Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana turo baki gaba

Murmushi yayi yace "Baby naga kina son Nasrin dayawa, sannan ita qawarki ce, yarimah Abokina ne, sainaga Kamar idan ta aure shi zakufi yin zmuncin sosai idan kuna zaune gari daya, sannan naga alama yasir yanason Najma, to menene abin damuwa anan?"

Tace"to ai ko yaya Sultan dinma ta aura zamuyi zumuncin,"

Yace"hakane, amma inaso kimin alfarma guda daya, itace kisa aranki cewa da yarimah da Sultan Dani da yasir duk abu dayane, gaba dyanmu yanzu munzama yan'uwa, sannan kisa aranki duk wanda ta aura acikinsu Babu damuwa"

Tace"shikkenan "

Ya kalleta yace" to Baby pls, aji Dani "

Tace" nikam kallo zanyi "

Wayo yayi mata yace" kai kai aikuwa akwai abinda nakeso na nuna miki adaki "

Cikin sauri tace" haba Dan Allah? "

Nan da nan yaga tahau 🤣🤣yakuma tabbatar lalle Baby yarinya ce
Cikin Wayo yace" eh da gaske nake"

Miqewa tayi takama hannunsa tace"tashi Muje "

Dadi yakama shi yace to, sannan sukai cikin daki

Suna zuwa ya kashe wutar dakin yazare ta yayi kan gado da ita, shagwaba tafara tana cewa" Allah nidai um um pls ka saukeni "

Wasanni yafara aika mata, nan da nan jikinta yamutu tayi luf tana karbar saqon, ganin yanayi mata abubuwa tayi shiru ta daina musu yasa yadora bakinsa akunnenta yayi mata rada cewa" kinajin dadin? "

Cikin kunya ta daga masa kanta, yace" to duk abinda nayi miki kema kimin kinji? Ya qarasa maganar yana kissing wuyanta, wannan karon kam bata iya bashi amsa ba

Daga nan abubuwa sukaci gaba da wakana, ta gurzu sosai awajan sa, harta godewa Allah, bayan yasamu nutsuwa Yakalleta yace "Baby na Allah yayi miki albarka, koda yaushe dadi kike qarawa, Pls menene sirrin?"
Cikin kunya ta boye fuskarta ajikinsa takasa magana, yace "yanzu ma kinji zafin?"

Ahankali tace" ba sosai ba"

Yace "Ahankali zaki dainaji gaba daya kinji?"

Ta daga masa kai, hannun ta yana yawo acikin sumar kansa Mai laushi



*** ***** ***



Wajan sha biyu da rabi na dare, tana kwance tana chat da yan group dinsu na makaranta, taga Sabuwar number na kiranta, mamaki ya kamata, itade tasan cewa Babu Wanda yake kiranta a irin wannan lokacin
Dauka tayi tace "hello"

Kai tsaye Babu bata lokaci yace "kina tareda yarimah Nasir"

Gabanta ne yafadi sarai taganeshi amma saitace"waye hakan? "🤣

Ajiyar zuciya yasauke yace" nasan kin ganeni, ba maganar wasace tasa nakiraki ba, inaso in fita haqqinki ne insanar dake cewa zan turo iyayena gidanku,sabosa a nemamin aurenki "

Mamaki ne yakamata tace "iko"

Shima yace "sai d'an iko"

Tace"to ban amince ba, saboda akwai Wanda nake tare dashi"

Yace "kinsan cewa Zan iya nemanki, why zaki bawa wani dama harki saurare shi? Saiki bashi hakuri"

Cikin ranta tace yau naga karfin hali, nasan cewa zai iya nemana, Wato saboda ina hasashe sai iya nemana sainaqi kula wani

Afili tace "bazan iya bashi hakuri ba, saboda ina sonsa"

Kai tsaye yace"nima ina sonki, ba kuma zan iya hakura ba, kinga inada aikin yanzu, dama nafada miki abinda yasa nakirakin, saboda nafita haqqinki ne, sai anjima "

Cikin sauri tace" Karka turomin kowa gidanmu, saboda bana ra'ayinka, kuma naga ai ba dole ko? "

Kansa yadafe 🤦🏻‍♂yace" meyasa kika cika rigima ne Nas ?kinga bandamu da kisoni ko Karki soni ba, soyaiyar danake miki ta wadatar, sai sunzo "

Yana fada mata haka qit ya kashe wayar, tazubawa wayar hannunta ido 🤔




















Sharhi Dan Allah 🙏🏻





Manage today is monday










Mrs Usman ce ✍🏻🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)

Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Younique jhermerl, kayi yanda kaso dashi bro, ina godia sosai 🙏🏻


51&52



Ajiyar zuciya tasaki tace"tokode jiyake nima baiwar sa ce? 🤣
Kaine kake sona kake nema a wajena amma kaine zakamin iko da isa? To karka fasa turowa, kaga yanda nima Zan murda nawa kanbun ikon 😒
Datar ta rufe tadena chatting dinma gaba daya, gaba daya mutumin nan yagama dagula mata lissafi, yama raina mata hankali wallahi

Da wannan tunanin tayi bacci



*** ***** ***



Da sassafe wajan karfe shida yafara tashin ta daga bacci, bata dade da kwantawa ba bayan tayi sallar asuba danhaka baccin dadi yake mata yace"Baby! Baby!! tashi"

Cikin baccin ta taji kiran aranta tace yau nashiga uku yau kuma ina zai kaini? 🤣
Yasake cewa "Baby nah tashi mana"

Idonta me cike da bacci ta bude ta kalleshi dagashi sai kayan motsa jiki

Shima yazuba mata ido yana Kallanta,yace "Dan Allah kidena kallo na haka🤣saikisa nakasa fita wallahi"

Tace "ina zaka?"

"ina zamuje dai, tashi zakiyi mufita motsa jiki" 🤣😳

Tace "motsa jiki kuma? Na menene motsa jikin? 😳A a wallahi Allah ni bacci nakeji jeka" ta qarasa maganar tana narkewa

"Baby nide Dan Allah ki tashi mutafi, Baby kinamin wannan shagwabar tayaya zanji qarfin jikina, pls tashi, dake Zan dinga tafiya kullum"

Tace "inane wajan"?

Yace"cikin gidan nanne, tashi ki cire wannan kayan mutafi "🤣

Cikin damuwa tatashi, Allah nagani baccin be ishetaba 🤣
Vest tasaka tareda dogon wando

Yaje gaban mirrow yadauko mata ribom yakama gashin kanta ya daure 🤣sannan yace" Muje "


Futowa harabar gidan sukai sannan yajata baya suka fara gudu, Tun tanayi da Dan guzarinta har qarfi yaqare tazube awajan tana maida numfashi 🤣🤣

Yadawo ya tsugunna agabanta yace"

Sannu, 🤣kin gaji ko? "

Cikin haki tace" wallahi nagaji, wannan idan ciki ne da mutum ai saiya zube 🤣🤣

Daria maganar ta ta bashi yace" to yanzu ba cikinne dakeba, tashi muci gaba "

Kuka tafara yimasa marar hawaye tace" Allah nikam nagaji, Dan Allah ka daina tashina"

"to shikkenan ya isa yi shiru, tashi mutafi"

Kallansa tayi tace "kai dinfa?"

"nima na hakura, tashi Muje muyi wanka akwai Inda zamuje"

Hannunta ta meqa masa yakama yadago ta sannan suka yi cikin falo hannun su sarqe dana juna



*** ***** ***



Kallansa yayi Cikeda kunya, sai Saukar dakai qasa yake 🤣yace"To Abba Alhamdulillah aiki ya kammala, saide in akwai wani abun dabai muku ba saiku sanar azo asake wani "

Abba yayi Murmushi" haba yasir, komai yayi wallahi, bamuda bakin dazamu gode muku, saide muce Allah yasaka kawai "

Yace" to Abba, babu damuwa muma mun gode 🤣"

Mamaki yakama Abba, shide asaninsa yasan cewa da idan yasir yazo duba aikin gidan nan Alhaji yake cewa 🤔to yanzu kuma yaji wani sabon suna daya samu, kome hakan yake nufi?

Watsar da tunanin komai yayi acikin ransa, yace" idan kunyi waya da Muhammad din kasake yimasa godia kafin muma muzo har gida muyi musu godia "

Yasir yace" to insha Allah za'a fada masa "

Abba yafara tafiya zai shiga gida yana cewa eh, yauwaa mungode sosai, har yadanyi nisa yajuyo yaga yasir a tsaye awajan 🤣

Cikin ransa yace to kode yasir akwai wani abu ne?" 🤣yadawo baya yace "yasir yanaga ka tsaya ne, ko akwai wani abu?"

Sosa qeyarsa yayi yace"abba dama inaso zamuyi magana ne "

Abba yace" ikon Allah, haba yasir Kamar wani Baqo, ai anzama daya, inaa jinka meke tafe dakai? "

" Am Abba dama ina so ne ayimin lamuni 🤣nafara zuwa mugaisa da Najma "

Daria takama Abba yace" to, to, masha Allah, abu yayi kyau, kuma haqiqa kayi tunani Mai kyau daka fara tuntubar gida da maganar, dama bata tsaida kowa ba, Dan haka zaka iya zuwa duk lokacin datake gida idaan Babu makaranta, saboda yanzu zata fara zuwa makaranta, sannan idan kagama shirya wa mu awajan mu Babu matsala zaka iya turo iyayen ka "

Wannan karon yasir kasa kallan Abba yayi, Cikeda kunya yace" to Abba nagode, Allah yaqara girma, "

Abba yace" amin amin "

Daga nan sukai sallama, yana ganin shigar Abba gida shima yafada cikin Mota, yadauki wayarsa yaturawa Najma text,

" ina tayaki murnar samun zankadeden saurayi yarinya "

Alokacin da saqon yashigo wayarta Murmushi tayi ta tura masa da amsa cewa"

Mutum de yana murna yasamu 'yar fara zata taimaka ta soshi "

Shima yaana ganin shigowar nata text din yayi Murmushi, yatada Mota yabar kofar gidan



*** ***** ***



Bayan tagama shirya wa tsaf ta kwashe kayanta na amfani daga dakin tayi dakin mk dasu

Alokacin yafuto daga wanka yana shirya wa sai ganinta yayi tana shigowa da kaya

Yace"yawwa gara da Allah yakawo ki, daukomin kayan dazan saka "

Ajiye nata kayan tayi, tafara duba masa kayaiyakin, taga duk irin shegun kayan nan nasane Tajuyo tace masa

" irin wannan ne, wanne Zan kawo ma? "

Kallan kayan yayi, ya kalli fuskarta yaga tawani sha kunu irin bataso dinnan
Sai yayi Murmushi yace" kidauko min wasu, tunda ai naga bakya son wadannan din "

Tace" A a idan sudin kakesan sakawa nakawo ma"

Cikin kalar tausayi yace "A a nina isa nasaka kayan da Gimbiya Nawal bataso? Inzo ince inason wani abu nima acemin ba'aso?"

Murmushi tayi tayi masa hararar wasa sannan tadauko masa wasu kayan ta ajiye masa, ita kuma tafara shirya nata kayan
Yace "ajiyesu zakiyi anan ne?"

"A a nan dakin nadawo gaba daya"

Yayi Murmushi yace"kema dakin ya yankeki kenan "😉

" ba dakin ne ya yankeni ba, nime dakin ne ya yankeni "

Yace" Kamar gaske, matar da ana tabata zata fara kuka "

Ajiye kayan tayi tadawo wajansa tace" yakamata ka shirya fa, na baka kaya amma kaqi sakawa kana Jan magana "

" ke nake jira kizo ki shirya ni ai, inba hakaba kijini awajan baqa "

Kayan ta dauka tace" meyayi zafi, tashi nasaka ma "

Miqewa yayi tafara saka masa kayan, janbakin data saka ya kallah ya girgiza kansa yace" bazakai fita da wannan abun ba, yayi saurin saka bakinsa akan lips dinta yanasha

Batayi masa musu ba, saima taimaka masa datayi wajan maida masa martani

Lokaci daya tsayuwa ta gagaresu, suka fada kan gadon
Daqyar tazare bakinta cikin nasa tace "kagani ko"

Yace "kode mufasa fitar ne"? 🙊

Tace "A a Muje, tunda muka zo banga ko'inaba"

Cikin rad'a yace "pls Baby"

Tace"kabari mudawo"

"kinyi alqawari?"

Tace "nayi"

"kindeyi alqawari" 🤣

Tace"me Babban suna nayi "🤣

Daga nan yatashi aka gama shirin, sannan suka fita yawo, waje waje sukaje yadinga nuna mata, tana manne ajikinsa, wajan daya birgeta su tsaya suyi photo
Kowa ya gansu saisun birgeshi


('yar'uwa Karki yarda ki raba daki keda mijinki, koda ace kinada kaya dayawa kwaso wasu kidawo nasa dakin, koda fada kukai tunda kuna daki daya hakan zaisa dolen dole mijinki yamiki magana idan yanemi wani abun yarasa, amma kika bari kowa yana nasa dakin Hmm i pity you sister 🤔wallahi saide kiji tashin motar sa wataran🤣🤣)



*** ***** ***



Tun bayan wayar dasukai da ita yarasa sukuni, karfa yaje da gaske take bata son nasa 🤔
Toda yaya zaiyi kenan?
Kai yasan ma wasa take kawai Dan yaji haushi ne yasa tafadi haka, meyasa ita bata sonsa bayan yanmata dayawa suna sonsa? Sannan meyasa yake gani a idonta cewa shidin baya birgeta?

Yanzu yaya zaiyi? Kada yaje yasamu Mai martaba da magana aje gidansu tafuto fili tace bata sonsa 🤔daga nan kuma shknn mutuncinsa zai ragu a idon mutanan masarautar su, ace yatura mutane a Inda yasan cewa ba'ayi dasu

Gara yaje ya nemeta suyi magana gaba da gaba, yasan a hakibar dayake ciki, duk da zuciyarsa tana zargin cewa Nasrin batada Wanda takeso, kawai tafada ne

Dan haka cikin sauri ya kira mk yayi masa bayanin halin da ake ciki, sannan shima yaqara bashi hakuri tareda fatan alkhaairi

Number yasir ya nema ya kirashi, yace ya temaka yaturo ya bincika masa adress din gidansu Nasrin yaturo masa

Shikuwa yasir gidan bincike 🤣nan da nan yasamu daga wajan Najma yatura masa komai🤣🤣



*** ***** ***



Kamar wani Wanda take da tabbacin zai sota tanarke masa tana magana tanata shagwaba, tace"kuma yanzu idan katafi yaushe zaka dawo kafara aiki? "

Saida yadan daga kafada sannan yace" eto may be this week insha Allah "

Tace" ka tabbatar zaka dawo? "

Kallanta yanayin datayi masa maganar yayi, yarasa meyake damun yarinyar nan tunda yazo company take ta shige masa
Allah yasa de ba abinda yake tunani bane
Ajiyar zuciya yasaki yace" insha Allah Zan dawo "

Tace" to shknn, sai munyi waya, zan kiraka idan kaje, sannan kacewa su mamanku wata qawarka tana gaisheta "

Yace" gimbiya de, gimbiya aita wuce qawata, saide nace gimbiya Sahla tana gaisheta "

Murmushi tayi tace" kaga ni Babu wata gimbiya, ka daukeni Kamar kowa "

Yace" to shknn, sai wani lokacin "

Itama tace" toba damuwa saina kira "

Daga nan takoma cikin Company shikuma yafuto



*** ***** ***




Tunda yasako hancin motar sa layin gidan da aka tabbatar masa da cewa shine nasu Nasrin yake hango wata yarinya a tsaye da wani a kofar gida gabansa yayanke yafadi

Ahankali yake tuqa motar har yaqaraso kusa dasu, shikam yana ganin su amma su basa ganinsa kasancewar glass din motar me duhu ne

Magana yafara yi shi kadai, tabbas wannan yarinyar itace a tsaye da wani, kenan da gaske take da tace akwai wanda takeso, tayaya ma zata kulani bayan tana sauraron wannan gayen? 🤔Babu abinda Zan fada masa, dole ma nasan yanda zanyi nashawo kan yarinyar nan taqarfi da yaji Dan inba hakaba saide naga ankawo min IV nabikinsu 🤣🤣
Handle din motar yakama zai futo saikuma yafasa, yajirasu suka gama firarsu da yaya Sultan, har sukai sallama akan idonsa

Sultan yazo ya wuce tagaban motar amma baima kalli motar ba

Shikuwa yarimah yana wucewar Sultan yayi sauri yabude motar yafuto yadoru a bayanta

Dab da zata shiga ya cinmata sai ganin mutum tayi agabanta🤣

Yaune karo na farko data taba ganinsa cikin kaki na soja

Matsawa tayi zata wuce cikin gida yasake shan Gabanta tareda kama hannunta yariqe, Baice da ita komai ba yazuba gwiwoyinsa biyu aqasa yace "please Nas Dan Allah ki daure ki aure ni"
















(tab ! yau maza sun ragargazo 🤣🙊)














Abinnan na kullum de 😉ai kun gane












Amnah ✍🏻
🌺NI DAKE🌺

(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub

Dedicated to Itz sadeek

53&54


Hannun ta taqwace tace"kasakarmin hannu na, nadade da fadama gaskiya "

Hannunta yasaki yayi shiru, sannan yamiqe tsaye ya kad'e jikinsa 🤣Yakalleta yace" waike me kike dauki kanki ne? 😳🙊
Kinsan waye ni? Kinsan girma da martabar danake dashi? Bana tsugunnawa saide a tsugunna min akwashi gaisuwa, nazo gabanki na tsugunna inaso ki aure ni, cemiki akai banda masu sonane kome? Ba komai yasa namiki hakaba saidan nafita haqqinki,"

Yanunata da hannu 👉🏻sannan yace" ki kiyayeni "


Haushi ne yaqara kama Nasrin, lalle ma mutumin nan, 🤔ashe tuban muzuru yayi🤣ta kalleshi tace"
To tunda kanada Wanda suke sonka menene zaka tsaya a wajena? Ai saika kai kanka can "

Yace" Ok haka kikace? "

Tace" eh, kaje wajansu, amma ba wajena ba "

Shima cikin bacin rai yace" aikuwa wajan ki zanzo, kuma aure dole yarinya "🙆🏻🙊

Yana fadar haka ya barta a tsaye awajan,tareda shigewa cikin Mota

Kallan bayan motar sa tayi, tasaki Tsaki sannan tashige cikin gida, Allah da taso tausaya masa, amma tunda taji yace akwai masu sonsa sai taji ranta ya sosu akan wannan furucin nasa, to wai ma miye nata najin haushi akan yace ana sonsa? 🤔🤣

Yana driving amma kawai Tsaki yake saki, yayi tattaki yataho tundaga Abuja har kano saboda yarinyar nan amma ko Ruwan nera biyar bai samu ba bare yasamu abinda yakawo shi wajan ta 🤣🤣
Qarshe ma duk bada kan dayayi duk yatashi abanza 🤣
Wayarsa yadauka ya kira mk, a lokacin yana office yana tsaka da aiki, yadauki kiran

Yarimah yace" mk naje wajan yarinyar nanfa amma Babu nasara🤣

Kai intaqaice ma bayani ma da wani Yaro naganta, sannan har tsugunnawa nayi agaban ta amma ta watsa min qasa a ido "

" to meyasa bazaka nuna mata a aikace ba "?cewar mk🤣

Yarimah yace" MK wannan yarinyar fa ba Kamar sauran yanmatan dana hadu dasu bane, dana riqe hannun tama qwacewa tayi "

" to meyasa bazaka jata kushiga cikin gidan kayi musu bayani ba? "😳🙆🏻

😳Zaro ido yayi, yace" A a mk kafini iko 🤣, saikace wata baiwa ta? "

Mk yace" to shikkenan Nas ka zauna kallan ruwa... Shima dayan saurayin nata bari na kirashi ince ya matsa number" 🤣🤣

Cikin mamaki yace "kasan shine?"

"yes yayan Baby nane"


Yarimah yace"tab, akwai qura, dannaga gayen yahadu gaskiya, zansan abinyi yau d'innan insha Allah "


Mk yace" ok" tareda kashe wayar


(wai nikam mk abayan wa kake ne🤔🤣"



*** ***** ***



Ummi ta dubesu tace "haba Alhaji, kuma yanzu fisabilillah saboda wannan kuka taso tundaga kano? Aini da kun fadamin ma bazakuzo ko'inaba"

Abba yace"haba Hajiya ai yaba kyauta tukwici, yaro yayi abin alkhaairi dayawa Babu abinda zamuce daku sai godia, ta silarsa Nawal tasamu lafiya, ga gyaran gida, ga kuma aiki daya samawa yara, kinga ai dole muzo muyi muku godia "

Murmushi tayi" ai Alhaji Allah yakamata ku godewa, kuma mu dama iyaye a kullum addu'ar mu shine Allah yabamu yaya nagari, mace ko namiji inde nagari ne ai sun zama abin so ga kowa, Allah zaku qara godewa daya baku Nawal amatsayin 'ya, domin kuwa taa Sanadin ta ne komai yafaru "

Yace" wannan gaskiya ne, ai shima muhammadun mun kirashi zaamu sake yimasa godia amma kuma bai daukaba "

Ummi tayi Murmushi tace" to ai gara dabai daukaba Alhaji, ai anzama daya, shi Salisu yana tare da Yasir ko? "

Abba yace" eh shi Salisu tareda Yasir zasu dinga yin komai, shikuma Sultan yana nan "

Tace" eh haka yake fadamin da mukai waya, Allah ya temaka yayi jagora "

Liman dayayi shiru yace" yanzu hajiya ashe ke iyalin Alhaji Kabeer ce amma kika kasa sanar damu lokacin dakikaje gida "?

Tace" to baba ai gara kar a bayyana din, Inda ace nafada muku aida saboda mahaifinsa zaisa kubashi yarinyar, amma yanzu da aka baiyana gaskiyar komai ai gashi ba'aji kunya ba daga baya "

Malam yace" wannan gaskiya ne, Allah yabawa yara zaman lafiya, ya basu zuri'ah tagari "

Cikin farin ciki Ummi tace" Amin amin Malam "



*** ***** ***


Washe gari jiniya da kuma qaran sarewa yacika unguwar su Nasrin 🙆🏻
Mutane dayawa suka futo domin ganin abinda yake faruwa
Motoci ne kusan guda shida manya masu tsadar gaske

Wata farar Mota aka budewa wani mutum dattijo yafuto sai kirari ake masa, sai baza binjima suke ana gyara kintsi dakyau 🤣

Iso sukasa ayi musu, yaron dayayi musu jagora zuwa gidan da kansa yaleqa yafara kwala sallama

Baba mahaifin Nasrin yafuto, yana ganin wannan manyan baqi fuskarsa tacika da mamaki yaqaraso yana sannunku da zuwa, barkanku da zuwa

Nan da nan yagabatar musu da abin zama, babu bata lokaci wannan dattijon yafara magana "sunana Alhaji Ahmad Is'haq, wazirin qasar gombe, munzo neman iri ne wannan gidan, yarimah yagani kuma yanaso, dan haka Mai martaba yabamu dama muzo munewa yarimah auren yarka," 🙊


Baba yace " wallahi anbashi 🤣, nide a iya sanina yarinya batada kowa, a fadawa Mai martaba ahakan ma mune da godia "🤣

Waziri yayi qasa da murya yayiwa wani dake gefensa magana, nan take aka dauko kudi dami biyu sannan wasu fadawa guda biyu suka tashi da gudu suka bude bayan Mota aka futo da akwatuna guda biyar aka jeresu agaban baba

Waziri yadubi baba yatura masa damin kudin gabansa yace"ga kudi da akwatuna nan amatsayin kayan nagani inaso, sannan Mai martaba yana jiran amsar ka ta lokacin da kakeso azo ayi aure "

Baba yace" afada masa yarinya anriga anbashi, duk lokacin da fada ta shirya za'a iya daurawa "

Wazirin yace" masha Allah, Allah yayi maka albarka, masarautar gombe tana godia, daga yau za'a hana yarinya fita ko'ina, akwai bayi da za'a turo mata su fara kula da ita kafin zuwan ranar da masarautar gombe zatazo tatafi da ita "

Baba yace" Allah yakaimu, Allah yaja da ran sarki"

Daga nan suka tashi suna daga Babbar riga har saida Waziri yashiga Mota sannan suma suka shiga suka tafi


Wajan biyar saura tadawo daga makaranta, tunda tashigo layin su taga sai Kallanta ake

Gabanta yafara faduwa kadan
Tana shiga gida taci karo da akwatuna atsakar gida

Babanta ya kirata daki yayi mata bayanin komai tace"Baba yarimah kuma?
Yaya Sultan fa yana sona "

Baba yace" aini baki fadamin hakanba Nasrin, kuma mutanan nan ba kai tsaye sukace abasu ba, sunce min neman iri sukeyi, keda Sultan ku kukai kuskure dabaku kawo maganar gidaba, danhaka kiyi hakuri kawai Allah yasa hakane yafi alkhaairi "

Cikin sanyin jiki tatashi tashige dakinta, tunani tafara Wato tanan yarimah yabullo mata kenan, shine maimakon ma ya lallasheta harta yarda shine zai tashi yaturo manya? Hawaye masu dumi suka zubo mata, meyasa zaiyi mata haka? Meyake ji dashi?



*** ***** ***




"sahla abinda kikeso bana tunanin zai iyu"

Jikinta yayi sanyi, tace "meyasa zakace haka Sultan? Bankai matsaayin dazaka soni bane? Kokuma kaine bakada ra'ayin mace kamata?"

Yace "ba haka bane sahla, kinada komai, hankali nutsuwa, sannan kinada kyawun sura ta yanda kowanne namiji yaganki dole yaji kin masa, saide kinfi karfina, hakan yasa Tun farko banfara nemawa kaina matar da tafi karfina ba, saina nemi daidai Dani"

Gabanta yafadi tace "kana nufin akwai wadda kakeso?"

Yakalleta yace "wannan haka yake"

Tace "Sultan ina sonka, danhaka bazan hanaka auren wadda kakeso ba, amma mazai hana ka aure mu mubiyu? Tunda Allah yabaka damar hakan, sannan ni kishiya bata dameni ba, karka Manta daga gidan sarauta nataso, Tun ina yarinya da kishiyoyi na bude idona, amma bazan takura ma, na baka dama kayi magana da ita, idan kana ganin Babu matsala nata bangaren shikkenan "

Tausayi ta bashi, Awannan lokacin wacce yarinya ce Mai kyau da aji kamar sahla zata baiyanawa namiji abinda yake ranta?
Sannan yafada mata akwai wadda yakeso still bata karayaba tace taji tagani tana sonsa ahaka

Ajiyar zuciya yayi, yace" to shikkenan sahla, insha Allah zanyi magana da ita, duk yanda mukai da daddare Zan kira ki "

Bata iya yimasa magana ba, kawai de ta girgiza masa kai tayi gaba, yayinda yabi ta da kallo, sahla nada komai, yarinyar baza'a fada mata kyawun diri ba




*** ***** ***



Bayan ya idar da sallar magrib yadauki wayarsa ya kira Nasrin, duk da cikin ransa yana shakkar yimata maganar Dan yasan halin mata da kishi

Tana dauka yaji muryar ta Kamar tana kuka yace "Nasrin lafiya? Meyake faruwa?me aka miki?"

Tace "yaya Sultan dama yanzu nake shirin kiranka akwai maganar danake so muyi"

Yace "nima yanzu haka dawowa ta kenan daga wajan aiki, wata yarinya tatareni da wata magana shine nakeso nakiraki nafara jin ta bakinki sannan inyi mata bayani"

Tace "wacce irin magana?"

Yace "akwai wata yarinya wajan aikinmu daya da ita, sunanta sahla, ta fadamin cewa tana sona, idan Babu damuwa kuma zaki amince tanaso na aureku tare"

Murmushi tayi Mai ciwo tace "yaya Sultan kenan, daka sani daka amince mata ma kai tsaye"

"mekike fada haka Nasrin? Ke dinfa?"

"yaya Sultan anyimin miji agida, shine maganar danace inaso nakiraka yanzu muyi,"

Yace "Innalillahi wai da gaske kike?"

"da gaske nake yaya, dazu ma suka tafi masu neman auren"

Yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un waye hakan?"

Tace "sunansa yarimah Nasir, dan gidan sarkin gombe, abokin mk ne mijin Nawal"

Cikin mamaki yace "abokin mk? Kuma kikace Dan gidan sarkin gombe?"

Tace "eh"

Yace "tab, to ai yarinyar danake fada miki yanzun qanwarsa ce, ta fadamin cewa itama yar gidan sarkin gombe ce, sannan ranar dana fara haduwa da ita a company nace mata ni mk ne yaturoni, sai tamin aikuwa tasan shi abokin yayanta ne"


Nas tace "to wallahi shine"




"ikon Allah, kice d'an sarki yamin qafa🤣
Shi daya tashi sai yabi ta sama, matsalar da muke fuskaanta kenan yanzu kanason yarinya ka naso ka aure ta amma bazaka fara fadawa iyayen ta ba, saide kaje wajan yarinya, gashi yanzu inaji ina gani Zan rasaki"

Tace "zamu rasa juna de yaya Sultan"

"kiyi hakuri Nasrin, haka ubangiji ya tsara mana, dama can yariga ya rubuta cewa zamuyi alaqa da 'yan gida daya, Yaya da qanwa"

Hawaye suka zubo mata, batare data ce komai ba takashe wayar, tasan cewa yanzu kam tarasa Sultan, saide kuma wani bangaren na zuciyarta tanajin yarimah aranta, ajinsa yana birgeta, kawai wannan ikon nasane bataso, taga kuma abin Kamar a jininsa ne, yanzu yaturo mata mutane amma koya kirata wanne irin abu ne wannan?



*** ***** ***



Wajan karfe goma da rabi ya kira wayarta
Tana ganin kiransa ta amsa wayar jikinta asanyaye
Yace "gimbiya Sahla"

Cikin sanyin jiki tace "na'am, inajin ka, Yaya kukai?"

"kinsan Allah akoda yaushe yana tareda bayinsa masu hakuri, may be hakurin da kikai kika dauki qaddara kika sa aranki zaki iya zama da wata shiyasa Allah ya juya lamarin zuwa ga yayanki"

"bangane ba, me kake nufi?"

"sahla yayanki ya rigani, yama tura manyan sa ayi masa Tambayar auren ta,"

"kana nufin yaya Nasir ne yake sonta shima?"

Yace "hakane Sahla, kuma iyayen ta sun bashi"

Tace "ashe ni da yayata nake kishi bansaniba?"

"ai bakiyi kishi ba, dangana kikasa aranki, kuma sai Allah ya sauya al'amarin sa"

Tace "hakane, kayi hakuri, nasan yanda so yake, kuma nasan cewa kana sonta, amma inama albishir da cewa insha Allah

1 Comments On NI DAKE
avatar
amal

11 months ago

Reply

Awesome

Please Login or Register in order to submit comment