Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juyowa ta kalleta. Suka haɗa ido, ba shiri gabanta ya ƙara tsnanta bugu.
Haka kawai ta ji ba ta yarda da wannan kiran da ta mata ba, ta haɗiye wani kakkauran miyau, sannan ta soma takowa zuwa gareta. Kusa da ƙofar ɗakin ta tsugunna.
“Ungo shanye!”
Habiba ta faɗa tana miƙo mata wani abu a kofi, kallon abun dake cikin kofin kaɗai ya haddasawa Rabi faɗuwar gaba fiye da ta da. Ta juya kallonta kan Habiban, ta ga yanda ta tsareta da ido.
Hannunta na rawa ta kai ta karɓi kofin, sai da ta raintse idonta, ta yi bismillah, sannan ta kafa kai ta shanye abun cikin kofin. Taste ɗin bakinta ya mata wani iri, dan abun sam ta kasa gane na miye, sai dai tana da tabbacin koma miye sharri ne. Kofin ta aje mata a gabanta, ta miƙe, ta kama hanyar fita.
Habiba ta bi bayanta da kallo tana murmushi, tasan kamar yanda yayarta ta faɗa mata ne, komai ya zo karshe tun da ta sha wannan abun, saura kuma jiran ganin sakamako.
“Honeynah, Ya kika yi shiru?”
Muryar Yaya ta faɗa, yayin da yake kallon Rabi'a, wadda ke zaune a kan wani benci dake bakin shagon, shi kuma yana daga cikin shagonsa, wayar Anti Saratu riƙe a hannunsa, yana tura mata abubuwan da Rabi'an ta lissafa masa.
Rabi'a ta sunkuyar da kanta ta na murmushi.
“Ni kam ina san wannan kunyar taki, tarbiyyarki da kyawunki su ne ke ƙara min shauƙin ƙaunarki Rabi'ata...”
Rabi ta ƙara sinne kai tana wani murmushi me kama da dariya.
Shi ma Yayan murmushin ya mata, yana juyar da kansa ga turin da yake mata. Kafin daga bisani ya shiga ba ta labarin yanda wasan jiya ya kasance, dan yasan yanda take matuƙar san ball, kuma shi ma yana tayata.
Sai da suka ɗan taɓa hira, sannan ta masa godiya ta fito daga shagon. Wata mota ta ga ta yi parking a bakin titi, kasancewar shagon Yayan a bakin titi yake. Fuskar Mama ta gani a gaban motar zaune a gefen drivern.
Kanta ta girgiza kawai ta yi gaba, ta zo wucewa ta kusa da wasu matasa dake kan benci suna hira, hirar ta su ta ɗauki hankalinta.
“Wannan 'yar gidan tsohon najaduncan ce ko?”
Na kusa da shi yace.
“Ko ba Mama ba ?, Ita ce, kai kuwa barewa ba ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ?... Ai kamar Kumbo kamar kayanta ?”
“Allah ya kyauta mana kawai...”
Sauri ta ƙara, gudun kada ta ji abun da zai sa ta fashe da kuka nan take.
Daga can cikin motar Mama ta shagwaɓe fuska tana kallon sabon Alhajin da ta yi.
“Gaskiya Baby ni sati zamu yi”
Alhajin ya yi dariya irin tasu ta goggagun 'yan bariki.
“Baby Mamancy! Ai sai yanda ki ka ce, idan kin ce mu yi wata ma babu wata matsala”
Daɗi har ran Mama, ta je ta yi wata a England ita da wannan Alhajin?, ai har ta hango irin kuɗin da za ta yi.
“Shikenan, zuwa yaushe za mu tafi?”
Alhajin ya shafo ƙaton tumbinsa, sannan yace.
“Nan da next week, kawai dai ki zama cikin shiri, sannan ki aikomin da hotonki na passport”
“To sai na jika”
Ta faɗi tana masa wani farrr da ido, sannan ta kama ƙofar motar ta buɗe.
Idan ka hangeta daga nesa, cewa za ka yi sam ba ta haɗa jini da hausawa ba. Wata matsataiyar duguwar riga ce a jikinta, sai wani ɗan fingil-gilin mayafi da ta riƙoshi a hannunta.
Small knotless barid ɗin dake kanta, wadda aka kitsa mata ita da wani golden attachment ta sauƙo tana lilo a gadon bayanta. Fatar jikinta har wani pink-pink take, don tsabar man bleaching ɗin da take shafawa. Ga wani nose ring da ta saƙala a gefen hancinta. Duk wanda zai mata kallo ɗaya, a tashin farko zai kirata da karuwa!.
Ko sallama babu, haka ta sa kai a cikin gidansu. Habiba da har lokacin na zaune a ƙofar ɗaki ta miƙe tsaye tana washe baki. Ganin Maman ma na fara'a.
“Umma, mu shiga daga ciki”
“To...To!”
Habiba ta faɗi cike da zumuɗi, ɗakin nata suka shiga, ta tsaya tana kallon Mama, tana jiran abun da za ta faɗa.
“Wannan sabon Ahajin da na yi ne, tafiya ta kama shi zuwa ingila, kuma yace da ni zai tafi”
“Ayyirri!...Yirriri!”
Habiba ta rangaɗa guɗa tana kama danannen hancinta hancinta.
“Ni na san ban yi haihuwar banza ba, ni da kaina na san cewa na yi farar haihuwa... Ingila fa Mama?, Ƙasar turawa ?”
“Nan fa”
Mama ta tabbatar mata murmushi kwance kan fuskarta data sha mai.
Saratu da Rabi dake ɗaki suna iya jiyowa komai, zuwa lokacin Fatima ba ta ɗakin, dan Anti Saratu gama mata faɗan ta tashi ta fice ta bar gidan gaba ɗaya. Anti Saratu ta girgiza kai cike da takaicin mahaifiyarta da ƙanwarta.
Rabi da ta fara kallon wasan a waya ta kalleta.
“Ba ƙunci ya kamata ki yi ba... Ki musu addu'a kawai”
Anti Saratu ta yi murmushi.
“A kullum ina yi Rabi, amma gani nake kamar abun nasu ba na ƙare ba ne”
“Kada ki ce haka Anti Saratu, Allah ma jiroƙon bayinsa ne, ki dage da addu'a, Allah zai amsa miki ”
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*09*
~~~
*Someday, you will get everything you deserve, and it will be beautiful*
***
*Shekara ta 2000*
*Kano...*
“Aliyu!, Aliyu! Wai kana ina ne ?!”
Zaid ke ƙwalawa Aliyu kira, bayan da ya dawo gidansu bai tarar da shi a inda ya barshi ba, sanye yake da wannan uniform ɗin islamiyyar da ya rage musu.
Babu datti a jikin kayan, kasancewar ya na ɗaukowa ruwa a tuƙa ya musu wanki, sai haske da yadin kayan ya fara, alamun ya na jin jiki.
Hannunsa na dama riƙe da ledar ƙosan da ya samu ya siyo, bayan ya je ya yi bara a bakin titi, Bara?!, a yanzu ita ce abin da yake dan ya samu ya kawowa ƙaninsa abin da zai ci.
Sati ɗaya kawai Maman Naufal ta yi tana basu abincin da ba ya ƙosar da su, daga nan idan ya shiga gidan sai ta ɗaure fuska, har ta kai da ta ce masa kada ya ƙara shigowa gidanta.
Ga shi su kuma babu gidan da suka sani a unguwar, da ma gidan nata ne kawai suke ɗan shiga, ganin yunwa za ta lahanta masa ƙani ne yas sa ya fara barar, sai ya tafi bakin titi ya tsaya yana roƙar jama'a. Da haka yake ɗan samun abun da zai kawowa Aliyun ya ci.
To yau da safe ma ba su tashi da komai ba, hakan ta sa da wur-wuri ya fice ya tafi barar, sai da ya shafe sama da awa uku. Sannan ya samu na siyan wannan ƙosan...
Tunaninsa ne ya katse, a sabda ya ɗora idonsa a kan Aliyu dake durƙushe a bayan gidansu. Hankali tashe ya yi cilli da ledar ƙosan ya yi kansa yana kiran sunansa.
“Aliyu! Aliyu! Kai Aliyu me ya ke faruwa da kai haka ?”
Ya tambaya a sanda ya ɗago shi, ya na kallon fuskarsa da tai jawur, kasancewarsa me farin fata, ga idanuwansa sun yi ja, kuma a 'yan kwanakin Zaid ɗin ya gano cewa dukansu sun rame. Sannan ya san ba komai ba ne face yunwa, musamman ma Aliyu da sam ba ya iya jurewa yunwa.
“Yunwa kake ji ?”
Zaid ɗin ya tambaya yana miƙar da shi, da ƙyar Aliyu ya iya gyaɗa masa kai, a hankali Zaid ɗin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya miƙar da Aliyun gaba ɗaya.
Kama shi ya yi har suka shiga cikin ɗakin da suka saba kwana, ya zaunar da shi a bakin katifarsu, sannan ya koma bayan gidan ya ɗauko ledar ƙosan da Allah ya temakesu bai zube ba, ya haɗo da wani plate da suka saba cin abinci a ciki, sannan ya ɗebo masa ruwa.
Ya dawo ya zauna kusa da shi, ya juye masa ƙosan a plate, tare da tura masa shi gabansa.
“Ka ci Aliyu”
Aliyu ya kalli ƙosan, sannan ya kalli yayansa, ƙwarin gwiwarsa, farin cikinsa, uwa, ubansa duka a halin yanzu Zaid ne.
Sai ya kai hannu ya ɗauko ƙosan guda ɗaya, me makon ya kai bakinsa, sai ya kai setin bakin Zaid.
Zaid ya kalli ƙosan, sannan ya kalli Aliyu, wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo masa, a hankali ya buɗe bakinsa, Aliyun ya ƙarasa saka masa ƙosan, yana taunawa hawayen na ƙara kwaranyo masa.
Ya kai hannunsa ya ɗauko ƙosan shi ma, sannan ya kaiwa Aliyun baki, Aliyu ya karɓa ya na murmushi, da haka suka cinye sannan suka sha ruwa. Sai kuma suka zauna suna biya tilawar islamiyyarsu, dan bayan faruwar iftila'in nan sun ɗan je.
A lokacin biyan kuɗin wata ne malaman suka korosu, makaranatar safe kuwa l ba su kusanceta ba, dan sunsan babu me barinsu su shiga basu da uniform, kuma ga shi term ya kawo ƙarashe. Karatun ƙur'anin dai shi suke ɗan taɓawa da ka.
Bayan sun yi sallahr azahar, Zaid yace zai fita ya nemo musu abin da za su ci na rana.
“Zaid ka tafi da ni... Ba na san zama ni ɗaya”
Cewar Aliyu ya na miƙewa, Zaid ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya, sannan yace.
“To muje”
Aliyu ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya yana kama hannun Zaid. Har suka fito daga cikin gidan, Zaid ya ɗauki wani ƙyallen tsumma ya ɗaure ƙofar gidan, kana suka kama hanyar bakin titi.
Idan daga nesa ka gansu za ka ce mutum ɗaya ne, kasancewar komai nasu kala ɗaya ne, farin fatar, kyan fuskar, hatta da takunsu iri ɗaya suke, na Zaid ne kawai yafi nutsuwa. Idan wannan ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sai ka ga wannan ma ya ɗaga, abun nasu gwanin ban sha'awa.
A sanda suka fita titin, Zaid ya nunawa Aliyu wuri yace masa ya zauna, shi kuma zai je ya na barar.
Aliyu ya zauna yana kallon yayansa, yanda yake miƙa hannu yabna barar sai da ya sa shi kuka. Wai yanzu su ne rayuwarsu ta koma haka, su ɗin da suke da gata, suke da uwa, wadda ta ɗauke musu kewar uba, su ɗin da ba su nemi komai sun rasa ba, amma cikin ƙiftawar ido, komai ya sauya, LABARINSU ya sauya, rayuwar ma baki ɗayanta ta sauya.
“A taimaka mana sadaka fi sabillilahi...”
Cewar Zaid yana miƙawa wani me shago hannu, mutumin ya miƙe a fusace.
“Kai! Ba ɗazu ma ka zo ba?!...”
Kafin ya ƙarasa yaron shagonsa yace.
“Jiya ma sai da ya zo”
“Sh*ge, da ma da irinku ake haɗa baki ana mana sata, bar nan wurin!”
Ya ƙarashe yana hankaɗashi, har sai da Zaid ɗin ya faɗi ƙasa, da yake hakan ba komai ba ne a wurinsa, sai ya miƙe yana bawa mutumin haƙuri, don ba yau aka fara masa irin hakan ba.
Kamar wucewar walƙiya haka ya ga tahowar Aliyu da gudu, kuma kafin ya fahimci abun da Aliyun ke ƙoƙarin yi, har Aliyun ya yi tsallen albarka, ya kifawa me shagon nan mari.
“Kut!, Babbar buhun ub*ncan!, kayyasa! Ni ka mara yaro ?!”
Cewar me shagon yana kama baki. Aliyu da ya gama fusata a sanda ya ga an hankaɗa masa ɗan uwa yace.
“Eh ɗin, na mareka, ko akwai abun da za ka iya?”
Ya faɗi idonsa ƙyam a kan mutumin, babu wani alamun tsoro tare da shi, ji yake ma kamar zai iya kikkifa masa marin da ya fi haka, ga shi dai ba shekaru gareshi masu yawa ba, amma zafin zuciyarsa ya fi na ɗan shekara ashirin, ji yake a kan yayansa babu abun da ba zai iya ba. Ko dan sunansa Aliyu ne ?, Oho.
Zaid ya kamo hannunsa ya na jansa baya.
“Zo mu tafi Aliyu...”
“Rabu da ni Zaid, sai na nuna masa martaba da kimarka a wajena”
Nan fa me shagon nan ya shiga zage-zage yana masifa, har maƙotan shagunansa suka fito. Ɗaya daga cikin masu shagunan ne ya kamo hannunsu Zaid, ya ja su zuwa gefe.
“Ni kuwa yara ku ba 'ya'yan wannan likitar ba ne ta bayan layi ?”
Mutumin ya tambaya, yana ganin kammanin customern tasa a fuskar kowannensu. Aliyu bai iya bashi amsa ba, kasancewar zuciyarsa na tafarfasa, har yanzu ji yake marin da ya yi wa me shagon nan bai wadatar ba, kamar ya na buƙatar a ƙara masa, soboda abinda ya yiwa Zaid ɗinsa.
Zaid ne ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan yace.
“Eh, mu yaranta ne”
“Kwana biyu ba na ganinta, fatan dai lafiya ?”
Zaid ya sunkuyar da kansa ƙasa.
“Yau wata biyar kenan da rasuwarta, gobara ce ta kama a gidanmu, kuma a lokacin da gobarar ta kama tana cikin gidan...”
“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un... Wallahi yara ban sani ba.... To yanzu ku da wa kuke zaune?”
“Ba mu da kowa, mu kaɗai ne”
“Subhannallahi, shi yasa kuke bara ?”
Zaid ya gyaɗa masa kai, don da ma shi ne yake bashi amsar.
“To kunga, ku zo ku zauna a shagona, na sai muku abinci ku ci, da yamma idan Allah ya kaimu, zan kaiku gidan marayu, ai za ku iya zama a can ko ?”
Da sauri suka kalleshi, sannan kuma suka kalli juna, ba musu suka gyaɗa masa kai. Mutumin me suna Ila ya yi murmushi, har wa yau ya na tuna irin alkairin mahaifiyarsu gareshi.
Domin akwai wata rana da ta taɓa zuwa shagonsa ta iskeshi ya yi tagumi, ta tambayarsa; lafiya? shi ne ya shaida mata da matarsa ce ta shaihu, ga shi ko na yanka ba shi da shi.
Har wa yau ya na iya hango murmushin da ta yi a lokacin, sannan ta lale maƙudan kuɗaɗe ta damƙa masa, tare da faɗin a sha hidumar bikin suna lafiya. Har da kukansa a lokacin, don Allah ya sani yanda yake a cikin buƙatar kuɗi. Da ma jarin nasa ma bai taka kara ya karya ba.
*
“Na ji buƙatarka Malam Ila, sai dai a gaskiyar batu, ba mu da gurin zaman mutum biyu, yaro ɗaya kawai za mu iya karɓa, saboda yanzu haka ma gidan nan a cike yake da yara, yaro ɗayan ma za mu karɓeshi ne kawai dan ka dage”
Cewar shugar gidan marayun da Malam Ila ya kai su Zaid, zaune take a kan kujera, yayin da take kallon Malam Ila dake tsallaken kujerarta, Zaid da Aliyu kuma na tsaye daga bayansa.
A yau sun ci abincin da rabonsu da cin irinsa tun watanni biyar da suka wuce, wato ranar da Mommansu ta rasu, Malam Ila sai da ya tabbatar da sun ci sun ƙoshi, sannan ya kawo su nan wurin. Cike da fatan zuwansu wurin zai sauya rayuwarsu, amma maganar da matar ta yi ita ta murmushe wannan fatan nasu har garinsa.
“To yara kun dai ji... Yanzu mecece mafita ?” Cewar Malam Ila yana juyowa ya kallesu.
“Malam Ila mun gode da temakonka.... A gaskiya ba za mu iya rabuwa da juna ba, gwara kawai mu haƙura...”
Cewar Aliyu. Bai ko rufe bakinsa ba Zaid ya ɗora da:
“A'a Malam Ila, ba za ayi haka ba, ku ɗauki Aliyun kawai, ni na haƙura!”
*
Tsaye suke a harabar gidan marayun, yayin da Malam Ila ke kallonsu yana sharar ƙwalla, Aliyu kuma na kuka, Zaid na bashi baki.
“Hey! Don't cry, na ce maka zan riƙa zuwa ina dubaka...”
Shi dai Aliyu hankalinsa bai kwanta ba, dan ba ya jin zai iya zama a wurin nan. A kan idonsa Malam Ila da Zaid suka fice daga wurin.
Ashe ƙarshen ganawarsu kenan, ahse ba za su ƙara ganawa ba sai bayan wasu shekaru masu tarin yawa. Dan a cikin kwana uku kawai ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku.
Malam Ila da Zaid na fita, Malam Ilan ya kalli Zaid.
“To Zaidu, tun da ka zaɓi ka koma gidanku ka ci gaba da zama, sai ka koma can ɗin, amma duk safiya, rana kuma dare, ka riƙa zuwa kana karɓar abinci a wurina”
“Na gode Malam Ila, Allah ya saka da alkairi”
“Kai ai ba komai, ku yaran kirki ne, 'ya'yan mace ta gari, Allah ya maka albarka”
*Present day...*
*Room No.45, National Hospital, Abuja.*
KULIYA POV.
Daga kan gadon marasa lafiya, Abubakar ne kwance, yayin da na'urar oxygen ke maƙale a kan fuskarsa, kasancewar ba ya iya numfashi me kyau.
Daga gefen gadon kuma, Kuliya ne tsaye, riƙe da hannunsa, hawaye ya ke sharewa akai-akai. Idan zai iya tunawa, rabonsa da kuka tun ranar da ya bar garin kano, ranar da ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku.
Amma a yau sai ga shi ya na kukan tsoron rasa amininsa, babban abokinsa, wanda idan ka ɗauke Anna, kaf duniya babu me iya jurar halinsa in ba shi ba, kuma ba ma haka ba, a yau ɗinan Aabubakar ya sadaukar da rayuwarsa don ceton tasa rayuwar.
Shi ɗin da bai aje kowa ba bayan Annan, shi kuma da yake da mata, yara har da ƙanwa da kuma 'yan uwa, ya iya sadaukar da rayuwarsa don kawai ya ceceshi.
Daga gefe kuma Symon da hannunsa ke ɗaure da bandage ne, sakamakon raunin da ya samu a artabun da suka yi da 'yan ta'addar nan, sai Sharon wadda ke hawaye, sai kuma Kamis, Sani da Mubarak sun yi jigum-jigum cike da jimamin abun da ya samesu, don gaba ki ɗayansu abun ya shafa.
Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, kawun Abubakar wato Alhaji Musa ya shigo, tun bayan da aka gamawa Abubakar ɗin tiyata yace su kira masa shi, su kansa ba su san dalilin hakan ba.
Jin sautin muryarsa ne yasa Abubakar buɗe ido a wahalce, sannan ya kalli kawunsu wanda gaba ɗayansa yake a ruɗe.
“Abubakar?! Me ya sameka haka?”
Da ƙyar Kamis ya iya masa bayanin abun da ya faru. Kawu Musa ya zauna a kusa da Abubakar ta ɓangaren dama, yayin da Kuliya ke riƙe da hannunsa ta ɓangaren hagu.
Da ƙyar Abubakar ya kai hannunsa kan abun oxygen ɗin yana ƙoƙarin cire shi daga kan hancinsa. Ganin hakan yasa Kuliya saurin kai hannunsa kan na Abubakar domin hanashi yin abun da yake ƙoƙarin yi. Cike da dauriya Abubakar ɗin ya girgiza masa kai.
Hakan yasa jiki a sanyaye Kuliyan ya janye hannunsa daga kan na Abubakar ɗin, har ya samu ya cire abun, sannan ya kalli Kawu Musa.
”Kawu... Za... ka... iya... Tuna... Wassiyar Ummuna... Ta ƙarshe ?”
A rarrabe maganara take fita, haka kuma a wahalce, cikin wani sauti mara amo.
Hawaye na yi wa Kamu musa zuba ya gyaɗa kansa, don bi da bi maganganun matar wan nasa ta dawo masa, a sanda take kwance a aibiti cikin halin ciwon naƙuda, rai a hannun Allah, kamar dai yanda ke faruwa ɗanta a yaunzu. Hawaye ya gangaro daga idon Abubakar, da ƙyar ya iya haɗiye wani abu sannan yace.
“Dukkan wasiyyunta na cika su, na reni Mishal da kaina... Na bata kyakkyawar rayuwa... Na... Na bata farin ciki... Abu ɗaya ne ya rage...”
Ya ƙarshe yana ritse idonsa, yayin da Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cike da tausayawa. Kawu musa ya gayɗa kansa.
“Na mata alƙawarin in dai Allah ya yarda zan aurar da Mishal ga miji na gari, sannan kafin... kafin na bar duniya, zan barta a hannu na gari...”
Kawu musa ya girgiza kai cike da sallalami.
“Ka dena faɗin haka Abubakar, Insha-Allah za ka miƙe a kan ƙafafunka...”
Abubakar ya yi wani murmushi me ciwo.
“Ba na tunanin haka Kawu Musa... Ba... Ba na jin zan ta... Tashi, don haka nake so a ɗau rawa Mishal aure yanzu-yanzun nan!...”
Wani irin dokawa zuciyar Kuliya ta yi a cikin kunnuwansa. Ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta fashewar glass, kamar glass ɗin windown da aka jefa da dutsi.
Wai me ma yake ji ne ?, kawai dan an ce za ayi wa wata yarinya aure ?, sai gabansa ya yi irin wannan dukan ?, wai shikan wata jaraba ce ke damunsa kan wannan yarinyar ?. Kafin ya gama shawara da zuciyarsa, Kawu Musa yace.
“Waye mijin ?”
Abubakar ya ƙara matse hannun Kuliya dake cikin nasa, sannan ya juyo ya kalli Kuliyan.
“Al... Aliyu Zaid... Bichi... Ku... Kuliya!, Babban abokina... Na san kaf duniya, babu wanda... Zai... Zai iya riƙe Mishal in... Ba shi ba... Don haka shi ne mijin nata!...”
Sakan ɗaya... Biyu... Uku.
RAJA POV.
A karo na uku ya ƙara jan akwatin dake hannun mutumin da suka zo karɓar kaya a wurinsa, kuma shi ma mutumin kamar ɗazu yaƙi ya saki akwatin.
Raja ya ɗaga kansa sama, sannan ya sauƙe.
“Ka cika gardama, ni kuma ba na san gardama, ka fahimta ?”
“Kuɗin da kuka bamu bai cika ba, don haka sai kun ciko za mu baku kaya”
Mutumin ya faɗi yana kallon idon Raja. A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya gyaɗa kansa, tare da sakarwa mutumin akwatin.
“Na fahimta”
Ya faɗi yana neman bindigarsa a aljihun wandonsa na baya, kuma yana kamo bindigar, ya fiddo da ita, sannan ya saitata a kan mutumin, bai yi wata-wata ba, ya matsa kunamar. Ƙaran harbin bindigar ya karaɗe wurin.
Mutum ukun da suka zo tare da wanda aka harba suka yi ƙoƙarin guduwa, amma sai Rhoda da Zuzu dake tare da Raja suka buɗe musu wuta.
A nitse Raja ya sukunya saitin gawar mutumin dake yashe a ƙasa, ya kai hannunsa sannan ya finciki akwatin.
“Kun yi wa kanku, babu kuɗi, sannan babu kaya... Ko dan ga ta rai ma ai kun yi!”
Daga haka ya miƙe ya juya, Rhoda da Zuzu na take masa baya.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
_“Kamar yanda na maka bayani tun daga farko... Ina son na fito takarar sanata ne... Don haka ina buƙatar wasu 'yan kuɗaɗe masu yawa... Wanda zan yi amfani da su wurin yin campaign, kasan yanda mutanen Nigeria suke!, Kaji ne, sai da tsaba, idan ba su ganka da wani abun duniya ba, ba za su ko kalleka ba, bare su zaɓeka... Don haka na ce ka dawo kusa da ni.... Don ku min aikin da ya fi wanda kuke yimin shi a garin kano!...”_
Tar muryar Alhaji Bala ke fitowa daga cikin laptop ɗin dake gaban Raja, zaune yake a kan kujerar falo, Rhoda na zaune a gefensa. Waɗanan su ne ire-iren maganganun da suka yi da shi a ranar da suka tattauna da shi a ganawarsu ta farko. Ba tare da sanin shi Alhji Balan ba, Raja ya naɗi komai ta cikin wata na'urar ɗaukar hoto da magana, wadda ya saƙala a gaban rigarsa a waccan ranar.
Rhoda ta ɗaga hannunta, tare da bubbuga kafaɗarsa.
“Mun yi aiki me kyau Raja... Ina tunanin wannan hujjar ma kaɗai ta ishe mu... Ba ma buƙatar wata...”
Bisa ga mamakinta sai ta ga ya girgiza kansa, ya na jingina da jikin kujera.
“Basu isa ba Rhoda, muna buƙatar wasu”
Cike da mamaki take kallonsa, wata hujja za su buƙata bayan wannan ?, 'yar wannan maganar tasa da suka naɗa wadda ba ta wuce mintuna biyu ba, ita ce ta shigo da su wannan rayuwar da ba ta su ba. A ganinya wannan kaɗai ta isa ta hutar da su aikin bautar da suka sha tsawon shekaru huɗu.
“Rhoda, ba ni da ke kaɗai Alhaji Bala ya zalinta ba, ya zalinci mutu ne da dama... Kuma ba shi kaɗai ne yake zalincin ba, har da ɗansa Usman... Kin san yara nawa Usman ya yiwa fyaɗe ?”
Cike da ƙunar zuciya Rhoda ta girgiza masa kai, dan kuwa maganarsa ta tuna mata da bayanta, rayuwarta ta baya da mahaifiyarta. Dama abun da ya zamo sanadiyyar rabuwarsu da mahaifiyar tata.
“Kusan yara mata goma ya yi wa fyaɗe!...”
Idonta ta rintse tana kawar da kai. Raja ya zauna da kyau, sannan ya kamo hannaunta.
“Kada ki damu, za mu ga ƙarshen komai, za su kwashi kashinsu da hannayensu, sai an ƙwatawa kowa hakkinsa... Ba ni... Da ke kawai ba... Kowa Rhoda, i mean each and every body da suka taɓa zalinta”
A hankali wata ƙwalla ta sauƙo daga idon Rhoda, ta kwantar da kanta a kafaɗar Rajan, shi kuma ya shiga bubbuga bayanta, alamun rarrashi. A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cikin faɗin.
“Wannan hujjar ta yi kaɗan mu kai babban mutum irin Alhaji Bala ƙasa, muna buƙatar hujjojji masu tarin yawa, waɗan da ba wai ƙasa kawai za su kai shi ba, rugu-rugu za su yi da shi... Za mu kai masa wannan kayan, kuma kin san daga haka zai ƙara yarda da mu, mu kuma daga haka za mu ƙara ƙaimi wurin kai shi ƙasa!”
Rhoda ta share hawaye, tana yarda da maganar ɗan uwanta ɗaya tilo da ya rage mata a duniya, tun da har ya faɗi tasan zai cika, zai aikata duk abun da yace... A idanunsa kawai take hango irin faɗi tashin da ya riƙa yi a rayuwarsa don kawai ya ga ta samu gobe me kyau.
“Lokacin sallah ya yi, zan je masallaci”
Ya faɗi yana miƙewa, sannan ya dafa kanta, ya fice daga falon.
A balcony ya haɗu da su Zuzu. Suna zaune sai zuƙe-zuƙensu suke. Wutar da ya hango a jikin tabar Jagwado ce ta sa hayyacinsa ƙoƙarin rabuwa da gangar jikinsa.
Suma kuma sai a lokacin suka lura da shi, don haka suka

Please Login or Register in order to submit comment