Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyar, cikin gidan babu wani motsi kamar babu kowa, alhalin akwai mutum har biyar a cikin gidan.
“Wallahi wannan mara mutuncin ne!....”
Wani matashi ya faɗi daga cikin gidan, bayan ya sauƙe labulen ɗakin da suke ciki. A tsorace ya yi maganar, kuma daga yanda jikinsa ke rawa zaka fahimci hakan kalar tsoron da yake ji.
Cikin halin ko in kula wani cikin mazan dake ɗakin yace.
“Wai wa kake nufi?”
“KULIYA!”
Kusan a tare gabansu su duka ya buga, ciki kuwa harda wanda ya furta sunan, KULIYA!, wani suna ɗaya da yake firgita duk wani me laifi a garin abuja da kewatenta.
Sunansa kawai kan sa cikin mai laifi ya ɗuri ruwa, KULIYA wani irin bahagwan mutum ne, wanda ba'a gane gabansa bare bayansa, ga saurin fushi da fusata, bashi da imani ko kaɗan.
A razane suka miƙe tsaye gaba ɗaya, kuma ɗaya bayan ɗaya suka shiga leƙa windown dan tabbatar da abinda ɗayan nasu ya faɗa.
“Yanzu miye abun yi ?”
Ɗaya daga ciki ya tambaya, fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali.
“Kawai mu miƙa wuya”
“Kai baka da hankali, mu miƙa wuya fa?”
“To mu ci gaba da zama har ya shigo ya harbe mu”
Daga harabar gidan, Kuliya ya fiddo da bindigarsa wadda ke saƙale a bayansa, sannan ya nufi hanyar shiga cikin gidan gadan-gadan.
“Kuliya!, what are you trying to do ?”
Wannan macen cikin nasu ta faɗi tana bin baya sa.
“Sharon, kar ki takuramin!”
“Ba'a bamu umarni ba, dole sai mun jira umarni.....”
Sharon bata rufe bakinta ba, Kuliya ya raɓata ya wuce cikin gidan. Cike da takaicinsa ta ɗaga kanta sama tana girgiza shi, har abada Aliyu ba zai taɓa sauyawa ba.
Matasan nan na tsaye a cikin ɗakin, suna ta nemawa kansu mafita. Basu ankara ba suka ji an banko ƙofar ɗakin, kuma a cikin ƙasa da sakan sittin.
Ƙarar harbin bindigar Kuliya ya cika gidan. Kafin aka samu wani harbin da ya fito ba daga bindigar tasa ba!.
*Kano....*
*11:30pm*
Motoci biyu ne parker a wani filin Allah, wurin ba gida gaba da baya.
Duka fitilun motocin a kunne suke, kasancewar babu wani haske a wurin bayan na motocin. Motocin na kallon juna ne, yayin da wasu mutane shida ke tsaye a tsakiyarsu.
“Ku bamu saƙon”
Muryar macen cikinsu ta faɗa, wasu gardayen maza ne guda uku a bayanta, alamun dai tare suke. Yayin da take fuskantar wani matashi, wanda shi kuma mutum ɗaya ne tsaye a bayansa.
Matashin ya yi murmushi.
“Ku bamu kuɗi tukunna....”
Ya faɗi cikin rainin wayo. Sai macen ta yi murmushi, tana kawar da kitson kalabar attachment ɗin da ya sauƙo mata kan fuska.
“Ka...bamu saƙon!”
Ta maimaita masa abinda ta faɗi tun farko, sai ya kuma yin murmushi.
“Ku kira ogan naku ya zo ya karɓa muku....”
Daga cikin motar dake bayan su macen, mutum ɗaya ne zaune a gidan gaba, kansa a sama, yayin da bayansa ke jingine da jikin kujera. Waƙar lonely at the top dake tashi a cikin motar yake biyawa, yayin da idanuwansa ke a lumshe.
“Zuwan RAJA nan ba zai mana daɗi ba, dan haka ka bamu saƙon, mu juya....”
A wannan karon fushi ne kwance a fuskar matashin.
“Waye shi ?, kira mana shi ya zo ya ƙwata da ƙarfinsa”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga budurwar tana murmushi. Sannan ta juya kanta kaɗan, ba tare da ta kalli bayanta ba, idonta a kan matashin ta kira sunan na cikin motar.
“RAJA!”
A hankali mutumin cikin motar ya buɗe idonsa dake rufe, kafin ya sauƙe kansa, idonsa ya sauƙa a kan mutanen dake gaban motar tasu, ɗan guntun tsaki ya ja. Sannan ya buɗe ƙofar motar ya fito.
Hannunsa kan ƙofar motar ya ci gaba da kallonsu. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya kai hannu ya sodai tattoo ɗin kan zakin dake bayan wuyansa, ya fara takawa zuwa wajen da suke tsaye.A gaban matashin ya ja ya tsaya.
“Ka bamu kayan za mu juya”
Muryarsa me cike da kamala da kuma nutsuwa ta furta, idan ka ji muryarsa ba tare da ka ganshi ba sai ka rantse da Allah ba daga bakinsa ta futo ba, dan sam yanayinsa baya kama da yanayin muryar tasa.
“Sai kun bamu kuɗi tukkuna“
Raja ya kuma yin guntun tsaki, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Kana ji ko bana san jayyaya, sannan nakan jima banyi fushi ba, ka bamu kawai mu juya”
Wannan karon muryar tasa cikin wani irin taushi ta fito.
“Ni ma ba na san jayyaya.....”
Bai ko gama rufe bakinsa ba, Raja ya ɗauke shi da mari, sannan ya ci kwalarsa da hannunsa na dama, tare da zaro bindigarsa da hannunsa na hagu, ya ɗorata a kan matashin.
Yaron dake tsaye a bayan matashin ya fiddo da tasa bindigar ya nuna Raja da ita, yayin da mutanen Rajan ma suka fiddo da tasu bingidar. Matashin ya shiga ƙoƙarin motsa bakinsa cike da tsoro.
“Shhhhh!”
Rajan ya faɗi yana ɗauke bindigar daga kan matashin, tare da ɗora bindigar a bakinsa, alamun ya masa shiru.
“Ba na san jayyayya!......”
Ya ƙarshe yana maido da bindigar kan matashin, cike da tsoro matashin ya gyaɗa kansa, sannan ya yi wa mutuminsa alama da ya basu kayan.
Da sauri mutumin ya juya cikin motarsu ya buɗeta, sannan ya ɗuko wani brief case, ya danƙa a hannun macan nan, ita kuma macen ta miƙawa ɗaya daga cikun mazan dake tsaye a bayata.
Kuma har zuwa lokacin Raja na riƙe da kwalar matshin nan, sannan bindigar Rajan sete a gosbinsa.
Sai da mutumin su Rajan ya buɗe brief case ɗin, ya tabbatar musu da sahihancin abin da ke cikin brief case ɗin, sannan Raja ya saki matashin.
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya maida bindigar bayansa, yana kallon matashin da shanyyayun idanuwansa, hannunsa ya kai yana gyarawa matshin kwalar rigar jikinsa. Da farko saida matshin ya razana, ya ɗauka cewar wuya zai shaƙe masa. Kuma har lokacin cike da tsoro yake kallonsa.
“You are such a good boy, ka kyauta, da ka yi abinda na ce”
Kuma daga haka ya juya. Da hannu ya yi wa yaransa alama da su shiga mota.
Har motar tasu ta bar wurin matashin na tsaye a wurin yana kallonsu, a ransa yake hasaso irin masifar da ogansa zai masa idan har yasan cewa ya basu kayan ba tare da sun bashi kuɗi ba.
*Unguwar Karkasara....*
*12:30am*
“Da kyau Raja!”
Cewar Garuje, wanda yake shugaba a wurin Rajan, yana faɗin hakan tare da bubbuga kafaɗar Rajan. Bayan da ya duba kayan da ya aikasu su karɓo masa.
Raja ya yi murmushi yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Ka ga yanzu nan muka gama waya da me gida, yana ta tambayata akan kayan....”
Garujen ya kuma faɗa. Kuma yanzun ma Rajan bai ce masa komai ba, sai juyawa da ya yi ya kalli yaransa huɗu dake tsaye a bayansa,Rhoda, ta hannun damansa kenan, sai Zuzu, Alandi da kuma Jagwado. Sannan ya juyo ya kalli Garuje, a hankali cikin nutsuwarsa wannan kamillaliyar muryar tasa tace.
“Kai ma ka sanni ai”
“Ai dole ne ma na sa me gida ya maka kyauta, sbd wannan ƙwazon da ka nuna”
Lumsassun idanuwansa na ci gaba da kallon Garuje, yayinda ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
*No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja*
KULIYA POV.
Har zuwa yanzu a idonsa yana ganin abinda ya faru a ɗazu, ɗazun da ya buɗe ƙofar kai tsaye wuta ya buɗe musu. Bai ankara ba ashe wani daga cikinsu yana riƙe da bindiga, kuma shi ne ya yi yunƙurin harbinsa. Sai de cikin ikon Allah sai ya bashi damar kaucewa, bullet ɗin ya samu bango.
Kuma bayan ya juya ta kalli bangon da bullet ɗi ya fasa, juyowa ya yi ya kalli yaron da hannunsa ke karkarwa, kuma bai jira komai ba, ya riƙe gaban rigar yaron, ya shiga dukansa da hannunsa, har saida yaransa suka shigo sannan suka raba shi da shi......
“Yau ma halin aka sake?....”
Muryar Wata dattijuwar mata ta dawo da shi zahiri. Hannunsa na dama ya sauƙe daga kan bakinsa, kafin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
Bai cewa matar komai ba, har ta samu wuri ta zauna kusa da shi, matar ta ci gaba da kallonsa tana nazarinsa.
Kamar kullum, kamar yanda ya taso a wurinta, kamar yadda ta rene shi, sanye yake cikin baƙaƙen kaya, wasu jogger set ne sanye a jikin nasa, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin rigar.
Idonta ya sauƙa a kan hannunsa na dama, rauni ta gani, kuma da ma ɗazu tun da taga labarai, ta ji an sanar da cewa hukumar DSS sun yi kame a wani gida, har sun kashe mutum ɗaya, ta tabbatar da shi a cikin aikin.
Dan yanda tasan Kuliya, haka ta san yunwar cikinta, bata jin akwai wani da zai faɗa mafa halayensa. Hannun nasa ya farfashe daga kan yatsunsa, alamun dai ya daki wani abun da shi.
Kanta ta girgiza sannan ta miƙe ta bar falon. Jim kaɗan sai gata ta dawo, hannunta riƙe da plate ɗin abinci, sanna firstaid box. A kan coffe table ta aje masa abincin, sannan ta ɗauki firstaid box ɗin ta ɗora akan cinyarta kafin ta buɗe.
Hannun nasa na dama ta kama sannan ta shiga shafa masa maganin zafi a wurin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana kallonta. A duk sanda Anna zata nuna masa kulawa, idan ya kalleta sai ya ga fuskarta na rikiɗewa tana koma irin tata.
Mahaifiyarsa, mahaifiyarsa da a duk sanda zai tuna da ita sai ya tuna da mahaɗinsa, ɗan uwansa, abokin tagwaitakarsa, Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya ƙara sunansa a gaban nasa sunan, sai dai kuma idan ya ci gaba da san zurfafa a cikin tunanin LABARINSU na baya zuciyarsa ƙuna take, wani abu ne ke maƙale masa a wuya, shi bai faɗa cikinsa ba shi bai fito daga bakinsa ba.
“Ga abinci ka ci”
Anna ta faɗi a sanda ta gama shafa masa maganin,tana miƙa masa plate ɗin. Yanda yake kaiwa lomar abincin ne kawai ya shaida mata da kalar yunwar da yake ji, bisa ga dukkan alamu ko da aka yi buɗa baki bai ci abinci bw.
Masifar zurfin cikinsa da miskilancinsa da kuma taurin kansa shi ne ke haɗata faɗa da shi, dan da ace bata kawo masa abincin ba, haka zai ƙaraci zamansa a gidan, har ya tashi ya tafi ba tare da ya ce ta bashi abincin ba, alhalin shi ne wanda ya siyo kayan abincin. Kuma bama iyaka kayan abinci ba, komai ma na gidan shi ne ya siya.
“Aliyu!”
Ta kira sunansa a hankali, shi ma kuma sai ya saki spoon ɗin hannunsa ya juyo ya kalleta.
“Dan Allah ka rage yawan fushin nan, ka rage wannan zafin zuciyar taka”
“Anna ba na iya controlling kai na, as far as zan ga ana aikata laifi bana iya hana kaina ɗaukar mataki!......”
A karo na biyu ya yi magana tun bayan zuwasan gidan, tun da ya gaisheta cikin jimla ɗaya bai sake cewa komai ba sai yanzu.
“Haka ne, amma ya kamata a ce kana ragewa, ka riƙa sanyaya zuciyarka, Aliyu babu macen da zata aureka da wannan halin naka”
Ransa ya soma ɓaci, ita Anna ana gabar tana yamma, shi ya faɗa mata cewa zai yi aure ?, shi fa sam babu aure a lissafinsa, bai shirya masa ba, kuma baya jin zai shirya masa ko a nan gaba.
Sai dai ban san abinda Allah ya ƙaddaro ba, bai san ƙaddara da zata kasance ƴan kwanaki ƙalilan ba, ƙaddarar da Allah ya hukunta zata faru a 'yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara ce da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura.
“Ni na faɗa miki cewar aure nake san yi ?!”
Annan ta yi murmushi, jin muryar tasa na fita a zafafe, ko bai buɗe baki ya faɗa mata ba tasan cewa ransa ne ya ɓaci. Kuma shi da ma haka yake, abu ɗan ƙalilan ne ke ɓata masa rai.
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama yana ƙoƙarin saita kansa, dan sai bayan muryar tasa ta fito ne ya fuskanci abinda ya yi.
“Sorry Anna, zancen auren ne bana so”
Har a lokacin Anna na iya tsintar sauran fishin da bai gama sauƙe shi ba, kuma da ma shi haka muryar tasa take, kullum cikin darari, ba'a iya maganar arziƙi da shi ta minti goma, kullum idanuwansa a waje kamar me zarewa mutane su.
“Aure shi ne cikar kamala Aliyu, duk wannan muƙamin naka, da dukiyar da ka tara, da wannan shekarun naka, ba zasu baka kimar da aure zai baka ba!....”
Bai ƙara kallonta ba, bare ya amsata, dan ya lura da yau so take suyi faɗa.
TALLAH!
Salma's Graphics:
•Muna haɗa book cover.
•Banner
•poster
Kuma duka a kan ₦ 300 kacal.
Domin neman ƙarin bayani: 08130172702.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*© SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*03*
~~~
_-*If it doesn't set your soul feel free, then it isn't love...*-_
***
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja*
*07:30am*
“An ya kuwa kina ganin abun nan zai iyu ?, jiya fa ba kiga irin faɗan da muka yi da shi ba, wai ka wai dan na mata faɗa, sai ciwonta ya tashi, ko a ɗakina ma bai kwana ba.....”
Muryar Hajjara ta faɗi ta cikin wayar da take da ƙawarta Fati. Tsaye take a jikin wardrobe, yayin da hannunta na dama ke riƙe da murfin wardrobe ɗin, na hagun kuma riƙe da wayar da take.
“Wai baki yarda da ni ba ne ?, na faɗa miki shifa wannan aikinsa ba irin na sauran ba ne, aikinsa ma ya fi yankan wuƙa kaifi, ke hatta da alburushima baya faɗawa aikinsa saurin ci ba, ke de kawai ki yi abinda na ce miki, za ki kira ki bani labari....”
Hajjara ta yi dariya tana rufe wardrobe ɗin, sannan ta juyo tana kallon Fahima da ke wasa a kan gado.
“In dai har kuwa maganin nan ya yi aiki, ni nasan abinda zan baki”
Tana iya jiyo muryar Fatin cikin dariya.
“Za ki kira ki bani labari....”
Daga haka suka tattauna a kan shirin da suke, kafin ta sauƙe wayar, ta ƙarasa jikin side drawer ta buɗe, ta ɗauko maganin da Fatin ta aiko mata. Ta yi murmushi a fili, sannan ta furta.
“Yau zan ga ƙarshen ƙauna!....”.
MISHAL POV.
Tsaye take a kitchen ɗin gidansu tana dafa noodles, sanye take da baƙar skirt ɗinta ta uniform, sai farar long sleeve oxford shirt ɗin da take sakawa a ƙasan suit ɗin uniform ɗin, sai dai babu suit ɗin. Kanta parker cikin ponytail, jelar na reto a gadon bayanta.
Sallamar Hajjara ce ta sa ta juyo ta kalli bakin ƙofa, a zuciyarta kawai ta amsa sallamar, sannan ta ɗauke kanta ta ci gaba da aikinta.
Hajjara ta yi murmushi, ta ƙaraso cikin kitchen ɗin, ta yi birki a gefen Mishal. Sai da gaban Mishal ya faɗi, sannan ta ɗago da kanta ta juya ta kalleta.
Dan ta fita tsayi, da ma girman jikin ne da ita kawai, ba ta cika tsayi ba. Murmushin da ta ga kwance a fuskar Hajjaran ne ya ƙara tsoro tata, duk da ita ba gwanar tsoron ba ce.
Kuma kafin ta yi wani tunanin, Hajjara ta kai hannayenta ta kamo na Mishal dake riƙe da spoon. Da sauri Mishal ɗin ta janye hannayenta tana zaro ido.
Dole ma da wani abun da wannan matar ta shirya, ta daɗe da sanin cewa ba santa take ba, dan ba iyaka jiya ne ta taɓa tada mata da ciwonta ba.
Tana yawan ja mata matsololi da dama, bata santa!, haka take yawan faɗa mata, to me zai sa yanzu tazo tana mata murmushi.
Dakewa ta yi, dan bata san ta ga rauninta, bata san ta gane cewa ta ji tsoronta.
Hannunta ta kai ta kashe gas ɗin, sannan ta ɗauke ƙaramar tukunyar da ta ɗora noodles ɗin, ta juyeta a cikin lunchbox ɗinta ta fice ta bar mata kitchen ɗin, in yaso duk masifar da take ji da ita ta ƙare a kanta, ta ci kanta ta sha baƙin ruwa.
A parlo ta iske Mama Ladi na bawa Daala abinci. Ta yi murmushi tana aje lunchbox ɗinta a kan coffee table. Sannan ta zaga ya zuwa kan sofa, ta ɗauki suit ɗinta a inda ta ajeta, ta saka a jikinta.
“Mama ni zan wuce, ga Baba Ali nan ya zo”
Ta faɗa yayin da take gyara zaman hairband ɗin dake kanta, bayan ta ji horn ɗin motar Baba Alin.
“To a dawo lafiya, banda rashin ji”
Ta yi murmushi tana ɗaukar jakarta, tare da saɓata a bayanta. A dai-dai lokacin Abubakar da Hammad suka sauƙo a tare.
Tana kallonsu har suka ƙaraso cikin falon, ciki-ciki ta gaisheda Abubakar, dan ba wani sosai suke shiri da ita ba, saboda faɗan da yake mata.
“Yaya, gap ɗin nan ya haɗe, yaushe za mu je kasa a cire min braces ɗin nan?”
Abubakar ya miƙe tsaye, kuma ba tare da ya kalleta ba yace.
“Sai mun dawo daga meduguri....”
“Wallahi da gaske nake Aky, ta haɗe fa, idan baka yarda ba zaka iya gan!.....”
“Ya isheni haka! Ke dole ne duk abinda kike so sai an miki ?!, To ba zan kai ki a cire braces ɗin ba!”
Cikin tsawa da ƙaraji yake maganar, ya ma manta waye gabansa, dan haka kawai yake ganin baƙinta yau, maganarta ma baya san ji.
Mama Ladi ta miƙe tsaye mamaki na cinyeta, tasan ba yau ya saba mata faɗa ba, amma kuma ba ya mata cikin masifa haka, kuma ba ya mata faɗa sai ta yi laifi, amma ita a cikin wannan maganar da ta yi bata ga abun lafi ba.
Ba ƙaramar tsorata Mishal ta yi ba, ta ji ƙofofin numfashinta na neman ɗaukewa, amma duk da haka ta daure ta shiga baza idanunta a falon. Tsaye a bakin kitchen ta ga Hajjara na wani irin murmushi me kama da na mugunta.
Dama ita tasan za'a rina, shi yasa sam bata yarda da matar wan nata ba, dan ko abincinta bata ci, ita da kanta take girka abincinta.
“Ka yi haƙuri Aky!...”
Da ƙyar ta furta hakan, muryarta a shaƙe, dan bata san numfashinta ya ɗauke.
“Baki da magana da ta wuce hakan ai, ke kullum cikin aikata laifi, yau kina wannan gobe kina wancan, ni kenan kullum cikin sintiri a hanyar makarantar ku!, Kin girma amma baki san kin girma ba, saboda Allah yanzu yarinya kamar ke ace bata san ciwon kanta ba?, to bari ki ji na faɗa miki idan har baki kama kanki ba, wallahi sai na saɓa miki!”
Har yanzu cikin ƙaraji yake maganar, yayin da Mishal ta runtse idonta tana kawar da kanta gefe, duk da isashiyyar iskar dake falon ita sam bata iya jinta a huhunta, sam bata jin wata iska na kai mata inda ya dace.
“Haba Abbakar? Ya haka dan Allah?”
Mama ta faɗi cikin tausasawa.
Abubakar na maida numfashi kamar wanda ya yi gasar tsere ya kalleta. Kafin a fusace ya fice daga falon.
Hajjara ta ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, duk ƙaunar duniya sai a ce Mishal, komai Mishal komai Mishal, hatta da makarantar da take ta fi ta Hammad tsada, kuma har mota ya siya mata tare da ɗaukar mata driver, bayan ita nata ɗan a school bus yake tafiya. Koma dai miye yau ranta ya yi fari tunda har ya mata faɗa. Ta kaɗe gefen rigarta ta yi sama, dan taje ta bawa Fati labari.
“Zauna Mishal...”
Mama ta faɗi tana zaunar da ita, tare da sauƙewa jakar bayanta, ta ciro littafi a ciki ta shiga mata fiffita. Kafin ta samu ta dawo hayyacinta.
“Kin sha maganinki ?”
Kai ta gyaɗa mata tana miƙewa, ba tare da tace mata komai ba, ta ɗauki jakarta haɗi da lunchbox ɗinta ta fita.
Mama ta bi bayanta da kallo, zuciyarta cike da tausayin yarinyar.
“Allah ka kawo mata sauyin rayuwa!....”
Wata ƙila ta faɗa a bakin 'yan amin, wata ƙila Allah ya zaɓeta ne dan ta zamo silar yin addu'ar wani abu dake shirin faruwa kwanaki masu zuwa.
Addu'ar tata, ita ce ta zama silar faruwar wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwarta a 'yan kwanaki masu zuwa. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryuwar wasu lamura.
*Brickhall School, Kaura district, Abuja*
*09:40am*
RABI'A POV.
“Gashi, driverna na bawa saƙo ya siyo min, kuma ya ce ya nema amma bai samo irin wannan ɗayan ba, sai ɗan kwali ya samo...”
Cewar Mishal, yayin da take miƙa mata lalle ɗan kwali.
Rabi'a ta sa hannu ta karɓa. Tsaye suke a bayan ajujuwan makarantar, a ƙofar store, inda ake aje kayan share-share na makarantar.
Rab'a ta juya ta kalli dama da hagun inda suke tsaye.
“A ina zamu yi kenan ?”
“Ga kujeru a can, muje mu zauna”
Kuma da ga haka, suka ƙarasa inda kujerun suke, suka zauna, sannan Rabi ta shiga haɗa lallen. Yayin da Mishal ke dudduba jakarta, a ciki ta ɗauko biscuits, ta buɗe ta shiga ci. Cike da mamaki Rabi'a ta kalleta.
“Bakya azumi ne ?”
Mishal ta yi murmushi, har karafunan braces ɗin da aka sa mata suna bayyana.
“Wahala ce ba zan iya ba, ga zuwa makaranta ga azumi, inaaa!”
Rabi'a ta yi dariya, a kamaninta idan ka ganta sai ka ce tana da wasu shekaru masu yawa,amma da zarar ka yi magana da ita ko na minti uku ne za ka fahimci yarintarta ƙarara.
“Shekarunki nawa ?”
Mishal ta dakata da taunar biscuits ɗin dake bakinta, ta ɗan ɗaga olive green colour eyes ɗinta, tana san ta tuna shekarun nata. Kafin ta sauƙe su a kan Rabi'a dake ɗaure ledar lallen da ta gama haɗawa.
“I’m 17, next year zan cika 18....”
Rabi ta ɗage girarta cikin murmushi tana kallon lallen da ta gama ɗurewa.
“Ki ce babbar yarinya ce...”
Mishal ta yi dariya, wani abu da ba kasafai ta cika yinsa ba.
“Ke fa shekarun ki nawa ?”
“Ki ƙara biyu a kan naki”
“Sha tara ?”
Rabi'a ta gyaɗa mata kai. Ganin ta gama haɗa lallen yasa Mishal maida sauran biscuits ɗinta cikin jaka, tana karkaɗe hannunta, tare da taune sauran wanda ke bakinta.
Ta miƙawa Rabi'a hannunta na dama, sannan Rabi'a ta fara zana mata lallen.
“Wow!, Amma fa ta yi kyau”
Mishal ta faɗi a karo na barkatai, sanda aka gama zanen lallen, ta ɗaga hannayenta sama yafi sau a ƙirga, sai kallon lallen take tana sakewa. Ba za ta ce when last rabonta da ba.
“Nawa ne kuɗin lallen ?”
Sai ta ga Rabi'a ta haɗe rai.
“Shekaru nawa na baki ?”
“Biyu”
Ta masa tana mamakin abinda ya haɗa tambayar da ta mata da kuma wannan batun.
”Kinga kenan ni yayarki ce, kuma ina matsayin yayarki ai bazan karɓi kuɗin lallenki ba...”
“Yanzu mun zama 'yan uwa kenan ?”
Rabi'a ta gyaɗa mata kai tana murmushi.
“Adawiyya ?”
Zuciyar Rabi'a ta dunguwar a lokaci guda, Adawiyya?!, kaf duniyar nan mutane biyu ne ke kiranta da sunan, Ummanta, da kuma yayarta Baby!.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger state*
*05:30pm*
“Wai har sun muku hutun?”
Cewar Saratu, yayin da takewa Rabi ƙananun kalba.
“An musu dai”
Rabi ta bata amsa. Suna zaune ne a ƙofar ɗakinsu, bayan Rabi'an ta dawo daga wurin aikinta ne ta share gidan tas, duk da wahalar rana da kuma aikin da ta je ta yi, ga kuma azumin dake bakinta.
Amma haka ta share gudan tas, kuma bayan ta gama ta ɗora da wanke-wanke. A lokacin Saratun tace mata ta zo su fara kalbar, tun da ta riga ta tsefe.
“Ai har ke, tun da de ba za ki je makarantar ba har sai an koma”
Rabi dai bata sake cewa komai ba, dan tun da ta ambaci kalmar 'makaranta', tunaninta ya tafi ɗazu, ta shiga tuna abinda ya faru tsakaninta da sabuwar ƙanwarta a ɗazun.
“Jibi za mu tafi garinmu, a can za mu yi bikin sallah”
Muryar Mishal ɗin ta katseta a ɗazun. Sai kawai ta yi murmushi.
“Ina ne garin ku ?”
“Maiduguri”
Mishal ta bata amsa tana firfita lallen hannunta da iskar bakinta. Rabi'a ta gyaɗa kanta. Tana ƙara tabbatarwa da kanta hasashen da take a kan Mishal ɗin, na kasancewarta shuwa arab.
“Shikenan, na san zuwa yanzu an koma break, bari naje na share inda aka ɓata, ki kula da kanki, Allah ya dawo da ku lafiya, sannan ki gaida Mamanki idan kin koma gida”
Ta faɗi tana ƙoƙarin tashi, amma maganar Mishal ɗin ta gaba ita ce ta hanata tashin.
“Mamata bata raye, kuma tun a sanda zata haifeni ta rasu, ban san babana ba ma, lokacin da cikina ya rasu, tare da yayana kawai na taso.....”
Rabi'a ba za ta iya cewa ga abinda take tunanin ba a lokacin, tasan dai kawai ta tsirawa ƙaramar yarinyar ido ne, tana nazarin ya akayi ta rayu tsawon shekarunta babu iyaye. Ita da ta rasa iyaka mahaifiya ma kawai rayuwarta ta hargitse bare ita da ta rasa duka biyun.
Kuma bama wannan ba, ba ma ta sansu ba, bata taɓa ganin ko ɗaya daga cikinsu ba.
“Ke Rabi? Tashi ki zo ki soya mana doyar nan!”
Muryar Habiba ta dawo da ita zahiri, a hankali dubanta ya kai kan Habiban dake tsaye a kansu.
“Umma ki bari mana na ƙarasa mata, saura guda biyu fa....”
“Ban yi niyya ba, yanzu nake so ta tashi ta min aiki na....”
Ba tare da Rabi'a tace komai ba, ta shiga ƙoƙarin jan doguwar kalbar dake riƙe a hannun Saratu dan

Please Login or Register in order to submit comment