Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na son ki bani kunya, na san matata jarumace, dan haka ki nuna ƙwarewarki... Daga mijinki abun somki... Zaid (Raja)_.
Dariya ta ɗan yi tana aje takardar. Abun be bata mamaki ba, dan ta ga ƙoƙarinsa a jiyan da tace masa ya bari sai gobe kuma ya bari ɗin, ashe shi bai haƙura ba.
Sauƙa ta yi daga kan gadon tana hamma. Kamar jiya, yau ma bata jin daɗin jikinta. Ita ta rasa abun da yake damunta a kwanakin nan, sai ta yi ta amai, ga kasala, ga kuma rashin san cin abinci da ba ta yi.
Sallah ita ce abu na farko da ta fara yi, kafin ta shiga gyaran gidan, bayan ta gama gyara gidan, ta ɗora girki, tana gama girkin ta faɗa wanka. Bayan ta fito daga wanka ta saka wani baƙin leggings, da wata baƙar long sleeve high neck shirt, ta ɗora kimonohnta a kan kayan, sannan ta kawo wani baƙin baby hijjab ta saka. Ba ta yi kwalliya ba, dan da ma ita ba gwanar kwalliyar ba ce. Mai kawai ta shafa a jikinta, sannan ta ɗauki backpack ɗint ta saka kayan sport ɗinta a ciki.
Ta fito ta zauna a danning ta fara cin abinci, sai da ta kusan gamawa sannan Rhoda ta ƙaraso, ba ta yarda sun tafi ba, sai da ta zubawa Rhodan abinci ita ma, Rhodan na ci Rabin na bata labarin ɗan uwan Aliyun da suka gano. Ita kuma Rhodan na ba ta bayani a kan shari'ar da za su shiga gobe.
Da haka har suka gama, sannan Rhoda ta ɗaukesu zuwa can acadamy ɗin. Bayan da Rhodan ta kaita sai ta tafi, tare da faɗa mata cewar; idan sun gama, ta mata waya, ita kuma za ta zo ta ɗauketa.
Rabi ce zaune a kan kujerar jira, sanye take da wannan jerseyn da kum wandonta, wanda ta saka leggings da kuma long sleeve high neck shirt a ƙasansu, ƙafarta sanye da football shoes. Kanta kuma rufe da baby hijjab, yanayin shigar tata akwai gwanin ban sha'awa, dan kaf matan dake wurin babu me irin shigarta, ba za ta ce babu musulmai a cikinsu ba, amma babu bahaushiya ko bafulatana ɗaya a cikinsu, duka 'ya'yan iyamurai ne. Shi ya sa ita ta fita da ban a cikinsu.
“Rabi'a Muhammad!”
Me tantancewar ya kira sunanta da ƙarfi, hakan ya sa ta amsa tana miƙewa. Inda ya nuna mata ta ƙarasa ta tsaya. Har zuwa yanzu ba ta da wani isasshen kuzari a jikinta, ga cikinta da take jin yana yamutsawa, kamar za ta yi amai. Amma kuma ba za ta bari hakan ya zama ƙalubale gareta wurin cimma burinta ba, ita ta sa kanta cewar za ta iya, kuma da yarda Allah za ta iya ɗin. Za ta yi abun da za ta bawa kowa mamaki, ciki kuwa harda 'yan uwanta na haɗejia.
Ball aka sa musu a tsakiya ita da wata yarinya da ta karanta sunanta a bayan rigarta, wai ita ‘Chioma’. A yanayin girman jiki ta fi Rabi ƙiba, amma kuma Rabi ta ɗan fita tsayi, gata a ƙasa duf, ta ci doya da tuwon mama Iyabo ta ƙoshi.
A sa'ilin da aka hura usur, a lokacin suka fara gudanar da wasan. Tashin farko sai da Chioma ta ci Rabi'a har sau biyu. Kasancewar ita Rabin babu kuzari a jikinta. Bayan sun ci gaba da wasan, Rabi ta kaiwa Chioma wani yanka, wanda ya sa Chioman ta yi amfani da ƙarfinta ta hankaɗa Rabi gefe. Faɗuwa ta yi, hakan ya sa gwiwar hannunta kurjewa da grass carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin.
Tashi ta yi zaune tana kallon Chioma ɗin. Me ya sa ta yarda kan cewa Chiomar za ta iya kada ta?, ita ma fa macace kamarta, babu wani abu da ta fita da shi, dan kawai ba ta jin daɗin jikinta sai ta saki jiki Chioma ta na nasara a kanta?, ya isa haka! Menene ba ta gani ba a duniya, ta shiga halin da ya ɗara wannan ma, ta ga ƙalubale a rayuwa wanda ba ta taɓa sanin zasu afko mata ba ko da a mafarki kuwa. Dan Chioma tana 'yar kudu ba shi ke nuna cewar ta fita ƙarfi ba, su ma matan arewa suna da tasu jajircewar, ya kamata ace ta nuna musu hakan.
Cike da ƙarfin hali da na gwiwa ta miƙe tsaya, sannan ta koma aka ci gaba da wasa, wannan karon a zafafe take wasan, hakan yasa ta riƙa cin Chioma har sai da lokacinsu ya ƙare. Couches ɗin dake wajen ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin har yanzu Rabi'an ba ta manta da wasu abubuwa da ta koya daga garesu ba.
“Ina taya ki murna mrs. Zaid!”
Cewar ɗaya daga cikin Coach ɗin nasu yana miƙa mata hannu alamun su gaisa, hannun nasa ta kalla, yayin da take dafe da guwar hannunta na dama wanda ke mata ciwo. Kanta ta girgiza masa tana faɗin.
“Sorry sir, but ni matar aureci”
Hakan ya sa Coach ɗin janye hannunsa a sanyaye.
Daga nan kuma sai aka turasu sashen fara ɗaukar darasi, tun a ranar aka fara musu training kuma ba su suka gama ba sai ƙarfe biyar na yamma.
*
Rhoda ce ke tuƙa motarta a kan titi, tana tafe tana biya waƙar Dalling Jesus dake tashi a motar.
“I love you so much darling Jesus... My darling Jesus... Darling Jesus...”
Wayarta ce ta yi ringing, hakan ya sa ta faka motar a gefen hanya, tana kashe waƙar. Ganin Zaid ne ke koranta ya sa ta kai hannu ta ɗau wayar tana ɗaga kiran.
“Kina ina ?”
Abun da muryarsa ta fara tambaya kenan bayan da ta ɗaga wayar, amon muryar tasa ya bata tsoro, dan sautin nasa na ɗauke da wani abu me kama da damuwa ko tsoro. Kamar me san tantance wani abu, ta shiga wulƙita idonta a kewayen wurin da take.
“Ƙarfe shida yanzu, na kai Ammatanka gida ne... Kai wai ina ma ka shiga ne?”
Ta ƙarashe tana jefa masa tambayar. Sai ta ji ya yi shiru, kafin yace.
“Ki koma gidan ki ɗaukota, sannan ki kawota Hymill hospital!”
Damm, gaban Rhoda ya buga.
“Zaid! Zaid!. Me yake faruwa?. Ka ga ɗan uwan naka?”
Ta tambaya a kiɗime.
“Ki je ki zo da Adawiyya... Ɗaki me lamba ashirin da shida”
Daga haka ya katse kiran ba tare da ya jira abun da za ta faɗi ba. A hankali Rhoda ta sauƙe wayar daga kunnenta, duk yadda aka yi ba lafiya ba. Dan haka ta tayar da motar da sauri ta juya kan motar zuwa gidan Zaid.
RABI'A POV.
Rhoda na aje ta a gidan ta shiga wanka. Kuma kafin ta bar banɗakin ma sai da ta yi amai, ta rasa abun da yake mata daɗi, ko mai ta ci ba ya zama a cikinta sai ya dawo. Haka ta ɗaura towel ta fito jiki ba ƙwari. Duk da yau tana cikin farin ciki sosai, domin a yanzu ta na ganin labarinta ya gama cika, tun da har Allah ya mallaka mata Zaid a matsayin miji, ya sa mahaifinta shiryuwa, ya ganar da Habiba da 'yarta Mama tafarki madai-daici, sannan ya nuna mata auren Anti Saratu, ya kuma cika mata burinta na ci gaba da buga ƙwallo. Ita kuwa me za ta ce? Da ya rage ta dage kan ibadunta, don ta nunawa Allah jin daɗinta kan ni'imomin da ya mata.
Ta ƙarashe tunanin tana saka wata doguwar rigar atamfa. Wayarta ta dawo ta ɗauka, ta aikawa Zaid kira, dan ta na so ta ji daga gareshi, tana san ta ji wani hali yake ciki, shin ya haɗu da Aliyun?, ko ba su haɗu ba?. Sau huɗu tana shiga amma ba ya ɗagawa, hakan ya sata shiga mamaki, a gefe guda kuma sai tsoro ya fara shigarta.
Ta kama hanya da niyyar barin ɗakin aka turo ƙofar ɗakin da ƙarfu, Rhodan da ta tafi a ɗazu ce ta dawo, cikin wani irin birkitaccen yanayi da Rabin ta kasa gane masa.
*Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja*
*07:00pm*
MISHAL POV.
Zaune take kan wata kujera dake bakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Aliyu bayan zuwansu asibiti a daren jiya. Abun da likitocin suka rara sanar musu shi ne, ya rasa jini da yawa, haka aka gwada na Zaid, sannan aka ɗiba ganin ya dace da nasa. Kuma tun safe ake ƙara masa jinin. Bai ƙare ba sai da azahar, amma har zuwa yanzu bai farfaɗo ba.
Ita kanta ba ta san in da kanta yake ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kawai tana nan ne, amma hankalinta ba ya tare da ita. Tun a ɗazu da safe da suka gama zirga-zirga. Zaid yace mata ta zauna,shi zai tsaya a kan komai. Kuma tun lokacin take zaune a nan ɗin. Babu yanda Zaid ɗin be yi da ita ba kan ta ci abinci, amma fur haka taƙi. Ko sallah ma ba ta jin ta yi. Gani take kamar Aliyu tafiya zai yi ya barta, kamar shi ma zai bi Abbanta, Mamanta da yayanta. Wata ƙila ita ba ta da sa'ar zama da kowa a rayuwa, haka Allah ya tsara tata rayuwar, ba tare da yin zama me ɗorewa da makusantanta ba, wata ƙila haka za ta ƙarar da rayuwarta cikin kaɗaici.
A hankali Zaid da ya dawo daga masallaici ya zauna ɗan nesa da ita. Kallonta kawai yake yana san sanin me ya kamata ya yi?. Ga ɗan uwansa a cikin wani hali na mutuwa ko rayuwa, ga kuma matarsa da ke cikin tashin hankalin rasa mijinta, shi kansa idan za'a rarrasheshi so yake, dan ba ya so Aliyu ya sake tafiya ya barshi, ji yake kamar ya saka igiya ya ɗauresu da juna, gudun kada wani abun ya kuma zuwa ya gifta a tskaninsu.
Sai de kuma a matsayinsa na namiji, kuma babba, dole ne ya haɗiye nasa tashin hankalin, ya san hanyar da zai bi dan ganin ya kwantar da hankalin matar ƙaninsa.
Bakinsa ya buɗe zai yi magana, idonsa ya sauƙa a kan Rabi'a da Rhoda da suka shigo corridor ɗin ɗakunan.
A hankali Rabi ta yi a jiyar zuciya bayan ganin mijinta cikin ƙoshin lafiya, sai de hankalin nata be gama kwanciya ba sai da ta tafi da gudu ta yi wurin da yake, miƙewa tsaye ya yi yana kallonsu. Rabi ta manta da Rhoda dake bayanta, da kuma Mishal ɗin da hamkalinta bai ma kai kanta ba. Ta yi saurin rungume mijinta tana shafa bayansa. Shi ma riƙeta ya yi da kyau a jikinsa, yana jin kamar ya fashe mata da kuka. A hankali ta sake shi tana ci gaba da duba jikinsa.
“Me ya faru?...”
Ta tambaya tana yawatawa da idonta a kewayen wurin da suke, bata rufe bakinta ba idonta ya sauƙa a kan Mishal dake zaune a kan kujera, ta sunkuyar da kanta ƙasa, gashin kan nata a yamutse, ga jinin da ya fara bushewa a gefen fuskarta. A kiɗime ta zauna kusa da ita tana rungumota jikinta. Mishal na jin kanta ya sauƙa a kafaɗar Rabi ta saki kukan da yake cin ruhinta tun safe. Kukan da Mishal ɗin ke yi ne ya ƙara karya zuciyar Rabi. Mishal na rungume a jikinta ta juyo da kanta ta kalli Zaid dake tsaye yana ƙoƙarin hana hawayensa zuba.
“Raj! Me yake faruwa wai?”
Zaid ya ɗan kawar da fuska yana ɗaga kafaɗarsa.
“Aliyu ne ba shi da lafiya”
Sunansa kawai da ta kira ne ya ƙara karya zuciyar Mishal, ta ƙarawa kukanta ƙarfi tana ƙanƙame Rabi a jikinta. Da Zaid ya ga ba zai iya ɗauka ba, sai ya yi wa Rhoda alama da ta biyoshi, ya kama hanyar barin corridorn.
Duk yadda Rabi ta so Mishal ta kwantar da hankalinta ya gagara. Kukan ma da ƙyar ta sakata ta dena shi. Sai hawayen da take gogewa. Sai wajajen ƙarfe takwas Zaid da Rhoda suka dawo.
Zaid ɗin ya umarci Rhoda da ta ɗauki Rabi da Mishal ta kaisu gidansa, kuma ita ma kar ta tafi, ta zauna ta kwana tare da su. Kamar wata gawa haka Rabi ta miƙar da Mishal ta shiga janta zuwa waje, dan bata ma san inda take saka ƙafarta ba, duk inda aka jata bi take kawai.
Rhoda da Mishal suka shiga mota, yayin da Rabi da Zaid suka tsaya daga can nesa da su. Rabi ta goge ƙwallar idonta ta tausayin mijinta da kuma ƙanwarta, ta kai hannunta ta dafa kafaɗar Zaid ɗin ta dama.
“Ka ci abinci?”
Kansa ya juyo ya kalli fuskarta ta cikin hasken fitilun dake wadace a harabar asibitin. Nan take idon nasa ya cika da ƙwalla. Sai ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya na barin hawayen fita daga inda ya tsaresu tsawon ranar.
“Ban ci ba”
Ya amsa mata a raunane. Rabi ta ci gaba da kallonsa, tana jin ina ma tana da damar da za ta buɗe zuciyarsa, ta cire wannan damuwar da yake ciki. Ƙwalla ta kuma gogewa tana faɗin.
“Na ga ko wanka ma ba ka yi ba. Amma ya kamata ace ka ci abincin”
Sai ya ɗago da lumsassun idanuwansa ya ɗorasu a kanta yana ɗage kafaɗarsa ta dama.
“Adawiyya ta ya kike tunan zan iya cin abinci a irin wanna yanayin da nake ciki, ni yunwar ma kanta ba na ji. Kaina ne kawai ke min ciwo, ji nake kamar zai tarwatse!”
Sai ta ɗan yi tattage tana riƙe kan nasa.
“Ka ga ba?. Yunwar ce ta saka mata ciwon kan, ka daure ka taɓa wani abun, sai ka sha magani, Aliyu ba zai ji daɗi ba idan har ya ji cewar baka ci abinci ba!”
Kiran sunan Aliyin ya sa wata ƙwalla ta ƙara sauƙowa daga idonsa. Rabi ta saka hannyenta ta share masa duka ƙwallar.
“Na san kana da dauriya da kuma juriya, ka ƙara kan wadda kake da ita, Allah zai tashi kafaɗun Aliyu!...”
Da sauri ya saka hannyensa biyu ya kewaye waist ɗinta yana janta jikinsa tare da fashewa da kuka mara sauti. Ita ma Rabin kukan take. Tana shafa ƙeyarsa. Sun jima a haka kafin Zaid ɗin ya saketa ya na share ƙwalla.
“Ki san yanda za ki kwantarwa da...”
Sai kuma ya yi shiru, dan sunan nata ya kwanta masa. Rabi ta kai hannunta na hagu ta kama chain ɗin wuyansa, sannan ta yi amfani da hannunta na hagu ta kama wuyan rigarsa tana janyo shi gaba, kafin ta saka sarƙar a cikin rigar tasa tana faɗin.
“Mishal?”
“Eh Mishal... Ko sallah ba na jin ta yi, dan Allah ki kula”
Kanta ta gyaɗa tana sharar tata ƙwallar.
“Na je na an min gwaji, kuma na ci, dan har training mun fara!”
Bai iya ce mata komai ba, sai kansa da ya gyaɗa, daga haka suka yi sallama, shi ya koma zuwa cikin asibitin. Ita kuma ta nufi motar Rhoda.
Ko da suka isa gidan, wanka tasa Mishal ta yi, kafin ta bata wasu kayan cikin kayanta tace mata tasa. Sawar ta yi, sannan Rabi tace mata ta yi sallah tana zuwa. Sallar ta fara kafin Rabin ta dawo.
A falo ta iske Rjoda kwance a kan kujera tana waya da Zakar, yayin da take sanar masa halin da suke ciki a yau. Ba ta ce mata komai ba ta wuce kitchen. Ta shiga kiciniyar girka musu abinci. Kasancewar babu wani isasshen lokaci, ya sa ta yi gaggauwar girka musu jallof ɗin taliya.
Duka ta jiye musu it a tray, sannan ta fito da ita ta aje a falo, zuwa lokacin Rhodan ta gama wayar tana zaune tana danna wayar tata.
“Bari na kira Mishal...”
Ta faɗi tana nufar ɗakinta. Ko da ta shiga sai ta iske Mishal ɗin zaune kan darduma. Ba ta san me take ba,amma bisa ga dukkan alamu ba sallah take ba. Sai ta shiga cikin ɗakin tare da nufar inda take.
“Ƙanwata!”
Ta kira sunanta tana dafa kafaɗarta, firgiyar da da Mishal ɗin ta yi ya ankarar da Rabi cewar tunani take.
“Kin idar da sallahr?”
Mishal ta gyaɗa mata kai.
“Mishal! A yanzu Aliyu ba ya buƙatar kukanki ko damuwa, addu'a kawai za ki masa, da yardar Allah zai tashi!”
Wata siriryar ƙwalla ce ta biyo kuncin Mishal.
“Anti Adawiyya idan na tuna maraicina sai na ji kamar zan fasa ƙara. Ba ni da kowa fa, Aliyu shi kaɗai ne ya rage min, bayan shi ban da kowa. Idan ya mutu kuma ya zan yi?!”
Da sauri Rabi ta girgiza mata kai.
“Insha-Allah zai warke, zai tashi kin ji?”
Ta faɗi tana jan Mishal zuwa jikinta. Kafin ta saketa a hankali tana share nata ƙwalla.
“Mu je mu ci abinci...”
Mishal ta girgiza kanta. Rabi ta zare mata ido tana faɗin.
“A gidana ba'a min musu, dan haka salin-alin ki tashi mu je mu ci abinci”
Duk da halin da Mishal ke ciki be hanata yin murmushi ba. Tashin ta yi suka fita, a falon suka zauna a kan carpet suka fara cin abincin. Ko rabi ba su yi ba, Rabi ta ji amai na taso mata. Dan haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta da gudu.
“Lafiya?”
Mishal da Rhoda suka faɗi a tare suna miƙewa tare da bin bayanta da kallo.
“Zauna ki ci gaba da cin abincin, ni zan je na dubata”
Cewar Rhoda. Ba dan Mishal ta so ba, haka ta zauna tana ta kallon ƙofar ɗakin Rabin.
“Sannu! Sannu kin ji... Sannu!”
Rhoda ke ta jerawa Rabi sannu, wadda ke ta amayar da taliyar da ta samu shiga cikin. Bakinta ta wanke tana jingina da bango, bayan da ta gama aman.
“Baki da lafiya ne?”
Rabi ta girgiza kai tana dafe cikinta.
“To sannu”
Falon suka dawo, inda Rabi tace ita fa ta ƙoshi, dan haka su su ƙarasa cin abincisu. Babu yadda Rhoda ba ta yi da ita ba kan ta daure ta ƙara abincin, amma tace ita ta ƙoshi. Haka suka ƙyaleta su ma suka ci gaba, da ƙyar Mishal ta iya cin abincin da yawa. Kafin Rabi ta ɗauke trayn ta kai shi kitchen, ta fito tana faɗin.
“Sai mu kwanta ko?”
Rhoda ta miƙe tana faɗin.
“No, ku de ku je ku kwanta a ɗaki, ni a nan zan kwana!”
Rabi ta girgiza kanta.
“A'a... Ke ma zuwa za ki yi mu kwanta, gadon fa babba ne, zai ɗaukemu mu uku”
“Ok, mu je”
Da haka suka koma ɗakin, gadon kuwa tas ya ɗaukesu su ukun, har da sauran space. Rabi da Rhoda ne kawai suka yi bacci, ban da Mishal ɗin da ta kwana ido buɗe. Dan ba ta jin za ta iya baccin, hakan ya sa daren ya mata tsawo, fiye da sauran dararen da suka shuɗe a rayuwarta.
*Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja*
ZAID POV.
Zaune yake a kan kujera ɗaya dake cikin ɗakin da Aliyu ke kwance. Ya kafe Aliyun da ido, kamar idan ya kira sunansa zau amsa. Hannunsa ya kai ya shafa sumarsa tun daga gaba zuwa baya. Sannan ya dawo da hannun nasa kan bakinsa.
Aliyun dake kwance kan gadon marasa lafiya, ba ya iya numfashi sai da temakon na'urar numfashi. Ba ya jin zai iya ko da rintsawa. Dan gani yake kamar idan ya kumshe idonsa na minti ɗaya, Aliyu zai iya ɓacewa. Haka ya ci gaba da zama a wurin, har zuwa asuba.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*27*
*END*
~~~
*“How sad to miss someone, who you know doesn't miss you...*
***
*No.86, Garki 2, Abuja...*
RABI POV.
Tun da ta tashi sallahr asuba bata koma bacci ba. Amma da Mishal da ba ta samu bacci jiya da daddrae ba ta koma baccin. Sai Rhoda a bata farka ba. Gyaran gidan ta shiga yi. Bayan ta gama kuma ta ɗora girki, bayan nasu wanda za suci, har da na su Zaid ta girka, ta juye musu nasu a cikin was warmers masu kyau, ta saka a basket ta aje.
Nasu kuna ta kai kan danning ta jera. Ɗakinta ta koma, ta je ta taso Mishal da Rhoda, tace musu su tashi su yi wanka. Ita kuma ta fice ta shiga ɗakin Zaid. A can ta yi wanka, ta ɗauki ɗaya daga cikin kayanta da suke can ta saka, ta fito.
Sanda ta koma ɗakin nata, Mishal ce a banɗakin tana wanka, ita kuma Rhoda ta yi wanka tana shafa mai.
“Rhoda kaya na kuwa zai miki?”
Ta tambaya tana buɗe lokokinta. Rhoda ta juyo ta kalleta.
“Ai ba zai iyu na saka kayanki ba ma, yau za mu shiga kotu, dan haka kayan aiki ya kamata na saka, so ba sai na sauya kaya ba,zan tafi da wannan, daga can kuma sai na wuce Kaura”
Cike da gamsuwa Rabi ta rufe lokarta, bayan da ta ɗaukowa Mishal wata doguwar rigar atamafa da take da tabbacin za ta mata dai-dai, dan kansu ɗaya da wadda ta bata ta saka jiya.
Zama ta yi a bakin gadonta,tana buɗewa wayarta dan kiran Zaid, sai de kuma wayar har ta yi ringing ta katse bai ɗaga ba. Sai kawai ta aje wayar, don ta san da ma balalle ya ɗaga ɗin ba.
A lokacin Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta ɗaure da towel.
“Ga kaya, sai ki sauya”
Rabi'a ta faɗi tana mata nuni da doguwar rigar atamfar dake aje a kan gado, Mishal ta kalli kayan, sannan ta ƙaraso ta ɗauka, ta koma banɗakin dan sakawa.
Cike da jin tausayinta Rabi ta girgiza kai, idanunwata ba ƙaramin kumbura suka yi ba, saboda tsabar kuka.Wayar Rhoda ce ta yi ringing, hakan ya sa ta ɗaga wayar tana fita waje, dan kiran daga headquarter su ne.
Bayan wani lokaci, Mishal ta fito daga banɗakin, jikinta sanye da doguwar rigar. Ba tare da ta saka komai a jikinta ba ta zauna a kusa da Rabi. Fuskar nan cike da damuwa, kana ganinta za ka san cewa tana cikin tashin hankali, idonta ya jeme, fuskar nan ta yi jajir.
“Ga hijabi ki saka”
Kallon hijabin ta yi, kafin ta karɓa tana miƙewa tsaye.
“Mu je mu ci abincin to”
Rabi ta faɗi tana dafata, bayan da ta gama saka hijabin. A falo suka haɗu da Rhoda, wadda ta gama wayar da ta tafi yi, daga nan suka wuce danning suka ci abinci. Kafin suka shirya fita daga gidan.
*Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja.*
KULIYA POV.
Zaune yake daga bakin gadon marasa lafiyar dake dakin da aka kwantar da shi. Ya zuro ƙafafunsa ƙasan gadon. Jikinsa sanye da kayan marasa kafiya da ake bawa pertinent ɗin asibitin. Hannunsa na dama, sanye cikin arm sling. Daga gefen damansa kuma, Zaid ne zaune yake kallonsa ta gefen ido, dan jinsa yake kamar wani baƙo a gurinsa.
A ɗazu bayan da ya dawo daga masallacin sallahr asuba, ya tarar da Aliyun ya buɗe idonsa, amma kuma yana kwance a kan gadon, hakan ya sa ko ɗakin ma bai ƙarasa shiga ba ya juya da sauri ya tafi kiran nurses. Tare da nurses guda uku suka dawo, su suka dakatar da shi a waje, su kuma suka shiga ɗakin. Jim kaɗan ɗaya daga cikinsu ta fito, bayan ɗan wani lokaci kuma sai gata ta dawo ita da likitan da ya duba Aliyun. Sun jima sosai a ɗakin, dan har sai da ya ƙagu.
Sai ga su sun fito, da sauri ya shiga tambayar likitan jikin Aliyun. Likitan ya sanar masa da komai lafiya, dan har sun saka masa arm sling, gudun kada ya cika yawan motsa hannun. Amma kuma sun masa wata allura, wadda ta sa ya koma bacci, amma daga lokacin zuwa ƙarfe bakwai na safe zai iya farkawa. Da haka hankalinsa ya kwanta, har ya dawo ɗakin ya zauna ya ci gaba da gadinsa, har zuwa lokacin da ya farka.
“Ya... Ya kake?”
Cewar Kuliya, dan be ma san me ya kamata ya tambayi ɗan uwansa ba, wanda Allah ya haɗasu bayan shuɗewar shekaru masu yawa da rabuwarsu. A ɗazun da ya farka cewa ya yi Zaid ɗin ya ara masa wayarsa, akwai wanda zai kira. Bayan da Zaid din ya ba shi wayar, sai ya kira Anna ya sanar mata halin da yake ciki. Kuma tun bayan wannan maganar, wata magana bata ƙara shiga tsakaninsu ba.
Zaid ya juyo ya kalleshi, me makon ya amsa tambayar da ya masa, sai ya ja ɗan uwan nasa ya rungumeshi. Duk cikinsu babu wanda be zubar da ƙwalla ba, dan faɗar kalar kewar juna da suka yi ma ɓata baki ne.
“Wannan ne abun da ya kamata ace ka tambayi yayanka bayan kun haɗu?!”
Cewar Zaid yana shafa kansa bayan da suka saki juna. Kuliya ya share hawaye.
“Ban... Ban san me ya kamata na ce ba ne?”
“Dama kai kana rasa abun faɗe ne?”
Sai suka yi dariya.
“Ina Mishal?”
“Wa? Ko matarka ?”
Sai Aliyu ya sunkuyar da kansa yana faɗin.
“Eh ita”
“Suna gidana, ɗazu na ga kiran matata, na san nan da anjima za ka sun iso...”
Daga nan kuma sai aka buɗe babin hira, suka shiga bawa juna labaran abubuwan da suka faru a rayuwarsu bayan rabuwarsu, daga Zaid har Aliyun, Allah ne

Please Login or Register in order to submit comment