Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan zuwa, yazama dole karfe bakwai ki tashi ki gyara gida, banason qazanta,idan ba hakaba toki dauka ankawomin kene kawai nadinga faffalla miki mari"
Yadora hannunsa akan kunnansa yace"kinji abinda nace?

Cikin rawar murya tace "naji"

"Ok tashi kibar gabana"

Ahankali ta tashi tashige cikin daki, hawaye suka zubo mata, tashare tatada kabbarar sallah

Wayarsa ya dauka yakira Nasir "Nas ina zaka samomin mutumin daya iya zanene?"

"mk wanne irin zane kuma? Ko akwai gidan da kakeso azana maka?"

"no Nas, inaso azanamin photon yarinyar nan ne, zan ajiye shi a d'akina"

Nasir yace"aikuwa akwai wani mutum dana sani ya'iya zane, ya qware wajan zana mutum "

" yawwa Nas, toka turomin shi gobe pls "

Nasir yace" to Babu damuwa "
daganan yatashi yafice daga gidan


*** ***** ***

Bai dawo gidaba sai bayan sallar magrib, yana doso cikin falon da shashshekar kukanta yafara cin karo, meyasa ne yarinyar nan kuka baya mata wahala, komai kuka, cak yaja ya tsaya abayanta batare daya qaraso cikin falon ba

Cikin kuka tace "ni wallahi umma nagaji, dazu dasafe kusan mutuwa nayi,"

Umma tace"to Nawal menene auren ne? sokike koda yaushe kijiki cikin jin dadi da kwanciyar hankali Kamar kina gida?ai bazai iyuba, ki yi hakuri watarana sai labari "

Wahaye ne suka zubo mata tace" Ummah wallahi DANA SANI tun farko Nuhu na aura 🤣🤣, nasan bazai taba wulakanta niba "

Ummah tace" Nawal, kina gidan wani amma kina maganar Nuhu, kiyi hakuri kede kiyi masa biyaiya, Karki kuskura kirageshi da haqqi d'aya kinji abinda nafada miki, sannan Zan yiwa Sultan waya idan yasamu lokaci yazo yaganki tunda kuna kusa "

Jin yaya Sultan zaizo yasa tasaki ranta, tace" to shknn sai yazo "

"Nuhu" ya maimaita sunan cikin zuciyarsa

Bai kalletaba yazo yawuce tagabanta yayi d'akinsa, amma ransa idan yayi dubu toya baci, kan gado yafada, sannan yafara magana a bayyane "wannan yarinyar yaudarar Ummi kawai take,rannan takira masa sunan Sultan, yau kuma Nuhu, Wato data sani shita aura, gani dan'iska yarinya tana zaune agidana amma tana kiramin sunayen qarti, Allah yakawo shi lafiya, ai naji tace Allah yakawo shi lafiya, to Allah yakawo shi lafiyar🙊😳😂Zan yi maganin abun "

Yaanaji aka kira sallar isha'i yamiqe yafita, a lokacin bata falon, yaana zuwa masallaci bayan yayi sallah yadawo gida, awajan maigadi ya tsaya yace" Dayyabu "

Cikin sauri yaqaraso ya rissina," gani ranka yadade "

" Dayyabu daga yau kakoma gidan gona kace subaka wani aikin injini, sannan kafin katafi inaso cikin gaggawa ka nemomin wani me gadin amma ba tsoho ba, sannan kuma ya kasance sunansa Nuhu 🙆🏻🤣🙊

"to yallabai aikuwa akwai wani yaron abokina daya dade yana neman ai kinyi, shima sunansa Nuhu, zankawo shi ranka yadade"

Yace "Babu damuwa Dayyabu, zaka iya tafiya"

Shima juyawa yayi zuwa d'akinsa

*** ***** ***

Washe gari Kamar yanda yace haka ta tashi dawuri tayi duk ayyukan gidan, har kayan kallo saida ta goge sannan tahada abinci break, tadauki wani zata kaiwa maigadi taje ta tarar baya nan, daki tadawo tayi kwanciyar ta, tunanin maganar ummah tafara, kuma garama kawai ta kwantar da hankalin ta, tunda shide auren nan anriga andaura, garama tayi hakuri ta rungumi qaddara tunda har tasamu ma uwar miji take sonta sosai, ai saita godewa Allah, shikuwa tasan cewa Babu maganar soyaiya a tsakanin su, kawai de za'ayi zamane domin samun ladan aure, amma Babu maganar soyaiya

Nasrin takira, amma bata dagaba, data sake kira saita turo mata da text cewa suna lacture ne

Ta gaji da zaman haka Babu wani aikin yi, kawai saita janyo akwatunanta tafara debo qananun kayanta Wanda dama tana saka abinta agida, sauran atamfofinta kuma suma saita ciresu tashirya su, bata dauki komai a kayan auren taba, saisu brezia da panties dakuma kayan bacci, tana gama shirya wa
Ta futo falo zatai kallo

Sai ganinsa tayi tareda wani mutum da kaloli agabansu da alama zane zasuyi
Komawa daki tayi ta dauko mayafi, tazo tagaidasu, baqon ne kawai ya amsa, itama bata damuba taje takunna kallo ta dauki remote takoma can gefe kan kujera tana abinta

Tana jinsa yadubi mutumin yace "Yawwa kanajina? Shi idon yarinyar, haka zaka zanashi shiba manyaba, shiba qananu ba, kuma shiba yan madedetaba"
😳🙊😂

Cikin sauri ta juya ta kalleshi, wata irin daria ta kamata😃
Murmushi tayi kawai taci gaba da kallonta

Shima mutumin yace "Amma yallabai Kamar yaya kenan za'a zana, kace ba manyaba ba qananu ba ba 'yan madedetaba"

"to kai bakasaan aikinkaba da in angwadama abu zaka kasa ganewa?, nacema ita yarinyar Kamar tana tahowa ne daga nesa kagane? To haka naga idon nata, sannan shikuma bakinta...

Mutumin ne ya katseshi yace" bari ayi idon tukunna yallabai "

Shiru mk yayi, Mai zane yazana ido ya nuna masa, yace" haka yayi?"

Karbar takardar yayi yaga wasu irin fici-ficin ido daya zana 🤣🤣
Takaici ya hanashi magana😖
Kawai saiya zubawa Mai zanen ido yana kallansa😒 😒

Yace" yallabai yanaga kayi shiru? "

Takardar ya wulla masa yace" nikam idon 'yan chaina nace ka zanamin ne?"

Shima yace" to ai yallabai, kwatancan nakane narasa gane kansa 🤔ba madedetaba, ba qarami ba, ba Babba ba🤣🤣

Nawal dake gefe tana jinsu ta kwashe da daria 😃, sai qyalqyala daria take

Juyowa yayi yana Kallanta, aransa yace"ashe tana daria, 🤔dariyar tamata kyau "

Saiya juya ya kalli Mai zanen yace" kasan qananun yara basu cika hankali ba, muci gaba da abinda yakawoka "

Mai zanen ya maida hankalinsa wajan zanen amma duk yanda yazana sai yace baiyi ba, sunyi haka yakai sau hudu, daga qarshe kawai dafe kansa yayi da hannunsa 🤦🏻‍♂yace" jeka na sallameka "🤣

*** ***** ***

Da yamma tana kwance afalo tana karatun qur'ani a zuciyarta 🤣sai ganinsa tayi yasauko daga d'akinsa, daga shi sai three quater, da rigar marar hannu, gefen hannunsa ta kallah taga anzane shi da wani zane irinna yan wrestling, kallo d'aya tayi masa takauda kai cikin ranta tace gayu mutanan Allah 🤣

Saida yazo dede kanta ya tsaya, yafara qwalawa sabon maigadi kira, cikin isa yafara cewa "Nuhu"

Amma maigadi baijiba, yasake cewa "Nuhu kai" 🤣🤣

Da gudu yaqaraso har cikin falon, mata shi ne amma da alama yanada iyali
Kayan hannunsa ya watsa masa "dauki wannan Nuhu, maza maza kaje ka wankesu yanzu"

Cikin ladabi yace "to yallabai angama"

Yadebi kayan zai fita yasake cewa "kai Nuhu" 😂

Nuhu yajuyo yace "na'am"

Yace"idan kagama wankin ka wankemin motocina gaba dayansu"

Yace "to yallabai"

Zai juya yatafi yasake cewa "idan kagama ma kaga compound din gidannan yayi datti kasa tiyo ka wankeshi gaba dayansa kajiko Nuhu" 🤣🤣

Bawan Allah yace "to yallabai angama," yafice da sauri
Shikuwa cikin gadara yace "yawwa Nuhu, maza" sannan ya wurga mata harara yayi cikin dakinsa🤣🤣

Tashi tayi zaune tabishi da kallo, Wato da ita yake, shiyasa yaketa nanata sunan Nuhu, saboda jiya yaji tace dama Nuhu ta aura 🤔🤣

Afili tace lalle ma mutumin nan, aikuwa Zan rama

*** ***** ***

Haka zaman su ya kasance har tsawo kwana uku, kuma kullum zata gyara masa gida ta goge, sannan bata denayin girki dashi ba, kullum sai tayi amma ba yaci
Haka ya tattara yawuce Dubai batare daya fada mata ba
Tafiyarsa tayiwa Nawal dadi, saboda tana shiga irin wadda takeso, Babu aiki kullum, ita kadai ce agidan saide ta gyara falo da Dakinta kawai
Har yayi sati biyu, Tun tanajin tsoro harta denaji

Ummi ta kirashi awaya, tace"Baffah shiru ake jinka katafi, yaushe zaka dawo ne?kasanfa yanzu kanada iyali, idan kasan zaaka dade haka aida saiku tafi tare, Pls yaushe zaka dawo? "

" Ummi itace tace ai Babu damuwa natafi, tafison kusa dake "

" to koma de mekake kakamo hanya kataho gida,"

" to Ummi insha Allah "

Ummi tana kashe wayar saita kira Nawal domin ta tabbatar da maganar Baffah, tana kira bayan sun gaisa tace" yaya Baffah ina fatan yana lafiya? "

Zuciyar Nawal daya tace" lafiya kalau wallahi Ummi, dazu ma yafice 🙆🏻😂"

Ummi ta jinjina kai tace toki gaishe shi 🤣, daga nan sukai sallama

Shiru tayi tana tunani, haqiqa Baffah yayi sa'ar mata, amma ita kam sai du'a'i🙊😂

Bayan kwana biyu Sultan ya kirata yace yashigo Abuja zaizo gidan nata, cikin murna ta tashi tafara yimasa girki Mai dadi
Lokacin dayace yazo unguwar da temakon Nuhu maigadi 🤣yaqaraso
Cikin murna ta rungumeshi, shima cikeda murna yabata kayanda yasiyo mata, qananun kaya dakuma fruit
afalo ya zauna ta gabatar masa da abinci, yaci sosai, sannan tahada shi da Nuhu yarakashi gidan Ummi suka gaisa dashi sannan suka dawo gida

Sun dade suna fira, ya kalleta sosaai yace"Baby ki kwantar da hankalin ki, naga duk kin dan rame, kinga idan ummah ta tambayeni yana ganki ba zataji dad'i ba idan nace kin rame "

Damuwa ta bayyana a fuskarta tace" to yaya insha Allah "

Sai wajan yammah yace zai tafi, tara koshi yar bakin gate, futowa sukai daga gidan suna tafe suna fira, ya dakata ya kalleta" to Baby nah, kijuya kikoma gida, "

Idonta ne yayi raurau zatai kuka

Yace" au sai kinyi na gadon de 🤣🤣"

Da taga yana mata daria kawai saita fashe masa da kuka, tace" Allah yaya ni banajin dadin gidan nan"

"bayanta yabubbuga yace" kiyi hakuri kinji, wataran zaki saba, "yasa hannu ya share mata hawayen idonta

Karaf a idon mk da'aka daukoshi amota daga Airport, cikin sauri yaacewa direba" dakata "

Direba ya tsaya, saida yagama ganin komai, har zuwa lokacin da Sultan yajuya yatafi, sannan itama tashige gidan

Lalle yau yarinyar nan zata tattara tabar masa gida, ashe maza take kawowa idan yafita, wannan shine Nuhu, shine nuhun datake cewa sai yazo kenan

Kallan direba yayi, "mu qarasa direba"

Suna zuwa cikin gida yadauki jakar sa yashige ciki, direct Dakinta yawuce ya murda handle din amma yaji arufe

Alokacin ita kuma bata jishi ba tana toilet

Dakin sa yawuce, yafara hargitsa sumar kansa, ko masallaci bai iya fitaba, saide yayi sallar adaki

Zuciyarsa ce ta bashi shawara akan ya qyale yarinyar saboda gudun raini
Nan take yadau shawarar data bashi
Har dare yayi ya kwanta, Nawal batasan yazoba, saboda kawai falo tazo ta agyara, sannan tayi wanke wanke takoma daki

Tun karfe goma yakashe wutar dakin ya kwanta bacci, amma baccin ya gagara daukarsa
Kawai sune suke fado masa a idon zuciyarsa

Tsaki yasaki, to menene ma Zan damu Dan takawo saurayinta gida, nida ba sonta nakeba

Wata zuciyar tace dashi to meyasa kake kishinta?
Girgiza kansa yafara yi, wannan ba kishi bane🤣🤣haqqin aure na nake karewa🙈

Har shadaya tayi bai runtsa ba, yatashi yafara zagaya dakin yana tunanin mafita

Yakoma ya kwanta, daga qarshe de mk har qarfe daya na dare idonsa biyu yakasa bacci 😂

Dirowa yayi daga kan gadon yana cewa "kai wallahi bazai iyuba, dole naje ta fadamin uban waye yace takawomin saurayi gida🙆🏻😂

Da gashi sai jallabiya, yasauko qasa, yana zuwa yatura kofar dakin yayi sa'ah abude take

Ganinta yayi tana bacci hankalin ta kwance, doguwar Rigace a jikinta ta bacci Mai Dan kauri, ta dauki fillo ta rungume, yanda ta rungume fillo din yasa nashanunta sake baiyana awaje

Kasa dauke idonsa yayi akanta
Yaqurawa Kirjinta ido yana kallo
Amma daya tuno yanda yaganta ta tsaya da wani, sai ransa yabaci
Fillo din datai matashi dashi, yafara bubbugawa "ke"

Bata tashi ba, yasake bugawa da karfi "ke, ki tashi nace"

Juyi tayi ta kalleshi da idanunta cikeda bacci, yanda ta kalleshin kadai yasa jini da jijiyar jikinsa de na aiki nawucin gadi 🤣

Ta yunqura ta tashi zaune tace "lafiya?"

"biyoni"

Ta shi tayi tasaka hijabi tabiyoshi abaya

Taga yanufi harabar gidan itama ta doru abayansa
Wajan motarsa sukaje, yabude Mota yace "shiga"

Ta shiga ta zauna tana cewa ikon Allah, karfe daya da na dare ko Ummi
ce Babu lafiya? 🙆🏻😳

Shima shigowa yayi yaja motar aguje sukabar gidan, ya dade rabonsa da driving, haka yake sharara gudu akan titi

Tajuyo tadubeshi tace "ina zamuje ne?"

Fuskarsa atamke Babu alamun Fara'ah yace "kezan tambaya, kifadamin inane gidan sa yake?"







(tofa 🤔kishi yakama maza)








Sharhi please 🙏🏻


















Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE 🌺

(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub


Banyi tunanin NI DAKE yanada masoya hakaba,yau wannan labari yasa nasamu alkhaairi ta yanda zansai data inci gaba da posting abina 💃🏻💃🏻💃🏻, wannan shafin nasadaukar dashi ne ga cmrd Abdul Bauchi, Allah yabar zumunci


27&28

"gidansa yana kano"

Wani irin wawan birki yataka, kanta yasake buguwa da jikin kujerar datake zaune saboda batasa belt ba

Cikin masifa yace"ina fada kina fada "yafuto daga cikin motar, ya zagaya yabude mata gefen datake zaune yace" Futo"

Tajuyo ta kalleshi tace "ina Zan sauko?"

"kifuto kije gidansa, gara kikoma can dazama akan kidinga kiransa yana shigomin cikin gida"

Ta kalleshi, tasake kallansa dakyau "acikin wannan tsohon daren Zan futo daga cikin motar nan? Inje ina? Ina bacci katasoni kafuto Dani wannan wajan, Dan haka saide kamaidani"

Qugunsa ya riqe yace "Owwk, yanzu kuwa Zan futo dake, tunda ke wuyanki yayi qwari, bakida mutunci bakida tarbiya mijin ki yana fada kina fada, to yau kuwa NI DAKE dan halak kafasa" yana kaiwa naan yasa hannunsa yafusgota daga cikin motar, cikin sassarfa tafuto daga cikin motar tasaki qara saboda ta saddaqar ma tafadi aqasa
dasauri yasake fuzgota jikinsa ganin zata fadi, sai gata tafada saman Kirjinsa

Kuka tasaki Mai ciwo,tasake qanqameshi, sosai take rinza assala akan qirjinsa, hawayenta yana sauka ajikinsa, shikuwa yaqame yakasa aikata mata komai

Rigar dake jikintace ta bashi damar jin albarkatun qirjinta anasa, wani irin yanayi yajishi aciki, saboda duk matan dayake runguma bayajin hakan
Saukar hannunsa Nawal taji agadon bayanta, alamun sake rungumeta yayi
Kuka taci gaba dayi cikin kukan tace masa "yaya nanefa, dsme fathr and mothr"

Lokaci daya kunyar kansa ta kamashi, toda mema yakai shi aikata hakan? Shiru yayi yakasa magana saboda aida kunya yace jinake Nuhu ne🤣🤣

Akaro na farko, sai gashi yafara bubbuga bayanta alamun rarrashi 🙈🙊
Amma yakasa cemata komai, kuma yakasa rabata da jikinsa

Asalima daga bubbuga baya saiya sake matseta ajikinsa, ga motoci agefen titi d'aid'aiku suna wucewa

Jin yayi baya Kamar zasu fad'i yasa tayi saurin kallansa, shima Kallanta yayi ayayinda qafafunsa suka kasa daukarsu

Ahankali tafara zare jikinta daga nasa, shima bai hanata ba,motar tashige tareda rufowa,shima cikin rashin kuzari yashiga yaja motar suka fara tafiya
Babu wanda yace da dan'uwansa komai har suka qarasa gida

Nuhu yana zaune idonsa biyu, Dan yasan idan ya kwanta ma zasu dawo

Bude musu yayi suka shigo, yana tsayawa tabude motar tafice, cikin ranta tana cewa Allah yayayewa Baffah masifa, cikin dare tsabar bala'i 🤔

Shikuwa bayanta yabi da kallo yana tuna yanayin da yajishi ciki dazu, zaiso kasancewa cikin wannan yanayin akoda yaushe, but idan kuma yaci gaba da hada jikinsa da yarinyar ai Kamar yaci amanar Baby ne

Da wannan tunanin shima yayi ciki, sai a lokacin yasamu damar bacci 🤣🤣🤣

(yanmata Allah yahadaku da masu sonku na gaskiya masu kishinku)


*** ***** ***

Washe gari saida ta makara wajan aikin gida

Sai wajan karfe tara ta gama komai sai mopping datakeyi, taga ganinsa yafuto daga d'akinsa, cikin sauri tace masa "ina kwana"

Saida yaja wasu second sannan yace"lafiya, "
Yakalli Agogon hannunsa yasake cewa" karfe nawa yanzu? "

Ahankali tace" karfe tara "

" tome kike baki tashi kin tsaftace gidaba?

"kayi hakuri" abinda tace kenan, ta kalli hannunsa, taga
Zanin gado, ya tsaya yafara qwalawa Nuhu kira

Kallansa tayi, domin kuwa taga alama yauma wani wankin zai bashi, tace" Amma sainaga Kamar hakan bai kamata ba "

Ajiyewa yayi aqasa yace" owk, to sannu me masoyi 🤣, tunda bai kamata ba aike sai kiyi abinda yakamatan, kidauka kije ki wanke "

Batayi musu ba tace masa" to"

Shikuwa Baqin ciki ta tokare masa wuya, Wato data bari Nuhu yayi gara ta wanke
Zama yayi a kujera yadora kafa daya kan daya
Yana ganin ta tadauki bedsheet din tanufi wajan da machine yake

Cikin sauri ya Dakatar da ita, "kinga, juya kije kisan Inda zaki wanke, amma ba'a machine ba"

Girgiza kanta tayi tace"ga break fast can nagama"

Cikin bacin rai yace"bazanciba"

Bata sake yimasa magana ba tafice daga falon taje waje tawanke masa, tana cikin shanyawa motar Ummi tashigo gidan

Direba yayi sauri yabude mata kofa tafuto tace"Nawal mezan gani haka? "

Murmushi tayi tace" Ummi wanki nake wlhy, yau tashi nayi da wanki, yanzu ma kayana zandebo na wanke "

Tace" to sannu Nawal Muje ciki, "

Suna shiga ciki taga Baffah azaune kafa daya kan daya yana kallo

Ummi tace"Baffah yazakabarta ita kadai tana wanki? Idan bazakuyi amfani da machine ba ai saikuyi wankin tare😳🤣"

Yace "Ummi wanki kuma?"

Tace"au ita ba mutum bace kenan? "

Sumar kansa ya shafa yayi hanyar fita daga falon 🤣Ummi tace" ina zaka?dawo ka zauna

Dawowa yayi ya zauna, Ummi ta kalli Nawal tace"Nawal yata, jeki dauko kayan wankin naki "

" A a Ummi, nafada, gobe zanyi "

" kije kidauko nace"abinda ummin tace kenan

Cikin sauri taje tadauko kayanta kala daya na atamfa takawo wa Ummi

Ummi ta kalleta tace "meqa masa yaje ya wanke miki"

😳Zaro ido Nawal tayi, cikin rawar murya tace"a a Ummi, wallahi zanyi"

Ummi tace "to bani nisai nawanke tunda shi bazaki bashi ba"

Gabanta na faduwa tabashi kayan, yafizga ahannun ta yayi waje

Yana fita Ummi tace "Nawal kiyi hakuri, basai na tambaya ba, nasan wannan aikin Baffah ne, abu daya Zan fada mijin shine kidena tsoronsa, idan kika nuna kina tsoronsa taya gama dake, yanzu ina wayarki ?"

Tace"gata Ummi"

Ummi tace "tome kike jira? Tashi Muje kiyiwa mijin ki video yana miki wanki,🙆🏻😳 hakan zaisa soyaiya Mai qarfi ta shiga tsakanin ku ai, amma kuna zaune haka tayaya zakuso juna?

Musu tafara, amma haka Ummi tasata dole suka dauki waya zasu futo harabar gidan


Shikuwa yana futowa yayi watsi da kayan🤣🤣, Nuhu daya ganshi da kaya cikin sauri ya qaraso yasa hannu zai dauki kayan yana cewa "bari a temaka ma yallabai" zuciyarsa daya yasa hannu yadauki rigar hannunsa bai sauka a ko'inaba sai adede breast cup din rigar
🤣🤣

Cikin sauri ya kaiwa kayan wata irin fizga 🤣🤣yace"no Barshi kawai"

Shima Nuhu yariqe rigar, yana cewa "haba yallabai ba girman ka bane🤣🤣"

Awannan halin su Ummi sukazo suka samesu, shi yanajan riga Nuhu naja 😃😂

Yana ganin su Ummi ya fizge rigar, yajefata acikin boket din datai wankin, yafara wankewa

Ummi ta kalleshi tayi Murmushi, ta kalli Nawal tace "fara daukar sa mana mekike jira?" 🤣🤣
Cikin sauri yadago kansa mezata dauka? Yake tmbyr kansa

Sai gani yayi Nawal tadaga waya tana masa video
Baqin ciki ne ya hanashi magana, addu'ah kawai yake aransa Ummi tabar gidan
Yakama yarinyar nan

Saida Ummi tasata tadaukeshi tas, harya gama wanke rigar sannan suka koma ciki

Shima yana shigowa takama kunnansa ta riqe, saida tasake yimasa fada, sannan tayi musu sallama tatafi

Bayan sun rakata ta shiga Mota suka juyo ciki, cikin sauri yafara tafiya yanaso yakamata, tana ganin haka tayi gudu tashige dakinta tareda rufewa

Wajan Nuhu ya koma yafada masa cewa yaje yayi aikin dayyabu, shikuma dayyabu yadawo aikinsa nada

*** ***** ***

Har dare yana dakonta, amma bata bude kofarba, haka ya hakura yaje ya kwanta yana Allah Allah gari ya waye

Washe gari kuwa gari nayin haske bayan yadawo daga masallaci yashiga dakin nata, hamdala yayi dabai jishi arufeba
Akwance yaganta akan gado tana rawar sanyi

Qarasawa yayi wajan ta yace"ke meyake damunki? "

Zafin zazzabi yahanata magana, sai rawar sanyi take
Bargon data rufa dashi ya yaye, wani zafi ya dakeshi
Cikin sauri yakai hannunsa wuyanta yaji zafi sosai

Fita yayi daga dakin yaje kitchen ko zai samu abinda zai bata, amma Babu
Yakunna gas, yarasa me zaiyi? Saboda Babu abinda ya iya

Fridge yabude yadebi fruit yakai mata, batare da yayi mata magana ba yatasheta, yadora mata fruit din akan cinyarta
Kadan taci da kanta, sannan yabata magani tasha, ta koma ta kwanta

Agefen gadon nata ya zauna yakasa fita, tausayin tane ya kamashi, yau de kam badan wannan jinyar ba, sai jikinta ya gaya mata

Wannan shine karo na farko daya farajin tausayin ta, shi mutum ne Mai tausayi amma yarasa dalilin dayasa yakasa yiwa yarinyar

Kasa fita yayi daga dakin, yayi shiru kawai yana tunani, kusan minti ashirin dashaan maganin ta yaji yana sheshshekar kuka

Kallanta yayi, "me kuma aka miki?"

Cikin kuka tace Allah kuwa sanyi nakeji, nikam inajin mutuwa zanyi

Tausayi tasake bashi, yace "bari nayi waya akawomin allura saina miki"

Cikin kukan Tace "Allah ni banasan allura, wallahi bazaka min ba"

"jikin ki" abinda yace kenan ya shareta

Kuka taci gaba dayi, dukta cika masa kunne, yamiqe tsaye yace "bari kiga natashi nabar miki wajan saikisan da Wanda zakiyi🤣🤣"

Yamiqe yayi hanyar fita daga dakin take rushewa da kuka, dawowa yayi ya tsaya yace"kinaso kidena jin sanyin? "

Daga masa kai tayi

Yace" bari na temaka miki minti biyar "
yana fadar haka Yarufe kofar dakin yasaki labule,duhu yasake wanzuwa a dakin

Jin yace zai taimaka mata kuma taji shiru yasa ta bude idonta, sai ganinsa tayi yana kokarin cire jallabiyar jikinsa😳🙆🏻

Cikin sauri tafara cewa" A a, banaso, wallahi banaso"

Yace"yarinya, temako kika nema, kuma sai sanyi miki "
Rigarsa yacire yarage daga shi sai boxer
Tana ganin murdaddan jikinsa ta runtse idonta, gashi batada karfin hanawa

Tanajinsa yaja blanket din datake ciki shima yashige ciki, tareda mannata a Kirjinsa, Ahankali tafara kwace jikinta, amma haka yasa hannu yadawo da ita cikin jikinsa yarungumeta sosai, dumin da yaji a jikinta yasa yaqara matseta ajikinsa

Kansa yadora a wuyanta yana goga mata jikinsa ako'ina na jikinta
Hawaye ne yake silalowa daga idonta, babu damar qwacewa, body contact aka samu sosai atsakaninsu

Saiji yayi tayi shiru alamar bacci ya dauketa, memakon yasaketa saiya sake maida ta cikin jikinsa tareda lumshe idonsa
Tunaninsa ne yake neman barin jikinsa, Ahankali yatashi idonsa yayi jajir
Yafice daga dakin

Daakinsa ya koma yazauna yadafe kansa, yayi tunanin idan yasakejinsa acikin wannan yanayin zaiji sauqin abinda yakeji, ashe ba haka bane wata masifar zai sake ballowa kansa

Shide ba mazinaci bane, bazai so ya aikata yanzu dayake da aure ba, Dan haka dole zaiyi tunanin mafita, dole zai nemawa kansa mafita akan neman Baby, yazama dole yafara neman yarinyar ta kowacce hanya
Daga haka yatashi yashige toilet


Zuwa yamma jikinta ya warware, tana jiyo motsinsa afalo taqi fita, toda wanne ido zata kalleshi? Bayan yanda taganshi dazu Babu maraba da rashin kaya, wannan gajeren wandon Babu abinda baya nunawa, amma kuma ya akai taji jikinta da Dan sauqi? Bade wannan abin daya mata ne yasa hakaba? Tunani tafara inama ace daga wajan mk ne tasamu hakan? Da Babu abinda zai hana ta sallama masa komai, istighfari tayi tareda lumshe idonta takoma cikin bargo


*** ***** ***

Ummi ta kirashi awaya ta sanar dashi cewa zataje saudia umara, tanaso sutafi da Nawal

Haka kawai yaji aransa cewa bayaso yarinyar tayi nesa dashi, Dan haka yace wa Ummi ba zataje ba
Ummi tace yayi hakuri sati biyu zasuyi kawai, shima saiya tafi Dubai idan sun dawo saiya dawo
Badan ransa yasoba ya amince, cikin satin yatafi, suma kuma asatin suka tafi umara

Tunda suka je datage da addu'ah akan Allah ya nuna mata mk koda a tv ne sau daya arayuwarta, sannan tayi addu'ah akan Allah ya cire mata sonsa daga cikon zuciyar ta, saboda tasamu dama da qwarin gwiwar yiwa mijinta biyyaiya
Daga qarshe tayiwa Baffah addu'ah akan Allah ya shiryeshi idan mai shiryuwa ne 🙊🤣🤣😂

Amma Ummi kam maqasudin zuwan nata da Nawal shine akan tayiwa Baffah addu'ah Allah ya shiryeshi, domin kuwa ita addu'ar mata akan mijinta, batada hijabi awajan ubangiji

Sunyi siyaiya sosai, Ummi ta kashe mata kudi baana wasaba, duk wani kayan ado na yanmata tasiya mata

Har suka dawo Nigeria lafiya, takira su ummah ta dinga basu labari, Inda tace ta ajiye musu tsarabar su duk lokacin dazasuzo da Baffah zata kawo musu 🤣

Kwananta biyu da dawowa amma Baffah bai dawoba
Tunani tafara, ko yaushe ne zaman aurensu zai daidai ta? Gaskya yakamata tafara kawowa gidan nan nasu gyara

Tsamm tamiqe tashige cikin d'akinsa, komai neat Babu wani datti, dakin ya birgeta, haka kuma Babu abinda Babu sirkin baqi aciki

Afili ta furta "wannan mutumin yana son abu baqi da alama"
Bedside drower tajawo taga wata hadaddiyar akwati aciki

Jikin akwatin kadai ma antsarashi sosai, ciki sauri ta bude taga wasuma zobuna guda biyu na azurfa,qarami da Babba, irinsu daya sak, anyi musu ado da Baqin stones, acikin stones din anyi harafin 'B' da farin kala

Kalla tayi tasake kallah, B da B tome yake nufi? Shide nasa B din tasan cewa Baffah take nufi to amma dayar fa? Wata zuciyar tace da ita Budurwarsa yake nufi mana, wadda yake kuka akanta, yake kiran mutum takanas azana masa ita

Baqin ciki yakamata, duk hakuri da biyaiyar datake baya gani shi watama yake yiwa hidima, zoben hannun ta takalla, ita kuwa saida Ummi tasashi yasiya mata

Rufewa tayi tamayar masa tafice daga dakin zuwa falon, tadauki waya takira Nas

"Nas yakike ya garin?"

"lafiya Beauty, yagida yame gida?"

Adede lokacin yashigo cikin falon, dawowar sa kenan daga Dubai

Itama sarai taganshi, taci gaba

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment