Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama

Murmushi sukai dukansu, Nas cikin ranta tace Nawal ana can ana karbar hadda🤣

Anan wajan Ummi suka zauna sukaci gaba da fira
Sannan Najma tashige daki tafara hada musu kayansu



*** ***** ***



Kuka takeyi qasa qasa tana shagwaba
Ya sunkuyarda kansa yayi kissing gashinta Mai laushi dayake jiqe da ruwa alamun tayi wanka
Yace"Baby nah, shikkenan fa, daga yanzu fa bazaki qara jin ciwon komai ba "

Cikin kuka tace" ba kaine kace min iya baki zaka shaba "

Yace" Baby danaga kema kinaso shine fa nad'anyi kadan, kuma Baby nah ninefa Baffan ki, ai kinsan bazan cutar dakeba "

Hawaye yazubo mata tace" tanawa kuma "🤣

Daria ta bashi, saida ya murmusa sannan ya rungumeta ajikinsa yace" to kiyi shiru, Baffan ki yayi laifi, kiyi hakuri kinji, ni daga yanzu ma sai kince kin amince zanyi "

Harararsa tayi ta maida kanta qirjinsa, sai kukan shagwaba take masa, shikuma yakasa daina lallabata, kwantar da ita yayi sannan shima ya kwanta, yaja musu bargo, Ahankali yatura hannunsa cikin rigarta, yana wasa da ita, yace" gobe da sassafe saimu tafi gidan Ummin ko 🤣

Tace"niba Inda zani," 🤣

Yayi Murmushi tareda dora bakinsa cikin kunnanta yana mata rada, wadda ni kaina banajin Mai yake fada mata

Yinin ranar haka yayi shi yana riritata, yahanata aikata komai, tana zaune shine yake mata duk abinda takeso, kulawar data rasa a wancan lokacin tasameta a yanzu




*** ***** ***




Washe gari su yasir suka shirya, zasu tafi,🤣Har wajan azahar Babu labarin mk bare Baby
Ummi tace kukirasu mana awaya, jiya sunce min zasu shigo ai🤣

Najma tace "Ummi nide nakirata wayarta akashe Tun dasafe"

Yasir yace "to bari na kirashi kawai"

Yakira harta gama ringing ba'a dagaba 🤣yasake kira nanma ba'a amsaba, sai ana ukunne yadaga cikin muryar bacci 🙊😳

Yasir yace "Abokina mun shirya fa, zamu wuce"

Daqyar yace"Yas ka fadawa Ummi tayi musu abinda yakamata kawai, ba zamu samu damar shigowa ba "

Yace" Ok "tareda fadawa Ummi yanda sukayi🤣

Murmushi tayi aranta tace dama nasani 🤣qarya Baffah ya shirya min

Cikin lokaci qanqani tahada musu duk abinda yakamata, sosaai tasa akayi musu tsaraba, sannan tarakosu har gate sukayi sallama dasu


Basu dauki lokaci Mai tsawo ba suka sauka akano, kai tsaye gidansu Najma yasir yakai su
Sannan yayi musu sallama yayi gida
Haka suka dauki kaya niqi niqi sukai cikin gidan

Najma na gaba tabude gate tashige
Itama Nasrin tazo zata shige ga kaya ahannun ta gaduk ta gaji, bata wani lura ba saiji tayi taci karo da mutum

Babbar ledar hannunta tafadi aqasa
Tayi taga-taga zata fadi cikin sauri yariqo hannunta
Yace "Sannu Nasrin, ba kiji ciwo bade ko? Yana tambayarta yana kallan goshinta Kamar zai daura hannunsa awajan 🙊

Cikin kunya tace" yaya Sultan Babu komai wallahi, banji ciwo sosai ba "

Yace" Ok,"
Yasa hannu zai daukar mata ledar data yar aqasa itama tasa hannu zata dauka, nan take hannunsu yahadu, wani irin yarrr sukaji, atare kowa ya janye hannunsa



Najma na Qarasawa cikin falon nasu taga ummah da mama da wata baquwar fuska azaune, yarinya ce bazata wuce sa'ar suba


Ummah tace" sannunku dazuwa Najma, ya hanya? "

Tace" Ummah wallahi alhmdlh, nahau jirgi de🤣🤣"

Gaba dayansu sukai daria mama mariya tace" Najma ga Surayya fa, amaryar Nuhu ce 😱🤣, dazu yakawo ta mu gaisa "

Najma tace" yaushe Nuhu yayi aure? "















(ina labarin mutanan bakin gate ne? 🤔)






Fan's na facebook yaya hakurinmu na shekaran jiya? 😱Dayawa basuga posting ba, Allah yaqara kiyaye wa gaba🙏🏻








Dan Allah inka karanta kamin Comments ko sharhi kafin kawuce 🙏🏻








Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub


Wannan page din gaba dayansa na sadaukar dashi ga 'yan group dina NIDAKE fan's, inajin dadin yanda kukemin sharhi kullum bakwa gajiya, i luv you All wallahi 💋💋💃🏻💃🏻💃🏻


47&48



Ummah tace"wallahi muma bamu jiba Najma, sai yanzu kawai muka ganshi da amaryar sa"😀
Ta qarasa maganar cikin daria

"um to Allah ya basu zaman lafiya" ta kalli surayya tace"zomuje ciki amarya "

Surayya tatashi cikin kunya tabita daki



*** ***** ***



Wata irin kunya ce ta kamashi, meyake shirin faruwa dashi ne akan qawar qanwarsa? Cikin kuskurin kunya yace" bari nakai muku kayan ciki "

Cikin sauri tace" A a wallahi yaya Sultan Zan iya, nagode "tana fadar haka tadauki ledar tashige cikin gidan itama Gabanta na faduwa, meyasa taji wannan yanayin awajan yaya Sultan? Innalillah... Allah yasa de kada yayi mata wata fassarar ta daban 🙆🏻

Tana wannan tunanin tashige gida anan su ummah sukayi mata sannu dazuwa itama tashige cikin daki zata huta daga nan kuma Najma ta rakata gida



*** ***** ***



Ahannun sa yad'auketa Kamar jaririya, yabude kofa daga baya yayi hanyar swimming pool da ita
Dagashi sai vest da wani guntun wando, yayinda itama yasaka mata wata 'yar qaramar riga wadda iyakarta cinyoyinta kanta Babu komai kawai daure gashin tayi da ribom, saida suka qarasa wajan sannan ya tsugunna yadora ta akan cinyarsa yazura qafafunsa cikin Ruwan

Qanqameshi tayi tace"dan Allah karmu shiga, Allah tsoro nakeji"

Lakace mata hanci yayi "matsoraciya kawai, tobaga niba, ai tare zamuyi wankan"

Tace"um um, nikam banaso abinda mutum zaizo yasha ruwa "

Daria yayi, ta kalleshi tace" mai Babban suna daria tanama kyau, but bakayi "

Kallanta yayi" ko kinaso nadinga yiwa yanmata kinga saina samo miki Abokiyar zama"

Tace "Dan Allah kadena wannan mafarkin"

"Ok mafarki ma nake ko?"

Tace "emana, ni kadai ce agidan mijina, babu wata fara bare baqar dakake mugun so"

Yace"inye, d'an sake fada naji, "

" mezan fadama? "

" kalmar dakika fada ta mijinki, duk da baki fadamin ba gashi yanzu kishi yasa anbaiyana "

Murmushi tayi taboye fuskarta aqirjinsa

Kallanta yayi Cikeda tsananin so, yanda ta kwantar da kanta aqirjinsa Kamar Baby saiya birgeshi
Ahankali yafada cikin Ruwan tana riqe ahannun sa

Zabura tayi tasake rirriqeshi, yace" wai tsoron menene? Nida nakeso mudinga zuwa kullum muna hutawa awajan "

Tace" um um, nide Allah ban yarda ba "

Murmushi yayi yasa hannu yazare ribom din kanta, kasancewar suna cikin Ruwan nan take gashinta yajiqe, yadebi ruwa ya watsa mata afuskar ta, kukan shagwaba tafara tace" Allah saina rama "
Kafin yace wani abu tadebi Ruwan itama ta zuba masa afuskar sa, haka suka dinga watse watsen ruwa, suna zuba daria

Kallan jikinsa tayi taga dantsan hannunsa duk anyi masa wannan zanan tace" Dan Allah kadena wannan zanen "

" meyasa? Ado nefa "

" nikam banaso, nafiso na kalli fatar mijina haka "

Yace" um Baby nah kenan, Baby me miji, kiyi hakuri insha Allah wataran Zan daina, amma inason sa sosai "

" meyasa bazaka dena yanzu ba? "

Yace" kawai nima hakan nakeji ajikina, Kamar bazan iyaba "

" ai kuwa dolema zaka iya denawa tunda kai Babban mutum ne ba Kamar sauran mutane ba, ana ganin girman ka, ana ganin qimarka, bazai iyu kadinga abu irinna samari marasa jin magana ba"

Shiru yayi yana nazarin kalaman ta, gaskiya tafada masa, but amma ai yana ganin hakan Kamar ba komai bane, ajiyar zuciya yasaki yace "Inasonki Baby nah"

Taji dadin maganar sa, but taso ace ayanzun ya amince wa maganar ta cewa yadena yi d'in, ba ita kadai ba, Ummi ma zataji dadin hakan
Amma sai tayi shiru bata sake yimasa magana ba, gudun kada ta takura masa, gara abi komai asannu

Hannu tasa tad'anja masa gashin dake kwance aqirjinsa, Wanda ya kwanta sosaai saboda Ruwan daaya jiqashi

Ahankali yasaki yar qaramar qara yace"Aucch!!, Baby Allah saina rama nima "yafadi hakan yana kawo hannunsa zuwa qirjinta

Daria tasa tafara kokarin saka hannunta awajan, amma yahanata damar hakan, ya tsaida ta acikin Ruwan tareda manneta da jikinsa, bai sake taba yariqe ta ajikin nasa, hakan ne yafara haaifar musu da wani yanayi, 'yar qaramar rigarta ya janye kadan, abubuwa suka bai yana, sannan yahade bakinsu waje daya



*** **** ***




Najma ta kalli Nasrin tace"Nas kinyi shiru, kokuma duk gajiyar hanyar cene? "

Ajiyar zuciya tasaki, har yanzu idan tatuna abinda yafaru tsakaninta da Sultan takan tsinci kanta cikin wani hali,tarasa meyasa
Abin ya kasa barin qwaqwalwar ta

ajiyar zuciya tasauke tace" gajiya ce kawai Najma, tashi ki rakani gida please "

" gida, haba kibari da yamma basai mutafi ba, kinga nima saina dawo wajan magrib, "

Tace" to Najma Babu damuwa, kinga Beauty har yanzu ko waya🤣"

" Hmm ki qyale yarinyar nan tana can tana soyaiya tama Manta damu, ai sai nayi mata tas wallahi 🤣

Murmushi Nas tayi, anan sukaci gaba da firar duniya, har yamma tayi sannan suka shirya suka futo



*** ***** ***


Suna kwance afalo akan kujera, tana kwance akansa yayinda yake wasa da gashin kanta, yace"Baby nah tashi Muje nayi miki wanka, yamma tayi "

Murmushi tayi," yanzu saikace wata Baby ace wankan ma sai anmin, nika Barshi zanyi da kaina "

Yace" to tashi Muje kiyiwa mijinki "

Shiru tayi, tana boye kanta a qirjinsa yace"yakamata ki hada mana kayanmu fa mutafi cirani" 🤣

Daria tasaki tace"ai kaine kafara, saika dinga saka Nuhu aiki, bayan shi baisan komai ba"

Yace "to kinga laifi na? Mutum Mai mace Kamar wannan tana cewa da wani ta aura" 🤔

Murmushi tayi tace"abinci fa, banyi ba, kuma gashi dare nayi "

" kibarshi kawai zanyi waya sai akawo abinda kikeso "

Tace" A a, zan iyafa, kabari naje nayi "

Riqeta yayi yace" um um Baby, nabaki wahala dayawa yakamata kema ki huta, kada kiyi aiki ki gaji nazo anjima kice baki san zanceba "yaqarasa maganar cikin sigar wasa

Murmushi tayi masa kawai tace" bari nakira su Najma, karsuce namanta dasu"
Yace"to ai wayarki tana daki Tun jiya, amma kikirasu da wannan "
Yabata wayarsa, ta karba takira Najma suka gaisa harda su ummah, ganin number data kirata dashi yasa tasan cewa suna tare da mk shiyasa batayi mata tsiya ba
Number Nasrin takira, Nasrin tana dauka tace" Hello yaya Sultan "

Mamaki yakama Nawal tace" Nas yaya Sultan kuma? Beautynki cefa "

Dafe kai Nasrin tayi🤦🏻‍♀tace" wayyo Beauty kiyi hakuri, wallahi Najma ce tabawa yaya Sultan number ta, to muna waya dashi yanzu sai kiran ya katse, kuma sai naki kiran yashigo to nayi tunanin shine, shiyasa na kirashi kai tsaye "

Nawal tace" to Nas kode da yaya Sultan din za'ayi ne? "

" kinji da wata magana beauty daga waya? "

Itama tace" to ai dama daga wayar ake farawa daga nan kuma sai maganar saka rana "🤣

Tace" to injuninki sonjin gulma, ba abinda kike tunanin bane, nikam sai anjima "tafadi haka tareda kashe wayar

Nawal tayi Murmushi afili tace" Nas kenan, Allah ya tabbatar miki da alkhaairi qawata Mai bani shawara"🤣

Kallanta yayi yace"mekike nufi? "

Tace" wai tana waya da yaya Sultan ne, yayana Wanda yazo kwanaki, shine take fadamin "

Yace" Sultan kuma? Amma yarimah fa? "

Tace" yarimah Kamar ya? Yana sonta ne?"

Yace" no a wannan yanayin sai anfuto fili ance wance ina sonki? Nakega koda alama mutum ya nuna ma zaka iya ganewa, amma gaskiya ina tunanin yarimah yana son yarinyar nan, duk da bamuyi maganar dashi ba"

Tace "to amma meyasa bazai fada mata ba? Kana nufin yanzu yaya nane zai hakura kenan🤔

Yace "no, dukansu ai abu guda ne awajan mu, Abokina dakuma yayanah, kawai saita Zabi Wanda yamata acikinsu, Sultan ko yarimah, kinga ita tahada Sarki da d'an sarki 🤣"

Tace "um saita hakura dasu gaba dayansu nabata yaya Salisu"

"waye yaya Salisu?"

Tace "shine Babban yayanmu, har yanzu bakasan yan gidanmu ba"

Yace "wai kina nufin yayunki biyu kenan maza?"

Tace"emana, Yaya Sultan yana canji a lagos shikuma yaya Salisu yana zaune a shago akasuwa "

Jinjina kansa yayi yace" to amma sunyi karatu ne? Meyasa basa aik?

"kowa yayi karatu mana, aikin ne basu samu ba, inason yaayuna sosai, suma suna sona, kokadan basason bacin raina"

Yace "tofa yanmata nah, Allah yabarku tare"
Tace "amin


Baisake yimata magana ba yadauketa sukayi ciki daki, kai tsaye toilet yakai ta suka fara wanka, amma har suka gama taqi yarda ta kalleshi, sai janta yake da magana danta kalleshi amma firr taqi yarda
Bayan sun futo sun shirya, yace zaije yadawo, tayi masa fatan dawowa lafiya, sannan tayi kitchen, zobo tahada masa Mai dadi, takoma daaki tadauko rubutun da Malam yayi mata ta zuba musu aciki, sannan tasaka a fridge

Daki takoma tadauki wayarta takunna takira Najma, tace"najma dazu ina tareda mk ne, daan Allah kuyi hakuri, wallahi banyi zaton hakaba, naso nazo to ina bacci kuka taho shikuma Yaqi tashin a

Najma tace "um um Baby, aimu mukaga duniya🤣daga cewa kije bada hakuri shikkenan mukaji shiru, to yanzu ina angon yake?"

Tace"wallahi yafita "

Najma tace"to ki gaishe shi, saida safe"

Daga nan sukai sallama



*** ***** ***




Yana barin gidan ya kira yasir awaya bayan sun gaisa yace"yas Dan Allah idan kaje gidansu Baby nah akan aikin da ake musu, Pls akwai yayunta maza guda biyu da muka magana akan su dazu, inaso katuromin duka takardunsu ta Email dina, kokuma kabasu Email din su turomin gaba daya"

Yace "to Abokina insha Allah za'a turo, ga gaida Ummi"

Daga nan sukai sallama, yasake kiran yarimah, a lokacin yazo gidan Ummi, kafin yafuto daga motar yafara magana dashi
Daga dayan bangaren yarimah yace "mk yau kaida kanka kake kira?"

"wallahi kuwa, yauwa Nas ya mgnr wannan yarinyar ne kuna waya kuwa?"

"wacce yarinya?"

Mk yace"ina nufin qawar Baby nah "🤣

" Ok wai Nas kake nufi? Bama waya, mk yarinyar tana birgeni but naga Kamar zatai rashin ji ne" 🙊

"Ok toba damuwa, bye"

Cikin sauri yarimah yace "wait mk mekake nufi? Meyasa kake tambaya ta?"

"no Babu komai,kawai tambaya nayi"

Yace "to shknn kawai ina ganin zanyiwa Mai martaba magana idan naje gida, saiya tura mutane a nemamin auren ta"

(da kace kai miskili ne🤔)

Mk yace"duk yanda kayi "

Shima Nas din yace" Ok ka gaida amarya "batare dayace komai ba ya kashe wayar, yana ganin wannan itace hanya mafi sauqi dazai hada yarimah da Nasrin, idan yaso ita kuma acikinsu saita Zabi Wanda yamata kawai

Futowa yayi daga cikon motar yashige cikin gidan


Ummi taana zaune sai ganinsa tayi, suna hada ido ya sunkuyarda kansa qasa, yaje Gabanta Yazauna aqasa kafet yace "Ummi ina wuni"

"lafiya Baffah, ina Nawal"

"tana lafiya Ummi, tana gida, batasan zanzo nan bama"

Tace"ok to alhmdlh, haka akeso "

Addu'ah yafara cikin ransa Allah yasa kada tayi masa maganar qin zuwansu
Kuma sai akai dace ba tace dashi komai ba

Shine ya katse shirunsu da cewa" Ummi inaso muwuce Dubai this week idan kin amince"

Tace"haba Baffah, kai da matarka tayaya zan hanaku tafiya,? Kawai de abu daya nake jira awajan ka har yanzu, Kaai kuma naga alamar bakada niyya akansa"

Yace"Ummi mekike so?"

Tace" takardar Danace kabawa Nawal kwanaki kace bazaka iyaba saide ta addmission🤣🤣, shine har yanzu naji shiru Babu takardar addmission Babu labarin ta "

Murmushi yayi yace" Ummi daso nake anema mata makaranta mai kyau a Dubai saita fara karatun ta idan munje yanxu, nima inci gaba da ayyukana, amma yaya kika gani? "


Farin ciki yakamata, tace " Alhamdulillah, kayi tunani Mai kyau Baffah nah, ilimi shine hasken rayuwa, sannan zaka shiga da matarka duk Inda kakeso, gaskya naji dadi, Allah yayi muku albarka"

Yace"amin Ummi "

Anan Yazauna suna fira jefi jefi tace yasamu sutafi adamawa gaba dayansu suga Nawal din itama ta gansu kafin su tafi Dubai, yace insha Allah zai shirya musu tafiyar gaba dayansu

Sai dare yabar gidan Ummi, ya yi musu take away yanufi gida





*** ***** ***



Tana zaune tana kallo ita kadai yashigo, tashi tayi ta karbi kayan hannunsa, yayinda yaja ta jikinsa yayi rungumeta yace"haka ake tarbar maigida "
Tayi Murmushi kawai, shida kansa yahada musu Abincin, taje tadauko zobon data hada musu, bayan sun gama cin Abincin ta zuba musu suka sha gaba dayansu, tana kallansa har wani lumshe ido yake🤣🤣itade fatanta daya Allah ubangiji yaqara shirya mata mijinta, yakuma shirye su baki daya

Bayan sun gama kowa yayi wanka, ya rungumeta suka kwanta, babu abinda yamata, taji dadin hakan sosai, yayinda anasa bangaren baiso hakanba, kawai de baisan takura wa Babynsa ne


Washe gari da kansa yayi abinda yakamata ya shirya musu tafiya Adamawa shida ita dakuma Ummi
Jirgi sukabi, aikuwa nan da nan sukaje, anzaga da ita dangi taga kowa, shi kansa yaji dadin zuwa saboda yadade rabonsa da garin, manyan kayan daya saka da taimakon matarsa 🤣sai suka qara masa kwarjini dama gashi da abinsa

Kowa yaji dadin yanda ya ganshi musanman iyayen sa maza

Washe gari suka dawo Abuja, Nawal taso taje gida amma haka yahanata yace duk lokacin datake son zuwa gida kofa abude take sai tazo ta gansu takoma amma banda yanzu


Babu yanda ta iya haka ta hakura,daga nan sukai shirin tafiya Dubai, Inda yad'auki matarsa suka lula, saide fatan Allah ya saukesu lafiya














('yan whtspp abin kuma harda sibaran na baiye🤔,? Please 🙏🏻masu daukomin littafi sumin posting a whatsapp ni bana posting sai dare, only facebook ne kawai nake musu posting da safe saboda nasamu damar ganin Comment din mutane naji ra'ayin su sannan nayi reply, bazai iyu nayi posting lokaci daya sannan na yiwa masumin sharhi reply ba, thts why nake rabawa, amma wasu suna daukomin sumin posting kuma mutum yamin sharhi ko Comment nagani nayi shiru bazaiji dadiba tunda nina nemi amin sharhin, da niyya nake hakan wasu atura musu da safe wasu da daddare, amma posting din jiya ma can naganoshi yana yawo a groups din mutane 🤔,
Ban hana kowa turawaba but sai dare nake posting a whatsapp, Allah yasa kun fahimceni 🙏🏻🙏🏻









Amnah El Yaqoub ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub


Dedicated to ❤ALKAWARI HAUSA NOVEL✊🏻kuyi yanda kukeso dashi wannan page din nakune 'yan Amana😘😘😘💃🏻


49&50




Saukarsu gidansa anan Nawal taga duniya iri-iri, hannun ta nacikin nasa amma kawai binsa take hankalinta yana wajan kalle-kalle

Har suka shigo falon bai saki hannun taba,anan taga duniya, saitaga gidansu na Nigeria ma aiba gida bane akan wannan
Kan kujera yafada yana fadin"wash, Baby nagaji wallahi, please yakamata ayimin ko massage ne nasamu "

Kallansa tayi tace" mai Babban suna, Muje mufara sallah de kaci abinci sannan wanka "

" Dan Allah Baby pls stp tellng me dis name, kawai nide kisake min wani "
" yanzu duk muhammadu ai Mai Babban sunane, menene laifin sunan? 🤣
Sannan ko acikin wayata muhammadu kasamin saboda baka sona, "ta qarasa maganar tana juya masa baya alamun fishi

Saida yadafe 🤦🏻‍♂sannan yasa hannu yajuyo da ita tana facing dinsa," Baby menene kuma abin fishi anan? Nine nace miki bana sonki?sannan saboda wa nayi hakan? Idan zakimin adalci saboda ke nayi, duk a dalilin kine hakan tafaru, Baby na NI DAKE dole ne muyiwa junanmu uzuri tunda kowa saboda dan'uwansa yayi hakan"

Baki ta turo gaba taqiyin magana yakama kunnansa da hannunsa biyu yace"sorry, nayi laifi kuma ina qara neman tuba a gareki, amma pls a sauyamin sunan nan, kinji? Ya qarasa maganar cikin kallan qwayar idonta
Tadaga masa kai

Tashi yayi tsaye yameqa mata hannu yace"oya tashi Muje namiki wanka muyi sallah "
Babu musu tabashi hannunta, yaja ta zuwa wani dakin daban, Wanda ba nasaba yace" toga dakinki, idan akwai abinda bai yi miki ba sai kiyi oder akawo miki "

Kafin tayi magana yafara cire mata kaya yace" wanka "

Batayi masa musu ba itama ta tayashi yagama cire mata kayan, ta daura wani Dan qaramin towel, kallanta yake kawai yana hadiyar yawu, ita kanta ta lura da yanda yazuba mata ido tasan abuqace yake da ita, amma saita share shi tashige cikin toilet din

Tana shiga toilet din yasaki ajiyar zuciya tareda fadawa kan gadon, cikin ransa yana cewa yarinyar nan zata kasheni



*** ***** ***


Tana kwance adaki wayarta tayi qara, number ta duba taga Kamar number da yasir ya kirata rannan a Abuja

Dauka tayi tareda sallama
Yace"yanmata adon gari idan baku bagari "

Tanajin muryar tagane cewa shine" ina yini "

Yace" lafiya kalau, ya kike yaya samari "

" suna nan kalau suna gaisheku "

Dasauri yace" haba? "
Mamaki ne yakamata, tace" da gaske nake"

Ajiyar zuciya yasauke yace "Najma inaso zamuyi magana dake,amma bansaniba ko kinada lokaci"

Jin yanda yayi magana cikin nutsuwa Babu alamar wasa yasa tafahimci cewa lalle maganar me muhinmanci ce tace "to inajin ka yanzu ma inada lokaci"

Yace "Najma wallahi Tun lokacin dana fara ganinki kika kware min 🤣
Alokacin nakasa dauke idona akanki, kuma Tun daga lokacin kike kwance acikin zuciyata, bansaniba ko zaki amince da buqatata"

Jikinta ne yayi sanyi, kunyar sa duk saita kamata, takasa bashi amsa, dayaji shirun yafara yawa yace"najma ko akwai damuwa ne? "

Tace" A a, saide bana tunanin za'amin aure agida yanzu, saboda makaranta ma Zan tafi, Baby ma da kaga anyi mata aure yanzu akwai dalilin dayasa, amma banda wannan abban mu bazai mata aure ba "

Yace" naji bayaninki, amma aure baya hana karatu, ni kaina Zan iya nema miki makaranta, fatana kawai kibani dama nashiga cikin jerin manema auren ki"

Tace"bazan iya baka amsa kai tsaye ba, saide na baka dama kasamu Abba nah kuyi magana, duk abinda yayanke akaina shikkenan "

Dadi yaji acikin ransa, cikin murna yace" yawwa nagode, yanzu de hakan ya nuna ana sona"

Cikin wasa tace"tabdi waye zai soka bayan duk kun tsufa, kundade agida Babu aure "

Daria ce ta kamashi yace" yarinya tsada muke shiyasa, "

Tace" baabu wani tsada arahace tamuku yawa "tana fadar haka takashe wayar, shima anasa bangaren ya zubawa wayar ido yanaji aransa Kamar yasauke wani nauyi dake kansa



*** ***** ***



Tunda yazo wajan take ta kallansa, taga gayen yahadu sosai, amma kuma tayaya zata iya masa magana? Gashi da alama baya shiga harkar daba tasaba, domin kuwa tunda yazo kamfanin bataga yayiwa kowa magana ba, ta kalli dressing din jikinsa duk da kayan bamasu tsada bane wankan yamasa kyau, gashi fari kyakykyawan gaske

Daga kanta tayi sama tana tunanin hanyar dazatabi ya yi mata magana da kansa batare data zubar da ajinta wajan yimasa maganaba

Ahankali tatashi daga Inda take tawuce ta gabansa taga baima kalleta ba🤣

Tasake dawowa tawuce taga ya maida hankalinsa kan wayar dake hannunsa 🤣🤣

Haushi yafara kamata, ta kalli mutanan wajan taga kowa harkar sa yake baabu ma Wanda yasan ta nayi Dan haka tafara tafiya Ahankali saida tazo daidai kujerar dayake zaune tadafe kanta tareda runtse idonta🤦🏻‍♀tace"wayyo Allah na kaina saita fara tafiya luuuu zata fad'i da niyya ita ala dole jiri ne yadebeta 🤣
Dago kansa yayi Dasauri yaga mace tana kokarin fado masa aka 🙊
Dasauri yaamatsa aikuwa sai gata tafadi agefen kujerar dayake zaune 🤣

Yace"subhanallah, baiwar Allah lafiyarki kuwa? "

Yamutsa fuska tayi tace" kaina, kaina ne yake min ciwo sosai, ko zaka taimaka min da ruwa? "

Dasauri yace" to "yaje ya nemo ruwa yakawo mata tasha, tace" nagode bawan Allah, "

Yace" Sannu, zaki iya tafiya ne? "

Kallansa tayi wai zata iya tafiya, kamar idan bazata iya dinba daukar ta zaiyi 🤣🤣mutumin da tataho zata fadi ma yaamatsa tafadi awajan 🤣

Tace" Zan iya tafiya, nagode sosai "

Yace" Babu damuwa "

Tashi tayi zata tafi taga de idan tatafin nan shikkenan fa ba lalle tasake ganinsa ba Dan haka tace" Amma bawan Allah yaya sunan ka pls? "

Yace" Sunana Sultan Muhammad lawan "

Murmushi tayi tace" suna Mai dadi, ni sunana Sahla, daga gombe nake, amma ina aiki anan kamfanin, sannan ina zaune agidan yayanah dayake aiki shima anan, nice yar gidan sarkin gombe ta qarshe "

Cikin mamaki yace" kice gimbiya ce "

Taji dadin yanda ya kula ta, tace" hakane, amma mekazoyi naan? "

Yace" akwai wani mk shine yaturoni ayimin Interview "

Fara'ah tayi tace" laaa yaya Muhammad kenan, nasan shi ai, abokin yaya nane "

Yace" Allah sarki "

Tace" Dan Allah kasamin number ka, saimu dinga gaisawa wani lokacin "

Mamaki yakama Sultan daga haduwa sai karbar number 🤔, amma saboda karya hanata taji Babu dadi kawai saiya bata, anan tayi masa godia tareda tafiya



*** ***** ***



Abinci suka gamaci, ya kalleta yace"Baby nah, nagaji Muje mu kwanta "

Kallan idonsa tayi, lokaci daya tahango tsantsar fitina aciki
Tace" Amma inajin dadin kallon nan "

Yace" Baby, Baby rigima, Pls tashi mutafi kin riga da kinsan abinda nake so "
Kafin tayi magana wayarsa tayi qara, sunan yarimah Nas ne yabaiyana, yadauka daga can bangaren yarimah yace" MK pls turomin number qawar Babynka "

Yace" Ok Nasrin kenan?"

Yarimah yace" eh "

Kashe wayar yayi, yazari wayar Nawal yadauki number sannan yatura masa
Kallansa tayi tace" number Nas zaka bashi?? "

Yace" emana, may be zasu gaisa ne "

Tace" amma fa kasan yaya Sultan yaana sonta, meyasa kakeson hadasu ne? "

" Baby yarimah yanason yarinyar nan, sannan yayanki yana sonta, da yarimah da Sultan duk abu dayane, dukanmu Kamar yan'uwa ne, kibarshi ya kirata shima Sultan din ya kirata saita Zabi Wanda takeso, "

" nide nafiso ta auri yayana, kodan zumuncinmu, amma naga take takenka sokake kawai kahada ta da yarimah"
Ta qarasa maganar

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment