Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da waya Nasrin tace"qawata maigida bayanan yatafi cirani "🤣🤣
Harya wuce yajuyo ya kalleta, shine yake tafiya cirani?
Shareta yayi yashige daki, itama bayan sa tabi da kallo ranta na quna idan tatuna da zobunaan data gani

Tashi tayi tashige cikin daki tace" Nas kiban shawara, inaso nakawo qarshan matsalar gidan nan "

Nas tace" to yanzu kuwa Zan baki shawara, menene yake miki Wanda bakyaso?"

" Nas bayacin abinci na, babu magana Mai dad'i, kullum acikin aikin doka nake, karfe bakwai dede nafita nafara aiki, sannan kayanda Ummi takeso yadena sawa ta zubamin ido tana jira taga result amma har yanzu nagagara yin komai"

"Beauty maganar gaskiya itace kinada tsoro, kuma dole saikin dena jin tsoron sa sannan ne zaki gyara gidanki"

Tace "Nas haka Ummi ma tace"

"ato kingani, dole saikin dena tsoron sa, sannan tunda kinyi biyyaiya ai kin fita haqqinsa, tunda haka yakeso kema ki zama mahaukaciya, zaku fi dedetawa"

Nawal tace"a a fa Nas, Karki bani shawarar dazanzo ina kuka daga baya, kinga shawarar zuwa Abuja ga yanda ta qare mana 🤣🤣sannan shawarar zuwa makaranta haka kikasa nazo qarshe nahadu da Ummi nanma Abba yahauni da fada🤣🤣🤣"

Nas tace" Karki damu, ki gwada wallahi "

Daga nan sukai sallama


Tana kashe waya tace" goben wasan zai fara




Washe gari ta dinga jira yafita, bai fitaba, sai yamma yafita, yaje gidan Ummi

Tana ganin fitarsa tashige cikin d'akinsa, kayansa qananu Wanda suke crazy da riguna Wanda taganta da yaga ko kadan ce, tadinga debowa tana zubasu akan gado😳😳

Saida ta kwashe duk kayansa crezy sannan taje harabar gidan ta zubasu waje daya
Kitchen takoma tadauka fetir 🙆🏻😳

tadaga bakin jarkar ta kwara musu😳😳🙆🏻

Sannan ta qyasta ashana ta banka musu wuta

Nan da nan wuta takama kaya taanaci

Adede lokacin yadanno hancin motarsa cikin gidan yaga hayaqi yana tashi, ga Nawal a tsaye a gefe
cikin sauri yabude motar yafuto yaqaraso wajan


Kayansa yagani yanaci da wuta 😳yace"kai kai kai kayana kika qonamin? "

Tace" to menene amfanin su? Banaso naga kana sakawa, sannan amatsayina na matarka, inada haqqin hanaka sakawa "

" nikike na fadawa wannan maaganr saboda rashin kunya? Kewai mekike taqama dashi ne? Bafa sanki nakeba inada wadda nakeso, bazakizo har gidana ki nemi ki dagamin hankali ba"

Dama ga haushin wannan zobunan daga gani adakinsa yana cin ranta, cikin bacin rai tace"to ni din cemaka akai inasonka?inada Wanda nake sosai nima mutum Mai tausayi da hangen nesa "

" Karki sake ambatar sunan wani a cikin gidannan, sannan abu na qarshe, yafara tafa hannunsa yace"nagaji da halin ki, ki tattara kayanki kitafi gida, saina nemeki "

Maganarsa tabata tsoro, amma data tuni shawarar Ummi data Nas saita dake tace" wallahi Babu Inda zanje, "


" Ok haka kikace? "

Ta kalleshi tace" qwarai kuwa BAFFAH haka nace "

Yace" nikike kira da Baffah,? "ya iyo kanta gadan gadan

Tana ganin haka ta kwasa aguje, shima yadoru a bayanta

Kasancewar da hijabi a jikinta sai hijabin yake ta tashin iska🤣🤣










🙆🏻😱Ko'a'ina wannan gudu zai tsaya?









Wani lokacin zakuna ganin posting kadan, saboda mkrnt danake zuwa, wataran kuma zaku iya jina shiru, amma insha Allah zanyi kokari naga ina turo muku ko yaya ne







pls sharhi Dan Allah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻











Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


29&30


Cak yatsaya daga gudun dayake tareda juyawa gida, yana haki yana cewa saide ki nemi wani gidan amma ba nanba

Ita kuwa tsabar tsorata ko Juyowa batayi taga yana binta ko baya binta
Saiji tayi tayi karo da Mota, Allah yarufa Asiri motar bata gudu,shiyasa bataji ciwoba, sai haki take, takasa daidaita numfashinta, Dasauri tafuto daga cikin motar cikin mamaki ta kalleta"Nawal, keda waye kike gudu haka Kamar kinyi gamo? "🤣

Dago kanta tayi Dasauri jin muryar Ummi
Cikin haki tace" Ummi mutafi gida, zai dakeni "

Ummi tasa hannu ta dagota tace" Babu abinda zai miki, tashi mukoma gidan "

Bayanta takoma tabuya Kamar yana wajan tace" A a Ummi, mutafi gida Dan Allah "

Ummi de cikeda mamaki tajata tasata amota, suka juya zuwa gidan Ummin

*** ***** ***

Yana dawo wa gidan yasa dayyabu ya gyara wajan data bata, sannan yawuce d'akinsa tareda dafe kansa da hannunsa duka biyu, duk Ummi ce ta janyo masa wannan rainin awajan yarinyar nan, amma banda haka kisa hannu ki dauki sutura ki qona? Wardrob dinsa yaduba yaga Babu komai takwashe qananun kayan sai manya 😭wani kayanma rabonsa daya waiwaicesu ya Manta

Yasan bazata wuce gidan Ummi ba, Dan haka bazai damuba

Dole yatashi ya nemawa kansa mafita, wannan zaman Babu Inda zai kaishi, yanada abubuwa dayawa dasuka tsaya masa arai, kuma yarasa dawa zai tattaunasu, yakamata ya nemi wani mutumin Mai ilmi sosai

daga nan yatashi yayi masallaci domin sallar magrib


*** ***** ***


Zaune suke afalo, Ummi nakan kujera Nawal na zaune aqasanta
Ummi ta kalleta "Nawal ki fadamin gaskiya, menene yahadaki dashi har kike wannan gudun?"

"Ummi nice nayi masa laifi, kayansa na qone masa, saboda banaso yana yawo acikin kayan, kuma banida qwarin gwiwar dazan iya hanashi, shiyasa nayi tunanin qonesu"tana qarasa fadar haka hawaye suka zubo mata

Ummi tace" to menene abin kukan kuma? Ko akwai wani abu bayan haka?"

" Ummi cewa yayi natafi gida saiya nemeni "

Ummi tayi tagumi tama kasa magana 😱, Kallanta tasake yi tace" Nawal Baffah yataba biya miki haqqinki na aure? "

Tambayar tayi mutuqar yimata nauyi, cikin sauri ta sunkuyarda kanta qasa

Nan take Ummi ta gane Babu abinda yafaru, sannan tace" Nawal ina wayonki yake?keda kike yar zamani, keya kamata kiyiwa mijin ki shiga Mai kyau ta daukan hankali harki jawo hankalinsa gareki, aishi ba dutse bane, dakinja hankalin sa cikin Ruwan sanyi zaki bashi umarni yabi, ciki harda hanashi saka kayan, ni kaina banaso yadinga wannan shigar Nawal, abin yana mutuqar damuna, yan'uwan mu dasuke yola dayawa daga cikin su gani suke zuba masa ido nayi kawai naqyaleshi, namiji Kamar yaro ne awajan matarsa Nawal, keda kanki zaki iya sarrafa abinki ayayinda yashigo hannun ki, to amma Babu damuwa, zanyi maganin abun, zansa sabira taje tadauko min wayarki, sannan kishiga daki Karki kuskura naqara ganin koda kafarki ne afalo, zansa agyara miki wani dakin kikoma can gaba daya, kada kifuto harsai nabaki umarni "

Cikin nutsuwa tace" to Ummi, mungode "🤣🤣


Sannan tatashi tashige dakin ummin


*** ***** ***

Yana zuwa gidan, Ummi taganshi fuska atamke, da alama akusa yake

Tea takesha yayinda take aiki a computer, yana zuwa yafada kan kujera tareda dora kansa akan cinyarta

Fuskarta Babu alamun Fara'ah tace"ina cinyar taka matar"

Kallanta yayi "yanzu Ummi laifi ne danna Dan kwanta?"

"Babba ma kuwa, kakoma wajan matarka, inkuma ciki kakesan komawa to 🤣"

Ahankali yatashi yafara leqe leqe ko zaiga Nawal, ta kalleshi, sarai tasan ita yake nema, sai tace masa "yaya Nawal din take?"

Cikin ransa yace tofa 😳kenan batazo nanba?

Sumar kansa ya shafa yace"tana nan lafiya Ummi "

Kamar an tsikareshi yatashi yace" Ummi bari inje masallaci, saida safe"

Tace"toshikkenan ka gaishe ta, saida safenku "

Yana fita yatsaya ahabar gidan, to ina yarinyar nan tatafi? Karfa ace gidan tatafi, to amma tayaya zatayi gangancin hawa motar haya bayan da aurensa akanta? 🤔

(waannn aure😂)

Direct masallaci yaje yayi sallar isha'i, bayan an idar bai tashiba, saida yabari kowa yafice daga masallacin sannan ya qarasa wajan limamin suka gaisa, liman yace"muhammadu mungode sosai da kokari, ana yawan aiko mana da sadaka, mungode sosai, Allah yajiqan mahaifa

Cikin yanayi na damuwa yace"amin Malam, dama akwai abinda yake tafe Dani "

Liman yace" to inajin ka muhammadu "

" Wato Malam, wasu 'yan watanni dasuka wuce naje ta'aziyya kano, saina hadu da wata yarinya, tundaga lokacin nake mafarkin ta, kuma Allah da ikonsa banga fuskar ita wannan yarinyar ba, saide wani sashi na fuskarta,naji wasu yara daga bayanta sun kirata da Baby, wallahi Malam ina cikin halin damuwa, ina buqatar kyakykyawar shawara, saboda yarinyar tana yawan zuwamin cikin mafarki
Kwatsam rana daya sai mahaifiyata tahadani aure da wata, bana sonta, itama yarinyar bata sona, to tunda akai auren, Allah yasaakamin kishinta acikin raina, ina mutuqar kishinta, bansan dalili ba, yanzu hakama de maganar danake ma mun samu sabani da ita nace taje gida saina nemeta "

Liman yace" subhanallah, subhanallah, muhammadu akwai matsaloli Wanda dole kaine zaka gyara su da kanka, na farko muhammadu ba'a taba samun kishi saida soyaiya, muhammadu Allah yasaka maka qaunar matarka acikin ranka batare daka shirya ba, kana sonta, yakamata kajata ajikinka ka koya mata yanda itama zata soka, idan ka kwantar da hankalin ka ka rungumi abinda mahaifiyarka tamaka Zabi dashi sai kaga ta Sanadin haka Allah yabaiyana ma ita waccen yarinyar dakake mafarki, sannan kai namiji ne kanada damar dazaka iya auren mace hudu, bare guda biyu, saboda haka ka tsananta bincike akan yarinyar harka sameta, kahada su su biyu, zakafi samun nutsuwa acikin zuciyrka, kuma muma anan zamu dage dayima wasu 'yan addu'o'in "

Yace" Wato Malam, ba auren ne matsala ba, matsalar shine adalci, bazan iya musu adalci ba, ni kaina nasan cewa bazan iyaba, idan nace zanyi to haqiqa na yaudari kaina "

Murmushi liman yayi yace" karka damu, wanaan duk wani abu ne dayake hannun Allah, insha Allah ubangiji yana sane dakai, idan kayi addu'ah zai duba lamarin"

Shiru yayi, jikinsa yayi mutuqar sanyi, yace"to Malam nagode "

Liman yace" Babu komai muhammadu, ai Zan iya yima komai karka damu "

Daga nan yafuto daga masallacin jikinsa a mutuqar sanyaye

Direct gidansa yawuce, afalo ya zauna yadafe kansa da hannunsa🤦🏻‍♂ tareda lumshe ido, afili ya furta" tayaya? Iname hakan tafaru Dani? Me zance da Baby idan naganta? Tayaya zanso wannan yarinyar bayan nariga dana mallaka wa Baby zuciyata da gangar jikina?

Fillon dake gefensa na kujera ya dauka yayi jifa dashi, da karfi yadaga murya yace "Baby!!!!"
🤣🤣🤣

Gaskiya dole nanemawa kaina mafita, wayarsa ya dauka yakira Yasir
"hello Yas"

"na'am mk yahutu"

"to alhmdlh za'ace" 🤣

Yasir yace"aikin daka turonifa yadade da qarewa, dama inaso kasamin lokaci nazo akwai maganganun danake so mu tattauna akai"

Yace"Ok Babu damuwa, but kafin nan inaso ka bincika min wata yarinya agaba da layinku take"

Yas yace"yarinya kuma mk? Yaushe kayi aure? Sannan....

Cikin sauri yace "Yas" ya Dakatar dashi

Sannan yaci gaba da cewa "sunanta BABY, yarinya ce qarama, tana saka wannan Baqin abun a fuskarta, inaso ka tattaromin baya nanta cikin one week"

Yana gama magana yakashe wayar, sannan yafara tunanin ina ita kuma wannan yarinyar tayi?










My fan's kuyi manage da wannan, da ace Babu posting aganina gara asamu ko kadanne💃🏻








Dan Allah masu labe kufuto kuyi sharhi pls 🙏🏻











Amnah El Yaqoub ✍🏻🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


31&32

Yaci gaba da tunanin
To yanzu idan bataje gidan Ummi ba gidan uwar wa zata tafi?

To kode gidan tatafi da gaske? 😳, gata yarinya ce shi yaro baya qarya tsaf zataje ta zayyanewa iyayen ta komai tace yace saiya nemeta, sukuma su zagi Ummi suce Tun aure baije ko'inaba har ansamu matsala 😂
Shikuma Ummi tasakoshi agaba 😱

To yaya zaiyi tunda liman yace yakamu dason matarsa 😒dole hakuri zaiyi ya rungumi qaddara, inyaso saiya hadata da Babyn, amma ba haka yasoba, domin kuwa bai tsarawa kansa cewa zai hada Babynsa da wataba

Tsam yatashi ya yi daki ya kwanta, yana tunanin yanda zai shawo kan lamarin zuwa gobe



*** ***** ***


Washe gari dasafe tsaf ya shirya cikin qananun kaya, riga green wadda ta kamashi saiya dora milk din suit asama, saikuma wando jeans

Kai tsaye gidan Ummi yanufa, a lokacin tana zaune afalo tana break fast ita kadai

Kusa da ita yaje ya zauna jikinsa yana gogar nata, Yace"Ummi walijam "(ina kwana)

Ahankali ta ajiye cup din dake hannunta, tashafa kansa tace" sejam kalau Baffah nah, where is your wife? "

Gabansa ne yafadi, kansa yasara, da gasken de bata nan din kenan, hannunsa yasa yadafe kansa🤦🏻‍♂yace" Ummi wai yarinyar nan batazo nan gidan ba kenan? "

Yi tayi Kamar batasan komai ba tace" tacema zatazo ne? "

" no bata fadamin ba, Ummi yarinyar ce batajin magana wallahi, laifi tayimin shine nace tatafi gida saina nemeta "

Ummi tace" ikon Allah, to kaga kenan kai da kanka kabawa kanka amsa, tunda cewa kayi tatafi gida, may be tatafi gidan ne, "

Cikin shagwaba yace" to Ummi meyasa ba zatazo nanba saita kama hanya taje ta shiga wata motar tana hada jikinta dana wani"

"ikon Allah, Baffah nanfa ba gidansu bane, tayaya miji zai sallami yarinya ita kuma takama hanya tatafi gidansu?"

"to Ummi ba 'yarki ceba, zata iya zuwa mana"

Ummi tace"to batazo ba, da menene yahadaku har abin yakai haka? "🤣

" Ummi yarinyar nan takama kayana ta qonesu duka, batasan kudin dana kashe akan kayanba, takama ta babbakesu, 😂sannan naayi mata magana waini yarinyar nan zata kalli tsabar idona tace Dani BAFFAH "

" to menene aciki danta qona kayan? Ka fadamin sau nawa ina karbe irin wannan kayan awajan ka amma kabada oder wasu? Kaga yanzu ma kanada right din dazaka sake wasu, may be tunanin ta bazai iya daukar ganin mijinta kullum yana yawo ana kalle mata jikinsa ba, shiyasa ta qona 🤣

Sannan yarinyar nan tunda akai aure baka zaunar da ita kafada mata cewa bakasan a kiraka da Baffah ba, kamata yayi Tun farko kafada mata cewa ni sunana Muhammad, Ummi na tana kirana da Baffah, amma gayu yasa namaida sunana zuwa MK
Saboda haaka kaga ni anan ma banga laifin yarinya ba, Dan tace Baffah, koda cewa tayi me sunan baban Ummi, 🤣🤣ba zanga laifin ta ba

Baffah ka kiyayi kanka da Rayuwar nan, ada de nasanka da tausayi amma zuwa yanzu nasan cewa d'ana ya sauya, ya koma marar tausayi, Baffah ina sane da cewa Babu abinda yashiga tsakanin ka da yarinyar nan na auratayya, idan kai bakada lafiya ita yarinyar haka take?

Shiru yayi Kamar ruwa ya shanyeshi 🤣
Kuna zaune gida daya bazaka saukewa yarinya haqqinta ba? To yanzu ai shikkenan komai yazo qarshe, tunda ka sallameta zuwa gida kaga ai saitaji dadin auren wani, tunda batada iddar kowa akanta, yamaka kyau "

Ahankali yace" Ummi kiyi hakuri, nima bayin kaina bane, amma insha Allah zangyara, za'a bata haqqinta "🙊🙈😳

Tace" zancen yaushe kuma?ai magana ta qare "

" kiyi hakuri Ummi, yanzu ni zanje saudia, akwai binciken danasa yasir yayi min, inaso nayi addu'ah akan Allah yasa adace, ita kuma nasan zata dawo ai"

Ummi ta kalleshi galala 🤣🤣sannan tace"shi aikin har yakai ka tsaya ka nemi matarka muhinmanci? "

" Ummi nace miki zata dawo "

Tace" to shikkenan, tunda batada zuciya Allah yadawo da ita lafiya "😂😂

Shima Babu kunya yace " Amin " 🤣🤣

Sannan yaja abincin datakeci Gabansa shima yaci kadan, yamiqe yace" Ummi nina tafi, sai zuwa jibi Zan dawo insha Allah "

Ummi tanata kallan wannan qarfin hali irinna Baffah tace" Baffah tonyi jata? "(ina zaka)

Yajuyo yace" Ummi nace miki saudia Zani, addu'ah ce zata kaini inaso nayiwa abin d'awafi "🤣🤣

Tace" to, Allah ya temaka "shima yace amin, sannan yafice


*** ***** ***


Washe gari bayan ta tabbatar Baffah baya garin, ta tura sabira itada driver sukaje gidan suka daukowa Nawal wasu daga cikin kayanta, da wayarta, Ummi ta karbi wayar takasheta, sannan ta kaiwa Nawal kayanta daki, jikinta harya qara kyau saboda babu abinda take, kullum tana daki, fatarta har wani sheqi take, wani lokacin nede take taya Ummi cike wasu takardun, dataimakon Ummi, haka abubuwa 'yan qanana saita dinga koya mata tana rage mata su

Bayan tabata kayan tasa sabira ta gyara mata wani daki kusa da ita tace takoma can da zama, idan takama dole Ummin zata shigo da kanta, sannan tabata wayarta tace gatanan amma kada ta kunnanta, domin kuwa ta hanyar wayar kadai ma Baffah zai iya bibiya yasan Inda take

Abangaren Baffah kuwa 🤣Tunda yaje saudia kullum yana masallaci yana addu'ah Allah yasa aikin daya bawa yasir adace

Allah ya bayyana masa Baby cikin gaggawarsa bata shaidan ba, idan kuma Allah yasa tayi aure, kokuma anrasata to Allah yacire masa sonta daga zuciyarsa yasaka masa son matarsa sosai, domin samun kwanciyar hankalinsu

Sosai ya tsaya yayi addu'ah, sannan yafara haramar dawowa gida


Ummi kuwa sabira ta aika wajan wata aminiyarta datake oder kayan mata daga Sudan, aka hado mata magunguna masu inganci dakyau, babu kunya take zaunar da Nawal adaki ta gwada mata yanda zatayi amfani dasu, idan kuma nasha ne da kanta take hada mata tabata tasha, tunda Nawal najin nauyi harta saba

Banda lokaci data ware take koya mata kissa iri iri da kalamai masu dadi duk najan hankalin Baffah 🤣🤣

Lokaci kadan kuwa taqara sauyawa, abubuwa suka qara yawa, baccin ta takesha idan Ummi bata nan tana wajan aiki, babu ruwanta da gyaran gida karfe bakwai🤣🤣, sabira tanayin komai.


*** ***** ***

Washe gari yadawo, kai tsaye gidansa yasauka, amma abinda ya bashi mamaki shine baiga Nawal tadawo ba

Babu abinda yadauka agidan kai tsaye yawuce gidan Ummi

Ummi tana ganinsa tace"oyoyo da mutanan saudia, ashe kadawo? "

Zama yayi agefen ta yace" Ummi nadawo yanzu "

Tace" to mutanan saudia maraba, 🤣yanaganka haka?ina tsarabar tamu? "

Cikin ransa yace ita Ummi baabu ruwanta Tambayar tsaraba ma take 🤣🤣afili yace" Ummi wacce tsaraba nida naje addu'ah "

Tace" ai jinake kataho min da zam zam insha inyi alwala in yi sallah akan Allah ya baiyana min yata Nawal "

Cikin sauri ya kalleta yace" Ummi wai kina nufin bata dawo ba? "

" bata dawoba Baffah, sannan nakira wayarta akashe, may be lokacin daka koreta da wayarta tatafi, ni tsoronama kada iyayenta suzo sucimin mutunci 🤣🤣"

Kansa yadafe da hannu🤦🏻‍♂ yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Ummi yanzu yaya za'ayi? "

" abinda za'ayi shine ka shirya kaje kabawa iyayenta hakuri kadawo da ita gida, Dan nikam bazan iya tunkararsu da wannan maganar ba, ido da kunya 🤣"

Yace" to Ummi nida a wanne garin takene taka maimai? 🙆🏻😳😂

Ummi tace"Lahaula wala quwat, yanzu Baffah dama tunda akai auren nan baka shirya muku tafiya kunje gidan iyayen yarinyar nanba? "

Sumar kansa ya shafa, yayi shiru 😂

Taci gaba da cewa" Amma kuwa Baffah wannan abun kunya da yawa yake, to idan kaje gidan me zakace musu? 🤣🤣

Shiru yayi, daqyar dai yace"Ummi ba dad'i tone tone "😒

Tace" Baffah ai dole na tona🤣🤣, kana zaune da mace bakasanma inane garin su ba "

Yace" kiyi hakuri, ki fadamin sai naje nabasu hakuri tadawo d'akinta 🤣🤣"

" to Baffah tunda ka dage 'yar kano ce, zanturoma adress din gidansu saika shirya kaje "

Saida tafadi haka yatuna da maganar Nawal datake cemasa yayanta gidansa yana kano, yace" to Ummi nagode, zan shirya gobe da safe naje, saboda yanzu nagaji "

Tace" kai kadai zakaje ne ko tareda gurds? "

" nikadai zanje, zanbi flight din dazai fara tashi insha Allah "

Tace"to Allah yakaimu, idan kaje kabasu hakuri sosai Dan Allah" 🤣🤣🤣

Shiru yayi mata baice da ita komai ba 🤣🤣


*** ***** ***



Washe gari karfe tara agidan Ummi tayi masa, a lokacin itama tafuto tsaf zata tafi wajan aiki
Zuba masa ido kawai tayi tana kallansa ganin yanda yayi wata irin masifar yin kyau, yadi yasa Mai mutuqar tsaida light blue, yasaka hula baqa da Baqin takalmi, sai Agogon sa qirar gucci shima baqi , sai gyara Babbar riga yake🤣🤣


Ummi tace "Baffah? Yaushe rabonka dasaka irin wannan kayan kuwa? Anya kuwa kaga kanka a madubi kaga sai yanda kayi kyau?

Murmushin yaqe yayi 😊yace" Ummi barka da futowa, nima Zan wuce yanzu"

Tace"to Baffah idan kaje kabasu hakuri sosai Dan Allah "

Yayi tunanin zata bishi sai yaji tana qara yimasa maganar bada hakuri, fuskar nan atamke yace" saina dawo"😂

Yafice daga gidan aka daukeshi zuwa Airport, ahanya yakira Yasir awaya yafada masa cewa Yaturo masa da motoci zuwa Airport din Malam Aminu, zai shigo gari yau 🤣🤣

Itama umm saida taga fitarsu daga gidan sannan ta shiga Mota driver yajata suka tafi

Suna zuwa Airport kallo ya koma samah, duk Wanda yasan mk, saiya sake juyawa ya ganshi saboda shigar yau ta dabance🤣🤣

Sosai jama'ar wajan suke Bashi girma saboda ba qaramin mutum bane, shide kawai saide yadaga musu hannu

Jama'ar dasuke cikin Airport din kowa kallansa yake yanda ake bashi girma, sunsan cewa lalle wannan akwai wani abu aqasa🤣🤣

Basu bata lokaci ba, jirginsu yalula zuwa kano, suna sauka yaga motocin da yasir yaturo masa dasu

Bude masa akai yashiga, sannan yabawa driver adress din da Ummi taturo masa

Da tambaya da Komai suka sako kansu cikin unguwar tasu Nawal, saide abinda ya yi mugun d'aure masa kai shine meyasa suka biyo ta dede wajan daya taga ganin BABY?

Shide kawai yayi shiru, amma gabansa faduwa yake, kuma yarasa dalilin hakan, Dan haka saiya danganta abun da zuwa garin su Baby ne🤣🤣


Yana wannan tunanin motar su ta tsaya a kofar gidansu Nawal

Driver yace "yallabai mun iso"

Yace"Ok "

Fita direban yayi Dasauri yabude masa motar, sannan yafuto yana qarewa gidan kallo

Mus'ab yafuto daga gidan, yaga motoci har guda uku a kofar gidansu saiya tsaya kawai yana kallo 🤣🤣

Mk ya kalli yaron, yaga yana yanayi da Nawal, saiya kirashi yace" boy zonan"

Mus'ab ya qarasa, shikuma mk ya tsugunna daidai tsawo yaron yace "anan gidan kake?"

Yaro yadaga kansa

Yashafa kansa yace "maigidan yana nan? Ina nufin Babanku 🤣🤣"

Yace "eh yana nan, tsaya nakirawoshi" yajuya da gudu zuwa cikin gidan

Shikuwa miqewa yayi tsaye yana kallan gidan yana tunani aransa, yanzu Awannan gidan dako masinjansa yafi karfin zama aciki anan Nawal take rayuwa?
Kai Allah yaraba Baby da irin wannan rayuwar🤣🙊
Gaskiya gidan suna buqatar temakon gaggawa

Yana wannan tunanin Abba yafuto, yana dago kansa yaganshi, babu laifi mutum ne dattijo Mai kamala

Abba kuwa yana ganinsa yayi mutuwar tsaye

Wannan ba shine yaron daya temaka musu ba? 🤔

MK dayaga Abba yatsaya kawai yana aikin kallansa saiyayi sauri ya qarasa ya bashi hannu tareda tsugunnawa yace"Barka da futowa Alhaji "

Abba yace" barka de yaro, MK ko?

Girgiza kansa yayi, alamun eh, amma cikin ransa tunani yake A'ina kuma wannan mutumin yasan shi?

Abba ya katse masa tunani da cewa "baka ganeni ba ko?"

Cikin nutsuwa yace"eh, gaskiya ban ganekaba, Alhaji Dan Allah kuyi hakuri, yaron wajan hajiya Halima ne daga Abuja "

Gaban Abba ya yanke yafad'i cikin zaro ido😳yace" kardai kaine mijin Nawal? "

Ahankali ya Girgiza kansa

Jikin Abba yayi bala'in sanyi, yace" ikon Allah, Allah buwayi gagara misali, to qaraso daga ciki mk🤣, nan ai gidanku ne, qaraso qaraso ciki "

Babbar rigarsa yaqara gyarawa, 🤣🤣tsabar baya sakawa, sannan yabi bayan Abba suka shiga cikin gidan, amma cikin ransa tunani yake meyasa wannan mutumin yake ta kiransa da MK Ne?













Idan naga Comments zaku iya jina gobe, amma idan banganiba gaskiya saide kujini jibi, kafin nan masu labe sunyi magana 🤒🤒













Sharhi please 🙏🏻














Mrs Usman ce ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek


33&34


Ummah tana girki atsakar gida sai jitayi Abba yana cewa "shigo, shigo bismillah mk"

Cikin ransa sauri ta kalleshi jin sunan mutumin da 'yarta tadage shi takeso

Abba ya kalli Ummah Safiyya da baqo nake tafe, yau de ga mk har gida🤣"

Ummah tatashi tsaye tace" da gaske shine mk Alhaji? "

Qurii yayi da ido yana Kallanta, nan take yagane tsananin Kamar dasuke da Nawal, kenan mahaifiyarta ce, saide ita kuma wannan din baqa ce, abinda yakeso kenan Tun yana yaro sai gashi kuma Allah bai bashi ba

Abba ya kalleta cikin tabbatar wa yace" wallahi kuwa safiyya, shine mk, yau gashi Allah ya nuna mana mk 🤣🤣

Jin sunata cewa mk, mk, yasa cikin kunya ya sunkuyar da kansa qasa yace"Alhaji ai Muhammadu sunan "😃

Murmushi Abba yayi, yace" to muhammadu mk, mushiga daga ciki"

Kai tsaye Abba yakai shi cikin d'akinsa, ummah kuwa kawai mamaki take wai a'inama Alhaji yagano wannan yaron?

Yaya akai suka hadu? Tana tsaye tanata tunani Abba yadawo tsakar gidan cikin d'aga murya yace"safiyya ina yaran gidan suke ne kunbar mk Babu Ruwan sha🤣🤣

Saiga mama mariya tafuto daga dakinta yace"Alhaji sunan wanaji kakama yanzu? "

Daria takama Abba yanda yaga tafuto Dasauri haka, cikin Murmushi yace" yanda de kikajin "

Tafa hannaye tafara tace" yanzu fisabilillahi saida 'yar nan tayi aure sannan ya bayyana😂"

Ummah ma daria kalaman mama mariya suka bata, wai sannan ya bayyana saikace watan sallah 🤣
Ta kalli Abba tace" Alhaji Babu yara ko daya agidan nan, Najma tatafi kafe zatayi registration na jamb, su nura kuma banma san Inda sukai ba, saide mus'ab kawai, amma bari na kawo masa "

Yace" eh kikawo masa d'an abin sha, daga nan sai kuzo ku gaisa "

Shikuwa mk duk abinda suke yana jinsu, to wai shi me yayi ne aketa wannan mamakin akansa? Wacce yarinya ce yaji ance saida tayi aure sannan ya bayyana Kamar wani tauraro 🤔

Abba yana dawowa dakin yace" kayi hakuri, munbarka Babu ruwa, safiyya zata kawoma

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment