Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanbaka kulawa fiyeda wadda zata baka"

Yace "kinyi alqawarin hakan?"

Tace "insha Allah"

Ajiyar zuciya yayi, gefen kansa nayi masa ciwo, kuma yasan hakan baya rasa nasaba da wayar da yayi da Nasrin, fatansa daya Allah yakawo masa agaji



*** ***** ***


Kusan sau shida yana gwada kiranta amma yakasa, dazaran yayi dialing number saiya katse 🙊🙆🏻
Cikin ransa yace to kode tsoron yarinyar nan nafara ne? Tun dazu nakasa kira? Koda yake abinda nayi matan ne Kamar ban kyauta mata

Dakewa yayi yafara kiranta a karo na bakwai, a lokacin shabiyu saura amma idonta biyu, tarasa wazata fadawa damuwarta taji dadi, tayi kiran Nawal amma bata sameta ba
Adede lokacin wayarta tafara qara, tana ganin number taganeta, tashare taqi dauka
Yasake kira, still bata daukaba sai akaro na uku sannan ta dauka tayi shiru

Shima yana jin haka cikin ransa yace to tasamu labari kenan 🤣

Kwanciya yayi akan gadon yace "Zumata" 🙊🤣

Tanajin sa tayi shiru, shima yasake cewa "Zumata dake nake fa kinyi shiru"

Zuciyarta ta karye, dab take da fashewa da kuka, cikin rawar murya tace "mezan maka kuma?"

Murmushi yayi yace "kiyi hakuri Nas, nasan nayi miki laifi, amma ga yarimah yana neman tuba awajan ki, Nasrin ina sonki, inaso kibani dama na nuna miki yanda nake jinki acikin zuciyata, Nasrin nazo har gida domin nasamu hadin kanki amma kinqi bani wannan damar, shiyasa na turo su, amma kiyi hakuri, yanzu ma idan kina buqatar nasake tsugunna miki saina sauka daga kan gado na nemi yafiyarki, "yana gama fadar haka yafara kokarin Saukowa daga gadon

Tanajin motsinsa ta cikin wayar, Ahankali ta fashe da kuka Wanda bata samu tayishi yanda takeso ba dazu

Yana jin kukanta yadafe kansa 🤦🏻‍♂yace" nashiga uku, wai ke bakya jin rarrashi ne 🤣? Adinga yimiki magana daya? "

Tanajin ya hauta da fada ta tuno yaya Sultan, shide baya yimata tsawa ko kadan
Aikuwa saita sake rushewa da kuka 🤣

Girgiza kansa yayi, ya gyara muryar sa zuwa ta lallashi yace "Nas, Dan Allah kiyi hakuri kinji tawan?daga yau yarimah bawanki ne sai yanda kikai dashi, kidena kukan kinji Zumata?"

Ahankali ta rage sautin kukan nata, harta daina duka, sai ajiyar zuciya take

Cikin ransa yace tab akwai aiki agabana kenan🤔🤣🤣

Saida yaji tadena kukan gaba daya sannan yace" nine nayi miki laifi ko? "

Tace " um"

Yayi Murmushi yace "to na daina kinji?"

Ta daga masa kai Kamar yana ganinta
Yasake cewa " kinyi addu'ah?"

Tace "um"

Yace "to share hawayen Zumata Tun kafin nazo na share mikisu da baki na"

Maganar sa tabata kunya, amma saita share sanin cewa shidin Dan duniya ne

Dayaji shiru yasake cewa "kin share?"

Tace "um" 🤣


Yace "to shikkenan, saida safe ki kula min da kanki Zumata muachhh 💋"
Yasakar mata kiss ta wayar
Cikin sauri ta kashe wayar, tana Tambayar kanta dama haka yake 😱?ana ganinsa sumi sumi da shegen iko ashe haka yake? 🤣

Shima a nasa bangaren Murmushi yayi, yanzu de dole ne yakoyi lallaba mace kenan🤔
Shida ake lallabawa anayi masa biyaiya yanzu saide yayiwa wata 🤣




*** ***** ***


Kayan bacci ne ajikinsu Wanda ake kira dashi da Babu...
Tana kwance ajikinsa bacci na neman daukarta , yayinda yake shafa gashin kanta, wayarsa tadauki qara

Dauka yayi tare da cewa "yarimah ya ake ciki?"

Yarimah yace "mk anwuce wajan ai"

Murmushi yayi yace "congrats angon Nasrin"

Tanajin haka tafara kokarin tashi daga jikinsa, yamaidata yahanata tashi 🤣
Saida yagama wayar da yarimah sannan Yakalleta yace "ya akayi Baby nah?"

Tace "kaifa nagama ganeka, na lura kwata kwata bakasan yayana da Nasrin, yanzu haka nasan dasa hannunka aciki"

Murmushi yayi yace "Baby nah kenan, Baby bazaki ganeba qawarki tanada hankali, yayanki yana nutsuwa, sabanin mu, mun tashi cikin mutane daban daban har hakan yasa wani lokacin mutum zai kauce hanya, yarimah nasan yanmata sosai, amma baso na aure ba, yanzu daya samu qawarki sai kiga adalilinta yadena wasu abubuwan, Kamar ni dakika hanani zane ajikina kika hanani saka kayan dabasu dace ba "

Kallansa tayi tace" kana nufin ka dena? "

" qwarai kuwa Baby nah, bana ra'ayin su yanzu, kwata kwata ma basa cikin raina, nasan ummu da sauran yan'uwan mu zasuji dadin hakan "

Cikin murna tace" Alhamdulillah Allah na godemaka "ta rungume shi a jikinta sosai

Kissing din kumatunta yayi yace" Baby na irin wannan runguma haka ai saiki sa nasaki layi "🤣

Itama kissing din nasa kumatun tayi tace" nikam yanxu bacci nakeji, kabarmu muyi bacci Dan Allah, yauwa yaushe zamuje gida? "

Wata irin daria yayi yace" keda gida ai saikin samu ciki "🤣

Cikin sauri tace" ciki? "

Yace" emana, anufinki haka zamu komawa Ummi Babu tsaraba?"

Tace" to bagara Muje mudawo ba, wayasan ranar yin cikin"

Kallan qirjinta yayi sun wani qara girma sa cikowa, ga shegen baccin datake yi kullum, yasan cewa yanzu haka tanada ciki,yakai hannu kan qirjinta yajanye rigar yace "Baby nah meyasami yan biyu nane naga sun qaru"

Kallan hannunsa tayi yana matse mata jiki yana wayance wa da tambayarta 🤣tace "wallahi nima haka nagani, Tun dadewa naga sai qaruwa suke"

Murmushi yayi yace "kode bakida lafiya?"

Tace "A a ni qalau nake"

Yasake cewa "yaushe zakiyi period ne Baby nah?"

Saida ta tayi shiru alamar tunani 🤔sannan tace "Tun last week yakamata ace nayi, amma banga komai ba, amma kasan wani lokacin dama yana haka idan zai sauya time"

Daria ce ta kamashi, shikkenan yasamu amsar da yakeso yace "to Allah yakawo shi lafiya"

Tace "Amin, ya maganar zuwa gidan?"

"nafada miki saikin samu ciki zamuje" 🤣

Shagwaba tafara yimasa tace "cikin daba rana, Dan Allah Muje ko sati daya ne muyi kaji"

Cikin wasa yace mata "aikuwa ciki Babu rana, shikkenan Baby kema Ummi ta shafa miki, haihuwa daya zakiyi shikkenan, 🤣🤣, itama dayar ba yanzu ba tunda gashi har yanzu Babu cikin"😃













(jiya banida charge kunjini shiru, Pls kumin uzuri kuna raina wallahi,🙏🏻)









Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek

55&56


Murmushi tayi ta maida kanta jikinsa tace "Allah Babu ruwana nikam banceba"

Yace "aikuwa ko munyi waya da ita idan tacemin yaya Nawal de har yanzu shiru, zan fada mata kince tashafa miki"

"wallahi Babu ruwana, karma kasani aciki"

Yayi Murmushi yace "nima wasa nake miki Baby nah, amma gaskiya gida ba yanzu ba, saikin fara zuwa makaranta tukunna, idan kuka samu hutu sai Muje"

Kallansa tayi "wai Dan Allah da gaske kake?"

"da gaske nake mana, zaki fara karatu insha Allah"

Tace "kai Alhamdulillah Allah na gode maka, yaude kana bani abubuwa masu dadi, kace kadena saka kaya, kadai na yin zane ajikinka, gashi kuma yanzu anyi min maganar makaranta"

Yace "hakane kam Baby, kwata kwata basa raina, nima hakan naji, amma tsaya nabaki waani abun dadin yanzu"

Tace "Aaa naqi wayon"

Yace "please"

Tace "naji amma kadan"

"nayarda Baby nah" kafin tayi magana yafara aika mata da saqo



*** ***** ***



After 3 weeks

Tun Nawal tana zuba idon ganin period harde tagaji tahaqura, ta zauna tana tunani ance idan mutum baiga period dinsaba tofa yanada ciki, jikinta yayi sanyi, yanzu itace zata haihu? Tareda mk?
To amma kuma ita bataga wata alama datake tareda ida ta masu ciki ba, ita ba amai ba, ba laulayi ba, saide kawai baccin datake yawan yi Kamar Mai cutar bacci, Dan haka ta yanke shawarar yimasa magana dazaran yadawo daga wajan aiki


Da daddare yana dawowa tayi masa, bayanin komai yace "nifa na dade da sanin Baby nah tasamu ciki"

Kallansa tayi tace "Amma shine kaqi fadamin kaketa tsokana ta? Duk Dan karnaje gida?"

Yace "wallahi, Dan nafison saiya futo sosai sai Muje, irin haihuwa yau ko gobe din nan, saboda ko Ummi ma naqi sanar da ita, nasan cewa ina fada mata zatace namaidake, nikuma banaso mata ta tayi nesa Dani"


Tace "kuma yanzu saboda zuwa gida sai kaqi fadamin? Bayan kuma kasani? Yanzu de Dan Allah kayi hakuri Muje, wallahi nayi missing, nasan itama Ummin idan ba fada mata mukai ba, bazata ganeba,"

Yace "ita Ummin? Zata gane mana, yanzu de ki zaba komu tafi saudia kokuma mutafi Nigeria"

Cikin sauri tace "gaskiya nafasa gidan, nazabi saudia, gidan wataran maje" 🤣



*** ***** ***



"Najma Kamar yaushe kikega yakamata ace na turo maganar bikinmu?"

"um ina ganin idan nakusa gama makaranta ma yayi"

"haba tawan, kullum saide na kwanta na rungumi fillo? No bazai iyuba, gaskiya kisake mana wata shawarar"

"to idan nayi rabi"

"kinga aure baaya hana karatu, gashi Nawal ma zata fara nata karatun kuma da auren ta?, Pls kibani dama kawai na turo"

Saida ta danyi jimm 🤔sannan tace "to shikkenan idaan ka shirya saika samu Abba kuyi magana"

Yace "Alhamdulillah kokefa, kinga nima yanzu ai naji qamshin angonci" 🤣

Hararar wasa tayi masa sannan sukaci gaba daya firarsu gwanin sha'awa



*** ***** ***



Nasrin ta daina fita ko'ina, dededa maqota masu kula da ita basa barin ta taje, kullum cikin gyarata suke
Suna kuma qara koya mata abubuwan da bata sansu ba Wanda suka shafi masarautar gombe

Ayayinda Nasiru iko🤣yake qara cigaba da bawa zumar tasa kulawa, Dan dole tayi hakuri ta kwantar da hankalin ta, tunda shima yasakko yabada kai



*** ***** ***



Cikin satin mk ya shirya musu tafiya umarah shida Nawal, abinda yabata mamaki shine suna zuwa saudia taga ummanta da Malam da mama mariya da Abba, dakuma matar Malam wadda yake aure a yanzu saboda wadda ta haifi Abba ta dade da rasuwa

Abin yayi mutuqar bata mamaki, itakam wanne irin so mk yake mata? Mutum biyar, duk a dalilin ta, lokaci daya taji sanshi yaqara ninkuwa acikin ranta, taji Babu abinda zai nema awajan ta ta hanashi mutuqar bai sabawa shari'ar musulunci ba

Kasa yimasa magana tayi, saide yinin ranar Haaka tayi shi tareda ummah, Inda ita kuma ummah batayi qasa agwiwaba wajan qara Jan hankalin yarta akan kyautatawa miji

Sai dare,sunyi shirin kwanciya shikam harma yafara bacci ta kalleshi tayi Murmushi, kullum ita yake tashi idan tana bacci, Dan haka itama yau shi zata tasa

Kansa tafara shafawa tace "MK" 🤣

Cikin bacci yabude idonsa yace "sunan dakika sakamin kenan?"

Tace "no, sunanka ai daban yake, kai haske ne Wanda yake haskaka cikin zuciyata, daga yau katashi daga Mai Babban suna kakoma nurul qalb,mk kuma kawai inajin dadi ne duk lokacin dana furta sunan abaki dakuma zuciyata"

Murmushi yayi, yajanyota jikinsa yace "inajin ki, fadi maganar ki Baby nah"

Tace "dama godia zanyi ma, akan abubuwan dakamin, bansan wacce irin zuciya garekaba

Kanada zuciyar taimakon mutane, Wanda kasani da Wanda baka saniba, mekake so na mallaka maka shi a wajena, ka fadamin duk wani abu da kakeso a wajena, insha Allah zanyi makashi inde ina dashi "

Lakace mata hanci yayi yace" zuciyar ki, ita kadai nakeso awajan ki Baby nah "

Tace" shikkenan? "

Yace" yes ita kadai "


Tace" ka dade da samu, Tun kafin nasan waye mk na mallaka masa zuciyata "

Yace" nagode amarya kuma uwargidan mk "daria sukasa dukansu, yaja musu bargo suka kwanta



*** ***** ***



Bayan dawowar su daga saudia su Abba suka dawo gida yayinda Nawal da mk suka koma Dubai, yana cigaba da bawa cikin ta kulawa, kuma har yau basu fadawa kowa tanada ciki ba, kawai so suke subawa mutane mamaki


Sahla tunda taji ana shirin sakawa yayan ta rana tafada wa maman su itama akwai wanda takeso, mahaiyarta bata dauki Tsawon lokaci ba ta sanar da Mai martaba, shikuma yabata dama cewa ta sanar dashi idan da gaske yake yaturo magabatansa

Lokacin data sanarwa da Sultan shima baiyi qasa a gwiwa ba yafadawa su Abba
Abba ya Jinjina wannan al'amari gidan sarki guda 🤔
Yace masa to zasu shirya suje insha Allah

Acikin satin kuwa Abba yafadawa Malam suka shirya suka tafi da wasu daga cikin abokan yayun Abba na family
Yanda suke dauki abun ba haka yazo musu ba, domin kuwa sun samu tarba Mai kyau daga gidan, basuyi tunanin mutane irin wannan zasu musu tarba Kamar haka ba, sai kuma aka basu mamaki

Su Abba sunje da nufin neman aure sai mutanan gombe sukace kawai asaka musu rana🤣, domin kuwa akwai dan'uwan yarinyar shima yana neman aure akano inyaso sai ayi bikin gaba daya
Sannan kada su takura wa kansu suyi iya abinda addini kawai ya tsara

Sosai su Abba sukai farin ciki, sun san kuma cewa lalle Sultan yar mutunci yake nema

Haka suka dawo da goron saka ranar su, Tsawon wata biyu🤣🤣

Shima Salisu dayaga kowa de yamatsa aure aure 🤣ga Sultan anyi magana ansa rana
Ga Najma ma da akai magana yara duk sai aure suke shirin yi 🤔

Dan haka shima yafuto da tasa wata yarinya anan unguwar su, akai magana shima


Lokacin da 'yan masarautar gombe sukazo kano maganar saka ranar Nasrin, anan aka saka wata biyu Kamar dai na Sultan da Sahla

Shikuma Salisu da yasir saisun gama gidansu sannan za'a saka ranar biki, amma yanzu de kawai anyi magana, Najma naci gaba da karatun ta, yayinda ta Salisu ma yanzu ne zatayi candy 🤣



*** ***** ***



*After 1 year*


Zaune suke afalon Ummi shida ita, wata yarinya bul-bul da ita Mai kama da mk sak tana dauke ahannun Nawal tana bata nono

Qwacewa tayi daga bakin yarinyar tace "to ya isa haka Ummi nah, ai kinsha da yawa"

Kallanta yayi, ya ajiye computer dake hannunsa yace "A a wallahi bata abinta tasha, idan kin Barshi me zakiyi dashi?"

Tace "mai Babban suna yarinyar nanfa Tun dazu takesha"

Hannunsa yasaka cikin rigarta yana kokarin futowa dashi 🙊
Yaciro guda daya yace "bata tasha, muda abinmu"

"to sokuke ku qarar Dani?ga madara nan abata mana, yarinya sai jarabar cin abinci" 🤦🏻‍♀

Yace " to wata biyo? 🤣"

Tace "wallahi kai, Dan nide bana cin abinci kasani"

Yace "nima kinsan banaci"🤣


"to naji dauke hannunka daga kai kar Ummi tazo"😃

Yace "nadauke hannu na ki qwace ki hana yarinya shan nono, narasa me zakiyi dashi, abin nan dai nawa ne, daga ni sai Ummi nah,"

Yaqarasa maganar yana kama hannun yarinyar yana mata wasa 😊



Rayuwar gidan mk da Babynsa kenan, suna zaune lafiya saide abinda baza'a rasa ba, wannan kuma dama ansan Zomu zauna Zomu saba ne, harshe da hakori ma wataran ana sabawa

Yarinyar su d'aya Mai kama da mk, babu Inda tabar ubanta, suka sanya mata sunan Ummi Wato Halima, suna kiranta da Ummi itama


Nawal nayin karatun ta a Dubai lokaci zuwa lokaci suna zuwa gida idan sun samu hutu a makaranta

Wani lokacin shida kansa yake sakata ta shirya suje gidan marayu da asbiti domin kai musu ziyara, hakan da yakeyi ba qaramin dadi yakewa Ummi ba, saboda tana ganin Kamar bai Manta da halaiyar mahaifinsa ba


Sultan da Sahla suna zaune agidan su lafiya, Inda take dauke da ciki na wata uku, suna zaune a Abuja, dasafe su shirya su tafi wajan aikinsu, idan sun dawo gida
Suyi aikin komai tare, hakuri da daukar qaddara irin nata shine yaja hankalin Sultan yafada cikin sonta batare daya saniba

Yayinda Najma suke shan amarcinsu akano cikin gidan ta Mai shegen kyau, watan su biyu da aure "

Shima Salisu yana zaune da matarsa lafiya



Mutanan iko kuwa, 🤣an saduda, anbada kai,Nasrin tanata yin shagwaba son ranta, suna zaune a Abuja, da Dan qaramin cikin ta na wata biyu

Lokaci zuwa lokaci suna ziyartar juna itada Nawal, rayuwa Mai juyawa kenan, wataran qunci wataran farin ciki

Abaya sunsha wahala da gwagwar mayar rayuwa,musanman Nawal amma Haquri yabata komai



*** ***** ***



Kallanta yayi "Baby nah yakamata afara kokarin nemawa Ummi qani fa"

"qani kuma? Yarinyar da ko yayeta ba'aiba"

Yace "nikam gaskiya nagaji kawai sonake kiyita haihuwa"

Tace "saikace wata inji? 🤣Wato na tsufa da wuri kaje ka Auro wata irin fatar dakake so 🤔"

Murmushi yayi yajata jikinsa ya rungumeta yace

"Baby nah kenan,Allah yabarmin ke,🌺NI DAKE🌺 mu kasance tare har Abadah"


Itama ta rungumeshi tace "Amin mijina"




TAMMAT BI HAMDULLAH

Anan nakawo qarshan wannan labarin nawa Mai taken NI DAKE,Allah yabamu ikon yin amfani da abubuwan dasuke ciki masu kyau, yabamu damar watsi da marar kyau


ABIN LURA:


Hakuri, shine idan kayishi Awannan lokacin zaka samu riba, mutum yamaka laifi tattarashi ka watsar karka sawa kanka hawan ruwa, inde wannan Rayuwar ce kana zaune agiidanka zakaga abinda zai biyo baya

Tausayi da taimakon mutanan da baka sansu bama, Awannan lokacin abinda yafi mana qaranci kenan, Inda ace mutane zasuyi koyi da abinda mk yakeyi na taimakon mutane, da anji dadi, bai santaba Babu dangin iya Babu na baba, amma yatai maka mata daga ita har dangin ta, gashi sunyi aurensu suna zaune lafiya.


GODIA :

Hafsat Hausa novel (H2)

Khaleesat Haiydar Hausa novel

Nidake fan's

Best Hausa novels

Prince and princess hausa novel

Wanda yace... novel fan's

💋Meenat novel💋

❤Alkawari✊🏻hausa novel

Novels and kitchen 📚🍲


Ina godia sosai yanda kuke bibiyata Tun daga farko har qarshe, dama sauran Wanda ban fadaba


JINJINA GA:

Hajiyar...🌹
Maman Ahmad
Mom haneef
Samirah yahya niger
Fatimaxahara
Maman dr.insha Allah
Fatima me voice🤣
Hajiya qarama
Khadijat Aminu
Ummu farouq
Maman khalifa
Saudat
Mom asas
Futuha luv💋🧕🏻
Shamsiyya dahiru
Ruqaiyasalisu
Anty ~zubaidah
fateema shu'aibu abdulla
Mrs isma'eeil ce💃🏻
🌹Mom hydar
🌹🌹🌹Nana
Khadeejat😎
Salma hamman sa'eed
🌺Baby🌺
Ummu haneef
Maman basma

Saudat
Maman sadiq🙋🏻
Sumyb
Mrym
Mmn khalil and rukky
Ummu affan
Hashmart
Rabiat Mafida Suleiman
Bashirm Halima
Khadija bashir
Fatima abdulqadir tatu
Deefat
Fati sd
ماشاء الله ❤

Bazaqu qirgu ba😱



Group dina na whtspp Zan rufeshi zuwa jibi insha Allah, saikuma nafara wani novel din Zan bude wani


Daga qarshe duk Wanda na yiwa laifi a Sanadin wannan littafin yayafemin 🙏🏻

Mutara asabon novel dina Mai taken DANGI DAYA, kai dagajin sunan kasan kwamacala ce ta family, Wanda zaizo muku bayan Sallah insha Allah 🙊😃

Karku Manta da sunan... DANGI DAYA


miss you All😢







Amina Muhammad El Yaqoub jigawa state✍🏻

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment