Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nema sai yazama family 😉🤔







Muhadu zuwa gobe insha Allah




Sharhi, sharhi, sharhi Dan Allah 🙏🏻






Share please










Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE...🌺

(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek



9&10


Cikin ranta tafurta " murya mai dadi"

Najma ta futo daga toilet tana goge Ruwan fuskar ta
Dasauri tace "Najma waye yayi wannan maganar?"

Cikin mamaki Najma tace "magana kuma? A'ina? Wani kikaji yayi magana ne?

Gashinan naji wani yace" babu damuwa " Dan Allah Najma jeki ganomin waye, inasan naganshi Najma" (😳)

"Baby kanki daya kuwa? Nida nake toilet ina zanga wani Wanda yayi magana?"

" please Najma, wallahi inasan nasake jin muryarsa" (😱🤔)

Kallan kincika damuwa tayiwa Baby 😒kawai tafice daga dakin, tana futowa tayi kicibis da Abbansu
Tace "subhanallah Abba meyafaru kake kuka? Kaida waye Abba?

Ledar hannunsa Mai daukeda kudi ya nuna mata" kudi... Kudin aikin Nawal wancen yaron yabiya, yanzu yace yadauki nauyin tafiyarmu qasar waje aje ayi mata aiki Acan "

Mamaki da tsananin murna ta baiyana a fuskar Najma, domin tasake tabbatar da maganar Baby tasake cewa" Abba ko shine yayi magana yanzu Baby tajiku?

Daga kansa yayi alamar eh, sannan yace"shine Najma, gasucan sun tafi shida shugaban asbitin"

Wajan da Abba ya nuna mata ta kallah, ta hangosu suna tafiya saide bayansu tagani, bataga fuskar kowa ba kasancewar Sunbasu baya, saide jama'ar datagani sunada yawa sun kai kusan mutum ashirin like wani gwamna, 🤔hakan ya tabbatar mata dacewa lalle ko waye wannan ba qaramin mutum bane

Juyowa sukai cikin dakin itada Abba
Tana zuwa ta fada jikin Nawal ta rungumeta cikin murna tace "Babyyyyyy"

Tace "Najma zaki karyani,"

Daria tayi tace "Baby anbiyamiki kudin aikin ki, yarinya kiyi murna kin kusa hawa jirgi" 🤣🤣

"me kike nufi Najma?"

Najma tace "eh da gaskiya nake, mutumin dakikaji muryarsa yana magana da Abba, shine yabiya kudin aikin ki gaba daya" ta kalli Abbansu daya zuba musu ido yana kallansu cikeda qauna tace "hakane ko Abba?"

Yace "hakane, yakarbi account number likitan dayake dubaki, zai turo masa kudin ta account dinsa, tare zamuje da shima ma, Ga wani kati dayabani ma yace ba sai mun sai ticket ba kawai idan munje airport din mubasu muce inji MK"
Yamiqawa Najma katin

Takarba tagani tace "Abba katinma kansa wallahi yayi kyau Dan qarami dashi"

Murmushi Abban nasu yayi baice komai ba, dadi yakeji aransa jiyake Kamar ansashi a aljanna ya maqale yaqi futowa🤣🤣🤣

Ta kama hannun Baby tasaka mata katin cikin tafin hannun ta tace"To Baby kema riqe katin da hannunki kiji, Ga kati nan daga MK"

" MK "
ta maimaita sunan cikin ranta yayinda take shafa katin da hannun ta babu damar gani😭
Me hakan yake nufi kenan? Mukhtar, muddassir, musa, mus'ab, muhsin, muhmood, muzaffar, mustapha, ko mubarak?

(niko nace duk ba daya🤔kin Manta da sunan babanki Baby )

Najma ce takatse mata tunanin ta hanyar qwace katin tabawa Abbansu "Abba Ga katinku wannan ba magana zatayi ba"

Abba yakarba yayi Murmushi, yana sake jin dadi cikin ransa, saide wani abu dayake masa yawo a qwaqwalwarsa shine yaro Kamar wannan meyasa iyayen sa zasu zuba masa ido su Barshi yana irin wannan shigar? 🤔
Kobashida da iyaye ne maraya ne? To inba iyaye ma ai kana da makusanta wadanda zasu iya fadama gaskiya

Kawarda tunanin yayi aransa yadauki waya yakira Malam, yana dagawa yace "muhammadu yaya kukai da likitan?"

Abba yace "Malam ai zance yawuce" 🤣

"Kamar ya kenan?"

"yanzu de kana Gida ne??

Malam yace" eh ina Gida "
" to ganinan zuwa "cewar Abba tareda kashe wayar

Yakalli Najma" bari naje naga Malam, anjima Zan dawo mu qarasa tattaunawa da likitan naku"

Tace "to Abba agaida su mama, kace musu kuma abincinmu"
Yace "to babu damuwa Najma" tareda ficewa daga dakin

Yana fita tace "Najma shine nace kidubo minshi kikaqi ko"

Kallanta tayi cikeda mamaki tace "Baby anya kuwa wannan rashin lafiyar bayan idanunki Data taba banda tunaninki? Nafita nagansu har sunyi nisa, tukunna ma kinsan da mutanan dayake tare? Sunfi su goma sha, haka zanje na ratsasu ingano miki shi?
Kidauka ma naganshi, tayaya kike tunanin zance yazo nan d'akin ta yanda zaki sake jin muryar tasa? Baby adauka ma yazo dakin, tayaya zaki ganshi?

Wani irin qullutun baqin cikine yatokare mata wuya, sai yau tayi baqin ciki da rashin idonta, cikin ranta tace "Allah ya'isa tsakanina da kai Anwar" 😭

Ganin idonta nason kawo ruwa yasa Najma takama hannunta tace "kiyi hakuri Baby, insha Allah zakiji sauqi, murna yakamata kiyi kinji? Ta shi Muje kiyi wanka"

Ahankali tasauko daga kan gadon, Najma tasaka mata takalmi aqafarta, ita kuma ta qarasa saka kafar tata ciki, sannan tajata zuwa toilet din


*** ***** ***

Abba yana zuwa wajan Malam yanemi tabarma ya zauna yabude ledar kudin hannunsa yadauki dubu dari biyu yace "Baba Ga kudin ka"

"mekake nufi muhammadu? Kosunqi karba ne?"

"ai Malam yau Allah ne ya aiko mana da wani bawan Allah, ashe a'irin wannan zamanin akwai mutane masu qarancin shekaru da halin qwarai irin nasa? Wallahi Malam wani baqo asbitin sukayi, nikuma naje Zan bawa likitan namu kudin shine wannan yaro yace yadauki nauyin komai nata, intaqaice maka bayani de Malam wallahi yaron nan yace afitar da Baby qasar waje ayi mata magani "

Malam yace" Allahu akhbar, Allahu akhbar, Allah Mai iko, Allah Mai yadda yaso, muhammadu kaga ikon Allah ko? Kaga amfanin hakuri da yafiya ko? "

Abba yace" nagani Malam, wallahi najima ina mamaki "

" ba abin mamaki bane muhammadu, ikon Allah yawuce nan, yakamata yau na zauna tareda almajirai ayiwa yaron nan saukar alqur'ani akan Allah yadafa masa, Allah kuma yaqara yimasa budi ta hanyar halak "

Abba yace "amin Malam, yanzu de Ga kudin naan, Allah yahutar dakai 🤣"

Malam yace "A a muhammadu ai wannan kudin ba duka Zan karba ba, ka dauki dubu dari aciki kahada dana wajan ka a budewa Salisu shago babba yadinga juya kudin, idan Allah yayiwa abin albarka sai kaga Gida anhuta watarana"

"toshknn Malam, bari nawuce can Gida suma nayi musu bayani, zuwa anjima Zan dawo dasu Sultan suma muhadu ayi sauqar tare damu"

"bazaka tsaya talatu ta kawoma abin kari ba?"

Murmushi yayi yace "a a Malam zanci agida, agaida mutanan gidan" 🤣

"to muhammadu zasuji"



*** ***** ***

Suna zaune a dakin kowa yayi shiru, sai Najma datake waya da antynsu maryam dake zamfara
Amma gaba daya hankalin ta bayakan wayar da Najma takeyi, tunanin ta yatafi wajan tunawa da daddadar muryar datayi magana da Abbanta, tarasa meyasa muryar takasa barin cikin ranta, to wai ita menene natama na dagewa akan saita ganshi? 🤔🤔

Muryar Najma ce ta katse ta, ta hanyar kama hannunta tasaka mata wayar tace "Ga anty maryam tana magana"

Ajiyar zuciya tasauke tace " Hello anty"

Itama anata bangaren tace "Baby nah ya jikin naki? Dafatan de bakya tunani ko?"

"bana tunani anty, jiki da sauqi, yaushe zaki zo?"

"zanzo Abba ya hanani zuwa, amma insha Allah zanzo, yanzu naji Najma tacemin anbiya kudin aikin ko?

" eh wallahi anty wani yabiya "

" to Allah yasaka masa da alkhaairi, bari nakira gidan, sai anjimanku "

Tace" to anty "

Sunayin sallama da anty maryam nura yayi sallama suka shigo tareda Nuhu

Najma ce ta amsa musu, ita kuwa tanajin harda muryar Nuhu acikin masu sallamar tayi shiru

Sannunku da zuwa nuhu, Ga waje ku zauna mana, inji Najma

Yayi Murmushi yace" to Najma yaya Mai jiki?

"jiki da sauqi Nuhu, gatanan"

"to Allah yasawaqe, Allah yarufa Asiri"

Tace "amin," sannan tamiqe suka fice daga dakin itada nura

Yana ganin fitarsu yace "ya sayyida, yamukaji da hakuri kuma?"

Tace "Alhamdulillah," ataqaice

Yace "wallahi banida labari saboda inata kiran wayar taki akashe, sai da nazo Gida shine nakejin wannan mummunan labari"

Tace "wallahi kuwa"

"to Allah yabaki lafiya, ya ajiye leda me yallow da baqa cikeda fruit yace toga wannan kyasha"

Haushine yakamata wai ga wannan kyasha, saikace wadda take gani🤣

Saita daure tace "to"

Daga nan sukai shiru gaba dayansu, sai shine yace "to ya labari"

"babu"

Yace "to shknn my heart Rabin raina, naga Kamar kin gaji, bari natafi"

"to sai anjima"

Kallanta yayi yasaki Murmushi, ganin fuskarta tayi futu-futu alamun batai murna da zuwansa ba

Yanada fita Nasrin tashi go dakin ita dasu Najma, itama suka gaisa dashi sannan yatafi tareda nura

Tana qaraso wa dakin tace "Beauty"

Lalume tafara itama tana nemanta
Tace "Nas ina kike?"

Kama hannayenta tayi tariqe "Beauty na, ya jikin naki?"
"jiki da sauqi Nas, kinga Anwar yahadani da masifa ko"

"gaskiya bai kyautaba wallahi, amma ai akwai Allah, waima menene yahadaki dashi ne? Dama kinsan shine?

Nan take taabata labarin komai, Nasrin tayi ajiyar zuciya tace" Gaskiya akwai marasa imani agarin nan, amma kiyi hakuri Allah zai saka miki "

Najma tace" A a mukam ai munga sakayya Nasrin,🤣🤣 dan dazu wani bawan Allah ma yazo yabiya mata kudin aikin daza'a yi mata duka wallahi"

Nasrin tace "Dan Allah"

Kafin Najma tayi magana Baby tace "wallahi Nas ba kiji muryar sa ba me dadi, inajin maganarsa bansan lokacin dana saurara ba danna cigaba da saurarensa"

Gaba dayansu suka juya suna Kallanta cikeda mamaki

Najma tace "ni Baby ba Nuhu ne yazo yanzu bane?"

"shine mana, to Dan Nuhu yazo sainaqi fadar abinda ya birgeni?"

"gaskiya ne, amma kinsan hakan bai kamataba, tunda mutumin nan yana sanki, kuma kowa agida yasan dashi, sannan kema yan'uwan sa duk sunsanki, bai kamata kidinga yimasa wulakanci ba"

Nasrin tace "wannan gaskiya ne, wulakanci bashi da da dadi, especial ma akaan mutumin daya nuna yana sanka, idan bakya sansa kai tsaye ki fada masa mana"

Cikin haushi tace "bazan fada masaba Nas, shi mahaukacin inane da bazai gane cewa ba'a sansa ba? Na nuna masa nanuna masa to menene kuma na dagewa bazai rabu daniba"

Nas tace "kai wasu mazanma de sai abarsu" 🤣🤣

Najma tace "wallahi kuwa, mukam ina ruwanmu, tafadi haka tana janyo ledar fruit din gabanta 🤣🤣
Dauko ayaba tayi tameqawa Baby tace " Baby Ga ayaba daga masoyi🤣"

" banaso Najma bazan ciba "

Tasake dauko apple tace" toga Tuffah"

Cikin bacin rai tace "nace miki bazanciba bazan ciba dole nene? Kaje ma andanna ma wani asirin aciki"

Gaba dayansu suka sa daria, ganin yanda tayi kicin-kicin da fuskarta, lalle Nawal batasan Nuhu 🤣


*** ***** ***

Abba yana zuwa Gida yatarasu su Salisu da sauran yan Gida yafada musu abinda yafaru kowa sai murna yake yana hamdala, mama mariya tace "gaskiya Alhaji naji dadi, yanzu kaga sai kasai mana Mota maikyau wadda za'a dinga nunamu ana cewa oh su mariya ana can ana hawa motar wane da wane" 🤣

"mariya anya zakiyi hankali kuwa?kudin da ko zuwa hannu na basuyi ba? Yanzu mariya koda kudin nan sunzo wajena wacce irin Mota Zan siya? Me Mota zata tsinana min? Jinake Ga yara nan agabanki har mutum uku, nura, saifu dakuma Najma, aisu yakamata ace kinyi tunani sun tafi makaranta, to kinga ni bazan sai wata Mota inbar 'ya'yana cikin jahilci ba"

"to Alhaji nawane sukai karatun babu aikinyi?Ga Salisu nan shekararsa nawa dagama karatu babu aikinyi, ko 'yar adaidaitar nan baisamu tajaba🤣🤣
Shikuma Sultan gashinan kullum a qarqashin wasu yake, shima babu na kansa, haba ni wallahi nagaji da kashe kudin karatun nan babu aikinyi "

" kinsan da hakan kika daga hankali lokacin da Nawal zata tafi makaranta kikace saide Najma taje?"

" Alhaji Dan Allah kayi hakuri kabar wannan maganar, tare Muke da yarafa "cewar umma

Abba yace" Allah ya kyauta,to nide naje wajan Malam mungama magana dashi, kudin dana saida filina guda daya, yaqaramin dubu dari akai, Dan haka za'a budewa Salisu shago yaci gaba da juya kudin, koda ace ba'a samu albashi ba, akwai abin dogaro daki, kai kuma Sultan Ga kudin ka, kakama hanya kakoma bakin aikinka, daan Allah karnaji karnaga kayi fada da kowa musanman Anwar, domin kuwa nasan halin ka "

Sultan yace" to Abba, amma cikin ransa bai qyale ba, bayajin akwai Wanda zai taba Baby yaqyaleshi, babu shi

sannan yaci gaba da cewa amma Abba wannan kudin kabar shi wallahi, ahada da shima a kudin shagon, Allah yaqara hore mana gaba dayanmu"

Dukkaninsu suka aamsa da amin

Saif yace "Abba kuma yaya Baby tare dawa zasu tafi qasar wajan?"

"Dani da ita dakuma likitan dayake kula da ita, Dan kudin ma ta hannunsa zaizo, dole anjima Zan koma naji yaya zai tsaara mana tafiyar"

Cikin farin ciki ummah tace "to Allah yasaka masa da alkhaairi, shima Allah ya bashi Wanda zasu taimaka masa Kamar yanda ya temakemu"

Abba yace amin, tareda miqewa, ya kalli su Sultan dasu nura yace "anjima kuje gidan Malam akwai karatu, nima Zan biyoku idan nadawo daga asbitin"

Suka amsa masa da to, shikuma yayi cikin d'akinsa

*** ***** ***

Saida aka kawosu har kofar gidan su sannan ya kalli abokin nasa "MK mungode sosai, Allah yasaka da alkhaairi ubangiji Allah yayi ma...

✋🏻Dakatar dashi yayi ta hanyar daga masa hannu," Yas babu godia tsakanina dakai "

" to shikkenan, nagode sosai, yanzu Abuja zaka wuce?"

" no , bazan shiga Abuja ba, saboda Ummi ma batasan nazo ba, ina ganin Zan wuce Dubai"

"toka shiga mana ku gaisa dasu mama"

Murmushi yayi kawai batare dayayi magana ba, Wanda hakan ya tabbatar wa da yasir cewa bazai shiga gidanba, Dan haka yace "toba damuwa Allah yakaika lafiya"
Ya yunqura zai fita daga motar yayi sauri yace "Yas"

Zuciyar yasir daya yajuyo yana kallansa yace "na'am?"

Cikin ransa yace To yanzu dana kirashin mezan cemasa? Kasan Baby? Kokuma ina zanga Baby? Yarinyar da sunan ta kawai yaji baisan taba, baisan kamarta ba, saide Beautiful lips dinta daya gani sau daya
Dan haka yashare kawai

yace "shikkenan babu komai ma sai munyi waya kawai"

Yasir yace " Ok , tareda fita daga motar, sukuma sukaja suka tafi


*** ***** ***

Washe gari kuwa kudi suka shigo ciki account din Doc.yanemi Abba suka fara shirye shiryen tafiya Abania , kuma alhmdlh komai sunyi shi cikin kwanciyar hankali, cikin kwana hudu jirginsu yatashi daga MALLAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT zuwa

TIRANA INTERNATIONAL AIRPORT dake ALBANIA ( nene tereza )

Abangarensu Yasir suma sun tafi Germany shida qaninsa, already shi din Dan boko ne daya samu budewar ido awata qasa, shiyasa suma basu sha wahala ba wajan tafiyar tasu tareda Mu'azzam da taimakon likitan dake duba qafar yaron



*** ***** ***

Abu Dhabi
Babban birnin Dubai


Babban d'aki ne mai mutuqar girma daya amsa sunansa daki, babu wasu takarce masu yawa a dakin face gadonsa da wardrob, sai kujeru masu Ruwan zuma dasuka qara qawata dakin

Sai Dan qaramin kafet ashimfide agaaban gadon Mai launin baqi da Ruwan zuma

Da wata uwar plazma dake manne abangon dakin, tanada girma sosai kadan yarage tacika bangon dakin, girman ta yayi yawa, saikuma dressing mirrow dake cike da kayan qamshi, akan bedside drower computer sace qirar Apple Mai launin baqi

Kwance yake yana bacci hankalinsa kwance, bargon daya rufa dashi shima baqi ne da Ruwan zuma irin me laushin nan Kamar jikin mage

Gaba daya ya tattare bargon zuwa gabansa ya rungumeshi🤣

Mafarki yake ga wannan de me mashin dinnan yataho da dugu zai sake kad'eta, cikin sauri kuma da karfi yace "BABY!!! "

Adede lokacin yafarka daaga mafarkin da yakeyi, yatashi zaune tareda yaye bargon daya rufa dashi yayi wurgi dashi gefe guda yana maida numfashi Kamar Wanda yayi tseren gudu

Jikinsa na kalla babu vest ajikinsa bare riga, qirjinsa gashi dayawa baqi ya kwanta, sai gajeren wando ajikinsa Mai launin baqi 🤗











Kai Nawal yakamata kisayaya wa mk haka 🤔🤔🤔koba hakaba fan's









Please sharhi sharhi sharhi Dan Allah 🙏🏻🙏🏻



Share please 🙏🏻

















Amnah El Yaqoub ✍🏻🌺NI DAKE...🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub


Dedicated to Itz sadeek


11&12


Baqin ciki ne da takaici suka kamashi, wai meyake damunsa ne?shikkenan daga ganin yarinya duk yabi yad'aga hankalin sa akanta? Yarasa meyasa zuciyarsa take azalzalarsa akanta, qwaqwalwar sa takasa goge sunanta,meyasa yadamu da lamarin yarinyar haaka? Yanaji aransa yanaso yasake ganinta koda sau daya ne, but meyasa hakan? Ba kasafai fararen mata suke birgeshiba because of acikinsu yake, kullum suyake gani, kuma su din yatashi yaana gani, koda ace soyaiya zaiyi bashi da ra'ayi akan farar mace gara yayi mix shi fari ita baqa 🤔

That's why yakesan abu baqi, hatta kayansa kuwa da Komai na cikin d'akinsa da toilet dole sai kaga baqi

Amma kuma ya daga ganin yarinya zai mamuqata acikin ransa harda wani mafarki, kuma yarinyar ma qanwar qanwar bayansa, kawai hakurinta ne yabirge shi

Afili yafurta "Tausayi ne kawai, ba abinda nake tunani bane, Tausayi ne kawai" (🤣🤣tofa)

Daga haka yatashi tsaye gajeran wandon nasa duk ya baiyanar da shacin komai 🙈
miqa yayi tareda kallan murdaddan hannunsa sannan yashige toilet


*** ***** ***


Kwanansu daya da zuwa qasar ta Albania aka gama duk wani shiri akan aikin idonta, sun riga sunbiya kudin komai washe gari za'a yi mata aiki

Washe gari kuwa tunda safe aka sauya mata kaya basufi minti ashirin ba aka shiga da ita d'akin da za'ayi mata aikin

Abba yayi shiru yana tunani, da yanzu fa a Nigeria za'ayi mata wannan aikin nanda wasu watannin, domin kuwa shide yasan kansa, yasan cewa bashi da hanyar dazai saimu wannan kudin saide Ahankali adinga ta rawa harya biya

Likitan daya rakosune ya bubbuga kafadar Abba "Alhaji kayi hakuri, ba wani aiki ne dazai dauki dogon lokaci ba, insha Allah lafiya zasu futo"

Abba "yace to likita Allah yasa, Allah yasa adace"

Yace "amin Alhaji"

Ko cikakkiyar awa biyu basuyiba suka futo,tana kwance akan gadon yayinda likitoci guda biyu suka turo gadon zuwa dakin da aka basu
Cikin sauri Abba yatashi yanufesu saide basu tsayaba saida suka danganata da d'akinsu

Daukarta sukai suka dorata akan gadon, suka gyara mata kwanciya, annad'e idonta da bandeji fari, kanta babu dankwali gashinta Mai tsantsi yazubo har bayanta

fita sukai daga dakin, likitan daya jagoranci aikin ne yashigo dakin fuskar sa daukeda Murmushi, ya d'aura mata ruwa sannan yadubi Abba da likitan "congratulation, aiki yayi kyau angama lafiya, yanzu anyi mata allurar bacci, zata dauki tsawon lokaci tana bacci kafin tafarka
Idan tatashi kada kubari ta dinga sunkuyar da kanta qasa, duk wani abu dazaisa ta sunkuya qasa ba'aso tayi, saboda yin hakan zai iya haifar da wata matsalar, insha Allah zuwa gobe za'a cire mata bandejin sai kuma mugani yaya ganin nata zai kasance, shin zata gani kokuma sabanin haka, amma mude anamu bangaren mungama aiki normal babu wani problem, saide muyi fatan rashin matsala bayan tafarka "

Murmushi ya wanzu afuskar Abba, har likitan yagama bayani kawai cewa yake insha Allah, insha Allah" 🤣

Likitan dasukazo dashi daga guda yabawa dayan likitan hannu suka sake gaisawa yayi masa godia da jinjina sannan shikuma yafice yabar su a dakin

Waje suka nema suka zauna bakin Abba yakasa rufuwa sai farin ciki yake

Yadauki wayarsa yakira Nigeria
Umma yakira a lokacin wayar tana hannunta, Dan tunda yace mata yau zasuyi mata aiki ta riqe wayar tana jiran kiransa yashigo, kiran nashigo wa kuwa tayi sauri tad'aga

Cikin farinciki Abba yace" Safiyya, kiyi farin ciki kiyiwa Allah godia, anyi aiki lafiya, gatanan a kwance tana bacci, likitan yace zuwa gobe zasu cire mata abin idonta, sai muyi addu'ah kuma Allah yasa anyi a sa'ah"

Tace "Alhamdulillah, Allah abin godia"

Salisu da Sultan dake gefenta sunajin furucinta suka fara Fara'ah
Sultan yace "wayyo umma Dan Allah sakata a handsfreee"

Shi kam Salisu qwace wayar yayi daga kunnanta yasaka musu ita a handsfree, nanfa sukaji komai, Kamar ba samari ba haka suka d'auki ihun murna, hakan ya janyo hankalin yan gidan duk sukayo falon ummah kowa yana tofa albarkacin bakinsa, yau kam mama mariya ma daka ganta zaka tabbatar tayi farin cikin jin wannan labarin 🤣

Anan fa Gida ya kaure da murna, kowa yana hamdala cikin ransa, Abangaren umma kuwa addu'ah take ta kwararowa wannan bawan Allah daya biyawa yarta mace qwaya daya kudin magani


*** ***** ***

Doc. Yadubi Abba "Alhaji zandan fita nasiyo mana wasu abubuwan dazamu buqata kafin allurar tasake ta insha Allah Zan Zan dawo"

Abba yace "to likita adawo lafiya"

Likitan nafita Abba yakama hannun 'yarsa yariqe yana Kallanta, fatansa daya Allah yasa adace akan aikinda akayi

Yana zaune shiru har likitan yadawo da kaya ahannun sa, rigar sanyi ce yasiyowa kowa da kuma fruit da sauran abubuwan dazasu buqata


*** ***** ***

"usy yakake yagari"

"lafiya Sultan , ya kwana biyu"

"alhmdlh wallahi, ina kaga Anwar ne? , inata nemansa banganshi ba, Allah yasa yana gari🤣"

Usy yace"aikuwa Anwar baya nan, idan baiyi sati d'aya da barin gariba to yakusa sati gaskiya, me yafaru? "

Sultan yace" wallahi nemansa nake ruwa ajallo usy 🤣, akwai maganar da zamuyi Mai muhinmanci "

" kai Sultan ka fadamin gaskiya mana, meyake faruwa kake neman Anwar? "

Saida Sultan yayi ajiyar zuciya sannan yace" wallahi Usman ina fad'ama qanwata ya lalatawa idonta, yarinyar fa har makancewa tayi, mu kaje gidansu muka sanar da ubansa Allah shine mutumin nan yayi mana korar kare🤣"

Usman yace" Bala'i, anya kuwa Anwar yasan cewa ita qanwar ka ce? "

" inma bai saniba idan yaganni yaganta ai dole zai gane, saboda sonake na tisa qeyar yarinyar, na sata agaba Muje tarama abinda yayi mata da hannunta, munje munkai qara wajan yan sanda, amma wani daga cikinsu yabamu shawara akan mujanye case din, saboda Mai unguwa sale zai iyayin komai akan hakan, kuma idan mukaje kotu za'a iyayin watsi da qarar, shine nakeso na kamashi itama ta lalata nashi idon kaga anyi 50 50 kenan 🤣yayinda ubansa yakaimu kotu kaaga anan dole a saurari qarar, tunda mu yanzu idan muka kaishi babu abinda za'a yi masa
Amma kaji usy wai ahaka Abba yake cewa narabu dashi "

" kata'i, shine abinda yafuto daga bakin usy🤣🤣sannan yace "Sultan wannan ai ba abin yafiya bane, idan ku kunyi shiru ai anbashi damar dazai sake yiwa yar wani haka"


Sultan yace "kaima de kafada"

"Amma Sultan baka kyauta minba dabaka kirani munje tare daku gidanba, narantse da Allah dakunje Dani inba saina wankawa Mai unguwa sale mari ba 😳🙊saide yasa adaureni,"

Sultan yace "abinda nasoyi kenan Abba ya katseni"

Usy yace "wallahi Anwar bayanan, yaje Uganda, amma inde yadawo Zanzo har Gida nafadama"

"Usman lagos zankoma, Abba yace natafi, sannan itama yarinyar yanzu suna Albania anayi mata aikin idon Acan, sai sundawo sannan zanzo naganta, ina fatan a lokacin Data dawo shima Anwar yadawo, zanzo naganta kaga a lokacin saina ritsa shege🤣"

"good hakan yayi, Allah yasa lokacin dazaka zodin shima yadawo"

"usy koda baidawo ba Zan jinkirta zuwan nawa har sai lokacin daya dawo, nide abinda nakeso dakai shine daka ganshi kamin waya"

"to shikkenan Sultan saika jini,"

Daga haka sukai sallama



*** ***** ***


Washe gari tunda asuba Abba dayai sallah a dakin nasu yafara karatun qur'ani Ahankali, karatun dayake ne yatashi Nawal daga baccin datake

Ahankali ta yunqura ta tashi, Dasauri Abba yaqaraso ya riqeta "Nawal kina buqatar wani abu ne?"

"Abba fitsari nakeji, kuma da yunwa ma🤣"

Yace"to bari akira likita", yana fita yadawo da wata mace, itace takamata har zuwa toilet tayi fitsari tareda wanke baki, suka futo "

Gadon tamaidata ta kwantar, itade mamaki yagama kasheta cikin sauri tace" Abba bata barni nayi alwala bafa "

Adede lokacin likitan dasukazo dashi yashigo dakin tareda bata amsa" ai saide kiyi hakuri har acire miki wannan abun na idonki sannan ki rama sallolin dake kanki, keda ba'aso ko abu ne kidauka aqasa saboda idonki "

Abba yayi Murmushi yace" to kinji "


Sannan suka gaisa, itama ta gaishe su tayi shiru, Abba yace" kidinga addu'ah fa, anjima zasuzo su cire miki wannan abun na idonki, idan anyi nasarar aikin idonki zai bude"

Murmushi tasaki tace "to Abba zanyi" cikin zuciyarta kuwa murna ce fal, idonta zai bude zataci gaba da ganin su ummanta
Wata zuciyar tace mata toshi kumafa?mutumin daya ceci Rayuwar ki daga fadawa makanta ta din-din-din? Murmushi tasake saki ita kadai, to kodan tasake jin muryar sa ai dole ma ta nemeshi, bare kuma yayi mata wannan kirkin ai dole ma ta nemeshi a duk Inda yake (tofa😳🤔)

Shide Abba yaga tana ta faman Murmushi, amma bai kawo komai aransa ba, yadanganta hakan da murna akan maganar dayayi mata

Sai wajan sha daya saura sannan likitoci suka shigo dakin nasu kusan su uku
Ba ita da akaiwa aikiba hatta su kansu likitocin idan kadubi fuskar su zaka tabbatar suna cikin shakku, kowa fatansa asamu nasara akan aikin nata

Gabanta kawai luguden faduwa yake, yanzu idan aka kunce mata tace bata gani shikkenan fa tariga tazama makauniyar karfi da yaji

Wanda zai cire mata ne cikin sigar rarrashi yace "ki kwantar da hankalin ki kinji?sannan yafara warware mata bandejin Ahankali

Mutanan

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment