Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fasa gidan.
Yasan ƙanwarsa da dauriya, ba komai takewa kuka ba tun tana ƙarama, tana iya jure komai duk zafinsa, dan haka tun da take kuka, dole ciwon nata ba ƙarami ba ne.
Kamata ya yi, sannan ya miƙar da ita yana shirin fita da ita daga kitchen ɗin. Sai da suka zo wucewa ta kusa da Hajjara, Mishal ta kalleta, kamar ba ita ceke yin gunjin kuka yanzu ba. Sai da ta faki idon Abubakar, sannan ta ƙiftawa Hajjara ido ɗaya, tana murmushin da ke nuna ita ta yi winning gasar.
“You lose!”
Ta furta hakan a iyaka kan leɓenta kawai, wanda Hajjaran dake ganinta ce kaɗai za ta iya gane me ta faɗa. A sanda Hajjara ta zube a ƙasa tana runzar kuka.
A lokacin Mishal ta dawo da nata sabon kukan, tana riƙe hannunta. Hakan yasa Abubakar ƙara ruɗewa, don bai ko Hajjara bai waiwaya ba.
*Nizamiye Hospital, Sector S. Cadestral zone, Life Camp, Abuja*
“Kamar yanda na faɗa maka ne, yanka ba wani sosai ya shigeta ba, dan haka ba wata damuwa, za ku iya tafiya...”
Likitan da ya duba Mishal ne ke korowa Abubakar bayani, wanda gaba ɗaya hankalinsa ya gama ta shi.
Daga can wata kujera dake gefe a office ɗin kuma, Mishal ce zaune, daga ita sai long sleeve Oxford shirt ɗin uniform ɗinta, suit ɗina na aje a gefen kujerar da take kai. Kanta a ƙasa tana tuna abun da ya faru ɗazu.
A ɗazun bayan da Hajjara ta rarumo wuƙa, sai ta ɗorata a tsintiyar hannunta sannan tace.
“Zan yanka kaina, dan na rabaki da Abubakar, zan zubar da jini na fansa, dan na shiga tsakaninku, zan yanka kai na yanzu, sannan na kira shi na ce kece kika yanka ni...”
Kuma tun kafin ta gama faɗin abun da za ta faɗa, Mishal tai wuf ta ƙwace wuƙar daga hannunta, sannan ta ɗora a nata hannun ta yanka kanta. Ta kuma yi sauri ta danƙawa Hajjaran wuƙar, kafin ta faɗi ƙasa, shi ne ta kurma wannan ihun tare da saka kuka.
Sai kawai ta yi murmushi a fili, yanzu da ace ba ta yi hakan ba, da yanzu ita ce a ciki, ta rasa me ta tsarewa Hajjara da ta tsaneta haka, ba ta san me ta yi mata ba.
Hannunta na hagu ta ɗago, ta kalli plastern da aka saka mata yanzu, sannan ta ɗaga kai ta kalli Abubakar da ya zo ya tsaya a kanta yana kallonta cike da tausayawa.
“Sannu Hafsat, tashi mu je”
Sai ta miƙe tsaye, tare da kai hannunta na dama ta ɗauki suit ɗin.
Wayar Abubakar ta yi ƙara a sanda suka fito daga office ɗin, hannunsa ya sa a aljihu ya ɗauko sannan ya amsa.
“Hello Sharon, howdey?!”
Daga cikin wayar Sharon tace.
“Fine sir... Kuliya ne ya yi hatsari jiya, sannan an kwantar da shi a asibiti...”
“What?!, hatsari?!, a ina?, wani asibiti yake?”
Ya katseta tare da jero mata tambayoyin. A lokaci guda kuma ya dakata da tafiyar da yake, hakan yasa Mishal ma dakatawa tana kallonsa.
“Nizamiye hospital”
Sai ya yi shiru.
“Yanzu haka ina cikin Nizamiye hospital ɗin, wani ɗaki yake ?”
“Room No.18”
”Nagode Sharon”
Kuma daga haka ya sauƙe wayar.
“Ukti abokina ba shi da lafiya, muje mu duba shi”
Mishal ba ta damu da san sanin waye abokin nasa ba, dan haka kawai ta bi bayansa.
*Room No.18, Nizamaye hospital*
KULIYA POV.
“Yanzu miye amfanin irin wanna?!, Ka daba abun da ya sameka ka gani da idonka, kullum ina cikin maka nasiha a kan yawan gudun da kake da mota, amma sam baka kulawa, yanzu ga irinta nan!...”
Anna ce ke ta balbale shi da faɗa, yayin da take tsaye a kansa, kusa da gadon marasa lafiyar da yake zaune a kai. Ya jingina bayansa da gadon, gefen fuskartsa na manne da plaster, hannunsa da kuma wuyansa gaba ɗaya rauni ne.
Allah ne ma ya kawo masa abun da sauƙi, dan a sanda wannan babbar motar ta daki tasa sai Allah yasa ya fita ta wundo, sanda motar ta tashi sama.
Bayan ya faɗo sai ya gangara bakin titi, hakan ne ma yasa ya ji raunikan jikinsa. Kuma a sanda jama'a suka kawo masa ɗauki ya suma, don haka bai farka ba sai cikin daren, shi ne ya tsinci kansa a asibiti.
“Yanzu idan ka ga motar taka ba za'a ce ɗan adam ya fita daga cikinta ba, saboda yanda ta kwankwatse!...”
Anna ta ci gaba da faɗi cikin faɗan da take, a hankali ya ɗaga kansa ya kalleta, sannan ya ce.
“Ki yi haƙuri Anna, amma ni ban san daga inda motar take ba, kawai da...”
“Ina za ka sani?, ai ba za ka sani ba!”
Kuma tana kaiwa nan ta figi jakarta ta fita, dan ba za ta iya jurewa ba, Aliyu kaɗai ya rage mata a duniya, duk da ba ita ta haife shi ba, amma ta na sansa, tana masa so irin na ɗa da uwa. Gawara ta nuna masa fushinta a kan abinda ya yi, wata ƙila ya fahimci kuskurensa ya gyara.
A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya shafa kansa. Duk yan da aka yi wannan haɗarin shiryyaye ne, dole ne ma wani ne ya shirya shi. Kuma ko kokonto ba ya yi, imma dai waɗan da ya taɓa sakawa ciki matsala ne, ko kuma waɗanda yake tunkara a yanzu.
Kan nasa ya sauƙe shafawa, sannan ya kalli side drawer, inda wayarsa da sauran kayan da ke jikinsa a jiyan suke aje. Hannu ya kai ya ɗauki wayarsa da ya buɗeta tun jiya ya ga yanda ta farfashe.
Bai damu da fashewarta ba, ya shiga daddanawa, duk da bata dannuwa da daɗin rai. Lambar Ram ya nemo, wani ma'aikacinsu wanda ya san kan computer, kuma ɗan baiwa wanda yake aikin ɓadda kama.
“Easy...”
Ya amsa gaisuwar da Ram ɗin ke masa bayan ya ɗaga kiran. Ya ɗaga kafaɗarasa a hankali,sannan yace.
“Me ka gano ?”
“Sir na samo location ɗin, sun sauƙa ne a wani gida dake Abacha road”
Muryar Ram ɗin ta faɗa daga cikin wayar. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa, sannan ya kashe wayar ba tare da yace komai ba. Ya kai hannu ya aje wayar tasa, kuma a dai-dai lokacin ne, ƙofar ɗakin ta buɗe.
Abubakar ya fara shigowa, biye da shi wata yarinya ce, mai kama da Abubakar ɗin, sai dai kuma ita yafinyar ta fi Abubakar ɗin hasken fata da kuma kyau. Zuciyarsa ta faɗa masa cewar yarinyar na da kyau, wani irin sihirtaccen kyau, wanda a kallo ɗaya za ka tabbatar da cewa ƙwarai, tana da kyau.
Amma kuma shi ba ya san raini, shi yasa bai ciki shiga sabgar mata ba, musamman wannan da ya gane cewa ita ce ƙanwar Abubakar ɗin da yake yawan masa zancenta. Kansa ya kawar yayin da Abubakar ɗin ya miƙo masa hannu alamun su gaisa. Gaisawar suka yi yana wani basarwa.
Kallo ɗaya Mishal ta masa ta sheƙar, dan ta ga alamun wannan mutumin ɗan raini ne, amma duk da haka sai wani ɓari na cikin zuciyarta wanda yake me hankali ya ce mata; ko ba komai ai abokin Akinta ne, kuma da gani ya girme mata, dan haka ya kamata ta gaida shi. Ciki-ciki kamar me ciwon baki tace.
“Ina kwana...”
Wani abu me kama da igiya ya ɗaure zuciyar Kuliya a ma'ajinta, ya ji kamar zuciyarsa ta gaza, ya ji yana san ya sake kallonta, amma dan kada ta raina shi, sai kai wai ya ƙi ya kalleta ma bare ya amsa gaisuwar.
Abun ya bawa Mishal haushi, duk da ba da ƙarfi ta yi maganar ba ai yaci a ce ya ji gaisuwar, bata iya ɓoye-ɓoye ko riƙe fushi ba, don haka ta kalle shi tace.
“Ba ka ji ina gaida ka ba ne ?!...”
Sai a lokacin ta kalli abinda ba ta lura da shi ba a kallo na farko da ta masa, kammanin fuskarsa, kammace sak irinta Antinta ADAWIYYA!, kenan yayanta ne?, ko ɗan uwanta ne ?.... Haka tunanin ya ci gaba da yawo a cikin kanta.
Ba Kuliya kawai ba, hatta da Abubakar kallonta ya yi, abun ya bashi mamaki, a cikin shekarunsa za'a iya kwasar nata, kuma a bar sauran da zai isa a bawa wani mai hankalin. Amma ko tsoro babu a idonta ta kalleshi take masa magana a tsaye. Idonta da ya kalla ne yasa gabannsa wani irin bugu, wanda sai da ya ji ƙaran bugun zuciyarsa a kunnuwansa. Ƙwayar idonta na da kyau kamar fuskarta, wasu irin olive green colour eyes gareta...
#Labarinsu
#SaiKaska
#TaurariWriter's
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*07*
~~~
*Once you taste a true love, ordinary will never do...*
***
*No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja*
A fusace Anna ta shigo cikin gidan, ta ja ta tsaya tana kallon Siyama dake zaune a falo, ita ta ma manta da Siyaman, wadda ta zo gidan a daren jiya. A yau da safe su na karin kummalo wayar Kuliya ta sameta, hakan yasa ba shiri ta tafi asibitin.
Siyama 'ya ce a wurin ƙanwarta, wadda ta rasu, su biyu ne yaran ƙanwar tata, Siyaman da yayarta Karima. Siyama ta zauna a wurinta tsawon shekaru, kafin zamanta ya koma gidan yayarta Karima, amma duk da haka Siyaman na kawo mata ziyara akai-akai.
Siyama ta miƙe tsaye da sauri, hankali tashe ta na duban Anna, dan Allah ya sani, ta raya abubuwa mabanbanta a cikin ranta, kan abun da ya samu masoyinta, saboda tun da Anna tace mata Kuliya ne ya yi hatsari hankalinta ya tashi, har da kukanta a sanda Annan ta tafi.
“Anna ya jikin nasa ?... Fatan ba wani mummunan ciwo ya ji ba?”
Anna ta kafeta da ido tana kallonta, tun ba yau ba ta riga da sanin cewa Siyama na san Kuliya, amma ita a ganinta kamar hakan ba mai iyu ba ne, ba za ta iya tilasta Kuliya kan ya auri 'yar ƙanwarta ba, duk da tasan cewa idan tace ya yi hakan ko da ba ya so zai yi, amma ba ta san tilasta masa yin abun da baya so.
Bugu da ƙari ma sam Siyama ba ta dace da Kuliya ba, ba wai kyau ne ba ta da shi ba, ba wai ba ta da hali mai kyau ba ne, a'a, sai don sam halayenta ba za du dace da nasa ba, Kuliya ba irin Siyama yake buƙata a matsayin mata ba. Anna ta mata banza, ta cire hijabin jikinta, tare da rataya shi a jikin kujera, kafin ta zauna.
Ganin haka yasa hankalin Siyama ƙara tashi, amma sai ta shiga ƙoƙarin danne hakan, ta yi sauri ta faɗa ɗakinta na gidan, ta shiga banɗaki, ta kulle, tare da sakin kuka, ta jingina da jikin ƙofar bayin, zuciyarta na mata zugi.
Ta sha addu'ar Allah ya cire mata san Kuliya a ranta, don ta san cewa wannan son maso wani take, kuma da ma hausawa sun ce ƙoshin wahala ne. Kuma gashi tana wahalar, saboda Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki.
*Brickhall school, Kaura District, Abuja*
RABI'A POV.
Bayan ta gama aikinta na safiyar yau, sai ta dawo senior section ta zauna, tana ta zuba ido ko za ta ga gilmawar ƙanwarta amma shiru. Har lokacin zuwa makatanar ya wuce, ɗalibai sun riga da sun fara darasa.
Ta miƙe za ta bar wurin, da zaton cewa wata ƙila yau ɗin ma ba za ta zo ba kamar jiya, sai kuma ta ja ta tsaya ganin Mishal ɗin na doso wurin, jakarta goye a bayanta, hannunta na dama riƙe da suit ɗinta, yayin da tsintsiyar hannunta na hagu ke liƙe da plaster.
Ganin plastern ne ya tadawa Rabi hankali, hakan ya sa ta dosheta da sauri. Tun daga nesa Mishal ɗin ma ta ganeta, don haka ta ƙara saurin tafiyarta tana sakar mata murmushi.
“Ƙanwata me ya samu hannunki ?”
Abun da Rabin ta fara tambaya kenan, bayan da ta isa gaban Mishal. Mishal ta ɗaga hannunta na hagu ta kalla, sannan tace.
“Ba wata damuwa fa Sisto, is not big deal, wani ɗan ƙaramin raunine na samu, and na je asibiti an yi treating ɗinsa, so forget about me, what happened to your own hand?”
Ta tambaya a sanda ta ga raunin hannun Rabin. Kuma maganar tata ta tunawa Rabin zagayen halin da take ciki. Fuskar nan wadda ke ɗauke da kammaninta ta tuna, amma sai ta share tace.
“Me too... Babu komai, just small injury”
Mishal ta ci gaba da kallonta tana mamakinta.
“Sis na tambayeki mana”
Rabi'a ta gyaɗa mata kai alamun tana saurarenta.
“Me yasa kike aiki a nan?”
Rabi ta ɗan juya kanta ta kalli inda suke, kamar me neman wani, sai kuma ta juyo ta kalli Mishal ɗin.
“Ƙanwata an fara darasi, ki je ki ɗauki karanatuki, na miki alƙawarin faɗa miki gobe idan Allah ya kaimu...”
Mishal ba ta ƙara cewa komai ba, sai kawai ta gyaɗa mata kai, kafin ta wuce. Rabi ta bi bayanta da kallo tana murmushi.
RAJA POV.
Tare da Rhoda suka fito daga estate ɗin da suka kama gida a ciki, magana suke kan yanda haɗuwarsu da Alhaji Bala za ta kasance a daren yau, don a ɗazu ya kira waya ya sanar da su cewara a yau ne yake so su haɗu.
A jikin wata mota dake fake a ƙofar gate ɗin estate ɗin suka tsaya. Ya na sauraron jawabin Rhoda, yayin da lumaassun idanuwasa ke kallon ɗaliban makaranarar tsallaken estate. BRICKHALL SCHOOL, shi ne sunan makarantar.
Lokacin tashi ya yi, dan ɗaliban tafiya gida suke, wasu a motoci ake ɗaukarsu, wasu kuma a school bus. Wata magana da Rhodabta faɗa ce ta jawo hankalinsa, hakan ya sa ya juyo ya kalleta.
Tunaninsa ya tsaya cak, sakamakon hoton da ya taho masa da fuskarta. Wannan fuskar da ke kwance a kan tasa fuskar, wannan fuskar da ke kwance a ta Aliyu, haka kuma ita ce kwance a ta Momma.
Da sauri ya juya ya kalli inda ya ganta, fitowa take daga cikin makarantar ita ma, sai dai ita ba ta sanye da uniform, yanayin shigarta ba zai bari ya yi tunanin cewa za ta iya zama ɗalibar makaranatar ba, kuma shekarunta ba za su bari a kirata da malama ba. To me take a nan ɗin?.
RABI'A POV.
Tana fitowa daga makarantar ta shiga dube-dube ko za ta ga ƙanwarta, dan tun da safiyar yau da suka haɗu ba su sake haɗuwa ba, gashi har an tashi. A maimakon ta ga Mishal ɗin da take nema, sai idanuwanta suka kallo mata wannan fuskar.
Tsaye a tsallaken makarantar, jingine jikin wata mota, sanye cikin T-shirt da jeans, gefensa kuma wannan matar ce da ta gansu tare a waccan ranar, kuma ita ma kayan jikinta irin nasa ne, ba don ta ga wannan ɗan uwan nasa na jikin hoton na miji ba ne, da za ta ce wannan macen ita ce 'yar biyun tasa. Ba wai dan suna kama ba, sai dan kayan da suke sakawa iri ɗaya. Last time ma da ta gansu kaya iri ɗaya ne a jikinsu, to gashi yau ma haka.
Wani abu da ta lura da shi shi ne, shi ma ɗin kallonta yake, kamar yanda ita ma take kallonsa. Turewa komai ta yi daga cikin kanta, ta soma tunkararsu, don ta samu ta bashi wallet ɗinsa da ya jefar jiya. Don da ma da ita ta taho, tana ta addu'ar Allah yasa suƙara haɗuwa.
Sai ta kasa magana a sanda ta ƙarasa inda suken, daga shi har wannan budurwar me kaya irin nasa sai kallonta suke, tsoro ya kamata, ta rasa abun cewa, sai ta shiga wasa da ƙarshen hijabinta ta ciki.
Raja ya ci gaba da kallonta, a sanda yake ƙara tabbatarwa da kansa wani abu, ko yaya aka yi, tabbas ya haɗa jini da wannan baiwar Allahn, abun ya wuce kama kawai, saboda ya lura da wata tawada a gefen fuskarta, wadda Mommansu ma tana da irinta.
Abun na ɗaure masa kai, shin dabma akwai sauran 'yan uwan Mommansu a duniya ?, amma me yasa basu neme su ba?, ko da yake ai Momman tace masa babanta ne ya koreta daga gidansa. Sai kawai ya ture komai, ya tsai da tunani ɗaya, ƙaddarar da ta haɗashi da wannan yarinyar, wata ƙila ita za ta sada shi da 'yan uwan Mommansu.
“Sannunki!”
Rhoda ta katse shirun da wurin ya ɗauka, kusan shuɗewar muntuna kenan, amma Raja da yarinyar babu wanda ya yi magana, shi ya sa ita ta ari bakinsu ta ci musu albasa.
Rabi'a ta ɗago ta kalleta, sannan bakinta na rawa ta ce.
“Sannu”
“Me kike nema ?”
Rhoda ta tambaya. Kuma kafin yarinyar ta amsa, Raja ya jiya ya kalli Rhodan, ko bai faɗa ba tasan me yake nufi, dan haka sai ta yi shiru, sannan ta juya ta koma cikin estate ɗin.
Ganin yanda yarinyar ta ke ta kame-kame ne yasa shi yi wa Rhodan alama da ta bar wurin, dan bisa ga dukkan alamu, ido ne ya mata yawa. Ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya sannan wannan salihar murya tasa, me sawa mutum ya yarda da shi a tashin farko tace.
“Ya hannunki?”
Rabi ta kalli hannun sannan ta amsa da.
“Ya yi sauƙi”
“Ya ya sunanki?”
Sunanta ?, to me zai yi da sunanta ?, ko de shi ya santa, ita ce ba ta da masaniya game da shi ?, ta haɗiye wani abu sannan tace.
“RABI'A!...”
Wani abu me kama da Allura ya caki Raja a ƙahon zuciya, zuciyar tasa ta shiga rawa a ma'ajinta, wani abu me kama da rauni ya shiga bin jikinsa, an kuma. RABI'A?!, Cewa ta yi sunanta RABI'A!.
Jin ya yi shiru ya sa Rabi ta ɗago da hannunta wanda ke riƙe da wallet ɗin, ta miƙa masa.
“Ga shi, wallet ɗinka ce da ka cillar jiya”
Her voice was innocent, babu wani abu a cikinsa sai nutsuwa da kamun kai. A hankali kammanninta suka shiga rikiɗewa a idonsa, daga Rabi'a yarinya zuwa shekarun Mommansa a sanda ta rasu. Sunansu ɗaya, kammanninsu ɗaya. Sai yake jin kamar Mommance ta dawo. Amma ba wannan ba, shi sam bai lura da babu wallet ɗin tare da shi ba, saboda bai nemeta ba, shi yasa bai kula ba.
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, kafin ya kai hannunsa ya karɓi wallet ɗin. Buɗewa ya yi ya kalli kayan ciki, babu abun da aka ɗauka, komai yana ciki yanda yake, kuma harda kuɗaɗensa ba ta taɓa ba.
“Aiki kike a nan?”
Ya tambaya, a sanda yake zaro kuɗi daga cikin wallet ɗin, Rabi ta ɗan kalleshi kaɗan, wai shi me ke damunsa ne?, yanayinsa kamar me jin bacci, haka ma muryarsa kamar wanda ya yi wani aiki ya gaji. Sai kuma ta yi saurin kauda idonta, ta kalli sauran ɗaliban dake tafiya ta ce.
“Eh...”
“Na fahimta”
Kuma ya fahimta ɗin, abun da tunaninsa ke gaya masa ne ya tabbata, aikatau take a wurin, bai sake cewa komai ba, ya miƙa mata duka kuɗin cikin wallet ɗin da ya fitar.
“Sunana Raja... Ki yi kuɗin mota da wannan, sannan nagode da ajiyar da kika min, AMMATA”
Abubuwa huɗu ne suka haɗu a maganar tasa, sunansa, kuɗin da ya bata, godiyar da ya mata, sannan kuma sunan da ya kirata da shi; AMMATA!.
Ta kalli dumin kuɗin da yake bata, sannan ta kalli fuskarsa, wannan lumsassun idanuwan nasa ne a kanta. Dan haka sai ta girgiza masa kai.
“Ni ma na gode, ka bar shi kai...”
Maganar ta bi iska, sakamakon hannunta na dama da Rajan ya kamo, ya danƙa mata kuɗin...
*
Rabi'a ta shawo kwanar layinsu, dai-dai kwanar da masu kayan siyarwa kan taru. Tsayawa ta yi a kusa da wani mai kifi dake soyawa. A kullum idan ta zo wucewa ta wurin sai ta haɗiyi yawu, saboda, kwaɗayin kifin da ke ranta.
Ita fa da abata kaza gwamma an bata kifi. Gabshi kuma gidansu ba kifin ake ci sosai ba, sun fi cin kaza akan kifin. Hakan ya sa ba sosai take samun damar cin kifin ba.
Hannunta na hagu dake damƙe da kuɗaɗen da Raja ya bata ta ƙara damƙewa, hakan ya tuna mata da yanda suka kwashe da shi a ɗazu.
A ɗazun bayan da ya kamo hannunta, sai ya saka mata kuɗaɗen, sannan ya ninke hannunta kan kuɗin.
Yayin da ita kuma ta saki baki da hanci tana kallonsa, wani abu me kama da ruɗani na kai-komo a cikin kanta.
“Idan na faɗi abu ba'a mun musu... Kin fahimta ?”
Ta shiga gyaɗa masa kai, kuma ba ta bar gyaɗa kan nata ba sai da ya saki hannunta. Ita kuwa ta fahimta, ba ta jin akwai wani wanda zai kaita fahimtar yaren nasa. A kan idonta ya ɗaga mata hannu, sannan ya bar wurin, ya barta da raunanniyar zuciya.
Ta haɗiye wani abu a fili, sannan ta juya zuwa wurin me kifin. Magana ta masa kan ya bata na dubu ɗaya, sannan ta miƙa masa dubu ɗayan.
Me kifi ya saka mata soyyayar karfarsar a takarda, ya ninke ya danƙa mata. Ta kamo hanyar gida ranta fes.
Tana kaiwa gidan ta faɗa ɗakinsu, sai da ta faki idon kowa, ta saka kifin a jakarta. Sannan ta fito tai alwalar sallar la'asar.
Ta yi sallar, kafin ta fito ta shiga yin ayyukanta da ta saba a gidan. Ta yi wanka ta saka kaya baya-baya. Ta dawo ɗaki ta zauna, tana ta dube-dube.
Anti saratu dake kwance a kan katifarta, ta lura da abinda take hakan ya sa tace.
“Rabi lafiya ?”
“Hmm, ina Mama ?”
Anti saratu ta yi murmushi.
“Ta tafi gantalinta, Fatima da Mahmud su na gidan kawu Abubakar. Umma kuma ina jin tana ɗakinta, faɗamin ta samu ne ?”
Ta tambaya ta na tashi zaune... Ran Rabi ƙal, ta tashi daga kan carpet ɗin da take, ta dawo bakin katifar ta zauna.
“Ina mutumin da na faɗa miki cewa ya temakeni jiya ?”
Anti Saratu ta gyaɗa kanta tana tuna zancen da suka yi jiya, sanda ta tambayeta a ina ta ji rauni.
“To ai na faɗa miki cewar ya cillar da wallet ɗinsa... Na ganshi ɗazu, kuma na bashi kayarsa, shi ne ya fitar kuɗin ciki gaba ɗaya ya bani, ya ce na yi kuɗin mota...”
Ta ƙarshe tana miƙa mata kuɗin. Bakin Anti Saratu buɗe ta karɓi kuɗin, ita da kanta ta shiga lissafawa.
“Rabi!... Dubu hamsin da uku ne fa?”
Anti Saratun ta faɗa ido waje, ita kanta Rabin sai da ta yi mamaki, duk da dama tasan kuɗin ba kaɗan ba ne.
“To da huɗu ne ma, tun da kin ga har kifin dubu na siyo”
Ta faɗi ta na miƙewa tsaye, tare sa nufar jakarta, ta fiddo da kifin dake duƙunƙune cikin leda, ta dawo ta zauna kusa da Anti Saratun ta miƙa mata.
“Rabi... Ko dai ya na ciki ne ?”
Ta tambaya a sigar zolaya, Rabi ta yi murmushi tana hango rashin tabbatuwar hakan, don ko da wasa ba ta hango hakkan ba, babu ma ta yanda za ayi hakan ta faru, dan akwai banbanci tsakaninta da shi, wani irin banbancin da take ganin tazararsa kamar, ta Mutum da lokacin mutuwarsa, dan mutum bai san lokacin da zai mutu ba. Haka ita ma ba ta san adadin tazarar dake tsakaninta da shi ba.
Kuma ita ta na ganin wata ƙila shi ma yana mata kallon wadda take kama da shi ne, ko kuma yarinyar dake buƙatar temako, ba ta san shi ba, ba ta san ya rayuwarsa take ba, amma tana da tabbaci kan shi ba sa'anta ba ne, akwai tazara me tarin yawa tsakaninta da shi.
Abun da ba ta sani ba shi ne, wannaan tazarar da take gani ta kusa zama kusa, wata iriyar kusa da za ta bata mugun mamaki. Amma kuma kafin faruwar kusan, sai wasu ƙaddarori sun gifta a tskani.
Ita ta buɗe musu ledar kifin,suka ci tare, tana tambayar Anti Saratun; kan yaya za su yi da kuɗin?.
“Abun da zai faru kawai zan aje miki su a wurina, idan kina buƙata sai kimin magana, ni kuma na baki...”
Rabi ta yi dariya tana kai wani kifin bakinta, yau tana cikin farin ciki, wanda ba za ta iya cewa ga dalilinsa ba.
RAJA POV.
Tsaye yake a gaban mutumin da ke amsa sunan ALHAJI BALA. Yayin da shi ma Alhaji Balan ke kallonsa. Fuskar Alhaji Balan na ɗauke da murmushin alfahari, dan sosai yake alfahari da Raja, though wannan shi ne karo na farko da suka fara haɗuwa, amma ayyukan da yake dominsa suna isowa kunnuwansa.
Yayin da shi Rajan yake kallonsa da wani gutun murmushi, salihar fuskarsa na wani irin haske da ba ka ce na miye ba, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Alhaji Bala ƙasa-ƙasa. Daga shi sai Rabbil izzati suka san abinda yake tsarawa a cikin kansa.
Suna tsaye ne a katafaren falon gidan Alhaji Balan, wanda ke ɗauke da maka-makan set ɗin kayan da kallo ɗaya za ka musu ka shaida tsadarsu.
Rajan na sanye cikin wani green khaki trouser, sai baƙar crew neck sweater, ƙafafunsa sanye cikin canvas baƙaƙe.
Alhj Bala ya ɗaga hannunsa na dama, tare da bubbuga

Please Login or Register in order to submit comment