Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Taci gaba da fadin,
Yanzu hakama yaron Dan shaye shaye ne ko manemin mata "

'Daga murya yayi yace" Nawal ! " asukwane ta futo daga cikin dakin dama jiran sammaci take 🤣
"Abba gani"

"Wacece wannan matar da kikaje kika yayimo?"

"Abba nima bansan taba"

"to naji d'aya, wayar waye wannan kuma ahannun ki?"

Wayar ta meqa masa tace "Abba itace tabani"

Batare daya karbi wayar ba yace "nahanaki zuwa makaranta shine kika take magana ta kika tafi, toshknn yamiki kyau kijirani ina nan dawowa kanki" yana fadar haka yafice daga gidan

Mama mariya tace"nikam tsoro ma matar tabani, daga gaanin ta irin matan nanne na birni Wanda idonsu yabude daga nan ta fice daga falon itama

Umma ta kalleta "ashe ni zaki yaudara kiyiwa qarya Baby ? 🤣, bakisan ramin qarya qurarre bane ko? Ai shknn, yanzu saiki san yanda zakiyi da matar da kika kawo, tunda kinji abinda tazo nema"

"umma Dan Allah kiyi hakuri, wallahi dana fita mukai waya da Nasrin din shi ne tacemin wai tana makaranta, shine naj...

" rufemin baki, maqaryaciya kawai, aina dena yarda da maganar ki Nawal, naga alama nema kike kifi karfina "

" umma Dan Allah kiyi hakuri insha Allah bazan...

Katseta tayi," tashi kiban waje ni"

Cikin damuwa ta shige daki, wayar hannunta takallah wadda maman Baffah tabata🤣🤣


*** ***** ***

"wallahi Malam matar tabani tausayi, da girman ta da Komai, sannan abinda yasa naqara tausaya mata shine, da bakinta tace ita tasan cewa danta bayajin magana, amma ta budi baki ta fadamin hakan, abinda yanzu yake wahala acikin neman aure kai tsaye afuto a fadama gaskiya, wasu 'yarsu tanada lalurar aljannu iyayen ta bazasu fad'aba, sai kaga sai anyi auren qarshe azo ana samun matsala, wasu kuma zakaga yaransu suna da wasu cututtukan amma akasa bayyana wa saboda nauyin abun dakuma tsoron cewa masu neman auren zasu iya fasawa
Amma ni bansan wanne irin rashin ji yaron nata yake dashi ba, amma ga number tabani tace ayi bincike akanta "

Malam yayi ajiyar zuciya sannan yace" Nawal kenan me jama'ah, ga Nuhu gakuma wani ta janyo🤣🤣
Wannan ba abin damuwa bane muhammadu, akwai mutane na a Adamawa, zansa ayi binciken insha Allah, duk abinda bincike yabamu saai akira yarinyar aji ta bakinta, mude Nuhu muka sani koba hakaba wannan bamu sanshi ba, da haka sai abata zabi acikinsu, "

Abba yace" to Malam nagode "

" Babu godia tsakanina dakai muhammadu, d'ana gari ai shine yake neman shawarar iyayensa"


*** ***** ***

Kemade Baby meya kaiki zuwa makaranta, yanzu gashi bayan kina cikin matsalar Nuhu kinsake danna kanki cikin wata matsalar "

" Najma nimafa matar nan kawai dagewa tayi akan saita biyoni, nayima tunanin kawai sallar zatayi tatafi, idan nasan zatazo da wannan maganar tayaya Zan barta tabiyoni, amma kowa sai laifi na yake gani, ya kukeso nayi ne "

" abinda zakiyi shine kizabi d'anta koki zabi Nuhu "

" Najma kinsan abinda kike fada kuwa? Bansan mutum ba, ban taba ganinsaba, kawai shikkenan saina amin ce "

" to Baby idan baki aminceba ai shikkenan saiki amincewa Nuhu "🤣🤣


*** ***** ***
Kallanta yayi yace
"to Ummi nizan wuce"

Ta kalleshi cikin jin dadi, ganin yasaka norml kaya qanana Wanda ba crezy ba tace"to Baffah, dawuri zaka koma kenan wannan karon, bazaka mana Dan kwana biyu ba "

" ai Ummi akwai ayyuka ne"

Cikin Murmushi tace "to Allah yadawo dakai lafiya, nayima alqawarin wannan dawowar da zakayi zanbaka wani kyakykyawan Surprice"

"Ummi naga sai farinciki kikeyi, meyake faruwa ne"

"A a Babu komai, kaide kawai saika dawo din"

"to Ummi Zan tafi"

Tace "Allah yakiyaye"

Yasake cewa "Ummi Zan tafi"

Tashi tayi tsaye tace Dan Allah naji, Muje, suka fice daga falon, har zuwa harabar gidan, Babban gida ne Mai mutuqar girma, wanda yatsaru da kyawawan motocin sa, har gaban motar dazai shiga tarakashi, tace "to Muhammadu adawo lafiya, Allah yakaika lafiya yadawo dakai lafiya, idan zaka dawo inada saqo"

"saqon me kikeso Ummi?"

"zobe nakeso kasa ayimin Mai harafin 'N' na gold sannan na yarinyar da bazata wuce 18 years ba"

Yayi mamakin maganar ta, amma saiya basar yace"to insha Allah "

" bakayi sallama da yafendo ba itama yau zata tafi "

" um ki gaishe ta kawai Ummi, taagaida mutanan gida "

" to shikkenan, sannan ta kai hannu takama kunnansa tace"yagaggun kaya "🤣

Dasauri yakai hannunsa kan kunnansa yace" Auch! Ummi bazan saba "

Badan ta yarda da maganar tasaba tacika shi, sannan aka jashi zuwa Airport


Wannan shine gidan Alhaji Kabeer Sule yola, ba qaramin me kudi bane, yataka matsayi na siyasa sosai da sosai, haka kuma yana daya daga cikin masu fada ajin 'yan siyasa, yana daya daga cikin mutanan dasuke tsaida d'an siyasa takara
Mutum ne Mai mutuqar tausayi, da temakon talakawa, yana kaiwa gidan marayu ziyara tareda temakon su, bayan aikin yi dayake temakon mutane dashi

Kowama nasane, yanada halin kirki, matar sa daya Hajiya Halima Jamal baba, itama yar adamawa ce sunyi aurensu tunna saurayi da Budurwa
Aikin dayake ne yasa suka tattara suka dawo Abuja da zama
'Dansu daya namiji suka saka masa sunan Baban Hajiya Halima, Wato muhammadu, kasancewar su fulani shiyasa suke kiransu da Baffah, saboda haka dabi'ar fulani take, idaan sun sakawa yaro sunan babansu sunayi masa inkiya da Baffah

Tun yana karami yataso shiru shiru marar son magana, babansa yadaukeshi yakai shi qasar waje karatu tundaga lokacin dabi'ar sa tasauya,yahana ace masa muhammadu saide mk, zama da abokai yasa yakoyi wasu daga cikin halin su marar kyau, Kamar shigar dabata daceba, haka kuma idan yaga mace ba komai bane awajan sa ya rungume ta, yayi kissing dinta, wannan abu yana yiwa iyayen sa ciwo, Dan haka suka dawo dashi gida aka maida shi makarantar mu tagida Nigeria, harya kammala secondry dinsa, tareda saukar alqur'ani da sauran littatafai

Daga baya suka maida shi qasar waje yayi degree da masters tareda phd, anan yahadu da Yasir sukai zama na mutunci har yake kiransa da Yas

A tunanin iyayen sa yadena wannan dabi'ar, ashe abin ba haka yakeba, cigaba ma aka samu akan da, domin kuwa har Dan kunne sakawa yake

Kwatsam rana daya Allah yayi wa mahaifinsa rasuwa, tundaga lokacin harkokin uban yadawo hannunsa, ta bangaren siyasa ma dashi ake komai, yanda mahaifinsa zai kira meeting aje haka shima yakeyi, taronsu na qarshe shine Wanda suka gudanar dashi a qasar kuwait tareda mahaifin Anwar da kuma sauran yan jam'iya

Kasancewar sa matashi yasa yake shiga motar dayaso, yasa kayan dayaso, yayi kwalliya irin yanda yakeso, sauran kasuwancin mahaifinsa dakuma kamfanunnuka Ummi ce take kula dashi, wasu daga cikin harkar kasuwancin nasu kuma shine yake gudanar dashi a Dubai

Ita kuma Ummi take gudanar dana cikin gida Nigeria

Arayuwarsa bayaso a kirashi da muhammadu, saide MK,Wato Muhammad Kabeer, amma dangin su na yola kowa muhammadu yake cewa Babu ruwansu da wani mk, shima kuma haka yake amsawa Babu yanda ya iya😖

Amma sunan Baffah, Ummi ce kawai take kiransa dashi, bayan ita Babu mai fada masa sunan

Abokin sa daya, yarima Nasir, daan sarkin gombe ne, amma yana kiransa da Nas

Yanzu haka shekararsa 34 amma ba aure, kuma Babu wadda yake kulawa, sai zuwansa kano da Allah yahada shi da Baby🤣


Yana mutuqar son mahaifiyarsa, idan ka naso yasoka toka Mutunta mahaifiyarsa, tausayi da temakon mutane Babu abinda yabari na mahaifinsa, har kama, inde kasan mahaifin sa to kana ganin mk zaka gane shi


Wannan shine labarin MK🤗


*** ***** ***

Cikin satin su Abba suka gama bincike akan Ummi, amma basuji dadin labarin dasuka samu akan danta ba, Dan haka Abba da kansa ya kirata yafara yimata maganar awaya, kai tsaye tace masa zata biyo jirgi tazo, sai su qarasa maganar azahiri, tunda wannan ba qaramar magana bace

Washe gari Nuhu yaturo wani dan'uwansu Abba, Kamar yaya yake awajan Abba

mutumin
Yace Nuhu ne yaturo shi yanaso abashi dama yakawo wa Nawal kayan gaisuwa saboda kar wani
Yarigashi
Abba yadubi mutumin yace bawai Yaqi Nuhu bane, wallahi tallahi yanason Nuhu, amma Nuhu yanada gajen hakuri, ita yarinyar ma tace bataso, yanzu haka kokarin janyo hankalin ta sukeyi
Daga nan mutumin yatafi, Abba yace yau nagamu da Nuhu, ni wannan yarinya yaya Zan mata ne? 🤣🤣

Acikin satin Ummi tazo kano, Umma tana ganin ta ta karbeta a mutunce
Abba yakira Malam awaya, ba'a dauki lokaci ba Malam yaqaraso

Nawal tana dakin mama mariya itada Najma, tunda taji baquwar rannan tazo takasa fita saboda gani take kowa haushin ta yakeji, bayan batada laifin komai

Malam yadubi Ummi bayan sunyi gaishe gaishe yace"baiwar Allah kinzo garemu da Babban al'amari, gashi kuma mu munyi bincike mungano cewa yaron wajan ki har neman mata ma yanayi,😳 ga kuma shigar dabata daceba, kinsan kuma ba kowanne ubane zai iya daukar yarsa yabawa irin wannan yaron ba "

Ummi ta jinjina kai tace" Baba nasan d'ana, shi yasa Tun farko ban boye muku ba nafada muku cewa bayaji, nasan cewa yana saka kayaiyakin dabasu daceba, amma neman mata kaam bayayi, Inda yanayi Tun farko bazan boye muku ba, akwai qanwata uwa daya uba daya, itace tabani shawara namasa aure zai daina irin wannan shigar da temakon matarsa, nikuma nayaba da hankalin 'yarku, uwa uba tanada hakuri, shikuma d'ana yanada tausayi, nasan cewa da temakon ta zansamu Allah ya shiryamin shi, yana fita wasu qasashen yana ayyuka yanzu hakama bayanan,kuma banaso yasan da maganar auren, nafiso kafin yadawo ayi musu auren,

to kaga baba bazai iyu duk Inda yaro zaije nadinga binsa ina ganin me yakeba, amma itaa matarsa dole duk Inda zaije tana tare dashi, kuma idan taga yayi ba daidai ba zata tsawatar masa🙊, bayan neman aure harda neman alfarma nazo akan kuban 'yarnan taku Dan Allah, saboda inasonta har cikin raina Kamar d'ana, sunan yaron nawa Muhammad Kabeer ammma ina kiransa da Baffah, saboda sunan babana yaci "

Malam yayi ajiyar zuciya yacemin" to munji baya nanki, kuma insha Allah duk abinda muka yanke zamu sake tuntubarki "

Tace" to nagode baba, bayan kunyi nazarin, idan kun amince inaso adaura musu auren ad'an qanqanin lokaci ,banaso ayi wasu bidi'a saboda albarkar auren kawai muke buqata, idan kuma baku amince ba daan Allah karku boyemin kawai ku sanar Dani, ina nan ina jiran wayar taku "

Daga nan sukai sallama da ita tatafi, Malam yadubi Abba yace" akira masa Nawal," Umma taje da kanta ta kirata

Malam yadubeta yace"Nawal, kwanaki anzauna dake akan zaki kawomin Wanda kikeso, kin samo wani? "

Jijjiga kanta tayi, gaabanta na faduwa

Malam yasake cewa" to yanzu Nuhun za'a baki? "

Hawaye ne suka zubo mata,zancen zuci tafara, karfa naje ahad'ani da mutumin da ban saniba daga qarshe nazo ina DANA SANI, bayan kuma BURINAH a rayuwa shine mk, to shikuma mk ya gujeni bare inyi tunani tsakanin shida Nuhu WAZAN ZABA?
inama ace zan zamo SHALELAN MK wata rana? Haqiqa danaji dadi arayuwata

Ahankali ta girgiza kai alamar a a

Yace" to shikkenan tashi kije sai abaki wannan bawan Allah da matar nan tazo da maganar sa "

Kuka tasa musu tace" Malam wallahi bana sonsa, banfa sanshi ba,
Dan haka karku bani shi "
Malam yace" Nawal auren wannan yaron Kamar jihadi ne zakiyi, ni kaina abin alfahrina ne ace jikata ta shiryar da wani, tashi kije Allah yamiki albarka"

Daki tashige take kuka tuquru, yanzu shikkenan Babu mk, wacce irin qaddara ce wannan? Ita tana haukanta ashe bama mk din zata aura ba, wanine daban, tayaya zata soshi? Inaa bazai iyuba, bazata iya sonshi ba

Acikin satin Abba da Malam suka fadawa Ummi cewa sun amince, kai tsaye tatafi yola tasamu danginsu maza ta turasu akayi komai aka gama Kamar yanda al'ada ta nuna, aka saka ranar biki kwana kusa, haka gida suka fara shirye shirye aka sanarwa da dangi na kusa bikin Nawal ya matso, anty maryam batayi qasa a gwiwa ba tataho, Umma ko kallan Nawal batayi, anty maryam ce take mata komai, amma cikin ranta tausayi ne fal na 'yar tata

Najma tayi rarrashi harta gaji, abubuwan tsumin da anty maryam take bata batasha, zuwa take tazubar dashi, Data gano haka sai take tsayawa akanta sai taga tasha komai
Abubuwan datake sha yasa jikinta yayi kyau,ko'ina yaciko yayi bulbul musanman Kirjinta, Kamar zai tsolewa mutum ido

Jiki kaam yayi kyau har ya gaji amma zuciyarta Babu dadi

Cikin satin mutanan yola sukazo da sadakinsu ahannu, aka daura auren Muhammad Kabeer, tareda matarsa Nawal Muhammad lawan akan sadaki nera dubu hamsin Kamar yanda Ummi takeso

Sannan suka sake bawa iyayen amarya hakuri kan rashin zuwan Ango, baya qasar idan yadawo zaizo tareda amaryarsa tanuna masa yan'uwanta, amma yanzu yarinya kawai suke buqata, basa buqatar akaita da Komai


Duk yan unguwa kowa saijin labarin auren Nawal yayi, saboda bakowa ne yajiba
Aranar kuma suka dauki amarya, a lokacin da zasu tafi ta qanqame ummah, ita kanta umman kuka take sosai, Najma kuwa daki tashige ta dinga rasgar kuka

Malam ne da kansa yayi mata nasiha Mai shiga jiki akan biyaiyar aure, kuma yanemi tayi masa alqawarin zatayiwa mijinta biyaiya, atake ta dauki alqawari

Yan'uwan umma da Abba mutum biyar ne sukabi amarya, sai anty maryam da Salisu, Sultan yace zaije daga baya

Sunkai amarya lafiya, sun samu tarba Mai kyau, tunda su kaga gidan suka tabbatar ba qaramin gida Nawal tajeba

Kai tsaye Ummi tace akai mata Nawal cikin Dakinta su zauna tare kafin mijinta yadawo, duk lokacin da yadawo qasar saisu shirya d'akinsu dakansu irin yanda sukeso🤣🤣

Washe gari tasa aka musu komai suka dawo gida ta jirgi

Sauran yan'uwanta da sukazo daga yola suma duk sun koma, tunda ba wani event da za'ayi

*** ***** ***

Da yamma Nawal na dakin Ummi tana sallah, bayan ta idar tayi addu'ointa tashafa, tafada duniyar tunani, Allah sarki ummah, kome Najma takeyi yanzu? Hawaye suka zubo mata, tashare
Turo dakin Ummi tayi tashigo Tace"Nawal tashi mukoma falo mana, banaso kina yawan tunani fa, kid'aukeni Kamar ummanki kinji?

Ahankali tace "to Ummi"

Futowa sukai falon, Nawal de tanata ganin tsarin gidan wannan uwar tv din kadai ma ta isa kagane cewa ba qananun mutane bane

Zazzabi yanaso ya rufeta saboda bata saba da esi ba, gara gara de fanka🤣🤣
Ummi na lura da ita tace "meyake damunki?"

Ahankali tace "zazzabi nakeji kad'an"

"subhanallah, bari narage wannan esin saikici abinci kisha magani ki kwanta, Baffah baya nan dasai yamiki allura ya iya sosai"🤣
Amma bari na kirashi nafada masa yana da patient
Wayarta tadau ta kirashi bugu daya yadauka"Baffa yaushe zaka dawone? Kanada maraar lafiya "

Gabansa ne yafadi yayi zatan itace batada lafiya" Innalillahi Ummi meyasameki? "

Tace" kaga nide kawai kataho inason ganinka "
Daga haka takashe wayar

Nawal dake gefe Cikin ranta tace "tofa nikuma nashiga uku, banzo bama ana ban labarin baffa inaga nazo kuma 🤦🏻‍♀🙆🏻

Abinci taci tasha magani, ta kwanta, har dare de bata wani sake da Ummi ba, har washe gari, taji zazzabin nata yasauka

Harma ta gyarawa Ummi 'Dakinta, wdrb d'in da Ummi tace tabude akwai kaya aciki tasaka, shita bude tasaka wata doguwar riga ready made, rigar tamata kyau, sannan tafitar mata da shape dinta, shafaffan cikinta ya kwanta, hips dinta yasake futowa aciki, amma batayi batayi kwalliya ba, sannan tafara goge mata dakin



Ummi na falo kawai sai ganinsa tayi yashigo hankali tashe
Cikin murna tace "oyoyo Baffah nah, sannu da zuwa,"

Zama yayi akan kujera jagwab yadafe kansa 🤦🏻‍♂yace "yanzu Ummi fisabilillah , kinsan qalau kike shine kika tasoni?"

Cikin Murmushi tace"to yanzu bagashi naganka ba, dama akwai maganar danakeso muyi dakai "

Kafin yayi magana ta d'aga murya tafara kiranta "Nawal! Nawal!
'yata Nawal

Cikin ransa yake fadin Ummi da kwashe kwashe take wallahi,kowa ta kwaso harta bata iznin shiga cikin dakinta? 🤔

"ya kalleta yace" Ummi kinyi Sabuwar mai aiki ne? "😳🙆🏻😱

Kallansa tayi tace" A a, ba Mai aiki bace, Matarka ce Baffah, aure namaka ai "🤣

Cikin sauri yazabura yamiqe tsaye yace" wai wanne Baffan kike nufi ne? "

















Mutara zuwa gobe


(kullum de maganar guda daya itace hakuri, mudinga hakuri da junanmu yan'uwa, sai kaga Allah ya azurtaka ta Inda baka taba zatoba, idan kukai dogon tunani zaku gane cewa Shifa Anwar Kamar alkhaairi ga Rayuwar Nawal, yayi mata cin mutunci tayi hakuri ta dauki qaddara daga qarshe ga abinda hakurin yajamata, Sanadin ta yan'uwan ta zasu shiga makaranta, still sunyi karo gashi de shine da laifin amma itace ta bashi hakuri, Sanadin hakurin gashi Allah yahadata da mahaifiyar mk cikin Ruwan sanyi, itafa duniyar nan idan kayi hakuri ka dauketa asannu wallahi zakaga daidai arayuwarka, abinda nakeso mutane su gane har nake wannan haqilon typing din wallahi shine fa'ida da amfanin hakuri)


Masu cewa nayi 2pages kuyi hakuri, duk Wanda kukaga anyi muku posting dinsa to aranar na zauna na rubuta, bazai iyu nayi sau biyu ba, mu lallaba ahakan de🤣



















Sharhi sharhi pls🙏🏻


Sorry Nuhu kaban tausayi wlhy😭

Yaya zaman mk, Baby, da Ummi zai kasance? kubiyoni🤗






















Amnah El ✍🏻🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


21&22


"To Baffah nawa nake dashi inba kaiba?"


Kansa dake masa barazanar rabewa biyu yadafe🤦🏻‍♂, jiri-jiri yafara daukan sa yatafi luuu zai fadi tayi saurin tashi ta riqoshi tareda zaunar dashi akan kujera
Idanunsa sun kad'a sunyi jajir, yafara furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un" sai kuka 😭
Kuka yafara Kamar qaramin yaro

Ita kanta Ummi jikinta ne yayi mutuqar sanyi, al'amarinsa yayi masifa tsoratata, rabon dataga kuka a'idon Baffah ita kanta ta manta

Kuka yake sosai yadafe kansa da hannayensa duka biyun, cikin hawaye ga idanu yayi jajir yajuyo ya kalleta "why Ummi? Ummi meyasa? Meyasa zakimin haka? Ummi akwai yarinyar danake so, akwai yarinyar da d'anki abin sonki yake mutuwar so Ummi, ina cikin tashin hankali kullum sai nayi mafarkin ta, naqi sanar dakene saboda inaso saina nemota, haba Ummi, meyasa Dan Allah?" yasa tafukan hannunsa Yarufe idonsa dasu Idanunsa naci gaba da tsiyayar hawaye

Adede wannan lokacin tafuto daga cikin dakin Ummi, Gabanta ne yafara faduwa ganin wani hadadden gaye yana kuka tuquru, ko shine Baffan? Ta tambayi kanta
Tsananin mamaki yakamata Babba Kamar wannan yana kuka

Ummi ce tadago taganta, cikin sanyin jiki tace"zoki zauna Nawal "

Jin ankira sunanta akusa yasa yadago kansa yazuba mata wani kallo me kama da harara,still idanun nasa na zubar da hawaye, gabansa ne yafadi Wanda shi kansa baisan ma'ana da dalilin hakanba, kuma arasa waza'a aura masa sai wannan ficiciyar yarinyar dazai iya karyawa Tun adaren farko

Adarare taje kusa da Ummi ta zauna tareda sunkuyar da kanta

Ummi ta dubeshi "Baffah, naji bayaninka, kayi hakuri Umminka tamaka laifi, tayima aure batareda saninka ba, nayi tunanin Zan iya zartar maka da kowanne hukunci ne amatsayina na mahaifiyar ka, amma kayi hakuri"

Wani sabon hawayen ne yazubo masa, yasaka hannu ya share, "A a Ummi, kiyi hakuri ba haka nake nufi ba, kin kalli zancena ta wata fuskar ne, kiyi hakuri"

Quri Nawal tayi da ido tana kallansa harya gama maganar, Gabanta yana faduwa da sauri


Tausayinsa ne yakama Ummi, tace"shikkenan, Allah yayima albarka, bansan cewa akwai yarinyar da kakeso ba,amma yanzu ma lokaci bai qureba, duk lokacin daka sameta, zaka iya auren ta, amma yanzu de, ga yata Nawal nan, Baffah ka riqemin ita amana, "

Wani irin qullutun Baqin ciki ne yazo wuyan Nawal, kowa yanada Wanda yakeso amma antashi anwani hadasu da juna, jin cewa yanada wadda yakeso yasa mk yafado mata arai, batasan lokacin da hawaye suke silalowa daga idanuwanta ba

Jin bece komai ba yasa Ummi tasake cewa "Kayi alqawari?"

Still baiyi mata maganaba yadaga kansa

Hannunta ta miqa masa tace "bani"

Ahankali ga idanu jajir yace "ban siyoba"

"baka tabaamin qaryaba, banaso kafara, qaryar bata dace dakai ba kwata kwata," tasake miqa masa hannu batare datace komai ba

Ahankali yasa hannu cikin cikin wandon jeans din jikinsa yadauko wata akwati yar qanqanuwa irin wadda zobe yake zuwa aciki, yadora mata atafin hannunta

Budewa tayi taga zoben Dan qarami dashi yayi kyau, atsakiyarsa akai harafin 'n' din, saika zuba ido sosai zaka gani

Ta kalleshi tace yayi kyau sosai, gashi ka karba kasaka mata, hakan zai nunamin cewa alqawarin daka daukamin nacewa zaka kula da ita yana nan "

Zuciyarsa Kamar zata fashe saboda haushi, ya karbi zoben yariqe baiko kalli Inda takeba

Ummi ta dubi Nawal tace" 'yata share hawayen ki, kiyi hakuri kinji, tashi kije yasaka miki zobenki "

Hawaye ne yazubo daga idonta Ahankali ta tashi taje gabansa ya tsugunna, amma ta kasa kallansa, wani irin kwarjini yaamata, yanzu wannan Babban ne mijinta?take tambayar kanta

Ummi ta kallesu tace" menene haka Kamar wani me laifi dame neman yafiya?please kutashi tsaye mana"

Ahankali ta miqe tsaye, shi kuwa saida yadebi wasu seconds sannan yatashi tsaye shima

Ummi tace "Nawal bashi hannu"

Ahankali tadaga farin hannunta dayaji zanen fulawa tamiqa masa

Ganin Ummi tana wajan yasa yakai hannunsa yakama nata hannun, wani irinsa zirrrr yaji tundaga kansa har tafin qafarsa, duk rungume rungumen mata da yakeyi bai tabajin hakan akan kowaba sai akanta
Tafin hannun nata laushi, Ahankali yafara tura zoben harya gama saka mata, yana gamawa yasaki hannun nata, yakama hanyar fita daga falon

Ummi tace "ina zakaje?"

Cak ya tsaya a Inda yake, bai juyo ya kalleta ba yace "Ummi Zan fita ne"

"kadawo ka zauna, koka Manta kai Ango ne?, sannan idaan zaka fita matarka yakamata ka fadawa"

Baqin ciki ne yakama shi, Kamar zai fashe da kuka haka yadawo ya zauna yakawar da kansa can gefe, kwata kwata Yaqi kallan Inda take ma

Har azahar haka suke wannan zaman kuramen, Ummi tana lura dasu kuma ba tayi musu maganaba ta qyalesu, tasan cewa rashin sabo ne kawai, zuwa Dan wani lokacin zasu saba

Ummi ta kalleta tace" Nawal tashi kizuba mana abinci, Karki zubawa Baffah da yawa, bayasan cin abinci "

Cikin nutsuwa tace "to" ta tashi tanufi kitchen din


Kamar yanda Ummi tace haka tayi, amma tana tsugunnawa agabansa da abinci yamiqe tsaye

Ummi tace"ina zakaje? "

" masallaci zanje Ummi" abinda yace kenan

Tace" idan ka'idar kadawo gida "

Bece da ita komaiba yafice, haka kuma yana idarwa yadawo ya zauna yayi tagumi 😱🙉yana kallan tv
Shide wannan zama kawai Dan dole yake yinsa🤣🤣


*** ***** ***

"umma ashe Najma batada lafiya, saida nazo yanzu naga jikin nata"

"Nasrin wallahi kinganta nan tunda Baby tatafi takwanta jinya, zazzabi yarufeta, datawo nan ta kwanta a'inda Baby take bacci"

"Allah sarki, Allah yabata lafiya, Umma yaya wajan Babyn kuwa? Inata kiran wayarta akashe"

"eh nima Tun dazu nake kiranta bata shiga, amma nasan idan tabude wayar zata kira mu"

Jinjina kai tayi tace"Allah sarki Baby, toshknn umma bari natafi gida, "

" to Nasrin ki gaida mamanku, ga wannan kikai mata "tabata wata leda

Tace" to umma sai anjima "


*** ***** ***

Har dare suna zaune kowa yayi shiru, yana zuwa sallah Ummi zatace yana idarwa yadawo
Har qarfe tara na dare suna zaune suna kallo

Amma shikam kawai yana kallan photon cikin ne, amma baya fahimtar komai, Baqin ciki ne cike da ransa fuskarsa Babu alamun annuri atamke

Ummi ta kalleshi "Baffah adakina nace Nawal ta zauna kafin kadawo, tunda kadawo gobe saikuje ka nuna mata dakin naka, saiku sake gyara shi zuwa yanda kukeso"

"No Ummi kawai kibarta anan din zaifi,"

"wai Baffah meyake damunka ne? Cemaka akai itama yarinyar tanaso ne?"

Cikin ransa yace"tanaso mana, idan bataso ai bazata yardaba, shi Dan bai saniba ne, aida bazai yarda ayi ba, ciki ciki yace mata "Ummi bansaba kwana da kowa bane ad'akina, bayan hakama d'akin yamana kad'an"

"duk wannan uban dakinne zakace yamuku kadan? Saikace wata giwa?" 😂

Shiru yayi baice komaiba
Sai cika yake yana batsewa

Ummi ta kalli gefen da Nawal take zaune, sai taga har tayi bacci

Ta maida Kallanta gareshi tace "laa Baffah kaga yarinyar nan har tayi bacci, d'an meqamin ita daki"

Dasauri ya kalleta saboda jin furucinta

Tace"yi sauri mana yarinya tana bacci a kujera kar wuyanta yayi ciwo"

Takaici ne yakamashi, wai Ummi daga ganin yarinya duk tabi ta rikice

Tashi yayi sai qunci yake yaje kanta ya tsaya, amma bashi da niyyar tabata

Ummi tace "mekake jirane?"

Kallanta yayi yaga hankalin ta ma yana kan tashar datake kallo

Hannun rigar jikinsa yafara tattarewa Kamar Wanda zaiyi wanki 🤣
Sannan yakai hannu zai dauketa, hannun nasa bai sauka ko'inaba sai akan hips dinta, cikin sauri yajanye hannunsa daga wajan
Sannan yadauketa cimak yayi dakin Ummi da ita, Kamar yanda ya zata haka yaji, batada wani nauyi, to dama wannan ficiciyar yarinyar ina zataga wani nauyi

Saida yakai ta har kan gadon Ummi sannan ya kwantar da ita, garin d'ora kanta akan fillo hular datasa akanta tafadi gefe, dogon gashinta yazubo akan hannunsa, gashin nata yabi da kallo yaga sai sheqi yake kuma da alama zaiyi santsi

Cikin sauri yajanye dayan hannunsa daga jikinta, Wanda gashin yazubo

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment