Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana a bakinsa kuma bai yarda da abunda Faty ta fada ba, amma ganin idon surukansa yasa bece komai ba. Yace "ni natafi kasuwa dan nakusa makara"



Mama ta kasa dauriya da abunda ya samu Mimi tasa kuka, hajja da tun dazu take kukan itama ta qara volume Faty itama tasaka nata kukan. Mimi ganin mama da Faty na kuka (mutanen data fiso fiye da komai) itama ta saka nata kukan (tunda abun ya faru sai yanxu tayi kuka.


Kamar jiran nata kukan suke, kowa yayi shiru da nasa kukan parlourn yayi tsit sai sautin kukanta. Faty ta yunqura xata tashi taje gurinta mal manu yayi mata alama ta zauna. Sai da tayi 43 minutes tana kuka baji ba gani, sannan tayi shiru dan kanta.


Mal manu ya garo kujerarsa yaxo kusa da ita ya dafa kanta "MARYAMU kiyi haquri kinji, wata rana sai lbr, haqiqa mijinki ya cutar dake, amma kiyi haquri wlh duk wanda ya toxarta aure saiya wulaqanta, sakayyar aure a duniya Allah ya ke yinta. Allah ya baki wanda ya fishi, in shaa Allah wannan hawayen da kika xubar a dalilin baqin cikin aure sai Allah ya sa kin xubar da hawayen farin ciki fiye da wannan, Allah ya albarkaci rayuwarki" duk suka amsa da Aminnnnnnnn



Faty ta miqe xata tafi gurin aiki, mama ma ta miqe. Mimi tai saurin tashi tabi bayan mama. Hajja tace "maryam da kunyi xamanki anan kin dan murmure bakyaje wannan gidan naku haka ba suyi ta kasaki a fefe ana tallanki.


Mama tace "Hajja barni intafi da ita, hankalina sai yafi kwanciya" Mal manu yana jinsu yayi musu shiru domin daga uwar (mama) har yar (Mimi) tausayi suke bashi. Sai yake ganin rayuwar Mimi kamar ta mama acan lokacin da ya wuce, tabbas tarihi yana shirin maimaita kansa akan Mimi. Yana fata itama nata qarshen labarin yayi kyau (Mimi) kamar inda na fadimarsa yayi kyau. Yanason yarinya fiye da duk jikokin da yake dasu, yana ganin wasu halayyar MARYAM (matarsa Hajja) a tare da Mimi kamar haquri da sanyin hali, biyayya da kuma ibada. Kai hatta tafiya Mimi irin ta hajja take yi, afuskane kawai basa kama (tafi kama da mahaifinta AL AMIN, kamar photocopy dinsa ce) yana wannan tunanin har suka fita tsakar gida. Ya kwalawa mama kira "Fadimatu" ta amsa "naam Baba"



Ta sameshi yace "duk sanda kikaga tana kuka karki hanata, kibarta tayi ya isheta, baqin cikin zai ragu. Rashin kuka alokacin da abun kuka ya sameka kan illata lfyar kwakwalwa, shiyasa daxu na barta tayi kukanta, tashi kije Allah ya yi muku albarka ke da zuri ar ki" tace amin Baba Allah ya saka da khairan.


Umma kawai suka samu a tsakar gida tana yanka salak, ta tashi ta bisu har daki tana cewa "maryam meya sameki haka duk kika tsummace? Jiya nake cewa baffanku ya kamata aje a ganoki, tunda aka kaiki babu wanda yaje (kuji qarya)" sukai mata shiru har ta gama surutunta. Daga dakinsu gurin Anty ta nufa ta kai mata kanun labarai, tun kafin a gama fada mata ta nufi dakin mama.


Tana xuwa tace "maryam!😳 yanxu cikin ne yasa kika tarkato kika taho gida? Yara qannan bayanki suna gidan miji a zaune inma cikin ne sai dai mugansu dashi ya girma? Koda yake da alama cikin na wahalar dake duba da yadda duk kika qare, yo uwarki ce har yanxu bata daina abun mutanen da ba, wai ita kunya bata xuwa gidanku mu ba haka muke xarya gidan namu yayan ba" itama har ta gama haukanta basu tanka musu ba. Mama ta tashi tana tunanin hali irin na matan gidan wai ai wata biyar ba a ga mutum ba, amma in anganshi ko irin nuna murna nan ta yaushe gamo.



Mama ta dumamawa Mimi tuwon shinkafa miyar kuka tasa yajin daddawa ta isketa har bedroom kwance a saman gado ta kai mata "mimina tashi kici" ta girgixa kai alamar bataci mama ta hayo gadon ta dagata ta zaunar da ita tace "nasan mutuwar aure Mimi, nasan ciwon sakin aure. Musamman saki irin naki na wulaqanci amma babu yadda zaki da hukuncin Allah, barin kanki da yunwa bashine solution ba." ta karbi tuwon ta faraci, mama ta qura mata ido tana kallonta, tana son gano cikin da akace Mimi tana dashi. Ita sam abun bai mata dadi ba, dan dai babu yacce xatai da hukuncin Allah ne.



Acan kasuwa kuwa Baffa yini yayi yana xirga xirgar neman Badaru, tun yana xuwa da kansa har ya gaji ya dunga aika yaransa. Sai dai amsar dayace baixo kasuwa ba yau, kuma abun kamar hadin baki shima abban Badaru yau be zoba. Kuma Badaru yaqi xuwa kasuwar ne saboda yasan sai Baffa ya nemeshi.



Koda ya koma gida bai nemi mama ba duk kuwa da cewa ita keda girki, ta karbi girki da yamma. Wanda hakan ke nuna laifin Mimi ya shafeta, itama ta fison haka. Tasa yarta da jikanta (Dady dan Faty wanda ke xama a hannun Maman) agaba sukai kwanciyarsu.


Sai dai yadda Mimi ta kwana jiya, haka ta kwana yau. Ta dunga farkawa a firgice, kuma duk farkawar da tayi xataga mama xaune tana kalkonta. Farkawa ta qarshe da tayi tasamu mama tana sallah. Ita sai yanxu ta tuna in masifa ta sameka kana addua. Dan haka ta miqe taje tayo alwala ta fara sallah kamar motsatstsiya, duk sujjadar da tayi takance "ALLAH HUKUNCINKA NE WANNAN BANYI FUSHI BA, ALLAH KA QARAMUN JURIYA"



Da sassafe Baffa ya yiwa gidan alh inuwa tsinke, yana bacci xuwan kiran Baffa ya iskeshi. Sama sama suka gaisa Baffa ya karanta masa abunda Badaru yayiwa Mimi. (saboda da abun ya tayar masa da hankali, abunka da wanda ba a taba sakarwa ya ba). Wata irin kunya kunya ta rufe alh inuwa, ya tashi ya shiga gida yace da Baffa yana xuwa.


Yasamu Umma a kitchen ya labarta mata abunda Badaru yayi, gabanta ya yanke ya fadi ta xauna dabas a qasa tana sallallami tace "alh meye abunyi yanxu? Har Badaru yayi saki ba tare da saninmu ba. Maxa kirawoshi yazo ya maida ita tunkan abu yayi nisa" ba musu ya dakko waya, dan shima abunda yake shirin yi kenan.


Dajin kiran ABBA da sigar da yayi masa magana, yasan lbrin sakin ya ruskesu. Saboda haka ko wanka beyi ba ya tashi ya nufi gidansu yana qudurce cewa sai dai ayi duk wacce xa ai amma wlh ya gama xama da maryam.



Dake Bahaushe yace baya bata da kadan, be dade da fita ba mumy (Adda halima) yayar mama da Faty suka yiwa gidan tsinke. Sukai sa a yabar muqullin a gurin wani me shagon kofar gidan, suka shiga suka kwashe duk wata kayan sakawa na Mimi (suturu) mumy taiwa wani me furniture waya yaxo ya kwashe kayan dakin ya siya kuma ya siya da daraja tunda sababbi ne kuma sun samu kulawar Mimi. Kayan Badaru dake drawer mumy tasa Faty ta dau akwatin Mimi daya ta loda masa kayansa a ciki. Kayan da tayi amfani da su kuwa kamarsu tukwane, tea flask da food waemers, jugs cups plates duk tasa aka dunga rabawa maqota. Kayan abinci kuwa dana tea da lemuka duk tace a bar masa duk da kuwa Faty ta fada mata bashi ya siya ba, shinkafa kawai yake siya a gidan, mumy tace duk hada ki bar masa Faty shine matsiyaci, mukam ai bamu gaji tsiya ba. Ai mun auna arziqi tunda ya sakar mana yar. Dan ni dama gaba daya Badaru be mun ba a mijin Mimi.


Maqota da aka basu kaya suka dunga shigowa godia, suna yaba hallayar kirki irinta Mimi da alhinin rabuwa da ita, wasu harda kuka sunai mata fatan alkhairi. Wanda ya sayi Kayan yana gama fita dasu suma suka fito hannun Faty dauke da system (laptop) din Mimi da fos dinta suka qulla gidan suka bawa mai shagon muqullin, drivern mumy ya loda kayan a mota dake seinna ce tas ta dauke suka shiga suka tafi.



Badaru kuwa yana xuwa bai shiga gidansu ba, saboda kar Umma ta takura masa ya mayar da maryam, direct sitroom ya nufa gurin abbansa da Baffa ya gaishesu cikin daure fuska dan karsuce lallai ya maida Mimi. Abbansa cikin fada ya fara yi masa jawabin abunda Baffa yazo dashi, bayan ya gama ya bashi umarni da ya maida Mimi dakinta. Badaru ya motsa ya qara daure fuska yace "gaskiya abba kayi haquri nagaji da xama da ita, yarinyar Sam bata ganin girmana duk tsawon wannan lokacin haquri nake da ita" Baffa da yazo da nufin ciwa Badaru mutunci akan sakin Mimi yayi saurin sakkowa jin Badaru yace bazai maida Mimi ba. Cikin sanyin murya yace "haquri xakai Badaru duk matan haka suke duk wanda ka ganshi da matarsa sun dade haquri yake da ita" ya fada cikin qanqan dakai.


Badaru ya qarayin fuskar shanu yayi burus da lallashin da Baffa ke masa yace "Baffa tunda na auri maryam ban isa insata abu tayi ba, Kullum cikin yimun gorin ilimi take wai ta fini ilimi. Yanxu kuma akan bautar qasa ta tada balli wai sun kusa tafiya, nace ta bari lokacin yayi inga yacce za ai sai kawai tahau xagina wai bansan darajar ilimi ba. Dan haka ni na haqura da ita taje can ta auri wanda yasan darajar ilimi" hmmmmm (ni kuwa nace kuji qarya) ya ciro takadda daga aljihunsa ya miqawa Baffa ga takaddarta nan, dan Allah suyi gaggawar xuwa su kwashe kaya saboda xan saki gidan in karbe ragowar kudina.




Baffa ya bishi da kallo har ya bar gurin, cikin yaba rashin kunyar Badaru. Amma kuma baiga laifinsa ba tunda ya xayyano abunda Mimi tayi masa dole ya fusata. Abbansa ya dubi Baffa "to alh kaji abunda maryam tayi masa, bata kyauta ba sam inai mata kallon mai hankali. Inaga yanxu muyi haquri da batun kome tunda ya ruga ya fusata, inda rabon xama gaba a sasanta."(kuji tsabar san kai) Baffa bece komai ba sai gyada kai yayi ya tashi ya fita.



Badaru na shiga gida, ya tarar da ummansu a kofar sitroom din a tsaye idonta cike da kwallah. Ga dukkan alamu taji duk abunda ya wakana. Yana shiga ta fidda hannu ta tsinka masa mari, wanda hakan yayi dai dai da shigowar abbansa. Ta kalkeshi tace " wlh tallahi nasan maryam bazata taba aikata abunda ya fada ba, sharri yayi mata. Ai suffar macen da xatayi hakan daban take. Maryam ka saka ko Badaru? Macen arziqi, baka kyautawa kanka ba inajin kamar yar cikina aka saka, inason maryam. Kuma wlh sai kayi nadamar rabuwa da maryam. Kaje duniya ce" Abban ya daka mata tsawa "ke! Karkiwa dana baki akan wata maryam, ko shi kadaine ya taba sakin aure?" itam ta daka masa tsawa cikin fusata tace anyi masa, ko ka fini sansa ne. Badaru sum sum ya fice ganin abun nasu zai zama fada.


Ko daya koma gida yaga gidan fayau kuma yaga tulin kayan abincin da suka bar masa harda kyautar akwati sai duk jikinsa yayi sanyi, amma daya tuna da Nafee da kuma soyayyarsu sai yaji wani kwarin gwiwa ya shigeshi.

******** ********************



Baffa ya riga su mumy isa gida, ya iske mama a gida bata fita aiki ba dan bata da kwarin gwiwar yin hakan. Lokacin wajen 10:30 na safe, yaran gidan duk sun tafi makaranta sai masu aikin gidan tsofaffi guda biyu wadan da ke wanke wanke da shara. Ya tsaya a tsakar gida ya kwallawa mama da Mimi kira, gabansu ya fadi a tare dan yanayin kiran kawai xai fada musu abunda kiran ya qunsa. Suka fito Mimi ta tsuguna mama ta tsaya daga gefensa, matan gidan ma duk suka fito. Ya kalli Mimi ya daka mata tsawa "keee! Kinwa kanki daga gidan iyayen mijinki nake naje naji irin rashin mutuncin da kika shuka har ya sakeki, kin cuce ni kin batamun tarihin gida, ba a taba bazawara a gidana ba sai a kanki, wai har kece kike zagin mijinki na aure akan xaki tafi hidimar qasa. Irin tarbiyar da nai miki kenan? To tunda kinqi xaman gidan aure akan bautar qasa bazakije bautar qasar ba in anfara tafiya, kuma tunda kika dawomun gida a matsayin bazawara bazaki huta ba. Ya kalli shashin da yan aikin ke tsaye cirko cirko yace ku! Na hutar daku, kuma xanci gaba da biyanku albashinku, kubar mata aikin daga yau na maidashi doka tayi shara tayi wanke wanke kuma tayi girki, ya wulla mata takardar sakin a fuskarta yace ga certifacate dinki nan na xaman gida kitashi ki fara aikinki tun daga yanxu. Ya kalli shashin da mama take yace kuma duk wanda ya sabamun doka akan aikin dana sakata Allah ya isa"



Kowa ya watse wasu cikin farin ciki wasu akasin haka, Mimi ta nufi bakin famfo ta tara ruwa ta fara tulin wanke wanken, sam idonta babu digon kwallah.



Bai dade da fita ba, su Faty suka shigo. Drivern ne ya shigar musu da tulin a kwatinan Mimi, sannan suka zauna ana gaisawa. Faty tace "mama ina Mimi xan bata fos dinta" Maman tace tana waje tana wanke wanke, mumy da Faty suka hada baki sukace "wanke wanke kuma 😳" Faty taci gaba da cewa waya sata wanke wanke ina masu aikin gidannan? "


Baffanku ne ya sakata, yanxu yazo yana fada yaje gidan su Badaru har sun bashi takaddar ta, shine ya dora mata aikin gidannan gaba daya. Faty najin haka ta dau jakar xata tafi, mumy tace mata "Faty ki zauna ki huta mana" ta kalli mummy idonta taf da hawaye tace " me xan xauna nayi mumy Baffa na shirin kashemun yar uwa. Kuma wai mama tanaji tana gani baxatai magana ba" tasakai ta fice.



Mumy ma ta miqe, ta kalli mama kanta a sunkuye, ta miqa mata tulin kudi "gashi kudin kayan dakin Mimi ne dana siyar ki ajiye mata" mama tace to akwai na sadakinta ma a hannu sai inhada mata.


Mummy ta nisa ta fesar da iska cikin bacin rai tace "lokaci yayi da xan hada alh Buhari da human right akan abusing din maryam da yake yi (qungiyar kare haqqin Dan Adam)" mama ta xaro ido jin abunda da Adda halima tace. Cikin sanyin jiki tace "Adda kiyi haquri ku gyaleshi yarsa ce yana da iko akanta" mummy ta daka mata tsawa " daallah yimun shiru shashasha ki zauna ya kashe miki yaya da bakin ciki sukenan kike dasu, shi bashi da asara. Wlh fadima inbaki tashi kin kwatarwa yayanki yanci ba wlh saina hadashi da human right" itama ta juya ta fice.




Har inda maryam ke wanke wanke taje ta dafa bayanta, ta dago ganin mumy yasata yin murmushi, mumy tace "mamana kiyi haquri na ya qare akan lamarinki acikin gidannan na kusa in kwatar miki yanci kinji." tace " to mumy ai ba komai ma wata rana bazan ba, wata rana ko ganina saiya gagara sai dai aje kabarina ayimun addua" tace hakane Mamana Allah ya saka miki, Allah ya albarkaci rayiwarki amma kafin ki mutu in shaa Allah sai kinji dadin rayuwa.



Mrs 😊
[9/30, 1:03 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by rahman Mohammed (hajia)

Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page 2⃣9⃣

Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)


A hankali aikin da Baffa ya dora mata ya fara xamar mata jiki, duk kuwa da farko tana ganin wahalar aikin. Gidansu babban gidane wanda shararsa kawai aikine, sannan ga uban wanke wanke saboda yini ake da fita da abinci daga gidan domin adadin mutanen dake karbar abinci a gidan suna da yawa. Ko dattijan da suke aiki a gidan (masu wanke wanke da shara) sau tari aikin yawa yake musu, sannan ga wanke toilets din dake tsakar gidan. Batun girki kuwa dama da coal suke yinsa bisa manyan tukwanen tasa, kuma me girki ita keyin girki sai dai masu aikin su tayata da wanke wannan yanka wancan. To lokaci daya Baffa ya dorawa Mimi duk wannan aiki. ( qalubalenku iyaye, miji ya wulaqanta yarinya ko kuma ya korota ku iyaye memakon ku karbi qaddara ku kwantarwa da yarinya hankali, a a sai a tsiri muzguna mata da sunan hukuncin ta naqin xaman aure. Wlh kuji tsoron Allah irin haka inba a samu me hangen nesa ba kome haquri sai ta gudu ta shiga duniya. Haba ai abun yayi yawa gidan miji ba dadi gidan iyayema ba dadi) Da yake tana da qarfin zuciya duk sai aikin yaxo mata da sauki. Takan tashi tun asubar fari ta fara shara, ana kira taje tai sallah da azkar sannan ta dora breakfast ta zauna wanke wanke. Bakwai da rabi na safe ta gama breakfast sannan ta rabawa yan makaranta ta wanke bandakuna, taje gaida Baffa wanda intaje baya amsawa sai dai cin mutunci da gorin zawarci da yake biyo baya. Kafin taje gyara dakin mama takan tarar Maman ta gyara ta wanke toilet a qoqarinta na ragewa Mimi aiki.


In mama ta tafi aiki takanji gidan yayi mata xafi bata samun sukuni sai 11 tayi lokacin da take dora abincin rana ko kuma in dady ya dawo daga skul ya zauna yayi tayi mata shirmen yara ko kuma tayi masa homework.


Kafin kace meye wannan lbrin mutuwar aurenta yayi fitar dango, ta hanyar Anty da Umma. Karma Anty taji lbr domin gida gida take aiken mutuwar auren Mimi, kamar me rabon katin biki. Inda kuma baxata iya xuwa ba ta buga waya ta fada. Har gara Umma takan boye farin cikinta akan mutuwar auren, amma Anty a fili take nuna murnarta.


A irin hakan lbr ya riski fauxa qawar Mimi wacce suke maqota na kusa, da farko bata yarda ba a ganinta in hakane Mimi xata fada mata. Dan haka taje gidan da kanta, ta iske mugun lbr kuwa domin ganin da taiwa Mimi tana tulluqar aiki ya tabbatar mata da ingancin maganar.


Can cikin dakin Mimi (dakinta na yan matanci) suka qule. Fauxa ta riqo hannunta Mimi ta bude baki xatayi magana fauxan ta tsaidata tace "basai kince komai ba qawata, nasan halin da kike ciki ni da ke qadadarar da Allah ya dora mana kenan. Allah ya sa muci jarrabawa" ta fada tana share hawaye, Mimi ta goge mata hawaye tace "kiyi haquri fauxa, bakiji daga bakina ba ganinayi kyakykyawan lbr ake fada" tace nagane Mimi kuma banyi fushi ba, Allah ya bamu haqurin jure halin da muke ciki" Mimi tana murmushi tace amin qawata.


Tun daga ranar Kullum sai fauxa da shigo debewa Mimi kewa, in ta dawo daga aiki (tana aiki a wata private skul). A duk sanda ta shigo Anty kan saki shewa tace " ayyuririri bazawara qawar bazawara 🀣 Allah ya sa a dade anayi zaurawan asali." babu wanda ya taba tanka mata. Kuma daya abun takaicin shine : Baffa yasan tana haka amma bai taba hanata ba ko ya tsawatar mata, wanda hakan yasa ta qara qaimi wajen cin fuskar Mimi. Ga kwanuka da ake batawa da gangan da kuma bata gida duk dan a qara mata aiki. A duk sanda fauxa ta shigo taga Mimi na aiki takan Sabe mayafinta ta taya Mimi aiki.



Bayan haka kuma, Anty Kullum cikin gayyato mutane take dan suxo suga Mimi, kuma takan yi musu jagora har dakin mama a cewarta wai suxo suga gyatumar da tai wata 5 a gidan miji auren ya mutu. Ko kunyar idon mama bataji, kuma abun sha awa daga mana har Mimi babu wanda ke tanka mata, ko ya nuna damuwa kan abunda tayi. Wanda hakan shike baqanta mata rai kwarai, domin ta fiso su tanka mata.


Abun na Anty sam babu shaawa, kamar ba mace ko kuma bata da yaya mata. Ko tayi alqawari da nata mijin bazai taba sakinta ba.



Daya matsalar itace : muguwar rashin kunyar da Mimi ke fuskanta daga qananan yaran gidan yan mata, dan sau tari sukan bangajeta su wuce sai dai ta kauda kanta tayi kamar bata ganiba. Domin suna yine fisa umarnin iyayensu, wadanda ke zaman shirin ta tanka su cimata mutunci. Dan tashaji Umma na cewa " mutum bazai kasa xaman gidan aure ba, sannan ya dawo gida ya takurawa qananan yayanmu."


Duk mai imani inyaga Mimi a wannan lokaci saiya tausaya mata, domin ta qare ta mole tayi wani yagwal da ita. Babu rashin ci babu rashin sha, amma duniya ta juya mata baya. A wannan lokacin sai ta kwammace xaman gidan Badaru akan mazan gida. Wai dama haka mutuwar aure take? Tambayar da take yawan yiwa kanta kenan. Kota ina babu sauqi, sai a gurin ubangiji. Ta haqiqance babu mai santa yanxu sai mama da fauxa da kuma uwa uba ya Faty.



Faty tun daga ranar da suka debo kayan Mimi bata kuma xuwa gidan ba, domin sam batasan ganin Mimi cikin halin da Baffa ya sakata.


Mama ce ta lura da soshe soshen da Mimi takeyi, ta turketa ta tambayeta babu kwana kwana ta fadawa mama infection ke damunta. Dan haka mama ta bugawa Faty waya tace gobe tazo ta tafi da Mimi asibiti, qaiqayin bandaki na damunta.



Saboda tasan da xuwa asibitin tun qarfe hudun asuba ta tashi ta fara aikinta, bakwai dai dai ta gama Faty taxo suka dau hanya.


Likitan mata ta gani, ya basu kwaje kwaje, saboda Faty ya sa basubi layi ba suka gama da wuri suka kai masa result din. Ya duba yace "nikam banga ciki a jikin result dinta ba, amma ta iya yiwuwa akwaishi, matsalar magungunan da tayi ta amfani dasu suka cushe mata mahaifarta ya kuma haifar da rashin xuwan period dinta. Ya kalli Mimi yace ko anan gaba ki kiyayi cusa abu a gabanki, gurin yana da rauni kuma yana da saurin karbar kwayoyin cuta. Kinga dalilin cushe cushen da kikayi yasa ciwon qaiqaiyin tsanani a jikin ki. Amma yanxu ga magani nan da allura inkikayi amfani dasu yadda ya dace duk qarfin ciwon sanyi zai rabu dake, kuma suna da qarfi sosai kici abinci sosai kafin kisha" sannan ya rubuta wani abu a takadda ya bawa Faty yace " wannan maganin kinsan yadda ake amfani dashi, duk sanda jinin al adarta yaxo shedar ta warke daga ciwon kenan sai ki siya ki saka mata acan ciki ki tabbatar ya taba mahaifarta, tunda kince sister dinki ce xaki iya yi mata a gida basai kun dawo ba"



Suna kan hanyar xuwa gida daga asibitin Faty ta gallawa Mimi harara tace "Mimi har magani kike cusawa a jikin ki dan ki burge Badaru ko? Mutumin da baisan mutuncinki ba?" Mimi ta marairaice tace " wlh ya Faty ban taba shan komai ko cusa wani abu a jikina ba, kinaga kazar da kuka yimun ma kafin a kaini ko dandanata banyi ba. Kawai dai lalura ce Allah ya doramun" Faty ta sauke fushinta dajin abunda Mimi tace, kuma tasan tabbas hakan ne domin kazar ma itace ta cinyeta bayan Mimi taqi ci. Dan haka ta

Please Login or Register in order to submit comment