Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

natafi saudia nayi addu'ah akaan Allah yabaiyana min ke, ashe bansaniba kece kike tare Dani, ashe dake nake tare harna bata lokacina wajan kiran Mai zane yazanamin ke, nasan cewa nashiga haqqinki amma pls kiyafemin, yayi qasa da muryar sa yace "kinji?"


Kai tsaye ta jefo masa tambaya a maimakon amsa "dama kana surutu haka?"

Murmushi yayi yace"ina yiwa Ummi, sannan Inayiwa Nawal lokacin da kishinta yakama ni nakira Mai sunan saurayinta nadinga zuba masa surutu akan ya wanke min motocina duk Dan taji haushi 🤣, saikuma Baby nah dazan zauna inyi ta miki zance idan kinaso"

Itama Murmushi tayi, tace "Sai yanzu nagane ma'anar zoben nan guda biyu Wanda aka sakawa kowanne harafin B ajikinsa"

Yace "yes Baffah & Baby, means BB, wato har bincike kikai adakina bayan qone kayan?"

Rufe idonta tayi, da hannunta 🙈tace"kayi hakuri, shawarar qawata nabi "

Yace" nadade dayafe miki Baby nah, yanzu bani labarin mk "

Kafin tafara bashi labarin suka jiyo alamun tafiya a kofar dakin, anqi ashigo amma kuma sai taku ake agaban dakin🤣🤣

Zaro ido yayi😳 yace" Ummi ce wallahi namanta, "yayi sauri yaduro daga gadon
Yanda yasakko din har daria yabata 🤣

Futowa yayi daga dakin aikuwa saiga Ummi a kofar daki tana safa da marwa ta kuma kasa shiga🤣🤣

Ta kalleshi tace" Baffah yadaga baka minti biyar ka shanyani awaje sama da Rabin awa😒"

Kansa ya sunkuyar yace" Ummi kiyi hakuri wallahi namanta 🤣"

Tace" Baffah, Baffah, Baffah nakiraka sau uku kabar yarinyar nan tahuta, likita yamin kashedi cewa abarta tahuta Baffah, karnaji karna gani Baffah 🤣"

Daria ta bashi, wai shine yazama haka awajan Ummi 😀, kansa aqasa yace" Ummi insha Allah bazakiji komai ba "

Tace" to shikkenan, nina tafi da kina, "

Dadi yaji har ransa, yace" to Ummi afuto lafiya" 🤣

Saida yaga tafiyar ta sannan ya koma cikin dakin, a lokacin har bacci yafara fizgarta, Ahankali ya janyo ta jikinsa yace"tashi yarinya ai baki isaba saikin bani labarin mk tukunna "

Ahankali ta bude idonta tace" mk, nikuwa nice Zan baka labarin mk 🤣🤔, in fadama a Sanadin neman mk Babu irin azabar daban shaba🤣"

Nide Tun a asbiti danaji kana magana da Abba nah lokacin daka biya mana kudin aikin idona, tundaga lokacin narasa gane kaina, nide fatana kawai naganka koda saudaya ne arayuwata, gashi baabu idon ganin ka, nasa Najma ta ganomin kai tacemin ai itama bayanku tagani, baabu yanda na iya haka na hakura, damuka dawo daga qasar waje nasamu number ka awajan Doc. Nakiraka a lokacin da aka sakoni agaba agida akan na auri Nuhu, narasa ya zanyi, dole tasa ta nemeka, da nufin in fadama cewa agida za'a bani wani amma inaso kazo kayi magana da Abba nah, akan yabar maganar Nuhu, tunda shi idan yaganka zai ganeka, kuma zaiji nauyin yimaka musu, amma ina kiranka kahauni da fada kace na yiwa iyayena biyaiya, daga qarshe ma kakashemin waya "

Dasauri ya kalleta yace" wai kece? "

Daga masa kanta tayi, yace" Innalillah... Ashe ni a lokacin abnda nadade ina nemane yazo har gida yasameni amma nayi watsi dashi? Kiyi hakuri Baby nah, a lokacin raina yabaci ne, bana amsa waya cikin week end, amma kuma ke kikai takira harkikasa na karya dokata 🤣"

Tace" Babu komai, sannan taci gaba da fadin, banida niyyar in fadawa d'a namiji cewa ina sonsa, amma saboda matsi dana samu agida kuma naga da gaske de za'a Auramin Nuhu, hakanne yasa nake nemanka ido rufe, amma narasa ka, har wataran qawata Nasrin zasuzo Abuja biki itada qanin ta nabiyo ta muka zo da nufin zamu nemo mk muyi masa bayani, har biki yakusa qarewa bamu samekaba

Qarshe de munje wajan dinner na futo waje naga wasu motoci suna wucewa sai naji wasu samari dake gefena suna cewa mk yashigo gari, daganan hankalina yatashi muka tare adedeta mukahau, yace mana bazai hau Babbar hanya ba, duk da haka muka ce mude yabi damu tako'inane, kawai fatanmu mutaro motocin dake gabanmu, wallahi ina fad'ama kawai sai adedeta tafadi aqasa😳🙆🏻daqyar aka ciromu daga ciki🤣

Wata irin daria ce tazo masa wadda bai shiryaba 🤣yadinga daria, ta zuba masa ido tana kallansa, itade tunda take dashi bata taba ganin dariyar saba, ya kalleta cikin daria yace "duk saboda neman mk din ?

Cikin shagwaba tace" shine kakemin daria ko? "
Tafara kokarin juya masa baya, Ahankali yasa hannunsa ya juyo da ita yace" kiyi hakuri nadena, shikkenan? "


Amma please ki fadamin waye yazuba miki shaltos a idonki? "

" wallahi wanine sunansa Anwar, amma ai komai ma yawuce, Tun a lokacin ma nace nayafe masa

Koba haka bama tunda shine yayi silar haduwata da mk ai kaga dole nayafe masa "

" Kamar yaya mekike nufi? "

" haduwa nayi dashi a makaranta, har mukai karo wayata ta fashe, anan nahadu da Ummi, ranar dana fara ganinta kenan, tadinga bani labarin Baffah ahanya, a raina nace gaskiya ta nasan wannan Baffan kowaye "

Jinjina kansa yayi yace" kin tabbatar kin hakuran komai yawuce? "

Tace" na hakura, nayafe masa "

" Baby anya kuwa bazan cutar dakeba? "

" mekake nufi? "

" Baby hakurinki yayi yawa, sainaga Kamar Zan shiga haqqinki azaman da zamuyi nan gaba "

Turo d'an qaramin bakin ta tayi gaba tace" nide Dan Allah kadena wannan maganar, to menene? "

Lips dinta ya kallah, yamatso da fuskarsa zuwa tata fuskar sajensa ya goga mata awuyanta yace" to shknn nadena, ina son lips dinki Baby, yana birgeni sosaai, arayuwata ina son baqar mace, amma zuwanki cikin rayuwa ta ya sauyamin komai, i luv u"

Tace"nagode "

" ba godia zakimin ba "

" tome zanma? "

" abinda mata takewa mijinta idan yace yana sonta "

Tace" menene abin? "

" in nuna miki? "

Daga masa kai tayi alamun eh,
Yace" to rufe idonki "

Babu musu tarufe idonta
Yana ganin haka yadora bakinsa akan nata
Dasauri ta bude idonta tareda qwace bakinta cikin shagwba tace" Allah nifa akwai zafi pls kabari "

Shagwabar tata tabirgeshi sosai, wai irin dadi yakeji aransa, daga qarshe de ga Baby Akwance a qirjinsa 🤣

Batare dayayi mata magana ba yayi Murmushi kawai tareda cigaba da abinda yafara



*** ***** ***



"haba bawan Allah, ya kana ganin mutane da kaya niqi-niqi ahannu amma katsaya akan hanya duk ka babbake wajan, idan baka temaka ka karba ba, aibaka tare hanya bako? 🤔

Tab to aishi Tun dazuma dayake Kallanta daga nesa baisan harta qaraso wajansa ba🤔🤣

Ajiyar zuciya yasaki yabata hannu yace"tokawo kayan "

Tace" A a, Barshi wallahi, dama kawai hanyar nake buqata"

Kai tsaye yace "to shikkenan, ga hanyar nan zoki wuce 🤣"

Cikin mamaki ta kalleshi,tace"wannan irinku ne bakwa yiwa mutum kara 🤣🤣
Inba hakaba daga cewa kabarshi saikace ga hanya nan? "

Yace" hanya kika nema, kuma nabaki, nace kikawo kaya na kince a a, danhaka ga hanya nan, kaya kuma idan kin gaji ki ajiye daya anan, idan kin kai guda dayan saiki dawoki dauki wannan din 🤣🤣"

Kafin tayi magana Nura yazo wucewa yace" yaya Najma wannan kayan kinfi minti talatin akansu🤣

Tace "to Nura ya zanyi?"

Nura yace"ke komai sai anmiki "🤣


Yakalli Yasir dake tsaye agefen ta ya bashi hannu suka gaisa
Daga nan yayi gaba yabarta anan, dama suna qarasa debe kayan gidan ne suna kai wasu maqota


Shima yasir ya kalleta yace" wallahi kuwa, injunin mutum san jiki ai saiyayi, nima kinga tafiyata nan🤣🤣"

Duk suka watse suka barta awajan, bayansa tabi da kallo ga mutum de har mutum amma ba zuciyar taimako, 🤣ta girgiza kanta taja kayan tayi waje




*** ***** ***



"Ummi Albishirinki"

Tace "goro Baffah"

"Ummi Nawal fa itace Baby nah"

"bangane ba Baffah me kake nufi, wacce Babyn taaka?"

"Ummi Baby nade danace miki ni ita nakeso, ita nake nema, ita nakeso nagani na aureta, kikace Idan naganta saina aureta daga baya"

"Baffah, kasan banasan qarya ko?"

Yace"Ummi da gaske nake wallahi, gatanan ki tambyeta "

Ummi ta kalli Nawal tace" yata wai hakane? Garin yaya hakan tafaru? "

Kafin Nawal tace wani abu yafara bata labarin komaai, har zuwa yanzu dakuma binciken dayasa yasir yayi masa akanta

Ummi tasaki ajiyar zuciya tace" ikon Allah, Baffah kaga amfanin biyaiyarka agareni ko? Amma Awannan ranar bana mantawa haka ka zauna kanata min kuka wiwi🤣

"haba Ummi Dan Allah, adinga tone tone dai 🤣

Tace" to alhmdlh, gaskiya nafi kowa murna wallahi, ubangiji Allah yaqara hademin kanku, yabaku zuria tagari nima naga yara agabana sunata wasa, har gidan namu yayi kyan gani, suzo suna cemin Ummi bamuda biro, Ummi book dina yacika asaimin sabo🤣"

Nawal najin haka tatashi Dasauri tayi cikin dakinta, cikeda kunya 🙈


Haka zaman su agidan Ummi ya kasance, koda yaushe tana samun kulawa awaajansu, Ummi bata sanya wajan gyarawa Baffah matarsa🤣, babu ruwanta da wata kunyar surukai, kawai jin Nawal din take Kamar 'yarta, kwananta uku ta warke ras, batajin ciwon komai, haka kuma har zuwa wannan lokacin Babu abinda yaqara shiga tsakanin ta da mk, domin kuwa Ummi takafa ta tsare

Akwana na hudun ne suna zaune a dakin Ummi dukansu, tace "Ummi inaso naje gida Dan Allah"

Ummi tace "haba Nawal, gaki ga mijinki, aishi zaki tambaya"

Juyawa tayi ta kalli Baffah tace "Dan Allah kaji?"

Cikin damuwa yace"yaushe ma akai auren dazaki fara fita? 🤣🙆🏻

Kawai kiyi hakuri next time sai Muje

Kamar zatai kuka tace "kaifa rannan kaje, Dan Allah kabarni naje kaji mai Babban suna"

Yace"naji, amma kwana biyu zakiyi kidawo, inba hakaba Zan biyoki "

Ummi ta kallesu a boye,taga alama sauda dama suna mantawa da ita awaje 🤣
cikin ranta tace oh ni Halima ina ganin duniya, aikuwa idan kuka dawo din saide ku wuce gidanku 🤣

Nawal kuwa cikin murna tace" yawwa Baffan Ummi nagode "

Yace" keko Hmm "

Murmushi tayi masa tareda hararar wasa, duk Ummi tana ganinsu, saide kawai yi tayi Kamar batasan mesuke ba🤣



Washe gari kuwa Ummi da kanta ta shirya mata tafiyar, tasiya mata kayaiyaki dayawa Kamar su yadi dasu shadda Wanda zata rabawa mutane, dakuma Wanda zata kaiwa yan gida, cikin sanyin jiki oga yarakata Airport da kansa tareda direba
Saida jirginsu yatashi zuwa kano sannan suka koma gida, ahanyarsu ta zuwa gida yakira yasir yace, atura mata motoci suje Airport su dauketa idan tasauka saisu kaita gida

Haka akayi kuwa, motoci hudu yasir yatura mata, Kamar wata matar Governor
Jirginsu nasauka kuwa suka dauki komai nata suka saka amotar, tana ganin haka tasan aikin Baffah ne

Kai tsaye gidansu suka nufa, amma suna zuwa layin gidan taga anrushe gidan anata aiki sosai, mamaki ya kamata, tacewa direba ya dakata daga nan kawai, basai sun qarasa kofar gidan ba, saboda Babu Inda Mota zata shiga

Umarninta yabi, ya dakata tasaauka, sannan suka biyo bayanta da kayaiyakin datazo dasu

Kamar wasa taganshi agaban ta, a yatsine ya kalleta yace "kaga yar Malam Shehu ansamu abinda akeso sai wani abu kike Kamar yar wani"

Murmushi tayi masa kawai tawuceshi batareda tace masa komai ba

Daya daga cikin direbobin da suka kawo ta yace, "Hajiya mekike buqata ayi masa?"

Tajuyo tace "ku rabu dashi Babu komai"

Shima cikin kuri yace "yoda meta isa tamin? ubana yana tsaya min akan komai, Mai unguwa saleh dogo"

Suma basu kulashi ba suka bita suka ajiye mata kayan ta, tareda Juyowa, su nura suna ganinta sukayo wajanta cikin murna


Su kuwa direbobi suka komawa wajan Mota, Wanda yadauko Nawal kai tsaye yakira mk awaya ya sanar dashi komai

Cikin bacin rai yace"shine yace muku shi yaron Mai unguwa ne? "

yace" yes Sir,namaji wani agefe ya kirashi da suna Anwar "

Ransa yaqara baci, matar tasa za'a ciwa mutunci? Kai tsaye yace" Am kanajina ko, ku dauko min shi kukawo shi Abuja yau "

Cikin ladabi yace" Angama Sir "tareda kashe wayar













(yau kam anyi typing 😇)















Amnah El Yaqoub ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


41&42



Bayansa sukai tabi batare dasun kamashi ba, har saida sukaje layin gidansu,yana tsayawa maigadi yabude masa get zai shiga suma suka futo suka kamashi, dayake qarfafa ne nan da nan suka dagashi samah zuwa cikin motar su 🤣

Maigadi yace "Innalillahi, bayin Allah meyayi muku?" 🙆🏻‍♂Yakalli Anwar yace" kai Anwar mekayi musu? "

Cikin fada yafara cewa" dalla ni kusakeni, ku ajiye ni nace"!!

Basu kulashi ba kawai suka dannashi cikin Mota, driver ya kalli maigadi yace"Baba muma umarni aka bamu daga sama mutafi dashi "
Yana fadar haka ya shige motar, baba maigadi yabisu da gudu yace" Dan Allah ku tsaya, ku fadamin ina zaku kaishi? "

Wanda yariqe Anwar ya leqo yace" Wajan mk "

Baba maigadi yace" wanene kuma mk? Kunawa Allah ku sauko da yaron nan, "

Batare dasun saurareshi ba sukaja motar aguje sukabar wajan
Shima yadora hannu aka🙆🏻‍♂ yayi cikin gida yana qwalawa hajiya kira.



*** ***** ***



Ta kalli Saif tace"kai yanaga gidan duk ya haukace da gyara? Yaushe aka fara gyaran gida? "

Yace" au wai dama baki saniba? Naga mijinki ne yaturo ayi aikin "

" mijina kuma? To yaushe? Ni wallahi bansaniba kuma kaga shima bai fadamin ba "

" aikuwa Tun ranar dayazo washe gari akazo akaga gidan da irin gyaran da za'ayi masa "

Dakatawa tayi da tafiya tace" to yanzu ina zamu zauna? "🤔

Nura yace" kede kitaho mana, gashinan angama bangaren mama, anan muke kwana, amma Babu komai aciki, kawai sai kaya da katifu, sauran kayaiyakin suna maqota "
Tace" Ok yanzu naji batu"

Suna shiga gidan Najma tataho da gudu suka rungume juna, mama mariya tace"Baby mutanan Abuja sannu da zuwa "🤣

Tace" yauwa mama, ina wuni "

" lafiya kalau Nawal, saiki kazo kuma kika ganmu kaca kaca ana maida mana gidan namu na 'yan gayu "🤣

Murmushi tayi kawai, tafada jikin ummah

Ummah tace" to Allah yakawo mu kuma, shikkenan ke kullum bazaki girma ba Nawal"

Tace "Ummah na dade banganki ba, ina yaya Salisu? Yaya Sultan yaje rannan, har kaya yakawomin"

Ummah tace "to naji Baby, dagani kije kici abinci kihuta"

Najma tace"wallahi kuwa, tashi Muje "
takama hannunta suka wuce daki

Suna zuwa takawo musu abinci sukaci, Tun kafin su gama cin abincin takira Nas tace mata tazo, aikuwa nan da nan tace gatanan zuwa

Bayan sun gama cin abinci, tatashi tayi sallah


Bata dade da idar da sallah ba Nas tazo, anan suka baje kolin fira

Nas ta kalleta tace"Beauty gaskiya yanzu ne kike a Beauty, kin wani qara haske da cika, menene sirrin ne, me mk din yake baki? "

" Hmm mezai bani kuwa banda kulawa, ko daki natafi to shima saiya bini, wani lokacin har kunyar Ummi nakeji "

Najma tace" gaskiya dole kiji kunya kam, bazaka sakeba, amma Baby dakika samu labarin shine mk wanne irin murna kikai kekuwa?

"Najma kenan, kuka nai tayi naqara godewa Allah, saina tuna lokacin danake kuka nake cewa ni bana sonsa, ke Awannan lokacin innasan mk ne har aji kaina? Ai gyara kawai za'a fada"

Daria sukasa gaba dayansu, Nas tace"to yaya labarin makaranta?
Nasan zai barki kici gaba"

"uhm bazan d'orawa kaina ba Nas, nasan bazai barni ba, idan nace zai barni ma tona yaudari kaina"

"Amma mutum kamarsa yakamata ace yabarki kinyi karatun ki, tunda yana shiga waje dadama, sannan yahadu da mutane dayawa, kinga idan kinyi karatun ki Kema zaki goge mijinki yashiga dake ko'ina"

Tace"Nas kenan, bakisan kishin mutumin nanba, kafin yagane cewa nice matar da yakeso, watarana yajini ina waya da ummah nake cewa ni dama Nuhu na aura, wallahi Nas haka mutumin nan yasamo sabon Mai gadi maisuna Nuhu, yadinga saka shi aiki, kuma sai yazo kaina ya tsaya zakiji yace Nuhu zonan, Nuhu yi kaza, Nuhu yi kaza, Yaya Sultan dayakaimin ziyara ashe yaganmu, wallahi cikin dare ina bacci yatasoni waina fada masa inane gidansa yakaini can 🤣kiji fa wata masifa, cikin dare wallahi "

Me Najma da Nasrin zasuyi inba daria ba, Najma tace" tab lalle kice kunashan drama agidan nan naku, Inda nice wallahi ce masa zanyi ga gidan can agaba, muyita tafiya muna zagaye gari zuwa asuba saimu koma gida 🤣"

Tace" A a cemasa nayi yaya nane, shine kuma daga nan yasakko "

Nas tace" tab, a a to me wannan Baqin kishin bazai barki kiyi karatu ba, saide Inda rabo, "

Tace" hakane kam, zan fara lallabashi da zancen harya amince wataran "

Najma tace" wayaga boy, saikace wani jariri saikin lallabashi ma sannan? 🤔

Daria tayi tace "to Najma zauna nan ina zaune wata tazo ta qwacemin shi, Dan Allah idan Zan tafi kubini Muje ko sati daya ne kuyi min"

Atare suka hada baki sukace "sati? 😳

Nas tace" bada niba, ba zanje idona ya makance ba, dade baku gane juna bane sai Muje "

Tace" haba Dan Allah, baku taba zuwa bafa, kuma nima yanzu ina gidan Ummi "

Najma tace" kema Baby kinsan Abbah bazai yardaba, ina laifin ma kwana biyu "

Tace" gaskiya a a kwana uku ko hudu"

Suma sukace saide kwana biyu, dole haka ta hakura tabarsu a kwana biyun "



*** ***** ***


"yarimah dafatan kashigo qasar"

"eh nashigo dazu mk"

"Alhamdulillah, akwai wani Yaro danake so akawoma shi, bashida hankali ne, shine nake so kakaishi Barikinku 🙆🏻‍♂akoya masa hankali"

"Kamar ya? Me kake nufi?" bangane akoya masa hankali ba "

" to idan yanada hankali ai bazai taba Baby naqyaleshi ba, shiyasa nace Zan turo maka shi "

" Baby BabyBade wannan yarinyar dakake mafarkin ba? "ka ganta ne?"

Yace"itafa Nas, naganta, kai itace ma yarinyar da Ummi ta aura min bansaniba lokacin inayi Dubai, labarin de da tsawo Nas "

" Ok to mk Babu damuwa, katuromin shi muga ko zai samu hankalin cikin yini daya" 🤣😢

Yace"Ok Nas,"



*** ***** ***



"yanzu Alhaji kazo ka zauna kayi tagumi baka dauki wani mataki ba ahaka kake tunanin zai sakar mana yaro?"

Hon. Mai unguwa saleh yadaga kansa yadubeta "hajiya yaya kikeso nayi ne? Na tabbatar akwai abinda Anwar yayiwa mk inba hakaba bazai kamashi ba, sai yau nayi DANA SANI akan turbar dana dora yaron nan, abinfa zai iya shafar siyasata"

"to yanzu Alhaji kai kana zaune, kamata yayi katashi kabi jirgi kaje ka bashi hakuri yasake shi, Alhaji karsu kasheshi ko suyi masa wani lahani"

"hajiya ba zuwanne matsala ba, kunyar hada ido nake da yaron, saboda yana ganin mutuncin kowa duk da cewa shine gaba damu"

"to yanzu Alhaji yaya za'ayi?"

"yanzu dare yayi hajiya, amma gobe Zan shirya dasafe sai naje naganshi"

Tace"to Allah yasa adace, Allah yasa ba wani abu suke masaba, kai wannan masifa dame tayi kama "😊



*** ***** ***





Da daddare bayan ta kwanta kasa bacci tayi, kawai tunanin sa take yi, jitake idan bataji muryar sa ba Kamar bazata iya baccinba, har wajan sha daya shiru bai kirata ba, ita kuma batada number sa, haka takira Ummi suka sake gaisawa a wayance ko Allah zaisa yana gida amma haka sukai sallama da Ummi ma batayi mata maganar saba
Haaka de tayi addu'ah ta kwanta, amma zuciyarta fal da tunanin mijinta


Shima a nasa bangaren tunanin ta yake, amma yana tareda yarimah Nasir ana gwadawa Anwar hankali, suna zaune a gefe suna fira, yayinda ihun Anwar sai tashi yake, amma ko ajikinsu

Sai wajan sha biyu saura yace "arabu dashi, shima saboda ya bashi tausayi ne yaron, duk kamarsa ta kauce, yasha wahala sai nishin azaba yake

Awajan yarimah Nasir yabarshi shikuma yayi gida, bayan ya kwanta yakira layin ta, a lokacin sha biyu da rabi, na dare, tayi bacci, saida yayi mata 7missed call amma bata jiba, haka ya kwanta cikeda damuwa

Da asuba tana idar da sallah tadauki wayarta taga kira har sau bakwai, ta duba number taga ansa muhammadu 🤣, cikin mamaki tace "muhammadu kuma? To waye yayi min saving number da muhammadu? Wata zuciyar tace kode mk ne? Kai tsaye tunanin ta yabata gaskiya, danhaka ta kirashi

Yadauka cikin Shagwaba yace" Baby nah shine kika qyaleni jiya kikai baccinki ko? "

Murmushi tasaki, cikin ranta tace ashe shine,afili tace" lokacin daka kira nayi bacci ne wallahi, amma kayi hakuri kaji me Babban suna? "ta qarasa maganar cikin sigar lallashi

Yace" naji, amma ki fadamin kinyi mafarkina? "
Tace" A a banyiba, kaifa? "

" Baby haka kawai ma ina mafarkin ki bare yanzu, ai kinsan dolene "

Tace" nima nayi mafarkin ka yau "

" da gaske? To fadamin naki "

" nayi mafarki kana kwance aqirjina "

" wayyo Baby Allah zakisa nabiyo ki yau "

" lala lala, kazo ina? Kayi hakuri nima fa gobe ne Zan dawo"

"to Baby duk kece ai kika rikitani, kinga gara nazo na tabbatar miki da mafarkin ki," shagwaba yafara yi Kamar ba mk din data saniba, "uhm uhm Baby nide kawai kisan yanda zakiyi Dani Allah kuwa kokuma ki Ganni"

Murmushi tayi tace"to ta yaya Zan iya yima wani abu bayan bama tare? "

" idan muna tarema nasan bazaki iyamin komai ba, bayan rannan ma haka kika cikamin kunne da kuka, har masu aiki kike kira"

Cikin shagwaba tace"toba kaine ba"

Yace "to naji, tuba nake, nasan yanzuma kin warke, ina yan biyu nah?

" Kamar ya? "

" Ok bakisan yan biyu ba? "

Tace" bansani ba, suwaye yan biyu "

" toki bari idan kindawo saina nuna miki su "

" um um Dan Allah ka fadamin "

Yace" gasunan ajikinki, masu laushin nan "

Cikin sauri ta rufe idonta, tace ka kwanta kayi bacci saida safe, dif takashe wayar
Shima Murmushi yayi tareda rungume wayar ya koma bacci yana jin Kamar itace atare dashi



*** ***** ***



Zaune suke afalon baqi, su su biyu, baqar jallabiya ce ajikinsa da alama yanzu yatashi daga bacci
Yadubi Hon. Yace" Mai unguwa naji abinda yake tafe dakai, kuma insha Allah zansa asaki danka, but bani yayiwa laifi ba, Mai dakinace, kuma batanan tayi tafiya zuwa kano, sai zuwa gobe ne akesaran dawowar ta, saide kadawo gobe kabata hakuri idan ta hakura shikkenan saika tafi dashi gida, sannan kuje kubawa iyayen ta hakuri 😳🤣

Hon. Yace "Babu damuwa wallahi, a hakanma mune da godia 🤣, nagode sosai ranka ya dade, insha Allahu goben Zan dawo, shima saiya tsugunna har qasa yabata hakuri"

Mk yace"shikkenan zaka iya tafiya "

Hon yasake godia sannan yafuto daga falon yana tunanin irin wannan karfin iko na mk, bashi akaiwa laifin ba sannan ita wadda za'a bawa hakurin bata nan saida dawo, ya naji yana gani de baza'a saki yaron nasaba harsai tadawo kenan 🤔🤣

Haka de yagama zancen zucinsa yawuce wani wajan da nufin goben zai sake dawowa



*** ***** ***



Kamar yanda suka tsara washe gari kuwa tayi shirin dawowa Abuja, wannan karon ummah da kanta tabata magungunan sanyi dakuma daka, Wanda zata dinga sha da madara, Tun awajan tahada wani tasha da kanta 🤣
Ummah ta girgiza kanta, wato yanzu dayake tanason mijin shine Tun kafin atafi akasha wani, ta kirashi awaya ta sanar dashi zataje gidan Malam suyi sallama kuma zata tahoda Najma da Nasrin, yace Babu damuwa zaisa yasir yayi musu duk abinda suke buqata

Tana zuwa gidan Malam bayan sun gama gaisawa tace masa ya temaka ya yi mata rubutu Wanda zata bawa Baffah yasha, akan Allah ya dauke hankalinsa dasaka wannan kayan, dama duk wasu sauran halaiya Wanda basu da kyau

Malam yace gaskiya wannan tunani ne Mai kyau, tana zaune yayi rubutun yabata, sannan tamai sallama tatafi

Sai wajan azahar sannan yasir yazo daukar su, saitaji Kamar kartabar gidan, amma haka sukai sallama dakowa

Kai tsaye Airport yakaisu, Najma sai baza ido take zata shiga jirgi, Yakalleta yace "basa banba, yau kuma munga ta kanmu" 🤣🤣

Tace"wallahi kuwa, saide mutum ya dauke idonsa idan bayasan gani"

Yace"mukuwa ina zamu dauke ido, ai gara mukalli rabonmu "

Kallansa tayi kawai tareda girgiza kanta

Acikin jirgin ma haka sukai tayi, yafad'a tafad'a


Har suka sauka lafiya gidan Ummi, cikin jin dadi tataresu, tagabatar musu da abinci, yasir ya kira mk ya sanar dashi cewa sun qaraso

Basu dauki lokaci Mai yawa ba sai gashi sun shigo falon tareda yarimah Nasir, dakuma Anwar harda Hon.

Nawal tana ganinsa cikin ranta tace ikon Allah, kaga wani Kamar Anwar 🤣🤣

Zama sukai akujerun falon mk ya nuna wa Hon. Nawal yace, "Mai unguwa ga wadda yayiwa laifin nan yaje yanemi yafiyarta"

Tun kafin Hon yayi magana sai ganin Anwar sukai agaban Nawal yana bata hakuri 🤣

Ummi dake gefe tace "A a wannan ba shine yaron daya jefar miki da waya a school ba?"

Cikin sauri yace "nine, nine wallahi 🤣
Kuma insha Allah nayi alqawarin Mai kama da itama bazan qara kallah ba"

Itama Nawal din Murmushi tayi, tasan cewa gaskiya jikin Anwar yayi la'asar 🤣tace"babu komai na hakura "

Mk yace" to shikkenan Mai unguwa, zaku iya tafiya, but kada kamanta de kaje dashi har gida kubawa iyayen ta hakuri, shi yaron naka yasan laifukan daya aikata mata "

Hon yace" angama yallabai, insha Allah ba zamuje gida bama sai munje munbasu hakuri "

Daga nan yace zasu

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment