Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mumy ce tagaji da xamanta ta koreta gurinsa.





Tana bude qofar ya taso ya dauketa gaba daya ta fara wuntsula qafa ya direta kan gado ya kifa kanta, ta hararreshi tace "ai bakacemun xakaxo ba kawai saina ganka" yace "nakasa xamane shiyasa na biyoki my luv" tace "yaushe xaka koma? " yace "cewa xaki yaushe xamu koma?" ta marairaice "haba ya Bature banfa je gidan mama ba" yace "tashi muje yanxu" tana hararsa tace "yanxu inmunje minti nawa xamuyi dare fa yay" yace "to shikenan gobe sai mu maida tafiyar da yamma sai in kaiki da safe wajen uku ki dawo ana laasar saimu tafi" ta zunburo baki cikin shagwaba tace "nifa gaskiya ba yini xanyi ba kwana nakeson yi" fuskarsa dauke da takaicinta yace "Allah inbaki maida bakin da kika zunburomun ba bazakije ba sassafe xan tasaki muyi gaba"





Maimakon tayi abunda yace sai ta miqe ta kwanta, ya leqa fuskarta yace "fushi kikai?" taimai banxa ya burkitoto ya fara kissing dinta yace "sry Mimi luv kinga aiki na baro na taho sabida na kasa haqura ki dawo, kinga kuma bai dace naqara kwana ba saboda gurin aiki dama mr Alex yace tunda na aureki na fara shiririta da aiki" haka ya dunga lallabata harta sakko.



Kamar yadda yayi alqawari da sassafe ya kaita gidan mama, suka gaisa ya tafi yace zai dawo daukarta bayan azahar don su tafi da wuri. Daganan gidan Faty ya nufa yaga Baby, Ahmad ya dunga yimasa tsiyar angon qarni shidai kunya yake ace matarsa nada ciki kowa yasan abunda sukai wai shin ya akaima suka gane. Yayi musu shiru sukayi suka gama.



Acan gida kuwa Baffa da mama kamar su goya Mimi, Baffa daxai fita kudi yabawa Mimi wai ta riqe ta dunga siyan duk abunda takeso. Matan gidan sun san abunda yake faruwa don alamun ciki sun bayyana jikinta.




Mama tasa Mimi agaba akan ta fada mata abunda takeso wanda babu acan tasa anemo mata. Mimi tace magarya sai yajin barkono Faty ta bata na daddawa.



Daya daga cikin masu aikin gidan mama ta aika kasuwar rimi suka siyo kurna, magarya, goruba bararriya, tsamiyar biri da dai dangin irin wadannan kayan har aya danya. Ta hadawa Mimi su kusan buhu guda ta daka mata yaji me dadi cikin bokitin roba. Matan gidan suka tsaya suna kallo wato ashe su duk ba son yaya suke ba yau sukaga yadda akeson yaya.



Mimi na kwance akan doguwar kujera tunda ta idar da sallah tayi filo da cinyar mama, mama tanata shafa kan Mimi dake bacci cikin tsanin son diyar tata lokaci xuwa lokaci takan sumbaci kuncin Mimi. Ahaka Bature ya shigo ya samesu, mama tadanji kunyar yadda yaga tana shafa kan Mimi. Yadan bugi qafar Mimi yace "maryam tashi qatuwarki dake kin kwanta a cinya" mama tana dan murmushi tace "auta ce fa Babana" yadan sosa. kai yace "au hakane fa" ta miqe ta shiryo dama tayi wanka, mama tahau sawa afita da kaya ana sakawa a motar Bature yayi mamakin wadannan kaya duk dasu xasu tafi kamar masu gudun hijira.



Ta rakasu har qofar gida tana jaddada musu su kula sosai, ta budewa Mimi qofar mota ta shiga ta rufe tace "autata a kula sosai kinji yanayin yanxu ba kamar da bane sai a hankali" Mimi tai rau rau xatai kuka tana kallon mama, ganin haka mama ta koma ba tare data qara magana ba itama tana share tata kwallar. Bature jikinsa yayi sanyi, banda aure waya isa ya raba da da mahaifi? Sai dai ko mutuwa.




Acan ma gidan mumy ta hadawa Mimi kayan gwadayi da yawa hardasu aya me suga da kantu. Ana idar da sallar laasar yaso su tafi amma mumy ta tsaidasu da abu mara dalili don kawai bataso su tafi su barta. Dady cikin qosawa yace "Halima Dan Allah kibar yaran nan sutafi kar suyi dare a hanya" tayi shiru can tace " nikam Bature ka haqura ka tafi mana kabar yarinyar nan a gurinmu xatafi samun kulawa" ya zaro ido yace "mumy 😳 tab inbar Mimi anan inxauna acan ni daya? Gidan ai yaxama kango inba maryam. Gaskiya mumy baxan iyaba nafiku buqatarta kusa dani kuma ina kulawa da ita ko Mimi?" mumy badan tasoba tace " to ai shikenan amma nikam hankalina baxai kwanta ba" yasa Mimi agaba lokacin biyar harta kusa suka shiga mota mumy tace "Dan Allah babana ka kulamun da ita gatanan amana a hannunka" yace "mumy ina kulawa da ita amma xan qara akai in shaa Allah xan kula da ita" suka tafi suna dagawa juna hannu.



Mumy tace "Allah yasa dai wannan rawar kan da yake ba takurawa yarinyar nan yake ba don namiji bashi da haquri sam akan mace mai ciki" Dady dake bayanta yace "ji yada girma to koma meyayi ba matarsa bace" tai shiru ta koma ciki.





Su Bature kuwa sunata sharara gudu akan titi don yanason su isa da wuri, Mimi ta fito da yajin ta na daddawa dake qulle a leda acikin jakarta ta dunga dangwala tana lasa Bature ya dunga kallonta aransa yana mamakin kwadayi irin na me ciki. Yace "yarinya keda kano kuma sai kin haihu" tace "haba kai ka soma?" yace "wlh da gaske nake duk abunda xaisa kixo angamashi sai dai inwani abun ne ya taso" tace "tab aikuwa dana kira mumy na mata kuka" yace "ai sai dai in xuwa xatai ta tafi dake amma ni ko tace in kaiki baxan iyaba" suna cikin hirar yaji shiru ya leqa yaga tayi bacci ya dora kanta kan kafadarsa suna tafiya suka tadda check point. Sojan ya buqaci Bature ya tada Mimi, yace masa matata ce bacci take yace "katashe dai in tabbatar" yadan bugi kuncin ta tashi tana kallonsa ya nuna mata sojan dake tambayarta tace "eh mijinta ne" yace "Allah ya baku xaman lfy" ta koma baccinta.




Bayan isha suka isa, sunayin ramuwar sallolinsu suka kwanta. Washegari da Farida suka kwance tsaraba ai kuwa suka hau kai suka dunga ci. Abun ya xame musu abinci Kullum suna fama da kayan kwadayi.





Sunje asibiti anyiwa Mimi scanning cikinta wata biyu babu sati daya. Yayin dana Farida yaje kusan 4 months babu yan kwanaki, Bature ya dunga kallon Dan tayinsa dake cikin Mimi ta cikin computer din. Ya shafa cikinta yana murna.




Xamansu suke me dadi yana bata kulawa duk wani motsi datayi tayi kyau tayi yar qiba irin ta ciki fatar nan kamar ansaka mata leda akai. Bata da kewa inyanan yana manne da ita inkuma bayanan hadimanta suna kewaye da ita suna mata fadanci da girmamawa kamar suyi mata numfashi. Da kayan kwadayinsu ya qare mama takanas ta loda musu wasu ta aika ta tasha Bako yaje tasha ya karbo musu, mumy ma Kullum cikin waya da vedio call tana ganin Mimi. Hajja ba a barta baya ba itama saqonta yana iske Mimi kota kirata. Safna kan shigo duk bayan kwana biyu tana duba amanar mumy da ya Bature. Ya Taheer ma bai taba shigowa gidan ba tunda aka kawo Mimi amma wannan karon hardashi amasu sintirin duba Mimi bisa umarnin hajja da mumy.





Bature kuwa Sam bashi da sukuni akan Mimi sonta yake kamar wani mahaukaci, baya gajiya da kusantarta sabida wani abu dayakeni yanxu dangane da ita bashi da sukuni inbai jishi jikinta ba. Abun burgewar itama bata nuna masa ta gaji koda yaushe tana maraba dashi.



Fauxa ta haihu su Mimi da Farida sukaje Lagos suka kwana uku bayan suna suka dawo Baby girl ta samu duk da dai 7 month ta haifi cikin (bakwaini) sunga gata gurin sunusi yarinya taci sunan Mimi (maryam) sunji dadin wannan kara da fauxa da mijinta sukai.





Suka koma Abuja cike da kewar juna, sukacigaba da rainan cikinsu.


Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 5⃣7⃣



Wata litinin da yammaci suna zaune suna hira ita da yan aikin gidan hadi da kallon wani film a tashar Max, tana sanye cikin atamfa riga da skirt dai dai jinkinta ta cokala dauri. Tana xaune kan centre carpet ta miqe kafa tana hambadar garin quliqulin dake gabanta yayin da su kuma wasu suna kan kujera wasu kuma suna zaune kusa da ita.



Wajen hudu da rabi Bature yayi sallama ya shigo, suka amsa suna gaisheshi ita kuma Mimi kallonsa take ganin ya dawo da wuri. Suka watse suka barsu a falon, ya matso kusa da ita yana cewa "Mimi da iyalanta kunajin dadinku" ta riqo hannunsa ta dora akan cikinta tace "ya Bature ai mutum rahama ne xaman kadaici ba koda yaushe yake da dadi ba, duk da akwai lokacin da mutum ke buqatar yaji ya kadaice" ta miqe ta kawo masa ruwa da kunun ayar da bata rabo dashi.



Ta rage masa kayan jikinsa takai daki ta dawo ta haye cinyarsa suna hirarsu, wajen qarfe shida yasmin tai sallama bayanta me aikinta ce dauke da Adil sai Bako daya dakko mata qatuwar trolley dinta.



Mimi ta taso da saurinta kamar xataci da baka ta nufi yasmin ta rungumeta tana cewa "Anty yasmin wannan ziyara taki da dadi take" yasmin dinma dariya take tana "Anty Mimi karki kadani ki yiwa Babynmu illah" ta karbi akwatin yasmin a hannun Bako xata shiga daki saiga little itama tana kici kici da tata akwatin. Mimi da gudu suka rungume juna da little tana cewa "yau gida yayi albarka" little tana dariya tace "name sake dama munso baki surprise ne shiyasa bamu fadamiki xuwanmu ba" ta karbi kayansu ta fara shiga dasu daki, little ta nufi Bature dake xaune yana kallonsu ta shige jikinsa yana shafar kanta yace "autar mumy yau kune a garin namu?" yasmin kuma matsawa tai tana gasheshi.




Mimi ta dunga xarya tsakanin falo da kitchen ita da masu aiki, sai da suka musu gabansu da duk abun buqata kana ta zauna suka gaisa. Tace "kuci abinci kuyi wanka ku huta" yasmin tace "bamu tare da yunwa ko gajiya don a jirgi muke" basuci abincin ba sukace saiko jimawa sunsha dai kunun ayar da dambun nama sannan aka zarce da hira anan takejin wai bikin qanwar yasmin sukaxo wanda za a fara jibi laraba kuma ita yasmin din anan suka sauka gidan Mimi sabida batason can don cikowa da sharing toilet.



Anayin kira Bature ya tashi ya shige ciki yayi shirin masallaci ya fita, su kuma sukai sallah. Yana dawowa isha ya taddasu cikin shirin fita Mimi na jiransa xasuje gidansu yasmin din don susan isowarta. Yace a dawo lfy suka dau hanya.



Acan gidansu yasmin hannu bibbiyu suka karbi Mimi duk da bata taba xuwa ba amma yawanci sun santa don sunje bikinta. Lallai ta samu karbuwa sosai a gidan don kamar su goyata manya da yara sai haba haba ake da ita, suna mata mitar bata taba xuwa ba itadai murmushi take a xuciyarta cewa tai masu kudinnan sai kana baya baya dasu inba haka sai suga kamar don abun duniya kake tare dasu. Aka shiga hirar bikin harda amaryar ta dakko anko ta bawa Mimi kyauta duk kuwa da cewar da yasmin tayi tayiwa Mimi amma tace itadai tayi niyya. Mimi ta karba tana xuba godia, har kusan 11 suna gidan Mimi taji dadi don yadda suka karbeta duk da kudin da suke dashi da kuma shedar kafirin girman kai da ake musu ita dai basuyu mata ba.




Ta ayyana a ranta ba qaramin soyayya yasmin kewa Audu ba don inba haka ba da bazatabar wannan daular duniyar gidan nasu ta auri Audu ba. Duk kuwa da cewa shima ya tara manyan kudade amma ko kusa baxa ahada kudinsa da ex gwamna ba kuma sanate a yanxu.




Suka fito suka shiga mota ita da little suna jiran yasmin da bata fito ba. Little kewa Mimi gulma "gaskiya ya Mimi ba qaramin so yan gidannan suke muki ba, jiba daga xuwa kamar su riqeki gaba daya. Wlh mugayen yan rainin wayone suna kallon mutum a dage inkaxo kafin ai maka dariya sai anji waye Dad dinka amma kinga ke daga xuwa kurtun farin jini ya fashe miki a gidan, muma fa don sunga babu abunda suka fimune duk da ubansu politician ne shiyasa suka sake damu" Mimi ta dunga dariyar maganar little tace"haka ake yawan fada ko yasmin dake qaunata mutane da yawa mamaki suke ana ganin aurena da ya Bature zaisa ta fara kishi dani, amma kinga babu matsala ko kadan" little tace "wlh kuwa har mumy mamaki take kuma tanasan kusancinku wai ko yasmin xatai koyi da wani halinki" Mimi tace "to Allah yasa amma Anty yasmin sai a slow wani lokacin kamar yar gwaya" haka sukaita hira ko ince gulma harta fito suka tafi.




Qiri qiri Mimi ta guji dakin mijinta ta koma cikin su suka kwana hira sai dab da asuba sukai bacci.



Cikin kwanakin bikin sunsha zarya don yasmin akwai qafar yawo, tajasu can ta jasu nan amma dai sunyi shar sunsha qunshi da kitson gashin kanti ita kuma Mimi dake akwai gashi da nata akai mata. Farida ma ba abarta a baya ba da ita aketa wannan zirga zirgar, sau tari sai Bature da ishaq su dawo gida matansu basanan. Bature yakance yasmin akwai shedanin yarinya, Mimi tun tana tambaya tace xasu fita ta waya harta dena tambayata.



Ranar juma a za ai dinner kuma itace ta qarshe a tsarin bikin sai wacce za ai asabar bayan ankai amarya da safe Audu ya iso, da daddare sukaje dinner din suka dawo harda Farida wacce Mimi ta bata ankon da amaryar ta bata kyauta.




Sun sami Bature shi kadai a falo yana xaune yana aiki a system, suka xube falon lokacin wajen 12 na dare Farida ta shige gidanta. Audu ya cire hular kansa, yace "ya Bature bakai bacci ba?" yace ina naga ta bacci kun barmin gadin gida?" duk sukai dariya, yasmin ta xauna kan kujerar da Audu ke kai ta dora qafarta kan cinyarsa bayan ta cire hills din qafartata tace "Dan dannamin qafata darling nagaji" ya gyara xaman qafarta akan cinyar ya fara ja mata yatsu yana matsa kafar.




Little kuma kusa da Bature taje ta dora kanta a kafadarsa, yayinda Mimi ke daya gefen nasa xaune batare data jingina dashi ba don ita kunyar su Audu take. Kamar an musu dole suka fara watching horror movie din da ake a MBC action, sunyi tsit Audu yana dann waya yayin da Bature ke aikinsa. Little ta qara shigewa jikin Bature cikin tsoro, Mimi ma dake gefe batasan lokacin data matsa jikinsa ba ta qanqameshi, ita da little sun hanashi aikinsa ta hanyar kankameshi sun hanashi motsi.




Wayar little tayi qara yasmin dake jikin Audu itama a tsorace qarar wayar tasa ta callara qara, suka dubeta a lokaci daya suma a razane suka fuskanci tsoro yasakata yin qarar kana suka kwashe da dariya har maxan.





Little ta dauki wayar tasa a handfree don Dady ke kiranta, a shagwabe tace "Dady ka tsoratamu wlh" yace "kiran nawa ya razanaki autata?" tace 'just muna watching horror film ka kira' yace "Ok" suka gaisa har Bature, Dady yana cewa ta dawo sunday lallai don monday xa a koma makaranta. Ya tambayi Mimi ta miqa mata wayar tace "Dady ina wuni?" ya amsa 'lfy mamana , ya jikin naki' tace "Lfy lau Dady" yace "to a dunga kula kinji, mumyn ki tananan Kullum tana xancenki" tace "to Dady agaida mumy, bata kusa? Yace "eh taje birthday din friend dinta" ya tambayi yasmin aka miqa mata wayar, itama hira sukai sosai kuma har tafi Mimi sakewa da Dady. Mimi kuwa tunani take shidai dan boko babu ruwansa, da ace yasmin ce yar uwarsu da sakewar da xatayi sai tafi ta Mimi don Dady yadda yakeson yayansa haka yakeson surukansa.



Hira ta balle bayan ajiye wayar Dady, har Audu ya fara hamma yace "ya Bature nidai bari inje in kwanta" yace "Ok nima baccin nakeji amma maryam da maryam (little da Mimi) sun sakani tsakiya ko motsi sun hanani yi don ma gobe weekend" Audu yayi dariya yace "tsofaffi ba kunsan kuna tsoron kuka fara kallah"



Yasmin tace "Tab lallai ma, kan uban can" duk suka juyo suna kallonta. Mimi tace "Anty yasmin lfy " tana haki kamar wacce tayi tsere tace "wani labari akeyi a grp dinmu na skul yanxu a watsap wata friend dinmu xa aiwa kishiya" ta fada tana nuna wayar hannunta fuskarta cike da tashin sense kace ita xa aiwa kishiyar.





Mimi ta dan maida numfashi tace "kai amma har kin bani tsoro wlh na dauka wani abun tashin hankalinne ya faru" tana kallon Mimi tace "akwai tashin hankalin daya wuce kishiya Mimi? Ai wlh da aimun kishiya gara in mutu" duk suka xaro ido suna kallonta cikin mamaki banda Audu don yasaba jin haka.




Mimi tace "lallai Anty yasmin kice randa ya Audu xai qara aure akwai world war 3" ta kalleshi hankalinta kwance sannann ta dubi Mimi da alama maganar da xatai har xuciyarta ba tare da la'akari da yayan mijinta dake xaune ba tace "ai wlh Mimi duk randa Audu yanemi qara mata kasheta xanyi, inkasheshi sannan inkashe kaina" Mimi cikin tsanin kidima tace "duk soyayyar da kike masa?" tace "yes gara in kasheshi da inyi sharing dinsa da wata"




Suka tsit babu me motsi kamar ta danna musu pause πŸ˜„. Bature cikin ransa cewa yake lallai yasmin saiti be isheta ba, koda yake yawancin mata haka suke akan kishi, ashe shi tasa matar data tsaya akan yayi mata alqawari kawai musulmin kishi gareta koda yake komai na Mimi unique ne.




Audu ya katse masa tunani inda yayi dariya ya kalli yasmin don sam be damu da wannan maganar da tayi ba da alamu ya saba ji, yace "kwantar da hankalinki Baby baxaki kashe kowa ba don ke kadaice xaki xama matata a gidan duniya in shaa Allah. Amma fa kinsan baki isa ki hana abani hurul ayni ba a aljannah πŸ˜…" duk sukai dariya jin shaqiyancin sa. Yaja hannun futsararriyar matar sa (inji hajja πŸ˜„) sukai daki. Suma duk suka watse Mimi tabi nata mijin yayin da akabar little ita kadai a dakin baqi.


Bature dariya ya dunga yiwa Mimi wai tabar mijinta sabida yasmin, yanxu yasmin da mijinta yaxo ta gujeta. Kai madallah da aikin yar duniya yasmin.



Ranar lahadi sukai shirin tafiya, duk taji babu dadi don tana da sabo. Little tace "ya Mimi don Allah Baby girl xaki haifo mana me irin gashinki" yasmin tace "harda ma skin colour dinta" Mimi taji kunyar maganar cikinta da sukai a gaban Audu tace "kaji Anty yasmin ni bani da komai ke mukesa ran ki haifa mana twins" ta zaro ido tace "ni da haihuwa kuma ai sainan da 10 yrs kema don bakisan yadda take ba shiyasa kikemun fatan in kuma, amma nasan inkikai kikaji yadda akeji baxaki kuma bari kiyita kwana kusa ba" Bature yana jinsu Audu kuma cewa "eh dake ance miki kowacce mace raguwace irinki ba" suka tafi suna marmarin juna Mimi tace da little "don Allah my little kina gama junior waec Ki taho nan muyi xamanmu kinji, xan fadawa Dady ma" little tace "to in law xanxo muyi ta yawo muna kashe selfie ina sawa social media ina cewa nayi hadu da Sasha Obama" yasmin tace "wlh kuwa yadda xa ai bare yanxu data kuma haske kamarsu tafi fitowa"



Bayan tafiyarsu Mimi ta xauna jugum, duk batajin dadi da suka tafi. Itadai Allah ya dora mata son yan uwanta duk kuwa nisan dangartakarta da nata tana sonshi.




Ya kalleta yasan matsalarta, duk son mutanensa Mimi ta fishi. Besan akwai ragowar matan dake qaunar dangin mijiba sai akanta, koda yake ita Mimi ba dangin miji kawai ba kowa ma so take koda kuwa masu yimata hidima Kullum tana cikinsu ko gani tai mutum baya walwala xata tambayeshi akwai problem ne? In tana da hanyar da xata temaka tana gaggawar kawo qarshen rashin walwalarsa. Wannan shiya siya mata mutunci da soyayya a wurinsu. Yasha ji tana fada musu sudin ba kasassu bane don suna aiki qarqashinta kawai haka Allah ya tsara musu.





Ya qarasa gurinta ya lallabata har yana mata macilili da qafafunsa tana dariya.


***** ****** ****** ******


Wani daren lahadi, lokacin cikin Mimi yakai wata uku daf yake da cika hudu ya fito yayi das a jikinta wanda kana ganinta xaka ankara she is pregnant.


Goman dare ta gama karatun novel din da aka turo a grp dinsu mai suna ZAKISAN KONI WAYE na Ummu maryam. Ta miqe ta kashe kaf kayan wutar dake falo ta nufi bedroom.



Ta tsaya bakin kofar kofar tana kallonsa sanye yake cikin kayan bacci blue me haske yana xaune kan gado ya jingina jikinsa da allon gadon yayinda qafafunsa ke miqe sanbal ya dora system akan qafar yana aiki as usual, fuskarsa sanye da glass wanda yake amfani dashi inyana kallon system don rage hasken, kuma ta hasken system dinne take kallon fuskarsa don dakin babu haske sai na fitilar gefen gado.



Ta taka a hankali ta isa gabansa ta kira ssunansa cike da shagwaba "ya Bature" yana jin yanayin yadda ta kirashi yasan halin ya motsa (shagwaba da kuma rigimar da take masa tunda tasamu ciki) yayi serving aikin da yakeyi kana yayi shutting down din computer ya ajiye kan bedside ya riqota ya xaunar akan jikinsa yace "ya akai Babyn yayanta?"




Ta narke ajikinsa tana shafa sajen fuskarsa da gashin daya kewaye qasan hancinsa zuwa habarsa tace "inason yin bacci ne, kuma kasan bana iya kwanciya ba ajinkinka ba kai kuma naga aiki kake" ya zare glass din fuskarsa ya ajiye yace "ai na ajiye aikin ranki ya dade, kinfi komai mahimmanci a gurina kedai kawai yi baccinki zuciya da jikina duk nakine" ta kalleshi cikin ido takai bakinta daf da nasa har hancinsu na haduwa tace "are u sure?" ya qara hada fuskarsu yace "i m sure soul" ta lumshe ido tana shaqar numfashinsa da yake sauka kan nata hancin tace "Duk duniya babu inda nake xama naji dadi sai kan qafarka, babu inda nake kwanciya naji dadi nai bacci gamsashshe sai qirjinka" ya kamota ya kwantar da kanta a saitin zuciyarsa yace "MARYAM AL' AMIN daka yau na mayar miki da wadannan wurare da kika ambata wajen xamanki da kwanciyarki har abada, duk sanda kike buqatar hakan kixo ki kwanciyarki" tai luf tanajin bugun zuciyarsa.



Washegari monday a wurin aiki mr Alex ya buqaci yaje supervising wani aiki da sukeyi da wata company. Ya fito cikin shirinsa na fita lokacin wani wurin 10:34 AM, Hanifa dake wajen office din ta miqe da sauri tace "sir xakaje wajen aikin ne?" yace "eh" a takaice, ta danyi qasa da murya cikin sigar lallashi tace "to inmaka rakiya mana?" yayi jim yana nazari kamar baxai amsa ba, can yace "Ok taho muje kya rubutamun report " ta dauki jakarta cikin rawar jiki tabi bayansa.





Wani irin farinciki take ciki lokacin da suke zaune bayan motar ita dashi driver na jansu, ta dunga hangosu a matsayin ma'aurata

Please Login or Register in order to submit comment