Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saratu, Mama, Fatima da Mahmud... Sai kuma shi baban nawa”
“Shi ne yasa kike aikatau a nan?”
Ya tambaya kansa tsaye, kuma ya lura da ta haɗiyewa wani abu, kafin wannan siriryar muryar tata tace.
“A'a, ba babana ba ne, matar babana ce”
Raja ya gyaɗa kansa ya na ƙara tabbatarwa kansa da abun da zuciyarsa ke zargi a kan yarinyar.
Ba tare da ya sake ce mata komai ba, ya tsayar mata mota kamar kullum, ta shiga sannan suka yi sallama. Sai da suka yi nisa, sannan ya juya ya koma layinsu.
Da Rhoda ya fara haɗuwa a bakin ƙofa, ta jingina da jikin ƙofar part ɗinsu tana kallonsa, fuskarta ɗauke da murmushi. Ransa ya haɗe ya na ɗauke kai, ya yi kamar be ganta ba.
Sai da ya zo wucewa ta gefenta, sannan ta ɗaga hannunta tare da saka masa wani fito me ƙarfi, har da wani tafa hannu, hakan yasa ya tsaya yana kallonta.
“Idan na ce you fall in love, sai ka ce ba haka ba, amma ga shi nan kullum sai ka karakata har bakin titi, idan ana cikin weekend sai ka riƙa ɓata rai, dude ko ka yarda... Ko kar ka yarda, ka... Faɗa.. can cikin kogin soyyaya! ”
Raja ya kai hannunsa ya dunguri kanta yana kamo wuyanta. Ya ɗaga kafaɗarsa yana faɗin.
“Cuzzie yaushe kika fara sa ido?”
“Sanda ka faɗa soyyayar gaskiya... Ba irin wadda kake a da ba”
Maganarta ta tuno masa da ita, Uchechi!, Wani sashi na kansa ya ambato masa sunanta, a hankali ya saki wuyan Rhoda, yana tuno alaƙar dake tsakaninsa da ita, kenan da shi ba son Uchechi yake ba?, to kenan da me yake ji a kanta?, kuma me yake ji a kan Ammantasa?. Tukkuna ma wani hali Uchechi ke ciki, tun bayan zuwansa Abuja ba su yi waya da ita ba.
Naushin da Rhoda ta sakar masa a ƙirji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa yana kallonta.
“Tunani ba? Ai da ma sai da na faɗa maka cewar ba son Uchechi kake ba, kuma ita ma ba sanka take ba, kuɗinka take so, kai ne ka kasa banbancewa tsakanin son gaskiya da na yaudara!...”
Kallon ta ya yi na wasu 'yan sakkani, kafin ya kamo kunnenta.
“Thunder go fire your head Rhoda! Ki ce har zarar zance kika koya?”
“Zaid...”
“Shiru! Ba na san wata magana!”
Sai ta yi shiru tana sosa kunnenta da ya saki, tare da turo masa baki gaba.
“Sorry”
Ta faɗi tana sinne kai ƙasa, janyota ya yi ya mata side hug, kafin ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama yace.
“Ke ɗin ce bakya jin magan Cuzzie... Maza mu je akwai aiki a gaban mu”
Nan da nan Rhoda ta dawo serious, tunawa da ta yi da aikin dake jiransu a gaba, aikin shigo da makaman da Alhaji Bala ya ɗorasu a kai.
*Hotoro, Ring Road, Kano...*
Uchechi ce zaune a ɗakinta, ta sa gabanta yamma tana kallon mirror, yayin da take zaune a kan stool, kallon fuskarta take a mirrorn, yayinda take neman wani abu a fuskarta da wata ƙila shi ya sa Raja yake mata abun da ya so, wata ƙila ba ta da kyau yanda ya kamata, ko kuma akwai wani tabo a fuskarta da ya sa Rajan ba ya san kusantarta.
Ƙofar ɗakin aka turo, kuma ba tare da ta juya ta kalli ƙofar ba, ta hango wanda ta shigo ɗikin, Mesoma ce, yayarta wadda take riƙe da ita. Ba ta juya ba har Mesoman ta zauna a bakin gadon dake bayanta, ta na ci gaba da kallonta.
“Wai Uchechi ba za ki manta da wannan Rajan ba?... Tun da har ba za ki iya sato zuciyarsa ba, kuma ba za ki iya samawa kan ki ruwan da zai kashe miki ƙishin ruwar ki a kansa ba, zai fi kyau ki manta da shi”
Juyowa ta yi ta kalleta.
“Mesoma ina san Raja... Ba na jin zan iya rabuwa da shi, duk munin abun da zai min kuwa, batun samun Raja kuwa zan daure na yi haƙuri har zuwa lokacin da ya tsara mana dan mu yi aure, tun da yace ba zan taɓa samunsa ba idan har ba aure muka yi ba”
Mesoma ta rage girman idonta tana kallon ƙanwarta.
“Hanyoyi nawa na tsara miki na yanda za ki samu kuɗi a hannunsa ?, Da na tsara mikin ba ki samu ba ?”
Uchechi ta girgiza kanta.
“Na samu, na samu abun da ban yi zanton samu ba”
“To me yasa da na tsara miki hanyar da za ki samu kansa ba ki bi ba?”
“Mesoma ba zan iya bin hanyar da kika tsara min ba, waɗannan hanyoyin naki sun yi tsauri da yawa”
Mesoma ta miƙe tsaye.
“So... That was the only way that i have, tun da kin ga ba za ki iya bi ba, sai ki yi ta zama cikin ƙunci”
Da sauri Uchechi ta miƙe tana kamo hannunta.
“Ki temaka ki nemo min wata hanyar”
“Ba ni da wata hanya bayan wadda na riga ma baki, idan kin ga za ki iya binta, fine, if not sai ki sa haƙuri a zuciyarki”
Mesoma ta kama hanya ta fice daga ɗakin, cike da neman mafita Uchechi ta koma ta zauna a kan stool, ta furzar da iska daga bakinta. Cike da takaici ta yi fatali da kayan dake kan mirrorn.
To wai ita ya za ta yi ne?, me ya kamata ta yi dan samun kan Raja?, wata hanya ya kamata ta bi don ta mallakeshi?!.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
“Wallahi Musa tun muna shaida juna ka kira wannan yaron da kuka aurawa jikata, ya faɗa mana ina ya kaita! In ba haka ba Wallahi sai nai maka abun da kowa zai zo yana nadamarsa!”
Muryar Jadda ke faɗin hakan cike da masifa, yayin da wayarta ke kare a kunneta, daga gefenta kuma Hajjara ce zaune tana ƙunshe dariyar muguntar dake cinta, dan ita ta kunno wutar.
Suna zaune ne a falon gidan, yayin da Jaddan ke ta sirfawa Ammu Musa buhun bala'i.
“Wai dan Allah Jadda haka ake rayuwa?, Ta ya za ki ce na kira mutum na tambayeshi inda ya kai matarsa?”
Muryar Ammu Musa ta faɗi cike da gajiyawa da halin Jadda.
“Au haka ma ka ce? To ka kyauta, Wallahi za ka ga abin da zan maka, shashasha, wanda bai san inda ke masa ciwo ba!”
Daga haka ta latse wayar ta cillar da ita gefe tana hucin bala'i.
“Gaskiya Jadda Ammu Musa bai kyauta ba, ta ya zai ɗauki 'yarmu ya bawa wani wanda ba musan shi ba? Ba mu sani ba ma wata ƙila ɗan ya kan kai ne?”
Cike da san tittilawa wutar fetir Hajjara ke bayanin, dan har yau ba ta manta da abun da Mishal ɗin ta yi mata ba, gashi dai takaba take, amma baƙin cikin Mishal ɗin bai bar ruhinta ba.
Aiko fiterin da ta bilbila ɗin ya sauƙa a tsakiyar zuciyar wutar, don ta tashi sama ta ƙara ruruwa fiye da yanda take ci a da.
“Aiko ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ko ni ko Musa, dan Wallahi ba zan zauna ina gani ya sabautar min da jika ba, duk in da zai je dole ya dawo ya sameni, dan Wallahi ba zan bar garin Abuja ba sai na san gidan da ya kai min jika”
Nan take murnar da Hajjara ke ti ta koma ciki, don kuwa ita ba haka ta so ba, ta so a ce da zarar Jaddan ta gama abun da za ta yi ta kama hanya ta koma Maiduguri, ita kuma a bar mata gidanta ita ɗaya, tun da yanzu ɗayar abokiyar gabar tata ba ta nan, sai ta mulka gidan san ranta, duk da Ammu Musa ya ce idan an yi arba'in za'a raba gado, don akwai dukiyar Mishal da Abubakar ɗin ya ba shi riƙo.
Wutar da take ganin ta hura sai ta dawo kanta,sakamakon mantawa da ta yi ba ta janye hannunta daga saman wutar a sanda ta tittila fetirin ba, Zama da Jadda?, tashin hankali kenan.
_____________________
_Wayyo Allah cikina!🤣🤣_
_Kai jama'a, wai aka ce idan za ka haƙa ramin mugunta, ka gina shi gajere, kuma an ce mugunta sayin faƙo, idan baka iya ba ka ɓata jikinka_
_Ga Uchechi a kan layi..._
_Wani ya faɗamin abun da zai faru a aanda Uchechi ta san cewa Raja ya faɗa soyyaya da wata_
_Sannan ga kuma Jadda a nata ɓangaren, da alama ita ma za'a fafata da ita_
_Ga kuma Uncle Kuliya a gefe, kada fa kumanta da ya ga Rabi'a, wani ya faɗa min meke shirin faruwa..._
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*12*
~~~
_-*I think the most beautiful thing you could ever experienced is finding someone who wants your all, even if your all is a mess*-_
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
“Wannan shi ne file ɗin next assignment ɗinka!...”
Cewar Chidera, a sa'ilin da yake miƙa masa file ɗin aikin da ya kamata a ce ya aiwatar a gaba.
A karo na farko tun bayan fara aikinsa, Kuliya ya ji wani abu me kama da tsoro ya kama shi a kan aikin, tun da yake bai taɓa ja da baya a kan ko wani aikin da ya sa ƙafa ba, bai san tsoro ko koma ba ya kan aikinsa ba, amma a yau sai ga shi ya na jin ɗar-ɗar na karɓarsa sabon assignment. A da shi da kansa yake neman assignment ko ba'a ba shi ba, ko ya karɓi na wani ya ƙarsa, amma a yau sai ya ke jin kamar ba zai iya ba, kuma tsoron da yake ba na komai ba ne, sai na gudun kada wani abu ya zo ya faru da makusantansa.
A da sam ba shi da kalar wannan tsoron, ko da rayuwarsa zai salwantar zai a kan aiki sai ya karɓa, bai damu da kowa ba dan ba shi da kowan da ya wuce Anna, tun da ya mallaki hankalinsa be san ya raɗaɗin zafin rasa makusanci yake ba, sai bayan da Abubakar ya mutu ta dalilinsa.
Kamar me shirin karɓar zunubansa haka ya kai hannu ya karɓi file ɗin, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga sannan ya kalli Chideran da ya fara masa bayani a kan aikin.
“Case ne a kan kisa da kuma fyaɗen da aka ma wata yarinya a Life Camp”
_“Dama na san wata rana dole za ku so ku san waye mahaifinku... A zahirin gaskiya Aliyu da Zaid ban san mahaifinku ba. An gayyace ni zuwa wurin bikin wata ƙawarmu ne.... Kuma a wurin aka zuba min abun gusar da hayyaci a cikin abun shana. Har aka samu wani ya haike min!. Kuma a lokacin ne na samu cikinku!...”_
Kalaman mahaifiyarsu kenan garesu, a ranar da Zaid ya tambayeta labarin mahafinsu, kuma tun bayan lokacin ya tsani wannan kalmar ta fyaɗe, a duk sanda zai jita, sai ya ji kamar an watsa masa maɗaci a kan zuciyarsa, ko da wasa ba ya son sauraron kalmar.
Don shi ko aiki aka ba shi wanda ya danganci fyaɗe hukuncin da yakewa me laifin ma da ban ne. A hankali ya gyaɗa kansa ya ba buɗe file ɗin.
*
Sharon, Kamis, Sani, Mubarak da Symon su ne zaune kan kujeru, yayin da suka kasa kunne suna sauraronsa.
“...Gaba ɗaya akwai tarin bayanai game da kisan, akwai hujjojin da 'yan sanda suka samo a wurin da aka yi kisan. Na farko, wuƙar da aka yi amfani da ita wurin kisan. Wuƙar na ɗauke da jinin victim ɗin, sannan akwai shatin yatsun me lefin a jiki. Hujja ta biyu kuma ita ce; autopsy report, bayanan da likitan da ya bincika gawar ya bayar sune; farko sai da aka mata...”
Kamar kullum, yau ma sai da ya tauna maganar kafin ya faɗeta, kallonsu ya yi gaba ɗaya, amma su ba shi suke kallo ba, ko wanne a cikinsu da takardar da yake dubawa, wadda ta ƙunshi bayanan case ɗin, hakan ya ba shi damar yin gyaran murya, ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.
“...Fyaɗe, kafin ya kasheta, kamar yanda na faɗa muku tun farko, ya yi amfani da wuƙa ne wurin yanka wuyanta, sannan kuma rahoton ya bayyana cewa makashin ba hagume ne, ma'ana yana amfani da hannun hagu!”
“Amma ni sai nake ganin... Kamar waɗanan hujjojjin ba su isa susa mu gano wanda ake zargi ba, muna buƙatar ƙarin wasu hujjojjin”
Cewar Sani, bayan da Kuliyan ya gam zayyano musu kaf bayanan cikin file ɗin. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa ya na kurɓar coffen dake hannunsa.
“Kai ma ka ce wani abu”
“So what are we gonna do next?”
Sharon ta tambaya.
“Zan yi magan da Ram, sannan zan yi magan da ɗansandan da ya kula da case ɗin kafin ya zo nan, na san za'a iya samun wasu bayanan”
Kuliya ya bata amsa.
“Amma ya kamata mu yi magana da iyayen yarinyar” Cewar Kamis yana aje takardar hannunsa.
“Ƙwarai wannan ma babbar makamace, wata ƙila za su iya bamu wani hint”
“But babu wani wanda zargi ya hau kansa?, i mean ko da ɗaya daga cikin mutanen gidansu ita yarinyar ne?”
Cewar Symon.
“A bayanan cikin file ɗin dai babu, amma idan muka nitsa cikin binciken ba za mu rasa ba”
Kuliya ya amsa masa yana sosa kansa.
“Gaskiya makashin nan ba shi da imani, kalli yanda aka yanka wuyan yarinyar, kuma a profile ɗin yarinyar na ga ba ta wuci 18 years ba” Cewar Mubarak, sanda yake kallon hotunan da aka wa gawar.
Sai da Kuliya ya ɗan yi jim, tunowa da ita da ya yi, ita ɗin da a yanzu zai iya kira da matarsa, ita ɗin da zai iya cewa zuciyarsa ta raurawa a kanta, ita ɗin da ta zama sanadiyyar haɗuwarsa da wata wanda yake ganin kamar ta jiɓanci rayuwarsa ta baya.
Haka dai suka yi ta tattaunawa a kan case ɗin, kafin kowa ya tashi ya fita, ya rage daga Kuliya sai Sharon, wadda suke ƙara tattaunawa kan yanda za su ɓullowa batun.
“Ya kwanan amarya?”
Sharon ɗin ta faɗi tana harhaɗa kan papers ɗin da suka barbaza, sai da Kuliya ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da.
“Tana lafiya”
Sharon ta ɗan yi murmushi tana rufe file ɗin dabta gama haɗawa.
“Na san yarinyar, ba ta da wasu shekaru masu yawa, na san ba lalle ma a ce tasan menene ɗaukar nauyin miji da na gida ba... Amma idan ka daure, ka yi haƙuri komai zai zo maka da sauƙi, ka yi ta ɗorata a kan hanya, za ta dawo dai-dai. hmmm?”
Sai ya aje mug ɗin hannunsa ya na gyaɗa mata kai, kaf abokansa ita ce mutum ta biyu da yake iya sauraron maganarta.
“Thanks for the advice”
“Not at all”
Ta faɗi da wani guntun murmushi a kan fuskarta, ta haɗa abin da za ta haɗa ta fice daga office ɗin.
Kuliya ya shafo kansa yana fitar da iska daga bakisa. Da alama wannan assignment ɗin zafin kai kawai zai ƙara masa, bayan wani ɗumin da kan nasa ya ɗauka.
*Unguwar Madalla, Suleja, Niger state*
RABI'A POV.
“To yanzu Rabi gurin wa zan tura su?”
Cewar Antu Saratu, bayan da saurayinta Fu'ad ya zo zance ya shaida mata da ya kamata ta sa masa ranar da zai turo magabatansa. Yayin da suke zaune ne a ɗakinsu, kan katifar Anti Saratun.
Rabi ta ɗan yi shiru tana nazari, can kuma tace.
“To me zai hana ki turasu wurin kawu Habu, ki ga shi ne kawai wanda za'a iya nemar aurenki a wurinsa”
“Kuma fa haka ne, kai amma na ji daɗin shawarar nan taki Rabi... Sam ni tunanin hakan bai zo cikin raina ba”
Rabi ta ɗan yi murmushi. Ta na so ta ga an yi wannan auren, ko ita ba ta fita daga rayuwar ƙuncin gidansu ba, wata ƙila ita anti saratun za ta fita daga rayuwar ƙuncin gudan.
Kusan sati biyu kenan da tafiyar Mama, duk wanda ya tambayesu ina Mama sai Habiba ta yi wuff ta ce wai ta tafi ziyara.
Hira suka ɗan yi kafin Rabi'an ta fara jin bacci, hakan yasa ta yiwa Anti Saratu sallama ta koma kan tata katifar ta shimfiɗe, sai dai kafin ta gama addu'ar baccin da ta saba yi, waɗanan fuskokin guda biyu masu kama da tata da kuma ta Umma suka gifta ta cikin idonta.
Hakan yasa ta buɗe idon nata, tana shafa addu'ar da ta ida, ba ta san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce mata ba, tunawa da ta yi da shi, wannan innocent voice ɗin, waɗanan drunken eyes ɗin, wannan nitsataiyar tafiyar da ma yanda yake ɗaga kafaɗarsa bayan shuɗewar duk wani ƙaramin lokaci.
Wai me kike shirin yi ne Rabi?, kar fa ki zarme da yawa, don ya na kama da ke ya sa kar ya sa ki dauka cewar shi sa'an ki ne!, Raj sam ba sa'an ki ba ne, kamar da kuke ba ita za ta sa ku dace ba, dacewa da ban kamanni ma da ban!. Yayan da kika samu shi ne dai-dai ke, kar kuma ki shiga shirin ɓallowa kanki ruwa!.
Wani yanki na zuciyarta ya ba ta wannan shawarar, kuma ta yarda da shi ɗari bisa ɗari, don da alama zuciyar tata na shirin sakata ɗaukar dala ba gammo, don kuwa sam babu haɗin zuma da maɗaci, Raja ba sa'anta ba ne ita ma ta sani. Saboda haka duk wani abu da za ta bari ya shiga tsakaninsu yaudarar kanta za ta yi.
RAJA POV.
Cike da mamaki suke kallon ire-iren muggan makaman da mutumin da Alhaji Bala ya haɗusu da shi ya turo musu wai su zaɓi wanda suke so, daga Raja har Rhoda babu wanda bai saba riƙe makami ba, amma kalar waɗanan makaman ko jami'an tsaron Nigeria ba su da irinsu.
“Zaid this thing is getting worst!”
Rhoda ta faɗi, mamaki kwance a kan fuskarta.
Raja be iya amsa mata ba, kansa kawai yake girgiza wa. Mamakin abun da yake gani ya hana shi cewa komai.
“Raja we have to do something about this”
Yanzunma kansa ya girgiza mata yana ɗaga kafaɗa, shi ji yake kamar an sakawa bak8nsa wani shirgegen kwaɗo an kulle.
Lalle Alhaji Bala ya wuce yanda suke tsammani, abun nasa ma ya wuce hankali, ko da wasa ba su taɓa tunanin cewa ya kai haka ƙarfi a harkar tasa ba.
Kallon hotunan kawai yake yana ƙarawa, ya rasa wanne daga cikin hotunan zai nazarta.
Ture ko wani tunani ya yi, dan yasan zuwa yanzu lokacin tashinsu ya kusa, hakan ta sa ya rufe laptop ɗin, dan ba ya so ko da wasa ya yi missing ganinta.
Rhoda ta bi shi da kallo a sanda ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa.
“Wait for me Abeg”
Rhodan ta faɗi tana miƙewa, tare da bin bayansa, dan so take ta je ta yi neman tsokanar da ta saba.
*Brickhall school, Kaura District, Abuja.*
MISHAL POV.
A karo na barkatai, Rabi'a ta kuma ɗaga jerseyn da Mishal ta kawo mata, ta juya rigar a hannunta ya fi sau abun da ya fi.
Yau gaba ɗaya ba su haɗu ba sai yanzu, kasancewar yau ita Rabin har ɓangaren hostel ɗin mata ta je yin shara, kasantuwar makarantar a haɗe take da boding. Wadda ta saba yi ma 'yan hostel ɗin shara ce ba ta nan, hakan yasa aka turata ta je ta yi.
Kuma ta na gama sharar hostel ɗin ta ɗora da ta makarantar, hakan ta sa ba su haɗu ba sai yanzu da aka tashi, ba wai iyaka jerseyn ta kawo mata ba, akwai wani baƙin baby hijab, da leggins, da kuma short ɗin jersyn, sai wani farin canvas.
Mishal ɗin ta faɗawa Rabi'a cewa Akinta ne ya siya mata mata kayan saboda da farko cewa ta yi ɓangaren ball za ta zaɓa a sport, amma bayan ta ga cewa ana koyar da kungu fu a makarantar sai ta sauya ra'ayi, hakan yasa ta aje kayan, yanzu kuma da ta ji cewar yayarta na son buga ball sai ta kawo mata su.
“Ki na ji ko?, gobe ki saka su, ina san na ga irin wasan da kike”
Cewar Mishal tana zuge zip ɗin jakarta, Rabi ta kalleta da mamaki.
“Na sa kuma?, da wa zan buga ball ɗin?”
Mishal ta yi dariya tana saɓa backpack ɗinta a baya.
“Akwai matan da suke buga ball a makarantar nan... Da su nake so ku buga”
Ido waje Rabi take duban Mishal.
“Ni zan buga wasa da su?”
Ta tambaya tana hango waɗanan marasa mutuncin 'yan matan dake yawan buga ball a filin.
“Seesee kin iya ball ko ba ki iya ba?”
Mishal ta tambaya. Rabi'a ta sunkuyar da kanta tana faɗin.
“Na faɗa miki cewar I can't recall when last na buga ball, amma na san na iya, kuma a yanzu ma zan iya buga ball”
“To me yasa kike jin tsoro?, na san tsoron su Precious kike, kisa a ranki cewar su ba su isa komai ba, kuna na san cewa kina ganin saboda ke ba 'yar makaranta ba ce shi ya sa ba za ki iya bugawa da su ba, ki barni da wannan, nasan yanda zan yi da su”
Rabi'a ta ci gaba da kallonta, kafin ta rungume ƙanwar tata da take jinta kamar ƙanwarta ta jini.
“Na gode sosai ƙanwata”
“Don't mention it Seesee”
Daga haka suka yi sallama, Rabi'a ta fita daga makarantar, kasancewar har zuwa lokacin Kuliya be zo ɗaukan Mishal ba, ya sa ta samu bencin me gadin makarnatar taeu ta zauna kusa da shi, za ta iya cewa for the very first ita ce yau ke jiran a zo a ɗauketa, kullum kafin ta fito Malam Ali ya riga ya zo, shi ma Kuliyan ya mata hakan na kwana ukun da suka wuce, amma yau sai ga shi ya makara.
Kamar yanda aka saba Rabi'a na fita ta haɗu da shi, to yau ba ma shi kaɗai ba ne, ya na tare da Rhoda, wadda zuwa yanzu suka ɗinke ita da Rabi'a, don sosai suke hira idan sun haɗu.
“Menene wannan Ammata?”
Raja ya tambaya a sanda suka jera su ukun suna tafiya, Rabi ta kalli ledar hannunta da yake magana a kai.
“Jersyna ce a ciki”
“Kin iya ball ne?”
Rhoda ta tambaya ido waje, Rabi ta gyaɗa mata kai.
“Wow?, da ma a arewa akwai matan da suka iya ball?”
Raja ya ranƙwashi kanta, ta yi sauri ta dafe tana sosa wurin.
“Me kika mayar da matan arewan ne?, ko da yake ai ke ma a arewan aka haifeki, don haka ba ki isa kin ce wani abu a kansu ba”
“To ai ban ce komai ba... Kawai dai ina mamakin abun ne”
“Wannan kuma ke kika jiyo”
Rabi ta yi dariya kamar yanda ta saba musu idan suna faɗa irin haka.
“Wani club kike?”
Raja ya tambaya.
“Bacerlona”
“Aaa!, ki ce ke tamu ce, mu 'yan PSG ne (Paris Saint Germain)” Cewar Rhoda.
Daga haka kuma sai hirar tasu ta koma ta ball, har suka iso bakin titi hirar ba ta ƙare ba, sosai Raja ya yi mamaki jin yanda Rabi'an tasan abubuwa da dama game da ball, kuma ya yi mamakin jin yanda tace musu ta na son buga ball, dama ce kawai ba ta samu ba. Su suka tsaida mata mota ta shiga, sannan suka juyo,suna tafe suna 'yar hira.
Kamar daga sama suka ji wata murya na faɗin.
“Hello!”
Hakan yasa suka kalli inda sautin muryar ya fito. Wata yarinya ce tsaye a gabansu, sanye cikin uniform ɗin makarantar Brickhall, a ƙiyasin shekaru ba za ta wuce 17 ba.
“Hy”
Rhoda ta amsa mata, yayin da idanuwan Raja ke kallonta ƙasa-ƙasa.
“Ko zan iya sanin sunanka Bro?”
Mamaki ya kama Raja, to me za ta yi da sunansa?, tukunna ma waye ce ita?.
“No, kada ka damu fa, ni ba 'yar yankan kai ba ce...”
Maganar tata ta bawa Raja dariya, hakan yasa suka murmusa a tareshi da Rhoda, ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.
“Sunana Raja, ke kuma fa?”
“I'm Mishal”
Mishal ta faɗi tana gyara zaman jakarta dake goye a bayanta.
“Me yasa kike son sanin sunana?”
Sai kuma ta yi shiru, da ma gajiya ta yi da jiran zuwan Kuliya, hakan yasa kawai ta fito ta fara tafiya da ƙafarta, kuma a kan hanyar ta ci karo da wannan me kama da Kuliyan, shi ne ta tsaya don ta samu ta masa magana, wata ƙila za ta tabbatarwa da kanta abun da take san sani.
“Akwai wani yaya na da yake min kama da kai that's all”
Ta zaɓi da ta masa wannan ƙaryar, don a ganinta wata ƙila ita za ta fi bada ma'ana, saboda babu yanda za'a yi ta faɗa musu cewar da mijinta yake kama, don ba ma lalle su yardar da cewar ita ɗin matar aure ba ce, to taya ma za'ayi su yarda?.
Ba ƙaramin duka maganarta ta yi wa Raja ba, wai meke shirin faruwa da shi ne?, farko Rabi'a, yanzu kuma wannan yarinyar na faɗa masa cewar akwai wani ɗan uwanta me kama da shi, sai dai kuma shi yasan basu da wasu 'yan uwa na kusa. Da ace ma Rabi'a ce za ta faɗi

Please Login or Register in order to submit comment