Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sultan Allah yayi maka albarka, Allah yaqara horewa

Yace" amin Abba "yayi qasa da muryarsa yanda babu Wanda yakejin meyake fada sai ita, yace" umma kiyi hakuri, insha Allah zamusan yanda za'ayi, Baby zataji sauqi insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji "

Umma batace komai ba, kawai de ta daga masa kai alamar to

Yana fita yakira Salisu awaya yasanar dashi cewa su hadu agida, ba'a dade bakuwa saigasu akan _keke napep_ sun qaraso
Bayan sun gaisa da Malam yace" ya ake ciki? Kunsami yaron kuwa?

Salisu yace "inaaaa wallahi har yanzu de shiru,"

Yace "nifa yaya akwai abinda nake tunani amma _first_ mufara zuwa naga Babyn tukunna

Malam yace" to shknn Sultan Muje, dama yau bamu jeba, Tun safe Muketa abu daya "

Gaba dayansu suka dunguma sukai asbitin, suna zuwa suka tarar dasu nura, saif, da Najma azaune kowa yayi shiru, Salisu yace" A a yakukai shiru, ai zakusa tadinga tunani"

Saif yace "yaya idan munyi magana ma kyalemu takeyi tana kuka, Tun yaya Najma na bata hakuri harta dawo tayi shiru

Idananun Sultan sukai jajir, Ahankali ya furta Baby nah"

Aitanajin muryarsa tatashi zaune, tace "yaya Sultan,kaine kazo? ina kake?yaya yanzu fa shikkenan bazan iya ganinkaba ko?
Qwalla tacika idon Sultan, qiris yake jira yayi kuka, Ahankali yataka yaje har Inda take zaune agadon, tanajinsa kusa da ita tarungume shi tasaki kuka
Bubbuga bayanta yafara yi Ahankali yace" kiyi shiru kinji, insha Allah zaki warke, zaki warke kidinga ganin kowa, kiga umma da Abba da mama
Kinji ko Baby na?

Daga masa kai tayi, yace "to _smiling_ "

Murmushi tayi, yayinda hawaye yasake zubo mata
Yace "fadamin wanne Anwar ne yayi miki haka? Yaya kamanninsa suke?"

Tiryan Tiryan take zayyano masa kamanninsa, har abinda yahad'asu bata boye masa komaiba

Tana kai aya yace "shine wallahi, aikuwa zaici ubansa🙊🤣

Malam yace" Sultan kasan shine? "

" nasan shi Malam, Anwar ne yaron _Honorable_ Mai unguwa Saleh dogo "

Malam yace" Dan gidan Dan majalissa ne kenan "

Salisu yace" aiba Mai unguwa ba, ko megari ne, wallahi sai yasan yataba Baby,kawai kai tsaye mutafi _police_ _station_"

Malam yace "A a Salisu, Muje Zan yi magana da mahaifin yaron, ba zamuyi gaggawar kai maganar wajan yansanda ba, yakamata mufara yimusu bayani tukunna"

Sultan yace "hakan yakamata Malam, nasan gidan, kuzo mutafi, cikin ransa kuwa fata yake yaga Anwar,"

Basu bata lokaci ba wajan zuwa gidan,
Maigadi sukaiwa bayanin cewa sunzo ne wajan __Honorable_ yace wallahi baya qasar, yaje _Kuwait_ , amma zata iya yiyuwa yadawo yau

Sultan yace" Matar gidan fa, zamu iya ganin ta?

Maigadin yace "wallahi hajiya taje Abuja dazu, sai jibi zata dawo"

Malam yace "to zamu iya samun number wayarsa?"

Yace "mezai hana baba"
Yafada musu suka saka, sannan suka tafi, ahanya sukaita kira wayar akashe, saboda baya qasar
Har yamma suna gwadawa amma basu sameshi ba, dole Salisu da Sultan suka sake komawa suga ko yazo amma Maigadi yace musu baidawo ba, daga qarshe ma sai number Sultan suka bayar akan idan maigidan yazo saiya kirasu yasanar dasu

Gida suka wuce suka huta sannan suka koma asbiti gaba dayansu, dukansu azaune suke ad'akin datake, kowa yana janta da fira, suna kokarin ganin tasaki ranta tadena damuwa

Sai wajan karfe biyar Maigadi yasanar dasu zuwan _Honorable_, basu bata lokaci ba sukaje Gida suka dauki Malam, wannan karon harda Abba, suka tafi susu hudu
Suna zuwa kuwa Maigadi yamusu iso, har zuwa wani falo Dan madaidaici, sunkusa awa daya azaune kafin yafuto yagansu, Sultan kuwa sai sakin tsaki yake shi kadai, Abba yajuya ya kalleshi, shide aransa yana cewa baiso aka taho da Sultan ba🤣saboda yasan hali

Babban mutum ne, yaci manyan kaya harda Babbar riga, idan kaganshi saika dauka mutumin qwarai ne
Yana qarasowa garesu, yanemi waje ya zauna, Malam yatashi ya bashi hannu suka gaisa Abba ma haka
Yace "sannunku fa, kuyi hakuri nabarku kuna jirana, kunsan yanayin sai Ahankali, shi talaka dayaji kazo gari tofa babu zaman lafiya, andinga yin dandanzo kenan agidan ka"

Murmushi Malam yayi yace "gaskiya ne, muma akwai abinda yake tafe damu, shiyasa kaganmu, munzo munsake zuwa akace baka nan, to kuma yanzu Allah da ikonsa sai gashi mun sameka"

Yace "gaskiya ne, ina jinku meke tafe daku?"

Malam yace "akwai yaron wajanka waishi Anwar, sun samu sabani shida yarinyar wajan mu, hartakaita Ga marinsa, shikuma yaro daga baya maimakon yayi mata hukunci dede da irin abinda ta masa, saiya dauki shaltos ya fesa mata a idanunta, har hakan yakawowa yarinyar makanta, yanzu haka tana asbiti, bata gani kokadan, sannan likitan dayake kula da ita yace...

"Dan Allah dakata tsoho ✋🏻" _Honorable_ yakatse Malam cikin sauri.

Sannan yaci gaba da fadin "wai wanne yaro kuke magana akansa ne? Kuna nufin Dan wajena Anwar? To ni nasan waye d'ana, na kuma san irin tarbiyar dana bawa d'ana, nasan bazai aikata hakanba, kai kodama ace yayi mata hakan waye yaja? Kukukace ta mareshi, to Dan haka hukuncinta takarba dede da irin laifin data aikata, koma meyayi mata ai itace sila, wacce yarinya ce me tarbiya zata dauki hannu ta shararawa namiji mari, kai ni banma yarda cewa d'ana zaiyi hakaba, yaron dako zagi bai iyaba🤣😱
Nariga da nasan cewa maula ce kawai take tafe daku, "

Yasaka hannu acikin Babbar rigarsa yadauko kudi dami biyu yan dari biyar biyar ya watso musu
Sannan yatashi tsaye yace Dan Allah kufice kubarmin gidana, abinda kukazo nema gashi nan kunsamu

" amma kaikam badan arziqi bane, nika kalla ka watsowa kudi? "cewar Malam

Kafafunsa yadaga 🤷🏻‍♂yace" _And so?_ "


" aidama shi jahilin mutum basai anfada maka bama kana ganinsa zaka gane hakan, dame kake taqama? Siyasar? Da bazarmu fa kuke rawa, Inda bamu zabekuba babu Inda zakuje, "yanunashi da hannu👉🏻yaci gaba da cewa wallahi wallahi kaji na rantse kafadawa Anwar cewa yakiyayi haduwarsa da Sultan, shi yasanni nasanshi"

Cikin bacin rai _Honorable_ yace"nikake nunawa hannu saboda gidanku babu tarbiya? "

Sultan yana zaune yatashi tsaye, yasake nunashi da hannun👉🏻 yace" an nuna maka, kayi...


" Sultan"

Abba ya kirashi


Juyowa yayi ya kalli mahaifin nasa, baiso yakatse shiba , idanun Abba sunyi jajir, tunda aka fara maganar shida Salisu basuce komai ba, Abba Yakalli Sultan yace

"wuce mutafi Gida"









Share🙏🏻
Comments 🙏🏻
Sharhi Dan Allah 🙏🏻😢


Me kuke ganin zai faru zuwa nan gaba?

Anya kuwa _Honorable_ Saleh dogo baiyi kuskure ba?

Muhadu zuwa gobe insha Allah












Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE...🌺

(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to *Itz sadeek* wannan shafin ma nakane kai kadai, zaka iya hana fan's na *Khaleesat haidar* karantawa🤣


7&8

Saboda tsabar baqin ciki suna tafiya ahanya amma babu me cewa komai, kowa takaici ya isheshi, Malam kuwa kukan zuci kawai yakeyi, yau shine aka watsowa kudi, suda ake zuwa wajansu ace su taimaka da addu'ah idan lokacin zabe yazo, ko kuma adauki kudi a turasu zuwa saudia domin suyi addu'ah akan Allah yasa suci zabe, yauga irin mutanan nan waninsu ya watso masa kudi

Abba kuwa kokadan baiji haushin abinda Sultan yayi ba, saima kunyar mahaifinsa dayakeji akan rashin kunyar da akayi masa da girmansa da mutuncinsa, shikkenan de yanzu rayuwa tazama sai inkana da kudi ne kakeda daraja

Tsaki Salisu yaja "Malam wannan shine abinda nake fadamuku Tun farko, da munje _police_ _station_ Tun farko da haka bata faruba"

Abba yace "ai yanzu ma bamu makaraba Salisu, nikaina banji dadin abinda yayi manaba, aqalla yakamata ace ya sauraremu, ko kuma yakira shi yaron yaji ta bakinsa, amma babu komai, da Allah muka dogara ai"

Shikuwa Sultan baice "A" ba acikin maganganunsu, haushi kawai yakeji akan dakatarwar da Abba yayi masa

Basu tsaya ko'inaba sai _police_ _station_ mafi kusa dasu, suna zuwa Abba da kansa yayi musu bayani, bayan sungama yin _report_ din Abba yace yanaso atura case din nasu zuwa _court_ cikin sauri

Sultan ya kalli Abba, cikin ransa yace lalle ran Abba yabaci, tunda har yayi maganar _court_ .
Dan sandan ya kalleshi yace "Alhaji, naji Kamar sunan Wanda kafada mana kace mai unguwa"


Abba yace "eh _honorable_ Mai unguwa saleh dogo nake nufi"

"ayanda muka shigar kace yaronsa ne ya yiwa yarinyar ka laifi, shine kakeso kotu tabima haqqinka, shin Dan Allah baba Zan iya sanin takamaimai abinda yake faruwa?"

Abba yadubeshi yakwashe komai yafada masa
Dan sandan ya girgiza kansa sannan yadubi Abba "Alhaji azahirance wannan _civil case_ ne, _case_ ne tsakanin kaida shi, tunda _issue_ ne akan 'ya'yanku, kanada damar dazaka kaishi kowace irin kotu, daga nan har kotun qoli, to amma abinji shine, zai dauki lauya kaima ka dauka, shifa Babban mutum ne, Dan majalissa, ayanda ka fadamin yanzu kace asbiti suna buqatar million daya da dubu dari da sittin, toshifa mutumin nan yanada linkin wannan kudin, cire wannan kudin acikin asusun bankinsa ba komai bane, kukuwafa baba? Yanzu haka nasan cewa fafutukar yanda za'ai kusamu wannan kudin kukeyi, yayinda yadauki lauya kuka dauki lauya zai sakar musu kudi ne qarshe shari'ar tatafi awofi, kai inma ba'a juya maganar takoma kan 'yarku ba, ace itace take zuwa har Gida nemansa shikuma ya aikata mata haka, waya daya zasuyi wannan _case_ din yatashi daga _civil case_ yakoma _criminal, case_ din yakoma tsakaninka kaida gwamnati, yan siyasa abin tsoro ne a yanzu Alhaji, yayinda suke nema awajan ka zasu isheka da dadin bakine, amma idan suka samu to zance fa yariga daya wuce, akan maganar kotun nan suna kwance agida zasusa aje har asbiti a lalatawa yarka rayuwa, inma bata mutu ba, shikkenan daga nan _case_ yaqare, ni aganina kuyi hakuri Alhaji, _honorable_ Mai unguwa saleh dogo, baqaramin azzalumi bane, kubarshi da Allah kawai, saboda in kunje kotu ma, kotun tasuce, amma idan baku yardaba, shikkenan, nima kaina me shige muku gabane akan tura _case_ din kotu "

Malam yayi ajiyar zuciya,yace" cuta kam angama cutarmu, haqiqa honorable ya zaluncemu, amma babu komai, munjanye wannan maganar, Allah yanaji, kuma yana gani "

Shima Dan sandan yace" toshknn baba, Allah yashiga tsakanin na gari da mugu "
Suka amsa masa da amin, daga nan suka wuce Gida batare dasun waiwayi asbitin ba

*** *** ***
*Washe gari*

Najma kiramin Besty na a wayarki, Tun shekaran jiya rabona da ita, banji muryar taba

Najma tace "to ai kema Ga wayar taki nan, jiya su nura sun kawo miki ita, nakunnata ma naga sunmiki charge saina kashe ta"

"to kunnamin kikiramin ita"

Najma na kunna wayar ta kalli yar'uwar tata "Baby akwai _pattern_ fa, yaza'ayi?"

Hannunta ta meqo "bani nazana kozan iya, aibashida wahala"
Najma tabata wayar, tazana baiyi ba, tasake zanawa _still_ baiyiba, tasake yi akaro na uku shima Najma tace baiyiba, daga qarshe de meqa mata wayar tayi, tace zanamin 'N', harafin sunana ne akai

Najma na zanawa yayi, ta shiga wayar takira mata qawarta Nasrin, hannunta takama tasaka mata wayar tace to gashinan tashiga

Nasrin nadauka tace "Beauty nayi fishi, Tun rannan nake kiranki wayarki akashe, bayan kuma nafada miki Zan kiraki, kinsanfa inbanji muryarki ba, babu zaman lafiya 😉ta qarasa zancen nata cikin sigar zolaya"

Wani qulltun baqin ciki ne yatokare mata maqoshi, idanunta suka cika da qwallah tace "Allah sarki Nas kiyi hakuri, kekam kinada damar ma dazaki Ganni" ta qarasa maganar cikin rawar murya

Nasrin tace "kekike nufi Nawal? Zaiyi wahala takirata da Nawal, saide in maganar dazata mata Mai muhinmanci ce, kawai Beauty take cemata Tun lokacin dasuka fara haduwa
Taci gaba da fadin, meyasa naji muryarki Kamar tana rawa? Kokun tashi daga kano ne?"

"idan tashi ne aida dadi Nas, bana gani Nas, idanuna sun sami matsala bazan sake ganinku ba, tana fadar haka ta rushe da kuka😭"

Najma ta fizge wayar takama yimata fada, sannan tasa wayar akunne tace "Nasrin, Baby batada lafiya, yanzu hakama muna asbiti, wallahi wanine ya saka mata shaltos a idanunta, amma ana nan ana neman yanda za'ayi suyi mata aiki"

Lokaci daya Nasrin tafara hawaye, shaltos Najma, yanzu shikkenan Nawal bata gani?wannan wanne irin rashin imani ne?

Zuciyar Najma tafara karyewa, muryarta tafara rawa alamar zatai kuka tace "to ya zamuyi" daga haka takashe wayar, sai kuka, ita kuka Nawal dinma kuka, tana kukan tafara yimata bala'i, wai ke Baby ba zakiyi shiru ba? Kinasane ance babu ruwa a idonki amma shine Tun dazu sai kuka kike, dame zamu ji ne, su Abba sunacan hankali atashe suna neman kudi, memakon ki kwantar da hankalin ki ta yanda suma zasuji dadi shine kike kuka, sannan Karki Manta har yanzu Abba baice dake komai ba, akan wannan abinda yafaru, kuma nasani kema kinsani dole sai yamiki fada sosai akan wannan marin dakika yi, saboda haka kuka banaki bane, Addu'ah kawai zamuyi "

Cikin kuka tace" Najma kemafa kukan kike"

"to Baby Dan ina kuka shikkenan kema saiki kama kuka? _please_ kiyi shiru, takama qanwar tata tarungume ta, kowa yana sharar hawaye


** *** **

Yana zaune atsakar gida yazubawa dan'uwansa dake kwance ido yana kallansa, abin duniya duk yataru yayi masa yawa, ace wai kasha wahala kayi karatun amma samun aiki ya gagara, har tausayin kansa yake da iyayensa idan yayi duba da irin Rayuwar da sukeyi
Wayarsa ce tayi qara, yadauko ta daga aljihun gaban rigarsa, _number_ dake kiransa ya zubawa ido yana kallo wannan ba _number Nigerian_ bace, _number_ wata qasar ne, dauka yayi da sallama abakinsa

Daga daya bangaren akace "Yas yakake"

Yanajin ance Yas yaharbo jirgin mamallakin muryar
Cikin girmamawa Kamar ba sa'ansa ba yace "MK ai ban ganekaba wallahi, naga ba _number Nigerian_ ba, kuma nide nasan cewa banda kowa awata qasar"

Cikin miskilancinsa Kamar anyi masa dole yace "Kamanta ni kenan"

"Haba mk baka Manta daniba, tayaya zanyi kuskuren mantawa dakai? Yaya aiki? Ya Abuja? Dafatan dai komai lafiya yana kuma tafiya Kamar yanda yakamata"

"yasir bazaka sauyaba, na tambayeka amsa kawai zaka bani, Eh namanta ka, kokuma a a banmantaka ba"😳🙊

Murmushi yasir yayi, Wato har yanzu abokinsa yana nan da d'abi'arsa ta rashin son surutu
Afili yace "to ban mantakaba mk"

Ajiyar zuciya yayi "naga saqonka ta _Email Already_ angama komai, yanzu hakama akwai taron danake san turaka zuwa _Algeria_ ka wakilceni"

Yace " _Algeria_ de da nakeji ana fad'a?"🤣

Shima yace " _Yes_ "

"to mk ba zuwanne matsala ba, akwai qanina dabayajin dadi, yakai _one_ _month_ yana kwance wallahi, kullum ana fama a asbiti amma abin saide godiyar Allah"

"subhanallah, haba Yas meyasa baka sanar daniba?"

"haba abokina, tayaya daga haduwar mu zanyita fadama matsala"

"meyake damunsa?"

Yas yace "jijiyar qafarsace tasamu matsala, baya iya takawa"

"wanne asbiti kuke zuwa?"

"asbitin Malam Aminu, yanzu hakama gobe zamu koma ganin likita Kamar yanda muka saba zuwa"

"bansan Asbitin ba, _but_ zaka Ganni gobe insha Allah,"

"amma mk baka qasar fa, Dan Allah kayi zamanka"

Anasa bangaren shima kawai girgiza kansa yayi Kamar yasir din yana gabansa tareda kashe wayar


Mama dake gefe ta kalli yasir tace "wayene kuma mk kuda bakwa rabo da lalata suna? 🤣

Yace" mama wannan shine Muhammad Kabeer, abokinane, tare mukai karatu dashi a _America_ , saudaya yataba zuwa kano shida babansa, shima dole baban nasa yayi masa sun kai ziyara gidan marayu, shine yazo muka gaisa dashi, tosai rannan yazo gaisuwa shine yaqaraso muka gaisa harma yace natura masa takarduna, tofa shine yanzu wai zaizo yaga jikin Mu'azzam nace masa ya zauna basai yazoba tunda baisan asbitin ba, sannan kuma bamaya kasar

Mama tace "wai wanne asbitin ne baisaniba? Asbitin Malam aminun? 🤔

Yace" wallahi mama baisaniba, sau biyufa yataba zuwa kano, zuwansa da babansa, dakuma zuwan dayayi rannan, saikuma wannan da zaiyi na uku, "

" Allah sarki, a a kyaleshi yazo, aiba'a hana mutum aikin lada, Allah yabarku tare kuma yabar zumunci "

Yace" amin mama "



*** ***** ***


"muhammadu"


"na'am Malam"

"yaya kukai da mutumin da yace zaisai filin naka? Abba yace" Malam ai mungama magana dasu sun riga da sun sayi guda daya dubu dari uku, Ga kuma Sultan yakawo dubu dari da ashirin shima Salisu dazu yakawomin dubu talatin kaga yazama dari hudu da hamsin kenan,"

Malam yace" toga wannan kahada dasu "

Abba yace" baba yaya zaka takura kanka har haka, kaima akwai dawainiyar Gida fa "

" kada kadamu muhammadu, idan banyimaba wazan yiwa? Karbi Dan Allah dubu dari biyu ne babu yawa, kahada dana wajan ka yazama dubu dari shida da hamsin, kaje kakaiwa likitan gobe da safe, kasake roqar alfarma akan suyi mata aikin, idan Allah yaqara hore mana kodaga bayane sai acika musu sauran "

Lokaci daya Abba yafara kuka, yarungume baban nasa yanayi masa godia, Malam yace" babu damuwa d'ana, Allah yakiyaye gaba, kaje gida kahuta haka nan "

Abba yana zuwa yafadawa ummah Halin da ake ciki, sosai ta nuna farin cikin ta, sai yanzu hankalin ta yafara kwanciya akan rashin lafiyar autar tata.


Washe gari Tun karfe takwas Abba yafita yabar Gida zuwa asbiti da kudin a hannunsa, saida yashiga dakin da Nawal take yaga jikinta sannan yatafi wajan _doctor_ , yana zuwa _office_ din nasa yatarar duk mutane sun Dan fara taruwa ana jiran isowarsa, yana tambaya akace likitan bai qaraso ba, dole sai dakin dasu nawa suke yakoma ya zauna yana jiran isowar doctor din

Najma tace "Abba inasu mama da ummah,"

"suna nan lafiya Najma, aide baba matsalar komai"

"babu komai Abba, kawai de matsalar Baby batasan cin abinci, Ga kuka datake faman yi"

kallan Nawal yayi datake kwance tana bacci, fuskarta tayi fayau, tasake yin fari yace"kuci gaba da hakuri, yanzu ma nazone nabasu wani kudin, insha Allah zuwa wani satin zanyi kokari aciko sauran, akwai wani gida dana gani Dan qarami nahaya dubu dari dari da hamsin ne shekara, shi nake tunanin kamawa mukoma can, sai a saida Wanda muke ciki acika abasu

Cikin rashin nuna damuwa tace "to Abba, Allah yasa adace"

*** ***** ***

Agogon hannunsa yakalla qirar gucci mai launin baqi, sosai launin Agogon yayi masa bala'in kyau kasancewar sa fari,Ga kuma gashi Mai laushi daya kwanta ahannun nasa Tun daga wajan tsintsiyar hannunsa
Tsaki yasaki bayan yagama ganin time, sun bata kusan minti talatin kenan basu qarasaba

Wani tsakin yasake saki, shi kansa baisan dalilin dayasa ya takurawa kansa zuwa garin ba, bayan Atsarin sa babu wannan tafiye tafiyen inde ba akan harkar aikinsa bane, saide kuma wani bangare na zuciyarsa fata yake Allah yaqara hadashi da ita 😱

Jingina yayi da kujera ya lumshe Idanunsa, gashin idonsa dogaye sai sukai masifar yin kyau daya hadesu waje daya, Ahankali ya bude fatar bakinsa yace "Baby, Baby Cutie " Wanda bakowa ne zaiji hakanba saishi kadai daya furta abinsa iya fatar baki "

Suna zuwa asbitin suka danna hancin motocin su ciki, wannan karon motocin guda biyar ne, guda biyu agaba, biyu abaya saikuma Wadda yake ciki a tsakiya, Dasauri excort dinsa suka futo gaba dayansu, wani daga cikin su yabude masa kofar dazai futo ya rissina yace "yallabai mun qaraso"

Yana fadar haka yaja gefe guda, Ahankali yabude Idanunsa yazuro kafarsa guda daya waje tareda daukar wayarsa yakira layin Yasir, bugu daya yasir ya dauka, yace "Yas ina harabar hospital din"

Cikin girmamawa yace "gani nan zuwa abokina"

Dasauri yafuto harabar hospital din yana kalle kalle, sai can ya hango motocinsa yanufi wajan, yana tunkarar wajan yana kuma kallan yanda daidai kun mutanan dasuke wucewa suna kallan motocin suma, amma wasu mutanan kawai suna kallan gurds din dasuke zagaya wa a wajan ne, kowa fuska babu Rahma

Yana qarasawa ya bashi hannu suka gaisa, yace "Yas garinku yacika go slow 🤣"

Murmushi kawai yasir yayi baice komaiba

Yasake cewa "yamai jikin?

"jiki da sauqi mk, mu qarasa ka dubashi mana"

Ahankali yafuto daga motar yana kallan yanayin asbitin

Yasir ya kalleshi yasake kallansa, badai har yanzu mk yana nan da wannan dabi'ar tasaba, zaizo waje irin wannan amma ko ajikinsa yayi irin wannan shigar, ba shigar qananun kaya ne damuwaba, amma yaya zaiyi yasaka wando Crazy😳🙆🏻‍♂, bayan jama'ah dayawa zasu ganeshi, kuma zasusan waye mahaifinsa

Haka de yayi shiru, yasan cewa akwai lokacin da zaiyiwa abokin nasa magana, lokacin dazasu yi zama na musanman


Duk Inda suka wuce kowa saiya kallesu, ganin irin jama'ar dasuke take musu baya da sunan tsaro🤣, shikuma yasir kunya yakeji aga abokinsa da wannan wandon, 🤣🤣shiba da saka wando ba shida jin kunya 😃
Amma kuma shi gogan ko akwalar rigarsa

Kallan yasir yayi "Amma Yas yakamata mufara zuwa muga director tukunna"

Yace "Ok to Muje mana, dayake yasir din yasan kan asbitin sosai, shine yayi musu jagora har zuwa office din director din, anan yasir yaga duniya, domin kuwa shi kansa director din yana ganin mk yatashi ya bashi hannu suka gaisa, saboda kana ganinsa zakaga Kamar babansa atare dashi, Dasauri yabude fridge zai gabatar musu da lemuka amma suka dakatar dashi
Shida kansa ne yayi masa bayanin komai, just kawai yazo garin ne shine yakawo musu ziyara, godia sosai director yayi musu, daga nan suka tashi suka fara zagaya wa cikin asbitin

Duk wani mahaluqi dayake cikin asbitin yasan cewa yau mamallaka asbitin sunada manyan baqi
Haka suka dinga ganin ma rasa lafiya, haqiqa duk Wanda yazo asbiti yaga marasa lafiya dole imaninsa yaqaru, hakan ta kasance agareshi shima, wasu daga cikin ma'aikatan asbitin suna zuwa sukaga wannan ikon Allah, sai suma suka shiga akaci gaba da ganin marasa lafiya dasu kasancewar safiya ce, ciki kuwa harda doctor din da file din Nawal yake hannunsa

Duk gadon dasukazo saiya basu kudi, haka yadinga rabon kudi, wasu daga cikin majinyata har kuka suke suna kwararo masa addu'ah, banda Wadanda yadauki nauyin biyan kudin maganin su

Suna zuwa inda mu'azzam qanin yasir yake akasa likitan dayake kula dashi yasake duba qafar tasa, ya kuma basu tabbacin zai warke nan bada jimawa ba

Mk ya kalleshi, "to doctor why not aturashi germany ayi masa aiki Kawai, ni ina ganin aikin zaifi tasiri akan magungunan da akesha wata da watanni"

Doc. yace "toba damuwa, inde kun shirya, ai saisuje din"

Yace "toshknn babu damuwa," ya kalli daya daga cikin gurd dinsa yace "ka karbi account number na wannan likitan,"

Yace "angama sir "

Yakalli yasir "ina fatan babu wata damuwa ko?"

Hamdala yasir yadinga yi cikin ransa, yace "babu damuwa abokina, nagode sosai da sosai"

Daga haka sukaci gaba da ganin marasa lafiya har su kazo ward dinda Nawal take, har lokacin tana barci, yayinda Najma ta shiga toilet, sai Abba shi kadai yanata zagaya dakin abin duniya duk yayi masa yawa😞yana jiran zuwan likita


Yana dago kansa yaga likitan nasu dayake jira tareda baqi suna tunkaro wajansu dasauri yafuto daga dakin ya tsaya abakin kofar dakin, suna qaraso wa yayi sauri yatare likitan yace "Alhamdulillah likita dama kai nake ta jira Tun dazu, yameqa masa ledar hannunsa, gashi likita, kayi hakuri ba'a samu kudin dukaba, amma zanciko sauran insha Allah, yasake miqa masa ledar yace gashi"

Haba bawan Allah, baka ganshi tareda baqi bane? Daya daga cikin likitocin yayi wa Abba magana


Tausayinsa ne yakama mk, Dan haka yadubi doctor din daya yiwa Abba magana yace "Barshi yayi magana mana, ya kalli Abba yace" Baba mekefaruwa dakai ne?

Abba yace "babu komai dana, baabu komai karka damu"

Likitan dake kula da Nawal najin abinda Abba yace cikin ransa yace wannan mutumin shikuma wanne iri ne? 🤔
(tambayeshi de🤣🤣)

Dasauri ya kalli mk yace "ranka yadade 'yarsa ce batada lafiya, anfesa mata shaltos ne a'idonta, shine yakawo wani daga cikin kudin aikin da za'ayi mata"

Kansa yadafe da hannunsa 🤦🏻‍♂yace"Shaltos? "

Doc. Yace" wallahi"

"to nawane kudin aikin?"

Kai tsaye doctor yace,"milion daya da dubu dari da sittin ne"


Yace "to banda kudin jirgi kana ganin Kamar nawa zaku kashe kaida ita da mahaifinta idan zaku kaita Abroad ,?

Likitan yayi tunani yace" miliyan biyar zata isa"

Yace "Ok, ya nuna daya daga cikin gurd dinsa yace ka bawa wannan account number din ka, za'a turo muku miliyan goma,😳😱kuje qasar Albania sunada likitoci masu kyau na ido Acan"


Gaba daya mutanan wajan shock ya kamasu 🥺

Yakaalli Abba yace "Baba, kashirya kakai yarka asbiti, Allah ya bata lafiya, yakiyaye gaba, yadauko wani qaramin kati daga aljihun jeans dinsa crazy🤣🤣ya bashi yaci gaba da fadin idan kunyi passport kada kusai ticket , dazaran kunje Airport kawai kubasu wannan katin kuce inji MK"

Hawaye ne masu dumi suka zubo daga idanun Abba, yaron gade shigarsa nan bata arziqi ba🤔🤣, amma Allah ya bashi zuciya Mai kyau

Har qasa Abba ya tsugunna yace "Allah yasaka da alkhaairi yaro, Allah yakiyaye gaba da bayanka, ubangiji Allah yarabaka da mahassada, mungode, mungode yaro... Yakarashe maganar cikin kuka... 😭😭


Adede lokacin tafarka daga baccin datake, takasa kunne tanajin Kamar shashshekar kukan mahaifinta, saide kuma batada halin ganinsa😭😖, Dan haka tayi shiru tana saurarennsu


Kunya ce takama mk, ganin baabban mutum aqasa yana masa godia, Ahankali yasa hannu dagoshi yace "kada kadamu"

Daga haka suka wuce zuwa dakin gaba shida sauran mutanan







MK mungode kaji😱😱😭




Waye mk d'innan ne daya fara cuso kai yana

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment