Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali idonta ya shiga lumshewa, bakinta na motsawa, ta na faɗar wasu kalamai da shi bai ma san ma'anarsu ba.
Ganin kamar shirmen nata ya ƙare ne ya sa shi miƙewa ya ɗauketa duka, sannan ya yi ɗakinta da ita, a kan gadonta ya kwantar da ita, sannan ya lulluɓeta ya fita.
Ɗakinsa ya koma ya yi wanka, ya sauya kayansa zuwa wanda ya saba sakawa na zaman gida a irin wannan lokacin, wato baƙin sweat trouser da kuma baƙar T-shirt.
Kitchen ya fara dubawa ko zai samu abinci, ya tarar da ta aje masa wanda zai iya ci, za ma ya yi ya na ci ya na murmushi a kai a kai, don shirmen nata ba ƙaramin nishaɗi ya bashi ba.
Bayan ya kammala cin abincin ya ɗan taɓa aiki a system ɗinsa, kafin ya fara jin bacci, system ɗin ya rufe, sannan ya nufi ɗakinsa dan ya kwanta, sai wata zuciyar ta raya masa da me zai hana ya je ya kwanta a ɗakinta, wata ƙila ta buƙace shi ko da cikin dare ne.
Ba tare da wani tunani ba ya nufi ɗakin nata, sai ya tarar da ta hargitsa kwanciyar da ya mata ɗazu, ba kamar. Murmushi ya yi ya na gyara mata kwanciya, sannan ya kwanta a gefenta ya na kashe musu wuta.
Janta ya yi jikinsa, sannan ya lumshe idonsa don yin bacci, ba jimawa kuwa baccin ya ɗauke shi, don a gajiye yake, amma kuma baccin nasa bai yi minti goma ba ya farka, saboda wani duka da Mishal ta masa da ƙafarta, sam ya manta da ba ta iya kwanciya ba.
Ƙafafuwan nata ya gyara mata, amma da aka jima sai ta ƙara lafta masa ƙafarta, tun ta na yi ya na gyara mata, har ya gaji ya rabu da ita, haka daren ya ƙare ta na ta bugunsa da ƙafarta.
Da asuba ya farka, hakan ya sa ya tashi ya koma ɗakinsa, ya ɗan watsa ruwa kaɗan, sannan ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci, har ya dawo ba ta farka ba, hakan ya sa ya mata tashin duniyar nan amma ko motsi ba ta yi ba, har ruwa ya watsa mata amma kamar an mintsin kakkausa, sai ya ƙyaleta ya koma ya kwanta a gefenta.
Wajejen ƙarfe 09:00 dai-dai wayarsa ta yi ringing.
Cikin bacci ya ji ƙarar, hakan ya sa ya buɗe idonsa, hannunsa ya kai ya ɗauki wayar, sunan 'Sharon' ya ga ya na yawo a kan screen ɗin, sai ya ɗaga ya na wani cin magani kamar ta na gabansa.
“Lafiya yau ka makara?”
Sharon ta tambaya bayan sun gaisa, sai da ya juya ya kalli Mishal dake baccinta tsakani da Allah, hankalinta kwance, kamar tsumma a randa, sannan yace.
“Hafsat ce ba ta jin daɗi, zan kaita asibiti”
Sharon ta ƙunshe dariyarta sannan ta ce.
“Allah ya ba ta lafiya, sai yaushe kenan?”
“Gobe”
Ya bata amsa a taƙaice.
“Sai goben”
Ya na gama sauraren hakan ya katse kiran sannan ya aje wayar a inda ya ɗauketa.
*
“Yau Sir ya na more amarci... Dan haka ba zai fito ba”
Cewar Sharon ta na kallon su Symon, wanɗan da suka zo suka sakata a gaba kan ta kira Kiloya ta ji me ya sa yau bai zo ba. Dariya suka kwashe da ita, daga nan kuma sai aka shiga hira a kan Kuliya da Mishal.
*
Ya kamata ace zuwa yanzu ta tashi, Kuliya ya faɗi a ransa, ya na kaiwa hannunsa tare da ɗan tattaɓa fuskarta.
“Ummmm!”
Ta faɗi cikin muryar bacci.
“Hafsat”
Ya kira sunan a hankali ya na kallonta, yayin da yake kwance a gefenta.
“Ummmmmm!”
“Ki tashi gari ya waye”
Idonta ta buɗe a kansa, sannan ta ƙara lumshewa, ta kuma buɗewa, kuma a lokacin ne ta gano abun da ke faruwa, Kuliya ne kwance a gefenta, sannan a kan gadonta.
Ba shiri ta tashi zaune ta na waige-waige, kamar me neman wani abun, ita dai tasan bayan ta yi sallar isha, ta zauna a falo ta ci abinci, sannan ta ɗora da magungunan da ya aiko mata a jiyan, maganin murar ma da yawa ta sha, wai duk don ya mata magani da wuri, saboda ita ba ta san murar nan, kasancewar idan ta na yi takura mata take yi. Kuma bayan hakan ita ba ta tuna komai ba.
Kuliya ya miƙe zaune ya na kallonta, abun da ta yi jiya ya dawo masa sabo, hakan ya sa shi murmusawa a fili.
“Kin tashi lafiya?”
Kallonsa Mishl ta yi a firgice, ta na san ta tuna wani abu da ta yi a daren jiya, amma ta kasa, ta kasa tuna komai, dole akwai wani abu da yake ba dai-dai ba.
“Har rana ta take ba ki yi sallah ba, ki je ki yi sallah”
A hautsine Mishal ta sauƙa daga kan gadon ta faɗa banɗaki da gudu, Kuliya ya yi murmushi ya na sauƙa daga kan gadon ya fita daga ɗakin.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*18*
~~~
*It's not hard to make someone feel loved.*
***
*No.181, Guzape, Abuja*
MISHAL POV.
A gurguje take aikin haɗa breakfast, don tasan yau ba ƙaramar makara ta yi ba, saboda ta na da tabbacin ma ko makaranta ba zuwa za ta yi ba, sai dai kuma akwai abun da ke ɗaure mata kai, me Kuliya yake ɗazu a shimfiɗarta, kuma ita da ta kwanta a falo me ya kaita ɗaki?, sannan shi ma me ya sa bai fita aiki ba yau?, abubuwan sun ɗaure mata kai.
Ga kuma kan nata dake mata ɗan banzan ciwo, sai jikinta da take ji a mace, haka ta yi sauri ta gama haɗa sandwich da kuma jallof ɗin indomie, tare da hot chocolate.
Ta kwashe komai ta jera a kan danning, sannan ta koma kitchen ɗin ta shiga wanke kayan da ta ɓata. Har ta gama ba ta ga Kuliya ya fito ba, sai ta shiga gyara gidan, kuma gyaran gidan ma har ta kammala bai fito ba, abun ya so ba ta mamaki, ta san ko a da da ba ta girki da shi ya na fitowa da wuri ya ci abinci, kuma ta hakan ne ta gane cewa ba shi da jimirin yunwa, amma ga shi yau bai fito ba, to ko de tunani yake ba ta yi girki ba?.
Da wannan tunani ta nufi ƙofar ɗakinsa, sau ɗaya ta ƙwanƙwasa, ta ji muryarsa ta yi gyaran murya a cikin ɗakin, tunaninta ya ba ta cewar wata ƙila wani uzurin yake yi da ba ya so ta shiga ta gani a lokacin, sai ta ci gaba da tsayiwa a bakin ƙofar, har kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta ƙara bugawa. A wannan karon magana ya yi.
“Shigo!”
Ta murɗa handle ɗin a hakankali, sannan ta shiga, tsaye ta ganshi jikin wani shelf ya na duba takardu, a karo na farko kenan da ta fara shiga ɗakinsa. Kallonta yake kamar yanda take kallonsa. Hannunsa na dama riƙe da wani littafi, da a jikin covernsa aka rubuta 'I was never yours'.
“Ina kwana”
Ta gaida shi kanta a ƙasa, kamar ba Mishal ba, don a duk sanda za ta ganshi sai ya ƙara girma a idonta.
Kuliya ya ci gaba da kallonta, sanye take da wani wide blue jeans, sai farar top da ta saka, wadda a jikinta aka rubuta 'Believe in your dreams' gashin kanta baje a bayanta, sai band da ta saka daga saman gashin, fuskarta fayau, babu ko da lip balm.
“Lafiya, ya jikin nake?”
Ya tambaya ya na aje book ɗin hannunsa. Ita fa ta ma manta da ba ta da lafiya, yanda ta yi overdose na maganin nan ba dole ma murar ta gudu ba. Sai ta gyaɗa masa kai.
“Na ji sauƙi... Na gama abinci, kuma na ga har yanzu... Ba ka fito ba”
Iko sai Allah, ita fa a rayuwarta ba ta ƙumbiya-ƙunbiya wurin faɗin abun da ke ranta, amma a karo na farko, sai ga ta tana inda-inda wurin faɗin wani abu.
“Aiki nake, shi yasa ban fito ba. Amma na gama, mu je”
Ya ƙarshe ya na tsayawa a gabanta, sai ta gyaɗa masa kai sannan ta juya, shi kuma na biye da ita a baya har danning ɗin. Abincin ta zuba masa, sannan ta zuba nata, suna ci ya na mata magana jifa-jifa, wani abu sabo, yau shi ne yake hira, ita kuma uwar 'yan surutun ta yi shiru, ta nutsu, kamar ba ita ba, saɓanin da da idan suna cin abinci ko in sun zauna irin haka ita ce ke masa surutai.
Bayan sun kammala cin abincin ya ƙara komawa ɗakinsa, ita kuma sai ta zauna a falo tana kallon tv, yayin da takewa Ayra susa.
Garam!, ta ji an bankaɗo ƙofar falon, ba shiri ta miƙe tsaye ta na kallon ƙofar, Jadda ce ta shigo ta na wani muzurai.
Hatta Kuliya dake ɗaki sai da ya ji ƙaran turo ƙofar, hakan ya sa ya fito, amma ko kafin ya isa falon ya hangi Jaddan ta na shigowa, hakan ya sa ya ja ya tsaya daga corridorn ya na kallonsu.
“Jadda!”
Mishal ta kira sunanta.
“Eh ni ce jikata. Zuwa na yi na ɗaukeki na tafi da ke. Dan na ga kamar shi kawun naki ba sanki yake ba. Shi ya sa na zo na ɗauke ki...”
“Ki ɗauke ni mu je ina?”
Mishal ta tambaya a sanda Jaddan ta riƙo tsintiyar hannunta.
“Maiduguri nake so mu koma, gwara ki koma can cikin 'yan uwanki, ko karatun ne ma ai sai ki ci gaba da yi”
Mishal na girgiza mata kai ta kai hannunta da bata riƙe ba ta kama na Jaddan dake riƙe da nata ta ɓanɓare.
“Jadda yanzu fa ni matar aure ce.... Ina kike san na je ba tare da izinin mijina ba ?”
Jadda ta rafka salati ta na kama baki.
“Ke Hafsat!, wai ke nan daɗin aure kika sani?! Wato ke gaki matar gida ko?, Ub*n me shi wancan matsiyacin ya baki da har kika manta da mu haka?”
“Jadda please, shi ɗin mijina ne a yanzu. Ba ki san shi ba amma kina zanginsa, dan haka kada ki sake.Dan idan kika kuma ba zan yi shiru ba”
Salatin da Jaddan ta rafka a wannan karon ma ya fi na ɗazu.
“Hafsat wai ko bakya cikin hayyacinki ne? Yo in ba haka ba ta ya za ki tsaya kina gaya min waɗanan maganganun kamar wata sa'ar ki?”
“Jadda ke ce ba ki riƙe girman ki ba. Wani daɗi zan biki ki bani a Medugurin?, Babu wani abu da za ki iya bani a Meduguri face ki saka ido kina gani jikokinki su ƙarasa lalatamin rayuwar da suka so su lalata min tun farko. Ke a ko da yaushe ba ki da abun faɗi da ya wuce cewa kina son jikokinki, kina san jikokinki, a haka ake san jikan?. Ta wannan hanyar da kika ɗauka za ki iya riƙe ni, saboda sanin halinki ya sa 'yarki ta cikinki kafin ta bar duniya ta gargaɗi yayana da kada ya bari na tashi a wajenki. Yanzu kuma da hankali na kike so na biki mu tafi can?, can ɗin da babu wani me iya bani kariya?”
Cike da mamaki Jadda take kallonta, wai yaushe ma Mishal ɗin ta yi hankali har haka?, Kamar ma ba ita ba, ko da yake ai an ce aure na gyara mutum, sannan yakan sa mutum ya nutsu.
“Ba za ki biyoni ba kenan?”
“Ba zan biki ba, ya fiye min alkairi na zauna a gidan nan, ko da Aliyu zai riƙa dukana ne, da de na biki mu tafi Meduguri, ballantana kuma babu wani abu da mijina ya rage ni da shi. Ko me na buƙata cikin gaggawa yake samar min da shi, bayan haka kuma ina san mijina, to me zai sa na biki?”
“Kin yi da 'yar halak”
Jadda na faɗin haka ta juya a fusace ta bar gidan, wasu hawaye masu ɗumi suka shiga sauƙowa Mishal a kan kumatu, wai yaushe rayuwarta za ta setu ne?, yaushe ne ita ma za ta samu dawwamammen farin ciki kamar kowa.
Hannu ta ji ya kewayeta daga baya, sannan ta ji sauƙar haɓarsa a tsakiyar kanta, kafin ya ƙara janta jikinsa, ba shiri wani kuka me ƙarfi ya kufce mata, ta sake shi kuwa.
Kuma cikin gaggawa ta juya ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannayenta suka kewaya ta bayansa, sannan ta ci gaba da yin kukanta me sauti.
Kuliya ya ɗora haɓarsa a kanta, sannan ya shiga shafa kanta da hannunsa na dama, hanunusa na hagu kuma ya na shafa bayanta.
“Shhhhh! Teddy Bear, komai zai wuce, komai zai wuce....”
Haka ya ci gaba da nanata mata a kunnenta, yayin da ita kuma ta ci gaba da rera kukanta a cikin jikinsa, dan kuka ne irin wanda ta jima ba ta yi ba, ba ma za ta iya tuna rabonta da yin irin kukan ba, ko a lokacin rasuwar Abubakar hawaye kawai ta yi, amma kuka irin wannan ba ta saba yinsa ba.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
RAJA POV.
Kamar kullum ya nazaune daga balconym ƙofar shiga gidan, ya saka ƙofar gate a gaba ya na ta kallo, ya tsinduma cikin kogin tunani da ya saba shiga, ya na ta linƙaya a ciki, ba tare da sanin madafa ko kuma gaɓar da igiyar kogin za ta kaishi ba.
“Zaid!”
Muryar Rhoda ta kira shi, hakan ya sa ya juya ya kalleta.
“Na samo address ɗin asibitin!”.
Be san meke faruwa a kansa ba a lokacin, amma shi dai kawai ya yi fatan ina ma zai lumshe idonsa ya buɗe ya tsinci kansa a cikin asibitin.
Wani irin gudu yake da motar, wanda ya wuce na hankali, shi da Rhoda ne, wadda ta saka ido ta na kallonsa kawai, yanda yake gudu da motar kai kace ce masa aka yi idan ya tafi a hankali duniyar ce za ta tashi ba tare da ya je ya cimmawa abun da yake san gani ba.
Cikin wasu 'yan muntuna sai ga su sun iso 'Vinca Hospital'.
“Sunanta Rabi'a!”
Raja ya faɗi cike da ƙaguwa, yayin da suke tsaye a reception, sai kai kawo yake, Rhoda ta dafa kafaɗarsa cikin san kwantar masa da hankali ya fi a ƙirga, amma sam ba ya fahimtar me take shirin faɗi.
“Zaid Aliyu!”
Da sauri suka juya daga shi har Rhoda, don ganin mahaluƙin da ya kira shi da wannan sunan, bisa ga mamakinsu, sai ya ga wani abokinsa ne da su ka yi jami'a tare, ba course ɗaya suke offering ba, amma sukan haɗu a cikin makaranta.
Duk da ya na cikin wani hali sai da ya yi wa abokin nasa murmushi, haɗi da miƙa masa hanu su gaisa.
“Me ya kawoka asibitinmu?”
Abokin me suna Huzaifa ya faɗa, Raja ya ɗan sosa kansa.
“Wata mara lafiya muke nema...”
Bai ko rufe bakinsa ba, receptionist ɗin tace.
“Ku yi haƙuri ranka ya daɗe, amma babu mu da mara lafiya me wannan sunan...”
Raja ya girgiza kansa.
“Kuma an tabbatar muku da ta na nan?”
Huzaifa ya tambayi Raja, Raja ya gyaɗa kansa a sanyaye.
“Da ga masaniya me ƙarfi muka samu labarin, kuma an tabbatar mana da tana cikin asibitin nan”
“Muje office ɗina, wata ƙila akwai wani temako da zan iya maka”
Daga haka kuma suka ɗunguma zuwa office ɗin Dr. Huzaifa.
Wuri ya nuna musu suka zauna, sannan shi ma ya zauna ya na tambayarsu.
“Kamar yaushe kuke ganin an kawota nan?”
“Sati uku baya haka...”
Rhoda ta bashi amsa,sai ya gyaɗa kansa ya na ɗaukan wayarsa, kira ya yi, kuma bayan wani lokaci sai ga wata nurse ta shigo hannunta riƙe da files.
Dr. Huzaifa ya karɓi fle ɗin ya na kallon fuskarta.
“Ɗakin nan kika shiga ba?”
Ya tambayeta saboda ganin yanda idonta ya yi jajir, alamun dai ta yi kuka, sai nurse ɗin ta sinkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsunta.
“Sakina!”
Ya kira sunanta, hakan ya sa ta ɗago da kanta ta kalleshi.
“Sau nawa zan faɗa miki ki dena shiga ɗakin nan, in har za ki riƙa shiga damuwa irin wannan, me nene amfani zuwa ganinta?”
“Na kasa iya hana kai na Dr., a duk sanda zan shiga na dubata sai na zubar da ƙwalla...”
Huzaifa ya miƙawa Raja file ɗin, wanda ya kafesu da kallo.
“Ki je kawai za mu yi magana daga baya”
Kanta ta gyaɗa sannan ta fita daga office ɗin.
“Akan wa kuke magana?”
Raja ya tambaya hannunsa riƙe da file ɗin da Huzaifan ya miƙa masa.
“Wata mara lafiya ce aka kawota asibitin nan, sati uku baya, Wallahi abun tausayi, wasu ne suka mata fyaɗe sannan suka cillar da ita a hanya, mutanen kusa da mu ne suka kawota nan, sati uku kenan amma babu wani nata da ya bayyana... Wannan file ɗin ya na ƙunshe da bayanan kaf marasa lafiyar da aka karɓesu a asibitin nan, a tsakankanin sati uku da suka wuce, ku duba, wata ƙila za ku iya samun wadda kuke nema”
Ya ƙarashe ya na musu bayani kan abinda ya sa suka biyoshi, amma sam Raja bai fahimci zancen nasa na biyu ba, wannan maganartasa ta farko ita ce ta sa hankalinsa a kwalba ta kulle, don zuciyarsa ce ta hango masa dacewar bayanen da aka basu, da kuma wanda shi Huzaifan yake faɗa, to ko de ita ce?, amma ta ya za ayi ta kasance ita?.
“Ina ne ɗakin mara lafiyar?”
Rajan ya tambaya ya na kallonsa, har Huzaifa zai ce wani abu, sai kuma hoton fuskar yarinyar ya haska a cikin kansa, rannan da ya shiga ɗakin don dubata ya kalli fuskarta, a lokacin ya ga kamar ya san fuskar tata a wani wuri, duk da ɗinkin da aka mata a gefen fuskarta, amma ta masa kama da wani wanda ya sani, a yanzu da Raja yake zaune a gabansa, sai fuskarta ta haska a cikin kansa, haɗi da tasa fuskar.
“Nan ne!”
Huzaifa ya faɗi ya na nuna musu ƙofar ɗakin, Raja ya juyo ya kalli Rhoda, zuciyarsa na dokawa a kunnuwansa, ƙafafunsa suka masa nauyi, don ji yake kamar abun da yake zargi shi ne zai tabbata.
Kamar mara lafiya haka ya kai hannunsa ya kama ƙofar ɗakin ya murɗa, tura ƙofar ciki ya yi, sannan ya shiga. Idonsa ƙyam a kan yarinyar dake kwance a kan gadon marasa lafiya, wasu na'urori ne ɗaure a jikinta, kuma babu sautin dake tashi a ɗakin sai na na'urorin.
Duk da wani irin fari da ta yi, duk da wani ƙaton yanka da ya gani a gefen fuskarta, duk da gashin kanta da ya yi alamar kamar an yanke, duk da yanda fuskarta ta yi wani irin fayau kamar wadda ta mutu, duk da yanda idanuwanta ke a rufe kamar gawa, bai hana shi gane taba.
Kuma ƙwaƙwalwarsa na ganeta, ta hankaɗo masa bayanan Huzaifa na ɗazu.
_“Wata mara lafiya ce aka kawota asibitin nan, sati uku baya, Wallahi abun tausayi, wasu ne suka mata fyaɗe sannan suka cillar da ita a hanya, mutanen kusa da mu ne suka kawota nan, sati uku kenan amma babu wani nata da ya bayyana...”_
Nan take ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta tashin bomb, a sanda kalaman suka tsaya, a lokacin ne ƙafafunsa suka ɗauki rawa, haka ma hannayensa, hatta da bakinsa rawa yake, duniyar ta masa. Wani irin shiru, sannan duhu ya mamaye injinan ganinsa.
Fyaɗe!?, fyaɗe!?, fyaɗe!?, Ita ma?, kenan ita ma sai da aka samu wani ya aikata mata wannan zalincin?, me ya sa haka?, me ya sa ƙaddararsa take zuwa a haka?, me ya sa tarihi yake shirin maimaita kansa?, me ya sa?, me ya sa?, me ya sa?!...
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*19*
~~~
*Love is; when you hug someone and they feels like home...*
***
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
A fusace Jadda ta shigo cikin gidan tana famar bambami, kamar wadda ta zauce. Hajjara na zaune a kan kujera tana taunar chewing gum, haɗi da latsa wayarta, wani ɗan iskan kallo ta bi Jaddan da shi, kafin ta ci gaba da kallon wayarta, daga gefen ta kuma Fahima ce zaune ta na wasa, yayin da Hammad ke zaune a kan dinning ya na cin abinci.
“Wallahi wannan yaron da aka aurawa Hafsat ya ɓatata, yo in ba haka ba ta ya za ayi na je na ce ta taho mu tafi, amma ta ce ba za ta zo ba?, wata ƙila ma shanyeta ya yi!...”
Haka ta dinga sambatu, har ta kai ɗakin da ke a mazaunin nata, ta riga ta yanke shawarar barin garin a yau, don babu abun da za ta zauna ta yi a Abuja, tun da wadda take zaune don itan ta ƙi yarda ta biyota, duk da wahalar da ta sha kafin ta samu adireshin gidan nata.
Kuma ta riga da ta yamie shawarar datse ko wace alaƙa dake tsakaninta da Mishal ɗin, tun da ita ba ta da mutunci, wai ita 'yar daɗi miji, tun da ta zaɓi zama da shi ga fili ga me doki, sukuwa kawai ta rage, kuma Allah ya bata sa'a, amma ita da Mishal kam ko a lahira!.
*No.181, Guzape, Abuja...*
*07:55 PM.*
YUSHAL POV.(ALIYU & MISHAL)
“Ga shi”
Muryar Kuliya ta faɗi, a sanda yake miƙawa Mishal wani ɗan ƙaramin bowl dake ɗauke da yankakkakiyar albasa.
Rai a cunkune Mishal ta kai hannu ta karɓa, sannan ta juya kan stove, ta buɗe murfin tukunyar da take dafa jallof ɗin shinkafa, ta zuba albasar, sannan ta rufe murfin tukunyar. Ta ajiye bowl ɗin ta shiga wanke hannunta a sink.
Kuliya ya ci gaba da kallonta, ya na nazarin yanayinta, tun bayan da suka yi wannan faɗan da Jadda bata dawo dai-dai ba, kuma saboda ya san ta na cikin yanayin damuwar ne ya sa shi dawowa gida da wuri. Amma duk da haka sai ya isketa cikin damuwar.
Ko bayan da ta gama wankewa hannunta, sai ta ci gaba da tsayuwa a jikin sink ɗin, ta shiga karanta wasiƙar jakin da ba ta da ranar ƙarewa.
A hankali Kuliya ya isa bayanta, sannan ya saka hannaynesa ya kewaye waist ɗinta, ya janyota baya, tare da mannata da jikinsa. Mishal ta rintse idonta, saboda da wannan sanyin da ya fara shiga kowace ƙofa ta gashi a cikin jikinta.
“Me yake damunki?”
Sai ta buɗe idonta, ta soma kallon garden ɗin gidan ta windown dake kusa da sink ɗin, amma bata ce masa komai ba.
A hankali Kuliya ya sunkuyo da kansa zuwa kafaɗarta, sannan ya manna mata peck a wuya, wanda ya sa ba shiri ta damƙe bakin sink ɗin.
“Me yake damunki?”
Ya tambaya wannan karon a cikin kunnuwanta, kuma murya ƙasa-ƙasa, wadda ta sa Mishal saurin juyawa a cikin hannayensa tana kallonsa. Hannayenta a kan kafaɗunsa, idonta a kan kyakkyawar fuskarsa. Peck ya mata a goshinta, hakan ya sa ta lumshe idonta.
“Me yake damunki?”
Ya kuma tambaya a karo na uku, yayin da goshinsa ke kare da nata, hancinsa a kan nata. Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta fara hawaye, da sauri ya zare hannayensa daga jikinta ya dawo da su kan fuskarta ya na share mata su.
“Ba ki yarda da ni ba ne ?”
Da sauri ta girgiza kanta.
“Na yarda da kai sosai, wata ƙila ma sama da yanda na yarda da kaina, ina cikin damuwa saboda rashin ganin Yayata, yau ma fa ba ta zo ba, jikina na bani cewar ta na cikin matsala”
Kuliya ya girgiza mata kai ya na cije laɓensa na ƙa. Tare da share mata wata ƙwallar dake bin fuskarta, ashe kenan hasashensa bai zama gaskiya ba, ba abun da suka yi da Jadda ba ne a ranta, damuwar Rabi ce a ran nata.
“Insha-Allah ta na cikin hali me kyau, ki kyautata mata zato, da yardar Allah zan nemo miki ita, wannan alƙawari na ne”
“Ka min alƙawari?”
Ta tambaya muryarta a raunane.
Kuliya ya gyaɗa mata kai ya na ci gaba da share mata hawayen, kwanciya ta yi a jikinsa tana sakin wani kukan, Kuliya ya gyara mata riƙo a cikin jikinsa.
“Ki na so mu yi faɗa?”
Ta girgiza kanta, hakan ya sa jikinsa motsawa, saboda kanta dake kwance a ƙirjinsa. Ya ɗaga kafaɗa yana faɗin.
“To ki dena kuka... Ke fa kina da ƙarfin zuciya, you are so strong Teddy Bear, so don't cry!”
Sai ta gyaɗa masa kai. Sautin tafasar tukunya ne ya ankarar da su girkin da suke, don dukansu sun ma manta da girkin.
Hakan ya sa da sauri Mishal ta fice daga jikinsa ta koma jikin stove ɗin. Shi kuma ya koma ya zauna a kan kujera ya na kallonta.
*Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja*
RAJA POV.
Zaune yake a kan kujerar dake kallon gadon marasa lafiya na ɗakin da aka kwantar da Rabi'a. Bayansa jingine da jikin kujerar, yayin da ƙarfen da aka saƙala drip ɗin da aka saka masa yake aje a gefensa, hannunsa na dama juma saƙale da allurar dake aika drip ɗin zuwa cikin jikinsa, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Rabi'ar dake kwance akan gadon.
A ɗazun suma ya yi, har sai da aka ƙaramasa ruwa, kuma ya na farkawa ya fito daga ɗakin da aka kwantar

Please Login or Register in order to submit comment