Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Shaltos a hannunsa

Cikin tsawa yace" kuriqemin ita nace "

Sake riqeta sukai, tanata kawar da fuskar ta, amma haka ya matso ya gwale mata cikin idonta

Haqorinta tasa tana kawo masa cizo amma haka yacire murfin Shaltos din yafesa mata a idonta, lokaci daya ganinta ganinta ya dauke

Yayinda tasaki wata irin qara tafadi awajan

Cikin tsoro jazy yace "gaye karfa Muje tamutu, yasaka hannunsa aka 🙆🏻‍♂na shiga uku idan akaji agidan mu"

Anwar yace "to Dan matsoraciya, dalla kuzo mu ware"
Cikin sauri suka shiga Mota sukabar wajan

Acan Gida kuwa umma takasa zaune takasa tsaye, har ana kiran sallar magrib amma shiru Baby bata dawo Gida ba

"ke kuma lafiya Tun dazu nashigo inata sallama kinyi shiru"

Kamar da ita yake magana ta yi burum tafuto daga Dakinta tace "rashin kawaici ne kawai irinna yaya, Tun dazu Baby bata dawo daga makaranta ba shine ta daga hankalin ta, ita Babyn yarinyar goye ce daza'a tsaya ana d'aga hankali akanta"

Abba yace"badake nakeba Mariya, kidenamin katsalandan "yajuya ya kalli umma yace" ke Safiya karfe nawa take dawowa yau? "

" Karfe biyar, wani lokacin biyar da kwata, kuma tabar wayarta agida saboda batada chaji

Jinjina kansa yayi yace" to bari Muje dasu salisu abi sawunta, "

Mayafinta tazara tace" maigida hankalina bazai kwanta ba Muje "

Fita sukai gaba dayansu, Mariya tatabe baki takoma daki

Da salisu da qannanta maza guda biyu dakuma umma suka tafi hanyar domin dubata

Kasancewar duhu yafara yasa suka fara haskawa, shiru basu gantaba, saida suka duba layin duka basu gantaba

Kamar wasa umma ta haska gefenta, taga baqi awajan Kamar abayar jikinta, sake haskawa tayi, gabanta yana faduwa, cikin sauri tayi wajan taga 'yarta ayashe aqasa
Salati tasaki cikin kururuwa tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un Alhaji gata anan, ai suna jin haka sukai wajanta gaba dayansu

Jijjigata umma tafarayi amma shiru bata numfashi, lokaci daya umma tasaki kuka" alhaji munshiga uku bata motsi, Jijjigata tasake yi da karfi tace "Innalillahi..."NAWAL"







(sharhi da Comments dinku shine zaisa nagane cewa labarin yayi muku, harma nasamu qwarin gwiwar cigaba da turo muku, duk Wanda yakeso naci gaba da turo musu Dan Allah yayimin sharhi ko Comments 🙏🏻




Wanan karon kai tsaye muka dannu cikin labarin mu😇, labarin *Nidake* yanada yawa, mutum zai gane hakanne ta page din farko da mukai yau😘


Wacece _NAWAL_ ?
Yaya makomar su _Anwar_ ?


Mutara zuwa gobe

















Amnah El Yaqoub ✍🏻
🌺NI DAKE...🌺

(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub


Deducated to *Abubakar* *Abdulbasir* Wanda akafi sani da *Itz* *sadeek* ,wannan shafin nakane, halalinka ne katurashi duk Inda kakeso😃🤗, Allah yabar zumunci


3&4

Cikin kuka umma taci gaba da fadin, "Alhaji shikkenan an lalatawa Nawal rayuwa, anyi mata pyade, Innalillahi ni safiya mezancewa ubangiji na akan amanar daya bamu akan 'ya'yanmu"

Lokaci daya kan abba yasara, yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,"

'yarsa dayakeji da ita, kuma yake sonta fiye da kowa acikin 'ya'yansa itace yau aka lalatawa rayuwa

jiri-jiri yafara ji, kafafunsa suka fara rawa nan danan yatafi zai fad'i aqasa, daqyar Salisu yataroshi yafadi ajikinsa

Yace" subhanallah sannu Abba "

Shi kansa salisun jikinsa rawa yake, wannan wacce irin masifa ce tasamesu yau?

Saida abba yadauki minti biyu azaune sannan nutsuwa tafara dawo masa, amma bai daina maimaita kalmar Innalillahi ba acikin ransa

Su kuwa sauran mazan guda biyu shiru sukai sun kasa magana kowa yana ganin ikon Allah

Umma tashare hawayenta idonta tafara janye abayar jikin Nawal zata duba wajan🙈😳

Ganin akwai qannanta awajan yasa yadubi Salisu yace "Salisu dauketa Muje Gida"

Cimak yadauketa yasata a qirjinsa Kamar yadauki jariri yayi gaba duk jikinsa babu laka, sannan suma suka biyoshi abaya, umma sai share hawaye take da gefen mayafinta

Najma ce tafuto daga Gida sanye da hijabi a jikinta dogo,zata tafi makarantar dare, tana ganinsu fuskarta tasauya alamar tashin hankali qarara

Tanufi Salisu tace "yaya Salisu, meyasameta?"
Kasa bata amsa yayi, yawuceta yashiga Gida, suma su umma sukabi bayansa

Daya daga cikin qannansu tayiwa magana "Nura meyasami Baby naga yaya yadaukota ahannu?"

Cikin sanyin jiki yace "wallahi acan layin muka tsinceta ayashe aqasa, amma naji umma tana cewa wai anyi _Raping_ dinta"

Hannu tasa abakinta tareda zaro ido waje🙊😳
Bata sake saurarensa ba tafasa zuwa makarantar tayi cikin Gidan

Mariya najin shigowarsu tafuto tana daura zani duk sukai falon umma, abba yadubi umma "safiya jeki dubata kigani, Allah yasa ba abinda muke tunani bane"

"Alhaji me za'aje aduba ni Mariya, karde garin karatun nan Baby taje tadauko mana abin fad'a acikin unguwa"
Babu Wanda baiji ciwon maganar taba, haka sukai shiru suka qyaleta

Umma ta shiga daki tafara dubata, saida ta cajeta ciki da bai sannan tasaki sanyaiyar ajiyar zuciya, tafuto falon nata tace "Alhaji babu komai, lafiyarta kalau, banga wata alama ta nuna cewa any mata pyade ba"

Gaba dayansu suka Dan saki ransu, kowa sai cewaa yake Alhmdlh

Abba yace "Nura dauko ruwa ashafa mata, da alama tayi doguwar suma ne"

Nura nakawo ruwa dukansu sukayi cikin dakin umma, abba ne da kansa yashafa mata Ruwan, yaji shiru batai motsi ba, yasake tsiyayowa medan yawa yashafa mata

Sai a sannan taja dogon numfashi tasaki ajiyar zuciya "nace kuyi hakuri, hakuri fa nake baku, Dan Allah Karku cutar da rayuwata,"

Abba yace "Nawal bude idonki, nine abbanki, kiyi nutsu kidena kuka, babu abinda za'a miki, bude idonki 'yata"

Bude idanunta tayi,tafara kalle kalle Kamar me neman wani abu, saide bata ganin komai, asalima duhu take gani qirim, hannu tafara meqawa tana tattaba jikinsa tace "Abba bana gani, bana ganinku Abba, Abba ina ummata take... Sai hawaye zirrr

Abba yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un "

Najma ce ta matso tafara jijjigata tace" Baby meyake faruwa? Meyasami idonki?kibude idonki dakyau, munefa agabanki, Ga mama Ga umma Ga yaya Salisu gasu Nura da Saif"

"nashiga ukuna ni Nawal, Najma bana ganinku, duhu kawai nake gani, shikkenan Anwar yacuceni, tsakanina dashi saide Allah yayi mana sakayya"

Ta kifa kanta agwiwarta tana kuka, dogon gashinta me santsi tuni yayi bankwana da ribom din jikinsa, sai gashin nata yasamu damar barbajewa agadon bayanta

Tunda tafara magana umma takasa cewa komai, kawai hawaye ne yake zirara daga idonta

Abba yadubeta "Safiya Dan Allah kidena wannan kukan,"

"ke Nawal fadamin wayene Anwar? Menene yahadaki dashi?

" Abba shine yafesamin shaltos a'idona, shida abokansa, "

Salisu yace" Innalillahi shaltos... Ki fadamin Dan gidan uban wayeshi, wannan wanne irin rashin imani ne?

Abba yadubeshi yace "kai Salisu dauketa Muje asbiti, daga baya maji abinda yafaru, mu gaggauta kaita asbiti yanzun"


Cimak Salisu yadauketa suka futo daga dakin, jikin kowa asanyaye, Najma tuni tafara kuka, yau yar'uwarta ce babu idanu,waye wannan Anwar din datake magana akansa?

Abba yace "saif kaje gidan Malam kafada masa abinda yake faruwa, mu zamu wuce asbiti, saiku samemu Acan" ya kalli mama mariya yace "mariya ki kula da gidan"

Najma ta kalleshi, "Abba Dan Allah zanbiku,"

Sanin shaquwar datake tsakanin sune yasa baiyi mata musu ba, gaba dayansu suka futo daga gidan, bakin titi sukaje sukatare adedeta guda biyu suka tafi

Saif yana zuwa gidan Malam yatarar dashi tareda dalibai masu daukar karatu
Saida ya tsaya suka gama sannan yamatsa kusa dashi yayi masa bayanin komai, Malam ya jinjina kansa yace "ikon Allah, to bari muje asbitin, Allah yabata lafiya, saif yace" Amin Malam "


** *** **

Yanda take rusa uban kuka takama hannun umma da yaya Salisu ne yasa dayawa daga cikin jama'ar asbitin hankalinsu yayo kanta
Umma tace" sai shegiyar rauta kikewa mutane, ba zakiyi shiru kiyi addu'ah ba, kukan naki ne zai dawo miki da idon? "

Salisu yace" haba umma, kiyi hakuri dan Allah "
Najma da nura ma suka fara bata hakuri

Suna yankar kati kai tsaye suka turasu wajan ganin doctor,Kamar yanda tayiwa iyayen nata bayani shima haka tayi masa, daga nan ya turasu wajan wani doctor din yafara duba idon nata

Takwas saura saif yaqaraso shida Malam

Tawaya suka kira su Abba sannan suka fada musu dede Inda suke, suka qarasa
Gaba dayansu azaune suke akujerun dake wajan, kowa da abinda yake saqawa acikin ransa, Salisu tunani yake akan ko wanene wannan yaron, sai Inda karfinsa yaqare akansa, saboda bazai taba yiwa qanwarsu qwaya daya tal aduniya haka yazuba ido yaqyaleshi ba
Wayarsa yadauko daga aljihun gaban rigarsa, yakira Sultan, yana dauka yace "Sultan akwai damuwa fa"

Shima daga bangarensa yace "wacce irin damuwa kuma ana zaune lafiya"

Yace"wallahi wani yaro ne yawatsawa Baby shaltos a'idonta, yanzu haka maganar danakema tace bata ganin komai, duhu kawai take gani, muna asbitin Malam Aminu, gasu Malam nanma duk sunzo "

Yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, saikuma yadawo yace" bantan uba🤣, kace akwai Yaqi, gobe Zan biyo Mota nataho Gida "

Salisu yace" a a karkai gaggawar zuwa kabari muga yaya zata kasance tukunna, yanzu de akwai likitan dayake duba idon nata, basu futo bade har yanzu "

" yaya Salisu alalatawa qanwarmu ido kace inzauna? Baby fa, Babynmu yaya Salisu, me wannan yarinyar zatayi da za'ayi mata wannan abun, nasan halin Baby yaya, ba zatayiwa wani mummunan laifin dazaisa ayi mata hakaba, yarinyar da magana ma bata dameta ba, Yaya Salisu sai kun ganni kawai "yana gama magana yakashe wayarsa

Malam yadubi Salisu yace" Salisu kunyi sallah ne?

Abba yace "ai Malam gaba dayanmu ma, babu Wanda yayi sallah, daga magrib har isha'i,"

Malam yadafe kansa, "kash, tokuje kuyi sallah, ni saina zauna"

Haka akayi kuwa, gaba dayansu suka tafi, shikuma yazauna da carbi a hannunsa yana ja, tareda zubawa dakin da aka shiga da Nawal ido yana tunani

Bayan sun dawo daga sallah ma saida suka dade azaune sannan likitan yafuto, gaba dayansu suka nufeshi, jikin kowa yayi sanyi saboda ganin fuskar likitan babu wani annuri

Malam ne yace "likita yaya ake ciki dangane da jikata?"

Ajiyar zuciya yasauke "gaskiya baba akwai matsala, idanunta sun riga dasun samu matsala _, I am sorry to_ _said_ bazata sake ganiba, _because of_ _Chemical_ din da'akai amfani dashi wajan zubawa idanun nata yanada qarfi sosai, yataba Ruwan idanunta sosai, Inda Allah yarufa Asiri ma akwai sauran ruwa acikin idanun nata, amma da babu ruwan gaba daya to gaskiya saide muyi kokari mucire qwayar idon saboda kada tafada ciki, "

Cikin kuka😭😭 tace" Innalillahi yanzu likita shikkenan yar'uwata tarasa idanun ta? Shikkenan bazata sake ganiba? Tadena ganinmu kenan? "cewar Najma

Malam ma yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, saida ya maimaita hakan sau uku, sannan yace yanzu likita babu wani kokari dazaku iyayi akan idanun nata?"

" um akwai abinda za'a iyayi akai, idan anyi mata aiki da yiyuwar idanun nata su dawo, ya danganta da irin ciwon mutum, ciwo ciwo ne, wani anayin aikinsa Naira million daya, amma wannan inada tabbacin za'a iya yimata a Naira million daya da dubu dari da sittin "

Cikin faduwar gaba Abba yace" million daya likita? 😳Yaro ina zamu samu wannan kudin? Kutaimaka kuyi mata wannan aikin likita, Ahankali saina dinga biyanku, wallahi tallahi ko Zan saida kadarata gaba daya kudin bazasu kai hakaba "

" baba ba laifi na bane, Inda inada damar yimata aikin babu ko sisi wallahi zanyi mata, nima ma'aikaci ne Kamar kowa, sannan ba aikine da mutum daya zai gudanar dashiba, kuma wannan shine gaskiyar maganar dana fada muku ko ina kukaje hakan take inde aiki kukeso Mai kyau, amma idan baku yarda ba zaku iya tuntubar Babban asibitin ido na qasa dake Kaduna, inyaso sai ayi mata aikin Acan "

Malam yace" yaro munji, baqin zancenka mukai ba, maganar anan guda dayace, ina za'a samu wannan kudin? Tayaya zamu samesu? Ta wacce hanya?

Yace "kuyi addu'ah baba, sannan kuma ku nema, Allah yaana tare daku," daga haka yayi gaba yashiga wani dakin

Umma tace "Alhaji ina ganin kawai mubar asibitin nan, mukoma gida, haka tata qaddarar take"

Salisu yace "umma wacce irin magana ce wannan? Muje mu nemo yaron daya yayi mata hakan, yazo yabiya kudin, ko kuma hukuma tayi mana maganin sa"

Girgiza kai Malam yayi "duk ba wannan ba, Dan Allah kuyi shiru mu nemawa kanmu mafita"

Idanun Najma jajir tashige dakin da aka kwantar da Nawal

Umma ma bayanta tabi, duk suka shiga dakin kowa yanemi waje yazauna, kowa yayi shiru,
Tana kwance amma hawaye ne yake tsiyaya daga idanunta

Malam ya dubeta yace" 'yata Nawal, kifada mana menene yake faruwa? Ya akai haka tafaru? "

Shiru tayi babu amsa, kawai hawayen baqin ciki ne yake zubo mata

Umma da idanunta sukai jajir saboda kuka tace" ka rabu da ita Malam, kabarta tayita zubar da hawayen, tunda dama ance sun qare idan tazubar dasu gaba daya ai shikkenan, "taana gama fada hawaye ya silalo daga idanunta

Malam yace" a a kukanta ko rashin kukanta ai babu abinda zai sauya qaddarar ubangiji "

Yasaka duban Nawal din" fadama na abinda yake faruwa "

Hannuwanta guda biyu tasa tashare idanunta sannan tace" duk ranar dazan tafi makaranta sai sunmin magana, bantaba kulasu ba, wata rana har munafuka suke cemin, waini ina ganin su subasa ganina, bantaba tanka musu ba, shine jiya wani daga cikin su Mai suna Anwar yazo yasha gabana yasa hannu zai yayemin niqab d'ina, nikuma zuciya ta d'ebeni namareshi,baimin komai ba a lokacin, sai yau suka tareni zasu watsamin _Acid_ , Allah bai basu damaba shine suka riqeni suka fesamin shaltos... Yaqarasa maganar cikin kuka

Malam yace "subhanallah, subhanallah, Nawal

Tace" na'am "

" wai shi wannan niqab din wajibi ne ko sunnah ?🤣, incede babu kod'aya? To daga yau namiki katangar qarfe tsakanin ki dashi 🤣🤣, kibar fuskarki abude kowa yagani, duk Wanda bazaice masha Allahu ba yayi miki wata maganar kice ((Li'ilafi quraishi))🤣inace shikkenan zance ya wuce?

haba Nawal, ina tarbiyarki take? Meyakaiki marin namiji? Nawal Inda wani nefa kai tsaye pyade zaiyi miki, kinga shikkenan yarusa miki rayuwa, yayi miki tabonda har jikokin ki sai sun samu labari, meyasa Tun farko baki sanar Dani suna bibiyar kiba? Kinga da hakan bata faruba, dana hanaki bin hanyar kwata-kwata, awanne Gida yake? Ko bakisan gidansu ba?

"bansan gidansu ba Malam, nide nasan koda yaushe a wannan wajan suke zama, anan nake ganinsu kullum"

Cikin huci yace"amma wannan yaron daya sake yazuba miki _Acid_ dinnan wallahi sainaje har Gida nazubawa uwar Data haifeshi "cewar Salisu

Malam yace" a a Salisu, ba'a maida sharri da sharri, ya maida dubansa Ga Abba, "yanzu yaya za'ayi? Yaya zamuyi asamo kudin ayi mata aikin?

Abba yace" Malam, banida Inda Zan samu wannan kudin, ko dubu hamsin baza'a samu awajenaba bare zunzurutun kudi har nera million daya da dubu dari da sittin, saide asaida gonakina, ahada da gidan damuke ciki, "


" Abba Dan Allah karka saida gidanka akaina, nasan haka Allah yaso yaganni shiyasa yamaidani hakan, Abba idan ka saida gidanka ina zamu koma? Mutafi Gida kawai Abba, Allah yasakamin, nabarshi da ubangiji, nasan zaiyi mana hisabi "

Saif yace" ke komai da anta'baki saikice hakuri hakuri, shima wannan din anufinki hakurin za'ayi? 😒

Nura yace "fad'a mata de, idan ke kin hakura, mu amatsayin mu na makusantanki bamu hakura ba yaya Baby"

Yakalli Abba yace "Abba kawai asiyar da gidan,bazamu juri ganinta ita bata ganinmu ba"

Najma ma tace "gaskiya kam Abba, kawai asiyar din, mutum dubu nawane suke zaune agidan haya"

Malam ya girgiza kansa, yana mamakin yaran, yanda suke qaunar junansu haka, yace "dare yayi, yakamata mu tafi gida, sai musan wacce shawara zamu yanke"

Ke Najma ki zauna tare da ita, su nura saisu dawo sukawo muku abinci, mu zamu tafi,zamu bincika muji gidansu yaron, kafin gobe kuma mud'auki mataki

Tace "to Malam, Allah yakiyaye hanya, Umma ki gaida mama

Umma tace" to Najma, ta kalli 'yar tata dukda ita bata ganin ta tayi musu saida safe suka tafi gida

Suna hanya Sultan yakira Salisu, "yaya Salisu yaya kukayi da likitan?"

"wallahi yace idanun nata suna riga da sun sami matsala, za'a basu million daya da dubu dari da sittin, suyi mata aiki"

"tabd'i jam, akwai damuwa kenan, wannan ko waye yatada mana qafar baya, inama zanga yaron nan"

"to wallahi de itama kanta tace kawai ganinsa take a hanyar ta tazuwa school batasan gidansu ba, yasan de sunansa Anwar"

"Anwar?"

"eh haka tace"

"Anya kuwa ba Anwar din dana sani bane?"

"eto may be kasan shi d'in tunda duk mutanan ku ne 🤣🤣"

Murmushi sultan yayi "kabari kawai yaya Salisu, sainazo goben insha Allah, ka gaidamin umma tah, ka kwantar mata da hankalinta kafin nima nazo nad'ora🤣Dan nasan dole ta damu antaba mata autarta

Salisu yace" to qanina Allah yakawo ka lafiya "

Awannan dare Malam bai runtsa ba, yana zaune akan sallaya yana addu'ah akan Allah yakawo musu Mafita, Allah yadubesu ya kawo musu dauki, Umma kuwa tana nan zaune itama da carbi a hannunta, tanaja tana kuma tunanin Rayuwar 'yarta qwalli daya aduniya,wadda zata kasance makauniya, domin kuwa idan tace zasu sami wannan kudin haqiqa ta yaudari kanta, ayayinda Abba yakasa zaune yakasa tsaye yanata zagaya d'akinsa yana tunanin Inda zai sami wannan kudin ya tallafi Rayuwar 'yarsa mafi soyuwa agareshi
Haka yayi tunanin yagama baisamu mafitaba, daga qarshe shima alwala yad'auro yazo yafara sallah

Wacece Nawal?

Itace 'ya guda d'aya tilo awajan ummanta maisuna safiyya,Abbanta Alhaji Muhammad lawan yanada mata biyu, safiyya ce babba,'ya'yanta uku, Salisu ne babba, saina biyu Sultan, saikuma yar' autarta Nawal

Saikuma mariya suna kiran ta da mama mariya, Tanada 'ya mace babba sa'ar Sultan ce, suna kiranta da anty Maryam, tana aure a zamfara state, saikuma Najma, wadda take sa'ar Nawal ce, tabawa Nawal wata biyu, sai nura dakuma saif, sai mus'ab Dan qaramin yaro

Rayuwar gidan tana tafiya ne cikin kwanciyar hankali, hakan kuma yasamo asali ne daga wajan umma, batada fada, kwata kwata batasan tashin hankali, mace ce me mutuqar hakuri
Yayinda mama mariya takeda Jan magana, abu kadan za'ayi amma tadinga magana akansa kenan

Gaba dayansu 'yan kanone, suna zaune a rijiyar zaki, Abba ne yake tare da mahaifinsa unguwa d'aya, Wanda aka sani da Malam, shine limamin unguwar su, Babban malami ne sosai, masani ne akan abubuwa dayawa, sosai yake shiri da Nawal
Fari ne tass, shima Abba saiya dauko farin sa, cikin ikon Allah kuma gaba dayansu yaran Abba babu baqi, kowa kamarsa daban amma farare ne gaba dayansu, yayinda Nawal tayi Kamar ummanta, babu abinda tabari na umma, kawai baqin umma ne batayiba, saboda umma baqa ce, tana doguwar fuska, girarta acike take, baqa sid'ik, tana da hanci madaidaici, amma _lips_ dinta _pink_ ne, kuma sirara, kasan cewar umma maza tafara haifa saiya kasance tanason 'ya mace, sai kuwa Allah yaabata, sukuma Salisu da sultan tunda aka haifeta suka dauki son duniya suka dora mata, kowa soyake yasata farinci acikinsu, sune suka saka mata suna BABY, daga nan kuma kowa yadena cewa NAWAL yake kiranta da Baby har 'yan unguwa, qannanta kuma nura da saif da mus'ab suke kiranta da YAYA BABY

Suma kuma yan dakin mama mariya suna santa, musanman Najma, sun shaqu sosai, basuyi halin uwarsu ba, nura da saif kuwa dayake sunada tsawo saiya kasance sunfi su Nawal girma, idan ka gansu saika dauka sune gaba da Najma da Nawal din

Nawal tanada matuqar hakuri, Dan wani lokacin har mamaki take bawa ummanta

Sau tari za'a yimata abu, Wanda zakayi tunanin zata rama, amma tana budar baki saide tace tayafe maka, shiru shiru ce baabu ruwanta, saide inka kaita maqura bata iya fishi ba
Daga ita har Najma shekararsu goma sha tara, amma Allah yayi mata sura me kyau da daukar hankali, agidama umma bata barinta ta zauna da qananin kaya saboda Allah yayi mata baiwa, Ga kyau Ga diri, tana hips manya, idan tana tafiya saika dauka tanayi ne Dan Jan hankalin ka, amma kuma kokadan ba hakan bane, yayinda _boobs_ dinta suke madaidaita

Amma a gareta ba haka tasoba, saboda tana qaunar qananun kaya, tanason sakasu koda yaushe, shiyasa take dabara tasaka qananun kaya saita dora baqar abaya akai tatafi makaranta, haka kawai takeson shigar qananun kaya

Mahaifinsu Alhaji Muhammad ma'aikacin gwamnati ne, amma yadade da ritaya, kawai yanzu yana karbar kudin fansho ne, Wanda kudin qalilan ne, na gidan ma bai wadacesu ba

Salisu bashi da aure, yana Dan neman kudi ne a kasuwa kawai, saikuma sultan yana wajan uban gidansa a lagos, yana koyan harkar canji, bashi da mutunci, Tun baby tana qarama baya bari atabata yaqyale, yana harka da samari masu ji da kansu, kuma suma sun sanshi saboda bashida kirki

Dukansu sunyi karatu saide babu aikin yi

Anty maryam kuwa daga candy akayi mata aure

Najma da Nawal suna candy suma suka zana jamb kowa yaci acikinsu, gashi baba bashi da karfin dazai dauki nauyinsu su biyu, Dan haka yace kowa ya hakura acikinsu, mama mariya tahau masifa tana cewa yan Dakinta ne bayaso suyi karatu, inba haakaba yabawa Najma mana, tunda yan dakin safiyya sunyi karatu harsu biyu

Haka yayi shiru yarabu da ita, amma shi kansa acikin ransa yafison Nawal tatafi, haka ka wai Allah yadora masa son yarinyar acikin ransa

Saide daga bayama da abin yafara zama tashin hankali kawai sai Najma tace ita hakura taci girma tabarwa qanwarta, kawai Abba yatura Nawal din

Wannan ne silarta tazuwa makaranta, Wanda Acan tahadu da qawarta Nasrin, tanada hankali sosai da sanin yakamata, lokaci zuwa lokaci suna ziyartar juna,


_Back to story_
Washe gari haka kowa yatashi jiki babu qwari, Umma idanunta har nauyi suke mata saboda rashin bacci
Abba kuwa Tun sassafe yafita yanata zagaya gari wajan abokansa neman bashi
Dakuma tallar gonakinsa da filaye guda biyu ko za'a sami masu siya

Daya daga cikin dillalin de yace masa zaiyiwa wani Alhaji magana idan zai siya zaizo yakarbi takardun sai suje suga wajan

Sai wajan shad'aya da kwata yadawo Gida, duk yagaji Ga yunwa tana damunsa kansa har ciwo yafara, Ga kuma tunanin Nawal datake asbiti, shi Salisu da Malam sun tafi neman sanin Anwar dakuma iyayensa

Kansa yasunkuyar qasa yana tunani, yana kuma addu'ah Allah yabasu ikon cin jarabawa

"Salamu alaikum"

Abba yadago kansa yace "wlkslm sannunku"

"yawwa sannu baba, masu karbar kudin wuta ne, _bill_ zaka bamu"

"to bari adauki muku"
Yatashi yashiga Gida yadauko yakawo musu

Dubawa sukai daya daga cikin su yace "baba wannan ai baka biya na wancen watan bama, amma yanzu babu damuwa kakawo dubu shida da dari biyar kawai"

Cikin haushi Abba ya kallesu "shi kudin wutar ne dubu shida harda 'yan kai?"🤣🤣

"eh baba, ai ahakanma anyima sauqi sosai"

"to bari kuji, ni banida wata dubu shida dazan bayar, ga _transformer_ can kafin ku qaraso nan gidana, zaku iya zuwa tundaga jiki ku tsige layin gidana a jikinta(🤣🤣)
Kunga nan gaba basai kun tsaya agidana ba, kawai tsallakeshi zakuyi,

(kunga laifin Abba? 🤔🤣




Waye Anwar?

Yaya makomar su Abba dangane da kudin dasuke nema?

Anya kuwa sultan bashi da alaqa da Anwar?



Dan Allah sharhi 🙏🏻inaso naji hasashen da kukeyi masoya nah🤗







Amnah El Yaqoub ✍🏻
🌺NI DAKE...🌺

(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub


Deducated to *Itz* *sadeek*


5&6

"A a baba, ba za'ayi hakaba,kakawo ko rabi ne sauran saika biya daga baya"

"nace kuje kuyanke"

"to shikkenan baba, mude akan aikinmu Muke" haka sukaje suka yanke wutar yana kallansu

Daga qarshe ma tsaki yasaki yana tunani, da kudin da ake nema awajansa zaiji koda wata kudin wuta, su wutar ta dama, a wannan yanayin dayake ciki wutar nan bata gabansa🤣🤣

"Salamu alaikum barka da hutawa Abba, dafatan mun sameku lafiya"

Juyowa yayi ya kalli maiyi masa maganar yace "A a sultan, kaine akan hanya"

"eh Abba nine wallahi, Yaya jikin na Baby?"

"to sultan jiki da sauqi za'a ce, sunacan asbitin de, bamu samu munje bama, muna nan munata fafutukar yanda za'ayi"

Sunkuyar da kansa yayi, zuciyarsa nayi masa rad'ad'i, yace "Allah yabata lafiya"

"amin ya Allah, tashi mu qarasa gidan" Sultan yatashi sukayi cikin gidan
Da ummansa yafara tozali tayi tagumi hannu bibiyu atsakar gidan, mama mariya tanajin sallamarsu tafuto daga d'aki tace "Alhaji ansamu miliyan d'in? (🤣)

Abba yace" eh ansamu mariya, ai kinsan su kudin zuwa ake adebosu a'inda aka ajiye

"Alhaji daga magana sai baqar magana?

Kafin Abba yasake magana Sultan yayi Murmushi, cikin ransa yace wannan Gida de yana nan yanda yake bazai sauyaba
Ya tsugunna qasa yace" umma tah ina kwana? Yaya jikin Baby? Ajiyar zuciya tasauke "Baby jiki da sauqi Sultan"
sannan yamaida kallansa ga mama yace" mama mariya yaya muka sameku?

Cikin baqin ciki tace "gashi kuwa kaganmu, gashi kagani da idonka yanda kasamemun, aiba saika tambaya ba, tunda ni banida matsayin da zakace Dani ina kwana"

Shide baice mata komai ba yayi Murmushi kawai, yasaka hannu a aljihun wandon jeans din dake jikinsa yazaro kudi yamiqawa Abba yace "Abba Ga wannan basuda yawa, dubu dari da ashirin ne, ahada dasu akai asbitin"

Tun kafin Abba yace wani abu mama mariya tace "yanzu kaida Sultan kana da dubu darin kabarmu mukecin fara da mai🤣

Yace" to mama kuyi hakuri "
Yakalli Abba yace" Abba ina yaya Salisu ne Muje asbitin naga jikin nata?

"Salisu Tun safe suka fita shida Malam neman gidansu shi yaron da Nawal tafada mana"

"Ok bari na kirashi, daga can saimu wuce"

Abba yace "to

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment