Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya tafiya

Suna fita, yaja yasir da yarimah Nasir part dinsa nada, ya cewa Ummi abawa sabira abinci takai musu



*** ***** ***



Abba da Malam suna tsaye a kofar gida, suna ganin yanda ayyukan ginin suke gudana, Salisu yafuto daga gida zai wuce kasuwa, kawai sai ganin wata Babbar Mota sukai tatsaya agaban gidan, gaba daya su ukun mamaki yakamasu waye yazo kuma? Kokuma baqi sukai? Basu gama wannan tunanin ba, Hon yabude Mota yafuto, shima Anwar yafuto, fuska duk ta kumbura saboda duka

Gaban Hon yafadi, ganin mutanan daya ciwa mutunci kwanaki yau gashi yazo neman yafiya wajansu

Suma mamaki ne yaqara kamasu, Mai yakawo Mai unguwa saleh dogo gidansu?










Sharhi
Comments
Share

Dan Allah 🙏🏻











Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


43&44


Ummi ta kalli Nawal tace "Amma Nawal sainaga Kamar kinsakewa yaron dayawa, bai cancanci ace lokaci daya kinyafe masaba, mutumin daya nemi ya lalata miki idanu"

Murmushi tayi Mai kama yaqe tace "Ummi menene Rayuwar ma gaba dayan ta, yau idan mune gobe bamu bane"

Ummi tace"wannan hakane, amma sanyin halin ki yayi yawa Nawal, sukuma maza ba'a yi musu haka, idan yayi miki abu yau yaga kinyi shiru gobe ma yaga kinyi shiru to jibi abinda yafi haka zaiyi miki, duk da nina haifi Baffah Nawal bana baki shawarar kiyi masa wannan hakurin, hakuri idan yayi yawa akwai cutarwa aciki,irin haka anayiwa mutum abu yana shanyewa wataran bazai iya shanyewa ba saide yafadi daga nan kuma ace mutum yanada wani ciwon Kamar hawan jini "

Tace" hakane Ummi, insha Allah Zan gyara "

" A a Nawal nasan ba de nawa zakiyi ba, tashi kije kikai wa mijinki a abinci "

Tace" to"
Tareda dayin kitchen



*** ***** ***


Hon. Mai unguwa ya kalli d'ansa, shima Anwar din ya kalleshi nan take kowa yagane laifin daya aikata shi Hon.yana ganin su yagane cewa sune mutanan da sukaje wajansa yayi musu korar kare
Shikuwa Anwar tunanin irin cin mutuncin daya yiwa Nawal yayi, Inda wata yarinyar cefa bazata yarda ba saita rama
Kawai daga mari ya qullaceta aransa saiyi mata abubuwa yake Kamar wata namiji, akan namiji dan'uwansa yakamata ace yayi haka bawai akan mace ba
Yafesa mata shaltos, yabigeta da niyya, ya take mata waya, sannan yanzu haka kawai batare datayi masa magana ba ya tsokaneta da niyya, kuma ko uffan bata ce masaba, lalle idan bai nemi yafiyar iyayen ta da ita kanta ba haqiqa Allah bazai Barshi ba

Hon. Mai unguwa yace "ina tunanin wannan shine mai gidan, mu qarasa"

Suna Qarasawa Abba yabata fuska 😠
Salisu kuwa fuska yayi yakawar dakai gefe🤣

Liman ne kawai yayi Murmushi yace "barkanku dazuwa"

Cikin kuskurin kunya Hon. Yace "yawwa sannu baba🤣, nan ne gidan muhammadu lawan ko?"

Liman yace "eh nan ne," yanuna masa Abba tareda cewa "gashi ma a tsaye, Mai yake tafe daku??"

Cikin sauri Anwar yace "neman yafiya" 🤣

Abba bai saki Fuskarsa ba yace"kuje munyafe "

Malam yace" A a haba muhammadu, baqonka annabinka inji bahaushe, "ya kalli Salisu yace" shiga gida ka dauki musu abin zama "

Salisu baice komaiba yajuya yashiga gida sai gashi ya dawo da Babbar tabarma

Anan kofar gidan suka shimfida musu kowa Yazauna
Mai unguwa ya gaida Malam da kansa, sannan ya gaida Abba 🤣

Bayan sun gaisa ya kalli Anwar yace" basu hakuri "🤣


Cikin ladabi dakuma tsantsar nadama yace"dan Allah baba kuyi hakuri, nazo har gida inaso ku yafemin akan abinda na yiwa Nawal, haqiqa nasan cewa na cutar da ita, amma nabata hakuri kuma tace tayafemin, sannan kuma ina qara baku hakuri bisa abubuwan dasuka faru "

Sai a lokacin Abba yasaki ransa" Babu komai tunda itama da kayiwa laifi tace ta yafema ai shikkenan "

Mai unguwa ya kalli Malam yace" baba Dan Allah nima ina qara baku hakura bisa abinda na aikata muku lokacin dakukaje gidana, nafiso shi yaron daya aikata laifin yafara neman yafiyarku sannan ni, domin kusan cewa lalle yasan ya yi laifi kuma yazo yabaku hakuri, Dan Allah naroqeku nima ku yafemin, bansan cewa yarinyar da Anwar ya aikata wa wannan abun matar uban gidana bace, da ko hanyar databi ma Anwar bai isa yabiba🤣
Amma munje har can Abuja suma sun tabbatar mana komai yawuce, sannan daga can ko gida bamujeba muka iyo nan "

Malam yace" Babu komai ai, dama koya zuba mata shaltos ko bai zuba mata ba dole Allah ya rubuta zata makance na Dan wani lokaci, ta wata silar daban, Dan haka muma munyafe muku, Allah yashiryeshi yakiyaye gaba "

Mai unguwa yasake duqar da kansa Kamar ba honorable Mai cikakkiyar izza ba yaqara yimisu godia sannan suka tashi zasu tafi, yadubi Abba yace" insha Allahu saqona yana nan zuwa gareku, idan kunyi waya dasu mutanan Abujan ace ina gaishe su🤣🤣

Abba yace "A a bama buqatar komai, kuje kawai"

Suna tafiya Malam yace "wannan shi ake kira gaba da Gabanta, kagade yanda mukaje har gidansa ya wulakanta mu, Inda ya sauraremu a lokacin aida baizo yanzu yana qaramar murya ba"

Salisu yace"Malam kaji wai harda cewa idan anyi waya da mutanan Abuja agaishesu, soyake yacefa idan anyi waya da mk a gaishe shi, Dan yasan sunzo har gida sunbada hakuri"

Abba yace"emana, siyasarsa yake so yakare kawai"

Malam tace "yanzu ai gashinan dole tasa d'annasa yasan darajar mutane, koma me sukayi masa a abujan bazai dameniba, ko banza anqara koyawa dansa tarbiya dakuma sanin haqqin d'an adam"

Haka sukai ta mamakin wannan al'amari, Wato kudi da iko sunyi a rayuwa, idan kana dasu bakada damuwa ta wani fannin, inba kudi da iko ba waya isa yasa Hon Mai unguwa saleh dogo yazo har qarqashin talakawansa da sunan neman yafiya?



*** ***** ***


Abincin ta tsaya tahada shi yanda ya kamata, sai farin ciki take wannan ne karo na farko da zata zubawa mk abinci yaci da sunan sunason junansu

Dauka tayi ta nufi part dinsa da Abincin, Tun kafin ta qarasa take jiyo,tashin surutunsu suna zancen ball🤣

Ahankali ta tura kofar falon ta shiga, duk suka juyo suka kalli kofar, yana ganinta yahad'e rai Kamar yanda suke ada can
Mamaki yakamata, amma saita share tayi musu sallama tareda ajiye Abincin, cikin Murmushi tace "toga abinci," tafara kokarin zuba musu

Nas yace"gaskiya ne kin kyauta, yau zamuci Abincin amarya, dama tunda akai bikin ayyuka basu barmu munzo ba "

Shide mk yana zaune baice da ita uffan ba, sai wani qara had'e rai yake

Murmushi tasake yi tafara zuba Abincin a plate, tsintar muryar sa tayi yace" Barshi, jeki kawai "

Cikin mamaki ta kalleshi, jikinta yayi sanyi, tace" kace kanason abinci "

" cewa nayi sabirah ta kawomin a binci, ki tashi kije kawai"

Tasake kallansa Babu damar tambaya, saboda yana magana sai bata rai yake yana qunci🤣

Tatashi tsam, tafuto daga falon batare data qara cewa komai ba

Tana fita, Yarimah ya dubeshi yace"menene abin bacin rai Dan zata zuba mana abinci? Shan kunu ai yaqare mk tunda tariga taga komai 🙊🤣

"please Nas Dan Allah ka qyaleni"

Yasir yace"fadan masoya dadin kallo gareshi, inama tana nan nafara video "🤣

Mk ya kalleshi yace" dalla Malam inzaka zuba mana abinci kazo ka zuba ma na"

"A a nikam munci abinci awajan Ummi Tun kafin kuzo, naqoshi"

Shima Nas yace "zanfi buqatar green Tea nima akan abincin gaskiya" 🤣

Yace"Ok, yadauki wayarsa maimakon ya kira Nawal saiya kira Ummi 🤣
Yace tabawa sabirah green Tea takawo wa yarimah 🤣

Adede lokacin Nawal tashigo falon, ranta duk ajagule
Ummi ta kalleta tace"yawwa Nawal kihada green tea ki kaiwa yarimah Nasir "
Tana fada mata tajuya tashige dakinta, dama futowa tayi tafadawa sabirah saqon kuma saiga Nawal din tadawo🤣🤣

Itama bataje hada shayin ba tawuce dakinta, tana zuwa ta zauna agefen gadon tareda tagumi hannu bibbiyu 😱

Najma ta dubeta tace" Baby menene kuma? "

Tace" Babu komai"

Nas tace"kuma kikai tagumi? "

Cire tagumin tayi tace" na kai masa Abincin shine ya koroni, ransa duk abace, ni bansan mena masaba "

Najma tace" kode kishin ne yatashi, tunda yana tareda abokansa kikaje? Kokuma Dan Anwar yazo yaaganki shine yake jin haushi? "

" Najma abokansa nefa, tayaya zaisa haka aransa? Inda bai amince dasuba ai ina ganin bazai gayyacesu zuwa gidan nanba, sannan shikuma Anwar aiba sona yakeba saboda me zaiyi kishi dashi? dade Nuhu ne bazan qarya ta ba Dan yayi kishi 🤣

Najma tace "to ai sai kije ki bashi hakuri,"

"ni wallahi tsoron sa nake Najma"

Daria sukasa gaba dayansu, Nas tace tsoron me? Mijin kinefa

"to idan na bashi hakurin zai hakura?"

Nas tace "mezai hana"

Tace "to Nas tayaya Zan bashi hakurin?"

Najma da Nas har hada baki suke wajan cewa "saimun fada miki?" 🤣🤣

Tace"to aini Allah daya bata ran duk yamin kwarjini, yanxu ma sunce akai musu green tea wallahi bazan kaiba, saide Najma taje 😃"

Najma tace" A a wallahi Babu Inda zani, kinsan halin wannan yasir din, nikuma idan yamin bazanyi shiru ba "

Nawal ta kalli Nas tace" Dan Allah Nas please 🙏🏻"

Nas tace" to, tashi Muje kitchen din muhada musu "

Kitchen din sukaje suka hada shayin yayi dadi sosai, Nasrin ta dauka tatafi
Da sallama abakinta ta shiga falon itama

Atare suka amsa mata gaba dayansu
Tace" ga tea nan inji Ummi "

Yarimah ya kalleta, yafara magana aransa wannan duk yanda akai 'yar jin kaice 🤔
Kice mana ga tea bai isaba saikin danganta abin da wadda ta aikoki? Wato bake kika sa kanki ba kenan 🤣

Yatsina fuska yayi yace" ita Ummin ce tabaki tace kikawo? "

Kafin ta bashi amsa yasir yace," Nasrin shine maishan tea din, hada masa kitafi kinji "

Tea din ta zuba a cup sannan tadauki suger zatasa
Yayi saurin katseta da cewa" waye yace miki haka ake hada tea? Saikin fara zuba suger tukunna sannan kizuba Ruwan zafin "

Mk da baiyi musu magana ba tunda tazo, yabude baki da nufin yiwa Nasir magana yace
" Nas "

Atare suka amsa 🤣ita tace na'am shima Nasir yace na'am 🤣

Mk yace" no Nasrin ba dake nakeba, yitafiyarki kije kihuta

Tana ficewa yace "Nas, kaga nanfa ba masarautar ku bace🤣
Kace wannan yarinya tayi shiru kasace cewa wannan? kudama masu mulkin nan dad'i na daku iko wallahi"

Nasir yace "har nakaika ikon? shikkenan Dan matarka ta batama rai saika huce akaina? 🤣

Daga nan yaja Tea dinsa yafara sha, yasir ya miqe yace" nikam nayi waje, zanje nadanga gari"

Mk yace "kace dai zakaje ka dauki waccen yarinyar dakuke raba abin fada kuje kuga gari" 🤣

Yasir yace "shikkenan daga cewa Zan fita saikace Zan dauki wata yarinya?"

Nasir yace"kaifa yasir baka gane shi bane, matar sa ce take damunsa, dakayi tafiyar ka ka share shi kawai, nima gida Zan wuce daga nan "

Yasir yace" ok bye "daga nan yafice



*** ***** ****




Nasrin na komawa daki tace "wallahi Najma gara da baki jeba, wani yarimah yawani hakimce sai yauqi yake, shi ala dole ya iya hada shayi 🤣, wallahi bashida mutunci," sannan ta kalli Nawal tace "kekuma kije kibawa mijinki hakuri dan yana nan fuska adaure wallahi 🤣, Abincin ma banga alamun yaci ba"

Najma tace "ai shiyasa naqi zuwa wallahi"

Tashi Nawal tayi tace "ni yanzu ya Zan masa"

Nasrin tace "ki masa komai ma, Pls idan kin fita kija mana kofar 🤣

Harararta tayi sannan tafice daga dakin
Harabar gidan tafuto anan tahadu da yasir zai fita, tace" kona turo su Najma su rakaaka unguwar? "

Yace" A a rabu dasu su huta "

Tace" A a wallahi, bari nakira su saiku tafi, suna zaune Babu abinda suke "

Ta manya yayi mata yace" kuma ai Zan gajiyar dake, ga wayata nan sakamin number ta kawai saina kirata, kinga kema kin huta 🤣🤣

Zuciya daya ta karbi wayar tasaka masa number, sannan tayi gaba, turawa tayi tashiga falon, a lokacin shima yarimah zai tafi, tayi masa sallama sannan tanemi waje ta zauna, saida mk ya rakoshi har bakin kofar falon, suna tattaunawa akan wasu takardu sannan yajuyo falon

Sarai yaganta azaune, amma saiyayi fuska zai wuce daki, ya d'an basar yana jira tayi masa magana, amma Nawal tayi shiru 🤣Dan haka kawai saiya qyaleta yayi wucewarsa cikin d'akinsa

Tana ganin shigarsa itama ta doru abayansa zuwa dakin, ba komai ta tuno ba sai ranar dayace bazata kwana masa adaki ba, take kiran yaya Sultan tana kuka, 🤣🤣

Ganinsa tayi Akwance agadon, ta qarasa ta zauna aqasa takama hannunsa ta riqe tace, "Mai Babban suna Dan Allah kayi hakuri, idan na batama rai kaji"

Juya mata baya yayi, batare dayace komai ba

Tasake cewa "haba Baffan Ummi, Babynka cefa, kayi hakuri kaaji nawan"

Nanma yamata shiru, ta kalleshi tarasa yazata masa, ga kunyar sa datake ji, yanzu kuma bayan wannan meyake so Dan Allah, ta taqarqare ta bashi hakuri amma ya qyaleta 🤔

Wata dabara ce ta fado mata, kawai saita hau kan gadon tafada jikinsa ta fashe da kuka, ya kalleta, jiyake Kamar yaqara mannata ajikinsa, amma saiya daure yafara janyeta ajikinsa 🤣
Tanajin haka ta qara maqalqaleshi, tana kuka qasa qasa, cikin muryar kuka tace "kayi hakuri nayi kuskure insha Allah bazan sakeba,"gashi ta maqalqaleshi sai goga masa jikinta take

Yarasa yaya zaiyi kawai saiya rungumeta sosai ajikinsa, yafara bubbuga bayanta yace" shikkenan komai yawuce, Baby nah meyasa kike da hakuri ne sosai? Meyasa lokaci daya zakice kin yafewa wannan yaron? Kinsan girman laifukan daya miki kuwa?

Tanajin haka aranta tace ashe fishin na Anwar ne🤣🤣

Cikin kuka tace"to so kake nace ban yafeba kukashe shi? 🤣

Yana yinsa yafara canjawa, cikin shaqaqqiyyar murya yace"to meyasa kai tsaye zakice kinyi hakuri, memakon kice abarshi sai next week zakisa asakeshi 🙆🏻🤣
Nima shiyasa nayi fushi nacewa Ummi tabawa sabirah abinci takawo min "

Hawaye ne suka zubo mata tace" to shikkenan kayi hakuri, inde hakan tasake faruwa Zan dauki mataki "

Hannu yasa ya share mata hawayen idonta cikin rada yace" toki daina kukan mana "

Shiru tayi ba tace masa koma ba, yafara shafa kanta yana rarrashinta yace" to kiyi hakuri nima nadena fishi dake, Pls kidena kukan kinji Baby nah "

Daga masa kanta tayi alamun to, amma hawayen baibar zubo mata ba

Yace" Baby nah nace nadena, bazan sakeba, inde akan fishi na ake wannan kukan toni nace na daina "

Cikin shagwaba tace" toba kaine kaqi cin Abincin ba "

Yanda tayi shagwabar kadai yasa yasume Akwance 🤣batayi aune ba taji yafara kissing dinta
Duk Inda yakai bakinsa jikinta kawai lasa yake, Ahankali yatura hannunsa ciki rigar jikinta yana abinda yaga dama, gaba daya yahanata motsi Mai kyau ajikinsa

Lokaci daya hankalin sa yatashi, yafara kokarin cire mata kayan jikinta
Dasauri ta riqe hannunsa tace "Mai Babban suna agidan Ummi fa muke, koka Manta"?

Muryarsa adisashe yace"Baby nah nasan tsoro kikeji shiyasa zaki hanani ko?pls Baby Allah bazanyi da zafi ba "

Tabbas wannan tunanin ne aranta, domin kuwa da hankalin ta bazataso sake gamuwa da Baffah ba, amma bata nuna masa hakanba sai tace" A a, kaga kome mukai Ummi dole zata sani "

Yace" tomu tafi gidanmu? "

Tace" Najma da Nas fa? Ina zasu? "

" kibarsu anan gidan mana, yasir ma anan part din zaai zauna fa, ba gobe zasu tafi ba? Saimu zo kuyi sallama dasu goben "

Kallan Idanunsa tayi taga duk ya qanqance saboda fitina, tace" to daga ni naje na shirya mutafi"

Dagata yayi yace "ba wani shiri, kawai dauko jakarki Muje muyiwa Ummi sallama muwuce, 🤣🤣

Tace" Mai Babban suna kartace munyi rashin kunya"

Yace"to kuma ni saiki barni namutu ko?"🤣🙆🏻

Tace" A a, sannan tatashi, shima yasakko daga gadon yabiyota abaaya, juyawa tayi ta kalleshi sama da qasa tace"Allah yasauya kaya kasaka Manya, inba hakaba ko, tam Ummi zataga wani abu "tana fadar haka tafice da gudu daga cikin dakin

Kallan kansa yayi yadafe kansa🤦🏻‍♂cikin zuciyarsa yace aiduk ke kika janyo hakan

Ita kuwa tana zuwa daki taga Babu su Najma, anan ta tabbatar sunbi yasir sun fita, kayanta tahada acikin jaka, har Ruwan maganin da Malam yayi mata duk tasaka su aciki dasu dakanda ummah tahado mata dataje gida

Ta shirya tsaf tafuto falo dauke da jakar ta, ganinsa tayi da key a hannunsa yana karkad'ashi, manyan kayane ajikinsa, cikin ranta tace um wannan bawan Allah fa da gaske yake

Yana ganinta yatashi yadauki jakar, sukayi dakin Ummi, da sallama suka shigo dakin

Ummi tana zauna a sallaya tanajan carbi sai ganin bayin Allah tayi 🤣suna shigowa daki da jaka ahannu, cikin mamaki tace,"lafiya?"

Saida yadan sosa kansa sannan yace"Ummi zamu wuce ne "

Ummi cikin ranta tace ikon Allah 🤣🤣

Sannan ta kalli Nawal tace" ina Zakuje? "

Cikin sauri yace" Ummi gidanmu zamu tafi "

Tace" to wannan karon banice zance kutafi ba kenan, kune zaku kai kanku? "

Rufe ido Nawal tayi cikin kunya

Ummi tayi Murmushi tace" to ku gaida gida, Allah yatsare hanya "🤣🤣

Nawal de ba tace komaiba tamiqe, shikuwa mk yace" Amin Ummi "🤣🤣









(mutara zuwa jibi insha Allah 🙏🏻, gobe Zan huta)









Sharhi please 🙏🏻😢






Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


45&46



Yaja jakar yayi gaba, Ummi ta miqe tsaye tace"toke ga wannan kitafi dashi, sai kidinga amfani dashi kullum "

Tabata wani Ruwan tsumi dayake cikin leda acikin wata qaramar jarka

Cikeda kunya ta karba tace" to Ummi "

Sannan suka futo daga dakin a lokacin har Baffah yasaka kaya amota 🤣
Ummi ta kalleshi tayi Murmushi, cikin ranta tace nima de yau nahuta 😃, shida kansa yabude mata gaban motar, tashiga ta zauna, shima ya zagaya yashiga, Ummi ta leqo da kanta ta window din da Nawal take tace"to Baffah tunda ba jira sai tafiya, yanzu sai yaushe kenan Zan ganku? Kosai nazo? "
Murmushi yayi yace" Ummi ai munada baqi, gobe ma zaki ganmu, insha Allah "

Tace" to shknn Allah yakiyaye "daga nan sukai sallama itama takoma ciki

Da kansa yafara driving din Ahankali, cikin nutsuwa, Mai gadi ya bude musu gate suka fita, sunyi nisa cikin tafiya Babu Wanda yake cewa dan'uwansa komai, itade Nawal Gabanta faduwa yake kawai, yayinda take kallansa qasa qasa taga shi hankalinsa Akwance yakema yana driving dinsa
Hannunsa ta kallah wanda yake juya sitiyarin motar gashi Mai laushi kwance a tsintsiyar hannunsa
Ahankali yajuyo ya kalleta, sannan yakama hannun ta guda daya yariqe cikin nasa hannun, dayan hannun kuma yana driving


Itade tayi shiru, duk jikinta yayi sanyi, karonta dashi na farko kawai take tunawa

Har sukaje gida Babu Wanda yayi magana acikinsu, maigadi na bude musu gate suka shiga, yana tsayawa tafuto ta jirashi, yafuto mata da jakar tasa hannu tafara ja, Kallanta yayi yace"yanaga duk kinyi wani iri ne? "

Tace" Babu komai fa "

" kode saboda kinbar ummi ne yasa hakan? "

Girgiza masa kai tayi

Yace" ok"
Yamatso yakarbi jakar sukayi ciki, dakinta suka shiga, yana ajiye mata jakar yafada kan gadon tareda kwanciya

Ta kalleshi tace "ina zuwa" bata jira amsar sa ba tafice
Kitchen ta shiga tafara hada masa abinda zaici,sannan tafara gyara kitchen din duk da ba wani abu yayi ba



*** ***** ***


"nikam dama gida muka koma wallahi, tafiya taqi ci taqi cinyewa, babu ko lemo bare mutum yayi tunanin samun Ruwan sha🤔

" to dake waye yace miki jin dadi kika futo yi? Babu Wanda zai siya miki ruwa, yanda kika futo haka zaki koma "🤣

Tace" to meyasa ka daukomu in hakane? "

Yace" Nawal ce tasani na futo daku, ke waye yace miki nine nake san tafiya daku? Aini banasan indorawa kaina nauyi🤣

Ajiyar zuciya Najma ta sauke sannan ta kalleshi dakyau tace"to Allah yarufa Asiri, Allah gamu gareka"🤣

Duk wannan surutun da Najma takeyi itada Yas, yarimah baisa musu bakiba, hakama Nasrin ba tace komai ba, tana de jinsu tana Murmushi, yasir ya kalli yarimah yace "yarimah ina zamu saukeka?"



Cikin aji yace "nan gaba kad'an zakayi"

Nas ta kalli bayansa ta harareshi afakaice, cikin ranta tace kowa zaiyi wa yanga oho 🤔

Sunayin gaba kad'an suka saukeshi, yafuto daga motar, yabar wayoyinsa aciki

Yasir yace"yarimah kayi mantuwa fa "

Ahankali yajuyo sai alkcin yatuna da wayoyinsa, dawowa yayi, ya sunkuya zai dauki wayar tsabar iko saiya kalli Nasrin yace" ke bani wayoyina "

Nasrin ta kalli Najma tace" dake yake "

Itama Najma tace" A a dake yake de, keda kike kusa dashi "

Ganin zasu raina masa hankali yasa ya kalli cikin idon Nasrin yace" dake nake ke zaki bani wayar ba ita ba"

Ta kalleshi taga ga wayoyin nan agabansa amma wai sai anbashi tace"naga gasunan agaban ka "

Yace" Ok bazaki bani ba kenan "

Turo baki tayi gaba, tadauki wayoyin tameqa masa batare data kalli idonsa ba, shima cikin ransa yace wannan yarinyar kanta rawa yake naga alama, Dan haka yasa hannu ya fizge wayarsa tareda yiwa yasir sallama yayi gaba

Harara tabishi da ita, cikin ranta tace d'an me quncin rai🤣🤣

Yasir ya kalli Nas ta madubi yace"nasrin ta yarimah, kiyi hakuri fa, haka yake, kinsan Dan sarki ne, yasaaba komai saide a yi masa, shiyasa zakiga komai yasa ayi baiyi da kansa ba "

Murmushi tayi tace" la Babu komai yaya yasir"


Yace"Nasrin ina kukeso nakaiku ne? "

Cikin sauri Najma tace" mukam ko ina nema ai zamuje, ai baifi bude idoba "

Yace" nifa cewa nayi Nasrin"

Tace "Najma da Nasrin duk abu dayane" 🤣



*** ***** ***



Shiru shiru yana jiranta bata dawoba, dan haka yatashi yafuto falo, qamshin dayaji a kitchen ya tabbatar masa cewa tana can, kai tsaye yashiga kitchen yaganta tana hda abinci

Rungumeta yayi tabaya, cikin rad'a yace mata" Baby nah, abinci kike mana? "

Tace" eh, gashinan nagama, Muje kaci abinci "

Daukar Abincin tayi tafuto falo, shima ya biyoba abaya, zama sukai tatura masa Abincin gabansa tace" to gashi, nasan kanajin yunwa "

"no saide kibani"

Kallansa tayi, tayi qasa da kanta, tayaya zata iya bashi abinci?meyasa yacika rigima ne Kamar qaramin yaro? Ta dago kanta tace"a a Dan Allah ka daure kaci kaji"

Baice da ita komaiba, ya janyo Abincin gabansa, yadauketa cimak, yadora ta akan cinyarsa, yadebo jallof din taliya dataji kayan lambu da kifi a spoon, yakai baakinta

Tace"nifa naci abinci, kaine bakaciba"

Yace "idan ba zakici ba, nima bazanciba"

Babu yanda ta iya, haka ta bude baakinta, yafara bata Abincin, d'an kadan taci tace taqoshi, yabata spoon din itama tafara bashi, bai ci dayawaba yace yaqoshi

Tadauki lemo a cup ta bashi yasha, ya kalleta yace"Baby, ina d'anjin yaji fa kad'an "

Kallansa tayi cikin mamaki, itada batasa wani abun yaji aciki ba


Cikin sauri tace "tsaya na tashi na kawo ma ruwa to" tafara kokarin tashi

Cikin sauri yamaidata kan cinyarsa, yace"no Baby Karki tashi "

Tace "yajifa kace kanaji, kaabari nakawo ma Ruwan"

Kallanta yayi yace"no ga Ruwan nan awajan ki "

" Kamar ya? "

Yace" gashinan awajan ki, ni naki nake san sha"

"mai Babban suna banganeba"

Murmushi yayi, yasaka hannunsa duka biyu ya tallafo kanta, sannan Ahankali yamatso da fuskarsa dab da tata, cikin nutsuwa yahade bakinsu waje daya


Lips dinta yakama yana tsotsa Ahankali, lokaci daya yanayin ta yafara canjawa, saboda abubuwan da ummah tabata tanasha agida

Zaman kan cinyar tasa saiya sake jefata cikin wani irin yanayi, shi kansa bazai so tatashi ba, saboda yin hakan Kamar tonuwar asirin halin dayake ciki ne

Tana tuno irin azabar da tasha a hannunsa, tafara kokarin raba baakinta danasa, Ahankali ta miqe zata tashi, yasake maida ta yazaunar da ita🤣

"ina zakije?"

Tace"kaga inada baqi, kuma kace gobe zamu koma,kabari sai goben kawai "

Ahankali yace" meyasa Baby?, aide nine nace zakiji goben ko? "

Ta daga masa kai

Yace" to da kaina Zan kai ki kunji, kuma nina fasa ma, babu abnda zanyi, kawai bakinki nakesan sha, shima yaji nakeji kinji Baby "

Kallansa tayi, taga idonsa yafara sauya kala

Shima Kallanta yayi, sannan yayi qasa da murya yace" insha? "

Ahankali ta daga masa kanta batare data ce komai ba


Bakinsa yamayar cikin nata yafara sha Ahankali, Tun tana jinsa harta fara maida masa martani aikuwa hakan tada fara ba qaramin rudashi yayi ba


Lokaci daya ya rikice yafara shafa Kirjinta Ahankali, abinda yake mata yafara fixgar hankalinta, batasan lokacin data sakar masa ragamar komaiba

Awajan yarabata da rigar jikinta, ya maida kansa kan breast dinta yafara sha, lokaci daya tasaki yar qaramar qara, ganin hankalinta baya jikinta yasa yadauketa cak sai cikin dakinta

Anan ya nuna mata soyaiya iri iri, sannan yafara neman hanyar shiga, tanajin haka, tadawo hayyacinta

Awannan lokacin idonsa yagama rufewa, itan kawai yake buqata, kokarin tashi tafara amma yasa hannu ya maida ta takwanta, yaja blanket Yarufe musu jikinsu
Lokaci daya tasaki qara tace"innalillah nashiga uku na "
Hawaye sukay zubo mata, domin kuwa banbancin sa danan rannan kawai kadanne

Sai runtse ido take tana hawayen wahala, shikuwa wasu irin surutai yake mata, ita kanta batasan Inda maganganunsa suka dosaba



*** ***** ***



Suna dawowa gida, su kaga daki wayam Babu Nawal Babu wasu kayan nata
Futowa falo sukai anan suke Tambayar Ummi, tace musu aisu Nawal sun dade agida🤣
Amma tace gobe zata dawo suyi

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment