Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tabu, domin uwarta tace baza a kuma yiwa yarta auren dole ba har tana barazanar dauke yarta su barmun gidana. Ni kuma inason matata kaga garin gyara kuskuren Badaru aurena zai mutu, gara kawai a haqura."



Abba ya kashe wayar cike da jin haushin Baffa, yana mitar kamar Buhari ya zauna mace na juya shi? To kada Allah ya sa maryam din ta dawo, metafi Badarun ai Badaru ba illah ce dashi ba babu inda xaije neman aure ba a bashi ba (kuji san kai?)


Badaru tunda ya gama jin abunda Baffa ya fada gabansa ya yake ya fadi, qirjinsa ya dunga bugawa sai yanxu ya tabbatar ya tafka kuskure. Tabbas yasan maryam bata sansa, wlh da yasan haka xata kasance da bai saketa ba. Ta xubar masa da cikin da yake ganin shine tsanin da xai dunga hadasu. Umma kuwa hawaye takeyi jin maryam ta bar xuriar ta, tasan Badaru yayi rashi.


Badamasi kuwa dake gefe fuskarsa a washe sai murmushi yake. Ya dunga godewa Allah a xuciyarsa, yace lokacin aurena yayi, maryam ta dawo. Jin fadan abba yaqi qarewa kuma Abban baya blaming kowa sai Mimi, shiyasa ya matsa gaban Abban, baice komai ba sai wayarsa da ya ciro ya kunna recording din da ya tabayi wanda Badaru ke tsagin Mimi da korarta daga gidansa. Yace Abba ku saurari wannan"



Sukayi tsit har Badaru suna sauraran recording din harya qare sannan Badamasi ya dora musu da sauran abunda yagani na zamantakewar auren da kai Mimi asibiti da yayi da kuma abunda yakeji lbr gurin abokan Badaru.



Jikinsu yayi mugun sanyi, Umma kuwa kuka take tana kallon Badaru a razane. Ta kalli Abba cikin kuka tace "Alh kaji abunda nake fada maka ko? Kake goyon bayansa, wlh nasan sharri yayiwa yarinyar nan, ai dole tace baxata xauna dashi ba saboda ya azabtar da ita, inma cikin ne ai baqin cikinka ma ya isa ya xubar da cikin. Kuma wlh indai nadama ce baka fara ba, ka cuceni ina qaunar yarinyar nan ka rabani da ita" ta qara fashewa da kuka. Abba ma ya kalleshi yace "baka cuci maryam ba, ba kuma ka cuceni ba kanka ka cuta. Na yarda da kai kasa ina jin haushin yar mutane ashe kaine babban dan iska, sabida haka kajira sakamako wlh sai Allah ya saka mata"



Badamasi ya matsa kusa da qafar Umma ya riqo hannunta yace "Umma share wahayenki, baki rabu da maryam ba, maryam xata dawo cikin xuriar ki kuma a matsayin surukarki, domin xan auro maryam. Idon kowa a gurin ya dawo kansa. Yaci gaba da cewa tun farko ni naga maryam, ni na fara sonta, ni nafara yi mata magana. Ina shirin inje innemi soyayyarta Badaru yazowa Abba da maganar aurenta ganin haka yasa na haqura, amma wlh da nasan Badaru haka zai maltreating maryam wlh bazan haqura in bar masa ba. Saboda haka Umma ban taba neman abu a wajenku ba yanxu nazo da alfarmar neman goyon bayanku akan neman auren maryam, ba haram bane dan Allah ku kauda kai a magoar mutane ku goyamun baya."


Umma ta share wahayen farin ciki, ta shafa fuskar Badamasi tace "na baka goyon baya 100%, nasan bazaka wulaqanta maryam yanda Badaru yayiba Allah ya sa rabonka ce" ya juya gurin Abba yace "Abbana inkace in haqura xan haqura" Abba ya kalli Badamasi a nutse yace " na baka goyon baya likita, indai har kun daidaita kanku da kaina xanje gurin Alh Buhari a karo na biyu in nai mar maka aurenta" ya dunga godia yana dariya ji yake indai Mimi ta amince nan da 2 wks xa ayi komai a gama. Yau yana da daurin auren abokinsa a Danbatta amma gobe in shaa Allah zaije su gana.



Badaru da tunda Badamasi ya fara magana yake kallonshi har ya gama, ya tashi idanunsa jajur da tsabar kishi ya tari gaban Badamasi cikin sigar rigima yace "oh dama ashe san maryam kake? Shiyasa ka hure mata kunne ta ciremun ciki ta gujemun sannan ka nado sirrinmu ka kawo ko? To wlh baka isa ka auri maryam ba indai ina numfashi, kai ko kunya bakaji ka auri tsohuwar matata? Ban taba neman abu na rasa ba, na auri maryam da farko kuma yanxu ma xan kuma aurenta domin wlh saina kasa ka, ka rubuta ka ajiye, inkuma ban aureta wlh sai dai ayi biyu babu kowa ya rasa."


Badamasi yaja da baya ya kalleshi yana dariya yace "ka saba yiwa kanka kirarin duk abunda ka nema kana samu, amma inkasamu baka iya alkinta abun, kaga kodan haka Allah xai iya jarrabarka, saboda haka maryam dai yanxu rabonace in shaa Allah gara kaje ka lallaba kucakar matarka ku zauna lfy. Kuma ni bazan fada da kai ba domin yau cikin farin ciki nake dan haka kaje ka nemi irinka looser kuyi "


Badaru yakai masa duka Badamasi ya tare tare da cewa kasan in dambe xamuyi wlh karyaka xanyi ka wani tara teba sai kace me ciki. Abba ya daka musu tsawa tare da ja musu warning. Kowanne ya fita yana hararar dan uwansa. Umma tace "Alh baraka fa xata bullo idan bamu tashi tsaye ba"


Abba yayi shirin fita kasuwa ya leqa dakin Badamasi yace "Bani wayarka ka saitamun gurin maganar nan, gara insami Alh Buhari in wanke yarinyarnan a gurinsa." Badamasi ya bashi wayar tare da bude masa recording din, yana xuwa play kawai xai danna.



Baffa naganin Alh Inuwa a shagonsa ya hade fuska, don a xatonsa xuwa yayi ya qara neman alfarmar mayar da Mimi. Amma sabanin haka sai yaji yana bashi haquri tare da neman itama Mimi abata haqurin, kana ya budewa Baffa recording din ya saurara.


Baffa yayi matuqar tsorata da lamarin Badaru, ya kalli Alh inuwa yace " kace dan iska ka kawomun cikin manyan kaya ni kuma banyi bincike ba na dauki salihar mace na bashi" Alh inuwa yace "wlh Alh bansan abunda Badaru ya aikata ba kenan, shiyasa na kawo maka abunda yayi kaji. Amma dan Allah kayi haquri kuma ka bawa maryama haquri babu hannuna a abunda aka aikata mata kuma wlh da nasan haka zaiyi da ban nema mishi auranta ba" Baffa yace " shikenan nagode da sanar dani da kayi shi kuma ya je dan kansa ya cuci marainiyar Allah"


Baffa yayi sakato yana tunani, lallai ya tafka kuskure a baya. Ya dauki ya yabawa dan iska yana zaginta da goranta mata, amma kuma duk abunda Badaru yayi bashi da laifi, shine babban mai lefi da bai riqe su da daraja ba kuma ya nuna maryam din ba wata bace.


Tausayin Mimi da soyayyarta ta dirar masa nan take, dole Mimi tace bazata koma gidan Badaru ba saboda ya zalunceta sannan ya biyota da sharri shi kuma ba bincike yahau ya xauna. Jin soyayyar Mimi yake har cikin bargonsa kuma yaji yana kunyar hada ido da ita da uwarta.



Badaru na zuwa gida ya samu Nafee a parlour tana kallo, ya kalli parlour komai kaca kaca ya kalleta da yake a kusa yake neman masifa yake sai yace "ke haka ya dace kibar guri ki xauna kina kallo dake ke jaka ce?"


Ta kalleshi sheqeqe tayi dariya tace " jakai dai, ni da kai in ban gyara ba kai baka da hannun gyarawa?" kafin ta ida fada ya kifa mata mari.



Batai wata wata ba ta dakko plate din da ta gama cin indomie yanxu ta jefa masa tana huci, sannan ta dora da cewa "ga dukkan alamu ka saba ganin tsohonka na jibgar gyatumarka shine kazo xaga gwada a kaina, to wlh duk randa ka qara dukana wlh saina sake maka kaciya 😳"



Ya tsorata da mutuqa da maganar Nafee, bece uffan ba ya shige bedroom dinsa, ya rasa abunda yake masa dadi. Shi yanxu yasan duk wanda ya fadawa abunda Nafee ke masa dariya zaiyi saboda yacce ya daukaki Nafee. Ya dunga juyi akan gado ya kasa bacci, har akai sallar laasar bai fito ba ga yunwa na addabarsa kuma yasan Nafee yau bazata bashi abinci ba. Ya tashi yayi wanka yayi sallah, ya zabo kayansa na qure adaka yasa. Gurin maryam xaije ya bata haquri ya nemi yafiyarta, yasanta da sauqin kai xata haqura su koma aurensu.


Ya samu Nafee zaune ta cokala dauri ture kaga tsiya tana sanaar (kallo), ya tsaya domin yayi mata magana, ta dauki remote ta qure volume alama batason jin abunda xaice, dan haka ya fice.



Ya dade a qofar gidan Baffa babu dan aike kuma bashi da no Mimi. Mimi ta fito domin zuwa gurin fauxa, tana sawo kai waje idonta cikin na Badaru gabanta ya yanke ya fadi ta diririce, ta juya da nufin komawa gida yayi wuf ya damqe hannunta yajata cikin sit room din dake soron farko.



Cikani, baka da hankaline xaka riqe mani hannu? "ta fada cikin fita hayyaci. Ya sassauta riqon da yayi mata, amma still yana riqe da ita karta gudu ya fara magana murya a kwance " maryam dan Allah kiyi haquri nasan na bata miki naci zarafinki na hadaki da iyayenki na tauye haqqinki na kuma toxarta ki. Amma wlh nagane kuskurena abaya na aureki ne dan shaawa amma xaman da mukai da ke nagane kyawawan halayenki da son addininki hakan ya jawo miki soyayya a gurina." Mimi tayi sakato tana kallonsa wai dama Badaru ya iya magana a hankali? Kuma dama yasan duk abunda yake ba dai dai yake ba? Tambayar da takewa kanta kenan.


A bangare guda kuma Baffa dake azumi (azumin kaffarar rantsuwar da yayi ta Mimi saita koma gidan Badaru, ya fara yau) ya dawo gida da wuri domin ya kawo salad din da yakeso a kwada masa yayi buda baki dashi. Yana xuwa soro aci burki dan jin maganganun dake fitowa daga sitroom. Da farko bai gane mai maganar ba, amma jin an ambaci sunan maryam ya gane me maganar da inda maganar ta dosa. A fili yace lallai wannan yaron bashi da kunya bari inje inyi masa tsakani da yata.



Sai dai muryar Badaru ta katse masa hanxari inda yaci gaba da cewa "maryam ki tunano rayuwar auratayyarmu me dadi πŸ™ˆ, ke bakya tunawa? Wlh kullum cikin kewarki nake da mafarkinki, ki dawo muje mu zauna duk abunda kikeso zan miki duk yan uwanki na gidan miji ke kadaice kika rage, kin wuce xaman gida ki dawo dakinki shine rufin asirinki"




Ta katseshi da cewa "xaman gidanmu yafiyemun zaman gidanka, kuma lokacin da sakeni ka wurgoni kofar gida baka duba cewa na wuce xaman gida ba sai yanxu? Rayuwar auratayya kuma da kake fada kaika santa har take maka dadi, abunda kawai zan iya dorarwa aciki shine: fyaden da kakemun duk daren duniya. Abubuwan kuma da kayimun a duk xamanmu na barka da mahaliccinka shi zaimun sakayya." tana kaiwa nan ta fusge hannunta ta kifawa Badaru mari, kafin ya gama mamaki ta kifa masa wani 😳.



Ta dora da cewa " yau alqawari ya cika, lokacin daka mareni a gidanka na fada maka cewa wlh saina rama gashi kuma na rama din. Zagin ubana kuma da kayi kace inje in haqoshi a kabari, bazan rama ba, domin nasan darajar iyayena sannan nasan duk daren dadewa naka uban xaije inda nawa yaje. Gida kuma basai nace karka kuma xuwa ba, saboda bata dalilina ka fara xuwa gidanba."



Baffa dake sauraransu yayi murmushi cikin jin dadin abunda Mimi tayi yace "yar halak kenan, tayi alqawari ta kuma cika maryam jinin Al amin ce domin ga halinsa nan a jikinta.

Ta fito ta koma gida memakon gidansu fauxa da tayi niyyar xuwa, shiyasa bata kula da Baffa ba dake tsaye a qofar fita. Badaru ya gama mamaki ya jawo qafafuwansa jiki babu kwari yayi hanyar waje, yaci karo da Baffa. Baffa ya nunashi da yatsa yace "karka kuma xuwarmun gida, in kuma ka kuma xuwa xan hadaka da hukuma" yana fadar haka ya shige gida.



Washe gari lahadi da yammaci aka aiko kiran Mimi, har taqi fita mama tace taje in Badaru ne taxo ta fada mata. Sai dai me tana fita taga Badamasi a tsaye. Tana ganin mutuncinsa dan haka tai masa iso sit room.


Ya xauna suka gaisa a mutunce ta tambayeshi mutan gida da gurin aikinsa. Yayi farin ciki ganin maryam din ta fara dawowa hayyacinta ba kamar lokacin da tana gidan Badaru ba, ya dunga hasketa da murmushi yana kuma jinta a xuciyarsa. Yayi mata jajan mutuwar aurenta, tace ba komai iyakacin xaman da Allah ya nufa kenan.


Ya karanto mata abunda ke cikin xuciyarsa, ta dunga kallonsa a kidime ba tace komai ba ta miqe da nufi fita. Yayi saurin shan gabanta yace "maryam wlh babu inda xaki sai kin fadamun matsayina a xuciyarki, inbaki manta ba nina fara sonki Badaru furtawa ya rigani indai ba so kike inyi hauka a kanki ba ki amshi soyayyta" itadai babu baka sai kunne, domin kanta ya daure da yawa.


Da yaga taqi magana saiya kamota ya sata a bango yayi mata rumfa da qirjinsa yasa hannu ya katangeta ta inda duk motsin da tayi saita taba jikinsa. Yakai fuskarsa dab da tata ya fara magana "Mimi ki laluba xuciyarki bazaki rasa soyayyata aciki ba, ba halinmu daya da Badaru ba soyayyar da nake miki bazata bari in cutar dake ba, xan kula dake xan baki yancinki, xakiyi duk abunda kikeso, bazan tauyeki ba irin rayuwar da kike mafarki xakiyi. Maryam fargabar me kikeyi? Bazan akiyeki kusa ba balle a dunga yi miki surutu, can gurin aikina xan tafi dake sai dai kixo da yawo."


Ganin cewa kamar baya cikin hayyacinsa yasa tayi niyyar yimasa dabara. Dan haka tadan dauke kanta daga fuskarsa, yayi saurin dawo da fuskarta kusa da tasa har tanajin numfashinsa, yace "yimun magana a haka in san cewa mafarkina ya kusa xama gsskiya." tayi qasa da murya tace "kadan bani lokaci inyi tunani inkuma yi istikhara"


Tunda ta fara magana, ya lumshe ido yana shaqar hucin bakinta. Sai data gama sannan yace "to shikenan, xanso hakan nima kuma nima zanje inyi sallatul istikhara. Saboda haka wani satin xan dawo saboda gobe xan koma Dutse" ya dakko kudin da ya ware zai bata 10k ya lalubi hannunta ya manna mata.


Ta kalli kudin ta kalleshi tace "ai basai ka bani kudi zan soka ba." ya kalleta hankalinsa ya kuma kwanciya da ita yace nasani maryam amma ai kyauta ce. Tace "nasani amma ka riqe wata rana ka bani" yayi murmushin cin nasara yace "to my soul"

Ya nemi ta bashi no dinta tace wayar na gida kuma bata ruqe no dinba, dan haka ya bata tasa xata kirashi. Dake ya makance a soyayya be gane cewa wayo taimasa ba, ba musu ya dakko katinsa na gurin aiki ya bata.


Mama tayi matuqar kaduwa dajin wai Badamsi keson Mimi, tace "duk da ba haramun bane ai ana barin halak dan kunya, kuma naji dadi shine gari. In shaa Allah ko wanda sunansa ya fara daga BA bazaki auraba. Yazaki qara fita yayi haukansa ya gama"



Ranar litinin ranar Baffa ya dau azuminsa na qarshe, kuma yau ya shirya tunkarar mama akan fushin da take dashi.


Da yamma ya shiga har dakinta, ya sameta xaune a kan kujera Mimi tana kwance tayi pilo da cinyarta tanacin chocolate. Tana ganinsa ta miqe daga kwanciyar, mama tace mata Mimi shiga ciki. Ba musu ta shige bedroom din.



Baffa ya xauna ya fara da bata haquri akan dukkan abunda ya dade yana yimata da kuma godia akan tunasar dashi da tayi, kana ya dora mata da abunda baban Badaru ya kawo masa yaji a waya da kuma abunda yaji da kunnensa Badaru na fadawa Mimi. Yace yagane kuskurensa kuma ya canja daga yanxu, kuma Dan Allah ko anan gaba taga yana nufin kauce hanya a wani abun tayi gaggawar tunasar dashi, domin yagane itadin macen arxiqice. Sannan yayi mata xancen tumunin takabarta yasa an fitar mata a kotu tasamu gidaje biyu da wajen miliyan biyu (saboda andade ana juya kudaden) ya karbi acct no ta da nufin tura mata kudaden ya kuma danqamata takaddun gidajenta.


Ya kwallah Mimi kira, ta fito ta tsuguna. Rayuwa kenan duk wanda yayi haquri zaiga haske domin wai yau Baffa ke neman yafiyar Mimi da kuma bata haquri akan abunda duk ya faru a baya.


Mimi tana hawaye tace "komai ya wuce Baffa, kai ubanane duk duniya bani da wanda ya fika, nima ka yafemun abunda nayi maka rannan saboda bani da xabi sai hakan shiyasa nayi" yace baki komai ba MARYAMU Allah ya miki albarka ya baki abokin xama nagari sakamon biyayyar da kikaimun.


Mama na gefe na share hawayen farin ciki, ta dunga godewa Allah. Tace da Baffa nagode da kulamana da dukiya da kayi. Amma inaganin wadannan ka karba ka riqemun."


Yace "riqe abunki Haj Fadima, nadai riqe na yayana Faty da maryam kuma suma na rubuta da shedu saboda halin rayuwa, gidajen dai xantsaya a xuba yan haya." tace to duk yadda kayi nagode.



Yace " to ai bazan yadda kin huce ba sai kin karbi girki, ga cefane can nakawo inaso aimun special girki dan azumin nake kuma nadade banci delicious dinki ba."



Mama ta miqe tabi bayanshi tana dariya tace " yau kuwa xakici domin xan tabbatar maka na huce." Umma da Anty da tunda ya shiga dakin mama suke tsaye suna jiran suga abunda xa ai suka qiqim qiqim ganin mama da Baffa tare suna dariya. Mimi ma ta biyo bayansu da nufin taya mama girki itama tana tata dariyar.


Mrs 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }

Writing & story by
Rahma Muhammad {hajia}

Editing by
Mmn khairat 😍


Page 1⃣4⃣


Cike da farin ciki Baffa ya shiga gidan, gami da kwalawa mama kira tunda daga tsakar gida, ta fito a gigice saboda Jin kiran farautar da yake mata ta iskeshi daki gami da yimasa sannu da xuwa. Ya amsa yana washe baki kamar bebe yaga wawan zama (Lol) sannan ya dora da cewa wani abun farinciki ne ya samemu fadima shiyasa ki ganni gida yanxu, wato yaronnan dan wajen Alh Inuwa shine yaga Maryamu yace yanaso, kuma ga dukkan alamu akusa sukesan auren dan Alh inuwa da kansa yayimun maganar ni kuma nayi dattako nace kawai in sun shirya su kawo kayan aure kawai ayi. Mama ta kalleshi shagarai tare da daure fuska tace, Alh wannan wane irin neman aure ne sai kace auren yar tsana? Daga yaro yaga Mimi yace yanaso sai ace ya fito anbashi? Ita mimin baza aji raayinta ba? Kuma banaji ma Mimi tasan maganar domin da tasani xata fadamun, sannan shin kayi bincike akan yaron? Ko kuma dan ansan mahaifinsa shikenan? Aure fa in anaso a zauna lfy sai anyi da yardar maauratan, kuma naga ai bakai da Alh inuwa ne zakuyi xaman auren ba, yaran ne masu xama saboda haka inaga ku basu dama su fahimci juna inyaso daga baya insun dai daita kwa shiga lamarin. Baffa dake kallon mama tun da ta fara magana a dage tare da fallara mata harara wacce ita sam bata kula ba, ya magantu da cewa sai yanxu nasan ke babbar mahaukaciya ce fadima. Ta miqe tsaye tare da qara daure fuska tamau tace hauka kuma? Yau kuma nice mahaukaciyar? Nan da nan kuwa ya dai daita nutsuwar domin ya farga da kasassabar da yayi (ya tuna da fadima yake magana wacce Sam bata daukar irin cin mutuncin da yakewa ragowar matansa, ta nuna masa tasan ciwan kanta dan haka ko fada xai mata yakan tausasa kalamansa) dan haka yanxu ma sai yayi saurin yin kwana da cewa ai kece naji kina qoqarin yiwa Allah butulci, shekarar maryam din nawa ana neman miji? Ba a taba budurwa mai shekarunta ba kaf danginki da nawa, sai yanxu Allah ya kawo kice ga xance ga magana. Ta kalkeshi tace ni ba butulu bace kuma ba butulcewa nai ba inaso ne dai a gina auren akan fahimtar juna da soyayya, amma tunda haka kace shikenan Mimi yarka ce kana da ikon xaba mata miji, Allah ya sanya alkhairi yasa tsohuwar gida ce. Yawwa yanxu kikayi magana fadima da tun farko abunda kikace kenan ai da ba a tsaya sa insa ba, amin Allah ya yi miki albarka cewar Baffa.

Maryam kwance saman gadonta acan hostel na law skul rubda ciki take tana danna system, qarar Waya ya katseta daga typing din da take a system din, ta tsurawa screen din wayar ido gabanta na dukan 3 3 , tun tana qanqanuwarta ta tashi da tsananin tsoron Baffa da kuma dison qiyayyarsa acan qasan zuciyarta saboda halin ko inkula da yake da al amarinsu, duk da cewa mahaifiyarsu awancan lokacin tana boye musu lamarin baffan garesu kafun su girma su gane, sai kuma alokacin mama take yawan cemusu halin Baffa garesu ajixanci ne irin na Dan Adam. Amma AL AMARIN MARYAM na jinkirin aure da kuma takura gami da gorin Baffa akanta yasa dison qiyayyar Baffa ta samu girma a zuciyar maryam wanda takai tayi yado ta zama tamkar bishiya mai rassa, domin ji takeyi kamar ta raba auren Baffa da mahaifiyarta domin auren Baffa ba abunda ya qari mama dashi sai muzgunawa da gori daga gurin matansa daga gareshi kuma xa a iya kiran abun da yaudara domin kulawar da take kwadayin yayanta su samu inta aureshi basu sameta ba. Wayar ta sakeyin qara akaro na wajen 4 wanda hakan ya yankewa maryam tunaninta, tai shahada ta daga wayar. Ta gaisheshi cike da tsoro da firgici, ya amsa farai farai tare da tambayar karatunta da kuma lokacin kammalawa, lamarin daya daure kan maryam tamau, acikin ranta ta farta Baffa da tambayar karatuna? 😳 first in history.

Bayan hakanne kuma ya zayyano mata dalilin kiranta a waya akan maganar Badaru, sai da ta nutsu kwarai sannan ta gane wadanda yake nufi domin ita tamanta da haduwarsu, amma kuma tayi mamaki dajin cewa wai har ana zancen qarbar kudi ba tare da sun zanta da wanda ya nuna raayin a kanta ba, (domin ita a zatonta wanda yayi mata magana shike sonta wato Badamasi) amma da yake mama batai musu tarbiyyar ja da maganar Baffa ba sai kawai tace masa to Baffa Allah ya xaba mana abunda yafi alkhairi, yaji dadin furucinta kwarai ya dunga samata albarka. Koda ta kashe wayar tunani ya cikata to meyasa yaya Faty da mama babu wanda ya mata maganar ko dai suma basu sani ba? Sannan ta shiga wassafa siffar guy din da azatonta shine Badarun, ta dan tabe baki 😏 tare da furtawa a fili "yayi babu laifi he is handsome " amma ba irin mijin da nake mafarkin samu bane duk da bashi da muni amma bashi da tsahon da nakeso daga da namiji " πŸ™ˆ ta rufe idonta cike da kunya kamar wani yana ganin. Wannan dare dai haka ta qareshi cikin tunanin irin nata

Please Login or Register in order to submit comment