Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake amsa waya 😳🙆🏻, idan ba week day neba baya amsa waya saide in shine ya nemeka "

Yace" to shknn mungode, sai anjima "

Yana kashe wayar yadubesu yace" to kunji,"

Murmushin yaqe Nawal tayi" tace toshknn likita mungode, insha Allah zamu fadawa abban, ngd "

Yace" toki gaishe shi nagode sosai "


Fitowa sukai daga office din jikinsu a sanyaye, ta dubi Nas tace" Nasrin mutumin nan yafi qarfina, sai hawaye sharrr "

" haba Nawal, ya zaki karaya Tun yanzu? "

" Nas kinajifa abinda akace akansa, yana wata qasa, idan yazo Nigeria ma sai Abuja, nida ko hanyar Abuja ban taba biba" 🤣

"ki kwantar da hankalin ki nace, akwai bikin wata yar'uwarmu da za'ayi a Abuja, zamuje bikin, kawai ina ganin ki shirya mutafi tare, insha Allah zamu hadu da shi"

Hawayen idonta tashare, "Nas kina ganin babu damuwa kuma agida za'a barni?"

"mezai hana, zanzo gobe da kaina nayiwa umma da Abba lissafin karya kawai saimu wuce🙊🤣"

"to shikkenan Nas saikinzo"

Haka suka futo daga asbitin tana qara kwantar mata da hankali


*** ***** ***


Tana zuwa kofar gidansu taga yashi dasu siminti dayawa an jibge, Data shiga gidanma duk suna nan atsakar gida tayi sallama tareda cewa"umma nadawo, ta kalli mama mariya tace mama nadawo "

Atare sukace to sannu

Hijaabin jikinta tacire taja kujera ta zauna tana cewa wash Allah, Saif daya futo daga daki yaja ribom din kanta, kasancewar babu kitso sai gashin nata yazubo agadon bayanta yace" yaya Baby yalasha "

" Saif banaso, inba idaan aljannu na suka tashi ba zakaji dadiba "

Yace" yasin su tashi, muda muke da Malam "

ta kalleshi tace "ina Najma?"

"tana daki tana Zumba"

Cikin sauri ta tashi tace"a a nima natafi "ta shige dakin mama mariya

Wata tsohuwar computer Salisu ce agabanta ta qure wakar zumba tana gani tana rawa
Itama kuwa ta shige sukaci gaba

(zumba wata rawace da masu qiba sukeyi domin motsa jiki, idan kana yawaita yi qibarka zata ragu, idan bakada qiba kuma tana qara futowa da mutum shape dinsa musanman mata)

Har wajan azahar suna abu daya, sannan sukaje sukai wanka saboda gumi dasuka hada


*** ***** ***

Washe gari kuwa Nasrin tazo gidan, da Abba tafara haduwa a kofar Gida shi da masu aiki suna kwaba siminti, ta gaishe shi ya amsa mata, tace Abba dama wajan ka nazo kaida umma "

Cikin mamaki yace" to inajin ki me yafaru, Allah yasa de lafiya, "

" Abba dama biki zamuje Abuja nidasu mamata, shine mama tace nazo na tambayeku tanaso mutafi tareda Nawal "

(😃🙊Nasrin Allah ya hore miki)

Abba yayi jim yana tunani sannan yadubeta" to kwana nawa zakuyi? "

" kwana biyar "

Yace" to shknn Babu damuwa, idan tafiyar ta tashi saiki zo kutafi "

Cikin murna tace" to Abba mungode, daga nan ta shige gidan, tana bawa Nawal labari tahau murna tana kuma fata Allah yahadata dashi

Saida Nasrin tawuni sannan tatafi Gida

Cikin satin kuwa tafiya ta kankama🤣, Umma tace nide Baby ki nutsu karkije ki dinga yimusu sakarci agida, sannan kuma kidinga saka kayan mutunci banda zama da qananun kayan nan"

"to umma insha Allah, Abba yazo har dakin yabata dubu sha biyar, ta karba tana godia shikuma yafice umma ma tabi bayansa, Najma ce tashigo dakin tace" Baby mutanan Abuja, 🤣🤣yau kuma sai Abuja "

Tace" wallahi kuwa, Abuja Kamar munje "

Najma ta kwashe da daria," to yaushe ita Nas din zatazo? "

" tacemin tana hanya, zatazo mutafi, amma sai munje gidansu, da yamma kuma zamu dauki hanya "

Najma tace" to mude tunda munbaki shawara kinqi dauka bamace komai ba "

" Najma kekike nufi? "

" A a Babu abinda nake nufi Baby, kuda zakuje kusha biki, amma inaso kisani Tun muna yara tare muka taso dake, banda umma Babu Wanda yasan halin ki sama Dani, haka kema kinsanni kinsan abinda Zan iya da Wanda bazan iyaba, saboda haka Babu abinda zaki boyemin nakasa sani, "

" aikuwa wannan karon tunaninki bai baki daidai ba "

Cikin daria tace" to Baby, adawo lafiya, Wanda baiji bari ba yaji hoho🤣🤣, idan kin hadu dashi kice yayarki tana gaishe shi "

Daga haka tafice daga dakin, ita kuwa ko a jikinta kayan ta ma taci gaba da shirya wa cikin jakar da zata tafi da ita

Da yamma suka dauki hanyar Abuja itada Nasrin dakuma wani qanin Nasrin din, sunata firarsu amota
Har Allah yasauqesu lafiya

Gidan yan'uwan su Nasrin din suka sauka Inda ake hidimar bikin, matar tanada faram faram Babu ruwanta, daga nanfa aka fada harkar biki, koda batada niyyar kwalliya Nasrin ce take sakata dole taayi, aikuwa sosai suke zuba kyau abinsu duk Inda suka wuce sai ankallesu musanman Nawal

Kwanansu biyu a Abuja Babu wani labari, nanfa tadaga hankalin ta, ta shiga damuwa, Nas tace "kiyi hakuri beauty insha Allah zamu ganshi kafin mubar garin nan"

Tace "toshknn Nas Allah yasa"


Washe gari za'ai dinner haka sukaci kwalliya, matar Data yiwa amarya itace tayi musu daidai misali

Aikuwa sunyi masifar yin kyau

Suna zuwa wajan dinner aka farayi cikin kwanciyar hankali

tadubi Nasrin tace "Nas nagaji da zaman nan wallahi, bari nadan fita nadawo,"

Tace mata" to beauty "


Tana fita wajan kuwa ga motoci nan birjik, ta jingina ajikin wata Mota
gawasu maza nan agefenta kusan su hudu suna firar su

Wani bawan Allah ne yaqaraso wajan ta yace mata " hi"
Kallansa tayi kawai batace komai ba

Yasake cemata "Baby girl mekike jira ne anan wajan ke kadai? Be kamata mata kyawawa irinku sudinga zama su kadai ba"

Tace masa "ko?"

Yace "sosai ma kuwa, ga motata can, mezai hana kishiga Muje ko shisha ne musha mudawo kafin agama dinner" 🙆🏻

Zaro ido tayi😳, cikin ranta tace"nashiga uku shisha? Gabanta yafara faduwa, gatada tsoro

Amma afili sai tace "A a nagode"

Yace"fine, to nide nagani inaso "

" kayi hakuri bawan Allah ansamin rana, wani watanne ma bikina "

Cikin rashin damuwa yace" to shikkenan, Babu damuwa, bye "

Bayansa tabi da kallo, oh akwai tantirai aduniya, Allah kaqara tsare mana imaninmu"

Wasu motoci ne guda uku baqaqe sukazo wucewa ta wajan, ba wani gudu suke sosai ba, mazan nan na gefenta ne taji wani daga cikin su yace " kace akwai harka, MK Yashigo gari kenan"

Gabanta ne yafara faduwa, tabi motocin da kallo bakinta yafara rawa wajan furta m.m...mk

Wani daga cikin su yasake cewa "ai mk yayi a rayuwa, kana ganifa duk samarin nan na unguwar su daya bayan daya ya nema musu aikin yi"

Wani kuma yace "nifa naji ance wallahi ba qaramin Dan shaye shaye bane"

Na hudun kuma yace "dalla Malam ware, kawai hassadar mutane ce, inde anga kanada shi yanzu za'a fara cemaka manemin mata, Dan giya, Dan ta'adda"

Kanta ne ya kulle, tarasa abinyi, kawai saita doru abayan motocin tana binsu cikin sauri, wayar ta tad'auka takira Nas tace "Nas futo futo, futo Nas ga mk can, futo futo Dasauri Dan Allah"

Ai afujajan Nas ta futo 🤣🤣tana waigawa damanta sai hango Nawal tayi tanabin wasu motoci Dasauri, itama kawai saita fara binta da Dan gudu harta tarota

Adede lokacin saiga wani me adedeta, Nasrin ce ta tsaida shi, yana tsayawa kuwa Babu neman excuse suka fada ciki, Nawal tace "Muje Muje Dasauri kabi bayan wadancen motocin pls "

Hajiya kuyi hakuri, doka tahana adedeta haya agarin nan, nima yanzu satar hanya nayi nafuto, amma idan aka kamani kulleni za'ayi"

Nasrin tace "Dan darajar Allah karufa mana Asiri, Muje Dan Allah, Babu abinda zai faru "

Cikin faduwar gaba yaja adedeta suka fara tafiya, Nawal kira take "kaqara sauri mu tarosu pls Malam"

Hajiya saide kuyi hakuri ina hawa Babban titi kamani za'ayi, saide mubi ta qasa

Nasrin tace "koma ta inane Muje, mude fatanmu mutaro motocin kawai"

Aikuwa saiya qara gudu sosai , kasancewar hanyar akwai gargada ana sabunta titin ne, me adedeta yaci karo da wani rami sai kiyaaaaa adedeta tafadi 🙆🏻😳

Agefen da Nawal take zaune Agefenta adedetan yafadi, Nasrin tafad'o kanta 🤣🙆🏻🙆🏻

Aikuwa sai suka dauki ihu da kururuwa Nasrin tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, jama'ah akawo dauki 🤣

Ita kuwa Nawal sai ihu take tana" cewa wayyo nashiga uku hannu na, na mutu na lalace 😂😂

Mutanan dasuke gefen titi ne suka taho aguje aka kawo musu dauki, aka samu aka dago adedetan, Nasrin tafuto, ita kuwa Nawal sai ihu take saida aka zarota

Sannan shima me adedetan aka bashi temako

Gaba dayansu sunyi tsumu tsumu agefe Nasrin na kuka Nawal na kuka🤣Babu Mai rarrashin wani

Maganar Najma ce tafado mata, gaskiya ne Wanda baiji bari ba yaji hoho 🤣🤣

Wani yace "yakamata kuje asbiti, me adedeta yace" a a Babu komai shi baiji ciwo ba, ya kallesu yace "saide yanmatan "

Suma suka fara girgiza kai, Nawal tace bamuji ciwo ba, hannu nane de yadan bugu idan naje Gida Zan dindima da Ruwan dumi🤣🤣

Wani yace "inane gidanku amaidaku gida? Nasrin tace" can hakane gabas "

Wani yace" ikon Allah, yarinya a tambayeku gidanku kice gabas, a a yamma ba gabas " 🤣😃

Wanda yace zai kaisu gidan ne yace" zaku gane hanyar? Sukace eh, yace" to kushiga Mota Muje nasaukeku "

Me adedetan suka bawa hakuri sannan suka shiga Mota, da kwatance da Komai suka qaraso gida, basu kumabi ta hanyar wajan dinner ba🤣🤣

Yana saukesu sukai godia, tareda shigewa Gida, Nasrin ta dubi Nawal tace "bari naje nadafa mana Ruwan zafin a kitchen" 😃

Tace "to" tareda shigewa dakin da aka saukesu

Tana shiga dakin ta fada kan katifa tafashe da kuka, 😭kuka take riris

(kuma fa abin ba dadi Nawal 🤔kayi tattaki tundaga kano zuwa Abuja 🤣🤣))

a wannan halin Nasrin tashigo ta sameta tace"Nawal wannan mk din kodan gwal ne yakamata ki hakura dashi 🤣, Allah yagani kinyi iya yinki, saiki barwa Allah sauran, ki godewa Allah ma dabaki ganshi ba da tunanin sai yafi haka 🤣🤣"

(gsky Nas kinji jiki 😃)

Cikin kuka tace" hakane Nas, insha Allah daga yau nadena bibiyar al'amarinsa, gaskiyar Najma ce datace yafi karfina, yanzu Inda naje nakarye Abba ya tambayeni dalili bansan me zance nasaba, nagode da temakon ki agareni Nas "

Itama Nas din idanunta ne suka kawo ruwa, lokaci daya suka rungume juna suna kuka










































Masu cewa nayi posting sau biyu arana kuyi hakuri wlhy bazan iyaba, kosau goma nake posting arana bazaku dena fadar hakaba saide in labarin ne yaqare 🤗



Sharhi please 🙏🏻

Share and Comments Dan Allah









Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE 🌺


Writing by Amnah El Yaqoub


Dedicated to Itz sadeek



15&16




Saida suka gama kukansu suka qare sannan sukai wanka da Ruwan dumin da Nas ta dora musu

Awannan daren Nawal bata iyacin abinci ba, Baqin ciki ne fal ranta, yau gata cikin garinda mk yake amma takasa ganinsa, amma Babu komai ko banza idan tatuna taga motocin sa zataji dadi, a yanda takesan ganinsa ko tayar motarsa tagani zataji dadi, kuma tasan cewa koda bata sameshi ba acikin tarihin Rayuwar ta zata rubuta cewa taga wani abu nasa (🤔)


Har cikin dare juyi kawai take takasa rintsawa, banda kanta dake mata ciwo sosai, jikinta da zafi kadan
Asuba nayi daqyar ta tashi tayi sallah Nas tabata magani tasha, wunin ranar haka tayishi a kwance adaki

Washe gari sukai shirin komawa gida Babu laifi taji dadin jikinta sai hannun ta kawai dake mata ciwo kadan
Anbasu kayaiyakin biki sosai su alkaki, tana zuwa gida aka fara yimata oyoyo sannan tabawa kowa tsarabarsa, sai dare bayan Abba yadawo taje tace masa tadawo tareda yimasa sannu da zuwa

Tana fita tsakar Gida ta dora Ruwan zafi, saida yadan huce sannan tasa tsumma tafara dindima hannun ta,🤣 Najma tashigo gidan tadawo daga makarantar dare, itama taja kujera ta zauna tace"naso yau Babu makaranta wallahi, inzauna naji labarin Abuja, Inda muka tsaya "😱

Cikin yatsina fuska tace" aike kinada lokacin zuwa ma, ni gashi makaranta tahana, dana dawo sai bacci, ga gajiya, "

Tace" hakane kam, kuma kekam dama ai mutuniyar Malam ce kinsan komai shiyasa, yawwa Baby bani labari mana, Yaya kukai dashi? "

Cikin takaici 😒tace" wakenan? "

" wakwa Zan tambayeki inba mk ba?, bashi kikaje ganiba? Ko harkun hadu ne kinyi masa maganar yayi miki shegen duka shine ki ke gasa hannu "🙊🤣

" Najma banaso, banaso wannan ma aiba yibane "

Najma tace" dama mena fada miki? Dabesa an daureki bama, namiki barka da abin ya tsaya ahaka "🤣🤣

Cikin qunan rai tamiqe tsaye, kanki akeji Najma, daga haka tawuce daki

Washe gari zama tayi agida batayi shirin makaranta ba, tade kira Nas tace mata idan taje tayi mata attendance, itama tace mata bazataba saboda tagaji saide su shiga gobe, washe gari kuwa ta shirya tsaf cikin atamfarta dinki riga da sket, dinkin yahau jikinta kuma yayi mata kyau sosai saboda bata cika saka atamfar ba kullum cikin qananun kaya take saikuma abaya,
Hips dinta Kamar zasu fasa sket din datasa, rigar ma ta kamata sosai kana iya hango albarkatun qirjinta
Sannan ta dora hijabi asama, tafuto falo taga umma bata nan, ta duba tsakar Gida ma bata nan, Dan haka ta duba dakin Abba anan taganta tana saka masa turaren wuta, tace"umma nawuce school "

" to akwai kudin Mota ne awajan ki? "

" eh umma inada canji, saina dawo "

" to Baby Allah yadawo dake lafiya "

Tana fita kofar Gida taci karo da Abbanta, Ahankali tace" Abba natafi school "

Yace" school kuma? Waye yabaki iznin zuwa makaranta? "

Tace" Abba dama.. dama..

"ba dama dama na tambayeki ba, cewa nayi waye yabaki iznin zuwa makaranta?"

" bakowa"

Yace "ina safiyya?"

"tana ciki Abba"
"to wuce kikoma Gida"

Tana wucewa shima yadoru a bayanta, yaganta afalo azaune kusada umma tayi tagumi
Yace"saffiya, danme kikabar yarinyar nan zata tafi makaranta? "

" Alhaji ai danaga bakace komaiba, shine nace Babu damuwa saita dawo, tunda tanasan makarantar "

" Ok to tunda bance komaiba kikace yanzu nace Aure Zan mata "

Cikin sauri Nawal tadago ido ta kalleshi Gabanta na faduwa

Umma tace" Aure kuma Alhaji, nawa Babyn take da za'ace za'ayi mata aure yanzu? Dawa za'a mata auren? "

" Kamar de yanda kikaji safiyya, aure zanyi mata da Nuhu 😳🙆🏻"

Nan take hawaye ya wanke mata ido ta shige daki tana kuka

Umma tace" Amma Alhaji kasan yarinyar nan bata sansa, wanne irin aure ne wannan? "

" safiyya ke kanki kinsan irin tashin hankalin da muka shiga sanadiyar rashin lafiyar yarinyar nan, Allah yayi mata kyau, duk ranar dabata saka niqab ba haka zakiga ana Kallanta layi layi idan tafita,Data saka niqab dinma bata tsira ba kinga de abinda yabiyo baya, munsan abinda zai biyo baya nan gaba? to Tun kafin kyanta yazame mana masifa gara na aurar da ita, ni kaina hankalina zaifi kwanciya, sannan yaron nan Nuhu yana santa, menene laifin sa, yaro da abinyin sa?

Ajiyar zuciya tasauke "hakane kam, Nuhu bashi da aibu, Allah yarufa Asiri"


Umma tabita daki tace "Nawal, kiyi hakuri da zabinda Abbanki yamiki, ba zaiyi miki zabinda zaki cutuba, Nuhun nan yana sonki, dole zai miki abinda kikeso idan kin aure shi"

"umma ni wallahi bana son Nuhu"

Cikin fishi umma tace "to ai shikkenan Nawal, tunda ba'a isa afada mikiba, tunda kin ajiye wani bayan Nuhun saikije kifada masa, da Dan qaniyarki kinsan bakya san nasa kika bari yadade awajan ki, meyasa kai tsaye bazakice bakya sonsaba?" tatashi tafice daga dakin

*** ***** ***

"hello abokina mutumin fa yashigo gari Tun jiya da daddare"

"usy da gaske kake?"

"wallahi da gaske nake, yanzu haka yana nan cikin garin kano"

"karka damu, yanzu Zan nemi izni awajan aikinmu, bazanbi Mota ba, akwai kudi a wajena kawai Zan biyo jirgi"

Usy yace "Allah Sultan, shegen gaye kana wutafa, saikazo din, idan kazo ka kirani"

Daga nan sukai sallama

Ba'ayi awa dayaba yasauka akano, kai tsaye Gida yawuce, yana shiga yatarar mama mariya atsakar Gida, tace"a a Sultan kaine ahanya Babu sani, koda yake kai dama idan zakazo ai baka sanarwa 😏"

" wallahi kuwa mama, aimu kullum muna kan hanya bama neman iznin zuwa, " 🤣daga nan yayi dakin ummah

Yatarar da ita zaune afalo, tace" Sultan, sannu da zuwa, lafiya kuwa kazo? "

" haba ummah lafiya mana, kawai nazo ganin Baby ne, jibi ma Zan wuce, ina takene Babyn? Ko tana school? "

" Baby tana daki Sultan, kuka take "

" kuka kuma? Subhanallah me akayi mata? "

Umma tace" Babanku ne yace zai mata aure, zai bata Nuhu saurayinta shine take kuka"

Cikin mamaki yace"Aure kuma ummah? Ana zaune lafiya? "

" to Sultan dasai ana tsaye lafiya za'a mata? "🤔

Qyale umman yayi ya shige dakin, yaganta takifa kanta akan fillo tana ta kuka, qarasawa yayi yadagota tana ganinsa ta fada jikinsa tana kuka, bubbuga bayanta yafarayi yace" kiyi hakuri mana Baby nah, insha Allah Abba bazai miki Auren dole ba, bazai baki Wanda bakya soba kinji ko?

Daga masa kai tayi

Yace "share hawayen ki kizo Muje wani waje"

Tace"to yaya, sannan tatashi daga jikinsa "

Shikuma yakoma falo ya zauna yana tunani wannan yarinyar za'a aurar, to ai ko waye ya aureta shirme kawai ya aura da shaagwaba 🤔😂

Yana wannan tunanin tafuto sanye da hijab, ya kalleta yace" waike bakida Dan mayafi ne shikkenan kullum zululum zululum cikin hijabi saikace wata 'yar limamai? 🤣😃

Umma dake gefe tace"ai jikarsa ce "🤔

Cikin shagwaba tace" to yaya me zansa? "

"kije kinemi mayafi, kullum kuna qunshe agida Babu Inda kuke zuwa daga makaranta sai Gida, ko nanda kaduna bakujeba tayaya ma zaku waye"

Umma tace "Ah aitaje Abuja 🤣"

Mayafi taje ta dauko acikin kayan ta tayafa, baqaramin kyau tayiba, yakama hannun ta yace"umma muntafi unguwa "
" tosaikun dawo"

Yana fita yakira usy awaya yace "usy na qaraso muhadu anan layin gaban gidanku"

"to Sultan gani nan zuwa"

Sunayin gaba kadan suka hadu da usy, Nawal ta gaishe shi ya amsa a mutunce, Sultan yace ina zamu ganshi ne?

Muduba majallisar farko tukunna "

Majallisar suka nufa, suna tafiya maganar Nuhu tafado mata arai, sai Hawaye zirrr
Sultan ya kalleta yace" kiyi shiru mana, kibari idan muka dawo saiki fadawa yaya Salisu kuje dashi kubashi hakuri, amma ni yanzu ko najema ba kulani zaiyi ba, cewa zaiyi bansan duniyaba🤣🤣"

Ahankali tace" to yaya"

Majalissar farko baya nan, haka suka koma ta biyu, itama baya nan daga qarshe de haka suka dinga neman Anwar waje waje
Kamar almara suka tsinci motar sa dede Inda ya watsawa Nawal shaltos a ido

Gabanta yafadi
Tariqe hannun Sultan sosai taja ta tsaya, tace "yaya ina zamuje"

"dukda baki tambayi Inda zamujeba sai yanzu?"

Ya fizgi hannun ta suka qarasa har gaban motar, usy yace "Allah yasa de yana nan "qwanqwasa motar Sultan yayi, aikuwa saiya sauke glass din motar, tana yin arba da fuskarsa ta runtse idonta, ta koma bayan Sultan tabuya

Cikin Murmushi yace" A a gayu ya garin ne, Sultan 2days kabuya"

Cikin haushi Sultan yace"kaga Anwar ba wannan maganar ce takawo mu ba, futo da Allah muyi abinda ya kawo mu🤣 muyi gaba"

Cikin sauri yabude murfin motar yafuto yace" lafiya? Mena maka kuma🤣?

Tass kakeji usy ya dauke shi da mari 🙆🏻

Cikin sauri Nawal tadora hannu a kumatunta Kamar ita aka mara😂

Sultan yashaqe masa riga yariqe shi sosai, yace"Anwar Dan uwarka qanwata zaka kallah kaciwa mutunci?"

Sai a lokacin Anwar yadago yadubi Nawal, to aishi baimasan wannan yarinyar ba, ina zaisanta yarinyar da kwata kwata ma Kamar ba bahaushiya ba

Yace "wallahi ban santaba," yasake Kallanta yace"ke kece kikace masa nayi miki wani abu? "

Tsoro ne yakamata, jikinta yafara rawa, kafin tace wani abu, Sultan yadora masa mari agefen kunnansa, yace" yarinyar daka fesawa shaltos, yanzu katuna? Nace yanzu katunata?"


Lokaci daya yatunata, dama qanwar Sultan ce? Yasan da haka tayaya zai tabata? Bayan duk Majalissar su kowa yasan Sultan ba'a ta bashi yaqyale

Cikin tsoro yace "tambyeta kaji, ba itace tafara mari naba?"

Usmn ya wanka masa mari yace"anmareka, kai Dan gidan ubaan waye da baza'a marekaba? "

Sultan kuwa hannu yasa cikin aljihunsa yadauko kwalbar shaltos ya miqa mata yace" karbi ki fesa masa, karbi ki rama abinda yamiki "

Tace "A a yaya, Yaya na hakura, wallahi nayafe masa"

Takaici yakamashi dama yasan zaiyi fama da ita, Cikin tsawa yace bazaki karbaba sainaci ubanki?
🤣

Kuka tafara tace "yaya Allah ya nasan bayinsa masu hakuri, karka Manta da wannan, Inda narama Tun a lokacin toba lalle Allah yabudi idona ba, Yaya nayafe masa wallahi, yajeshi kawai akwai ubangiji, idan ni nayafe masa, wata bazata yafe masaba "

Usy yace" kaci sa'a wallahi, amma duk da haka saimun daki rabonmu "

Shima Sultan ya wullar da shaltos din aqasa suka hau Anwar da duka, shi yanayi Usman yanayi, gaba daya suka kumbura masa fuska, sannan suka rabu dashi sukai Gida

Ahanya sai sababi Sultan yake mata" akan wannan halin naki wallahi idan kika Auri me mata wataran sai kishiyarki tamiki dukan tsiya, 'yar matsoraciya kawai "🤣🤣

*** ***** ***

"Am kagane mk, zaman nan ya isa haka, kaiba zance kake ba, kawai kawaniyi fuska kabarni inata zuba, yakamata mudan fita muzaga gari haka, akwai manyan yanmata nake fad'ama alaji"

Shiru yayi Babu amsa

Abokin nasa yakalleshi dakyau, yaga kwata kwata ma hankalin sa baya kansa

Tafin Hannunsa yahada guda biyu yatafa afuskar sa

Firgigit yadawo daga duniyar tunanin daya tafi

Rigace ajikinsa baqa marar hannu, murdaddan jikinsa ya futo fili, wandon jeans ne ajikinsa tree quater da kadan yawuce gwiwarsa, yayinda kunnansa guda d'aya yake d'aukeda yar qaramar barima irin wadda maza suke sakawa

Abokin yace "mk wht happnd to you?"

Cikin miskilanci yace "itace"

"wakenan?"

Saida ya dauki kusan minti biyu kafin yace"BABY"

"Who is she?"

Ahankali yace "bansaniba"

"A wacce qasar take?"😳

"kano"

Abokin yasake cewa "What?"

Cikin damuwa yace "yes, yanda kaji, naje gaisuwa naganta, qaramar yarinyace, tabani tausayi sosai"

"u see, abinda yake cutarka kenan akoda yaushe, tausayi tausayi, abinde kenan, kayi waya kasa aje adauko ma ita kawai,😳🙆🏻 inaga hakan yafi, akan kadinga wasting time dinka" 🤷🏻‍♂

Huci yayi, sannan yace"tafi qarfin yanda kake tunani YARIMA NAS "

Nasir yasake cewa" A a to 'yar wayece ita?? "

" shine abinda bansaniba nima, bansan meyasa nakasa cireta a raina ba, bansan taba, bantaba ganin taba sai ranar, ba duka fuskarta naganiba, but naga lips dinta, kai kanka idan ka ganshi awajan zaka mace,🙈 inaso nasake ganinta kosau d'ayane arayuwata, "

" but mk ya akai kasan sunan ta? You mean ba itace ta fadama ba? "

" yes, naji ankirata da sunan ne, damuwa ta daya shine mafarkin ta danake, but nasan cewa tausayin tane yasa hakan, wataran Zan dena, sannan a lokacin danaganta tasa irin wannan Baqin abun da mata suke sawa afuskar su, menene ma sunanshi?

(anya mk fan's zasu baka jikar liman kuwa? 🤔🤔)

Ajiyar zuciya abokin nasa yasaki, yadafa kafadarsa "mk kanada hankali kuwa? Kana mafarkin yarinya kana cewa tausayi ne yasa?"


(tambayeshi de🤔🤔)


*** ***** ***


Tunda suka dawo Gida hankalin ta atashe yake, taje dakin yaya Salisu yakai sau hudu amma baya nan bai dawo daga kasuwaba

Sai wajan yamma yadawo, aikuwa tanajin maganar sa tayi sauri tatafi dakin, kawai sai ganin ta yayi a dakin tashigo da sallama, yadubeta"Baby nah ya'akayi?"

Tace"yaya dama wajan ka nazo, "

Zama yayi agefen gado yace" to inajin ki, "

Hawaye ne suka zubo daga idonta, tasa hannu tashare, tace" yaya Abba ne zaimin aure "

Dasauri ya kalleta yace" aure kuma? Shi abban ne yace zai miki aure? "

Cikin kuka tace" haka yace yauda safe, wai zai bani Nuhu, Yaya wallahi ko kallan fuskar Nuhu banasonyi, qazami ne wallahi "

" tashin hankali, kinga yanzu de kijirani, zanje nasamu Malam saimuzo dashi muhadu mu bashi hakuri kinji? Amma kidena kukan nan kinji Baby nah? "ya qarasa maganar cikin sigar rarrashi

" tace to yaya saika dawo "
Daki takoma ta zauna takama carbi tanaja akan Allah yasa Malam yayiwa baba magana 🤣🤣

Aikuwa bayan sallar magrib saigashi sun shigo har gidan shida Salisu, Sultan ma yana ganin su yabisu, sukai cikin dakin Abba, mama mariya tana cikin dakin tareda Abba, tana ganin shigowar su Malam ta tashi tana gaishe shi, yace "mariya, jekiramin Safiyya kuzo tare"

Ta amsa tareda fita, sai gata sun dawo itada umma
Bayan sun zauna Malam yadubi Sultan yace "kai jeka kiramin Nawal"

Salisu yaje ya kirata, tana ganinsu Gabanta yafara faduwa, cikin ranta tana addu'ah Allah yarufa mata asiri, waje tanema ta zauna kanta aqasa

Malam yace"muhammadu yanzu Salisu yaje wajena da wata magana, zakayi auren Nawal, bazan hanaka yimata aure ba, amma Dan Allah abawa yarinya Wanda takeso "

Abba yace" hakane Malam, nan take yazaiyano masa dalilin dayasa yace zai mata auren, sannan yaci gaba da cewa, amma Malam gatanan, ta fadama abinda yasa batasan Nuhun "

Malam yadubi Nawal" jikata fadamin meyasa bakya sansa?

"Malam wallahi Nuhu qazami ne, bayasan tsafta, kuma ni dama

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment