Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta miƙe, amma sai Saratun ta mayar da ita ta zaunar.
“Gaskiya Umma ba kya kautawa, Wallahi wannan ba adalci ba ne, yarinyar nan ta je ta yini tana aikin bautar da ba ita take cin kuɗinta ba, dan ke take kawowa, sannan ta dawo ta yi aikin gidan nan, kuma yanzu ta samu ana ɗan mata kalbar da za ta yi adon salla sai ki ce baza'a mata ba ?!”
Habiba ta ɗan sunkuyo tana miƙowa Saratu bayanta.
“Da ke ni mama Saratu, na ce inji didim!, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci....”
Ta miƙe tana ci gaba da faɗin.
“Na taɓo uw*r ki Rabi ko?, To baki isa ba, dole sai ta tashi ta soya doyar nan!....”
Kafin Saratu ta sake cewa wani abu, Rabi ta yi wuf ta miƙe tsaye, tana ƙoƙarin ɗaure kanta da ɗankwali. Gashin kanta da tsayinsa ya ragu a yanzu ya kwanta luf a gadin bayanta, har yana reto.
“Gaskiya Umma na gaji!, Wallahi na gaji da abinda kikewa yarinyar nan a cikin gidan, ita ma fa 'ya ce, kuma ko baabaarta bata raye hakan ba ya nufin a cusguna mata. Umma kema uwar 'ya'ya mata ce, wata rana gidan wani za muje. Na tabbatar da idan uwar miji ko 'yan uwansa suka mana haka ba za ki ji daɗi ba. To ita ma kamar haka ne, tana da dangi bayan mu. Dan tsabar san zuciya irin naki yau shekarar yarinyar nan biyar a gidan nan, amma kin hanata ta je ta ga dangin mahaifiyarta, dan kar ta je ta faɗi irin azabar da ake bata a cikin gidan nan su hanata dawowa ki rasa baiwa. Wallahi Umma wannan ba adalci ba ne, ke ba kya tunanin wata ƙila wannan abun da kike shi ne ya zama sannadiyyar tagayyarar mu?, Ita 'yar taki ta fari, bata jin daɗin aurenta, sannan ni, shekaruna 27, amma na rasa mijin aure, ko sau ɗaya saurayi bai taɓa zuwa ƙofar gidanan yace yana sallama da ni ba, ga kuma Mama, wadda ta lalace da bin maza!.....”
“Ya ishe ni haka Saratu, ki rufa min baki ko na make ki a wurin!”
Saratu ta share guntuwar ƙwallar da ta zubo mata ta buɗe labulen ɗakinsu ta shige ciki.
Rabi'a da ke kiciniyar hura wuta ma ta share tata ƙwallar, saboda tunawa da ta yi da dangin Ummanta, ta tuna yanda suke matuƙarsanta da 'yar uwarta, sai kuma tunanin Anti Saratun, Allah ya sani kuma ita ma ta sani, ba ƙaramin cutuwa baiwar Allahn nan take da zaman gidan.
Kuma ta san cewa Anti Saratun na matuƙar san aure, dan tasha kamata tana kuka, kan abun da ke damun rayuwarta, sai dai ta zauna ta bata baki har ta samu ta yi shiru.
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
*10:30am*
KULIYA POV.
“Aliyu Zaid Bichi!”
Cewar shubansa, yayin da yake tsaye a gaban shugaban, ya ƙame cike da girmamawa.
Wani murmushi kwance a fuskar ogan. Kuma cikin abinda bai wuce sakan biyu ba, wannan murmushin ya sauya zuwa ɓacin rai ma bayyani.
“Kai wai me yasa ba zaka taɓa sauyawa ba?, yanzu saboda shashancin da ka yi, ɗaya daha cikin criminal ɗin ya mutu, kai kwata-kwata baka iya controlling fishinka ne ?!”
Kuliya ya ƙara ƙamewa yana kallon wani wurin da ban, dan da ma yasan hakan sai ta faru, ba ma yasan ya kalli fuskar ogan, dan idan har ya kalleta, zai iya hasaso kansa yana marin shugaban nasa, kuma wata ƙika ma hasashen ya zama gaskiya.
Dan baya san a ɗaga masa murya, daga an ɗaga masa murya yake kai hannu, shi kansa yasan cewa zuciyarsa a kusa da take, abu kaɗan ne ke tunzura shi. Ya ɗaga kafaɗarasa yana ci gaba da kallon wani hoto dake aje a bayan ogan nasa.
“A haka kake san zama kamar Lion ɗin ?...... Shi Lion ɗin da kake san zama sam ba haka yake ba, cikin basira da taka tsan-tsan yake gudanar da aikinsa, ba shi da saurin fusata kamar kai, ba shi da saurin kai hannu kamar kai!....”
Lion?!, wani suna guda ɗaya da yake ƙwarara masa gwiwa a kan aikinsa, wani sunan da ko jinsa ya yi sai ya ji jinin jikinsa na tafasa. Kuma ba shi kaɗai ne sunan Lion ke bawa ƙwarin gwiwa ba.
Kusan duka ma'aikatan DSS sun san sunan Lion, dan abu ne mayuwaci, ka je training ɗin DSS ba tare da an baka maka tarihi da kuma sunan Lion ba.
Duk wani jarumi da mai hazaƙa a hukumar burinsa kawai ya zama kamar Lion. Sai dai kuma duk da wannan nasara da kuma jarumta irin ta Lion ɗin, in ka ɗauke manyan hukumar tasu, babu wanda yasan kammanin fuskarsa, sunan nasa kawai ake ji, sai kuma ƙwazon da yake a aikin nasa, sunan nasa ma ba na ainahin kowa ya sani ba. Code name ɗinsa kawai suka sani.
Amma duk da haka yana burge kowa, dan duk wanda zai gwada wata jarumta da kuma san nuna role model ɗinsa sunan Lion za ka ji ya kira.
“Sam shi Lion ɗin ba haka yake ba....”
Muryar Ogan nasa me amsa sunan Chidera Kingsly ta katse masa hanzari.
“Lion yana da basiri, he is so intelligent, amd smart, ya san aikinsa, baya komai cikin fushi, cikin nustuwa da tunani yake gudanar da aikinsa.....”
Kuliya ya sauƙe kansa ya ɗora manyan idanuwansa a kan fuskar shugaban nasa. Kuma har zuwa lokacin bai ce komai ba, dan tun bayan gaida shi da ya yi a sanda ya shigo office ɗin, bai ƙara cewa komai ba.
Kuma shima Chideran yasan cewa ba lalle ya sake cewa komai ɗin ba, dan kowa yasan miskilancin bawan Allahn nan.
“Na san cewa yanzu haka ka rayawa ranka cewar; ka dalle min fuskata da mari!”
Wani abu me kama da murmushi ya faru a cikin zuciyar Kuliya, dan ya canka dai-dai, hasasowa kansa yake yayin da yake kashe sauraye a kan fuskar chideran, dan ba sauro ɗaya ba.
*
“Ehemm!”
Muryar Kuliya ta yi gyaran murya, alamun ya bawa wanda yake buga ƙofar izinin shiga, dan wannan ɗabi'arsa ce. Kusan duk wanda yake headquarter ɗin yasan da hakan.
Shi a ganinsa magana ma wani kayan gabar ne, amma idan masifarsa ta tashi yafi ub*n kowa iya ɗaga murya.
Zaune yake a office ɗinsa, yayin da yake daddana system. Kamar kullum; sanye yake da baƙaƙen kaya, wata baƙar suit ce a jikinsa. Hatta da long sleeve oxford shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin baƙa ce.
Ƙofar office ɗin ta iyo ciki, alamun dai wanda yake bayan ƙofar yana shirin shigowa. Suffar Abubakar ta bayyana a bayan ƙofar.
Kallo ɗaya Kuliya ya masa ya ɗauke kai, tare da ci gaba da danna laptop ɗin gabansa.
“Barka da safiya..... ni na gaida ka, tun da kai ba za ka iya ba gaisheni ba”
Abubakar ɗin ya faɗi yana ƙarasowa cikin office ɗin. har ya zauna a kujerar dake tsallaken teburin Kuliyan bai masa magana ba.
“Me yasa yau ka makara ?”
Muryar Kuliyan ta tambaya bayan wani lokaci, ba tare da ya kalli Abubakar ɗin ba. muryar tasa kamar da ga sama. Sannan amonta ya fito kamar kullum, cikin ɗaci da alamun ɓacin rai.
Dan shi kullum ba'a rasa abinda yake ɓata masa rai. Abubakar ya yi murmushi, to shi ya zai yi ne?, tun da Allah ya haɗa shi zama da mutane biyu masu murɗaɗɗen hali, tsakanin Kuliya da ƙanwarsa Misha!, Ya rasa wannene ya fi wani murɗewar hali.
“Ƙanwarka ce, ta yi rashin jin da ta saba a makaranta, sai da na biya ta can, sannan na ƙaraso nan”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Shi duka-duka sau ɗaya ya taɓa ganin ƙanwar Abubakar ɗin, ba ma sosai yake iya tuna lokacin ba, dan shekarun da ɗan dama.
“Dama autopsy results ɗin nan na zo karɓa, Kamis yace yana wurin ka”
Ba tare da Kuliyan ya kalle shi ba, ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, sannan ya buɗe wata loka dake jikin teburin nasa, ya ɗauko file ɗin,ya miƙa masa. Abubakar ya karɓa yana miƙewa tsaye.
“Na tafi...”
Ko kallonsa Kuliya bai yi ba, bare ya bashi amsa, kuma shi ma yasan ba lalle ya kalle shin ba. Yasan halin Kuliyan sarai. Har faɗi yake da bakinsa cewa; idan ba Abubakar ɗin ba babu me iya zama da shi a matsayin aboki.
Dan kaf duniyar nan Abubakar ɗin ne kaɗai abokinsa, ba shi da wani aboki da ya wuce shi, sai Sharon da suke ɗan jitiwa, ita ma kuma ba kullum ba.
*Badawa layout, Kano....*
RAJA POV.
“Raja dan Allah, dan Allah!.....”
Cewar wani mutumi a galaɓaice, yayin da yake durƙeshe a gaban Rajan. Kuma bai ko gama rufe bakinsa ba, Rajan ya ƙara tsinduma kansa cikin bahon dake aje a gabansa, wanda yake cike taf da ruwa.
Haka mutumin ya yi ta motsi da kansa a cikin ruwan, saboda azabar da yake ji. Zaune yuke a harabar gidansa. Yayin da Rhoda da su Zuzu ke tsaye a bayansa.
Waɗanan lumssassun idanun nasa na kallon mutumin da kansa ke fancal-fancal cikin ruwan sanyin. wannan innocent face ɗin nasa fayau!, banu wani abu da za ka iya tsinta a cikinta. Kai ba ka ce mamallakinta ne ke wannan aikin ba.
Ƙarar ringing tone ne ya karaɗe wurin. A hankali Rhoda ta duba screen ɗin wayar 'Oga Garuje', shine abun da ta ga an rubuta, dan haka da sauri ta ƙarasa kusa da Raja.
“Garuje ne ya ke kira”
Bai kalleta ba, sai ma bindigarsa ƙirar pistol da ya ɗora a kan fuskar mutumin da ya tsamo kansa daga cikin ruwan. Sannan wannan kamillar muryar tasa ta furta.
“Me yasa ka ci amanar mu?”
A nitse muryar tasa ta fito, cikin wannan sautin nata mai nuna tsantsar innocent ɗinsa.
“Dan Allah Raja....Dan Allah...”
Ji kake Tas!!. Ƙarar bindiga ya karaɗe harabar gidan. Me gadin gidan ya yi saurin faɗawa ɗakinsa. Duk da yasan cewa abun ba zai komo kansa ba. Amma wai me hausawa suka ce ne?, idan ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa.
Raja ya yi wani murmushi me kama da dariya, a sanda ya ga shigewar me gadin nasa. Kafin ya saki gawar mutumin nan da ya harba a ka. Jini har ya ɓata masa hannu.
Ba tare da nuna damuwa ko wani tashin hankali ba, ya sunkuya ya wanke hannunsa cikin ruwan bahon nan.
Kuma har zuwa lokacin wayar tasa na riging a karo na barkatai.
“Ina ji”
Nutsatsiyar muryarsa ta faɗi,bayan ya amsa wayar, cikin wannan kamala da kamewar tasa, kai ba ka ce shi ne ya kashe rai yanzu ba.
“Raja!, Oga ne da kansa ya yi waya, ya ce ya na buƙatar ka je ka same shi a Abuja....”
Raja zai iya rantsewa kan zuciyarsa sai da ta buga sau biyu a lokaci guda. Kenan tsawon shekarun da ya kwashe yana wannan aikin sun kusa ƙarewa?. Shekaru sama da uku ma rayuwarsa ya kwashe yana bautar da bai san ranar ƙarewarta ba. Sai a yau ne komai ya ke gaɓa. Komai ya ɗauko hanyar ƙarewa. Ya kawo inda ya ke matuƙar burin kaiwa.
Sai dai a yanayin fuskarsa ba za ka tsinci hakan ba, dan miƙewa tsaye kawai ya yi, sannan ya juya yana kallon su Rhoda.
Da waɗanan lumsassun idanuwan nasa, ƙwayar idon wadda ta kasan ce gray color tana kallon yanda su Zuzu ke magana ƙasa-ƙasa. Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce.
“Yaushe kenan ?”
“Ko zuwa nan da sati ɗaya ne, dan da alama ka koma can da zama, ka ga kenan sai an nema muku gidan da zaku zauna, da dai sauran su...”
“Na fahimta!”
Kuma da ga haka ya tsinke wayar.
“Alandi, Zuzu, ku fita da gawar nan da ga gidan....”
“An gama Oga Raja!”
Suka faɗi suna yin wurin da gawar ke yashe.
Sannan shi kuma ya yi hanyar shiga cikin gidan, da hannu ya yiwa Rhoda alamu da ta biyo shi.
“Rhoda, mun kai ga gaci....”
Wannan salihar muryar ta faɗi a sanda suke zaune a falon gidan.
”Me ya faru?”
Rhoda ta tambaya.
“Alhaji Bala ne da kansa ya ce na je na same shi a Abuja”
Cike da mamaki, murna da kuma farin ciki take kallonsa.
“Kenan mun kusa zuwa ƙarshe?”
Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce.
“Kusan zan iya cewa hakan”
“Kai amma fa na yi farin ciki...”
Ta faɗi da iyakar gaskiyarta, dan ta yi farin cikin, tana ganin kamar komai ya kusa ƙarewa, kamar an gama komai, kamar wannan wahalar da suka sha tsawon shekaru ta ƙare.
Kuma ba ita kaɗai ke wannan tunanin ba, shi ma kansa Rajan haka yake tunanin sun kammalla komai, komai ya zo gangara, gangarar da zata gangaro da ƙarshen wahalar da suka sha tsawon shekaru.....
Sai dai abinda bai sani ba shi ne; yanzu ne ma komai ya fara, a yanzu LABARIN zai soma, sai a yanzu ne babin ƙaddarar tasa zai buɗe.
Wani sabon babi fil!, wanda babu ɗigo ko ɗaya a ciki, sai na wanda ubangiji zai hukunta. Saboda wata ƙaddara da ke shirin faruwa 'yan kwanaki masu zuwa. Ƙaddarar da zata tarwatsa komai, ta kuma gyara wasu lamuran.
A dai-dai lokacin ƙofar falon ta buɗe, Jagwado ne ya shigo, dan da ma banda shi aka tafi yasar da gawar.
Lighter ce riƙe a hannunsa yana ƙyasta ta, yayin da sigari ke maƙale a bakin. A sa'ar da Raja ya ɗora idonsa a kan wutar, a lokacin ne kuma wannan tsoron ya shige shi, tsoron wuta da Allah ya saka masa tun bayan abinda ya faru da shi.
Baya san ganin wuta sam, domin wuta na ɗaya daga cikin abin da ta zama silar rabuwarsa da mutane uku da suka fi soyiwa a ransa. Da farko ta raba shi da mahaifiyarsa, sai kuma ta zo ta raba shi da ƙaninsa, ɗan uwansa abokin tagwaitakarsa. Sai ku ma Maman Rhoda, wata mace da ta taka rawa mai makuƙar muhimanci a cikin rayuwarsa.
Wani irin wahallallen nunfashi ya ja, ya samu kansa cikin irin yanayin da ya saba shiga a duk sanda zai ga wutar. Duk da yanda yake ta kokawa da tunaninsa kan kada ya koma baya, amma sai hakan ya ci tura. LABARINSA na baya ya soma kunno kai cikin nazarinsa.
_“Zaid, ku tafi, kada ku tsaya a nan.....idan kuka tsaya wutar za ya iya ƙona ku....ku tafi na ce!.....” _
Amon wannan sautin nata ya shiga maimaita kansa a cikin tunaninsa, falon ya shiga rikiɗewa yana komawa gidansu, gidan da suka rayu a ciki, gidan da suka ci gaba da kwana a cikinsa har bayan sanda wuta ta gama ɗaita shi, wannan gidan da suka gina yarintarsu shi da ƙaninsa a ciki.
Sannan hoton ya sauya a idonsa, ya na ganin yanda take watso musu kayansu ta window, yayin da ƙofar falon take a kulle, ta kasa fitowa bare ta buɗe ƙofar har ta samu damar tsira.
Sannan ya kallin kansa da ma ƙaninsa Aliyu dake ta kuka, ƙaninsa me tsantsar kama da shi, dan idan suka kalli juna sai ka ce kansu suke kallo a madubi.
Dan kammanin da suke ya ɓaci, tsayinsu ɗaya, farar fatarsu ɗaya, girman idonsu ɗaya, komai na hallitarsu ɗaya ne, in ka ɗauke ƙwayar idon Zaid da ta kasance ash, sai kuma totsiyar karen dake haƙorin Zaid ɗin. Amma hatta wata ɗabi'a ta ɗaga kafaɗa dukaninsu suna yi.
“Jagwado menene haka ?, Sarai ka sani cewar Raja ba ya san ganin wuta!”
Muryar Rhoda da ke wa Jagwado faɗa ta dawo da shi zahiri.
Bai ƙara ce musu komai ba, ya miƙe tsaye, tare da ɗaga kafaɗarsa ta dama, ya yi ɗakinsa, yana jin yanda Rhodan ta balbale Jagwado da faɗa, shi kuma sai aikin bata haƙuri yake.
_________________
_To fa.... Bana kuma nan muka leƙo?_
_Na ce ba, wai Rajan ne ko Zaid ne?_
_Dan ni na kasa ganewa, kamar Zaid da Aliyu mutum ɗayane, kamar kuma....._
_Ko da yake, ba sai na faɗa ba ai😂_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters
°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*04*
~~~
_-*What she really craves is a wild love, from a steady pertner...*-_
***
*1987*
Alhaji Ali Wakili, babban mutum ne me tarin arziƙi. Haifaffen garin haɗejia ne, kuma ya ci gaba da zama a cikin garin har bayan lokacin da ya fara tara iyali. Kasancewarsa mutum me nasibi a harkokin kasuwancinsa, ya sa shi gyara gidansu na gado, ya ci gaba da zama a ciki shi da 'yan uwansa.
Alhj Ali na da mata biyu, hajiya A'i, yaransu tara da ita mata biyar maza huɗu, matan sun haɗa da Lawisa, Fatsima, Kaltume, sai 'yan biyun gidan, Maryam da Rabi'a, Mazan kuma sun haɗa da, Abdullahi, wanda ya kasance shi ne na farko, sai Mansur, Haladu da lawan
Hajiya Kande ita ce matarsa ta biyu, yaranta huɗu da shi, kuma dukansu maza ne, Kabir, Sagir, Jamilu da kuma Jibrin.
Duka yaran gidan suna karatu, matansu da mazansu, kuma duk da kasan cewar sun taso a gidan yawa, akwai zaman lafiya a tsakanin yaran ahalin, dan iyayensu jajirtattu ne a kan tarbiyar yaran nasu.
Rana ɗaya da gaba ɗaya ahalain gidan ba zasu manta da ita ba ta kasance Asabat, inda labari ya riske su cewar an yi wa Rabi'a 'yar biyun Maryam fyaɗe.
Duk wani nau'i na tashin hankali babu wanda bai yi ba a gidan, dan da aka tambayeta ta shin san wanda ya mata fyaɗen?. cewa ta yi bata sani ba, dan hankalinta a gushe yake. Haka aka gama jajjaɓin lamarin kafin aka watsar da zancen, kowa ya ci gaba da lamuransa.
Bayan kwanaki da faruwar lamarin, Alhj Ali ya nemawa Maryam gurbin karatu a garin Suleja, dan haka ta tafi can ta ci gaba da karatunta. Watanta ɗaya da tafiya, alamun samuwar ciki suka fara bayyana tattare da Rabi'a.
Tun tana ɓoye abun har ya zo ya bayyana, har kowa na gidan ya sani. Alhaji Ali ya yi tsallen albarka ya ce sai dai a zubar da cikin. Itama kuma Rabi'a ta yi tsallen albarka kan cewar ba za ta zubar da cikin jikinta ba, hakan yasa shi kuma yace sai de ta bar masa gidansa.
“In dai har ba za ki zubar da cikin jikin ba sai dai ki bar min gidana Wallahi!...”
Haka ya faɗi, a ranar da yake watso mata kayanta ƙofar katafaren gidan nasu. Gaba ɗaya mutanen gudan sun firfito, an tsaya a bakin gate ana kallon abin da ke faruwa.
Babu yanda yayun Alhaji Ali ba su yi da shi ba kan ya yi haƙuri, amma ya ce Wallahi sai Rabi'a ta bar masa gidansa, dan baza'a haife cikin shege a gidansa ba. Ba zata ɓata masa sunan zuri'a ba.
Rabi'a ta tsugunna ta tattare sauran kayan da Abban nata ya watso mata, sannan ta haɗe su a wuri ɗaya, tana ta sharar hawaye. A hankali ta miƙe ta kalli idon Abban nata.
“Da na zubar da cikin jikin, gwara na bar maka gidanka Abba.... Ba zan roƙi ka bar ni na zauna a gidan ka ba, abinda ya sameni ƙaddara ce daga Allah, kuma shi ne zai temakeni na iya cinyeta.....Ni dai buƙa tata ita cee ka yafe min Abba!....”
Ta ƙarashe tana fashewa da kuka, babu wanda bai ji tausayinta ba a wurin, amma banda Alhaji Ali, wanda ya kawar da kansa gefe, ya gwammace da ya sallamarta, da ta ja masa a bun kunya, ace yau a gidansa aka haifi ɗan gaba da fatiha?, kuma ace 'yarsa ce ta cikinsa?.
“Na san ba lalle ka yafe min ba, amma ni dai ina meneman yafiyar taka, zan yi nesa da kai, zan yi nesa da gida, zan je na haife cikin jikina, kuma zan basu labarin abinda rayuwata ta fuskanta sakamakon fyaɗen da aka min ba tare da san rai na ba...Yaran da aka haifesu ba tare da aure ba suma 'ya'ya ne, ƙaddara ce ta hukunta zuwansu ba tare da auren ba!...”
Ba tare da ta sake cewa komai ba ta ɗauki sauran kayanta tana ta sharar hawaye, ta kama hanyar barin unguwar tasu.
Sai da ta yi tafiya mai nisa, sannan ta ji muryar mahaifiyarta na ƙwalla mata kira. Cike da mamaki ta juya.
Da gudu ta ruga wurinta tan kuka, suna haɗewa ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana sakin sabon kuka, Ita ma Hajiya A'in kukan take. Kafin ta share hawayenta ta ɗago da 'yarta. Hannunta ta kama sannan ta danƙa mata wata jaka.
“Akwai kuɗi, da takardun karatunki a ciki, sannan akwai takardun gidana na kano a ciki... Ban ce ki faɗawa kowa inda za ki ba.... Ni dai ina so ki je ki kafa sabuwar rayuwarki a garin kano, idan zai iyu bayan kin haifi yaranki, ki yi aure Rabi'a!.....”
Rabi'a ta ƙara faɗawa jikinta tana sakin sabon kuka.
“Aure be dace da ni ba Mama, sanin kanki ne babu namijin da zai auri macen da ta yi ciki ba tare da aure ba”
Hajiya A'i ta shiga kwantarwa da 'yarta hankali, tana haɗa mata da nasiha, har zuwa lokacin da suka yi sallama. sallamarsu ta ƙarshe kenan.
Rabi'a ta isa garin Kano lafiya, kamar yanda mahaifiyarta ta buƙata ta sauƙa a gidan da ta bata takardunsa, sai dai gidan babu kayan buƙata a cikinsa. Dan haka washe garin ranar da ta sauƙa a garin Kano, ta fita ta je ta yi siyyayar kayan da zata buƙata na amfanin gidan. Bayan ta samu sati biyu a garin, ta shiga fafutikar neman aiki, cikin sa'a ta samu aiki a wata asibiti, kasancewar aikin nurse ta karanta.
Haka rayuwarta ta ci gaba da gangarawa ita ɗaya, kullum cikin ƙunci da tunanin gida, Allah ya sani tana kewar gidansu, sai dai kuma ba za ta iya rabuwa da cikin jikinta saboda san gidan da take ba.
Sau tari ta kan zauna ta yi tunani a kan rayuwarta, da ma haka duk macen da aka mata fyaɗe ba tare da san ranta ba rayuwarta ke kasan cewa?. Kowa ya na nuna mata ƙyama, saboda kawai Allah ya ɗora mata ƙaddara?.
Watan cikin jikinta tara dai-dai, naƙuda ta tashi mata, Allahn da ya temaketa tana asibitin da take aiki a ranar, dan ba ta wani ɗauki hutu ba. Kuma ita kaɗai take rayuwarta, babu ruwanta da kowa a unguwar da take zaune ko a asibitin. Cikin ikon Allah ta sauƙa kafiya, ta samu yaranta 'yan biyu maza.
Bayan ta dawo hayyacinta ne ta raɗa musu suna da kanta, na farkon ZAID, na biyun kuma ta saka masa ALIYU.
Ba ta yi taron suna ba, dan bata da wanda za ta gayyata, mahaifiyarta kawai ta kira a waya ta faɗa mata. Hatta da Maryam, 'yar uwarta, kuma abokiyar tagwaitakarta, wadda ta fi shaƙuwa da ita fiye da sauran 'yan uwanta bata da masaniya kan inda take. Ita kanta Hajiya A'in taƙi faɗawa kowa inda Rabi'an take ba.
Duk da wahala irin ta renon tagwaye, haka Rabi'a ta reni yaranta ita kaɗai. Sosai take nuna musu soyyaya da kuma basu kyakyawar tarbiyya. A koda yaushe tana nuna musu su so juna.
Haka yaran nata suka taso masu tsananin kama da juna, banbancinsu a hallita biyu ne, shi Zaid yana da ash ɗin ƙwayar ido, yayin da Aliyu tasa take brown, sai kuma totsiyar karen dake a bakin Zaid, wadda shi Aliyu ba shi da ita.
Haka kuma halayensu sun banbanta, dan Zaid yaro ne me sanyin hali, ga haba-haba da jama'a, amma Aliyu mugun muskili ne, babu ruwansa da yawan magana, ga masifa, da saurin fishi.
Kuma har suka yi wayo ta saka su a makaranta, a cikinsu babu wanda ya taɓa tambayarata ina mahaifinsu. Ko a makaranta ma da sunan junansu suke amfani, shi Aliyu amfani da Aliyi Zaid, Zaid kuma yana amfani da Zaid Aliyu.
Tana ƙara nusar da su cewa ba su da kowa sai junansu. Suna primary 5 ne, Zaid ya taɓa tambayarta ina mahaifinsu. Kuma bata ɓoye musu ba, a lokacin ne ta sanar musu da komai da ya danganci ita kanta da kuma su.
Suna da shekara goma sha ɗaya, wata rana sun tafi islamiyya. Rabi'a na kitchen tana girki. Bayan ta gama girkin sai ta manta bata kashe gas ɗin ba. Ta koma ɗakinta ta shiga wanka.
Ta ɗau tsawon mintuna a banɗakin. Kafin ta fito, kuma tana fitowar, ta ji ƙauri na tashi, kamar wani abu na ƙonewa, hakan yasa ta fito falo, don ta duba abin da yake faruwa, me za ta gani?. Gaba ɗaya kitchen ɗin ya kama da wuta, kasancewar a falo kitchen ɗin yake. Har ya bawa falon, yana ƙoƙarin kama ɗakuna, a lokacin hankalinta ba ƙaramin ta shi ya yi ba . Ga shi labulayen ƙofar falon sun kama da wuta, babu damar ƙarasawa jikin ƙofar bare ta buɗe.
Haka ta dawo ɗakinta ta shiga kai kawo na neman mafita. Bata ankara ba har ɗakin ma ya kama da wutar. Ta shiga kiran mutane domin a kawo mata agaji, sai de babu wanda yake ji, bare a kawo mata agajin, kamar yanda take buƙata.
Kuma a lokacin ne, Aliyu da Zaid suka dawo

Please Login or Register in order to submit comment