Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idonsa ya sauƙa kan wata rumfar me ƙosai, wutar da ya yi arba da ita tana ci a cikin murhunta ta tuno masa ƙiyayyarsa da wuta.
*2008.*
*Gidan Maman Rhoda, Kano...*
*08:30 PM.*
“Zaid miƙo min kwanon can!”
Cewar Maman Rhoda tana nunawa Zaid kwanon dake ɗauke da farfesun kifi, Zaid ya ɗauki kwanon sannan ya miƙa mata, zaune suke a kan carpet ɗin dake falo, Rhoda na daga gefen Zaid, yayin da Maman Rhodan ke facing ɗinsu, girkin ranar da suka yi ne zube a gabansu, yayin da suna shirin cin abincin dare.
“Mom ni kifin nake so kawai”
Cewar Rhoda tana shagwaɓe fuska, Maman Rhoda ta wurga mata harara.
“An ƙi a baki kifin, da ci kike ?, Kifi na Zaid ne kawai”
Zaid ya kunshe dauriyarsa ya na shafa kanta, kasancewar ta jingina da shi, Maman Rhoda ta zubewa Zaid gaba ɗaya kifin, sannan ta bawa Rhoda tata shinkafar babu kifi sai miyar kawai. Rhoda ta turo baki tana ture abincin, sannan ta miƙe ta bar falon da hawaye.
Nan da nan Zaid ya shiga damuwa, don Allah ya sani ba ya son ɓacin ran 'yar ƙanwar tasa, don haka ya miƙe, hannunsa riƙe da kwanon abincin nasa.
“Zaid ina za ka?”
Ba tare da ya juyo ba ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan yace.
“Abincin zan je mu ci”
“Da ka rabu da ita kawai”
“Ba zan iya cin abincin ba tare da ita ba!”
Ya amsa mata a lokacin da ya ke ƙarsa fita daga cikin falon, Maman Rhoda ta girgiza kanta tana murmushi, soyyayar Zaid da Rhoda sai kallo, ko ka shiga tsakaninsu kai ne za ka ji kunya.
“I'm sorry Cuzie”
Zaid ya faɗi a karo na biyu ya na kallon Rhoda, wadda ta cunkune tana wani kawar da kai, wai ita a dole an ɓata mata rai, tana zaune a bakin gadonta, yayin da Zaid ɗin ke zaune kusa da ita.
Ya na murmushi ya aje kwanon abincin a kan cinyarsa yana buɗe kifin, ya guntsuro tsoka ya haɗa da lomar shinkafar, sannan ya kai mata saitin bakinta, kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta buɗe bakin ya saka mata.
“Story time!...”
Sai ta juyo tana kallonsa da kyau, ta harɗe ƙafafunta a kan gadon, tana buɗe duka kunnuwanta dan ta ji labarin da zai bata. Ta san labaran Zaid, babu na yarwa.
“Wani Gayene ya zo Wajen Budurwarsa. Saiya Kira Yaro Yace mai; Kai je Gidannan Kace Sani Striker Na Kiran Hassana. Yaro Ya Antaya,yace wai Ana kiran Hassana. Babanta Yace waye Ke Kiranta? Yaro Yace Sani Striker. Sai Babanta Yace; Je Kace Isah Defender Yace Bata Zuwa” (Labaran musha dariya).
Yana ba ta labarin yana kai mata lomar abincin haɗi da kifin, yana kaiwa ƙarshen labarin Rhoda ta tintsire da dariya. Abincin ya ci gaba da bata ya na bata wasu labaran, sai da ta ga ta kusa cinyewa, sannan ta karbi kwanon, ita ma ta shiga ba shi a baki.
Kamar daga sama suka ji an banko ƙofar falonsu, hakan yasa ba shiri suka miƙe suka bazama zuwa cikin falon. Abun da suka gani ya bala'in gigita duniyar ko wannensu.
Maman Rhoda ce yashe a ƙasa, Bala ya danne mata kai, ga sauran yaransa su Garuje tsaye a bayansa.
Bala wani me kuɗi ne a unguwar kusa da ta su Maman Rhoda, ya na bawa mutane bashin kuɗi, musamman ma mata, sannan ya kan ƙawarawa mutane da kuɗin ruwa me yawa, idan kika ka sa biyan bashin kuma sai ya nemi ya fanshe a kanki, ga shi da tara yara 'yan daba, kasancewarsa ɗan uwan sanata ya sa ake ɗaga masa ƙafa ya na cin karansa babu babbaka.
Lokacin da Maman Rhoda za ta biyawa Zaid kuɗin makaranta gaba ɗaya har zuwa lokacin da zai gama, kuɗaɗen hannunta ba su da yawa, hakan ya sa ta karɓi bashi a hannun Bala, suka yi da shi kan za ta riƙa biyansa da kaɗan-kaɗan.
Kwana nan kuma sai ya bijiro mata da maganar ta ba shi kanta kawai, ita kuma sai ta nuna ƙin amincewarta, harda marinsa a yammacin jiya.
Shi ne kuma yau ya iyo musu dirar mikiya a wannan daren. A cikin wannan daren Bala ya yiwa Maman Rhoda fyaɗe a kan idon Zaid da Rhoda, waɗanda ke riƙe a hannun yaransa su Garuje, sai da Zaid ɗin ma ya yi ƙoƙarin kaiwa Balan farmaki amma Garuje ya riƙe shi tare da buga kansa a jikin bango, hakan ya haddasa masa jiri da fashewar goshi.
*
Sosai Maman Rhoda take kuka, Zaid da Rhoda rungume a jikinta, yayin da suke tsaye a harabar police station, bayan da ta kawo ƙara kan zalincin da aka mata, faɗar sunan wanda take ƙara ya sa 'yan sandan korarta har da haɗa mata da duka.
Babban tashin ha kalinta shi ne yanda Rhoda da Zaid ke cikin damuwa, ba za ta iya ɗaukan baƙin ciki irin wannan ba, hakan yasa ta fita wajen police station ɗin, ta siyo fetir da ashana, ta ture Zaid da Rhoda gefe, sannan a kan idon Zaid da Rhoda da kuma sauran jama'ar station ɗin.
Maman Rhoda ta ɗaga jarkar fetir ɗin nan ta tittila a jikinta, sannan ta kunnawa kanta wuta, Rhoda na kuka tana fisge hannunta daga ruƙon da Zaid ya mata, yayin da wannan wutar ke ci a kan idon Zaid, komai na cikin kansa ya taɓu, tsoron wuta ya kama shi, ya zamana ba shi da wata abokiyar gaba kamar wuta.
Don a lokacin suma ya yi, 'yan san dake da imani a wurin ne suka temaka musu, ita kam Maman Rhoda babu abun da ya yi saura a gawarta, ta ƙone ƙurmus, Zaid kuma ya suma, Rhoda kuma sai kuka take, ta rasa inda za ta sa ranta, ita a tunaninta shi mq Zaid ɗin mutuwa ya yi.
Kwanan Zaid ɗaya a aibiti kafin ya farfaɗo, kuma yabna farfaɗowar babu wanda ya samu kusa da shi sai Rhoda, haka ya ƙanƙameta suka rera kuka me isarsu, kafin ya ɗauketa suka dawo gidansu.
Haka suka ci gaba da rayuwa, sai dai ba kamar yanda suka saba a da ba, kamar yanda Maman Rhoda ta bar musu kuɗinta da kayan ƙosai da kokonta, haka suka ci gaba da yin sana'ar, kuma a ɓangare guda suna zuwa makaranta, Zaid ne ya ci gaba da riƙe su har zuwa lokacin da shi ya kammala makaranta. Duk da Rhoda ce ke soya ƙosan, dan shi ya koma maƙiyin ganin wuta. Amma kuma ba ya bafinta ita kaɗai, duk inda za ka ganta to shi ma za ka ganshi.
Da haka ya yi applying wata University a nan cikin garin kano, don ba zai iya yin nisa da Rhoda ba. Da haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu, yau da daɗi gobe babu.
A lokacin da Zaid ya kammala karatunsa, sai ya shiga neman aikin DSS, aikin da ya sha burin yi tsawon rayuwarsa, aikin da yake kwana yake tashi da shi a zuciyarsa, aikin da suke da burin yinsa tun suna yara shi da ɗan uwansa.
Cikin ikon Allah ya samu, hakan tasa ya ɗauki Rhoda suka koma Abuja, kuma ita ma bayan ta gama makaranta sai ta ce tana san ta shiga aikin DSS ɗin, Zaid be hanata ba, sai ma shige mata gaba da ya yi har ta samu.
Shekerar Rhoda biyu da fara aiki, aka basu wani assignment me haɗari, wani assignment me ɗauke da sumatsi, wani assignment wanda ya shafi rayuwar ko wannensu, wani assignment wanda ya taho da guguwar ƙaddararsu, wani assignment wanda zai zama sanadiyyar faruwar wata ƙaddara, wadda za ta iya tarwatsa komai, sannan ta shirya wasu lamuran.
Assignment ne a kan wani me kuɗi wanda ake zarginsa da yin safarar makamai da kuma miyagun ƙwayoyi, Alhj Bala, wanda a lokacin yake zaune a garin Abuja. Daga Zaid har Rhoda babu wanda ya yi musu wurin karɓar aikin, don za su jefi tsuntsaye biyu ne da dutsi ɗaya.
Dole ta sa suka dawo garin Kano, don suna buƙatar bi ta hannun Garuje, babban yaron Alhj Balan, ƙarfi da ya ji suka koma 'yan daba, shi Zaid har da sauya suna zuwa RAJA. Sannan sun yi yarjejeniya da Rhoda kan idan sun kawo ƙarahen aikin za ta musulunta, babu yanda be yi da ita ba kan ta musulunta tun tana ƙarama, amma taƙi, sai yanzu ta yarda da hakan, shi ya sa Zaid ya zage damtse, don ya samu ya kawo karshen aikin ta ko wani hali, saboda ya na so ƙanwarsa ta samu rabauta, tun da Allah be sa Maman Rhoda ta samu rabon ba.
Kuma sun nemo wasu 'yan dabar kan titi guda uku, dan aikin nasu ya tafi dai-dai, Alandi, Zuzu da Jagwado, Zaid ya temaki rayuwarsu sosai, kafin ya ɗauke su aiki. Kuma a lokacin ne suka haɗu da Uchechi.
____________________
_Salmanians!... Ku ce kallon kitse mukewa rogo, ashe Raja ba ɗan ba ba ne, kai amma wanga bawan Allah an yi ɗan reni_
_Kada fa ku manta da sirrin zuciyar Zaid da ya bayyana ya fito fili, shin kuna ga Rabi za ta amince da shi?_
_Ku dai ku ci gaba da bi na sannu a hankali, dan ganin wata waina za mu toya a feji na gaba_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*14*
~~~
_-*The key element to happiness is; Knowing that you deserve to be loved correctly for the wild and beautiful soul that you are*-_
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
RABI'A POV.
Har ta kai gida ba ta cikin hayyacinta, ba ta sani ba ma ko ta haukace ne, haka ta riƙa yin abubuwa sukuku, har Anti Saratu ta lura da ita. Tana zaune a ɗaki ta takure wuri ɗaya, Anti Saratun ta shigo ta zauna kusa da ita ta na taɓata. Yanda ta zabura ya ankarar da Anti Saratun cewa tunani me zurfi ta faɗa.
“Rabi?! Wai me yake damunki?”
Rabi ta sauƙe ajiyar zuciya tana sunkuyar da kanta ƙasa, to wai ita me za ta ce ne?, ta faɗa mata cewar wannan Zaid ɗin da ta take yawa bata labarin suna mutunci ne ya yi faɗa da arniyar budurwarsa kanta, kuma ya furta cewa ita ce matar da zai aura nan gaba?, yin soyyayar sa da arniya ba laifi ba ne, dom ba haramun ba ne, amma yanda ya mari budurwar tasa, da yanda ya furta 'His wife to be' ɗin nan shi ne abun da ya tsaye mata a rai.
“Ba za ki faɗa min ba ?”
Rabi ta ƙara yin ƙasa da kanta, don ba ta san me za ta faɗa matan ba.
“Rabi! Kin san cewa ba ma ɓoyewa juna komai, duk damuwata ke nake faɗawa, me ya sa ke ba za ki faɗa min taki damuwar ba? Idan har ba zan iya temeka miki ki fita daga cikin dakuwar ba, ni me iya tayaki baƙin ciki ce”
Jin hakan ya sa zuciyarta tsinkewa, ba shiri hawaye ya sauƙo mata, hawayen da ta yi ta riƙe shi tun ɗazu don kar ya zubo, sai kawai ta kwantar da kanta a kafaɗar Anti Saratu.
“Anti Saratu wai ina zan sa kai na ne?.Ya ake so na yi?.Yau Zaid ya yi faɗa da budurwarsa a kaina, kuma ya faɗa mata cewar ni zai aura ba ita ba. Da ma ina da wannan muhummancin?”
Bisa ga mamakinta sai ta ji Anti Saratu na murmushi.
“Kowani ɗan adam ya na da daraja da muhummanci Rabi, kuma kowa ya na da tasa darajar. Ina me miki albirishiri da kasancewarki ɗaya daga cikin masu wanna darajar, saboda kina da daraja fiye da lissafinki Rabi!”
Rabi tasaki kuka me sauti.
“Yanzu ya zan yi da Yaya?, idan na rabu da shi ban masa adalci ba”
Wannan maganar tata ta tabbatarwa da Anti Saratu zarginta a kan Rabin tun lokacin da Zaid ɗin da take ba ta labarinsa ya fara ɗorata a taxi, daga Rabin har shi Zaid ɗin suna san junansu ne ba tare da sun sani ba.
“Rabi ki na son Zaid?!”
Tambayar ta saka Rabi fashewa da matsanancin kuka, ita ba ta san ya za ta yi da rayuwarta ba, ba ta ma san inda za ta sa kanta ba, ina za ta kai kanta da hakkin Yaya?, A gaskiya ta cuci kanta da har ta bari soyyayar Raja ta shiga ranta, haɗuwarta da shi kuskure ce, fara kula shi da ta yi ma kuskure ne, maganar da suka yi kuakure ce, komai ma tsakaninta da shi kuskure ne, a she da da take cewa tana son Yaya faɗi kawai take a baki, yanzu ta fara soyyaya, sai a yanzu ne ta faɗa ramin soyyaya, sai a yanzu ne ta saka ƙafarta a soyyayar, sai a yanzu ne ta fara jin shauƙin soyyaya, amma me ya sa ?, Me ya sa ƙaddarorinta suke zuwa a haka?, Me ya sa duk wani abu me kyau da ta samu sai ya guje mata, don kuwa ba za ta iya auren Raja ba, ko ta na son Yaya ko babta sonsa dole ne ta zauna da shi, don babu yanda za ayi ta kalli tsabar idonsa ta faɗa masa ba ta sonsa.
“Ina sansa Anti Saratu. I LOVE ZAID!, i... i... Love him, i feel like The word 'love' is not enough for me to explain the way i love him!”
Ta fito ta faɗi duk abun da ta san ta na ji a ciki zuciyarta, ba so kawai takewa Raja ba, har da ƙauna ma tana masa, don soyyayar tasu ta jini ce, su jinin mutum ɗaya ne, shi da mijin Mishal 'ya'yan yayar Umma wadda take yawan basu labarinta ne, su ne 'ya'yan me sunanta, su ne 'ya'yan da kakansu ya basu labari kan an sha nemansu amma ba'a same su ba.
Cike da tausayawa Anti Saratu ta ɗagota daga jikinta.
“Haƙiƙa Rabi kin gamu da jarabawa, amma babu yan da za mu yi, addu'a ita ce mafita, don haka sai ki dage da addu'a!”
*No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja*
“To yanzu Anti miye abun yi?”
Cewar Siyama cikin kuka, tun da ta dawo gidan Anti Kariman ma ba ta samu sukuni ba, don ji ta yi hankalinta ma ya fi tashi a nan ɗin. Anti Karima ta kalleta na wasu 'yan sakkani, gaba ɗaya ta sauya, kamar ba Siyamanta ba, ta rame ta ƙara baƙi, kamar kazar mayu.
“Ba de kin ce yarinya ba ce?”
Siyama ta gyaɗamata kai tana share hawaye. Anti Karima ta gyaɗa kai.
“To ai cikin sauƙi za mu yi maganinta, ba tare da kin ɗaga hankalinki ko kin tayar da nawa ba... Zo ki ji”
Siyama ta miƙa mata kunnenta, ido waje take kallon Anti Karima, bayan da ta faɗa mata abinda za su yi.
“Kuka ki na ganin babu matsala?”
Ta faɗa cikin karyewar murya.
“Mtswwww!, Wata matsalar kuma za'a samu, hakan kawai za mu yi”
Siyama ta gyaɗa kanta cike da gamsuwa, duk da ta na jin ɗar-ɗar a cikin ranta, amma sai ta dake ta miƙe ta shige ɗakinta.
Anti Karima ta bi bayanta da kallo cike da tausayawa, idan de har Kuliya ya shigo hannunsa ba za ta masa da sauƙi ba, dan sai ta rama abun da ya yiwa ƙanwarta. Ta yi ƙwafa a bayyane tana jan wani littafi dake aje kan coffee table.
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
Zaune take a falo ta na rubutu a cikin littattafanta, ta baje takardu da littatafi a ko ina, don wani assignment ɗin math aka basu me wahalar tsiya, duk da ita ba sosai take yin assignment ɗin math ba, wannan ɗin ma don malamin yace shi ne makin C.A ɗinsu. Shi ya sa ta dage take yi.
Ƙofar falon aka turo, Kuliya ya shigo ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar corridor, ita ma ba ta takura da sai ta masa magana ba, don ta lura da ba ƙaramin miskili ba ne, ta taɓe baki ta ci gaba da aikinta.
Bayan shuɗewar kusan muntina ashirin sai ga shi ya fito, sanye cikin wata baƙar T-shirt da baƙin sweat trouser. Fuskarsa kawai ta kalla ta ganta a haɗe, babu alamun rahama ko fara'a, da alama dai yau ransa a ɓace yake sosai.
A falon ya zauna ba tare da ya mata magana ba, sai wani cin magani yake, ɗagowa da kanta ta yi ta kalleshi, sannan ta ci gaba da rubutunta tana faɗin.
“Sannu da zuwa”
Ƙin kulata ya yi, don ransa a matuƙar ɓace yake, for the very first time a rayuwarsa ya yi falling assignment, wani abu da kaf tsawon fara aikinsa a wurin bai taɓa faruwa da shi ba, a ko da yauashe shi me nasara ne, kuma ba faɗuwar tasa ce kaɗai ta ɓata masa rai ba, sakin me laifin da aka yi ne ya fi ɓata masa rai. Kuma babban abun haushin shi ne, me laifin fyaɗe ya aikata, duk da tarin hujjojjin da suka gabatar a gaban kotu, haka aka kori ƙarar ba tare da la'akari da rayuwar ƙaramar yarinyar da aka lallata ba.
Mishal ba ta ƙara bi ta kansa ba sai da ta kakare a wani wuri, kuma ba ta da wanda za ta iya tambaya bayan shi, shi ɗin da a yanzu ba ta da kowa kamarsa, shi ɗin da take zaune da shi gida ɗaya a matsayin miji. Hakan yasa ta ɗauki littafin ta matsa kusa da shi tana faɗin.
“Abu Aswad ɗan temaka min...”
Wani kallo ya mata daga ita har littafin nata, kafin ya juyar da kansa gefe, yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. Mishal ba ta daddara ba ta ƙara miƙa masa littafin.
“Dan Allah ka ɗan temaka min iyaka nan ne na kasa...”
“Ke wai ba ki da hankali ne?! Ba ki ga a yanayin da na dawo gida ba?!, Ke ba za ki iya yi da kan ki ba?! Dole sai na miki?!”
Cike da hargagi yake mata magannar, yayin da ya miƙe tsaye, har wani ɗaga hannu yake kamar me shirin kai mata duka, cike da dauriya Mishal ta miƙe tsaye, don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ido cikin ido ta kalleshi, hannunta riƙe da littafin da kuma pen.
“Kai ba ka isa ka ce ba ni da hankali ba, don kawai ina yarinya ba shi zai sa a min kallon mahaukaciya ba, ina da hankali, na kuma san inda ke min ciwo. Don ka dawo gida ranka a ɓace sai ka huce a kaina?, Na ji ina da laifi don na maka magana yayin da kake cikin fishi, amma na roƙeka da kada ka sake min tsawa, saboda ba'a min tsawa!”
Tana kawai nan ta tattara kayanta ta yi ɗakinta cikin ƙunar rai. Kuliya ya dafe kansa ya na rintse ido, me ya shiga kansa haka har ya mata tsawa?, ya rab!, ya kamata a ce ya na iya sarrafa fishinsa.
*
Mishal na zaune a kan wata doguwar kujerar balcony ɗin ɗakinta, littafin math ɗinta ne a je a gefenta, don ta kasa wucewa wurin, ga kuma ranta da ya ɓaci, babban ɗan yatsanta na dama sanye cikin bakinta tana sha, tana kalon hasken farin wata, wai ko zuciyarta za ta washe da wannan baƙin cikin da Abu Aswad ya ɗura mata.
Ƙofar ɗakin ta ji an turo, hakan ya sa ta juya ta kalli cikin ɗakin, Kuliya ta ga ya shigo, ya na wani abu kamar mara gaskiya, hakan ya sa ta yi ƙwafa tana juyawa, ta ci gaba da shan hannunta.
Ƙaraaowa ya yi ya, ya tsaya a bayanta, sannan ya mata gyaran murya, Mishal ta yi kamar ba ta ji shi ba, hakan ya sa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, littafin math ɗinta dake tsakaninsu ya kalla, sannan ya kalli fuskarta ta cikin hasken farin wata da kuma na wutar nepa.
“Wai har yanzu ba ki dena shan hannu ba?”
Yanzun ma banza ta masa, a karo na farko Kuliya ya ji haushin kansa, ya ji haushin zuciya da ta ingiza shi har ya aikatawa amanarsa haka, a karon farko ya ji cewar ya yi nadama, ya yi nadamar yi wa wani masifa. Hakan yasa ya ɗaga hannayensa, tare da kama kunnensa.
“I am sorry Mishal!”
Wasu kalama da rabonsa da ya furtasu ga kowa tun bayan ranar da ya taso daga asibiti, bayan nan kuma ba zai iya tuna rabonsa da furtasu ba.
Cike da mamaki Mishal ta cire hannunta a baki ta juyo ta kalleshi, ba ta san shi sosai ba, amma tana da tabbacin ba saba faɗar kalaman ya yi ba, yadda suka fito daga kan harshensa ne ya sa ta tabbatar da hakan, sai kuma inkiyarta da ya kira, da idan zai ma ta magana sai dai ya ce Hafsat, amma yau Mishal yace, ga kuma kunnuwansa da ya riƙe. Sai ya zamemata kamar wani maraya
“Raina ne a ɓace, ni kuma ba na san a min magana idan raina ya ɓaci”
Kuliya ya faɗi yana ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, Mishal ta juyar da kanta gefe, ta na ci gaba da kallon farin wata, kafin muryarta ta fito.
“Hargagi da ɗaga murya ba ya saka mutum ya huce haushi, sannan ba ya maganin ɓacin rai”
Kuliya ya ci gaba da kallonta ya na mamakin hankalin da ya ga ta yi a yau, kamar ba wannan mashiririciyar ba.
“Me zan yi dan raina ya huce?”
Mishal ta juyo ta kalleshi, jin yanda amon muryarsa ya fito a sanyaye. Ba tare da tace masa komai ba, ta miƙe ta zagaya ta bayansa, shi ya ɗauka ma cikin ɗakin za ta koma, be za ta ba ya ji sauƙar hannayenta a kan kafaɗunsa duka biyu, dai-dai doron wuyansa, hakan ya sa ya lumshe idonsa a hankali, don sauƙar hannun nata a kan jikinsa ya sauƙar masa da wani yanayi mara fasaltuwa.
A hankali Mishal ta shiga matsa gurin tana masa tausa, idonsa a lumshe ya ɗaga kannsa sama, hakan ya sa kansa ya karu da jikinta, ita ma idon nata ta lumshe, dan ta ji sak wannan yanayin da ta taɓa ji a sanda ya rungumeta. Ci gaba ta yi da masa tausar, kafin muryarta ta fito a hankali, kuma har lokacin idonta a lumshe yake, kamar yanda nasa suke a lumshe.
“A duk sanda za ka yi fushi. To wannan kake buƙata!”
Kafaɗar tasa ya motsa, hakan yasa ta buɗe idonta.
“Shin za ki kasance tare da ni a duk sanda zan yi gushi?”
Wani abu me kama da farin ciki ya motsa a ƙirjin Mishal. Hakan ya sa ta kuma lumshe idonta tana danna masa kafaɗar.
“Insha-Allah”
Allah ne kaɗai ya san yanda abun da take masa yake sanyaya zuciyarsa, ya ji duk wata damuwa da ɓacin ransa sun bi iska.
A hankali ya buɗe idonsa, sannan ya janye kansa daga jikinta, hakan yasa ita ma ta buɗe idonta, sai ta ga ya na janyowa littafinta.
A kan idonta ya buɗe littafin, sannan ya tsaya nazartar problem ɗin, kafin ya shiga mata solving. Cikin abun da bai fi minti uku ba, ya gama mata, kuma har lokacin tana masa tausar.
“Nagode”
Ta faɗi a saitin kunnensa, ya ɗaga hannunsa na dama ya ɗora a kan nata dake kan kafaɗarsa. Hakan ya sa Mishal jin wani abu me kama da shock ɗin wutar nepa ya ratsa fatar hannunta.
“You are welcome!”
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
*10:00 PM*
RAJA POV.
“Zaid”
Rhoda ta kira sunansa, hakan ya sa ya ɗaga haɓarsa daga hannunsa da ya yi tagumi, ya juyo ya kalleta, zaune yake a kan kujerar dake ɗakinsa, gaba ɗaya tunani ya hana shi sukuni, ya kasa gane abun da ya kamata ya yi. Kallon Rhodan ya yi na 'yan wasu sakkani, sanye take da pyjamas iri na jikinsa, hannunta a dama riƙe da trayn abinci. Sai kuma ya juya ya ci gaba da kalon ƙofar bathroom, kamar me jiran fitowar wani daga ciki.
Rhoda ta girgiza kanta ta tako har gabansa, zama ta yi a kusa da shi, sannan ta aje taryn hannunta a kan coffee table, ta dafa kafarsa ta dama tana kallon gefen fuskarsa.
“Me cece damuwar?”
Hannunsa ya sa ya shafa gaba ɗayan fuskarsa, sannan ya sosa kansa.
“Wani tunani kike ga Ammata za ta yi a kaina?”
Rhoda ta yi murmushi.
“Dude! Babu macen da ta isa ta ce bata sanka, baka da wani aibu, look at your self Bro, you are dazzling, smart, athletic, stylish, chaming and elegant!”
“Ummm!, Yaushe ƙanwata ta girma haka?”
Ya tamabaya yana wani murmushi ɗan guntun murmushi, Rhoda ta yi murmushi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa. Sun ɗan ɗau lokaci a haka, kafin ta ɗago da kanta ta na ɗaukar trayn dake ɗauke da abinci.
“Yanzu dai ka ci abinci”
Ita da kanta ta shiga bashi a baki yana ci, don zuwan nata ya sauƙa-ƙa masa ruhi, saɓanin da da komai ya jagule masa. Maganarta ta ba shi ƙwarin gwiwa sosai, kuma ya ji cewar tabbas, babu abin da zai hana rabi'a ta so shi.
*Brickhall school,

Please Login or Register in order to submit comment