Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mari, a wannan lokacin Mimi watsi tayi da duk wata na urar dake jikinta ta taso ta nufo mumy da nufin hanata dukan Bature. Sai dai kafin ta qaraso ta fadi qasa.



Ya riga kowa isa inda take ya dagata ya maidata kan gadon ya kwantar, tana kuka yana kuka tana shafa kuncinsa inda hannun mumy ya fito rada rada.




Tana kuka tana cewa "ya Bature karka tafi ka barni gurinsu, zasu dunga yimun wannan tofin ni banaso xan bika ka kaini asibiti."



Be daddara ba ya kuma komawa gurin Dady yace "Dady na tuba karku rabani da Mimi yanxu, she is my wife nd my best friend, nafi kowa iko da ita ku bani abata kota warke ko bata warkeba ina sonta a haka kuma xan kula da ita."



Dady yana hawayen tausayinsu yace "SULAIMAN haqurin dai xakai, gata ake muku kaida ita." yana jin haka ya juya ya nufi qofar fita. Ganin haka Mimi ta fara ihu na fitar hankali tana kiran "ya Bature karka tafi ka barni, ya Bature ina sonka Don Allah karkaimun haka, bazan iya rayuwa babu kaiba" tana yunqurun tashi Faty da Audu na riqeta. Shima Bature yana kuka sharban kamar mace ya bar dakin ko juyowa baiba.



Babu wanda be xubar musu da hawaye ba, da kyar Audu ya danneta Faty tai mata allurar bacci.





Cikin minti bakwai bacci ya fara daukarta, suka cikata Faty ta gyara mata kwanciya. Ta qaraso gurinsu mama tace "mumy anya bamuyi kuskuren raba ya Bature da Mimi ba a wannan gaba? Shi ya tafi yana kuka kamar mace, ita kuma tana ihun kiransa cikin fita hayyaci."




Mumy ta share kwallar idonta tace "Faty inbamuyi hakan ba ya xamuyi? Bature da Mimi basusan komai ba sai soyayyar junansu, kuma indai ba haka mukai masa ba baxai bari ayi mata magani ba" Faty tace "to Allah ya bata lfy. "




Abun mamaki Mimi ko rabin awa bataiba tana bacci ta kuma farkawa cikin ihu, duk kuwa da qarfin allurar da akai mata. Kiran sunan mijinta take tana cewa yazo ya dauketa.




Mumy da Faty suka matso suna mata magana, mama kuwa tana gefe tana kuka. Ta kalli Faty tace "ya Faty kiramun ya Bature indai kina qaunata" mumy tace "maryam yi haquri yaje ya karbo maganin da aka rubuta miki." ta kau dakai daga barin da mumy take tace "ya Faty nace ki kiramun ya Bature inban ganshi ba mutuwa xanyi" Faty tace "Mimi mumy na miki magana" tace "ba ruwana da ita, baxan qara kulata ba tunda ta daki ya Bature" tana fada tana kuka.




Faty tai murmushi tace "mumy kinji lefinki shiyasa akaqi kulaki" mumy jiki a sanyaye tace "yi haquri maryam, bansan xakiji haushiba da ban dakar miki shiba"





Suna haka har yamma tayi, qarfe shida lokacin yan dubiya ya wuce. Likita yaxo Dady ya nemi sallama, babu dogon bincike ya sallamesu dalili kuwa shine suma likitocin yau sha biyun dare dai dai xasu shiga yajin aiki.





Aka dorata kan kujera sukai gida da ita, a lokacin magrib tayi Mimi har tagaji da ihun a kira mata ya Bature ta haqura. Amma tayi jigum babu ci, babu sha babu magana.




Bature kuwa yana fita asibiti anan tashar gyadi gyadi yaji ana ambaton motar Abuja, ya shiga ya zauna take qaramace tana cika suka tafi.





Xuwa laasar yana Abuja cikin gidansa har yayi wanka, bai fitaba har bayan isha ko sallah a daki yake.




Ishaq ya shigo har bedroom din ya sameshi, shima Baqo ne ya kaimasa tsegumin sulaiman ya dawo ya qulle kansa a daki. Ya dafa sulaiman din yana tambayarsa jikin Mimi, bai bashi amsa ba sai kuka ya saka masa kana ya dora da cewa "sun kwaceta ishaq, sun kwacemun maryam kuma mumy ce ta jagoranci kwacemun ita, abunda nake nufi shiya faru wai maganin gida xasuyi mata. Abunda ya gagari likita shi xa a xauna ace xa ayi a gida?" ishaq ya jinjina wannan lamari, kuma shima yana bayan sulaiman don be yarda wai iska ke damun Mimi ba, shi yafi ganin malรกria ce ta haddasa mata wannan ciwon.




Ya danne nasa damuwan ya lallabi sulaiman din da cewar ya bari a kwana biyu suje suyiwa Dady bayani da nuna masa takaddun asibitin sai su taho da maryam din. Dakyar ishaq yasashi yaci abinci ya bashi maganin bacci yasha ya kwanta.





Mrs Hajia ๐Ÿ˜Š
[9/30, 1:05 PM] โ€ช+234 706 296 6299โ€ฌ: ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐ŸผAL 'AMARIN MARYAM ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ


Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)


๐Ÿ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 6โƒฃ1โƒฃ



Saqon masoya na iso mani ta hanyoyi daban daban, ina godia sosai.



Matan Baffa suka fito suna kallon maryam dake zaune kan kujera babu magana, aka shigar da ita har dakin mama. Baffa ya nemi ganinsu gaba daya suka hallara dakin mama harda Rashida wacce ke zaune a gida yanxu.



Baffa yayi musu bayanin lalurar dake damun Mimi kuma ya nemi hadin kansu akan hakan karo na farko a rayuwarta. Duk iskancinsu wannan karon basu nuna ba suka dunga jimantawa suna mata sannu da fatan samun sauqi. Ya gabatar da Aisha a matsayin yar aikin Mimi wacce taxo xama da nufin temakawa Mimi.




Bayan fitarsu mama ta fadawa Baffa Mimi fa babu abunda taci tunda aka kawota kano, ada ana saka mata drip yanxu kuma da suka baro asibiti babu wannan maganar. Yace to tabari yaje sallar isha ya dawo zaisan abunyi.




Ya maza jikin kujerar Mimi yace "maryamu me kikeson ci?" tai masa shiru. Mama tace ai haka take tunda ta fuskanci mijinta baya kusa da koma kurmar qarfi da yaji.




Faty xata iya cewa taji dadin wannan yajin aikin domin ta samu damar jinyar Mimi, daga asibiti gida ta biyosu ya Ahmad ya biyota da akwatinta da ragowar kaya. Shima babu yadda beyi da Mimi ba tai magana taki, Faty tai mata alwala akai akai tai sallah taqi.




Baffa daga masallaci ya taho da wani malamin islamiyya maqocinsu, ya nuna masa Mimi. Yace suyi mata alwala, sukace da alwalarta. Ya fara karanto mata ayoyin korar shedanu amma shiru kakeji, sai da aka fara karanta ayoyin sihiri sannan ta fara ihu da kuka.





Yace a samo garwashi da sauri Rashida taje maqota ta samo, ya xuba turare aciki. Mimi da bata iya miqewa sai gata a tsaye tana neman hanyar gujewa wannan turaren hayaqin. Baffa da Huxaifa suka riqeta dakyar don abun ya girmi mata.




Xan iya cewa aranar babu wanda ya runtsa a gidan sabida ihunta, ko ince har maqota na kusa. Tun malamin nayin abu shi kadai har abun ya gagareshi aka kira wasu malaman. Sunkai 3:00 AM suna abu daya, sun jigata sosai sun gaji itama ta gaji duk jikinta yayi laushi ga ihu ga yunwa. Sai dab da asuba ta samu bacci aka huta.




Duk tajiwa kanta ciwo da wadanda ke riqe da ita. Malamin kewa su Baffa bayani cewa Mimi fa asiri akai mata wanda aka hadashi da aljanu marasa imani kuma haukatata akasoyi don haka wannan aiki sai annemi taimakon wasu malaman wadanda suka fishi sani don abun yafi qarfin mutum daya ko biyu.




Mama dajin haka ta dunga kuka tana cewa ita ba Mimi take tausayiba illah abunda ke cikinta shi da bashi da haqqqin kowa, hankalinta a tashe yake akan haka ganin yadda ake dambe da Mimi take burgima tana murje cikin.





Sassafe saiga mumy taxo da Dady harda wani malami, shima yaxo duba matsalar Mimi, lokacin bata tashi ba. Faty ta lallaba ta tasheta, cikin hukuncin Allah kuma ta tashi qalau sai dai babu magana.




Faty ta taimaka mata tai wanka, ta shirya ta kalleta tace "ya Faty nayi sallah?" tace "a a maryam ana binki salloli da yawa" Faty ta dunga gaya mata sallolin da xatayi da kuma adadin raka oin tanayi harta idar.




Aka kaita dakin Baffa gurinsu Dady, ta dunga kallonsu ba tare da magana ba, sai sune sukai mata sannu da jiki, shima bata amsa ba sai murmushi tayi.



Malamin yana kallonta yace "maryamu meke damunki?" tai shiru, ya kuma maimaitawa har karo 3 amma tai shiru. Ya guntsi ruwan dake hannunsa wanda yaxo dashi ya fesa mata. Ta yunqura da gudu tayo waje tana ihu, duk suka biyota ya bada umarnin a riqeta. Baffa ya riqeta tamau, shi kuma yacigaba da guntsar ruwan yana fesa mata tana tsala ihu kamar ta tsaga gidan.





Dake Dan Adam dai sunansa Dan Adam saiga Anty ta fito tana mitar cewa "wannan wane irin bala i ne? Jiya kin hanamu bacci yanxu kuma munsa haqarqarinmu xamu kwanta kin kuma tada iskancin ihu, ai wlh ko alhakinmu ya hanaki warkewa" wannan magana da Anty keyi karaf a kunnen Hajja wadda ke shigowa yanxu.




Ta qaraso tsakar gidan tana duban Anty fuskarta murtuk tace "jamila anya kuwa ke macece? Shin yarinyarnan itace ta dorawa kanta ciwonnan? Babu tausayi babu kyakykyawar kalma? Babu komai kiyi duniyace babu wanda ya wuce irin wannan lalura kuma inkasan farkonka bakasan qarshenka ba"




Mama tana kuka tace "Hajja ya isa, yanxu ba lokacin maida martani bane, kalli diyata Hajja so ake a haukatamun maryam. Allah karka kashemun yayan nan sukenan kabani guda biyu, Allah ka duba raunina ka rayamun su"





Kalamanta sun bawa kowa a gurin tausayi, malamin yacigaba da xubawa Mimi ruwan addua tana kuka harya qare. Yace zaije ya dawo sai an sake shiri kuma a cire mata duk rings din dake jikinta a barta ta azurfa kawai kana ya bada wani turare yace a shafa mata gaban goshinta.




Suka tafi shida Dady, Baffa ma ya fita kasuwa yana qara jaddadawa mama abawa Mimi wani abun taci. Mumy, mama, hajja dasu Faty duk suka koma dakin mama.





Hajja ta kwance ledar data zo da ita ta fito da qullin rubutu, ta juye a kofi ta bawa Mimi, duk da Mimi a lafiyayyarta batashan rubutu sai dai tofi amma yanxu dai babu musu tasha. Ta samu ragowar ta shafe mata jikinta, kana ta fara cirewa Mimi zubunan hannunta tana mitar cewa "bandaku yaran yanxu aiko wannan ya isa ya kawo muku shedanu, dan masifa zobe hannu da qafa" ta zaresu tas harna qafa ta miqawa mama.





Mumy ta juya kunun gyadan dataxo dashi a kofi tace "Mimi xokisha kinji" tayi shiru, ta kuma cewa "uwata taso kinji kisha" Mimi tsam ta miqe ta koma dokin qofa ta kwanta tana birgima da kuka.




Sukai sukai ta tashi taqi ga gida babu kowa duk maxan sun fice. Dakyar Faty ta lallabata tace mata "Mimi na menene? Me kikeso? Kinga ke kadai nake da ita fadamun duk abunda kikeso in miki kinji" tana sharbe hawaye tace "ni kusamun xobena ya Bature ne ya sakamun"





Hajja tace "baxa asaka miki dan qaniyarki, wannan dagajin maganar ba maryamu bace aljanace ke magana a makwafinta" Mimi ta qara xandara ihu tana turje turje, Faty dataga abun na qoqarin fin qarfinsu taje ta debo rings din gaba daya ta mayar mata hardana qafar kana aka zauna lfy.



Dakyar tasha kunun gyada rabin kofi aka saka mata turaren ta kwanta.




Ranar haka aka yini ana xuwa dubiya, da masu xuwa dan Allah da kuma masu xuwa ganin kalar haukan Mimi. Umman fauxa da hajiyan su Farida anan sukayini ana jimami, ciwon Mimi kuwa ya tashi yafi sau a qirga. Babban abunda ke daga hankali shine yunqurin fita take in abun ya tashi kuma taqi shan koda ruwa tun kunun da tasha da safe.





Haka suka yini qofa a rufe, Aisha da Faty na riqeta. Anty kuwa sai mita andamesu take, itadai Umma babu yabo babu fallasa bata nuna ta damuba kuma batai murna ba da ciwon.



Hajja sai azahar suka tafi tare da mumy, Hajja tace "xa a dunga kawo rubutu Kullum ana shafa mata kuma tana sha Mal manu ne yasa ake mata sauka."




Sai dare Baffa ya dawo tare da malamin, aka kuma xaman ruqiuya suka zagayeta ko wanne yanayi, tana ta ihu sun dade suna abu daya har wajen taran dare kana aka kyaleta.




Aka bada ruwan magani da man xaitun habbatus sauda malamin yace ai mata wanka da ruwan maganin sannan a mayar mata da wadannan mayukan sune na shafawarta koda yaushe.





Mama ta jata taje tai mata wankan maganin sannan tai mata alwala tace tai sallah tace "mama guda nawa xanyi?" mama ta fada mata tayi magrib da isha. Ta tashi tayi, Faty ta shafa mata maganin har gashin kanta.




Mama ta fita kaiwa Baffa abinci, yace taje ta kira masa Mimi. Mama tasata agaba ta kaita, ta xauna gaban Baffa mama na gefe tana cemasa "Baffa Mimi fa har yanxu bataci komai ba tun safe" yace "to ba komai" ya kalli Mimi yace "maryamu saka hannu muci" ta xuba masa ido ba tare da tayi magana ba. Ya fara gutsuro tuwon yana saka mata a baki, babu musu ta fara karba. Yanaci yana bata har suka cinye. Mama ta miqa masa jug din fura bayan ya wanke hannu, furar ma yana kurba yana bata harta suka shanye sannan ya bata ruwan saukar da akayo mata tasha. Aisha ta samo garwashi akayi mata turare ta kwanta.



Wannan daren dai da sauqi sun sami bacci don tunda ta kwanta bata qara tashi ba. Mama da Faty qarfe 4 suka tashi suka fara sallolin nafila har xuwa ketowar alfijir.




Kwana uku da xuwanta xa a iya cewa abun da sauki, an durfafi addua kota ina duk inda malamai masu korar aljanu suke xuwa ake, wani akai Mimi wani kuma yaxo har gida.



Babban abun tashin hankalin ciwonta shine yunqurun fita waje a duk sanda ciwon ya tashi. Wani maganin in anyi ciwon ya lafa wani kuma ya tadashi. Kudi kota ina kashesu ake, Dady yayi Baffa yayi sannan Audu ma yi yake kamar shine mijin.




Anty Kullum cikin mita take a cewarta wai Mimi taje Abuja xatai musu iyayi da nuna iyawa irin wacce ta saba su kuwa yan matan Abuja suka korota tare da haukatata, mijin kuma dayaga ta haukace ya kawota gida ya ajiye yaje yana holewarsa da yan mata.




Abun takaici kuma a gaban Mimi take furta irin wadannan kalaman, intana fada Mimi kan xura ido taitai kallonta.




Rashida kuwa har kusan tsine mata Anty tayi a cewarta wai Rashidan taqi sharar masallaci tanayin ta kasuwa, ko kuma tace "Rashida haka kikaga yafi miki ko? Kinqi xaman gidanki kinxo kina jinyar mahaukaciya.





Rashida kuwa duniya ce tai mata atishawar tsaki, domin mijinta irin maxan nanne masoyan mata ganin yana da kudi haihuwarta daya yayo mata kishiya. Ta tada hankalinta sosai ta fara yimata mugun hali da tsangwama kamar yadda tayiwa Mimi a baya, yarinyar mai wankakken ido ta ware bajewa Rashida makirci wanda takai har saรญda mijin ya korota gida da saki daya.




Rashida da Anty hankalinsu ba qaramin tashi yayiba, sunso rufe maganar sakin kar kowa yaji sannan ya maidata dakinta. Amma mijin yayiwa Baffa aike cewar azo a kwashe kayan Rashida xai amfani dakin. Baffa yazo ya rufe Anty da fada kuma ya fasa maganar sakin a tsakar gida, babu kunya Umma ta dunga sheqa dariya tana cewa Anty uwar bazawara tare da tutiyar ita ba a taba sakin yaranta ba. Da gorin Umma ya ishi Anty sai tasa Rashida a gaba sukaje har gidanta suka bawa mijin haquri tare da roqonsa ya maidata. Dake lokacin giyar amarci na kwasarsa suka hadu shida amaryarsa suka ciwa Umma da Anty mutunci.




Labari ya iske Baffa shima ya kuma ciwa Anty mutunci kuma yace su yayansa ba a abun wulaqantawa bane tun daga kan Mimi ya dawo daga rakiyar a sakar maka ya ka dunga roqon a maidata domin bakasan bala in daya hanata xama ba gidan mijin.



Da Anty taga babu nasara a wannan bangaren saita tsiri takurawa Rashida da gori a nata dabbacin tana ganin hakan zaisa Rashida ta gaji ta koma gidan mijin ta xauna qarqashin wulaqancin miji dana kishiya. A bangare guda kuma ga Umma Kullum tana gorantawa baxawara da uwarta (dama ance abunda kai shi ake maka, abaya ai da ita da Umma babu abunda basuyiwa Mimi da mama ba)




Da bala'in Anty ya ishi Rashida saita koma dakin mama gaba daya take xaune dakin Mimi. Domin maman dai da suka raina suka kuma dauka maqiyarsu ita kadai ke tausayawa Rashida da kwantar mata da hankali. Rashida gaba daya tayi sanyi, har yanxu tana kunyar mama da Mimi bisa abunda ta dunga yimusu a baya gashi yanxu sun saka mata da alkhairi.





Tun Faty da mama na dari dari akan Rashida karta cuci Mimi har suka saki jiki don sunsha gwadata su barta ita da Mimi su kadai a daki amma sukan samu komai lfy koda ciwon ya tashi Rashida bata bari Mimi taiwa kanta lahani sai dai suyi ta kokawa da Rashidan wani sa in harta jimata ciwo.



Dakin mama cike yake, gata, ga Mimi, Rashida, Aisha, Faty da yan jikokinta. Safe xuwa dare kuwa ba a raba gidan da baquncin mumy Umman fauxa hajian Farida sai yasmin.




Duk da Umma ta sararawa Mimi qiyayya tun lokacin bikin jafar amma yanxu abun yana neman dawowa, dalili kuwa kulawar da Baffa yakewa Mimi don yanxu babu mai kwana a cikinsu Baffa kan shafe dare yana xarya tsakanin dakinsa dana mama yana ganin lfyar Mimi. Mama kuma bata da shamaki a dakin yanxu koda wane lokaci shiga take, wannan dalili yasa Baffa yace babu xancen raban kwana sai bayan warkewar Mimi don sau tari Mimi da mama a dakin baffa suke kwana in ciwon ya tashi.




Wannan dalili ya sabun tawa Umma qiyayyar Mimi wacce ta kwanta a dalilin kyautatawar Mimi ga yayanta. Tana ganin Baffa yanawa Mimi soyayyar da ko yayan cikinsa bayayiwa.





Anasa bangaren Baffa tausayin Mimi yake sosai da santa fiye da kowa cikin yayansa domin yarinyar taga iftila 'in rayuwa kala kala.



****** ******* *********



Yau satin Mimi daya a kano, malamai sun sami kudi ba kadan ba a jikin su Dady, kowanne yana kwada tasa baiwar.




Jiki kam Alhamdulillah ana ganin sauqi sai dai babu magana sai dai tai jugum tana tunani. Magani kuwa sunkai buhu uku a dakin mama dana sha dana wanka sai kace yar mai ganye.





Ranar dai data cika sati ta kama monday, Rashida ta tafi aiki. Faty da Aisha sun fita Aisha taje raka Faty banki gida ya rage sai mama, a lokacin ne ciwon Mimi ya tashi, ta dunga ihun kuka tana burgima kamar yadda ta saba, mama ta dunga yunqurin riqe Mimi amma abun yafi qarfinta don tuni Mimi ta wullar da mama gefe guda tai hanyar waje, mama ta taso da gudu ta kuma riqe mimin. Mimi ta kuma angijeta tana cewa kirana ake yanxu xanje in dawo.




Duk wannan abunda ake Umma da Anty na ganinsu amma babu wacce tai yunqurin taimakawa, sai Umma ce ta miqe ta rufo qofar tsakar gida ta koma ta rabe wai tsoron Mimi take karta daketa. Anty kuwa tana xaune tana sakace tace "yo kaje a illataka ? tunda haukan ya motsa da akwai igiya kusa dana leqa ankira maxa an daureta."




Temakon Allah baya yankewa ana cikin haka saiga mumy da Audu ya kawota, mumy da Audu ne suka hadu aka riqe Mimi aka maidata daki dakyar. Aka kunna saudi qur an.




Mumy taiwa Anty tas da cewa "wanda yayi da kyauma yaya ya qare jamila bare ke da Kullum cikin aibata yayan mutane kike, da kina da hankali da kin gane mugun bakinki ga Mimi ya jawo mutuwar auren Rashida amma dake kedin jakace har yanxu baki karatun ta nutsu ba. Kuma Mimi batai gadon hauka ba dan haka ciwonta bana hauka bane." Anty tayi qus domin ta tsani a goranta mata mutuwar auren Rashida wannan abu shine weak point dinta yanxu.




A cikin satin jafar yaxo daga KD. Hankalinsa yayi mugun tashi lokacin da Anty ta sakashi a gaba ta fada masa karya da gaskiya akan ciwon Mimi. Kamar yadda take fadawa duk wanda ya shigo gidan cewa Mimi hauka take muraran kuma ta fita tsirara sai qarti ke shigowa da ita. Shi kuma Bature tunda yaga ta haukace ya sakota mota ita da me aikinta ya korosu kano har yanxu be kuma xuwa ba. A fadarta.



Ya tausayawa Mimi sosai, ya dunga xagin Bature a xuciyarsa ashe duk soyayyar da yake nunawa maryam yaudarace tunda har ya gujeta a halin lalura. Yasa ransa cewa lokacin da xai auri maryam yayi, koda Umma xata tsine masa saiya aureta, abunda kawai zai hanashi aurenta yanxu a halin lalura shine cikin jikinta inbayanshi da ahaka zaisa Baffa ya aura masa ita don ya nunawa duniya yana sonta.




Amma xai jira ta haihu, ya aureta ya riqe mata danta kamar shine ubansa, tunda ko bai aureta ba ai dan maryam dansa ne.



Shida yaxo da nufin yagaidasu ya koma a ranar saiya bige da kwana. Yaje gidansa xuwa yamma ya dawo, ya tarar Baffa da Mimi xaune akan tabarmar tsakar gida. Mimi na gefen Baffa yana bare mata dafaffiyar gyada yana xuba mata a hannunta taci.




Ya qaraso ya tsuguna yana cewa "Baffa ashe kana cikin gida, ai na axa baka dawo ba" Umma tai karaf tace "ai dole ka ganshi gida yanxu yar gwal babu lfy, yine yake jinyarta" yayi shiru babu wanda ya tanka mata. Jafar ya qurawa Mimi, ta rame sosai tayi duhu sai dan ciki kadan daya bayyana jikinta. Yayiwa Baffa jajen jikin Mimi, Baffa ya fada masa cigaban da aka samu. Anan suka xauna har magrib sukai jam'i daganan aka kawo musu abinci, kamar yadda suka saba Baffa naci yana bata tanaci har suka gama.



Mimi dai sauqi ya samu sosai, sai dai babu magana sai dai tai tabin mutane da kallo. Babban abunda ke damunta maganganun Anty na cewa Bature yaga ta haukace ya kawota gida ya ajiye, tun Mimi bata ganewa harta gane ta fara fuskantar maganar Anty fa gaskiyace tunda gashi tunda ya kawota kano ya ajiye ko awaya be kuma nemanta ba.



Taso qullatarsa bisa wannan abun da yayi mata, amma xiciyarta taqi bata hadin kai musamman inta duba farkon ciwonta acan baya irin yadda ya dunga jinyarta yana kulawa da ita. Sonsa take kewarsa ta dameta ainun, ciwonta kanyi kwanaki bai tashi ba amma babu magana.




***** ***** ******* ******




Acan Abuja kuwa Bature wata irin rayuwa yake me cike da loneliness. Baya kula kowa baya shiga shirgin kowa, yakanje aiki ya yini yana aiki babu hutu, wani sa in har dare yake kaiwa acan. So yake ya manta da Mimi da duk wasu mutane dake kano sabida abunda sukai masa. Amma hakan ta gagara don Mimi batai masa lefin komai ba, hasalima sun rabu tana ihun cewa baxata iya rayuwa babu shiba ba. Ya fige ya lalace ya tara gashi cunkus kansa da fuskarsa. Ishaq sai ya gaji da rashin ganinsa yake xuwa gidan, yayi fadan, yayi lalllashin, yayi nasihar , amma duk a banxa domin Bature ya xama kamar wani motsatstse. A office mr Alex yana tausaya masa yana masa nasiha, amma duk

Please Login or Register in order to submit comment