Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ma ya ga abun.
“To ai ba tsayuwa ya kamata mu yi ba, kamata ya yi mu duba mu ga mene a ciki, kafin mu san matakin ɗauka”
Da farko ba su yarda da shawarar tasa ba, amma daga baya sun amince, haka suka zagaye abun da suke da tabbacin mutum ne a ciki, da farko sai da suka ƙara tsorata, ganin jini a jikin bargon, kuma ba su ƙara tsorota ba sai da suka yi arba da abin cikin bargon.
“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un!”
Kusan a tare suka furta hakan, sakamakon ganin gawar matashiyar yarinya, babu sitira a jikinta, ga gefen fuskarta da aka mata wani faffaɗan rauni, sai kanta da ya fashe ya na zubar da jini.
A wannan ranar:
*Brickhall school, Kaura District, Game Village, Abuja.*
*10:40 AM.*
A karo na biyu, Fu'ad ya girgiza kansa, sakamakon bayanin da Principle ɗin makarantar ke masa, game da tambayar Rabi da ya yi, ba wannan ne ya fi ɗaga masa hankali ba, abun da ya fi ɗaga masa hankali shi ne; yau da safe Saratu ta kira shi ta na ta rinjin kuka, babu yanda bai yi da ita ba, dan kwantar da hankalinta amma ta ƙi saurarensa, har cewa ta yi za ta je makarantar ta duba da kanta.
“Nagode ranka ya daɗe”
Ya na faɗin hakan ya miƙe ya fice daga office ɗin, jiki a tsaɓule ya shiga motarsa, kai tsaye ya nufi Suleja.
A inda ya saba aje motarsa ya yi parking, wato bakin layinsu Saratun, ya fito daga motar tasa ya shiga cikin layin a ƙafa, a ƙofar gidan nasu ya tsaya, sannan ya kira Saratun ya sanar mata da zuwansa. Ko minti ɗaya ba ta ƙara ba sai ga ta ta fito a rangauce, kallo ɗaya za ka mata ka gano tashin hankalin da take ciki, yau ko Mama ce ba'a ganta ba tashin hanlalin da za ta shiga sai haka, babu abun da ya fi ɓata mata rai irin yanda Habiba ta basar da lamarin, ta shiga harkokin gabanta, don a yanzu haka ma ta na cikin gidan ta na suyar funkasonta hankali kwance , kamar tsumma a cikin randa, bayan ta tura 'yar mutane aikatau an rasata.
“Me suka ce? Ka ga Rabin? A ina ta kwana?!...”
Ta jero masa tambayoyin a birkice, idonta kawai yake kallo, yanda ya yi jajir, ba lalle ma a ce ta yi bacci daren jiya ba.
“Sarah, ki kwantar da hankalinki...”
“Fu'ad ka faɗa min gaskiya kawai!”
Fu'ad ya haɗiye yawu, sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa.
“Tabbas jiya Rabi ba ta bar can ba sai ƙarfe bakwai na dare, amma sun tabbatar min da bata can...”
Bai kai ga ƙarashe maganar ta sa ba, saboda kukan da Saratun ta sa kamar wanda ya watsawa ruwan asid me zafi a fuska.
KULIYA POV.
A hankali tayoyi motarsa suka tsaya a harabar makarantar Brickhall, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya fito daga cikin motar, sai da ya tsaya ya ƙarewa gine-ginen makarantar kallo, kafin ya nufi cikin makarantar, sai da ya yi tambaya kafin aka sada shi da office ɗin principal.
“Akwai wata yarinya da take muku aiki a nan, sunanta Adawiyya, shin zan iya ganinta”
Cewarsa, yayinda yake zaune a kujerar tsallaken teburin principal ɗin, mutumin ya ɗaga kansa sama cikin tunani, sannan ya sauƙe kansa.
“Mts!, gaskiya babu me wannan sunan a cikin masu aikinmu”
Kuliya ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama ya na haɗiyar yawu.
“Rabi'a fa?”
Da sauri mutumin ya gyaɗa kansa.
“Eh, akwai Rabi'a a cikinsu, sai dai kuma yau kwata-kwata ba ta zo aiki ba, don har wani mutum daga gidansu ya zo ya ce wai suna nemanta, don tun jiya rabonta da gida!”.
Wani irin ƙara zuciyar Kukiya ta yi, da sai da ya ji a kunnuwansa, ba ta zo ba?, ana nemanta a gida?, to me hakan ke nufi?...
“Laaaa, Abu Aswad!”
Cak, ya tsaya da tafiyar da yake, jin muryarta ta ambaci sunan da ta laƙaba masa, addu'a ya yi ta yi ta kada Allah ya sa su haɗu, amma sai ga shi an samu akasi, shi a yanzu kansa na cikin wani hali, saboda abubuwa sun cakuɗe masa, ya rasa mamakamar zaren, bare har ya san ta inda zai kama don ya fara saƙa mafitar lamarin, zuwansa makarantar ma bai masa wani amfani ba. Sai temakawa da ya yi wurin ƙara dagula masa lissafi.
Juyowa ya yi a hankali ya kalleta, gani ya yi ta ƙara nutsuwa, kamar ba ita xe6 wannan yarinyar me shirinta da aka aura masa ba, yarinyar da ko hula ba ta sakawa idan za ta je makaranta, amma yanzu ya lura da kullum ta na saka hular. Sai dai kuma hular da ta saka ba ta ɓoye raunin dake goshinta ba, kamar yanda ya saba ganinta, fuskar nan a jeme, babu ko kwalli, daga gefenta kuma wata baturiya ce da a shekaru ba za ta wuceta ba.
Da ɗaukinta ta ƙaraso gabansa, bakin nan buɗe ita a dole ta ga mijinta a makarantarsu.
“Wurina ka zo? Ai muna can baya, anti Adawiyya nake ta dubawa, don yau sam ban ganta ba!”
Dammm!, gabansa ya buga, amma sai dake, ya kasa ce mata komai, dan bakinsa ya masa nauyi, ji yake kamarya haɗiyi dutse. Kallonta kawai ya ci gaba da yi, yana saƙa da warwara a zuciyarsa.
“Ko ba wuri na ka zo ba?”
Ta tambaya, wannan fara'ar da take a ɗazu ta na shirin ɗaukewa daga kan fuskarta, sai ya girgiza kansa da sauri ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Dan ke na zo!”
Daɗi kamar ya kasheta da jin furincinsa, a jiya kawai Allah ne kaɗai ya dan adadin yanda ta kira sunansa a ranta, ita ba ta tabbatar da sonsa take ba sai a jiya, jiyan da kishinsa ya rufe mata ido har abun da ya faru tsankaninta da su Siyama, ya zo ya faru.
“Kin ci abinci?”
Da sauri ta gyaɗa masa kai, idanunta har ƙyallin murna suke, shi ma ya gyaɗa nasa kan.
“Da ma zuwa na yi na ga ya kike. Zan wuce gidan Anna”
Ya zaɓi ya mata wannan ƙaryar ne don kada ta zargi wani abun.
“Zan koma” Ya faɗin ya na shirin juyawa.
“A'a. Ka tsaya ku gaisa da Angelica, kuma ina so na nunawa sauran 'yan ajinmu kai, rannan na ce musu an min aure, amma babu wanda ya yarda”
Har yanzu dai wannan shiriritar na nan, kuma kafin yace a'a, har ta kama hannunsa ta shiga jansa, sai ya riƙe kalamansa ya shiga bin bayanta.
“Kai shashashu! Na ce muku an min aure kun musa ko? To ga ku ga mijinawa, sai ku tambayeshi ku ji!”
Abun da ta faɗi kenan a class ɗin nasu cikin ɗaga murya, kasancewar lokacin break ne, kowa na harkar gabansa, ido ya dawo kansu gaba ɗaya, sai kallon kallo ake, wasu na mawa mijin Mishal ɗin kallon sani, don ya na musu kama da wannan me sharar, sai masu masa kallon sani, saboda kullum idan an tashi suna ganinsa tsaye a tsallaken makarantarsu, wasu kuwa ma basu san shi ba.
*No. 213, Naf belly, Asokoro, Abuja.*
“Wallahi Aliyu ba ni da masaniya kan abun da su Karima suka aikata!”
Anna ke faɗin hakan cikin hawaye, bayan da Kuliya ya zo ya na sanar da ita haukan da Karima da kuma Siyama suka je gidansa suka aikatawa Mishal. Kuliya ya kamo hannayenta ya riƙe. Bayan ya bar Brickhall kai tsaye gidan Annan ya nufo.
“Na sani Anna. Na san ba za ki aikasu su yi wa matata haka ba, amma ina son na sanar da ke da ki jawa kowaccensu kunne, kan kada su ƙara taka ƙafarsu cikin gidana, jiya ma girmanki da darajarki suka ci, ba dan haka ba Wallahi ba zan barsu ba”
Anna ta share hawaye.
“Ba komai Aliyu, tashi ka tafi aikinka, zuwa yanzu na san ka makara, ka je kawai, ni na san matakin da zan ɗauka!”
Ya karkatar da kansa gefe.
“Ba za ki dena kukan ba?”
Anna ta ɗan yi murmushi tana share wani hawayen.
“Na dena, ka je kawai”
“Shikenan”
Ya faɗi ya na miƙewa, har ya fice Anna na kallonsa, ta san abun da za ta yi. Don ta zubawa su Karima ido suna ta haukansu ba wai don ba za ta iya taka musu birki ba ne, ba ta san cewa haukar tasu ta ƙamari ba, amma ba komai, Allah ya kaimu gobe, za ta yinwa tufkar hanci.
*Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja.*
Da gudu wata nurse ta fito daga wani ɗaki da aka kwantar da wata mara lafiya da ta baƙunci asibitin nasu a safiyar yau, hannunta na dama ɗore a bakinta, a ƙoƙarinta na tare kukan dake son cin ƙarfinta, ta jingina da jikin bango tana kallon ƙofar ɗakin, a hankali ta zame zuwa ƙasa, kukan da take ta yunƙurin riƙewa ya fito da ƙarfinsa.
Tun da uwarta ta kawota duniya ba ta taɓa ganin tashin hankali irin wanda ta gani yau ba, ta na jin labarin fyaɗe, amma ba ta taɓa ganin wanda aka yi wa fyaɗe ba sai yau, an ce mata idan ta fara aiki sai ta gamu da abun da zai sa ta kuka, a wancan lokacin da aka faɗa mata dariya ta yi, don ita ba ta hango yiyuwar hakan ba, sai a yau ta yarda da abun da aka faɗa mata, kuka take sosai har ta na dafe ƙirjinta.
Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, likitan da suka shiga tare da shi ya fito ya na sharar ƙwalla, kafin ya kalli nurse ɗin, shi kansa da ya kwashi tsawon shekaru ya na aikin bai taɓa ganin abu makamancin wanda ya gani yau ba, bare ita da ta ke sabuwa a aikin.
“Ke Sakina! lafiyar ki kuwa?”
Wata ƙawarta ta tamabaya, a sanda ta biyo corridorn ta ga ƙawar tata zaune a ƙasa tana kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa, juyawa ta yi ta kalli likitan, shi ma duk jikinsa ya yi sanyi, kansa a ƙasa kamar da aka ce shi ne ya aikata fyaɗen.
Hannunta ta kai ta kamo ƙawar tata tana miƙarta, tare da share mata hawaye, amma Sakinan sai ta ƙwace fuskarta ta na komawa gefe.
“Dan Allah Kausar ki bar ni na yi kuka. Bar ni na koka da abin da na gani. Kausar wasu mazan ba su da adalci, ba su da tausayi!”
Ta ɗaga hannunta tana nuna mata ƙofar ɗakin.
“Shi ga ki ga abun da suka yi wa wata yarinya. A shekaru dai na san yarinyar ba za ta wuce 19 ba, amma ki je ki duba ki ga yanda suka mata fyaɗe cike da rashin imani, mutum biyar Kausar, mutum biyar ko sama da haka ne suka haike mata!.Kuma ba su barta da wannan tambon ba, sai da suka ƙara mata da wasu raunuka a jikinta, gefen fuskarta da kuma kanta duk sun fasa mata, yanzu haka yarinyar ta shiga doguwar suma!”
Ita kanta Kausar ɗin sai da gabanta ya buga da mugun ƙarfi, don za ta iya cewa wannan ɗin sabo abu ne da ya shigo asibitin nasu.
“Me ya sa Kausar?. Me ya sa mu ba mu da 'yanci?, Kowa sai ya taka mu ya wuce yanda yake so. Me ya sa wasu mazan ba sa ganin mata da kimi?. Me yasa?... Sai zuwa yaushe ne za mu tsira?, sai zuwa yaushe?!”.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
RAJA POV.
Zaune yake a ɗakinsa, ya yi tagumi da duka hannayensa biyu, abun duniya ya bi ya isheshi, musamman yau da ya ga Rabi'a ba ta zo ba, abun ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, shi fa burinsa shi ne ya samu ya ganta don ya mata bayani, zai gabatar mata da kansa a ainahin yanda yake, zai faɗa mata gaskiyar komai a kansa, amma yau haka ya ƙaraci tsayuwarsa a ƙofar gate ɗin ba tare da ya ga gilmawarta ba.
Ƙofar ɗakin aka buɗe, sannan Rhoda ta shigo hannunta tiƙe da wayarsa. Kansa kawai ya ɗaga ya kalleta ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.
“Alhaji Bala ne yake ta waya. Yace ya na buƙatar kayansa cikin gaggawa”
“Mtswwww!”
Ya ja tsakin ya na kawar da kansa, shi ba ta Alhaji Bala yake ba, don matsalar Alhaji Bala sifili ce a wurinsa, babba kuma shirgegiyar matsla gareshi ita ce RABI'A!.
Ganin hakan ya sa Rhoda zama kusa da shi, sannan ta dafa ƙafaɗarsa.
“Na san halin damuwa da kake ciki, amma ya kamata ace ka sameta ku yi magana, ka faɗa mata gaskiya, wata ƙila ta saurare ka”
Fuskarsa ya shafa da hannayensa.
“Yau ba ta zo ba fa” Ya faɗi cikin wata murya me sanyi.
“Wata ƙila ta zo, ta ɓoye ne kawai dan kada ka ganta”
Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, ƙwarai, hakan za ta iya kasancewa, amma me ya sa shi bai yi tunanin hakan ba?.
“Ki na ga zan iya shiga cikin makarantar?”
“Me zai hana?”
Sai ya gyaɗa kansa, ya na hangowa kansa mafita a cikin kalaman Rhoda.
*No.181, Guzape, Abuja...*
*07:00 PM.*
MISHAL POV.
Tsaye take a kitchen tana juya stew ɗin da take dafawa, duk da yau girkin a makare take yinsa, saboda makarar da ta yi wurin dawowa gida. Ba tare da ta san lokacin da ya shigo ba, ta ji muryarsa a bayanta.
“Ana san magana da ke!”
Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya na tsaye daga bakin ƙofa, kallonsa da ta yi a yanzu shi ya tuna mata da shirman da ta yi masa yau da safe a school ɗinsu, don haka ta yi ta nuna shi a wurin 'yan makarantarsu tana faɗin ga mijinta nan.
“Waye yake san maganar da ni”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, dai-dai da lokacin da Mishal ta ɗaga tata kafaɗar ta dama, don kawai neman tsokana, ita ta rasa me yake ji a wannan ɗaga kafaɗar, mutum ya yi ta wani ɗaga kafaɗa?, shi ba tsuntsun ba, kuma ta lura da wancan ɗan uwan nasa ma ya na ɗaga kafaɗar.
Cike da mamaki Kuliya yake kallon Mishal, wato shi take kwaikwayo?, don ta na ga ya na ɗaga kafaɗa shi ne ita ma za ta yi?. Kuma ita ma ta lura da kamar fushi yake shirin yi, don haka ta yi saurin cewa.
“Waye yake son maganar da ni?”
Maganar tata ta tuna masa da batun da ya zo mata, sai ya share batun ɗaga kafaɗa yace.
“Yayarki Nimra”
Sai ta juya ta kashe wutar gas ɗin, sannan ta juyo ta kalle shi.
“Wayar tana ina ?”
Da hannunsa ya nuna mata falo, don shi gajiya yake da wannan surutan, ita ma kuma ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta raɓa shi ta fice tana dariya ƙasa-ƙasa.
Ƙamshin da stew ɗin ke yi ya ci gaba da shiga hancin Kuliya, don haka ya cewa kansa de yau ya kamata ace ya ɗanɗana abincin nata, sai ya shiga bubbuɗa pots ɗin da ta yi girkin da su, farar shinkafa ce sai wannan stew ɗin dake ta tashin ƙamshi, ga kuma coslow a gefe.
Tsakani da Allah abincin ya burgeshi kamar sauran abincinta, ga kuma yunwar da yake ji, saboda rabonsa da abinci tun safe, ya kai hannu ya ɗauki plate, ya zuba abincin iya yanda ya san zai iya cinyewa.
Sannan ya fara ci, bai taɓa zaton ƙaramar yarinya kamar Mishal za ta iya yin girki haka ba, a da duk ɗaukan zancen girkin nata yake a matsayin shirme, amma yanzu da ya ɗan-ɗana sai ya ji kamar irin wannan abincin yake buƙata a kullum domin ci.
Mishal na fita ta hangi wayar tasa aje a kan coffe table, da sauri ta ƙarasa wurin ta ɗauki wayar, gaisawa suka yi, kafin Nimran ta tambayeta yanayin zaman nasu, kana ta ƙara mata da nasiha, ita kuma Mishal ɗin babu abun da ta tambayeta sama da Daala, don ita kaɗai ta yi kewa.
Sai da suka gama wayar, sannan ta tashi ta nufi kitchen ɗin, zuciyarta ɗaya ta tura ƙofar kitchen ɗin, kuma abu na farko da idonta ya fara gane mata shi ne.
Kuliya tsaye a kusa da stove, hannunsa na hagu riƙe da plate, wanda yake cike da shinkafa da miyar da ta dafa, harda coslow a gefe, hannunsa na dama kuma riƙe da cokali, ya kai shi setin bakinsa ya na shirin kai loma.
Ba ƙaramar dariya ya bata ba, mutumin da a kullum yake gudun cin abincinta, yau shi ne ta kama ya na cin abincinta a ɓoye, amma sai ta riƙe dariyar, ba tare da ta ce masa komai ba, ta tsaya a kusa da shi, ta sauƙe tukunyar stew ɗin daga kan stove.
Kuliya ya ci gaba da binta da kallo, ya zaci za ta ce wani abun, amma sai ya ji ta yi shiru, har ta gama kwashe abincin duka, ta zubawa Ayra, sannan ta ɗauki nata ta zauna a kan kujerar island.
Ganin ya kasa ƙarasa cinye abincin nasa ya sa Mishal faɗin.
“Ka zauna ka ƙarasa ci”
Kuliya ya ɗan sosa ƙeyarsa, sannan ido ba kunya ya ƙaraso ya zauna a tsallakenta ya na ci gaba da cin abincin. Ita dai Mishal sai ƙunshe dariyarta take, duk da daga can ƙasan zuciyarta akwai wani abu ɗan ƙanƙani me kama da damuwa, kuma abun ya samo asali ne saboda rashin zuwan Adawiyya makaranta!, abu ne wanda tun bayan da suka ɗinke bai taɓa faruwa ba, ko a da can ba ta ganinta tana fashi bare yanzu, amma har can ƙasan zuciyarta take fatan kada Allah ya sa wani abu mara kyau ne ya faruwa da Adawiyyan.
*Washe gari...*
*Brickhall School, Kaura District, Game Village, Abuja.*
RAJA POV.
Cike da mamaki principal ɗin makarantar yake kallon mutumin dake zaune a tsallaken teburinsa, kamar ba shi ba ne jiya ya zo ya na tambaya a kan Rabi'a, yau kuma sai ga shi ya dawo da wani yanayi da ban, saɓanin wanda ya zo da shi jiya, stil kuma ya na sake tambayarsa a kan Rabi'an.
“Ka yi shiru, ko akwai matsala ne?”
Rajan ya tambaya, ganin yanda mutumin yake kallonsa, principal ya girgiza kansa.
“Ba haka ba ne, kawai dai yau kwana biyu kenan bat ta zo ba!”
Wani irin shiru ne ya ratsa office ɗin, kuma a cikin shirun, banda bugu cikin sauri babu abun da zuciyar Raja ke yi, wannan abun da yake ji a jikinsa ya fi ƙarfin tsoro, ji yake kamar ma ya haukace ne, me ya sa Rabi'an ba ta zuwa?, saboda shi ne?, amma me ya sa?, ko wani abu ne ya sameta?.
Da waɗanan tambayoyin fal a ransa ya bar office ɗin.
“Yayana!”
Ya ji an kira sunan a bayansa, amma bai tsaya ba, saboda halin da yake ciki ba zai barshi ya tantance da shi ake ko ba da shi ake ba.
“Ɗan uwa!”
Aka kuma kiran sunan, hakan ya sa ya tsaya sannan ya juyo, wannan yarinyar ce, wadda ta ce masa ya na kama da cousin ɗinta.
“Dama a nan kake ?”
Mishal ta tambaya a sanda take isowa gabansa, mamaki fal kanta, na son sanin me ya zo yi a makarantarsu.
“Na... Na zo neman wani ne”
Sai ta gyaɗa kanta.
“Ka same shi?”
Ta tambaya, sai ya girgiza kansa.
“A'a, ban same shi ba”
Ya faɗi yabna ɗaga kafaɗarsa ta dama, Mishal ta jinjina girman Allah a cikin ranta, sak Kuliya,duk da akawai 'yan banbance banbancea tsakaninsu.
“Faɗamin sunansa, na san kowa a makarantar nan, zan nemo maka shi”
Duk da halin da yake ciki sai da ya ɗan murmusa.
“Ba lalle ki san shi ba. Zan koma, na gode ƙanwata, ki kula da kanki!”
Haka kawai ya samu bakinsa da furta sunan, kuma bai jira cewarta ba, ya juya ya ci gaba da tafiya.
Mishal ta ci gaba da kallon bayansa, abubuwa da dama na mata kai kawo a cikin kai, tana son ta san me ya sa Anti Adawiyya ba ta zuwa, kuma ta na son sanin me ya sa Kuliya babya tare da ɗan uwansa, tabna son ta san me ya sa su duka suka zo makarantarsu, don ta san ko Kuliyan ma jiya ba wurinta ya zo ba.
*No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja.*
Siyama da Karima Yayarta da kuma yaran Kariman ne zaune a falo suna karin kummalo. Kowacce a cikinsu jikinta ɗauke yake da rauni, raunin da suka samu a zuwansu gidan Kuliya.
“Salamu Alaikum!”
Suka ji sallamar Anna, a yayin da take turo ƙofar falon, da sauri Karima ta miƙe tsaye, hakan ya sa Siyama ma ta miƙe, saboda sun san ba su da gaskiya.
Ɗaya bayan ɗaya yaran Kariman su uku suka riƙa gaida Anna, ta na amsa musu.
“Abdul ku je ɗakinku ku ƙarasa karin a can”
Babban ɗan nata ya amsata ya na haɗa kan ƙannensa wuri ɗaya, tare da ɗiban kayan abincin nasu suka yi ɗaki.
Kamar da Annan take jira, ta samu guri ta zauna tana musu kallon tuhuma, ganin yadda ko waccensu ta kafa inda-inda ne ya tabbatar mata da gaskiyar abun da suka aikata, duk kuwa da ta san Kuliya ba zai mata ƙarya ba.
“Yanzu ke Karima a matsayinki na babba, ya kamata a ce kin aikata abun da kika aikata?, Ko za'a kira abun da Siyama ta yi a matsayin yarinta naki ba za a ce yarinta ba ce, saboda kin fita shekaru da sanin ya kamata. Amma saboda ke babbar kwabo ce, kika wanki ƙafa kuka je gidan matar mutane kuka rufa mata duka ko?!”
Da sauri Siyama ta girgiza kanta, hawaye na ciko mata ido, musamman da ta tuna abun da ya faru a wacan ranar.
“Anna Wallahi. Wallahi ba mu...”
“Ƙarya kuke!, Idan ba ku ne kuka daketa ba za ta buga kanta da kanta a jikin bango ne, ta zo tace ku ne kuka mata dan kawai ta muku ƙazafi?”
Da sauri Karima ta gyaɗa kai.
“Wallahi Anna ba mu daketa ba, hasalima ita ce ta dake mu, duba ki gani...”
Ta ƙarashe tana nunnuna mata tabon raunikan jikinta. Anna ta yi dariya, irin kun rena min hankalin nan.
“Karima ko ƙur'ani za ki dafa kan wannan maganar taki ba zan yarda ba, jibe ki fa, yadda kike rusheshiyar nan da ke sai na yarda waccan 'yar fingilar yarinyar ita tai miki wannan raunin?, saboda ga Annan mahaukata ko?, to ni ba ma wannan ne ya kawo ni ba, zuwa na yi na ja muku kunne, babu ku babu gidan Aliyu, sannan babu ruwanku da sabgar matarsa, idan kuma ba ku ji ba ku je ku yi, Wallahi ni da kai na zan sa Aliyun ya hukunta ko waccenku, har ke Karima, tun da ba wani fikon arziƙi kika masa ba, in kun ce bakwa ji sai ku gwada mu gani!”
Tana ƙarashewa ta miƙe ta fita, don da ma abin da ya kawota kenan, Siyama ta zube a kan kejera tana fashewa da kuka.
“Kin ga inda kika kai mu ko Anti, yanzu ga shi bayan dukan da muka sha Anna ma ta ƙara mana da nata kashedin”
Karima ta matse ƙwalla, tunawa da irin dukan da suka sha da ta yi.
“Da ma ni sam soyyayar Kuliya ba ta karɓeni ba, ban da wahala babu abun da nake sha”
Ta ƙarshe tana miƙewa, tare da nufar ɗakinta da gudu. Karima ta yi tagumi tana jinjina sharri da kissa irin na wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar da suka rena, ko dan ai an ce ɗan hakin da ka rena.
____________________
_Gani nan na yi tagumi hannu bibbiyu_
_jama'a!, wai ina Rabi ta shige ne?, wani ya temaka ya nemo mana ita_
_Ku ni fa na kasa gano abun da ya faru tsakanin su Karima da kuma Mishal_
_Salmanians, shin kuna kusa?_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••••••••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*16*
~~~
*Don't be afraid of falling apart. Some of the must beautiful heart are built from tragedy.*
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
*Bayan sati uku...*
*No.181, Guzape, Abuja...*
*09:30pm*
MISHAL POV.
Kwance take a falo, ta duƙunƙuna cikin blanket, idanuwanta sun yi ja saboda kukan da ta ci, ta kunna tv ta tsura mata ido amma ba kallon take ba.
Damuwa da ruɗani ne suka saka rayuwarta a gaba, yau kusan sati uku kenan, amma Antinta Adawiyya ba ta zuwa makaranta, tun ta na ganin abun kamar fashi ne, har fashin nata ya zo ya soma bata tsoro, dan zuwa yanzu ma an kawo wata sabuwar me yim shara a makarantar, kullum sai ta yi kukan rashin sanin halin da Adawiyyan ke ciki, ga kuma kaɗaici da yake damunta a yanzu, ga shi dai ba wani jimawa suka yi da Adawiyyan ba, amma haka kawai take jinta cikin kaɗaici, yanzu haka ta hana idonta bacci ne dan jiran dawowar Kuliya, tun da shi ɗan sanda ne wata ƙila zai iya yin wani abu akan case ɗin yayar tata.
Ta na kwance a wurin har goma ta wuce, kuma sai a lokacin Kuliya ya shigo gidan rai a ɓace, wanda ya samo asali daga wurin aikinsa, Mishal na jin shigowarsa ta miƙe da sauri ta sha gabansa, kallonta ya yi na 'yan wasu sakkani, sannan ya shiga ƙoƙarin raɓata

Please Login or Register in order to submit comment