Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya na shirin siyan kayan furnitures Kawu Abdullah ya dakatar da shi da faɗin su ne za su yiwa 'yarsu kayan ɗaki, kuma hakan aka yi, don a jiya aka cika gidan da kayan furnitures da kuma na kitchen, da ma duk wani abu na buƙatar gida.
Kuma hatta da sadaki Baba ne ya biya masa, shi kansa ba zai iya misalta kalar farin cikin da yake ciki ba, babu abun da zai ce sai godewa Allah, domin kuwa ita ma Rhoda ya na gab da aurar da ita, saboda sun riga da sun ɗinke da Zakar, hujjojjin dake hannunsa kawai ya rage ya miƙa, da zarar ya miƙa su za'a kama Alhaji Bala, kuma kamar yanda suka yi da Rhoda daga zarar an kama Alhaji Bala za ta musulunta.
Sannan sun yi magana da Kawu Abdullah kan daga zarar Rhoda ta musulunta za ayi aurensu da Zakar ɗin. Don haka farin cikin da yake ciki ba me misaltuwa ba ne, baki ya yi kaɗan ya faɗeshi, sai dai kawai ya ci gaba da godewa Allah.
RABI'A POV.
Daga ɓangaren Ammatan Raja kuwa, duma suna can nasu ɗakin ana wa amaren kwalliya, cikin wata ɗayan ba ƙaramar rama ta yi ba, don har mutanen gidan sun fara zargin ko auren ne ba ta so, amma ta nuna musu ba haka ba ne. A can ƙarƙashin zuciyarta kuwa tunanninnika ne birgit ta ko ina, ita kanta a yanzu ba za ta iya cewa ga takamemen abun da yake damunta ba, amma ta san cewa ba ta jin daɗi, duniyar ba ta mata daɗi sam.
Don har zargin wannan auren take, tun bayan rabuwarta da Zaid a Abuja ba su ƙara magana ba, hasali ma rabonta da shi tun ranan da za su islamiyya ta hangeshi shi da su Yunus suna hira, bayan nan ba ta ƙara saka shi a idonta ba, idan za ta ce ga abun da ya ramar da ita to har da kewarsa ma za ta iya shigowa ciki, ta na son ganinsa, ko da faɗa ne ma su ɗan yi, amma wannan zaman nesan ba ya mata daɗi.
“Kai! Amma fa kin yi kyau Rabi'a”
Cewar Rhoda, a sanda aka gama ɗaura mata ɗankwalin farin leshin da suka yi ankonsa ita da Nafisa, kanta ta kalla a mudubi. Tabbas ta yi kyau, dan hatta da wannan tabon yankan na gefe fuskarta an ɓoye shi da hoda, kwalliyar ta bal'in hawa fuskarta. Hannunta ta kai kan ƙashin wuyan da ta yi a kwanankin, ta ɗan ja guntin tsaki ta na jan wayarta.
“Kai ku yi sauri ku fito ga masu ɗaukar hoto nan sun zo”
Cewar Jidda, a yayin da take shigowa ɗakin da gudunta, ta ci uwar kwalliya kai kace ita ma amaryar ce.
“Dan Allah Ummi ki yi sauri ki gama min”
Momi ta faɗa a sigar magiya, ta na kallon me kwalliyar.
“To”
Me kwalliya ta amsa, a gefe guda kuma Rhoda da Rabi ne suke ɗaukar hoto a waya, daga can kuma Kairiyya ce takewa Nafisa da Kulsum hoto a waya.
Haka suka gama shiriritarsu kafin suka fita. Dangi da jama'ar da aka gayyata haka suka riƙa zuba musu ruwan hotuna ana ta Allah sanya da alkairi.
Da yamma kuwa walima aka haɗa musu, amma ba su yi dinner ba, dan Baba yace ba za'a yi ba, duk da suna son yi haka suka haƙura saboda babu yanda za su yi.
*10:30 PM.*
“Ke wai ina za ki kai ni ne?”
Rabi ta tambaya tana kallon Jidda dake ta janta tun ɗazu, tafe suke a harabar gidan, har ta fara bacci saboda gajiyar da ta yi Jiddan ta taso ta tace mata wai ta zo ta rakata, maganar duniya ta yi amma Jiddan ta ƙi ta amsata. Har ta gaji ta rabu da Jiddan.
Mamaki ne ya kamata a sanda ta ga sun nufi ɓangaren samarin gidan, kuma kafin ta gano abun da ke shirin faruwa, har Jiddan ta buɗe ƙofar wani ɗaki, ta turata ciki, sannan ta ja yo ƙofar ta kulle. Ba tare da ta iya tsayawa ta ga abun da ke cikin ɗakin ba, ta yi saurin juyawa tana bubbuga ƙofar, tare da faɗin.
“Jidda!, ke Jidda! Wai miye ne hakan?”
Daga waje ta ji muryar Jidda na faɗin.
“Tsakar dare mijinki ya kira ni yace ya na san ganinki, shi ya sa na kawo masa ke!”
Dammm!, gabanta ya buga, hakan ya sa ta juya da sauri, ta shiga ƙarewa ɗakin kallo, kuma idonta bai tashi sauƙa a ko ina ba sai a kan Raja dake zaune daga can gefen gadon ɗakin, waya riƙe a hannunsa, ya kafeta da shanyayyun idanuwansa. Da ƙyar ta iya haɗiyewa wani yawu me ɗaci. A sanda ta ga Zaid ɗin ya miƙe ya na nufota.
Kanta ta kawar gefe tana ƙara matse jikinta a jikin ƙofar, banda lugudan bugu babu abun da zuciyarta ke yi, ƙamshin turarensa da ya cika hancinta ya sanar mata da isowarsa gabanta.
Zaid ya saki wani murmushi ya na ɗaga hannunsa tare da dafa shi jikin ƙofar, ya mata rumfa a tsakiyarsa. Rabi ta ji kamar numfashinta ba ya fita da kyau, kamar ma ba ta shaƙar isaka ne. Kuma hakan be isa ba sai da Zaid ya kai hannunsa ya kamo fuskarta, hakan ya sa ta lumshe idonta ta kuma buɗewa, saboda ji ta yi kamar ya ɗora mata ƙanƙare a kan fuskarta, sakamakon sanyin da ta ke ji na rata jijiyon jikinta, ba shiri ta rintse idanuwanta gam-gam.
“Ammatan Raja!”
Amon muryarsa da kuma sunan suka sa ta ware idanunwata tar, ya ilahi!, ashe haka ta yi kewar jin sunan nata daga bakinsa?, ashe ta yi kewar wannan muryar tasa?, ashe shi kansa ta yi kewar ganinsa?, duk ba ta fahimci hakan ba sai yau, sai yau da take tsaye gabansa, a tsakiyar hannayensa.
“Ba ki yi kewata ba?”
Zaid ya tambaya ya na motsa hannunsa a gefe fuskarta, Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, a hankali ta juyo da kanta ta kalli fuskarsa wadda ta kusa haɗewa da tata, hatta da ɗumin numfashinsa ta na jin sauƙarsa a kan fuskarta, tazarar tsakanin hancinta da nasa bata da wani yawa, hatta da jikunansu sun kusa haɗewa. Ba ta san me ya sa ba, amma ta ga yanda idanuwansa suka ƙara lumshewa fiye da yadda ta sansu a da. Sai de ba za ta bari abun da take ji ya rinjayi kanta ba, ba za ta bari wannan salihar fuskar tasa ta rinjayi tunaninta ba, ita ta san waye shi, ta san ainahin gaskiyarsa. Don haka ta sa hannayenta biyu, ta ture shi zuwa baya.
Sannan ta juya ta shiga fafutukar buɗe ƙofar. Zaid ya tsaya a bayanta kawai ya na kallonta. Babu yanda Rabi ba ta yi ba kan ƙofar ta buɗe ama ta ƙi buɗuwa, hakan ya sa ta juyo ta kalli Zaid dake tsaye a bayanta ya na mata murmushi.
“Ka buɗe min ƙofa,ina san na fita”
Kafaɗunsa duka ya ɗaga mata alamun shi fa babu ruwansa.
“Magana kawai nake so mu yi, da zarar mun gama, zan barki ki koma”
Muryarsa ta faɗa bayan wani lokaci, Rabi da ta ci gaba da kokawar buɗe ƙofar ta juyo ta kalleshi.
“Me kake buƙata?”
Ta tambaya idonta cikin nasa, Raja ya kuma yin murmushi ya na isowa gareta, hannunta na dama ya kama ya shiga janta, duk yadda ta kai da tirjewa sai da ya sadata da bakin gadon ɗakin. Ya zauna a bakin gadon, sannan ta ƙarfi ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Rabi'a ta shiga mutsu-mutsun ƙwacewa, amma fur Raja ya hanata.
“Idan har ba ki tsaya mun yi magana ba, ba zan barki ki fita ba, sai de ki kwana a nan”
Jin maganar tasa ya sa ta tsaya da abun da take, Zaid ya saka hannunsa ɗaya ya kama ƙugunta baya, jin hakan ya sa Rabi jan wata iska, idanuwansa ta ci gaba da kalla, kammar tana shirin gano abun da yake shirin furtawa a cikinsu. Mustu-mutsun ta ci gaba da yi hakan yasa yace.
“Sshhhhh!, ki dena”
Muryarsa ta fito a hankanli cikin duhun daren, kuma amon muryar tasa ne ya haddasarwa Rabi jin kasala, ba ta san lokacin da ta saka hannayenta ta ƙanƙame gaban rigarsa ba.
“Good girl”
Ya faɗi a setin kunnenta, jikin Rabi ya shiga rawa, wani abu ya shiga bi ta kan zuciyarta tun daga samanta har zuwa ƙasa.
“Wani abu nake san nuna miki”
Jin hakan ya sa ta yi saurin kallon fuskarsa. Wayarsa ta ga ya kunna, don haka ta kalli fuskar wayar, tar take iya ganin fuskar Habiba cikin wayar, sannan kuma kar sautin muryar Habiban yake shiga cikin kunnuwanta.
“Ke ce wadda aka cutar, dan haka dole sai da izininki maganar za ta iya zuwa gaba, shi ya sa na buƙaci da na nuna miki. Shin kina san ki shigar da ƙara a kanta?”
Muryarsa ta faɗa bayan da vedion ya kai ƙarshe, Rabi da idanuwanta suke a ƙafe ta kalli fuskarsa, abun da Habiban ta faɗi sam bai ba ta mamaki ba, tun ba yau ba ta san cewa Habiba ce a bayan ko wani abu dake faruwa da su, amma abun da ya ba ta mamakin shi ne, yanda Habiban tace ita silar yi mata fyaɗe, ko da yake ai abun ba na mamaki ba ne, tun da har Yaya ya ƙita ita kuwa me zai ba ta mamaki a duniyar nan.
Jin ta yi shiru ya sa Zaid ya matse hannunsa dake kan ƙugunta ta baya, Rabi'a ta zabura tana ƙara iyowa cikin jikinsa sosai.
“Kin yi shiru?”
“Ba na buƙatar shigar da wani ƙara! A saketa kawai, ta ci darajar Anti Saratu, be side ai ba ma ita ya kamata a kama ba, ga babban me laifi a nan!”
Zaid ya yi murmushi, duk kuwa da ya san cewa hakan za ta iya faruwa. Ita har wa yau a wurinta shi me laifi ne.
“Kar ki damu, za su kama ni ai, dubuna ce ba ta cika ba. Kuma ko sun zo kama ni zan ce su bari sai na yi ajiya tukkuna, sai su kama ni”
Girar Rabi ta haɗe cike da mamaki.
“Ajiya? A ina?”
Hannunsa ya ɗaga zai taɓa fuskarta, amma sai ta janye fuskar tata, sai ya yi murmushi.
“Well! Yanzu ba za ki gane karatun ba, sai nan da wani lokacin... Kuma miye na kawar da fuskar? A zaune kike a cinyata fa!...”
Tunowa da hakan ya sa ta zabura za ta miƙe, amma sai Zaid ya sa duka ƙarfinsa ya dawo da ita, ita kuma sai ta tura shi, kasancewar ya na riƙe da ita sai ya yi baya tare a ita, bayansa ya faɗa kan gadon, yayin da ita kuma take kwance a ƙirjinsa. Fuskarta yake kallo a hankali, yayin da ita ma take kallon tasa fuskar. Hannunsa na dama ya ɗago ya na kama fuskarta, kafin a hankali ya matso da fuskarsa, ya karkatar da ita gefe kaɗan, leɓɓansa masu ɗumi suka sauƙa a kan nata, ba shiri Rabi ta zaro idanuwanta waje gaba ɗaya, ta saka hannunta ta cukukuye gaban rigarsa, ta ƙanƙame yatsun ƙafarta da suka ɗaga sama saboda kwanciyar da suka yi, ta buɗe bakinta ta na shirin yin magana Zaid ya saka harshensa a cikin bakinta, shi kenan kuma!. Ɗan ragowar hankalin nata da ya rage Raja ya ɓarar mata da shi, ya ɗauketa daga wannan duniyar da muke ciki ya kaita wata can da nisa. Ba ta gane komai, ba kuma ta jin komai sai fitar nunmfashinsa a kan fuskarta, babu abun da take gani sai idanuwansa kusa sosai da nata. Kanta ya cilla zuwa wata nahiyar, ba ta fahimtar komai sai Raja da abin da yake mata a yanzu.
“Rabi'a!”
Jidda ta kuma kiranta a karo na barkatai, bayan da suka baro wurin Zaid, amma Rabi fur taƙi amsa mata, don haushinta take ji, duk abun da ya sameta a yanzu ita ta jawo mata, ita ta kawota wurin har Zaid ya yi amfani da damar hakan ya sumbaceta cikin wannan daren. Ƙwafa ta yi a ranta tana goge bakinta da hannunta, ita ji take ma kamar har yanzu leɓen nasa na kan nata ne, ji take kamar har yanzu harshensa na cikin bakinta, sarƙafe da nata harshen, shi take kamar har yanzu hannunsa na kan ƙugunta ne, ji take kamar har yanzu tana kwance a kan jikinsa ne. Ƙafa ta sa ta yi fatali da wannan tunanin da ya addabeta, a sanda suka iso ɗakinsu. Bargo ta ɗaga sannan ta kwanta kusa da Rhoda wadda ke kwance a kan gadonta ta na sharɓar bacci.
A kai a kai take jan tsaki har da ƙwafa, Jidda na jinta amma ta yi luƙus tana mata dariyar mugunta.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*23*
~~~
*The one thing that holds more power than ‘I love you’, is ‘I got you’...*
***
*No.86, Garki 2, Abuja...*
*09:00 PM.*
RABI POV.
A hankali ta zura ƙafarta ta dama cikin kitchen ɗin gidan, sai kuma ta tsaya ta na kallon irin yawan kayan dake cikin falon, sai da ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, kafin ta sako ƙafarta ta hagu ciki. Kamar sauran sassan gidan, shi ma kitchen ɗin ya haɗu.
A jiya danginta, wato 'yan uwan mahaifiyarta suka rakota har ɗakin mijinta, kuma a nan suka kwana, ba su tafi ba sai ɗazu da yamma, sun tafi sun barta cikin wannan gidan, bayan da suka mata nasihu kala-kala, sai de kuma ita ba ta jin ko nasiha ɗaya cikin nasihunsu zai yi aiki, don kuwa ba ta jin za su yi wani dogon zama ita da Zaid. Kowa a familynsu burinsa kawai ayi auren, to gashi an yi, ita kuma za ta san yanda za ta yi dan ya saketa, da ta ci gaba da zama da makashi, gwara ta koma can Haɗejian ta ci gaba da zama, . Duk da tasan cewa zuciyarta ba za ta so hakan ba, amma za ta haƙurƙurtar da ita, ta faɗa mata cewar zamanta da Zaid ba zai haifar da ɗa me ido ba.
Motsi ta ji a bayanta a lokacin da ta kai tsakiyar kitchen ɗin, da sauri ta juya ta na kallon bakin ƙofar kitchen ɗin, ganin Zaid tsaye a wurin kuma jingine da jikin ƙofa ya sa ta shiga dube-dube a kitchen ɗin, can ta hango set din wuƙa, ba tare da sake wata shawara da zuciyarta ba, ta rarumo wuƙa ɗaya daga cikin set ɗin, ta nuna shi da ita ido waje.
“Kada ka shigo nan!”
Raja na kallonta ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, hannyensa harɗe a ƙirjinsa, sai murmushi yake zabgawa, don shi a yanzu babu wani abu dake damun ransa, komai nasa ya hau seti, rayuwar ma sai ya ga kamar tana sauri ne. Wai yau Ammatansa ce a cikin gidansa, matsayin matarsa ta aure, halalinsa!. Duk barazanar da za ta masa ba za ta dame shi ba, don shi bai fara santa don ya bari ba, bai aureta don ya saketa ba, ya aureta ne don ya zauna da ita har zuwa ɗan lokacin da Allah ya ɗiba masa cikin duniya. Hannayensa ya ware, tare da zuba su cikin aljihun wandonsa, ya soma takawa zuwa gabanta.
Ganin hakan ya ƙarawa Rabi ƙaimi wurin ci gaba da cuna masa wuƙar a setinsa, sai de kuma ko gezau ba ta ga ya na yi ba, nufota yake gadan-gadan, har ya iso gabanta ba ta bar nuna shi da wuƙar ba, sai zare masa ido take kamar za su faɗo, kuma bai dena tahowa gareta ba har saida ya riski wuƙar, har tana taɓa jikinsa.
Da sauri Rabi ta janye wuƙar zuwa gefe, ba shiri ta cillar da ita can gefe ta na ƙara matsawa baya, shi ma kuma be fasa ba, binta yake ta na ja da baya, har sai da Rabi ta kai jikin wata cabinet.
“Ai ni na san ba za ki iya cutar da ni ba”
Ya faɗa yana kafeta da idanuwansa. Rabi'a ta haɗiye wani abu ta na kawar da kanta gefe, kuma ita kanta ta san gaskiya ya faɗa, ba za ta iya cutar da shi ba sam, ko me zai mata ita ba za ta iya masa koman ba. Amma saboda ƙarfin hali irin nata sai cewa ta yi:
“Me zai hana ba zan cutar da kai ba. Idan ta kama har kasheka ma sai na yi...”
Tana iya jin sautin murmushinsa. Raja ya fitar da duka hannayensa daga cikin aljihu, sannan ya mata rumfa a tsakiyarsu, ya ƙara matsar da fuskarsa kusa da tata dake kallon gefe.
“Ba za ki iya ko da cire silin gashi ɗaya daga jikina ba. Saboda... Kina... Sona, ki yarda kawai. Ko ki yarda ko karki yarda Ammatan Raja... You love Raja... Oh i mean Zaid... Yaya Zaid!”
Ba shiri Rabi'a ta ƙara ƙanƙame jikinta wuri guda, ta rintse idonta gam-gam, ta shiga kokawa da numfashinta dake shirin fita gaba ɗaya, hannunta dake kan rigar jikinta ta damƙeshi tare da rigar.
“You see... Magana ma kawai na miki ta sa kika shiga cikin wannan halin. Ina ga idan na...”
Ba tare da ya ƙarashe ba ya sauƙe hannunsa na dama, sannan ha sako shi ta bayanta, yana turota zuwa jikinsa, hakan ya sa Rabi ƙara ƙanƙame idonta, dan haɗuwar jikunansu sai ya sa ta ji kamar wani irin electric shock ne ya faru tsakaninsu. Kuma hakan be isheshi ya gama wargaza tunaninta ba, sai da ya sauƙe ɗayan hannun nasa ya kama gefen fuskarta da shi. Ya na ƙara kusanta fuskarsa da tata. Allah ne ya ara mata ƙarfin da ta yi amfani da shi wurin turashi zuwa baya.
“Dan Allah ka rabu da ni. Ni ba na buƙatarka a rayuwata, tun ba yau ba na faɗa maka haɗuwata da kai kuskure ne, ka ƙyaleni Zaid, dan Allah ka ƙyaleni!”
Ta ƙarashe hawaye na sauƙo mata.
“Ni kuma ina buƙatarki a rayuwata, ina sonki. Ina.... Matuƙar sonki, dan Allah ki fahimta”
Rabi'a ta share hawayen idonta, sannan a dake tace.
“A haka kake so na? Ni fa ba kamar sauran mata ba ce!. Ina da banbanci da su. Maza biyar... Biyar ne suka haikemin... A haka kake sona?... To ka sani ni ba ni da wannan martabar ta 'ya mace... Ban mallaki komai ba sai raina, idan ka ce za ka ci gaba da kusanta tata irin haka ina me tabbatar maka da cewar ran nawa ma zan rasa shi nan ba da jimawa ba!” Ta faɗi hakan ne don ta tunzurashi ya rabu da ita, kuma ta na ganin kamar ya manta abun da ya faru da ita ne, don da ace ya na tunawa da ba zai aureta a yadda take ba, shi ya sa ta yi ƙoƙarin tunatar da shi.
Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na shafa sumar kansa, me take so yace ne? Wata hanya zai bi don ya ganar da ita kalar san da yake mata?, da wani yare take so ya yi magana dan ta fahimci kalar son da yake mata?, tun kafin tsautsayin nan ya auku yake santa, yanzu kuma kawai dan ƙaddara ta sameta sai ya rabu da ita?, wannan ba me iyuwa ba ne, santa a cikin jikinsa yake, ba ya jin zai iya rabuwa da santa ko me za ta zama a duniya, kuma ya na fatan bugu na ƙarshe da zuciyarsa za ta yi ya kasance da sunanta ne. Lips ɗinsa ya lasa ya na sakin sumar kansa da ya riƙe.
“Ammata, ni...”
Ya nuna kansa, sannan ya ci gaba.
“Ba dan komai nake sanki ba. Ba na sanki dan kina da wani abu. Bana sanki dan kin mallaki wani abu. Haka kuma ba na sanki dan ina buƙatar ki wadata ni da wani abu. Zuciyarki kawai nake buƙata Adawiyya!. Da zarar kin mallakamin ita zan nuna miki so. Zan nuna miki yanda ake so. Zan koyar dake so. Zan nuna miki yanda ƙaryyayar zuciya, kan haɗe ta dawo me kyau fiye da sabuwa. Zan tabbatar da na ƙawata duniyarki Ammata. Ko da sau ɗaya ne. Dan Allah, ki gwada ni... Ki gwada mallakamin zuciyarki ki ga kamun ludayina. Na roƙeki, Please!”
Rabi ta buɗe idanunwata dake a lumshe ƙwalla wata na bin wata. Idon nata ta sauƙe a kan Raja dake durƙushe kan gwiwoyinsa a gabanta, ya na roƙonta abun da za ta iya mallaka masa cikin sauƙi. Ya Allah! Me ya sa wai ita nata ƙaddarorin basu da sauƙi ne?. Ta san da cewa soyyayar Zaid na ɗaya daga cikin ƙaddarorinta na duniya, wannan haka yake, kuma a rubuce yake.
Durƙusawar ita ma ta yi a gabansa ta na kallon idanuwansa.
“Raj ni ba ni da wani abu da zan baka. Fanko!.... Fanko ce ni, na zama wata kala, saboda kwai ƙaddara ta faɗa min. Ƙaddarar da ba ni na tsrawa kaina ba, ƙaddara ce fa Raj, ƙaddara ce, amma haka Yaya ya guje ni saboda wannan ƙaddarar da ban jarabci kaina da ita ba. kuma na san ko ba Yaya ba babu wanda zai iya aurena a yadda nake, kai ma kawai de ka dage ne. Amma ni da kai ba mu dace ba...”
Kafin ta kai ƙarshen kalaminta, Zaid ya saka hannyensa duka biyu ya janyota cikin jikinsa, tare da haɗe bakinsa da nata, ƙwalla me ɗumi na sauƙa daga idon ko wannensu, Rabi'a ta kama bayan rigarsa gam, dan ji take kamar za ta zame daga hannayensa, kamar ƙasa ce za ta tsage biyu, ita kuma ta rufta ciki.
A hankali Zaid ya saki bakinta ya na rungumeta, tare da shafa sumar kanta dake cikin ɗankwali.
“I adore you Adawiyya, i na sanki ko da ba kya gani. Ina sanki ko da ba ki da ƙafafu. Ina sanki ko da ba ki da hannaye. Adawiyya ko da mutuwa kika yi ba zan dena sanki ba... I love all of you!”
Kalamansa ba ƙaramin tasiri suka yi a zuciyar Rabi ba, don tsabar tasirin da suka yi, Rabi'a ba ta san sanda ta ɗago da hannyenta ta ɗora su a kan bayan Zaid ba, ta na ƙara ƙanƙameshi a cikin jikinta, tare da ƙarawa kukanta sauti.
Sai de kuma cikin sakan ɗaya... Biyu... Uku...
A cikin na ukun ta yi sauri ta tureshi, saboda wannan fuskar tasa da ta hango, fuskarsa a lokacin da ya harbi wani bawan Allah. Da sauri ta miƙe da gudu ta bar kitchen ɗin. Ɗakin da yake a matsayin nata ta faɗa tana bankowa ƙofar. Tare da jingina a jikin ƙofa, ta silale ƙasa tana fashewa da kukan da ba ta san daga ina yake fitowa ba, ƙafafunta ta takure a jikinta tana sunkuyar da kanta cikin kuka. Ita da Allah zai ɗau ranta ma da sai abun ya fi mata sauƙi, ƙaddarorinta suna da tsauri, ga su kuma a laye, wata kan wata.
Har ta bar kitchen ɗin kan Raja a sunkuye yake, da ƙyar ya samu ya ja da baya zuwa jikin cabinet, ya jingina da ita, sai sauƙe numfashi yake da sauri-sauri. Zai iya cewa a karo na farko kenan a rayuwarsa da ya yi nadamar shiga aikin DSS, wai me ya sa?, me ya sa komai nasa akan soyyayar Adawiyya yake da wahala haka?, ya tabbatar ba dan wannan aikin ba, da ba za ta ganshi ya harbi wani ba, da ba za ta ƙishi tana masa kallon makashi kamar haka ba. Duk sai ma ya ji ya tsani rayuwar, ji yake kamar kansa na tiriri. Cike da fusata ya ɗaga hannunsa na dama ya na dukan cabinet din dake bayansa. Ya gaji, dole ne ya ƙarƙare aikin nan cikin wannan satin, dole ya kawo ƙarshen komai.
*
Rabi'a na zaune a falo tana kallo. Jin wani sauti me kama da ƙaran kiran waya ya sa ta juyo ta kalli ƙofar ɗakin Zaid. Mamaki ne ya kamata a sanda ta fahimci cewa tabbas, sautin kiran waya ne ke tashi daga ɗakin, to be fita ba ne ko kuwa?, ita de ta san sassafe ya fice daga gidan, amma kuma yanzu ga ƙaran kiran waya ta na ji, duk yadda aka yi manta wayar ya yi.
Bakinta ta taɓe tare da juyowa ta ci gaba da kallonta, jin sautin kiran wayar na ƙara tashi ya sa ta ƙara waigowa ta kalli ƙofar ɗakin nasa. Ko de wani abu ne yake faru? Ta tambayi kanta a sanda take miƙewa. Ɗakin ta nufa. Sai de bisa ga mamakinta ba ta ga wani abu mekama da waya a ɗakin ba.
Har ta juya za ta fita, ƙaran kiran wayar ya ƙara dakatar da ita, hakan ya sa ta juyo ta shiga bin inda sautin ke fita. Can cikin loka ta ji sautin, don haka ta buɗe lokar, sai ta yi arba

Please Login or Register in order to submit comment