Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shi, ya dawo nan ya zauna. A hankali wata ƙwalla ta gangaro daga idonsa, bayan da ya tuna irin gararin rayuwar da take ciki, yanzu kuma ga wani baƙin tabo me matuƙar muni ta ƙara samu.
Amma alƙawari ya yi wa kansa, na babu abun da zai hana shi aurenta, ko da sama da ƙasa za su haɗe, ko da duniyar ce za ta tashi, ko da kuwa aurenta shi ne abu na ƙarshe da zai yi a duniyar nan, ba fyaɗ... Kasa ƙarasa kalmar ya yi a ransa, don haka kawai ya tsalleketa ya tafi tunaninsa na gaba; ko da cuta me karya garkuwar jiki ce tare da ita, ba zata hanashi aurenta ba, wani kalar so yake mata da ya wuce soyyaya kawai, sai dai soyyayar haɗuwar jini, kasancewarta ɗaya daga cikin ahalinsa shi ne ya ƙara ninka soyyayarta a ransa.
Ganin ruwan da aka saka masa ya ƙare yasa ya kai hannunsa ya cire allurar, sannan ya manne wurin da plaster, saboda kada jini ya zubo, miƙewa ya yi, duk da ya na jin jikinsa babu ƙwari, amma haka ya taka a daddafe har ya isa jikin gadon da Rabi'a ke kwance kamar gawa.
Zama ya yi a gefen gadon ya na kallon fuskarta, sannan ya kamo hannunta na dama, wanda ke saƙale da clip na wata na'ura dake jikinta, hannunsa ya saka cikin nata ya damƙe, dubansa ya dawo kan fuskarta. Wadda a yanzu ta sauya suffa daga tata ta da, sakamakon wani yanka dake gefen fuskarta na hagu.
Ɗinkin da ya ga an yiwa raunin ya sa ya fahimci girmansa, ga kuma yanda fuskarta ta ɗan tattare daga gefen hagun, saboda yankan da aka mata, amma duk da haka kammanin fuskarta ba su sauya ba.
Sai kuma gashin kanta da ya lura da kamar sun rage masa tsayi, duk da shi bai taɓa ganin gashinta ba, amma ya yana da yaƙinin cewa gashin kan nata ba haka yake ba, kuma ya fahimci kamar saboda raunukan dake kanta aka rage yawan gashin.
Idanuwanta a rufe, fatar bakinta ta yi fari sol, a kallo ɗaya idan ka mata sai ka ce maccacciya ce, shi kansa ba don Huzaifa ya tabbatar masa da tana raye ba da ba zai yarda da tana da ran ba.
Jikinta sanye yake da rigar asibitin, wadda take blue colour, sai farin bargon asibitin da aka rufa mata a rabin jikinta.
Ya tuna yanayin murmushinta, ya tuna sanyin maganarta, ya tuna nutsuwarta, ya tuna hankalinta, ya tuna yanda take kallonsa da idanuwanta masu kama da na Aliyu, ya tuna komai a kanta, hatta da ranar da ya fara ganinta sai da ya tuna.
Idonsa ya rintse a sanda hoton file ɗinta da ya buɗe a ɗazu ya dawo masa cikin tunani, wai mutum biyar ko sama da haka ne suka mata fyaɗe, sannan bayan haka ma harda raunikan a jikinta, ga kuma dukan kanta da aka yi, wanda shi ne maƙasudin shigarta doguwar suma. A hankali ya buɗe idanunsa nasa, wanda ya yi ja kamar sabon barkwano.
A dai-dai lokacin Rhoda da ya aika ta shigo ɗakin, juyawa ya yi ya kalleta, a sanda ta ke ƙarasowa ciki. Sai kuma ya ɗauke kansa ya na dawowa da dubansa kan Rabi'a. Ya ɗaga kafaɗarsa kafin yace.
“Me kika gano?”
Ya tambaya cikin wata murya me ɗaci, Rhoda ta haɗiye yawu sannan tace.
“Na yi magana da waɗanda suka tsince ta a lokacin, kuma su ne suka kawota wannan asibitin, amma su... sun ce a gefen hanya suka ganta, nannaɗe cikin bargo, ko... Ko... Tufafi... Ba... Babu a jikin... jikinta!...”
Raja ya rintse idonsa, jikinsa har karkarwa yake, ga kuma hannun Rabin da ya ƙara damƙewa cikin nasa, Allah ne kaɗai ya san yanda zuciyarsa ke tafarfasa, shi kansa ya na mamakin yanda yake iya riƙe kansa a wannan lokacin, amma shi ya riga da ya san kansa, ba ya iya ɗaukar ɓacin rai, ya kan jima ransa bai ɓaci ba, don ba komai ne ke ɓata masa rai ba, amma idam har ransa ya ɓaci to na kowa ma kan iya ɓaci.
“Bargo?”
Ya tambaya ya na ɗan juyowa da kansa ya kalleta.
“Eh bargo, kuma sun ce wata ƙila ma a kan bargon aka haike mata... Dan sun ga something like spam a ... A jikin bargon!”
Yanzu kam miƙewa ya yi tsaye, kuma ba tare da ya damu ba ya nufi kan wata chest drawer, ya kai hannunsa ya yi fatali da kayan kai, ƙaran abubuwan da suka fashe sai da suka razana Rhoda. Da gudu ta yi kansa ta na riƙeshi.
“Zaid!, Zaid! Ka nutsu, ka nutsu ka ji”
Ta faɗi hawaye na mata zuba, yayin da take bubbuga kafaɗarsa.
Ƙofar ɗakin aka turo, wata nurse ta leƙo da kanta.
“Lafiya kuwa?”
Rhoda ta juya ta kalleta.
“Lafiya, mun gode, za ki iya tafiya”
Nurse ɗin ta taɓe baki ta na jan ƙofar, da ma wucewa ta zo yi ta ji ƙara, shi ya sa gulmarta ta motsa, har ta kaita ga leƙowa don ganin meke going.
“Ka nustu ka ji?”
Cewar Rhoda ta na shafa ƙirjin Raja, wanda yake huci kamar wani zakin da ya je farauta bai samo komai ba.
Hannunsa ta kama ta zaunar da shi a kan kujera, tana shafa kansa. Idonsa ƙir a kan Rabi, wani abu me ɗaci yana kai kawo daga maƙogwaronsa zuwa bakinsa, ga wani ɗaci da zafi da ransa ke masa, ji yake kamar wuta ce kr ci a ƙirjin nasa, kamar da aka tsire zuciyarsa a tukubar tsire.
“Ga shi... Karɓi ka sha”
Kansa ya ɗan ɗaga ya kalli Rhoda dake miƙa masa cup ɗauke da ruwa. Karɓa ya yi ya sha, a lokacin da ita kuma Rhodan take zama a kusa da shi, hannunta ta kai ta share hawayenta.
“Wannan ba shi ne mafita ba Zaid, kamata ya yi a ce ka yi tunanin mafita ba wai fusata ba, akwai ranar da za mu huce haushinmu a kan wanda suka aikatawa Ammata haka”
Ya juyo ya kalleta ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, mafita? Tabbasa ta na da gaskiya, haka ya kamata ace ya kasance, kamata ya yi ace ya nemo wata mafitar da za su iya kama masu lefin, dan a nan me lefin ba ɗaya ko biyu ba ne, mutum biyar ake zargi, wata ƙila ma sama da haka.
Hannunsa na dama ya dunƙule ya ɗora a kan bakinsa, sannan ya rufe idonsa dan samun nutsuwa, ta yanda zai yi tunani me kyau. Kusan shuɗewar mintuna goma, sannan ya buɗe idonsa.
“Shin kin tambayesu da bargon suka kawota nan?”
Rhoda ta ɗan kalleshi.
“Idan ba da bargon ba to da ne za su kawota nan ɗin?”
“Correct, makamar mu ta farko kenan, ki tambaya mana Huzaifa, shin har yanzu wannan bargon ya na nan?, In har ya na nan, to wannan bargon shi ne madafarmu, ta hanyarsa za mu iya kama masu lefin”
“Ok”
Raja ya juya ya ƙara meda idonsa kan Rabi'a.
“Wallahi!, Wallahi!, Wallahi! Rhoda idan har... Na kama me laifin nan, ba zan sassauta masa ba, sai na tabbatar da na gana masa azabar da tun da uw*rsa ta kawo shi duniya ba'a taɓa masa ba, sai na tabbatar da ya yi wata ɗaya ba tare da ya ga hasken rana ba, sai na tabbatar da ya kwana a cikin fitsarinsa, sai na tabbatar da bai ƙara ko da kusantar macen da ba ta hallata gareshi ba, sai na ɗai-ɗaita rayuwarsa, wannan alƙawarina ne!”.
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
Tana zaune a bakin gadonta, yayin da take cire sliders ɗin ƙafarta, ƙafafun nata ta ɗauke daga ƙasa, ta ɗorasu a kan gado, tana jan bargo dan rufe ƙafafunta nata, aka turo ƙofar ɗakin.
Kallon ƙofar ta yi, a sanda Kuliya yake shigowa, ganinsa ya sa ta fasa kwanciya ta zauna, cike da mamaki take kallonsa.
“Me ya faru?”
Ta tambaya. Ba tare da ya amsata ba, ya zagaya ta ɗayan ɓangaren gadon ya zauna, ya na cire takalman ƙafarsa.
Mamakin dake kan fuskar Mishal a yanzu ya ma fi na ɗazu, ido waje take kallonsa.
“Wai... Wai me yake faru?...”
Ba ta ko ƙarasa faɗin kalaman ba, ya janyota jikinsa, tare da kwantar da ita. Idanuwanta suka ƙara girma wajen kallonsa. Wai me bawan Allahn nan yake nufi da ita ne?, me yake shirin yi haka?.
Sakata ya yi a tsakiyar hannayensa, ya kwantar da kanta a ƙirjinsa, ya matseta a jikinsa sosai, har wata ajiyar zuciya yake sauƙewa.
“Ab... Abu Aswad”
Kafaɗarsa ta dama ya ɗafa yana ƙara kewaye hannunsa dake jikinta. Alamun dai ya na jinta.
“Me ya faru?”
Ta tambaya ta na shaƙar ƙashin turarensa.
“Babu komai, kawai de ba zan iya ba ci ba tare da matata ba ne”
Muryarsa ta furta hakan a hankali cikin duhun daren. Shiru ya ƙara rasta ɗakin, jin yanda yake sauƙe ajiyar zuciya, ya sa Mishal saka hannayenta ta kewaye shi ita ma.
“Abu Aswad”
“Ummm Teddy Bear”
“I hate you”
Tana jin sautin murmushinsa a kanta.
“And i love you”
“I hate you ”
“I said i love you”
Kusan a tare suka yi dariya.
“Gobe akwai school, ki kwanta ki yi bacci”
Kwanciyarta ta gyara a jikinsa tana lumshewa idonta.
*One hug fixes everything...*
*Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja.*
RABI'A POV.
_“Na roƙe ku da girman Allah da kada ku taɓamin mutuncina, dan Allah, dan Allah kada ku haikemin!...”_
_Irin magiyar da ta riƙa yi wa samarin nan da suka saceta kenan a waccan ranar, babu kalar magiyar da ba ta musu ba, amma haka suka shiga da ita cikin wani gida, suka danganata da ɗaki._
_Duk da tashin hankalin da take ciki a wancan lokacin, bai hanata gane fuskokinsu ba, su biyar ne cas, sannan ɗaya bayan ɗaya ta na da hoton kowannensu a cikin kanta. Miƙewa ta yi kan gwiwoyinta a kan gadon da suka cillata, sannan ta haɗe hannayenta ta na binsu da kallo, hawaye na mata zuba._
_“Dan Allah, dan Allah, na roƙeku da Allah da kada ku aikata min haka... Dan Allah kada ku keta min martabata, dan Allah, na haɗaku da Allah, Wallahi ba ni da kowa, ba ni da komai, yanzu haka rayuwata ta na cikin wani hali, dan Allah...”._
_Kalaman suka tsaya a maƙoshinta, sakamakon ganin da ta yi kowanne a cikinsu ya na cire tufafin jikinsa, basu damu da ko kallonta ba, ballantana su saurari abun da take faɗi. kukanta ta ƙarawa ƙarfi ta na rintse idonta._
_“Wai me ya sa mutane ba su san Allah ba? An haɗasu da Allah amma sai ka ce da wani sheɗan aka haɗasu, me makon mutum ya bar abun da yake sai ma ya ƙarawa abun ƙaimi, dan Allah na roƙeku...”_
_Ta ci gaba da roƙonsu, a lokacin da Usee yace._
_“Kai duk ta bi ta cika mana kunne, dallah kusa ta yi shiru!”_
_Jaz ne ya ɗauko ƙarfen abun shisharsu me kauri, ba tare da Rabi ta ankara ba, saboda idanuwanta da suke a kulle, ta ji sauƙar yankan wani abu me kaifi a gefen fuskarta, hakan ya sa ta buɗe idonta da sauri, wani kalar raɗaɗin azaba ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, nan take ta ƙwala wani uban salatin da sai da gidan ya amsa, gefen fuskar tata ya yanku ba kaɗan ba._
_“Kai dallah mahaukaci! Cewa na yi ka sata ta yi shiru ba wai ta ƙara volume ba!”_
Cewar Usee ya na rarumar wata vase, sannan ya ɗaga ta sama, ya bugawa Rabi a tsakiyar kanta. Nan take Rabi ta ji wani dimmm, kamar injinan da suke aiki a kanta sun dena, komai ya tsaya cak, babu wani abu dake aiki, kan kace me, jini ya wanke mata fuska. Babu shiri ta faɗi a ka gadon._
_Duk da idonta a lumshe yake, ta na jin sanda suke rabata da tufafin jikinta, hakan ya sa ta buɗe idonta a wahalce, sai dai hoton abun da take gani ya koma ja, saboda jinin da ya wanke mata fuska, ba sosai take cikin hayyacinta ba, amma ta na ji ta na gani haka suka shiga haike mata ɗaya bayan ɗaya._
_Duk da irin raɗaɗin azabar da take ji, ba ta da damar yin ihun neman agaji, ta na kwance ne a wurin kamar gawa, amma da ko wace azaba da suke mata jikinta ya na amsawa, ko wanne a cikinsu sai da ya haike mata sau biyu, tun tana buɗewa idonta fa lumshe har sai da komai na kanta ya ɗauke, ji da ganinta suka yi nisa, numfashinta ya yi sama._
_“Usee kamar yarinyar nan fa ta mutu”_
_Usman ya ɗan karkato da kansa kaɗan ya kalli kan gadon, inda Rabi ke kwance malale cikin jini, babu tufafi a jikinta. Sai ya zuƙi sigarinsa, ya furzar ya na faɗin._
_“Ku ɗauketa ku cillar da ita, idan abun sha ya ƙare, me za ayi da kwalba?”_
_Ba tare da ɓata lokaci ba suka cika umarninsa, a cikin blanket ɗin dake kan gadon suka nannaɗe, sannan suka ɗauketa suka saka a mota, suka fita daga gidan. Sun ɗan yi tafiya me tsayi daga gidan Usman ɗin, kafin suka samu gefen titi, suka faki ido, duk da dare ne ,babu kowa a layin, suka cillar da ita a wurin kafin suka ƙara mai._
(Ya Ilahi ya Allah!...).
A hankali wata siririyar ƙwalla ta zubo daga idon Rabi wada ke kwance a kan gadon marasa lafiya, tana nan kwance kamar gawa, kuma idanuwanta a lumshe. Wata ƙwallar ce ta sake gangarowa daga idonta ta shiga kunnenta. Sannan a hankali bakinta ya buɗe, cikin wata dasasshiyar murya ta fara faɗin;
“Da... Dan... Dan A... Allah, kad... Kada ku... Kada ku min... Ka... Kar ku... Cutar... Cutar da ni... Ni...”
Haka bakinta ya ci gaba da faɗi, kafin kuma jikinta ya fara jijjiga, da alama duk abun da ya faru a waccan ranar take gani a cikin mafarkinta.
Cikin abun da bai wuce daƙiƙa ɗaya ba, ta wangale idanuwanta tar, ta na maida numfashi kamar wadda ta yi wani aikin ƙarfi, idonta ta ƙara lumshewa, sannan ta buɗe su tar.
Kafin ta miƙe zaune, ta na ta dube-dube, sai kallon ɗakin take, kafin dubanta ya dawo jikinta, tabbas ta na asibiti ne, to duk yanda aka yi ɓacin ran da Raja ya saka mata ne ya sa ta suma, shi ne aka samu wani bawan Allahn ya kawota asibiti, har ta yi mafarkin an mata fyaɗe.
Wanna hasashen da zuciyarta ta yi ne ya sa ta sauƙe ajiyar zuciya, haka ne ma, haba!, da ma in ba haka ba ta ya za'a yi ace an mata fyaɗe?!. Hannunta ta kai ta ciccire na'urorin da aka saka mata a jikinta, sannan ta shiga ƙoƙarin sauƙo da ƙafacunta ƙasa, ta daddafa har ta samu ta iya sauƙa daga kan gadon.
Sai de me?, miƙewar tata ke da wuya ta ji ƙasanta ya yi wata irin amsawa, ba wai amsawa ta zafi ba, a'a, ji ta yi kamar an saka wani abu an ɗaure wurin, duk da haka ba ta karaya ba, wannan hasashen da zuciyarta ta yi shi ne ya ba ta ƙwarin gwiwa da kuma na zuciya, haka ta tattaka cikin wani irin taku me kama da na 'yan koyon tafiya, ta nufi banɗaki.
Daɗewar da ƙafafunta suka yi ba su yi tafiya ba ya sa suke amsawa idan ta na taku, ƙofar bayin ta tura, sannan ta shiga, kai tsaye jikin mirror ta isa, kuma abun da ta gani shi ne ya rikirkito da duniyarta ƙasa. Wata tsawa da walƙiya suka haska a cikin kanta, wani irin tashin hankali da ba ta san akwai irinsa a duniya ba ya ziyarceta.
Wannan yankan da aka mata a gefen fuska, ya na nan, har da ɗinki an yi wa wurin, dan har ya warke an cire zaren. Sannan ga gashin kanta da aka yanke mata, gashinta da a da yake sauƙowa har gadon bayanta, shi ne yanzu yake iyaka kafaɗunta, ga kuma tabon dukan da aka mata a kanta. Sannan wannan raunin fuskar tata shi ne ya ɗan sauya kammanin fuskarta, duk da ba du ba, amma yanayin fuskar tata ya sauya.
Waɗanan alamomin su ne suka ƙaryata hasahsen zuciyarta, waɗanan alamomin su ne suka murmushe fatanta har garinsa, wanan alamomi su ne suka tabbatar mata da duk abin da ya faru a waccan ranar ba mafarki ba ne, gaskiya ne, da gaske ne cewar waɗanan mugayen samarin guda biyar, sun haike mata, da gaske ne cewar yanzu ita ba ta da wata martaba kamar ta sauran mata, kuma da gaske ne cewar ita yanzu ba budurwa ba ce, yanzu ita ba ta da wata kima da daraja wadda jama'a za su kalleta da ita, ba ta da wani abu da za ta nunawa mijin da za ta aura.
A lokacin da ƙwaƙwalwarta ta kai ƙarshe wurin zayyano mata waɗanan kalaman, a dai-dai lokacin ne ta ɗago da hannunta ta shafa fuskarta, ta taɓa kanta. Nan take ta ji wani kukan ɓacin rai da na tashin hankali sun haɗe wuri guda sun tsaga haƙwaranta, sun raba laɓanta, sun fito cikin 'yancinsu. Wani kalar kuka take me sauti, jikinta har rawa yake.
“Me ya sa ni ba ni da ƙaddara me kyau?!, me ya sa komai nawa yake rugujewa?! Me ya sa ni ba zan yi farin ciki kamar kowa ba?!, Me ya sa za'a zaɓi da a lalata min rayuwa?!, Me na yi haka?! Wani kalar zunubi gareni?!, Allah na tuba ka yafemin, Allah na roƙeka da kada ka ƙara ɗoramin wata jarrabawa bayan wannan, ya Allah na cutu, an cutar da ni, kai ne me girma, kai ne sama da kowa, kai ne sarkin da babu wani me milki irin nasa, Allah kana gani ya Allah! Ya Allah ka bi min haƙƙina!”
Cikin gunjin kuka da ƙaraji take furta hakan, ta na yi tana kallon sama, can kuma da takaici ya ciwota ta sa hannunta ta ture kayan da suke kan mirrorn. Sannan ta saki wani ƙaran takaici, ta riƙe kanta tana faɗin.
“Me ya sa komai sai ni?, me yasaaaa!”
Kuma a dai-dai lokacin aka turo ƙofar banɗakin.
RAJA POV.
Kamar Kullum, yau ma ya na zaune a gaban gadon Rabi ya na kallonta, yau kwanansa biyar kenan ya na jinyarta, kuma in har ya zauna a wurin nan ba ya tashi sai lokacin sallah, haka Rhoda za ta zo ta yi ta masa mitar ba ya san cin abinci, ko kuma ta kawo masa abincin, amma ba zai ci ba.
Wayarsa ce ta yi ƙara, alamun shigowar kira, sai da ta yi ringing kusan sau uku, sannan ya ja dogon tsaki ya na saka hannunsa a aljihu ya zaro wayar. 'Huzaifa' ya gani rubuce kan screen ɗin, sai ya ɗaga kiran ya na dawowa da dubansa kan fuskarta.
Huzaifan ne ya masa magana kan ya zo office ya na san ganinsa, ba dan ya so ba haka ya tashi ya je office ɗin. Kuma sun ɗan jima suna tattaunawa kan gwaje-gwajen da ya ce a yiwa Rabi'an, kuma an yi ɗin, sannan result ya yi kyau, babu wata matsala tare da ita, komai nata lafiya ƙalau, matsala ɗaya ce, ita ce wanan doguwar sumar da ta yi, kuma ga shi ba su san takamemen lokacin da za ta farfaɗo ba, duk da ya ji daɗin kyan result ɗin, sai kuma zuciyarsa ta cika fal da tsoron kada ya rasata, tun da sun ce ba su san lokacin da za ta tashi ba.
Da waɗanan saƙe-saƙen ya iso ƙofar ɗakin, sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, wani irin bugu zuciyarsa ta yi, a sanda ya kalli kan gadon ya ga wayam, kuma kafin ya yi wani tunani, ya jiyo kukanta haɗe da maganarta a cikin bayi.
Tsabar kiɗima bai san sanda ya saki file ɗin hannunsa ba, sannan ya nufi banɗakin da gudu.
Kallonsa ta tsaya ta na yi da jajayen idanunwata, waɗanda bai hango komai a ciki ba face ɓacin rai da takaici, bai san me ya da ba, sai ya samu kansa da kasa ƙarasawa cikin bayin.
Nan take fuskar Rabi ta rikeɗe zuwa mamaki ma bayyani, wai me ya sa Raja ba zai rabu da ita ba ne, ta ya aka yi ya san inda take?, tukkunna ma ta ya aka yi ta zo asibiti?, kuma ma me yake a nan ɗin?.
“Me kake a nan?”
Ta tambaya tana ja da baya, a wannan karon da Raja ya saurari muryarta, sai hankalinsa ya dawo jikinsa, ta farka!, Rabi'a ta farka, sai ya shiga takowa cikin banɗakin fuskarsa ɗauke da murmushi, a gefe guda kuma ga hawaye na zubowa daga idonsa.
“Ka dakata daga inda kake!”
Ta faɗa cikin ƙaraji, ta na nuna shi da ɗan yatsa. Cak, ƙafafun Raja suka tsaya, baki sake yake kallonta.
“Kada... Ka ƙara ko da taku ɗaya ne”
Still bai ce komai ba, kawai ya tsaya ya na kallon fuskarta.
“Ka juya ka fita, ba na san ganinka”
Wata iriyar hautsinawa zuciyarsa ta yi a ma'ajinta, bakinsa da zuciyarsa suka shiga rawa a lokaci guda, da ƙyar ya iya faɗin.
“Ni... Ni ne fa Ammata...”
“Kada ka ƙara kiran sunan!”
Ta faɗi a tsawace ta na nuna masa ɗan yatsa, idanunwata sun firfito waje, sannan ta ci gaba.
“Ba na san ganinka Zaid, ka fita daga nan, babu abin da ya haɗa hanyata da ta ɗan daba, me kashe mutane! You are a goon Zaid!”
Wannan karon muryar tata a raunane ta fito, kuma har zuwa yanzu ƙafafunta rawa suke, ta kasa tsayawa a gu ɗaya, saboda jikinta babu ƙarfi, hatta da maganar da take ƙarfin hali kawai take.
“Na yi nadamar saninka da na yi, na yi nadamar barin zuciyata ta fara sanka, na yi nadamar haihuwata ma da aka yi, na yi na damar komai a duniyar nan.... Da ma duka maza halinki ɗaya, baku da kirki, kanku kawai kuka sani, kun fi san kanku a kan komai, in dai za ku samu abu to kowa ma ya rasa, kun fiya san kai da yawa, wani mugu ya lalata rayuwar me sunana, shi ne har ta samu cikinka... Sannan kuma tsabar san kai irin na kakana, shi ne ya koreta daga gidansa, wai don ta ƙi yarda ta zubar da cikin jikinta ba... Daga nan kuma sai babana... Babana ya lalata rayuwar Ummana, yanzu kuma tawa rayuwar ce aka lalata, wasu mugaye ne suka lalata min rayuwa... Me ya sa ma na sanka Raja?, eh? Na ce me ya sa?!”
Ta tambaya tana nuna shi da ɗan yatsa, Raja da ya daskare a wurin dan tsabar mamaki ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, abubuwa da dama sun haɗu cikin maganar tata, na farko ta ambaci cewar zuciyarta tana sansa, na biyu kuma yau ita da bakinta take furta cewa shi jininta ne, ita da bakinta ta furta masa labarin mahaifiyarsu da shi kansa bai sani ba.
“Ka fita daga nan, idan zai iyu ka fita daga rayuwata!”
Ta faɗi tana nuna masa hanya cikin kuka, a memakon Rajan ya fita kamar yadda ta buƙata, sai ya ci gaba da takowa zuwa gabanta, kuma kafin ta yi wani yunƙuri ya haɗata da jikinsa, ya rungumeta sosai ya na sauƙe ajiyar zuciya.
Rabi'a ta saki wani sabon kuka, don da ma abun da take buƙata a irin wannan lokacin kenan, ta na buƙatar wani a kusa da ita, tana buƙatar jin ɗumin wani a jikinta, ta na san ta samu kafaɗar da za ta kwantar da kanta ta rera kukanta yanda take so. Don haka ta ɗago da hannayenta ta kewayasu ta bayansa ta ƙara ƙanƙameshi tana sakin kukan cikin 'yancinsa.
Raja ya ja hancinsa ya na ɗaga kansa sama, tare da ƙara riƙe Rabi a cikin jikinsa da kyau.
Sai dai kuma cikin sakan ɗaya... Biyu... Uku...
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*
A hankali motar Raja ta tsaya a bakin lungun su Rabi, daga cikin motar shi ne zaune a mazaunin driver, yayin da ita kuma Rabin ke zaune a gefensa. Sanye take cikin wata blue abaya, wadda Rahoda ta kawo mata ɗazu, ta yafa mayafin abayar a kanta, har zuwa gefen fuskarta na hagu da ta ɗan rufe gun ya kan nan.
A jiya da take cikin jikin Raja tana kuka, ta manta ma da wa take tare, ta manta a cikin jikin wa take, sai a sakan na uku da aka turo ƙofar bayin, a lokacin kuma hankalinta ya dawo jikinta, ta yi saurin sakin Raja ta na tureshi baya, sannan ta zuba idonta a bakin ƙofar bayin, inda Rhoda ke tsaye ta na kallonsu.
Kuma bayan faruwar hakan Rajan bai ƙara minti ɗaya a wurin ba ya fice, da Rhodan suka zauna har ta temaka mata ta yi wanka, ta ɗauro alwala ta zo ta shiga biyan sallollin da ake binta, duk da babu yanda Rhodan ba ta yi da ita ba kan ta fara cin abincin da ta zo da shi, amma fir ta ƙi.
Haka ta yi ta jera

Please Login or Register in order to submit comment