Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gashin kanta butsu butsu atsefe yake kuma tayi kusan kwana uku bata kwanceshi ta tajeba, ribbon din duk ya sakwarkwace.




Ya tako inda take tsaye ya kama hannayenta ya riqe yana kallon fuskarta, ta sunkuyar da kanta yajata sukai falo kan dinning ya xuba musu abinci a plate daya yace mata "maxa muci maryam" ta fara juya spoon ba tare data kai abincin bakinta ba. Ya qura mata ido cikin tausayin halin data saka kanta aciki, duk da babu kwalliya ko dis a fuskar amma ta masa kyau gashinta ya barbaxo gaban fuskarta ta rame kadan sabida damuwar data saka kanta ciki. Ya matso kusa da ita har kafadarsu na gugar juna ya dafa dan qaramin cikinta daya fito das ta cikin rigar yace "maryam daure kici abinci ko dan danmu dake cikin ki" ta dibi kadan ta kai bakinta daganan bata kuma ci ba. Shima ya dakata dacin nasa ya riqo hannunta duk biyun cikin nasa yana murxawa yace "maryam Dan Allah menayi miki kike irin wannan fushi haka babu ji babu gani?" tai shiru babu amsa yagaji da jiran cewarta ya kuma cewa "Dan Allah in akan Hanifa ne kiyi haquri, na tuba Mimi na, na baki haquri kuma tun a lokacin kin nuna kin haqura amma yanxu kin tsiro da fushi muna cikin xamanmu me dadi. Maryam kiyi haquri mu xauna lfy yan watanni muke da aure be dace ace haka ta fara bullowa tsakaninmu ba" har yanxu shiru batai magana ba, ya dakkota ya dorata kan cinyarsa yana shafa cikinta yana cewa "Baby na ka tayani bawa mamanka haquri, nayi missing dinku sosai. Mimi tunda kika tsiro da wannan hali naki duk gidan babu dadi har maids dinki basa walwala Mimi duk sun damu da halin da kike ciki, fadamun duk abunda kikeso inyi miki ki daina wannan fushin my luv" tai rau rau cikin muryar kuka tace "ni gidan ya Taheer nakeso naje" ya shafa kanta yana murmushi yace "wannan shiyafi komai sauqi my luv tashi muje" ya dakko mata siririn gyale ta rufe kanta suka tafi.




A qafa suke tafiyar tunda kusa suke tsiran maifi gidaje 5 ba, yana riqe da hannunta har cikin babban falo. Sun taddasu zaune kan dinning da kidz dinsu suna dinner, har gurin suka isa aka gaggaisa kana suka hadu gaba daya suna cin abinci. Mimi dai bata saki jikinta ba kamar yadda yake xato kuma batacin tuwon shinkafar dake gabanta, yadan dubeta yace "maryam ci abinci mana" Anty Rabi ta dora da fada mata ta dunga cin abinci sosai sabida abunda ke cikinta don xata iya jigata kuma ta jigatashi in batacin abinci sosai. Ganin sunyi mata caaa yasa taci loma uku dakyar duk kuwa da son tuwo da take da kuma uwar yinwar dake sakadarta. Ya Taheer baice komaiba amma yana kallonta cikin nazari.




Har goman dare suna gidan suna hira, ita kuma hakimar tana kan kujera a lafe bata samusu baki a cikin hirar amma fuskarta ta dan saki ba kamar daxu ba da suka shigo. Bature ya gaji kwarai so yake yaje ya kwanta sannan ya lallashi miminsa da kalaman soyayya su shirya don yagaji da wannan quncin nata.





Ya fara gyangyadi da hammar qarya duk don ya Taheer yace su tafi dare yayi, amma yaji yayi shiru sai zaqulo wata hirar yake. Ya qara wata hammar yace "Mimi taso mu tafi nagaji so nake in kwanta" tanajin haka ta koma kan kujerar da ya Taheer yake ta riqeshi tana kuka tace "ni baxan koma ba, nidai kabarni anan babu inda xanje" yayi sototo yana kallonta cikin tsananin mamaki ya yabawa makircin mace kwarai da gaske wato Mimi wayo tai masa ta shinfida masa gadar xare ta yaudareshi ya kawota gidan ya Taheer sannan ta nuna musu cutarta yake wato dai a fakaice qararsa ta kawo kenan? Ya danne duk wani bacin ran data haddasa masa ya kuma cewa "haba mana Mimi luv kefa kikace inkawo ki kuma nabi umarninki na kawoki sai kuma kiqi komawa? Daure ki taso mu tafi da safe xan dawo dake in xanje aiki."



Ta kuma shigewa jikin Taheer tace "wlh bazan bika ba, ka tafi kabarni, banason wannan gidan baxan koma ba."




Ya Taheer ya dago daka kallon Mimi dake jikinsa ya maida kallonsa ga Bature dake tsaye. Ya fara harar Bature, ya dafa kan Mimi yana kallon Bature yace "sulaiman yanxu wannan yarinyar kake cuta? Wannan salihar baiwar kake zalunta? Tun daga shigowarku naga yanayinta nasan akwai abunda ke damunta, amma ka bani kunya, ban zaci haka daga gareka ba. Aurenku da yan kwanaki har ka sako matsala cikin xamanku? Dama ka auretane don raba zumuncin iyayenku mata? Kasan matsala acikin aurenku na nufin matsala ga family dinmu gaba daya?"




Anty Rabi ta dubi Bature dake tsaye yana sauraran fadan Taheer kana ta maida kallonta ga Mimi wacce ke kwance kafadar Taheer din tana kuka wurjanjan. Ta matso kusa da ya Taheer tace "Abban sayyeed kabar fadan haka, lamarin aure ba a bawa mutum daya laifi, ka bawa Bature dama ya kare kansa mana" ya tareta da cewa "sulaiman shine babba sabida haka dole yayi haquri da maryam, kuma tunda kikaji ta dau matakin qin komawa gidansa abun babba ne."




Bature ya hadiye yawu dakyar yace "ya Taheer kayi haquri na karbi lefina in shaa Allah baxan kuma ba" jin haka jikin Taheer yayi sanyi ya dan yimusu nasiha da yin haquri a xaman aure kana yace "maryam tashi ku tafi Kinji ki dunga haquri da mijinki" duk da bata da taurin kai sunyi mamaki lokacin data noqe wuya, alamar baxata bishi ba.




Anty Rabi tajata daki don tambayarta meyayi mata haka wanda ya hanata komawa, amma juyin duniya Mimi taqi magana qarshe ma tasa kuka. Ganin haka ta fito falon ta samesu Taheer na qara yimasa fada. Mimi ta nemi guri ta kuma xama, Taheer ya matso gabanta cikin lallashi yace "maryam yi haquri ku tafi, gobe in nadawo aiki xanxo har gida ki fadamun abunda yayi miki, amma kafin nan ina nemar masa afuwa ki tashi ku koma"





Ta dubi ya Taheer bata da niyyar tashi ta saka kuka. Bature xuwa yanxu ransa ya gama baci da rainin hankalinta ya matsa kusa da ita ya riqo kafadarta ya fara magana .





"maryam karki raina mana hankali kinji, waye sa'anki anan? Ki fada mana abunda nayi miki kinqi, maryam sai yanxu xaki tsiro iskancin baxaki xauna dani ba? Sai da kikaga baxan iya rayuwa me dadi ba inbabu ke? Sai da kikaga farin cikin mahaifanmu ya ta'allaqa akan Dan dake cikinki? Meyasa kikeson duk saka wadannan mutane cikin baqin ciki? To wallahil azim in bacci kike ki farka, baxan sakeki ba koda bakya sona dole ki xauna dani, aurenmu mutu ka raba."




Kalamansa suka sakata saka sabon kuka, shima hawaye yake. Ya Taheer da Anty Rabi kuma tuni suka koma bayansu suna kallon wannan almara.



Bature ya miqar da ita tsaye ya fara jan hannunta yana cewa "taho mu tafi ko in sabeki in maidake dan dole, muguwa wacce batasan soyayyar gaskiya ba sai yaudara, wacce batasan farin cikin kowa ba sai nata"



Yayi gaba yana janye da hannunta ita kuma tana turjewa, taku daya, biyu, ana uku ta yanke jiki ta fadi wanwar. Sukayo kanta da gudu suna jijjigata da fadar sunanta, shi kuwa Bature na tsaye yana kallonta yasan Mimi pretending tayi don karta bishi.




Suna aikin jijjigata a gigice tana kwance sanbal shi kuma ya na tsaye hannu a aljihu yana kallonsu. A zuciyarsa ya raya bari yayi maganinta, yanufi kitchen ya bude freezer ya dakko ruwa me sanyi har ya fara qanqara ya nufi falon. Yasan dai ko suman gaske tayi ya xuba mata wannan ruwan zata farko balle pretending.




Yana xuwa ya bude ruwan daga tsaye ya fara tsiyaya matashi a fuska, sai dai har ya kusa juye mata goran ruwan Faro ko yatsanta be motsa ba. Ya Taheer ya daka masa tsawa da cewa "sulaiman! Kai mahaukacine da xaka dunga xuba mata wannan ruwan me sanyi? Baka ganin halin da take ciki ne?" yayi saurin yarda gorar ruwan don ya fara tsorata.




Ya fara kuka yana jijjigata da fadar sunanta yana cewa "maryam ki taimakeni ki tashi, maryam karki mutu ki barni, ki tashi maryam xan barki anan gidan tunda nan kikeson xama baxan qara tilasa miki xaman gidana ba. Ki tashi Mimi luv ya Baturenki baxai jure rashinki ba" jijjigata yake iya qarfinsa, amma ko gixau bata motsa ba tana yadda take.




Ya miqe ya dauketa a hanzarce ya fita da gudu ko takalmk be tsaya sakawa ba, su ya Taheer suma suka rufa masa baya.




Gidan ishaq ya nufa da ita, suna xaune shi da Farida wacce ta fara bacci akan cinyarsa suka ga Bature a kansu dauke da Mimi, baice komai ba ya shimfideta a gabansu kamar gawa, su ya Taheer suka shigo suma a gigice.




Maganar Bature ta katseshi inda yake cewa "ishaq, maryam ce, ka temakamun ishaq xan rasa maryam ka temakamun" ishaq a gigice ya fara duba tsintsiyar hannun Mimi, kana ya kai kunnansa saitin xuciyarta yaji tabbas tana bugawa amma ba yacce ya kamata ba. Ya dubi Farida wacce maganar Bature ta tasheta daga baccin data fara yace "dakko mun jakata ta aiki a ciki" da sauri ta nufi dakin.




Ya karba ya fara duba Mimi cikin kwarewa, yasa hannu ya dunga danna qirjinta da qarfi har xuwa wani lokaci kana ya dakko drip yayi wata allura aciki ya jona mata ruwan. Ya dago ya kallesu a tsaye cirko cirko duk sunyi zuffa kamar yacce shima ya hada gumi sharkaf kamar babu sanyin AC. Yace "shikenan doguwar suma tayi, wanda firgici ya haddasa mata amma yanxu mun shawo kan abun. Yanxu haka bacci take na mata allurar bacci ruwan kuma sabida jikinta babu abinci yayi weak shiyasa na saka mata."




Bature ya matsa kusa da Mimi dake kan doguwar kujera kwance, shi bai yadda bacci take ba gani yake ta mutu. Ya kara hannunsa a qasan hancinta yaji fitar numfashinta sannan ya yarda da maganar ishaq ya saki ajiyar xuciya.




Su ya Taheer suka matso suka dubata suma kana suka tafi, lokacin har har sha biyu tayi. Ya matsa ya daga kanta ya dora akan cinyarsa yana shafa gashinta don babu dankwali akanta.




Farida kuma ta shige jikin ishaq ita kuma kukan halin da Mimi ke ciki take, yayin da ishaq yake lallabata da cewa mimin bacci take sabida allurar da yayi mata amma ba a sume take ba kamar yadda Faridan ke zato.




Bature yana hurawa Mimi iskar bakinsa a fuskarta ya labarta musu abunda ya faruwa, sunyi mamaki kwarai sunanan zaune jigum jigum har ruwan ya qare.




Bature yayi niyyar komawa da Mimi gida amma sai ya tuna cewa maganar komawarta gidan yasata suma karya dauketa ya kaita ta farka tayi masa bore gashi babu mataumaki kusa, ya kalli Ishaq yace "inaga xan barta anan xuwa safe don karta farka tayi rigima" ishaq yace "hakan yafi don karma ta farko da wata matsalar kuma bana kusa" yace da shi "dakkota ku shiga daki Kaima ka kwanta don duk ka jigata"



Farida ta shiga bedroom din dake kusa da nasu ta shimfida musu sabon bed sheet ta kunna AC. Shi kuma ya dakko Mimi ya shigo da ita ya kwantar, ishaq ya qara dubata yaga babu matsala bacci dai take sannan sukai sallama suka fita. Yaje ya dauro alwala yayi musu addua ya tofesu shi da ita yajata jikinsa ya rungumeta a hankali bacci yayi gaba dashi, amma yanayi yana farkawa yanaganin halin da take ciki.




Kiran sallar farko ta farka kamar yadda ta saba, ta ganshi kwance a kusa da ita, ta miqe ta kunna wutar dakin lamarin da yasa ya tashi yayi saurin xuwa inda take ya kamota jikinsa yana tambayarta ya jikin nata.





Ta tureshi daga jikinta tace "nace banason gidan nan amma ka dawo dani ko? Na tsani gidan kaima na tsaneka" ya toshe mata baki yace "Mimi tsakiyar dare ne yanxu kiyi magana a hankali, kuma wlh ba gidan na maidake ba gidan su ishaq ne nan" ta cire hannunsa daga bakinta direct tace "karya kake nan gidanka ne, don me xakaimun haka? Don me xaka kaini inda banaso?"





Jikinsa yayi mugun sanyi wai yau Mimi kecewa yana karya ido cikin ido kuma tace ta tsaneshi. Ya dakko pic din Farida da ishaq dake kan bed side ya nuna mata tare da cewa "kinga pic dinsu ma, wlh gidan farida kike" suna wannan daru Farida da ishaq wadanda hargagin Mimi ya tashesu suka shigo dakin. Ganinsu yasa ta yadda cewa ba gidanta takeba sannan ta haqura ta dena masifar.




Ya temaka mata tayi alwala kafin a kira assalatu sukai raka atanil fajr, ya barta da Farida suka wuce masallacin asuba shida ishaq. Tayi sallar asuba babu batun azkar ta miqe ta kwanta Farida na kallonta tana hawaye, wai Mimi ce ta xama haka daga jiya xuwa yau. A iya saninta da ita inta idar da sallar asuba takan xarce da azkar kana ta dora karatun qur'ani bata komawa bacci sai bakwai da rabi xuwa takwas na safe, amma dake Dan adam ba bakin komai yake ba yau Mimi ce ke sallah kamar wata farin shigar shiga addini. A cikin sujjadar qarshe ta sallah tana kuka tana roqon Allah ya yayewa maryam wannan baqon lamari daya tunkarota.





Bature daga masallacin asuba gidansa ya zarce yaje yayi wanka yayi shirinsa na fita kayane kawai bai saka ba, ya saka wando 3 qt da t shirt ya dibarwa Mimi kayanta set biyu da brush da undis kana ya daukar mata wayarta da sosan wanka da mayunkanta da turare ya xuba a qaramar trolley don yaga abun nata nayi ne baisan ranar qarewar wannan hijira tata ba.




Shigarsa gidan ishaq ya sameta tana baccinta sosai, lokacin har 7:00 AM tayi. Ya matsa kusa da ita ya shafa fuskarta cike da soyayyarta da kuma tausayi, yakai bakinsa ya sumbaci kuncinta da lebenta. Ta bude ido tana kallonsa, ya mata murmushi ya tadata zaune ta jingina da allon gadon yace "morning my luv" ta qura masa ido ba tare data amsa ba, ganin xai makara a office yace "tashi muje in muki wanka" ta miqe ya ciro towel ya miqa mata, ta kalleshi da alamar batasan abunda xatai dashi ba. A hankali yace mata "cire kayanki ki daura" ta cire kayan ta daura kamar yace ta daura suka shiga bathroom.




Brush ma daya miqa mata sai da ya fada mata ta wanke baki sannan ta fara wankewa, don ya kwadata yace mata "to yi wankan mana maryam" tayi shiru tana kallon kwamin wankan daya cika da ruwan dumi da sabulai can ta kalleshi tace "ya akeyi?" gabansa ya yanke ya fadi, me wannan abun ke nufi wai? Mimi loosing memory tayi ko me?



Ya dauketa ya sakata cikin bahon wanka ya fara yimata, a xuciyarsa tunani yake wannan wace irin lalura ce ta samu Mimi haka siddan anya abun bai shafi brain dinta ba.




Tas ya sullube abarsa ya nadota a towel ya dakkota xuwa cikin daki, suna tafe tana kallon fuskarsa kamar yadda ta saba inyayi mata irin wannan daukar. Ya ajiyeta akan gado ya tsane ruwan jikinta ya shafa mata mai, yasa mata undis da body spray, ya saka mata doguwar riga don riga da zani baxai saku a gurinta ba yanxu tunda komai sai anmata. Yasa dankwalin rigar ya daure mata kanta yasa mata powder harda jan baki. Ya kalleta tayi kyau sosai don kwana biyunnnan bata kwalliya, ya kama kafadunta yana nuna mata kwalliyar da yayi mata cikin mirrow, ta danyi murmushi har dimple dinta ya motsa. Farin ciki ya rufeshi don ya kwan biyu bega hakan ba, ya ayyana maryam a matsayin farincikinsa don dan murmushin da tayi yanxu kawai ya samu raguwar abunda ke damunsa a xuciyarsa.





Cikin kwarin gwiwa ya riqe hannunta suka fita falo, ishaq da Farida na dinning tana hada masa breakfast yanaci yayi shirin fita. Sukai joining dinsu, farida ta gaisheta da tambayarta jiki, ishaq ma haka. Farida ce ta hadawa Bature tea ta xuba masa farfeson kan sa ta tura masa kana ta hadawa Mimi itama. Yaci abincin sosai don yunwa yakeji, ya kalli Mimi dake gefe batako taba abincin ba, ya dakko ragowar tea dinsa ya bata a baki ta shaye ya kuma qara mata da nata. Farfesun ma yanaci yana bata da cokali, a xuciyarsa yana tunanin kardai Mimi abinci ma sai an nuna mata yadda xataci ko anbata?. Yace mata "dauki ruwa kisha magani" ya fada yana xuba mata maganin da ishaq ya bashi yanxu a tafin hannunta, babu musu tasha maganin.






Ya saki ajiyar xuciya tare da godewa Allah don abun nata da sauki tunda duk abunda akace tayi tanayi babu musu, ya riqo hannunta yasaka mata wayarta yace "Mimi xan tafi office Kinji" ta daga kai ba tare da magana ba.





Ya kalli Farida yace "Farida kiyi haquri xan bar Mimi anan muga xuwa wani lokaci ko xata dawo dai dai, Dan Allah ki kula da ita karta xauna da yunwa in lokacin sallah yayi a nuna mata yadda xatai kuma abata abinci." Farida tace "haba sulaiman ka kwantar da hankalinka, Mimi kamar a gida take ko shekara xanyi ina kula da ita in shaa Allah baxan gaji ba xan kula da Mimi kamar yadda xan kula da kaina don nasan da ni wannan lalurar ta samu sai yadda qarfinta ya qare" yaji dadin kalamanta yayi mata godiya yace bari yaje ya taho da Aisha ta dunga temaka mata ganin itama faridan ga ciki jikinta. Tace "daka barta ma ai ma aikatan gidannan ma sun isa kuma nidin bana aikin komai sai muyi xaman ko Mimi?" ta fada tana dafa kafadar Mimi.





Yace "to bari inje in dawo" acan gidan ya tara ma aikatan kaf yayi musu bayanin madam babu lfy kuma tana gidan ishaq qarqashin kulawarsa ya buqaci Aisha ta shirya ta koma can ta taya Farida hidimar Mimi. Nan take wasu suka fara kuka, gaskiya mana kwana biyu take musu fiskar shanu, ya kallesu cikin soyayya don sun burgeshi a dalilin son me kyautata musu, yace "ba kuka xakuyi ba just kuyi mata addau ita tafi buqata" suka rude dayi mata adduar samun lfy, yana amsawa. Grace tana kuka tace "intaje church ran sunday xatayiwa madam special prayer" yayi mata godiya.




A gaggauce yasa kayansa na fita sannan ya fito da jakarsa a hannu yana gyara tie din wuyansa, ya tarar da Aisha ta shirya suka fita xuwa gidan ishaq.




Ya kai Aisha sannan yayiwa Mimi sallama yace "Mimi luv na tafi office" ya sunkuya dai dai fuskarta ya sumbaci lips dinta ya fita.




A office ya kasa nutsuwa kusan duk after 1 hour saiya kira Farida ya tambayi jikin Mimi ta kuma bashi tabbacin tana lfy.





Suma a gidan yini sukayi suna debe mata kewa, sunata hira amma banda ita, sai dai in anyi abun dariya takanyi murmushi. In lokacin sallah yayi sukan nuna mata yadda xatai alwala, in sukace tai sallah tana tambayarsu guda nawa xatayi lamarin dake saka Farida xubar da hawaye.
Abinci ma taci sosai sabida Farida hada musu tayi.



Lokacin tashi yanayi yayo gida, yayi farin cikin yadda ya sameta ta sake sosai suna kallo a falo tayi wanka ta sake Kaya. Ya qarasa yanawa Farida hannu da gida da kuma gajiyar kula da Mimi. Mimi tana ta kallonsa batare da magana ba, ya jata jikinsa yana tambayarta yata yini? Batai magana ba amma ta lafe a jikinsa.




Da magrib suka fita masallaci da ishaq suna hirar ciwon Mimi, ishaq na fada cewa xafin zazzafi kansa irin wannan matsalar amma a barta takwan biyu aga yadda jikin xaiyi. Bayan idar da sallah ya fadawa imam din masallacin cewar matarsa babu lfy asata a addua.




A gurin dinner ma yanaci yana bata a baki har sukaci suka qoshi. Yauma kamar jiya anan gidan suka kwana kuma yau sunyi bacci sosai da taimakon addua da maganin baccin da ishaq ya bata.




****** ******* ****** ****

Kwananta 3 a gidan ta sake sosai, duk da bata walwala bata kuma magana saiya xama dole amma dai abun da sauqi. Bature ya gane matsalar Mimi dai gidansane kawai bataso, duk da yaso kaita asibiti sabida taga likitan kwalkwalwa amma ishaq yana yawan fada masa cewa koda ya kaita babu abunda xasuyi mata a halin yanxu saboda ciki. Aisha na yawan tofa mata addu'o'i a ruwa da kuma ayatushshifa dake Aisha yarinyace nutsatstsiya me ilimin addini xafin talaucine ya korota yawan aikatau. Wanda adduoin Aisha su suka kawo Mimi wannan sauqin.




A ranar dai data cika kwana ukun a gidan da yamma ya dawo office ya shigo gidan kamar yadda ya saba, ya samu ishaq a gida sabida yau fitar dare zaiyi a aiki wato "call up duty" suna zaune shida Farida kan kujera daya, yayin da Mimi da Aisha ke kan carpet Aisha na matsa mata qafarta suna kallo. Yana shigowa ta taso da hanzari da nufoshi, ya dakata da tafiyar da yake yana kallonta tana sanye da atamfa dinkin riga da skirt sunyi caras jikinta fuskarta tayi tas saboda kitson da Farida tasa yar aikinta hanne tai mata daxu ganin jikinta da sauqi.





Tana xuwa ta shige jikinsa tare da cewa "ya Bature na" ya yar da jakarsa ta aiki ya dagata ya rungumeta kamar yadda yake in zai rungumeta sabida ya fita tsaho. Lamarin daya bawa su Farida mamaki, sun dade a tsaye rungume da juna kafin ya ajiyeta yana kallonta.



A gurin suka zube ta qura masa ido cikin shauqi tace "ya Bature i miss u" ya amsa yana qara shigewa jikinta yace "i miss u too Mimi luv" ta qara kallonsa tace "tashi mu tafi gida ya Bature" ya kalli sashin dasu Farida ke xaune suna kallonsu yace "na fada muku ishaq, Mimi bata cikin hayyacinta a wancan lokacin shiyasa ta furta bata sona batason gidana amma yanxu data dawo dai dai gashi da kanta ta buqaci mu koma" ya daga hannu yana cewa "Alhamdulillah, Allah nagode maka daka kawo mana qarshen wannan abu Allah kada ka maimaita mana"




Ya juyo ya hada bakinsa da nata ya farΓ‘ kissing dinta ko kunyar su ishaq da Aisha dake gurin bayaji. Dakyar ta banbareshi a jikinta, ya kalleta cikin burgewa yace "maryam taso mu koma gidanmu mucigaba da soyayyarmu mai dadi, taso Mimi luv mutafi ni da gidana munyi missing dinki da kulawarki."




Ta miqe tana rumgume gefen jikinsa ta juya tanawa su Farida waving suka fice. Sai Aisha ce ta tsaya ta dakko mata wayarta da kayanta na gidan.





Farida ta kalli ishaq tana jinjina wannan lamari tace SULAIMAN da MARYAM tsakaninsu sai Allah. Allah ka kare wadannan bayi naka daga sharrin maqiya don suna qaunar junansu.




Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }

Page

Please Login or Register in order to submit comment