba, Anty mami ce tayi komai har kwanan da Baby xata fara cin abinci in aka yayeta sai data aiko dashi. Ranar suna Audu ya kawo Sá da rago aka yankawa HALIMATU wacce little ta fara kiranta da MIMA. Ranar suna da yamma ya iso, Mimi ta bashi lace din fauxa ta fada masa fauxace ta kawo musu ya karba ya saka sanin matsayin fauxa gurin Mimi, itama ta saka aka dunga hotuna yana riqe da Mima. Fauxa taji dadin saka kayanta da sukayi.




Ta cigaba da rainon mima ita da mama, kuma a xamanta da Rashida ta dunga bata shawarar ta yadda ta koma ta haqura kodan Dan dake tsakaninsu. Taji shawarar Mimi, ta tatseshi kudi sosai kafin ta yadda a qara daura aure ta tare. Amaryarta dole ta kwantar da kai aka xauna lfy domin yanxu ita yakewa wulaqanci akan Rashida. Dama hausawa sunce bulalar da aka daki uwar gida da ita tananan tana jiran amarya dan haka ki dena murna dan mijinki na wulaqanta kishiyarki akanki dan wata rana ke xai wulaqanta.


Mimi tayi tas tayi kyau dake ansamu jego original, tayi shar kamar bata haihuba, tana yin arbain yaxo ya kwana suka koma tare. Mama ta dunga cewa su kular mata da mima, dan kowa yasan yadda mama ta dorawa mima son duniya fiye da komai a yanxu.




Tanata fargabar haduwarsu, kamar ya sani ya kyaleta sai data kwana 4 da dawowa lokacin ta saki jikinta sannan ya far mata. Ai kuwa ta dunga ihu suna kokawa, har ta tashi Mimi dake kan gadonta a gefe dole ya haqura karta tara masa yan aikin gidan a wannan daren. Kwana biyu ana abu daya ya gaji ya tambayi ishaq "ishaq wai in mace ta haihu qara matsewa take ne?" ishaq bai bashi amsa ba sai dariya da yunduga kyakyatawa, ya fuskanci matssalar Bature dan shima sunyi haka da Farida. Sai da ya gama dariyar ya bashi amsa "in mai kyan jiki ce tana kuma kamewa tayi tsam, musamman in suka samu kulawar jego. Kawai abunda xakai, kabi a hankali kamar daren farko da haka har ku saba" yabi shawarar ishaq, akuwa aka wuce gurin. A Kullum yakan godewa Allah da kuma fadawa Mimi cewa, shifa gani yake kamar ba daga jikinta mima ta fito ba kuma ko cikinta bai nuna alamar wata halitta ta kwanta ba, a taqaice dai Mimi tana cikin mata masu kyan jiki wannan flat tummy din da yake masifar so tananan ana masa gayu da ita.



Sukaci gaba da rainon mima,duk sanda ka duba dp din Bature mima ce a jiki, anty mami koda yaushe cikin aiken kayan mima take. Suna tsoron karta kuma samun ciki, hankalinsu ya kwanta da suka gane Mimi tana cikin irin matannan masu tsaftar shayarwa. Má'ana wadanda basa period in suna shayarwa dan haka suka sake suna gurxar amarcinsu.




Mima kyakykyawar gaske kamanninta da mumy sai qara fitowa suke, amma yar siririya ce sosai kamar little kamar yadda little tai musu fatan ta haifi irinta. Tana da sumar kai sosai kamar ta Mimi, ta taso cikin farin jinin mutane kowa sonta yake Mimi dai tana tsananin kau da kai akan mima kamar ba diyarta ba kowa ya sheda hakan.



Tana shekara daya Anty mami ta aiko da kudi da kaya akai mata birthday acan kano gidansu na sharada kuma kowa ya hallata an kashe kudi sosai. Mumy tunda aka haifi mima duk wanda xaiyi dinki acikin yayanta saita karbi ragowar kayan ta ajiyewa mima, kafin ta shekara antara mata natives sunfi akwati daya. Zuwansu kano birthday mumy ta bawa mama kayan ita kuma ta auna mima aka tsantsara mata dogayen riguna Kamar yan kanti masu jeluna, ta ajiye a gurinta dan tayi shirin dauke mima ne sabida son diyar take fiye da duk yayanta da jikoikinta (abun cikin kwai yafi kwan dadi)




Wannan karan kudin hayar gidanta yana xuwa gaba daya ta dauka ko shi mijin bai sani ba ta biya musu umra kusan su 6. Ita da Faty, mama da mumy, little da Bature. Kana ta biya wasu kudin aka hada harda yayan Faty da mima dan Mimi yanxu kudi take samu kota ina business dinta ya fadada kuma har yanxu bata daina yiwa mom adduar fatan alkhairi ba dan itace tushen komai.




Ranar da Bature yaji abunda Mimi tayi yayi mata godia da alqawuran soyayya sunfi cikin 80 leaves.



Mumy kuwa ta kasa boye farin cikinta kamar bata taba keta haxo ba, duk inda taje ko akazo mata kaji tana cewa "umra xamu ni da little da fadima. Maryam matar Bature ce ta biya mana dukkanmu" wannan karan ma matan Baffa suka kuma haukacewa, amma babu yadda suka iya dole mama ta dauki jikanta suka wuce.



Anyi umra lfy, Mimi tasha adduar fatan gamawa lfy a gurin duk wadanda ta biyawa umra din.



Basu jima da dawowa ba tayi shirin yaye mima kuma ta fadawa mama. Ana gobe xata yayeta mama taxo Abuja huxaifa ya kawota a motarta. Suka kwana, washegari juma a ta dauki mima xasu tafi, Bature kamar xaiyi kuka yace "Allah sarki mima yanxu na daina ganinki sai takalmanki da kekenki?" mama tace "to mara kunya baka isa dai ka hanani tafiya da ita ba, dan wannan yar tun tana ciki akaimun kyautarta dama jira nake a cire a gora intafi da abata" Mimi tana kallonsu tace "mama kamar yadda nayi alqawari a baya ba, na baki ita duniya da lahira, nasan xaki mata kulawar da koni baxan mata ba" tace "hakane uwata MARYAM" aka kwashe kayan mima tas har kekenta aka xuba a mota, dakyar aka banbareta daga jikin Bature tana kuka yanayi suka shiga mota suka tafi. Daga uban har yar sun bawa mama tausayi, ta dura mata freso ta bata rubutun yaye da akai mata ta jijjigata tai bacci. Mimi da Bature haka suka wuni wani iri, batasan tana son mima ba sai yanxu, gwarancin mima har gixo yake mata. Xuwa yamma zazzabi ya rufeta sosai ga ciwon nono. Yaje gurin ishaq ya karbo mata wani maganin ciwon nono wanda ya siyo musu ita da Farida a singapore dan ba a samunsa a qasar nan, tanasha ta watstsake xuwa dare kuma tayi mamakin ganin nononta bai fadi ba yananan dam dashi kamar bata haihuba maganin nada kyau shiyasa ba ko ina ake samunsa ba.



Acan kano mima ta saki ranta sabida maganin dangana da aka bata, tayi qiba sabida samun kulawa ta musamman, tuni ta shiga harkokinta ga yara a gidan ga kuma dady wanda duk abunda yaci saiya bawa mima. Kuma kulawa yake bata sosai ko shurin mima kayi cikin rashin sani saiya rama mata.



Mumy duk weekend saita turo an dauki mima ankai mata ita ta kwan biyu acan. Kuma Kullum little tana bisa hanya mumy tana cewa taje tagano mata mima kar mama tana wannan haqurin nata matan Baffa su dunga yiwa mima mugun hali yadda dukaiwa Mimi. Duk sanda little taxo tana komawa mumy da saqon qalau taga mima, kuma tana ganin mama baxata bari a taba mima ba balle ai mata mugun abu dan bata de haquri akan mima ko kadan.




Mima yar gatan iyaye da kakanni duk sanda taje gidan mumy saita dakko make up kit din Anty little kamar yadda take kiranta, ta xauna ta dame fuskarta kamar yadda taga little nayi. In little ta farga da barnar mima saita duddumeta intai kuka kuma taxo tana lallashinta.




Mimi da Bature kuwa soyayya aka balle kamar farkon aurensu, suna planning na calendar ko withdrawal method, dan Bature yaqi yadda suyi allura ko saka roba yace duk suna da illah kamar yadda ishaq ya fada masa.


****** ******* ******** **



Tafe take cikin motarta sanyin AC na bugata, tagaji liqis yau sunyi mahawara mai zafi a court amma Alhamdulillah sunyi nasara. BARRISTER MARYAM AL 'AMIN ce, wacce ta fara aiki shekara uku da suka wuce a matsayin lauyan mai xaman kanta wacce ta fito daga chamber din AL 'AMIN MEMORIAL CHAMBER. Itace ta qirqiri chamber din ta xuba lauyoyi irinta kwararru a qoqarinta na tunawa da babanta. Kowa yasanta akan aikinta sunanta yayi fice ne sabida tsayawarta wajen kwatowa yaran da akaiwa fyade haqqinsu da kuma matan da maxa kan saki su barsu da wahalar yaya, wanda ta haqiqance wayan sakin aure shike maida yara marayin tilas daga nan kuma yasa yara kwarara kota ina suna nemanrwa kansu abinci hakan kuma ke kawo yawaitar fyade. Duk wanda yasan maryam yasanta da sanyin hali da nutsuwa, amma in irin wannan case din yaxo gabanta babu mutunci Sam tsayawa take ta fafata tayi ragargaxa harsai anwa wanda aka kama sukunci. Barrister Mimi kenan, lauyan kare yara da mata kuma lauyan mijnta SULAIMAN A AZEEZ, domin a komai nasa na dukiya itace take tsaya masa.




Ta shigo falon a gajiye, ta cire rigarsu ta lauya, sanye take da suit riga da skirt ta dora Baby hijab a wuyanta. Ta rage kayan jikinta ya rage daga ita sai shirt da skirt. Ta nufeshi yana xaune akan carpet yana latsa system as usual. Yana ganinta ya dauke system din kan cinyarsa dan bawa Mimi maxauninta ta hau ta dare shi, yana cewa "hannu da xuwa my luv, ya shariar taku? Nasan kinyi nasara kamar yadda kika saba" ta zare glass din idonsa tana shafa gashin bakinsa da yatsanta kana ta kwanta akan qirjinsa ta kewaye hannunta a qirjinsa shima ya kewaye qugunta yana shafa gashinta tace "ya Bature munyi nasara kam, amma nasha wuya fa lauyan da gayen ya dauka yana da wayo amma qarshe Allah ya dorani kansa" yace "mashallah tashi muje wanka dama kenake jira" ta miqe ya dauketa suna dariya suka shiga bed room.




Sai da mima ta shekara biyar sannan Mimi ta samu ciki, watan haihuwarta na tsaya ya dau hutu itama ta dauka, Germany yakeson kaita ta haihu dan yace baxata qara haihuwa a 9ja ba tunda ta sha wahala a wancan karon. EDD dinta ya nuna saura 9 dayz ta haihu su kuma saura 7 dayz su tafi kamar yadda yake a visarsu. Suka wuce kano dan tanan zasu tashi.





Tunda sukaxo Kullum da daddare yan uwansa da matansu na kusa kan shigo bayan isha a hadu duka a babban falo aita hira sai goman dare suke watsewa.




Yauma sun hadu dukkansu, anata hira kamar yadda aka saba, Mimi na gefe guda ta baje ta tasa robar pop corn dinta agaba tanaci, wanda ya xama shine abincinta yanxu Kullum sai anje kwari an siyomata shi me madara. Cikinta yayi wani irin mugun girma wanda ake ganin kamar yan biyu ne. Tun jiya take jin ciwo amma tana sharewa dan tasan wasa farin girki haihuwar mima da haka ta fara amma sai data kwan ta wuni sannan ta haihu. Yanxu ma wani azabar ciwon kwankwaso takeji ko sauraran hirarsu batayi. Farida ta dubeta tace "besty yaya? Ko jikin ne?" ta kalleta itama da nata cikin dan kusan tare suka samu tace "a a ummu jidda (haka take kiranta yanxu) babu komai inason xuwa toilet ne" Bature ya miqe da sauri yaje ya dagata, dan inta xauna bata iya tashi saiya dagata, in kwanciya tayi bata iya juyawa saiya juyata sabida girman cikin. Xai rakata tace ya barshi yanxu xata fito fitsari xatai.



Ta wuce bedroom ta tsuguna akan gwiwarta tayi gofo dan baxata iya tsugonon fitsari ba. Wani masifaffen fitsari takeji amma ta kasayi sai nishi take.

Acan falo sukaji shirun yayi yawa yasmin ta tashi ta bita. Ta dawo da gudu tace da mutanan falon "wlh haihu xatai" Bature yayi wuf ya shige dakin, Audu kuma ya kira Faty a waya yace tai maza tazo mimi na labour.





Lokacin daya shiga kan Baby ya fito, ya gigice ya rasa yadda xaiyi tace "ya Bature ka zaremun Babyn" yace "to ya akeyi maryam?" tace "kunnansa biyun xaka dafe ka zaro" yayi yadda tace ai kuwa saiga qaton da namiji akan tiles din bandaki. Sunanan ahaka mahaifa bata fado ba, ita kuma sai ajiyar xuciya take yana mata hannu duk sun dame cikin jinin haihuwa, Faty ta iso, ta shiga ciki tasa safa ta taimaka mahaifa ta gado, baby ya cika gida da ihu. Faty tace "ya Bature dan fita ka bamu guri in gyarasu" ya watso mata harara yace "da Allah uwar iyayi kiyi mata abunda xakiyi mata kawai, ni dana karbi haihuwar?" tanajin haka tace "to riqeta in kwarfe mata jini" ya riqeta ta kwarfe jinin, Mimi ta kalleta tace "ya Faty sai anmun dinki ko?" tace "a a Mimi baki qaru ba, Allah ya baki da sauki."


Mama da mumy sukaxo a tare Audu ya kirasu ya fada musu, mama ta karbi gyara Mimi, mumy kuma ta yiwa Baby wanka. Cikin qanqanin lokaci sukai fes gida ya dau turaren wuta, aka fito da Baby su yasmin anata dauka da sauran mutane farida kuma cewa take yadda besty batasha wuya ba nima baxan sha ba ko ya ishaq? Sai yace mata eh maman jidda. Sai sha biyun dare suka watse, ya shigo bedroom din dauke da Mima a hannunsa tana tamai surutu. Su mama duk suna ciki, ya nemi gefen gadon ya xauna inda Mimi keshan tea.



Mima ta dane cinyarsa tace "ABBA wai kaine Dady na, Maman Abuja kuma mamana?" ya sumbaceta yace "eh mana ai shiyasa nake ce miki my lovely mumy, amma waya fada miki?" tace "yaya Dady ne" Bature yace "kinga wannan Babyn kuma qaninki ne" tace "to Dady na" ya dakko Baby yana kallonsa, kamarsu daya dashi sak, duk da yaron jaririne kamarsu da Bature bata buya ba. Ya miqe ya kwanta akan gadon yasa Mima da Babyn a tsakaninsu da Mimi sukai baccinsu, mama da mumy suka fita suka bar musu dakin.



A taqaice dai Germany din daba ajeba kenan, tunda abunda xai kaisu Allah ya kawoshi cikin sauqi. Ranar suna yaro yaci sunan "AL AMIN" Mimi tayi murna da sunan da babanta da yasa tana kiransa ABBA.


******* ****** *********



Rayuwa ta tafi, Mimi ta xama attajira sosai, ko aikinta ya isa ya riqeta balle business dinta wanda ya zama gagarumi ita kanta batasan adadin dukiyarta ba. Duk sanda ta fidda xakkah asibiti take xuwa ta gaida marasa lfy a fito mata da wadanda suke da lalura babu kudin magani kona aiki ta biya musu kuma dama ta dade da wannan buri tun tana qaramarta, sai kaga mutum ya rasa ransa ko ya nakasa akan kudin da basu taka kara sun karya ba, shiyasa take xuwa can takai

Please Login or Register in order to submit comment