Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita dashi, inama hakan azahiri ne da matsawa xatai jikinsa ta kwanta kan dantsensa tana wannan mafarkin har suka isa wurin.




Sun jima a wurin sosai don an dan samu mushkila, yatsa ya dudduba wurin da ake buqatar gyara yayi musu gyara, yayin da Hanifa ke gefe ke rubuta duk abunda ake.



A gajiye suka fito lokacin ankusa sallar azahar, garin yadau xafi sosai irin zafin damuna ga hadari ga kuma rana ta kwallare, suka shige bayan mota ya bawa driver umarnin ya qure AC shi kuma ya rage rigar jikinsa ya bar shirt ya sassauta tie din wuyansa.




Ya jingina bayansa a jikin motar kansa yanadan sara masa ya gaji sosai, kwatsam ya tsinci muryar Hanifa tana cewa "sir tunda mungaji mudan biya gidanka musha ruwa muyi lunch mana sai mu koma" yayi shiru yana tunani kafin yace "to shikenan muje" ya bawa driver umarnin ya wuce dasu gida" Hanifa kamar ta xuba ruwa qasa tasha don dama bata taba xuwa gidan ba, lallai asirinta yana tasiri akansa inba dan haka ba aiko kafin yayi aure bai taba kaita gidansa ba balle yanxu da yayi aure.





Suka shiga cikin gidan ya jagoranceta har main falo, ta xauna kan doguwar kujera kusa dashi. A kaikaice take kallon maka makan pics din Dake falon wato window size, Bature ne da Mimi a pics din wanda yafi jan hankalinta shine wanda suka dauka ita Mimi sanye da weeding gown wacce ta matseta tsam ta saqala hannyenta a wuyansa tayi qasa da kanta tana dariya, shi kuma sa hannayensa ya zarge qugunta ya hadata da jikinsa yana kallonta cikin soyayya, daganin pic din anyishine ranar dinner dinsu ta aure don kayan da suka saka ranar ne hanye jikinta. Sai wanda suka dauka tana sanye da baqaqen kaya riga da skirt ta riqe jar flower a hannunta shima baqin suit ne a jikinsa sun zarge hannun juna suna tafiya akai pic din wato walking picture suna kallon juna suna dariya. Ta hadiye wani abu wanda xa a iya kira baqin ciki da kishi tace a xuciyarta, Allah ka nuna min ranar da sulaiman zaimun irin wannan daqumar. Ya dauki wayar landline ya kira kitchen ya sanar yana da baquwa, kuku yayi saurin kawo ruwa da lemo sai snack ya fadamasa bai gama abinci ba amma ya kusa qarasawa yana mai bashi haquri da cewa besan xai dawo da wuri ba. Ya daga masa hannu alamar yaje, babu bata lokaci ya bar wurin.




Hanifa ta dauki fork ta faracin fruit din dake kan try, ta ciro pawpaw ta nufi bakinsa da ita, ga mamakinta saiya bude bakin ta saka masa. Ta qura masa ido yana taunawa, yayi dan murmushi yace "wannan kallonfa kamar baki sanni ba?"




Direct ta fara magana "sulaiman inasonka, ni kaina bansan irin wannan so da nake maka ba. Ya dace ace na rabu dakai tun lokacin dakai rejecting dina kayi aure, amma natacciyar zuciyata taqi bani hadin kai, Kullum da axabar sonka nake kwana nake tashi da ace nasan yadda xanyi in cirewa kaina wlh da nayi, amma dake Allah ne ya jarabceni dashi bani da mafita. Sulaiman bani da burin daya wuce in wayi gari ingannin a matarka dubeni sulaiman Kullum girma nake babu aure sabida soyayyarka" ya qurawa Hanifa ido tana kuka wurjanjan, kuma alamu ya nuna maganar da take babu qarya ciki don irin maganar nance wadda ke fitowa daga zuciya.




Tausayinta ya kamashi tabbas yasan tana sonshi amma bai zaci abun yakai haka ba. Ya fara magana cikin kwantar da halshe da lallashi "Hanifa kiyi haquri karki daukeni a mayaudari, mara tausayi ko wanda besan darajar soyayya ba. Baxan iya cemuki komai ba tsakanina da Mimi, abunda kawai nasani in na hada soyayya Mimi da wata xan xalunci dayar kuma baxan iya adalci ba"




Ta katseshi ta hanyar kwanciya a qirjinsa tasa hannu ta balle botiran rigarsa guda biyu ta zira hannunta tana wasa da gashin qirjinsa tana shafa nipple dinsa. Har yanxu hawaye ke tsiyaya a idonta. Ganin halin da take ciki yasa be hanata ba, saima hannu da yasa ya shafar bayanta a hankali jikinsa yana amsar saqon data ke aika masa.




Bata taba samun irin wannan damar akansa ba, wai yau itace bisa qirjin Bature har tana wasa kuma yana lallabata cikin kissa ta fara magana "Bandamu da rashin adalcinka ba sulaiman, ni dai burina in ganni a matarka koda kuwa a matsayin sadaka (kwarkwara) in hakan ta faru na rantse da Allah xan maka biyayya kuma xan yiwa matarka biyayya." cikin tausaya mata yace "Hanifa baza ai haka ba kidena ma fada, darajarki ta zarta ta sadaka kuma nidin ma ba sanki ne banayi ba just ina tsoron azabar ubangiji in na kasa adalci amma ki bari.........., "



SULAIMAN! Ya tsinci muryar Mimi ta kirashi wanda shiyayi dalilin katse masa maganarsa. Yakai idonsa kanta tana tsaye jikin bene wanda ke nuna alamar sakkowatta kenen hannunta riqe da qarfen benen na silver, idonta waje kamar xai fado xai iya cewa bai tabajin Mimi ta kira sunansa ba kai tsaye sai yau. Don haka yayi gaggawar janye Hanifa daga jikinsa, amma yana xaune ya kasa motsi kamar an dasashi a gurin.




A nata bangaren Mimi bata dade da barin falon ba taje sama tayi wanka saboda azabar zafin da ake tayi sallar azahar ta sakko kenan ta tarar da wannan aikin mijinta rungume da wata mace acikin gidansu na aure wannan al amari yayi matukar kidimata.




Ta qaraso kusa da inda suke xaune cikin bacin rai idonta rufe ta fara nunashi tana magana "sulaiman? Abunda kake kenan? Yau Allah ya tauna maka asiri don wulaqanci duk abunda kuke a office bai isheku ba sai kun biyo ni har cikin gidan aurena" yayi saurin tashi ya riqeta ganin ta horonce musu, ta fusgeta daga riqon ya kuma kamata nan take suka fara kokawa tana cewa karya tabata da hannunsa me dattin zina.





Dakyar ya kama qugunta ya riqe tsam dole ta dakata da kokawar, yace cikin rudewa "maryam me mukeyi a offfice din? Kardai zargina kike?" ta tareshi cikin masifa da hayagaga tace "zina kukeyi mana, kukayi acikin gidana ma bare a office wanda babu mai ganinku sai Allah" ta fincike jikinta daga nasa cikin tsabar masifa, ganin inbai cikata ba zaiwa Dan cikinta illah yasa ya cikata, ta nufi kusa da Hanifa dake tsaye tana kallon yadda Mimi ke casa sulaiman ta fara magana.



"ke kuma karya qazama taxi no garage sabida tsabar rashin class karuwancin naki har gida kikebin maza a memakon ki bari yaje kungi, banxa jaka barauniyar miji" wannan zagi yayiwa Hanifa ciwo kwarai wai yau ita ake kira da karuwa. Takai ido kan cikin jikin Mimi tabbas badon karta daki Mimi ta ballowa kanta tashin hankalu ba da wlh rufeta xatai da duka sai dai duk abunda xa ai ayi amma tasan yanxu inta daketa xata iya janyo mata bari, Itama cikin tata masifar ta tasowa Mimi "ke ni kike kira karuwa do.......,"





Bature yayi saurin tareta "ke ya isa haka da Allah kar kicemun komai inba haka ba in saba miki wlh" ya juya ga Mimi dake huci kamar ta rufesu da duka shi da Hanifa haqiqa hankalinsa ya tashi don baisan haka Mimi take ba. Ya qara riqota yana cewa "maryam don Allah kiyi haquri karki....... " bai kai qarshe ba ta fusge tace "kai sulaiman karka kuskura ka qara kai hannunka jikina don ni ba qazama bace irinka kuma ka s..... " ya hade bakinsa da nata ba tare data qarasa ba, tsotsarta yake kamar xai maidata cikinsa sai da ya tabbatar ta gama xuwa hannu kana ya cire bakinsa ta koma jikinsa yabar ta kwanta yana ganin haka ya dagata cancakas yayi saman bene da ita.




Hanifa tai mutuwar xaune ganin wannan abun, anci mata mutunci xata rama an hanata sannan kuma ya qalailayeta da soyayya sunyi sama lallai wannan yarinya jikinta da zaqi yake inba haka ba irin wannan rawar jiki da sulaiman yake akanta tayi over. Ta miqe cikin sanda ta bisu sama don taga qarshen film din.





Ta samu qofar dakin a bude kamar yadda ta xata don shauqi ya hanasu rufewa bayan haka kuma shi ke dauke da ita a hannunsa don haka bashi da damar rufewa. Dake gadon saitin qofa yake kallo acan ta hangosu kwance yana kwada mata wata irin soyayya, ta runtse ido da sauri ta nufi qasa tana dana sanin wannan gani da tayi musu.




Ta dauki jakarta ta fice gidan da sauri tana kuka kala biyu, na farkรด Kukan cin mutuncin da Mimi tai mata na biyu kuma kukan ganin da tai musu a halin auratayya wato Mimi bayan cin mutuncin da tai mata aka hanata ramawa har saka mata yayi da tsadaddiyar soyayya?



Su kuma a nasu bangaren sai bayan angama kashe arna sannan Mimi ta fara masa bore da kuka hadi da bugunsa wai ya cuceta ya shafa mata dirty. Ya samu ya riqeta jikinsa yace "maryam na rantse da wanda raina yake hannunsa ban taba zina ba, akanki na fara sanin ya mace, tabbas bani da mafita tunda kin ganni da Hanifa cikin wani hali amma wlh yaune farko kuma shima din lallashinta nake wlh ba abunda kike nufi bane ki bari inyi wanka in dauko miki qur ani in rantse" ta toshe masa baki tace "na yarda ya Bature basai ka rantse da littafin Allah ba, amma dan Allah kar ka kuma kawomin ita gidana" ya tsuguna gabanta yace "in shaa Allah shine farko kuma qarshe"



Yayi saurin canja topic don Mimi yau ta bashi tsoro yace "amma in anjima xamu kuma yi ko?" ta hade rai tace "fatana Allah yasa wannan jaraba taka karta xubar da cikin" ya matsota yace "waya fada miki? Kefa sokuwa ce ai kwari zai kuma yi kuma sannan baxaki sha wahalar labour ba in kinxo haihuwa" tsakaninta da Allah ta yadda tace masa "haba?" yace "yes my luv, kedai kawai kita bani ina rage miki aiki" tace "to ya Bature kamar kuwa kasan ana fadar wahalar haihuwa" ya gyada kai a ransa yace yaro dai yarone, yaro man ๐Ÿ“.Ya
dagata suka shiga toilet.



A daren Hanifa kusan kwana tayi tana kuka don abun sosai ya taba zuciyarta. Koda gari ya waye batai niyyar xuwa aiki ba don mugun haushin sulaiman takeji ga kishin ganinsa a shinfida da Mimi.



Can tsakiyar rana xaman kadaici ya isheta ta fito falo, tayi breakfast ta tambayi yan aikin gidan ummanta, sukace ta fice tun safe. A daddafe tai wanka ta tsira doguwar riga idonta yayi luhu luhu kanta kuwa kamar ya fashe sabida kukan data sha.



Gidan gwaggoriya ta nufa, tana xuwa ta samu gidan cike kamar koyaushe anata shelele, batare da tace komai ba ta shige bedroom din gwaggoriya ta kwanta kan gado, ganin Hanifa burkice yasa gwaggoriya ta sallami abokan shashancinta ta shiga dakin.



Ta yiwa Hanifa tambaya takai sau shida amma Hanifa ko kallonta bataiba tana kwance idonta kan rufin dakin, dole data gaji tai shiru tana kallon Hanifa da tunanin meya sameta haka?



Dan kanta ta tashi zaune bayan wani lokaci ta riqo hannun gwaggoriya tace "inada wata matsala ne a rayuwata bayan sulaiman?" sai hawaye wani na korar wani. Gwaggoriya ta qura mata ido cikin tausayi ganin yadda take kuka harda shashsheqa ita dai tanason Hanifa kuma batason take sawa kanta son sulaiman over don sunsha yawo a kansa da kashe kudi gurin bokaye.



Tace cikin tausayi "ya isa fadamun meya faru" Hanifa ta koro mata duk yacce akai jiya a gidan sulaiman din. Gwaggoriya tace "lallai wannan yarinya ta cimiki mutunci kuma wlh sai tayi danasani don lokacin dena kukanki yayi Hanifa, ki share hawayenki don dama ko bakixo ba xanje gurinki. Wata malama muka samu aikinta kamar yankan wuqa" cak Hanifa ta tsaya da kukanta tace "malama ko malami?" "malama macece" gwaggoriya ta amsa mata, Hanifa ta yatsina fuska tace "abunda maxa suka kasa shine xanje gurin mace? Allah ya kiyaye" gwaggoriya tace "kefa banxa ne Hani, wlh ta iya aiki kusan 2wks kenan da naje gurinta taimun aiki akan wata matar qusan gwamnati da nakeson a hadamu, tana bajemun aiki saiga matar har gidannan taxo nemana. Abunda yasa ban fada miki lbrinta ba bari nayi taimun aiki inga kalar bajintarta don banaso kiyi ta kashe kudin ki abanxa, amma tunda naga buqatata ta biye kece wacce na fara ayyana xan kai mata" Hanifa badan ta gamsu ba tace "to yaushe xamuje?" tace "yanxu xan watsa ruwa muje ai ba a bori da sanyin jiki" gwaggoriya ta tashi ta shirya a gurguje tace da Hanifa "akwai kudi a gurinki?" Hanifan tace "ko babu sai incire a ATM" suka fita suka hau motar Hanifa suka tafi.





Suna tafiya Hanifa ta kasa haquri tace "anya kuwa gwaggoriya ba fasawa xanyi ba? Jikina yana ban kawai yar 419 ce ba malama ba" gwaggoriya tai saurin bige mata baki da cewa "yimun shiru, indai kasa shakku akan aikinta ba yaci."




Suka isa unguwar can bayan gari babu mutane sosai, kuma gidane dan matsakaici maana ba kyau babu muni. Basu tarar da kowa ba sai wata a tsakar gida alamar maid ce, ta gaishesu tace "tana ciki uwar gidan" suka shiga.



Hanifa tai mamaki, sabanin malaman tsibbu data saba gani wannan fes take ga falo da kayan alatu dai dai irin namu na talaka, tana xaune kan kujera da wani murtukeken carbi tana taunar cingam.




Ta washe baki tana musu maraba alamar tasan gwaggoriya, suka gaisheta, kallo daya xakai mata kasan yar duniya ce ajin qarshe don alamu sun nuna ada can antaba bariki.



Gwaggoriya ta gabatar da Hanifa a matsayin qawarta sannan tai mata bayaninta tun farko har xuwa jiya akan sulaiman. Matar ta saita madubinta na tsafi saitin Hanifa, ta fara kallon cikin mudubin. Ita kuma Hanifa gabanta kamar xai fado duk da ba yau ta fara ziyartar irin wannan wurin ba amma yau ta rasa dalili duk a tsorace take.




Tafi minti 5 tana canjawa madubin gurin xama tare da kallon cikinsa kuma duk inda ta juyashi saita sashi saitin Hanifa. Ta gama naxarinta ta dago ta dubesu ta fara magana "kinsha wahalar bin malamai akansa amma haqarki bata cimma ruwa ba, duk wadanda kike bi suna iya qoqarinsu suyi miki aiki amma sai dai kash! Basa duba taurarin da suka dace da aikin" Hanifa da gwaggoriya suka dubi juna a tare, tacigaba da cewa "Duk da matarsa na yawan bata miki shiri da addua amma da anbi aikin bisa tsarin taurarinsa da tuni ankai gaci" Hanifa tai saurin tarar da cewa "yanxu meye abunyi ki taimakeni don Allah" ta dagawa Hanifa hannu alamar ta dakata sannan tace "ba a katseni in ina jawabi don nima fadomun ake ina fada" Hanifa ta qunshe bakinta tayi gum.





Uwar gida taci gaba "inbaki kawar da matarsa ba baxaki taba nasara a kansa ba don ko kinyi aiki xata bata miki, kuma shidin ma ai akwai aikinki a jikinsa don yana da raayi a kanki amma baxai tasiri ba sai kin kauda ita. Gashi kinyi dace akwai abunda ya dauke mata hankali daga yawan addua yanxu ,bayan haka ma baxamu wahala sosai ba wajen aiki akanta don acikin makusantanta akwai wanda ke aikin rabasu ita da shi." tai shiru alamar ta gama magana, Hanifa cikin imani da abunda akace tace "to yanxu ya kike ganin xa ai?" gwaggoriya kuma cewa tai "kawai a kasheta sannan ayi masa aiki ki shiga gidan kamar yadda tayi masa"





Uwargida ta kuma haska Hanifa da mudubinta wacce duk lokacin da akayi hakan Hanifa sai gabanta ya fadi. Tace "Sam ba asiri tai masa ya aureta ba kuma bata asiri, kawai hadine na soyayya." ta dubi Hanifa tace "kina da zabi guda biyu, na farko kodai a nakasata ta hanyar illata wata gaba jikinta, ko kuma a haukatata. Wannan sone kawai abunda xa a iya yi mata bayan haka babu damar raba aurensu ko kuma rabata da duniya" Hanifa ta kalli gwaggoriya cikin neman shawarar abunda ya kamata ayi.


Uwargida ta kuma kallon Hanifa tace "tana da ciki ko?" Hanifa taimata kallon mamaki, lallai aikin matarnan data raina xaici tunda harta gano cikin dake jikin Mimi. Uwargida ta katse mata tunani da cewa "inkina tunin akwai ko babu fa aiki baxai ba, don dole sai ansan matsayinta xa ai aikin" cikin imani da matar Hanifa tace "tabbas tana da ciki amma qarami ne"
Uwargida ta miqe ta fita waje ba tare da magana ba. Hanifa da gwaggoriya suka rikice da sambatun ingancin aikinta, Hanifa cewa take "wlh ji nake kamar na auri sulaiman, maryam kuwa in shaa Allah saita xama abar bawa sadaka akan titi wai ni ta kira da karuwa hmmm" tai kwafa.




Dawowar uwargida tasa sukai tsit, ta shigo dauke da wata mage qatuwa baqa wuluk ta akwantar da ita a gabanta. Ta kallesu tace "ki qaddara wannan maryam ce a xuciyar ki, sannan wannan mage tana dauke da ciki a jikinta kamar yadda maryam ke dauke dashi. Yanxu ki qaddara gaki ga maryam kuma kidau fansar abunda tai miki amma fa banda kisa" ta miqawa Hanifa wani qaton dutsen wuta, tace wannan dashi xaki amfani ki daki duk inda kikeson ya nakasa jikin ta.


Hanifa cikin tsananin farin cikin son daukar fansar cin mutuncin da Mimi tai mata da kuma baqaqen maganganun da har yanxu takejin sautinsu a kunnenta ta daga dutsen wutar ta bugawa magen dake kwance a gabanta a qafarta. Magen ta saki kukanta da qarfi "miyau" ta kuma dagawa xata kwada mata a daya qafar gwaggoriya ta tsaidata, "Hanifa me kikeyi haka kenan?" cikin farinciki Hanifa tace "gurguntata xanyi shegiya naga da qafar da xata dunga tafiya tana kada wannan qugun kinga kona aureshi ta gurgunce nice keda gida ko?"





Cikin takaici gwaggoriya tace "Dan bura ubanki ke wace irin jaka ce? duk wannan wahalar da mukasha a iya gurguntata xaki tsaya? Dagawa xaki ki daketa aka ta haukace ta shiga duniya ta haife cikin acan, kina aurensa gida ya xama naki keda yayan da xaki haifa ita kuma bai ganta ba balle abunda ta haifa suqare ita da Dan akan titi cikin hauka"




Uwargida ta kalli gwaggoriya cikin jinjinawa da baqar xuciyarta tace "gaskiya Hajiya kin iya mugunta ๐Ÿ˜‚" Hanifa cikin sauri tabi shawarar gwaggoriya ta daga qaton dutsen iya qarfinta ta bugawa magen akanta cikin rashin tausayi da imani, dakin ya gauraye da kukan magen cikin azabar da akai mata. Tanata birgima a gurin kunenta na zubar da jini, kimanin 17 minutes tana abu daya kwanin tausayi kana ta tashi dakyar tana dingisa qafa tana janta tai waje da gudu tana ihu.





Bayan fitar magen matar ta dubesu tana dariyar mugunta tace "aiki ya cika yadda wannan magen tayi haka xataita ciwo kafin daga baya ta shiga duniya a matsayin mahaukaciya me dauke da ciki. Kowane lokaci daga yanxu labarin haukacrwarta xai iya xo muku"





Hanifa ta kalli gwaggoriya bakinta yaqi rufuwa "qawata nagode da wannan shawara kinga ai duk san da yake mata ai baxai xauna da mahaukaciya ba ko?" gwaggoriya tace "inma xai xauna da ita ina xai ganta tashiga duniya?" sukai dariya cikin farinciki harda tafawa.


Hanifa ta maida kallonta kan uwargida tace "shi kuma me xa ai masa hankalinsa ya dawo kaina?" uwargida tace "babu komai, ai na fada miki da aikinki har yanxu a jikinsa itace ta hana aikin tasiri sabida taurarinta da nasa in sun hadu aikin asiri baxai tasiri ba, amma tunda kin kauda ita yanxu komai xai tafi dai dai. Maryam dai anshiga duniya sai dai uwarta ta haifi wata"




Kudi sosai ta cajesu akan aikin, babu wani jimami Hanifa ta biya suka tafi suna mata godia ita ma tanai musu. Suka hau mota suna hirar haukan Mimi suna dariya harda tafawa. Hanifa tana cewa xataso ganin Mimi a halin hauka ta fada mata cewa itace tai mata aiken a matsayin ramakon biki. Gwaggoriya tana tuqi tace "shegiya illah biyu kikai mata kin gurguntata kin haukatata" suka kwashe da dariya suka tafa. Kamar bazasu mรบtuba anbasu tabbacin zasuyi jiran duniya. Ta kai gwaggoriya har gida sukai sallama ta koma gida ta fara ramuwar baccin da batayi ba jiya.




Allah ya kiyashemu tabewa (amiiiinnn)



Mrs Hajia ๐Ÿ˜Š
[9/30, 1:05 PM] โ€ช+234 706 296 6299โ€ฌ: ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐ŸผAL 'AMARIN MARYAM ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ๐Ÿ™†๐Ÿผ


Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)


๐Ÿ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 5โƒฃ8โƒฃ



Kwana uku a tsakani, tana zaune da yammaci ita kadai sai yan aikin gidan wadanda suka kammala aikinsu suke tayata hira kamar yadda suka saba. Amma yau abun babu armashi domin uwar dakin nasu yau bata da walwala ko kadan, duk da ba hade rai tayi ba amma abun nasu babu armashi don basu saba ganin haka a gurinta ba. Sun maida hankalinsu kan kallon TV, yayin da ita kuma ta xuba tagumi tana tunani.



A haka ya dawo ya taddasu, suka dunga yimasa sannu da xuwa suna fita. Ya xauna kusa da ita, ga mamakinsa bata kulashi ba ko nuna tasan yana gurin a tunaninsa bata lura da xuwansa ba saboda zurfin tunani. Ya kira sunanta "Mimi" ta tago ta kalleshi na yan seconds kana ta maida taguminta, babu sannu da xuwa, babu drinks din data saba kawo masa inya dawo, babu rage masa kayan jikinsa balle aje ga hada masa ruwan wanka.



Ya tashi ya nufi kitchen, aransa yana tunani. Ada can yasha ji ana cewa Mimi miskilace ta gaske amma bai dau abun da wani mahimmanci ba balle da suka xauna yaga kyawawan halayenta, amma yanxu kam yaga illar wannan muskilancin. Yau kwana uku kenan tana masa halin ko in kula ko kuma yace tana gaba dashi, domin bata tanka masa kuma inyayi mata magana iyakacin amsarta eh ko a a duk da cewa na yau yafi tsanani.




Ya dakko ruwa yasha kana ya dakko lemo ya xuba a cup ya nufo falo, yasha rabi kana ya rage mata kamar yadda ya saba duk sanda yasha ruwa ko wani abun saiya bata ragowarsa tasha. Ya nufi bakinta da cup din, ta bude tashanye lemon tas ya ajiye cup din. Xaman jugum jugum ya biyo baya, ya gaji ya tashi da jakarsa ya nufi bedroom. A fili yace "Sam baxan yadda da wannan hali ba maryam, ai wannan ya zarce muskilanci ya koma mugun hali" bai fito ba sai magrib yayi wanka da shirin masallaci, ya wuceta a falo tana zaune inda ya barta.




Sai bayan isha ya dawo, yayi mugun mamaki daya sameta inda ya barta ko xama bata gyara ba. Cikin tsoronta yake a halin yanxu da hanxari ya taho gunta baice komaiba ya dagata yayi ciki da ita, ya cire rigar jikinsa yaje bathroom ya hada mata ruwan zafi ya dauketa yaje yana mata wanka, kallonta yake cikin mamakin halin data tsiro dashi. Ya gama yayi mata brush da alwala kana suka fito. Lotion ya shafa mata iya hannye da qafa, ya dakko mata doguwar shadda light yellow me laushi ta saka. Yasa mata dadduma da hijab ta kawo sallar magrib da isha tana idarwa ta miqe ta cire hijab din babu addu'a balle shaf'i wal wutir. Idonsa akanta,

Please Login or Register in order to submit comment