Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can bana sansa"

Abba yace "Malam ai kaji irin zancen nata ko? Menene laifin Nuhu, yaro da aikin yinsa da Komai,kwanaki har Gida yazo yasameni yacemin yasamu N-power, to me kuma za'a jira, ni banga aibun yaron ba, yajuya ya kalli Nawal yace" to ai saikije ki auri sabulu "🤣

Malam yace" A a ai duk abin baizo nanba, yadubi Nawal "Nawal bayan Nuhun kinada Wanda kikeso ne?"

Shiru tayi, itade tasan bata kula kowanne saurayi, shima Nuhun nacinsa ne yasa bai rabu da ita ba
Lokaci daya yafado mata arai, kode tace shi?

Malam yasake cewa "ke muke sauraro Nawal"

Ahankali cikin rawar murya tace "Malam ni.. ni.. ni MK nakeso"

Lokaci daya duk mutanan cikin dakin suka juya suna Kallanta cikeda mamaki

Abba yace wai yaron daya biya kudin aikin idonki?
Takasa bashi amsa 🤣

Yasake cewa "badake nake magana?"

Nanma tayi shiru 🤣🤣

Cikin tsawa yace "tashi kiban waje mahaukaciyar banza mahaukaciyar wofi"

Cikin kuka ta tashi tayi dakin umma da gudu

Abba ya kalli Malam yace "Malam ai kaga irin shiriritar tata, shifa wannan yaron datake magana akansa Dan bata ganshi bane take wannan haukan akansa, yaron daga ganinsa kwata kwata babu alamun tarbiya atare dashi, Malam da yageggen wandofa yake yawo🤣gaba daya jikinsa awaje, gawani aski da aka yimasa duk an d'ebe masa gefen kunnansa , shikkenan saboda rashin tunani Zan dauketa na bata shi "

Cikin sauri Sultan ya sunkuyar da kansa kar fadan yadawo kansa, domin kuwa shima irin askin ne akansa🤣🤔

Malam yace" muhammadu abi komai Ahankali, kayi hakuri ta kawo wani daban saika bata shi "

Abba yace" to Malam duk yanda kace haka za'ayi, danhaka ta gaggauta kawomin wani , inba hakaba kuwa Nuhun da bataso shizan bata"


Daga hakan taron nasu yatashi



Umma ko takan Nawal batabiba, harkokinta kawai takeyi, inbanda shirme irinna Nawal bakasan mutum ba tayaya zakace shi kakeso, banda rashin hankali

Nawal kuwa kuka take Kamar me adaki ita kadai, gashi umma a dakin Abba zata kwana, ita kadai ce a dakin, haka ta dinga kuka har wajan sha biyu nadare, sannan tashare hawayen ta, tafara zancen zuci, yanzu fa shikkenan batada wata mafita Nuhu zaa bata ko? Yaya zatayi? Kanta yasara tasa hannu tadafe goshinta, 🤦🏻‍♀wayar ta tajanyo zata kira Nas saita fasa saboda dare yayi, Kamar wasa tatafi kan number mk takalli number tasake kallah, har zata wuceta kawai saita dawo takira number

Kamar almara saiga waya yashiga, cikin sauri tatashi zaune tareda furta kalmar alhmdlh, wayar tana ta ringing anqi dauka, tunani tafarayi yau yaushe, afili tafurta" yau asabat, ance baka daukan waya sai rana kun aiki, to wallahi yau saide charginka yaqare amma bazan dena kiraba🤣🤣,
daga kan NAWAL zaka fara amsa waya cikin weekend

Tana kiran wayar akaro na shida taji and'aga













Mutara zuwa gobe





Duk group din dasuka jini shiru ban gamsu da Comments dinsu bane











pls sharhi Dan Allah







Share
Comments Dan Allah 🙏🏻

































Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek



17&18


Shiru yayi batareda yayi magana ba, wayar tasake dubawa taga de gashinan an amsa, cikin sanyin murya tace "salamu alaikum"

Dukda Idanunsa alumshe suke hakan bai hanashi budesu ba, cikin ransa yace"wow zazzaqar murya "
Afili kuwa daqyar yace" Wacece ke? "

Gabanta ne yafara faduwa, duk wannan qwarin gwiwar nata datake ganin zata iya tunkararsa da tayin soyaiyar ta saitaji takasa, cikin rawar murya tace" please da mk nake magana? "

" yeah" shine kawai abinda yace

"Dan Allah idan Babu damuwa inaso zamuyi magana"

"bana amsa waya a'irin wannan lokacin, na baki minti daya kifadi abinda ke tafe dake"😖


Cikin ranta taji sanyi, ko banza de yau tayi waya dashi tace
"inaso na gayyaceka zuwa gidanmu, akwai Wanda babana yakesan bani, nikuma bana sansa..

Katseta yayi ta hanyar cewa" to shine me? Sorry kiyiwa iyayen ki biyaiya, zakifi ganin daidai arayuwarki that's all "

Qit yakashe wayar sa, baccin daya fara daukar sama ya nemeshi yarasa, meyasa wani lokacin mata basuda damuwa ne? Inba rashin damuwa ba kina mace ki kwantar da hankalin ki mana, nawa Rayuwar ma take? Menene ma aciki Dan anbaka Wanda bakaso din? (kut🤔zaka gani)


gaskiya dole zai sake sabon sim crd gobe, daga zuwansa Gida shikkenan d'an weekend dinma baza'a Barshi yahutaba

To yanzu menene nasa aciki Dan za'a mata auren? Mezaije yamata?tokode sanar dashi zatai yaje amatsayin waliyinta, shiyasa tafara maganar ta naso ta gayyaceshi? 🤔🤣

Tsaki yayi tareda juyawa ya Yarufe idonsa,cikin ransa yace"kuma fa muryar yarinyar akwai zaqi "🤔

(jeka dai 😏ko banza akanta kafara karya aqidarka🤣🤣taqin daga waya

*** ***** ***

Hawaye masu dumi suka zubo mata, shikkenan kuma tata ta qare, Wanda take taqama dashi dinma yaqita, amma duk da haka bazata iya auren Nuhu ba, gara abata wani daban Wanda bata taba ganinsa ba, dade abata Nuhu, idan ta auri Nuhu da tsaftarsa zataji koda tsaftar Gida da yaransa, hawayen idonta tashare, ta futo tsakar Gida tayi alwala, sannan ta koma daki tatada kabbarar sallah, raka'a biyu tayi bayan tayi sallama tasake maida goshinta qasa ta karanta (la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin) sau arba'in da d'aya, sannan tafara kuka tana fadawa Allah buqatunta domin kuwa duk Wanda ya karanta wannan addu'ah to manzon Allah yace bazai dagoba face an amsa masa addu'arsa


Sai tsakiyar dare ta kwanta, washe gari haka ta tashi kanta nayi mata wani irin mugun ciwo saboda damuwa, Abba taje tafara gaisarwa ya amsa mata fuskar sa Babu yabo Ba fallasa😃

Sannan takoma wajan umma tsakar Gida tafara tayata aiki, anan take sanar da ita abinda Abbanta yace dangane da kawo miji

Shiru tayi batace komai ba, tome zatace? Wanda take taqama dashi din shima ya watsa mata qasa a ido, baabu Inda zataje tanemo wani mijin, zata jira har lokacin daza'a sake kiranta a tambyeta inyaso saita sanar dasu cewa subata koma wanene amma banda Nuhu 🤣🤣

Umma tace "kinyi shiru"

Ahankali tace "naji ummah"

Sai azahar yaya Sultan ya shirya yatafi bayan yagama kwantar mata da hankali cewa insha Allah zata auri Wanda takeso

Abincin kirki takasa ci, duk idonta yafada yini daya kawai,
Da yamma tana zaune afalo mus'ab yashigo yace "yaya Baby Nuhu yazo"🤣

Tana jinsa tayi banza ta share shi, qarshe ma tsakar Gida tadawo ta zauna, kusan minti talatin tadauka azaune atsakar Gida itadasu umma da mama, Yaya Salisu yashigo gidan yadubeta yace"ke ba Nuhu nagani a kofar gida ba? Koba wajan ki yazoba? "

Cikin haushi tace" ba wajena yazoba yaya, tunda in wajena yazo ai zai fadamin yaya "

Umma datayi shiru tana jinsu tace" ba wajan ta yazoba Salisu, wajena yazo, ai kasan bazawari nane"🤣🤣

Idonta ne yaciko da kwallah tatashi ta shige daki tadauko hijabi tasa tafice
Mama mariya tace "kuma de kun dauki Nuhun nan kunsashi aranku saikace wani dan'uwanku, tunda yarinya bataso aqyaleta mana, shi inbanda shegiyar jaraba da naci yau kakira mace gobe ka kirata kajera sati daya kana nemanta amma ita ko flash ai anan ma kadai zaisa kafara tuhumar kanka, amma saboda duhun kai Yaqi ganewa, ita yarinyar nan inkazo ruwan nera biyar ba baka takeba, ba kiranka takeba, ba text take makaba, amma kadage kai ala dole sonta kake? Wallahi Inda wajan Najma yake zuwa rufe kaina zanyi inje ince karya sake zuwa kofar gidan nan"🤣🤣

Umma tace "to Mariya tunda bata sanshi ai saita kawo wani"


Tana zuwa kofar gida ta ganshi a tsaye, farin yadi ne ajikinsa itade tunda takeda Nuhu bata taba ganinsa da wani kalar kayan ba, kullum cikin farin yadi yake, kallansa tayi daga saama har qasa, idanunta yasauka akan hannun rigarsa yayi duqun duqun yayi baqi, haushi yakamata, ba ance tunda bata sonsa meya hana ta fada masa ba? yau kuwa za'ayi ta taqaare, tace "sannu Nuhu"

"yauwa my heart"

Tace "Nuhu, akwai abinda nakeso nasanar dakai, maganar gaskiya Nuhu, ni bantaba sonka ba, kayi hakuri banajin Zan iya aurenka, abu ne me girma awajan mace ta kalli d'a namiji tace bata sonsa, zaiyi wahala mace ta fadawa namiji haka, amma tunda kaga nabudi baki nafadama hakan agabanka baqaramin rashin so nake maba, nanunama ta hanyoyi da dama yanda zaka gane amma kakasa fahimtata, hannunta tahade waje daya 🙏🏻Dan Allah Nuhu kafita daga rayuwa ta, bakamin laifin komai ba, haka kawai Allah bai sakamin sonka acikin zuciyata ba, "

Daaga nan tawuce gida tabarshi a tsaye

Batafi minti biyar dashiga gidaba saiga Nura yashigo da leda ahannun sa, yabawa umma yace" umma gashi inji Nuhu wai yaya Baby ta Manta, natane "

Umma ta karbi ledar

Mama mariya tace" Allah yarufa Asiri, aida kabar masa kayan sa, d'an me naci"🤣🤣

(mamafa tadage😂😃)



*** ***** ***

Washe gari Nuhu yadawo, wannan karon dayazo kiranta yayi awaya, tana gani tayi rejecting, haka sukai tayi har sau hudu sannan ta daga ana biyar
Yace "Malam Nawal nazo ina kofar gida"

Tace"akwai abinda nakeyi, meyahanaka kira ka fadamin cewa zakazo idan ina nan shikkenan idan bana nan basai kazo ba? "

" kiyi hakuri minti goma yayi yawa kindawo gida "

Tace" dama ai ko baka fadaba "

Umma tasamu afalo tazo zata wuceta tace" ke ina zaki? "

Ciki ciki tace" kofar gida Zani wajan Nuhu "

" yawwa nina Manta ma ga kayan daya aiko miki dasu jiya can a dakin Abban ki, takalmi ne da mayafi sai kuma mayuka da turare"

"umma kibadasu kawai ni banaso"

Daga nan tafice kofar gidan, ko gaisawa basuyi ba tace masa "gani"

Ya kalleta, "malama Nawal naji bayananki, ko menene dalilin dayasa bakya sona?"

"haka nan, haka Allah yasa"

"nima naga alamomin dakike nunamin, amma ban kawo komai arainaba, sai naayi tunanin yanayin ki ne haka, sannan ni inason ki Nawal, wallahi duk sati saina kaiwa malamai kudi sumin addu'ah akanki, 😳akan Allah ya tabbatar mana da alkhaairi"

"Innalillahi, Nuhu kace har wajan malamai kake kaini, to in Allah ya yarda Babu abinda zai sameni"

"ki saurareni Nawal, bawai da wata niyya naje wajan Malamai ba, nafada miki manufata"

"Nuhu, kaida kanka kace ka fahimci abinda nake nunama, kaga kenan kasan cewa bana sonka, amma shine kaqi rabuwa Dani, to daga yau nakawo karshan alaqarmu, Babu wani me tunani dazakace masa kaje wajan malamai akan wai Allah ya tabbatar mana da alkhaairi, saide in da wata manufar Nuhu "

Yace" to duk meya kawo wannan maganar ne?, kode agida ance za'a miki aure ne shiyasa kikace bakya sona? "

" nikuwa waye zaimin aure yanzu Nuhu, nifa nafadama kawai kai dinne baka minba "

Yace" toni ina sonki, kuma bazan rabu dakeba, sannan abinda baki saniba shine Tun jiya da kikamin wannan maganar nazo nasamu Abba ya fadamin komai, Dan haka yanzu nafara zuwa wajan ki, bazan dena zuwa wajan ki ba sainaga abinda hali yayi, muzuba mugani "(🤔🤔karfin hali)

Tace" Ok haka kace? "

Yace" haka nace Nawal, inason ki bazan raabu dakeba, sannan zuwa bazan fasaba, tunda ni ina sonki ban damu daki soni ko Karki soniba, muyi tayi NI DAKE, Allah yabawa Mai rabo sa'ah, abinda nasani shine bazan taba rabuwa dakeba "

Cikin Baqin ciki tace" to insha Allahu Allah yafika "
Daga nan ta fada gida

Tana shiga daki ta dinga kuka, idanunta sukai jajir, kanta har sarawa yake, Wacce irin masifa ce wannan? Dame zataji? da wulaqancin mk koda nacin Nuhu 🤣🤣?

Najma ce tashigo dakin taganta tana kuka, ta zauna agefenta tace" Baby kiyi hakuri, komai yayi farko zaiyi qarshe, kidinga addu'ah insha Allah zaki dace, ni kaina banji dadin hukuncin da Abba ya yanke akanki ba, amma insha Allah bazai baki Nuhu ba "

Cikin kuka tace" nagode sosai Najma "

Haka ta kasance Awannan gida har tsawon sati biyu, Abba yana hankalce da ita, yana kuma jiran takawo masa wani amma shiru kakeji, duk tunani yayi mata yawa, ta rame, idan tazauna ita kadai banda tunani Babu abinda take, haka zata zauna tana tunani inama ace ta auri mk suna Rayuwar su gida daya, koda ace baya sonta zata koya masa yanda zai sota, data tuna wulaqancin daya mata kuma sai fuskarta ta canja zuwa bacin rai, gashi bata zuwa makaranta bare tasamu tadan rage kewa, har yau ko Nas takasa bawa labari, tunda me faruwa kaam tariga Data faru, Babu wata shawara da Nas din zata sake bata ayanzu su aikata ta har afasa auren itada Nuhu, tunda abayama sun gwada wata dabarar abin bai yi musu dadi ba 🤣🤣🤣


*** ***** ***

Hankalinta yana kan computer dake ajiye agaban ta, idanunta sanye da medical glass, farar mace ce Mai kimanin shekaru hamsin aduniya,cikin sauri take typing a computer kai bazaakace tana kallan wani wajan daban ba, agefen ta wata matace azaune hannunta dauke da waya tana dannawa, suna mutuqar kama da juna, saide dayar bata kai me aiki a Cumputer tsawon shekaru ba


Cikin sauri yafuto hannunsa dauke da lemon steam na gwangwani, Rigace crezy ajikinsa fara me had'eda hula, duk gaban rigar atsatsage yake,🤦🏻‍♀ wandon jikinsa jeans me launin dark blue shima din crezy ne

Wucewa yazo yi ta Gabanta Kamar bega baquwar dake tareda ita ba

Hankalinta yana akan typing din da takeyi tace"BAFFA"

cak yadakata daga tafiyar da yakeyi

Still Hankalinta yanakan computer tasake cewa "Go and change your clothes"

Kallan kansa yayi tundaga rigar jikinsa har kan wandonsa cikin shagwaba yace"Ummi what's wrong whith wannan kayan? "

" kakoma ka canja nace, kokuma kafasa fita Inda zaka je "

Kamar zaiyi kuka ya tsaya, shi baiyi gaba ba, shi baiyi bayaba

Matar dake kusa da ita itama ta kalleshi sosai, cikin fuskar harara tace " Use muhammadu"(Sannu Muhammadu)


Kallanta yayi,da niyya yayi ya qyaleta, yatsani matar nan tazo gidansu

Ahankali yadawo yazo Gabanta ya tsugunna fuskar nan atamke yace" Walijam yafendo "(ina kwana yafendo)

Saida ta harareshi sannan tace" Sejam kalau"

Be qara yimata magana ba yamiqe yayi hanyar fita

Sake tsinkayar muryar ta yayi tanajin cewa "ban'isa dakai ba kenan"

Kallanta yayi "Ummi Babu Inda zanje, part dina zanje nahuta i am tired"

"dawo ga ayyukan office nan agabana sunmin yawa, kazo ka dauki wani kayi"

Dawowa yayi ya zauna badan yasoba yadauki takardun dake Gabanta yana dubawa, bayasan aiki cikin weekend ko kadan, yafison ranakun aiki kawai ayi aiki, ranakun hutu kuwa ahuta

Saida tagama typing din sannan tarufe computer ta dubeshi "akwai takarda da aka turomin daga Bayero university kano, akwai taro daza'a gudanar na murnar bude sabon department dinsu, so ina ganin kawai kaje, kaga nima saina huta,"

Kallanta yayi yace "Ummi kano?"

"eh kano"

"Ummi kiyi hakuri, amma bazan sake zuwa kano ba, 🤣🤣gaisuwar dakika turani kwanaki ma masifa tazamemin"
😳🙊😃

"subhanallah wacce irin masifa kuma acikin gaisuwar?"

"kede Ummi ki shirya kije, amma nide inkinganni alahira kai ni akai" 🤣🤣

Tsaki tasaki kawai tarabu dashi

Shima da yaji tayi shiru kawai saiya tattara takardun gabansa yafice daga falon

Yana fita yafendo ta dubi matar da aka kira Ummi tace "wai yanzu Addah haka zaki zubawa BAFFA ido kina kallansa?yaro yagirma harya gaji da girma baabu aure 🤣🙊"

"to yafendo yaya zanyi? Baffa yafara fin qarfina,"

"ga shawara Adda, mezai haana kimasa aure"

"to yafendo dawa?saide ko nahada shi da Bintu tawajanki"

"Adda Bintu da masifa muhammadu da miskilanci da rashin son raini wataran gidansu kamawa zaiyi da wuta" 🙆🏻🤣

Ummi tace "to Allah yashige mana gaba"


*** ***** ***

Wasu mutane ne suka aiko ana sallama da Abba a kofar gida
Abba na fita yaga wasu magidanta sunkai su hudu, ya basu hannu suka gaisa
Babban cikin su yace"Alhaji mune wakilan Nuhu, yazo ya samemu yayi mana magana akan cewa zakayi wa yar wajan ka aure, kuma kai ara'ayinka shi kakesan bawa, shine yace muzo mu nema masa auren, shi yana so ma abin karya wuce wata biyu "

Abba cikin ransa yace" to banda abin Nuhu basai agidan yarinya ance katuro ba"🤔🤣
Amma afili yadubesu yace "eh to akwai de yiyuwar wannan maganar din, amma de dadan sauran lokaci bha yanzu ba, afada masa insha Allahu idan abin yataso za'a nemeshi, ina jiran ita yarinyar ne akwai abinda nake sauraro daga gareta, idan naji shiru sai azo ayi maganar daga baya"

Cikin Fara'ah suka sake bashi hannu suma suka gaisa, sannan sukamasa sallama suka tafi

Abba yajima a kofar gidan kafin yashiga gida, Eh lalle yau ya tabbatar cewa Nuhu soko ne🤣🙊

Inbanda soko gidan iyayen yarinya aisune suke faraba cewa aturo

*** ***** ***

Bayan kwana biyu Nasrin ta kirata awaya, cikin sauri ta dauka"Nas nah, kwana biyu, Kamar kinsan ina nemanki,"

"beauty kenan idan kina nemana meyahana ki zo gidanmu, kullum saide nazo, wannan zumuncin inaga denawa zamuyi"

"haba Nas kiyi hakuri, ina cikin damuwa ne, akwai maganganu dayawa, ciki harda hanani zuwan makaranta da akai"

"menene yake faruwa?"

"Nas Abba aure zaimin, Nuhu zai bani, yanzu haka bana fita ko'ina , school din yace ya cireni"

"Innalillahi qawata Nuhu kuma? Kinga kishirya kizo muhadu a makaranta yau, saimu tattauna anutse, gashi yau ana taro a mkrntar baki gaba, harda sarki ma yazo, ga baqi sosai harda turawa wallahi"

"Allah Nas?"

"wallahi beauty, kema kisamu kifuto harkya dansha iska,"

"to Nas karfa asamu matsala a hanani zuwa"

"kinjiki da wata magana, cemusu zakiyi zakije school ne? Kicewa umma zakizo gidanmu shikkenan kawai"

"to shikkenan Nas bari nashrya"

"Amma fa Beauty kiyi kwalliya, Dan wallahi bakiga dalibai ba kowa yayi kyau"

"to Nas saimun hadu"

Tana kashe wayar dama tayi wanka, kawai Mai tashafa, ta bude jikinta da turare, wani less dinta ta dauko orange, da akai mata dinkin doguwar riga,gaban rigar anyi mata breast cup,


Dinkin yahau jikinta, yayinda ta nannad'e dogon gashinta tamaidashi Kamar ribom , tayi daurin dankwali Mai hawa hawa, tafitar da ribom din gashin nata 🤣 waje, sosai ta tsara kwalliya tayi masifar yin kyau tayafa mayafi da yaar qaramar jakarta, Kamar gaske taje wajan umma tace "umma kwana biyu Nasrin bata zoba, zanje naduba ta ko lafiya "

Umma tazuba mata ido tanaso tagano gaskiyarta, bataga alamun komaiba, Dan haka tace" to saikin dawo "

Tana fita bata jira adedeta a kofar gida ba, saboda tana tsoron baba yazo, cikin sauri tatafi bakin titi tatare wani tahau
Tana zuwaa school din takira Nas awaya, bayan sun hadu Nas tace" wow, wai beauty kinga yanda kikai kyau kuwa?"
Wallahi yau kike a beauty dinki, saide kuma kin rame"

"badole narame ba Nas, Nuhu yasakoni agaba"🤦🏻‍♀

"bani labari meke faruwa"

Nan take Nawal tabata labarin komai

"kiyi hakuri Beauty , Allah zai kawo mana mafuta, ki kwantar da hankalin ki, zomuje wajan taron"

Tafiya sukai wajan da ake taron, sai daga nesa suke hango sarki, tareda manyan baqi, pictures Nasrin tafara yimusu awayarta, sosai sukai kyau

Suna daga gefe a tsaye suna kallo Nas tace" Beauty bari naje nasiyo mana kek nadawo, kijirani

Tace "to Nas saikin dawo"

Kallan yanda aka qawata wajan kawai takeyi, Ahankali tafara zagaya wa kafin Nas tadawo,mutane ne suka fara tashi alamun harma angama taron
Dan haka ta dauki wayarta zata kira wayar Najma, hankalin ta nakan wayar kawai sai jitayi tayi karo da mutum, har wayar hannun ta tafadi qasa, dagowar dazatai kawai sai taga Anwar

Gabanta yafadi, tsoro yakamata, amma saitaqi nunawa, Ahankali tace masa "sorry


Shi kuwa yana ganin ta yaganeta, dama ga haushin dukan da yayanta yayi masa 🤣

Cikin fishi ya nunata da hannu yace "ke makauniyar inace ke? Kina tafiya bakya kallan gabanki??

Duk da tana cikin tsoro Ahankali tasake cewa" kayi hakuri "

Kafin yayi gaba saida yasa qafa yatake mata wayar, sannan yatafi

Cikin ranta tace" kanka akeji, ta sunkuya tasa hannu ta dauki wayarta "

Duk abinda suke akan idonta komai yafaru, yarinyar tanada hakuri, shi da niyya ya bigeta saboda yana kallan gabansa ita kuma hankalin ta yana kan waya, amma duk da haka itace ta bashi Haquri,sannan bata nuna bacin ranta akan take mata waya dayayi ba

Duban direbanta tayi," munzaali kana ganin abinda nake gani kuwa?"

"nagani hajiya, wallahi naga komai"

"Yaya kaga yarinyar?"

"ai tayi sosai hajiya, billahil lazi Kamar wankan inji" 🤣🤣

Murmushi tayi tace" sai nake gani tunda sun samu sabanin halaiya itada Baffah Kamar zasu zauna lafiya "

Cikin girmamawa munzaali yace" aaa sosai hajiya,wannan zata dauki komai "

Cikin takun nutsuwa matar tataka ta qarasa gareta tace "Qawata wayar taki tafashe ne?"

Dasauri ta juyo sukai ido hudu da wata mata, daka ganta kaga bafulatana

Murmushi tayi, abinda yafara futowa daga bakinta shine "ina wuni?"

Wani irin dadi taji yakamata, tace"lafiya kalau, gidanku anan kusa yakene kikaimu muyi sallah? "

Kafin tayi magana Nas ta dawo, tace" Beauty ina kika shiga sai nemanki nake? "

Tace ina nan Nas, ai kinga har antashima kawai Zan tafi gida"

Ita de Nas taga mace akusa da ita, bata tambyeta ba, tadubi matar ta gaishe ta, sannan tacewa Nawal" to sai munyi waya, ga kek din naki, ki gaida umma "

Tace" to Nas "

Tana tsaye tana kallansu cikin birgewa, daga gani qawaye ne makusanta

Ta kalli matar tace mata "to Muje"

Tafiya suka fara yi, matar ta dubeta tace" kinga ga Mota can Muje saiki masa kwatancen gidan "

Tace" to, amma cikin ranta mamaki take, wacce irin macece wannan, dole sai a gidansu zatayi sallar? Yanzu idan takoma gida Abba yace ina suka hadu matar tace makaranta yaya zasu qare dashi? Shknnn ita kuma tasan kawai yau asirinta yagama tonuwa 🙆🏻🙆🏻

Direban ne yazo da sauri yabude musu motar gidan baya, matar ta dubeta tace "shiga "

Ahankali ta shiga, tana shiga qamshi yaratsa hancinta, ga sanyin esi daya cika motar

Itama ta shiga dreba yaja suka fara tafiya

Suna kan hanya matar ta kalleta tace "sainaga Kamar wayar taki zata iya samin matsala,"

Murmushi tayi kanta na qasa tace "a a hajiya, Babu komai wallahi"

Cikin sigar wasa tace "lala ba sunana hajiya ba, sunana Halima, amma d'ana Baffah yana kirana da Ummi, kema zanso ki fadamin hakan, Yaya sunan kine?

Ahankali tace" Ummi sunana Nawal "

Murmushi Ummi tayi tace" Nawal daurin dankwalin naki yamin kyau, duk lokacin dazan fita unguwa idan Zan daura dankwali d'ana Baffah qwacewa yakeyi yace shizai daura min, yanaso yadinga min kwalliya "

Cikin ranta tace yau nagamu da uwa Mai jarabar son danta 🤔😂😂
Zance daya biyu sai ta saka shi ciki?

Amma kawai sai tayi Murmushi tace" Allah sarki "

Ummi tasake cewa" muga wayar taki? "

Nawal ta miqa mata wayar, tana karba tace" gashi kuwa har screen yafashe "

Jakarta ta zuge tadauko wata waya qirar iphone tabata tace" ga wannan wayar Babu komai acikin ta, zaki iya cigaba da amfani da ita kibada sadakar wannan dayar, nima Baffah ne yakawomin lokacin da zaizo "🤣🤣

Dasauri tace" a a wlhy kibarshi nagode, wallahi Babu damuwa Zan iya amfani da tawama ahaka,"

Ummi tace" a a, Nawal, Inda tare nake da Baffah to zai iya marinki, saboda bayaso kokadan yaga ana ja'inja dani" 🤣🤣🤣

Ahankali tace "to ngd sosai, Allah yasaka da alkhaairi," cikin ranta kuwa cewa take gara na karba inba hakaba kafin mu sauka saita gama fadamin komai na Baffah 🤣🤣

Da kwatance da Komai suka qaraso gidansu, tareda ita suka shiga gidan , Umma da mama mariya na ganin ta tareda baquwa suka karbeta hannu bibiyu,amma umma kam tambaya ce fal ranta, jira kawai take matar tatafi 🤣🤣

bayan tayi sallah tace" zata tafi amma tanason ganin maigidan
Aka tura Saif yaje yakira Abba amajallisa, har falon umma Abba yaqaraso yaga baquwar fuska, cikin Murmushi tace "Alhaji dama inaso ne zamuyi wata magana"

Abba yanemi waje ya zauna yace "to baiwar Allah gashi kuma bansan kiba"

Murmushi tayi tace "Sunana Halima Jamal Baba, ni mutuniyar Adamawa State ce, naga 'yarka Nawal ne amakaranta yanzu, Wato Alhaji gaskiya kayi kokari kuma ka jajirce akan tarbiyar yarka, nima hakan ne yad' au hankalina akanta harna biyota gida inaso kabawa d'ana Baffah auren ta idan Babu damuwa, bazan boye maba dana bayaji, amma inaso sanadiyar yarka yazama abin alfahri agareni, "
Ta ajiye masa number wayarta taci gaba da cewa" wannan itace number ta, kuma na baka dama kayi bincike akaina Kamar yanda shari' ah ta fada, zaku iya tuntubata daga baya domin naji duk abinda kuka yanke "


Tana gama magana taayi musu sallama tatafi
















Ina fatan zakumin uzuri duk lokacin dakuka jini shiru kunsan jiki da jini😉





Sharhi Dan Allah 🙏🏻














Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek




19&20





Shide Abba jikinsa asanyaye yariqe wannan number, yadubi umma yace "waye yabawa wannan yarinyar iznin zuwa makaranta ne?

" Alhaji wallahi nima bansan cewa makaranta tatafi ba, tacemin de zataje gidansu Nasrin "

Mama mariya tace" nifa Alhaji hankalina bai kwanta da matar nanba, kadubi fa hannunta duk gwala gwalai ne, sannan wacce uwace zata fadi laifin danta? (niko nace uwa tagari 🤔)

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment